Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tare da cewa.
"Karka damu a sake na ke ban takura ba, kasan ai ko wani ɗan adam komai gatansa ƙarshen mutuwa ce, yaje yayi rayuwa a ƙarƙashin ƙasa inda ba tabarma bare filo, ina tunawa da wannan kullum shiyasa bana jin wata damuwa dangane da zamana a nan Malam Dpo."
"Hakane kayi daban da ɗan uwanka, kai mutumin kirki ne."
"Ɗan uwana ma mutumin kirki ne fahimtar sa ne kawai bakuyi ba, jeka kai tsaye kan abinda ya shigo da kai nan ka ijiye maganar ɗan uwana a gefe."
"Hmmm! Okay we'll, Meyasa ka aikatawa yarinya fyaɗe shin baka san illar hakan bane laifi ne da zai iya kaika kurkuku na tsawon shekaru.?"
Dariya Nameer yayi tare da cewa.
"Bansan wannan maganar ba, wataƙila wani mai suna Nameer ɗin kuke nema amma wannan Nameer ɗin yasan darajar mace ba zai aikata abinda kuke zarginsa dashi ba meye hujjar ku daya tabbatar cewa ni ne mai laifin.?"
"Ba'a yiwa Police tambaya cikin tambaya Malam Nameer, ka bani amsar tambayata."
"Hmmm! Ikon Allah na amsa maka tambayarka kafin jefo tawa tambayar ko a ruɗe kake ne, Malam Dpo kasancewata anan bashi zai baka damar min tsawa ba, karka manta halacci."
"Hakane bazan manta halacci ba, sai a bangaren bawa ƙasata gudummawa to bazan ɗagawa kowa ƙafa ba, har yanzu bamu gama tabbatar da hujja akanka ba shiyasa ma muka ijiyeka cikin kulawa babu horo."
"Okay kuje ku cigaba da binciken idan har kun tabbatar ni ne criminal ɗin is okay ku karya ƙasussuwana karku raga min sai dai fa Malam Dpo idan ya tabbata Nameer bashi da laifi ɗan uwana bazai taɓa ɗaga muku ƙafa ba sai dai idan ni ne na dakatar dashi."
Nameer yayi Maganar yana sakin murmushi shima Dpo murmushin yayi kafin yace.
"Shikenan hakanma yamin."
Shima yayi Maganar yana tashi ya fice daga cell ɗin Sargent Dogo yazo ya kulle.




