Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ina ji a jikina zaka samu lafiya."
"A'a Ummi bazan samu lafiya ba kin sani na sani, kawai kimin wannan alfarmar."
Kanta Ummi ta kaɗa tace.
"Shikenan zan maka zan bar Hisham ya auri yarinyar nan ne kawai saboda kai Nameer amma Allah ya gani har cikin zuciyata bana kaunar ta, amma da sharadi ɗaya har sai mun koma asibiti an tabbatar da cewa bazaka rayu ba, sannan ne zan iya barinka ka ɗauki wannan kasadar Nameer."
Ummi tana faɗin haka ta juya da sauri tabar wajen tana kuka, Nameer wajen Hisham ya koma.


Yana zaune yayi shuru.
"Hisham na faɗa maka wannan gardamar zan rabata ni zan auri Jidda tunda dama ai ba jumawa zanyi a duniyar ba, kaga idan na mutu shikenan ka samu damar zama da ita na tsawon rayuwa."
"Hassan tun ɗazu yake kiran wayarka."
Hisham ya masa maganar tamkar baiji mai yace ba.
"Magana fa nake maka Hisham ba damuwata kiran Hassan ba."
Idanunsa ya ɗaga ya kalli Nameer kafin ya girgiza kansa.
"Hmmm! Maganar taka ce bata da daɗin ji Nameer, wa yace maka nidin mai tsawon rayuwa ne, kasan ƙaddarar mutuwa tace, kaga Nameer idan Allah yasa kana da tsawon kwana duk wahala da ciwo sai ka tashi kayi Rayuwar da Ubangiji ya diba maka, ka barni na ɗauki kaddara ta Jidda kaddarata ce kuma ni zan ɗauki kaddararta."
"Hisham kenan kaga mun gama magana da Ummi muddun kana son Auren Jidda to dole ne sai na fara rabaka da kaddarar da take cikin ahalin Jidda."
"Ka tashi muje gidan su Jidda na tabbatar da abinda kunnena yaji."
Kansa Nameer ya kaɗa yace.
"Shikenan zamu iya zuwa Hisham hankalina ya kasa kwanciya akan karar da Alhaji Sagir ya shigar da Company, watakila a gama shari'ar bana raye, ko mai zai faru Hisham karka bari Companyn mu ya wulakanta, ka kankaro mutuncin Abba, kayi ƙoƙarin ganin ka kare mana Company."
"Nameer shi kansa Abba bazai bari Companyn sa ya wulakanta ba, yafi Alhaji Sagir karfi da iko a cikin ƙasar nan, nasan a wannan lokacin Abba zai tauna tsakuwa dan aya taji tsoro wallahi Nameer bana jin tsoron wannan kotun da za'a shiga, ni nasan wanda ya je ya saka Alhaji Sagir ya shigar da Company ƙara, ba kowa bane face Mamabisola, tar na ke kallonta da idanuna, burinta ɗaya mu rasa komai a rayuwa bazan taɓa tona mata asiri ba, nafi so shi Abba ya fahimta da kansa."
"Me kake nufi Hisham waya faɗa maka cewa itace tasa Alhaji Sagir ya shigar da ƙara kotu."?
Miƙewa tsaye Hisham yayi tare da goya hannunsa a baya yace.
" *MAI GADIN GIDAN TA* Shine ya sayar min da wannan jaridar akan kuɗi Naira dubu ɗari b."
A razane shima Nameer ya miƙe yace.
"What! To amma meyasa zai fitar mata da sirri muddun gaskiya yake fadi baya tsoron abinda zaije ya dawo, kai mtsss to meye tsakanin ta da wannan kisan tasan wanda yayi kisan ne da har zataje ta zuga Alhaji Sagir.?"
"A'a bata sani ba kawai dai ta shiga ciki ne saboda ta samu taga mun wulaƙanta, shine ita burinta zai cika."
"Kai lamarin da mamaki Hisham, to Allah ya kyauta, ka tashi muje gidan su Jiddan."




_____________________________________







_Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to insha Allah Book One ya kusa zuwa karshe, alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._



*0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180*




*Like Share and comments my fan's🥰*






_UMMU NASMAH CE✍🏻_💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*




*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*





*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻




*FREE BOOK ONE 📚*



_Wannan littafin ba free bane na kuɗi ne Book one shine Free kuma mun kusa zuwa karshen Free zamu shiga Book two inda zaku cigaba da karatun wannan littafin akan 200 kacal ban tsawwala ba farashin da zaku iya biya na sanya dan Allah idan har kina son wannan littafin kina bibiyar sa kizo ki biya kudin ki, ki cigaba da karatun sa akan farashi ƙalilan, karki yadda ki kasance cikin ɗaya daga cikin masu cin hakkin wani 08147537180._




*_Page 59 to 60_*




Bakinsa HISHAM ya taɓe ransa duk a cunkushe ya ɗauki wayarsa tare da cewa Nameer suje.

Abba bedroom yabi Ummi ya dinga rarrashinta da ƙyar ya samu Ummi tayi shuru.


