Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hukunta sa, ki faɗa min waye ne."?
Kanta Yarinyar ta girgiza idanunta na kuma zubo da hawaye tace.
"A'a bazan faɗa ba idan na faɗa miki yayi alƙawarin tozarta rayuwata ta yacce zan gwammaci mutuwa fiye da rayuwa, ina tsoro shi ɗan masu ji da mulki ne a ƙasar nan."
Numfashi Jidda ta saki cikin ƙunar rai tace.
"Kalli ƙwayar idanuna ki gani akwai tsoron wani basarake ko mai kuɗi a cikin su, ki kalla da kyau ko akwai rashin amana da ƙwarin gwiwwa a tattare dani, ki kalla da kyau shin zaki iya yarda dani."?
Idanunta Yarinyar ta saka cikin na Jidda ita dai Basmah tana tsaye tana kallon ikon Allah a wajen Jidda.
"Ban hango tsoro ko rashin amana a tattare da ke ba, na yarda da kai sai dai shi ɗin hatsabibi ne zai iya cutar da Rayuwarki kema muddun kikayi ƙoƙarin taimakona."
"Wai shin waye wannan ya tsorata rayuwarki haka na faɗa miki ki yarda dani babu abinda zai samu Rayuwarki sai ma ƴanci da zaki samu muddun kika bani haɗin kai ki faɗa min waye shi sannan kema menene sunanki ya...........
"Jidda wai mey...........
"Ya isa Basmah ki daina katseni ki barni na kai aya, na ce ki faɗa min waye wanda yaso kasheki waye wannan wanda bai san mutuncin mace ba, wani dabban ne ki faɗa min."
Jidda tayi maganar cikin tafasar zuciya, a tsorace cikin rawar baki yarinyar tace. "Na....na......na... Nameer ab..dulzahir, Iyabo masu Companyn *_HISHAM RICE MILL LIMITED_* shi..shi...shi ne yaso yamin fyade NAMEER."
Wani razana Jidda da Basmah sukayi lokaci guda har Aisha sanda Maganar ta soki zuciyarta Basmah ne tace.
"Whatttttt! Ke Nameer Abdulzahir Iyabo kike faɗa, Iyabo dai wanda muka sani shahararren attajirin da babu kamar sa a wannan jihar tamu, shi kike faɗa, capp lallai kam babu yadda zakiyi Jidda muddun Nameer Iyabo ne babu abinda zaki iya a kansa."
Tayi Maganar cikin yanayin mamaki da damuwa domin kuwa zata iya rantsuwa da Allah NAMEER bazai ɗauru ba ba kuma zai kamu ba, murmushi Jidda ta saki na takaici tace.
"Yaruba Man nawawo, oh Rapping, rapping ɗinki zaiyi, Mema sunansa Nameer ko menene.?"
Aisha ce tace.
"Nameer, gaskiya Aunty Basmah ta ke faɗa miki Nameer hukuma ko wata ƙungiya bazasu iya kamasa ba saboda ƙarfin kuɗi da iko na Alhaji Iyabo."
"Ko waye ubansa sai ya kamu domin kuwa case ɗin fyaɗe, dawamammene akan dukkan wanda ya aikata ko yayi ƙoƙarin aikatawa, komai kuɗi da ikon ubansa sai ya tozarta tunda shi ɗan Akuya ne mai dabbar zuciya."



______________________________________



Sai tambaya ta ake Ummu Nasmah littafin Free ne ko na kuɗi muna son zamuyi payment sorry sister Book One Free ne idan kin matsu sai kinyi payment Saboda kunfi bukatar silent group marar hayaniya to Ummu Nasmah tana da special group wanda zakiyi karatu cikin nutsuwa babu yawan posting ko damunku da ture turen abubuwa idan kina buƙata sai min magana 08147537180




*UMMU NASMAH CE✍🏻*











*For more information 08147537180*
[5/12, 7:10 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*



*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*




*Masha Allah JALALA FAN'S son so nake muku fisabilillah ina jin daɗin comments ɗinku*