************



Tun daga get ɗin gidan ake bawa Mamabisola girmamawa har ta iso get ɗin da zai sadata da part ɗin Iyabo, kallon Wamimo tayi tace.
"Munzo ki nutsu domin muna bukatar makamin da zamu kuma hurawa Case ɗin wuta kin fahimta.?"
"Na fahimta kuma zan baki mamaki."
Murmushi tayi sannan suka shige part ɗin, sallama sukayi Ummi dake zaune tayi tagumi tana share hawaye jefi jefi Abba na gefenta shima yayi shuru Ummi ta amsa sallamar ƙarisowa sukayi Abba na ganin Mamabisola ya miƙe cikin girmamawa.
"Mama sannu da zuwa."
Ummi tayi Maganar tana zamewa ƙasa ta zauna kasancewar al'adar su ce idan babba na zaune a sama su suyi ƙasa, murmushi Abba yayi tare da zama gefen ƙafar Mamabisola cikin girmamawa yace.
"Sannu da zuwa Mama kece tafe ai da kirana kikayi nazo da baki wahala wajen zuwa ba."
"Babu komai Iyabo, zuwan ai dole ta kama yanzu ina zaune nake jin maganar da ta ɗaga min hankali shiyasa nace banci ta zama ba, dole nazo naji gaskiyar zancen, wai yaron nan da kake riko yayi laifin fyaɗe an kamasa.?"
Numfashi Abba ya saki tare da jin ƙunar rai wato ma har maganar ta fara zagayawa gari kansa ya girgiza tare da cewa.
"Ehh Mama da gaske yana hannun hukuma sai dai NAMEER bazai aikata wannan laifin ba, ina tunanin sharri ne kawai amma insha za'a san yadda za'ayi a wankesa mai gaskiya baya taɓa faɗuwa ƙasa Mama."
"Hmm ni kaina nayi mamaki ace yaro mai hankali da nutsuwa ya aikata wannan mungun aikin, to Allah ya fidda sa, amma dai.........
Sallamar Hisham itace ta dakatar dasu daga maganar, shi kansa bai kula da Mamabisola ba sai da ya shigo tsakiyar falon Sannan ya ganta idanunsa ya runtse muryar sa a dakile ya risina tare da cewa.
"Ina yinin ku."
"Da bami wuni ba zaka ganmu dan ƙwal ubanka, dama ai nace zamu haɗu ne komai daɗewa, idan arziki bai haɗamu ba tsiya ta haɗa mu, wato shine Tunde zaije Company neman aiki kasa a koresa kamar kare kai ga isasshe mai gadara da Companyn ubanka ko? Tunde dai ɗan uwanka ne babu abinda zai goge hakan ka fifita bare sama dashi, ina magana kana wani haɗe fuska kamar wanda na kashe maka uwa, to bara kaji wallahi ka gyara wannan shegen baƙin halin naka."
Ransa Hisham ya haɗa tare da kawar da kansa gefe yaƙi tanka mata ganin yayi shuru ne Mamabisola ta cigaba da cewa.
"Ina magana kamin shuru ka maisheni mahaukaciya."
Miƙewa Hisham yayi tare da cewa.
"Bani da amsar da zan tanka miki, ƙorafin da kika kawo wajen Abban bai isa ba sai kin biyoni har gida Tunde bai cancanci zama ɗaya daga cikin ma'aikatan mu ba, saboda mu muna ɗaukar masu ƙwazo ne da hazaƙa kuma masu riƙon amana Tunde bashi da ɗaya a cikin wadannan idan kin manta bara na tuna miki, Tunde sata yayi a Companyn da ya baro na makudan kudade, dan haka bama bukatar barawo a Companyn mu."
Yayi Maganar cikin izza tare da saka kai yabar wajen, Mamabisola wani irin ɓacin rai taji wanda ya sanya har tayi danasanin zuwa domin kuwa da tasan zatazo HISHAM ya faɗa mata magana tabbas da batazo ba, Abba ne ya nisa tare da cewa.
"Kiyi haƙuri Mama jikan naki ne na rasa yaya zanyi da zafin kansa kullum cikin faɗa nake masa amma tamkar wanda nake ƙara tunzura sa, kiyi haƙuri dan Allah, mun gama magana da Nameer cewa Monday za'a ɗauki Tunde a Company, to sai wannan jarabawar ta shigo amma insha Allah idan komai ya daidaita Tunde zai kawo takaddunsa a basa aiki a gurbin da ya kamata kiyi haƙuri dan Allah Mama."
''Hmm! Ba komai Iyabo ni kaina nasan halin Hisham, karka damu yanzu a wacce matsaya ake wani ƙoƙari kake wajen ganin yaron nan Nameer ya kubuta."?
"Ehh gaskiya har yanzu banyi wani yunkuri ba domin kuwa bani da ƙwarin gwiwwar da zan fara tunkarar matsalar Saboda Case ne mai girman gaske, amma insha nasan dole Hisham zai samo evidence da zamu iya kare sa, insha Allah zuwa anjuma zan kirasa sai muji abinda ya samo insha Allah duk abinda ake ciki zan sanar dake."
"Duk dai yadda za'ayi ka tabbatar ya kubuta domin kuwa yaron kirki ne mai amana, sannan karka yanke hukunci ba tare da ka sanar min ba."
Murmushi Abba yayi tare da cewa.
"INSHA ALLAH babu abinda zanyi ba tare da saninki ba kece uwata a yanzu ya zamo wajibi nabi umarnin ki."
"Hakane Iyabo shiyasa nake alfahari da kai domin kuwa kaine gatana a yanzu, sannan ka jawa Hisham kunne ya kiyayi faɗa min duk maganar da tazo bakinsa sannan ka tambayesa wani irin laifi muka aikata masa daya tsanemu haka, mu zamu koma."
Kafin Abba yayi Magana Ummi tace.
"Babu abinda kuka masa Mama kawai tsiya ce irin tasa insha Allah zan masa magana bazai kuma mayar miki da martani ba kiyi haƙuri."
Bakinta Mamabisola ta taɓe tare da cewa.
"Nayi hakuri Hmm! Ramata ina da yaƙinin cewa kece kike kitsawa Hisham duk abinda yake min domin kuwa kema ba ƙaunar uban Tunde kike ba ko an faɗa miki ban gane take takenki ba ne."
Ɗan zaro idanunta Ummi tayi zatayi Magana Abba yayi saurin katseta tare da cewa.
"Karkice komai ki shige sama."
Kanta Ummi ta kaɗa tare da bin umarnin Abba ta haura kafin ya dubi Mamabisola da Wamimo da ta nutsu tana sauraren su ya cigaba da cewa.
"INSHA ALLAH za'a masa faɗa muje sai drever ya sauƙeku."
Kanta ta girgiza tare da yin gaba Abba yabi bayansu.




**********
Misalin goma da rabi na dare Jidda ta yi shiru a ɗaki tana nazarin maganganun HISHAM duk da bata jin zai iya aikata abinda yake faɗa mata, amma zuciyar sa ta girgiza da maganar sa sosai tana son ahalinta fiye da komai a rayuwarta bata jin zata iya jurewa ganinsu cikin tashin hankali, numfashi ta saki tare da ɗaukar wayarta ta kira Aisha ringing ɗaya Aisha ta ɗaga.
"Kina asibitin ne."
Daga can Aisha tace.
"A'a na dawo gida tun ɗazu, saboda ƙanwar mahaifiyar Hajara tazo shiyasa na taho."
"Okay kina da numbern nasu ne ina son zanyi magana da ita hajaran ne."?
"Kai gaskiya Aunty Jidda babu numbern nasu nan domin kuwa banyi seving ba, nima ina son kiransu naji ya jikin nata na duba wajen calling banga numbern ba, amma dai tahota jikinta da sauƙi sosai harma ta zaga harabar Asibitin."
"Okay to shikenan ba damuwa da safe naje asibitin mun gode da ƙoƙari Aisha Allah ya biyaki ki gaishe da Ikko da Ahmad."
"Zasuji na gode Aunty Jidda sai da safe."
Aisha tayi Maganar tana katse kiran.
Numfashi Jidda ta saki tare da saka kanta ta kwanta ganin dare yayi har 10:30pm.
Sai dai me bacci ya gagari idanunta tunani da tsoro duk ya cika mata zuciya tana son ahalinta fiye da komai a rayuwarta su kuma ya'yan masu kuɗin nan ba imani garesu ba su tozarta talaka ba abun mamaki bane, numfashi ta saki tare da tashi ta ɗauro alwala ta hau sallah.


Washegari da safe bayan sunyi karin kumallo ne Umma ta dubi Jidda tare da cewa.
"Jiddatul kair."
"Na'am Ummana."
"Jidda dan Allah na roƙeki ki cire hannunki cikin wannan Case ɗin fyaɗen dan Allah na roƙeki a matsayina ta mahaifiyarki, ki barmu mu zauna lafiya, ina da hawan jini ga suger, bana bukatar tashin hankali, har yau ciwon baƙin cikin mahaifin Abdullahi bai wankewa zuciyata ba, ki barni dashi ma kaɗai ya isheni."
"Kanta Jidda ta girgiza tare da cewa.
"Shikenan Umma insha Allah na cire hannuna zanje na janye ƙarar farin cikin ku yafi min komai a rayuwata."
Tayi Maganar cikin sanyin jiki cikin zuciyarta ta fara saka, ita da take da niyyar zuwa asibitin taga yadda hajaran ta kwana sannan ta biya Police station ɗin taji ya ake ciki, amma gashi Umma na ƙoƙarin dakatar da ita, amma koma yaya ne bazan bar wannan Case ya tafi a banza ba, tayi Maganar zucin tana sakin ijiyar zuciya Umma ne tace.
"Shikenan jiddatul kair Allah ya miki albarka, yau zaki fita ne ko zamu a gidane."?
"Ehh Umma zan fita yanzu zanje gidan su Basmah na bata haƙuri jiya ta tafi cikin fushi akan wannan case ɗin."
"Hakan yana da kyau Basmah masoyiyarki ce ta haƙiƙa, idan kinje kya gaishe da babarta ta ko."
"Insha Allah zataji Umma bara na ɗauki hijabi na na tafi."
Da adawo lafiya Umma ta mata kafin Jidda ta miƙe ta shiga ciki ta ɗauki hijabinta ta fita, ko da ta fito ABDULWASI'U yana tsaye ƙofar gidan su da niyyar aikawa tazo tsayawa tayi tana dubansa kafin tayi Magana yace.
"Dama jira nake Abdu ya fito na aikesa yamin kiranki."
"Okay sai kuma gashi na fito meke faruwa.?"
Murmushi ABDULWASI'U yayi kafin yace.
"Kamar kuma naga sauri kike ai."
Cike da fara gajiya da maganganun sa tace.
"Eh idan ba damuwa zan iya tafiya idan na dawo na saurari abinda kake da niyyar faɗa ko."
Tayi Maganar tana saka kai tabarsa tsaye kansa ABDULWASI'U ya girgiza ya rasa meyasa Jidda bata ƙaunarsa duk da kyautatawa da biyayyar da yake yiwa iyayenta, numfashi ya saki ya koma bakin shagonsa.