*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻




*Free Book One*


*_Page 5 to 6_*




"Hmmm! Jidda ki tsaya iyakar matsayin ki, karki jawowa kanki da Mahaifiyar ki rigimar da bazaku iya ɗauka ba, Iyabo ba ƙaramin mutum bane a ƙasar nan ya wuce duk tunaninki daga Nigeria har ƙasashen duniya sunansa ya fantsama, dan haka ki riƙe mutuncin ki ki ƙyale wannan maganar."
Murmushin takaici Jidda ta saki cike da jin haushin maganar Basmah tace.
"Kin bani mamaki Basmah ban taɓa zaton bakya kishi da abinda ya samu mace ƴar Uwar ki ba, idan ƙanwarki aka yiwa haka zakice abar Maganar ne, na tabbata ko da mutuwa zakiyi zakice sai kin ƙwato mata ƴancinta, amma da shike ita wannan ba jininki ba ce shine kike cewa abar Maganar, wallahi bazan bar maganar ba koda zan mutu ta sanadiyyar haka sai na ƙwato mata ƴancinta, sai ya fuskanci hukunci komai gata da ikon ubansa Allah yana tare da mai gaskiya nayi imanin bazai bari na tozarta ba zai kareni, na ɗauki wannan kasadar."
"Hmmm! Jidda kenan yau ni kike faɗawa baƙar magana Saboda kawai na ce miki ki kula, Jidda tunda har kika min kuskuren fahimta a tsawon zamana dake tun yarinta, shekaru ashirin da biyu muna tare ai shekara ashirin da biyu ba kwana ashirin da biyu bane, idan wani yamin abinda kika min yau bazanji haushi ba, sai dai ki sani bazan fasa faɗa miki gaskiya ba saboda ina ƙaunarki bana ƙaunar abinda zai taɓa rayuwarki, amma idan kin zaɓi rayuwa a cikin tsoro da fargaba, bazan iya hanaki tafiyar da rayuwar ki yadda kike so ba amma ki sani bazaki iya faɗa da ahalin Iyabo ba."
Basmah tayi Maganar cikin ɓacin rai tana saka kai tabar room ɗin, yarinyar ce ta share hawayen ta tare da duban Jidda tace.
"Gaskiya take faɗa miki bazaki iya ja dasu ba domin kuwa suna da ƙarfin da bamu da kwatansa, ni na barsu da Allah kema dan Allah kibar maganar bazan yafewa kaina ba muddun wani mummunan abu ya sameki a dalilina."
"Ƙwarai kuwa gaskiya ne Aunty Basmah ta faɗa miki Aunty JIDDA dan Allah mubar wannan maganar mu barsu da Allah shine mai sakayya akan duk wanda aka zalunta dan Allah."
Aisha tayi Maganar cikin sanyin jiki, shuru Jidda tayi kafin zuwa can ta dubi yarinyar tace.
"Meye sunanki.?"
"Hajara." Ta bata amsa a taƙaice.
"Okay ki amshi wayar Aisha ki kira wani daga cikin gidan ku, bara naje na dawo."
Kanta Hajara ta ɗaga kafin Jidda ta tashi ta fice, Basmah ta hau dubawa cikin asibitin babu ita babu alamunta hakanne ya tabbatarwa Jidda Basmah gida ta koma, kanta ta kaɗa tare da ficewa ta tari adaidaita tace ya Kaita police station.
A bakin station ɗin mai adaidaita ya sauketa ta basa kuɗinsa kafin ta shiga ciki, First Dpo taso gani suka ƙi barinta ta gansa, hakanne yasa ta shigar da ƙarar NAMEER ABDULZAHIR IYABO, a tsorace ɗan sandan ya ɗago ya kalleta tare da cewa.
"NAMEER kike tuhuma da Case ɗin fyaɗe? Bazamu amshi Case ɗin nan ba."
Murmushi Jidda ta saki tare da ɗauko id card ɗin ta na aikin jarida ta nuna masa tare da cewa.