Jidda kanta tsaye mai adaidaita ta tare tace masa IBUNKU OLU CLINIC zai kaita can ta nufa, ta shiga mai adaidaitan yaja suka nufi hospital ɗin, bayan ya Kaita ne ta basa kuɗinsa 200 naira kafin ta shiga cikin asibitin darect ɗakin da Hajara take Jidda ta nufa domin kuwa tun jiya hankalinta yaƙi kwanciya ji take tamkar wani abun zai faru da Hajara maganganun HISHAM sun tayar mata da hankali tanajin zai iya komai domin ganin ya kuɓutar da wannan azzalumin ɗan uwan nasa, a tsaye taga wasu mata su biyu wanda bata sansu ba cikin tashin hankali gadon da Hajara ke kwance ta kalla wayam babu kowa cikin sauri tace.
"Waye ku ina Hajara wacce take kwance a gadon nan jiya, an sallameta ne."?
Ɗaya daga cikin matan ne ta kalli jidda tare da cewa.
"Mu ƙannen mahaifiyar Hajara ne, ba sallamar mu akayi ba, Hajara aka nema aka rasa tun jiya cikin dare anyi nema anyin nema kaf cikin asibitin nan da unguwar nan har gida an kira da sauran ƴan uwanmu amma Hajara bata nan hankalin mu yana tashe bamu san ina Hajara take ba."
Dafe kanta Jidda tayi tare da furta kalmar innalillahi wa'inna ilaihirraji'un.
"What ba'aga Hajara ba to ina ta shiga karfa a saceta innalillahi wa'inna ilaihirraji'un."







______________________________________




*Ina kallon SHARHINKU my fan's ina jin daɗin hakan sosai Allah yabar ƙauna.*



*Aunty Fauziya Auwal ƴar mutan jingau na gode sosai da kulawar ki Allah yabar zumunci Allah ya baki isasshen lafiya ya raya miki zuri'arki bisa tafarkin Manzon rahama.*




Share and comment my fan's.




*UMMU NASMAH CE✍🏻*





*For more information 08147537180*
[5/15, 7:22 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*



*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*





*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻





*_PAGE 5_*



Ƙanwar mahaifiyar Hajaran ne wacce suke kira da Baba jummai tace
"Ba'a ganta ba, mun rasa ya zamuyi tun daren jiya muke nan cikin tashin hankali abun kamar almara."
Numfashi Jidda ta saki tare da cije bakinta cikin zuciyarta take saƙa cewa.
(To waye zai sace Hajara garin yaya za'ace da bakinta da hankalinta an sace ta anya kuwa wannan abinda zai yiwu ne, to amma idan da gaske saceta akayi garin yaya hakan ta faru? ko dai Hisham ne, kai ina bazai yiwu ba babu ta yadda Hisham zai iya saceta a cikin wannan asibitin dole yasan idan aka nemeta aka rasa su za'a zarga, to amma fa hatsabibi ne Hisham zai iya aikatawa ta wata fuskar domin ba imani garesa ba, sai dai kuma ba Teddy bace ita bare ya saceta cikin sauƙi, Hmm! Lallai akwai lauje cikin naɗi, bai zamo lallai ace Hisham bane saboda dole yasan su za'a zarga, kai zaima fa iya aikata sacetan yadda yake jin kansa tamkar sarki.)
Tayi Maganar zucin tana sakin numfashi kafin ta dubi Wacce tayi Maganar tace.
"To amma garin yaya kuna tare da ita cikin room daya har a ɗauketa baku sani ba, sannan abun mamakin ma ta yaya akayi bakuji motsinta ba a matsayin ku na majiyantan ta dole dai idan har tasan saceta za'ayi tayi ƙoƙarin kururuwa, gaskiya kunyi sakaci.?"
Baba larai ce wacce suke tare da Baba jummai tace.
"Ba sakaci mukayi ba, ƴar nan Saboda cikin dare ma misalin 3:00pm na farka har na bata ruwa tasha, tashin mu sallar asuba muka nemeta muka rasa munyi tunanin ko gida ta koma muka kira ummanta muka tambayeta tace batazo ba muka duba cikin asibitin nan gaba ɗaya babu ita hakanne ya sa hankalinmu ya tashi kaf cikin dangi da abokan arziki da aka san zata iya zuwa an tambaya amma bataje can ba tabbas sace ta akayi, maganar bacci kuma shi bacci ai ɓarawo ne bamu da laifi."
"Hmmm! To an sanar da Police station ne sannan ina shi doctor dake kula da ita, sannan ina mahaifiyarta.?"
Jidda tayi tambayar cikin sanyin jiki, Baba larai ne ta kuma magana.
"Doctor ya je station zai sanar da abinda ya faru yanzu ma haka suna can tare da Mahaifiyar Hajaran."
"Okay wani statin ɗin ne.?"
"Wanda dai kika kai ƙarar wadanda suka yi ƙoƙarin mata fyaɗen can yace mana zaije tun ɗazu muke jiran dawowarsu muma."
"Okay muje station ɗin."
Jidda tayi maganar tana ficewa daga room ɗin bayanta sukabi kafin suka tari adaidaita zuwa Police station ɗin.