"Dama nasan zaiyi wahala ku bari a shigar da ƙara a kansa, sai kamar yadda ka gani a wannan ID CARD ɗin ni ƴar jarida ce wanda mutanen wannan ƙasar suke riƙe jaridar mu a ko wacce rana dan haka muddun baku amshi wannan ƙaran ba to wallahi zakuji mummunan labari akan wannan Police station ɗin naku, yadda ko wannenki sai ya rasa aikinsa."
Tayi Maganar tana ja gefe ta tsaya shuru ɗan sandan yayi a tsorace kafin ya miƙe cikin sanyin jiki ya nufi office ɗin Dpo Abbas Marafa, yayi nocking kafin dpo ya basa umarnin shiga, shiga yayi tare da sara masa.
"Sargent Bala ya akayi."?
"Sir wata matsala ce take shirin faruwa."
"Matsala kuma Sargent Bala, ta mecece."?
"Wata ƴar jarida ce ta shigo yanzu take shigar da ƙara akan NAMEER ABDULZAHIR IYABO."
"Whatt! Nameer to wani laifi take zarginsa dashi."?
Dpo yayi Maganar cike da mamaki domin kuwa bai taɓa jin wanda ya kawo ƙorafin ya'yan gidan ba sai yau kowa albarka yake musu da godiya saboda kyautatawarsu ga talakawa musamman NAMEER.
"Sir akan Case ɗin fyaɗe ne wai ya yi ƙoƙarin yiwa wata yarinya fyaɗe yanzu haka Yarinyar wai tana gadon asibiti kwance tana jinya."
Dafe kansa Dpo yayi tare da cewa.
"First time da aka fara kawo case mummuna akan ahalin Iyabo, is okay ka ɗebi jami'an mu kuje asibitin ku fara tabbatar da maganar ta, idan ya tabbata to wajibine aje ayi arresting ɗin NAMEER saboda kace yarinyar ƴar jarida ce gudun ɓatawa wannan station ɗin suna da kuma kare kakin mu ya zamo wajibi mu amshi Case ɗin, kana iya tafiya."
"Yes Sir."
Sargent Bala yayi Maganar yana ficewa numfashi Dpo ya saki har yanzu bai daina mamaki ba.
"Allah ya kyauta."
Shine abinda Dpo ya furta ya cigaba da aikinsa.
Ko da Sargent Bala ya fito harara ya watsawa JIDDA tare da cewa.
"Ana ganin mutum Allah ya rufa masa asiri za'a fara tunanin ta yadda za'a tona masa, to ta Allah ba taku ba insha Allah sharrinku a kanku zai ƙare."
Yayi Maganar yana fita ya haɗa jami'ai huɗu ya kuma leƙowa yace.
"Sai kizo muje asibitin mu tabbatar da ƙaryar taki."
Bakinta Jidda ta taɓe tare d da bin bayansa asibitin sukaje Sargent Bala da kansa ya yiwa Hajara tambayoyi ta kuma tabbatar da cewa lallai Nameer shine yaso mata fyaɗe, hakan yasa Sargent Bala da Jidda da sauran Police ɗin suka nufi IYABO Estate.
A bakin get ɗin farko na gidan Soja suka tare su duk da ganin motar Police ne, har sai da suka nuna takaddar ijinin da aka basu, sannan suka barsu suka shige, zuwa get na biyu wanda yake ɓangaren su Nameer, mai gadi shine ya buɗe musu get ɗin suka shiga, kafin suka fito tare da bawa maigadi umarnin ya shiga ya sanar da cewa ƴan sanda suna neman NAMEER, da ganinsu alaramma mai gadi bai yarda dasu ba sai dai ba tare da tsoro ba ya nufi cikin babban falon nasu kasancewar yasan ƴan sanda sun saba zuwa neman alfarma gidan, JIDDA da kallo take bin girma da tsaruwan gidan yanda akayi asarar dukiya wajen ginasa, bakinta ta taɓe ko kaɗan gidan bai burgeta ba.