Ko da isar su Police station ɗin sun sami Mahaifiyar Hajara da doctor zaune gaban Dpo daya fito harabar station ɗin cikin cell ɗin kuwa Nameer ne zaune, Jidda inda Nameer ke kulle ta kalla tare da cewa.
"Dpo wannan ɓatan Hajara akwai lauje cikin naɗi ta yaya za'ace ana wannan case ɗin a nemeta a rasa mutum ce fa ba dabba ba ba kuma mahaukaciya ba, bare ace rashin hankali yasa ta fice, ya kamata a binciki gidan Alhaji Iyabo ina zargin su da sune zasu sace Hajara domin rufe babin wannan Case ɗin."
Murmushi Nameer dake cikin cell ɗin yayi yana tsura mata idanu ko kaɗan baiji zafin maganar ta ba, Dpo ne yace.
"Nima zargin da nake kenan, sai dai koma waye yayi wannan aikin zamu ganosa very soon."
Yayi Maganar yana miƙewa tare da nufar cell ɗin ya dafa ƙarfen ƙofar yana duban Nameer dake zaune yana sauraron su yace.
"Ina kuka kaita domin nasan tana wajenku."?
Murmushi Nameer ya saki tare da cewa.
"Tunda kasan tana wajen mu mai zai hana kaje ka ɗaukota, Abbas Marafa kana zaƙewa da yawa fa ka fara ƙoƙarin fusatar dank dan Allah ka dinga kulawa kana tauna harshen ka wajen min tambaya, ina nan rufe ko kun buɗeni ne, bare naje na saceta."?
Dpo zaiyi Magana Jidda tayi saurin cewa.
"Ba'a buɗeka ba amma abokin cin mushenka yana can yana shawagi kamar tsuntsu, zai iya aikata hakan a madadinka saboda imaninsa yayi ƙaranci, zai iya komai domin ganin ya kuɓutar da kai, ɗan uwanka bashi da imani kamar dai Kai ɗin nan."
"Okay na fahimta Hisham kike nufi ko? let go ku kamasa sai ya muku magana da bakinsa idan shine bazai ɓoye muku ba, ɗan kanfai ne Hisham yana dai-dai da ƙugun kowa, gaskiya kina ƙoƙari wajen shigar da kanki cikin matsalolin da ba naki ba, zakiyi danasani kuma zakiji kunya a duk sanda gaskiya ta bayyana."
Nameer yayi Maganar cikin murmushi, Jidda bakinta ta taɓe ta kuma cewa.
"Wacce gaskiyar zan gani bayan wannan, hmm! Akanku dai bazan taɓa jin kunya ba bare kuma nayi wata danasani, a duniya babu wanda na tsani gani a rayuwata sama da kai da ɗan uwanka kuma tabbas sai kun fuskanci hukunci."
Tayi Maganar a fusace Dpo ne yace.
"Ba damuwa kuna iya tafiya zamuyi bincike kuma zamu samota nan da zuwa awa ashirin da huɗu, kai kuma Nameer zaka gane kuskuren ka."
Kanta Jidda ta girgiza mahaifiyar Hajara ne tace.
"Ranka ya daɗe dan Allah ku rufa min asiri ku nemo min ƴata, ita ɗaya Allah ya bani dan Allah ku rufa asiri bazan iya zure rasata ba."
Jidda ce ta riƙota tana cewa.
"Kiyi haƙuri Mama insha Allah Hajara Zata dawo cikin ƙoshin lafiya ki daina kukan kinji.?"
"Naji Jidda na gode sosai kina ta ƙoƙari akan Hajara tamkar ƴar Uwarki ta jini Allah ya biyaki da mafificin alkairi."
"Ameeen Mama wannan yiwa kaine muje, Baba larai mu tafi ku hau adaidaita ku mayar da Mama gida insha Allah komai zai daidaita ."
Tayi Maganar tana riƙe da ita suka fita tare, DOCTOR shima hannu ya bawa Dpo sukayi musabaha kafin ya tafi.






**********

Abba ne ya dubi Hisham da yake cin abincin tamkar yana cin magani yace.
"Hisham kamin shuru tun ɗazu nake magana ni ɗaya ko baka jina ne?."
Ɗago idanunsa Hisham yayi ya kalli Abba dake riƙe da cup ɗin block tea a hannunsa kafin yace.
"Ina jinka Abba me kakeso na ce maka Abba akan wannan lamarin kace babu ruwanka mu jira gaskiyar Nameer ta fitar dashi, to kuma meye amfanin sanar da kai wani abu, kabar maganar kawai."
"Hisham! Hisham! Tambayar ka fa nake kake min zancen banza munyi magana da commissioner jiya ina son sanin wani evidence kake dashi domin kuwa commissioner yace dole sai anje kotu muna bukatar barrister shiyasa nake son ji daga bakinka domin kuwa zaman Nameer cikin cell yana ɗagawa mahaifiyar ku rai dani kaina."
"Abba na gama tsara komai Nameer zai fito cikin aminci kabar komai kawai a hannuna, sai dai Abba ina bukatar 5million daga gareka ina son buga wasa ne dasu."
Ummi ne ta ture plat ɗin abincin dake gabanta tace.
"Wasa Hisham, 5million ne zaka buga wasa dashi saboda baka da hankali, ka dinga hankali da rayuwa Hisham, baza'a baka waɗannan kuɗaɗen ba, sannan ka tashi muje ka kaini naga yarona Nameer."
Hisham murmushi ya saki yace.
"Ummi kin sani bana wata aba wasa, wannan shine wasa na na farko da zan buga dan haka Abba kai nake saurare."
"Hmmm! Hisham kuɗi ba matsala bane, damuwata yanzu...............
"Nameer ya fito haka zakace."
Ta katse Maganar Abba tana shigowa gabaki ɗayansu juyawa sukayi suka mai da kallonsu kanta, Ummi ce tayi murmushi, shima Hisham murmushin ya saki tare da cewa.
"Aunty Halima kece.?"
"Eh Hisham ni ne."
Tayi Maganar tana zama a daining ɗin tare da cigaba da cewa.
"Yanzu nake samun labarin abinda ke faruwa da NAMEER shiyasa ma na taho cikin gaggawa, ta yaya za'ace da kuɗin mu da ƙimarmu da darajar mu, muna da ƙarfin iko a ƙasar nan gabaki ɗaya harma da tsallakenta, ace Nameer ya kwana a police station, wannan ƙasƙantar da ahalin mune, Hmmm! Yaya ya zamo wajibi muyi amfani da kuɗin mu da ƙarfin ikon mu NAMEER ya fito, kuma duk wanda ya masa wannan ƙazafin na rantse da Allah bazan ƙyalesa ba sai na hukunta sa."
"Hmmm! Yes Aunty Halima magana kikayi mai kyau, Amma Abba shi bazai yarda da haka ba, yafi yarda da gaskiyar ce, Aunty Halima a yanzu bama bukatar kashe ko sisi ko neman alfarmar wani akan case ɗin Nameer na gama komai Nameer zai fito gobe."
"Kamar yaya me kake nufi Hisham."?
Abba yayi Maganar yana ɗan zaro ido.
"Ina nufin Nameer zai Fito gobe, Aunty Halima nasan Ummi bazata bar Abba ya bani 5m ba, amma nasan zan iya samu a gareki."
"Zan baka kuɗin da kake bukata Hisham, zakaji alart, amma ta yaya zaka fitar da Nameer daga cikin wannan haɗarin."?
"Hanya ce mai sauƙi Aunty Halima, kuma na gama samun hanyar, nasan amfani akayi da wannan yarinyar wajen ganin an tozarta mu shiyasa nima nayi amfani da ita wajen ganin na kuɓutar da ahalina, muje

Please Login or Register in order to submit comment