A falo mai gadi ya samu Ummi da Tutu, Ummi ce ta dubi mai gadi tace.
"Alaramma ya akayi akwai abinda kake bukata ne.?"
"A'a Uwar gida babu abinda nake buƙata Police sukazo wai suna son ganin Oga NAMEER, sai dai Uwar gida a yanda na gansu kamar ba lafiya ba."
Murmushi Ummi ta saki tace.
"Meye abun damuwa saboda Police suna bukatar ganin NAMEER sun saba zuwa neman alfarma dan yauma bana rabe abinda ya kawo su kenan, ke Tutu jeki yiwa NAMEER magana yaje ya samesu."
Girgiza kanta Tutu tayi cike da tsarguwa da rashin yadda tace.
"No UMMI nima hankalina bai kwanta da yaya Nameer ya fita ya samesu ba gaskiya domin basu saba zuwa wajen sa, wajen Abba suke zuwa kai tsaye, dole dai akwai wata damuwar to amma wacce irin damuwa ce zaisa Police suzo neman yaya NAMEER, Ummi muje mu fara jin meya kawo su tukunna."
"Ƙwarai kuwa Uwar gida gaskiya Tutu take faɗi domin kuwa naga harda wata yarinya budurwa suka shigo sai famar haɗa rai take da alamu dai babu alkairi a tare da ita."
Alaramma mai gadi yayi Maganar cikin kulawa, Tutu ce tace.
"To kinji Ummi muje dai mu duba kafin a kira su yaya NAMEER ɗin."
"Gamu ko ba'a kira mu ba."
Sukaji muryar NAMEER ya doki kunnen su gabaki ɗayansu idanu suka ɗaga suka kalle su suna sanye cikin gezna baƙa iri ɗaya sun kafa baƙar hula sosai shigar ta musu kyau tamkar ƴan biyu haka suka fito, Ummi murmushi tayi tace.
"To gara da kuka zo kuwa, daru nake da wadannan rigimammun, wai Police ne sukazo nemanka, shine ƙanwarka ta ce baza'a kiraka ba sai anje anji abinda ya kawo su wai basu saba zuwa neman alfarma wajenka ba, wajen Abban ku suke zuwa, shi kuma wannan ustazun ƙaryar yace min bai yarda dasu ba wai harda wata mace suka taho, to koma dai menene ai banga abin tsoro ba, domin kuwa marassa gaskiya su ke razana ba masu gaskiya ba, kunji abinda yake faruwa."
Hisham ne yace.
"Zancen banza zuwan Police gidan nan kuma har wani abun mamaki ne, ƴan maula ne karnuka, ƙashi kawai suke nema da zarar an jefa musu zasu ƙara gaba, muje NAMEER bani da lokaci."
Kansa NAMEER ya girgiza kafin yace.
"Ƴan sanda sune ƙashin bayan al'umma Hisham sam mummunar magana akansu bai dace ba, da babu su bazaka iya tafiya kaje inda kake so cikin kwanciyar hankali ba, dan haka ka dinga faɗar magana mai kyau a kansu."
"Faɗa masa dai domin kuwa naga alamar Hisham ya tsani Police da yawa, kuje ku samesu kuji abinda yake tafe dasu." Ummi tayi maganar.
Bakinsa Hisham ya taɓe tare da yin gaba, bayansa NAMEER yabi yana cewa.
"Muje Alaramma."
Bayan NAMEER shima yabi suka fita, Tutu miƙewa tayi zata bisu Ummi ta dakatar da ita da cewa.
"Ina zakije, ba aiki na sanya ki ba, maza shige kije ki cigaba da aikin dana saki.?"
"Ummi ki bari naje naji tukunna sai na dawo na ƙarisa aikin."
"Bazan bari ba, bana son shashancin banza ki shige kije kimin abinda na saki."
Bakinta Tutu ta tura tare da shigewa kitchen.



A bakin motar Police ɗin suka tsaya, Nameer ne ya dubi Sargent Bala tare da sakin murmushi yace.
"Sargent Bala kaine kuma baka kirani ba, meke faruwa domin kuwa yadda na ganka dole akwai Magana kai ɗaya ka saba nemana yau kuma na ganku ku shida."?
Shuru Sargent Bala yayi cike da fargaba da tsoron yadda zai sanar da NAMEER abinda ya kawo su, HISHAM ne yace.
"Kai Magana ake maka ko kurma ne kawai, mtsss ko da yake ba sai kayi magana ba, neman kuɗi ya kawo ku ba."
Hisham yayi Maganar yana sanya hannunsa cikin aljihu ya zaro rafar 500 ya wurga musu tare da cigaba da cewa.
"Gashi sauri muke bamu da lokacin ɓatawa, muje NAMEER."
Hisham yayi Maganar cikin gadara da iko gami da wulaƙanci, cikin jin zafin abinda HISHAM yayi Jidda take bin kuɗin da kallo tare da ɗago kanta ta furta.
"Tirrr! Allah ya wadaran mutumin da zai wulaƙanta ɗan adam akan wasu ababen duniya, himm! Wai ɗan sanda jagoran al'umma ake wulaƙantawa ake jefa masa kuɗi saboda sun lalata mutuncin kakinsu da son abun duniya har ake musu kallon ƙasƙantattun mutane kare ake jefawa abu ba mutum ɗan Adam ba, gashi kuma kun sunkuyar da kanku kun kasa faɗa musu abinda ya kawo ku, to sunce su sauri suke basu da lokacin ɓatawa tunda ku kuma kuna da lokacin jiransu sai mu samu waje mu zauna mu jira har su dawo ko."?
Jidda tayi maganar tana jefawa Hisham mungun kallo Nameer sai yanzu ya ɗago idanunsa ya kalleta, Hisham kuwa murmushi ya saki zaiyi Magana NAMEER ya ɗaga masa hannu tare da cewa.
"Sargent Bala ɗago idanunka ka kalleni ka faɗa min meya kawo ku."
Sai yanzu Sargent Bala ya ɗago kai tare da cewa.
"Ranka ya daɗe ƙara aka shigar akanka shine Dpo ya mana umarnin muzo muyi arresting ɗinka."
"Ƙara kuma aka shigar a kaina? Waye ya shigar da ƙara a kaina kuma akan me yake tuhumata.?"
Sargent Bala Jidda ya nuna da yatsa tare da cewa.
"Wannan itace ta shigar da ƙorafi akanka, akan Case ɗin fyaɗe, kayi haƙuri ranka ya daɗe muje office sai ka ƙarisa jin Case ɗin."
Wani irin hasala HISHAM yayi tare da jefawa Jidda kallon tsana domin kuwa tun a maganganun ta na farko ya fuskanci tacacciyar marar kunya ce.
"Whattttttt! Kai kasan abinda kake faɗa kuwa NAMEER ake tuhuma da Case na fyaɗe, hmmm! Da alamu ku mahaukata ne da kuka debo ƙafa kuka sako wannan Yar tashar a gaba wai kunzo kama Nameer, to bara kuji ko da NAMEER ya aikata wannan case ɗin bazai kamu ba, bare kuma ɗan uwana bazai taɓa aikata wannan ƙazamin aikin ba, mtsss nonsense! Let go NAMEER."
"Hmmm! Ɗan tasha shi ke gane ɗan tasha, ashe kuwa kaine cikakken ɗan tasha tunda har ka gane ƴar tasha hmmm! Wasu dai ba mutane ba domin kuwa sam basa gane gabas bare kuma yamma."
Jidda tayi maganar tana taɓe bakinta, Hisham hannu ya ɗaga zai ɗauketa da mari, Nameer yayi saurin riƙe hannunsa yana girgiza masa kai.
"Nameer meyasa zaka riƙe hannuna akan wannan daƙiƙiyar jaka ƴar matsiyata, waye ita meye ta ke taƙama dashi da har zata tako ƙafarta cikin gidan nan ta taka mu, tabbas kinyi kuskuren da baki taɓa irinsa ba a rayuwar ki, tunda har kika fara tunanin taɓa ɗan uwana to ki fara ƙirga ranakun tashin hankalin ki, duk wanda ya taɓa ɗan uwana na rantse da Allah sai naga ƙarshen sa, wallahi sai na tozarta rayuwarki da ta ahalinki, daga yau kin shiga komar HISHAM ABDULZAHIR IYABO iyayenki ma kwanciyar hankali sai ta gagaresu zaki ga yadda ake tsantsar tozarci ƴar matsiyatan talakawa."






______________________________________



*Share and comment my fan's i really love You*






*UMMU NASMAH CE✍🏻*





*_For more information 08147537180_*
[5/13, 7:10 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*



*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*





*_JALALA FAN'S INA ƘAUNAR KU INA JIN DAƊIN SHARHINKU ALLAH DAI YABAR ƘAUNA MU CIGABA DA GASHI_*




*_FREE BOOK ONE_*




*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻



*_Page 7 to 8_*




Murmushi Jidda tayi tare da harɗe hannunta a ƙirji tana yiwa Hisham kallon mahaukaci Nameer ne yace.
"Ya isa haka Hisham, meye haka meya kawo iyaye cikin wannan maganar, iyaye suna da mahimmancin da taka su mungun haɗari ne a rayuwa, koda basu haifeka idan sun kai girman haifar kamarka to iyayenmu zamu kirasu, karna kuma jin ka zagi iyayenta, please Hisham ka dinga dannar zuciyar ka."
"Da ka barsa ya cigaba da zagin domin kuwa mahaukacin kare shike haushi, Malam Hisham dan Allah karka fasa tozarta ni, idan kuma ka fasa to baka amsa sunan gidan ku ba, idan kai mahaukaci ne ni kuma likitar mahaukata ne zanyi maganin haukarka, karka fasa."
Jidda tayi maganar tana jan doguwar tsuka tare da juyawa ga Sargent Bala ta cigaba da cewa.
"Idan kunga dama ku kamasa idan kunso ku ƙyalesa, ni kuma bazan fasa ƙudiri na a kanku ba ku tuna da wacece ni."
Tayi Maganar tana juyawa tabar wajen ba tare da ta tsaya taji me Sargent Bala zai ce ba.
Wani irin hura zuciyar Hisham yake tunda yake a tarihin rayuwarsa babu wanda ya taɓa tsayawa a gabansa ya faɗa masa magana yadda ta masa cikin tsawa mai rikitarwa Hisham ya jawo kwalar Sargent Bala yace.
"Waye ita! Dame ta dogara waye ya ɗaure mata gindi ƴar uban waye Minister ne ko shugaban ƙasa ko gomna ka faɗa min na rantse da Allah sai na tozarta ta sai na bambance mata tsakanin aya da tsakuwa, sai na zamo sanadiyyar lalacewar rayuwarta idan ban aikata hakan ba ni ba jinin Iyab..............
Saurin toshewa Hisham baki NAMEER yayi yana janye hannunsa daga rigar Sargent Bala, cikin taushin murya NAMEER yace.
"Cool down Hisham ba komai ake ɗagawa hankali ba, kar ƙaramin abu ya tayar maka da hankali ma, kayi haƙuri ka koma ciki ni zanje station ɗin rago shike tsorata marar gaskiya kuwa gumi yake bana da matsala ko jin zafin akan Sargent Bala yazo tafiya dani aikinsa yake ka barsa yayi aikinsa kaje ka sanar da Abba abinda yake faruwa, muje Sargent Bala."
"Bazai yiwu ba Nameer mutuncika ya wuce ka shiga cikin motar Police, bazai yiwu ba hakan ba mai yiwuwa bane, Sargent Bala kaje ka cewa Dpo ni Hisham nace NAMEER bazai zoba, ku fice ku bar gidan nan ko na sunce muku karnuka suyi maganinku."
A ɗan tsorace Sargent Bala ya ɗago ya kalli Hisham domin kuwa yasan zai aikata duk abinda ya furta NAMEER ne yace.
"Sargent Bala kuje zanzo a motar gida ɗan uwana baya son na shiga motarku bazan shiga ba amma zanzo karka sanar da Dpo sakonsa domin kuwa baku da laifi aikinku kuke kuje."
Kansa Sargent Bala ya ɗaga tare da bawa sauran Police ɗin umarnin su tafi, NAMEER kallon Hisham yayi tare da cewa.
"Baka cika bibiyar jarida bane shiyasa baka santa ba, tabbas zata iya ɓatawa station ɗin su suna muddun basuyi abinda tace ba, ba ƴar kowa bace face ƴar Jaridar Aminci mataimakiyar shugaban Aminci na santa domin kuwa na juma ina son na kai mata ziyara sai dai kuma gashi ita ta riga kawo min, naji daɗin hakan sosai."
Cike da rashin fahimta Hisham yace.
"So whatt! Idan ƴar Jaridar ce, tukunna ma ya akayi kasan wani abu a kanta kana da alaƙa da ita ne.?"
"Hmmm! Yanzu ba lokacin tambaya bane Hisham, ka koma ciki ka sanar da Abba abinda ke faruwa ni zanje station ɗin sannan karka fasa zuwa gidan Mamabisola kamar yadda muka shirya dan Allah kaje."
"Ta yaya zan Barka ka shiga cikin station kai ɗaya sam bazan iya barinka ba tunda ka dage sai kaje sai dai mu tafi tare babu gidan Mamabisolan da zanje muje kawai."
"Bazamu tafi ba tare da ummi tasan abinda ke faruwa ba, kaje ka sanar da ita ta yadda zata fahimta ka tabbatar hankalinta bai tashi ba."
Kansa Hisham ya girgiza tare da juyawa cikin gidan cikin wani irin mungun yanayi, yana shigewa NAMEER ya buɗe mota da sauri sauri ya shiga tare da jan motar ya fice.


Falon ya koma cikin sanyin jiki tare da zama gefen Ummi, Ummi cike da mamaki take dubansa tare da cewa.
"Lafiya Hisham ka shigo haka cikin wani irin yanayi, ina shi NAMEER ɗin yake, kun fasa

Please Login or Register in order to submit comment