Ko da sukaje unguwar su Jiddan Hisham kansu tsaye suka shiga, Umma ce kawai da Basmah a tsakar gidan Jidda tana dakin ta, darduma Umma ta shimfida musu Basmah hankalinta duk yana kan Hisham tana jin baƙin ciki da kunar rasashi duk da a ranta ta saka sai ta ƙwaci Soyayyarta, bayan sun gaisa ne Umma ta fahimci kamar suna cikin damuwa, nisawa tayi tace.
"Nameer kamar akwai abinda yake faruwa ko, naga kamar duk jikinku yayi sanyi.?"
Numfashi Nameer ya saki tare da kallon Hisham kafin yace.
"Umma tabbas akwai abinda ya kawo mu sai dai fa Umma ban san ta yaya zamu fara miki maganar nan ba ina jin nauyin maganar."
"Nauyi kuma Nameer ni ai uwa ce, ku faɗa min damuwarku babu komai."
Ganin Nameer na wala wala yana jin nauyin tambayar yasa Hisham cewa.
"Umma magana ce akan neman aurena da Jidda, Abba yasa anyi bincike akanku, kuma ankawo masa sakamako marar daɗi, har hakan yasa iyayena suna son min katanga da Jidda, Umma da gaske ne duk wanda ya auri zuri'arku Auren farko sai ya mutu? Umma ance ke maza huɗu kika aura duk basa fin sati da Auren suke mutuwa, ance dalilin da yasa kenan kika bar cikin Yan uwanki kika dawo gefe, sannan kuma ance mahaifiyarki ƴar bari............
"Ya isa haka Hisham wadannan tambayoyin ma kaɗai sun isa, domin sune matsalar mu ba sauran ba."
Tunda Hisham ya fara magana Jidda ta fito take jinsa har Nameer ya dakatar dashi hankalinta ne ya tashi gumi ya keto mata bata san sanda hawaye ya biyo idanunta ba, umma kuwa innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ta hau furtawa a cikin zuciyarta shikenan ranar da take tsoron zuwanta tazo numfashi Umma ta sauke kafin tace.
"Hisham idan har iyayenka sun maka katanga da Jidda to kabi umarninsu domin kuwa bazasu cutar da kai ba saboda duk wanda zai soka yaso farin cikin ka a duniyar nan bayan sune, *_Wannan ba ƙarya aka faɗi akanmu ba tabbas ƙaddarar da ke cikin zuri'ar mu ne sai dai bani da tabbas idan Jidda tana ɗauke da wannan kaddarar saboda ita jinin gidan ubanta ne ba gidan mu ba, duk da acikin ya'yan mata da ke gidan mu da yawa sun gajemu dole a guje mu Hisham, tabbas mazan aurena huɗu suka rasa ransu babu za'ida aciki, Hmm! Ance muku goggona tana rainon ƴan bariki ko shine tambayar da Nameer ya dakatar da kai ga yinta gareni ko, shima gaskiya ne babu ƙarya a ciki, kaje ka yiwa iyayenka biyayya ka rabu da Jidda zata iya rayuwa ko ba Aure, ko da ta rasa mijin Aure, ai shi Aure Sunna ce ba farilla ba, farilla ce dole ba Sunna ba, manyan malaman Musulunci sunce idan mace batayi Aure ba har iya tsawon rayuwarta ba haramun bane kuma Allah bazai tambayeta akan meyasa batayi Aure ba, na gode da KULAWARKU da soyayyar da kuka nunawa yata Hisham da kuma ɗawainiyar da kukayi gareni, kaje ka yiwa iyayenka biyayya Allah ya muku albarka ya baku mata na gari_*."
Umma tayi Maganar cikin sanyin jiki, Wani irin kuka Jidda ta sanya sautin kukan ta shiya dawo da hankalin su Hisham gareta, dubanta Hisham yake cike da tausayi Muryar Nameer sukaji yace.
"Umma dama munzo mu tabbatar da gaskiyar maganar ne, bani da lafiya umma, munje asibiti sun tabbatar da cewa ina da Cutar KANSAR ƘWAƘWALWA sunce bazan haura wata biyu ba a duniya zan mutu, nayi magana da mahaifiyar mu cewa ni zan ɗauki kasadar Auren Jidda, tunda dama ni mutuwa zanyi dan haka zan aureta idan na mutu Hisham ya auri matar sa, a ina dangin mahaifin Jidda suke Umma zamuje mu nemi aurenta."
"Subahanallah! Nameer abinda ke faruwa da kai kenan innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Amma Nameer wannan ba ɗaukar kasada ba ce zakayi faɗar likita ai ba faɗar Ubangiji ba ne Nameer insha Allah zaka samu lafiya."
"A'a Umma karki hanani, babu wanda ya taɓa kamuwa da cutar nan ya rayu, ki duba kiga yadda take kuka ko hakan ya isa ya nuna miki ƙarfin soyayyar da suke yiwa junansu ina da halin taimakawa ɗan uwana bazan barsa ya shiga wani hali ba, ki mana addu'a da fatan Alkairi kawai."
Tunda Nameer ya fara Maganar Hisham yaji wani kishi yazo masa ya tsaya a wuyansa, idanunsa ya runtse, yana ji Umma tace.
"To shikenan Nameer Allah yasa haka yafi Zama Alkairi, amma fa ka sani bazan waiwaici bayana ba, bana son tuna abinda ya wuce, akwai baffan ta a cikin garin Gombe sai dai kuje wajensa ya baku Auren Jidda amma bazan iya faɗa muku inda Ahalinta suke da zama ba saboda babu Alkairi a tsakanina dasu."
Kansa Nameer ya girgiza cikin zuciyarsa ya furta _tunda har aka samu baffan ta to tabbas za'a samu cikakken ahalinta._
"Shikenan ba damuwa idan mun gama magana da Abba zamuzo sai a bamu numbern wayar baffan nata mu zamu koma."
Nameer yayi Maganar yana tashi shima Hisham tashi yayi sukayi sallama da Umma jidda da Basmah bayan su HISHAM sukabi suna tsaye jikin Mota har yanzu Jidda hawaye take sun juma suna tattaunawa akan lamarin, Nameer ya tabbatar da cewa shine zai raba wannan gardamar sai dai ita Jiddan har cikin zuciyarta bata amince da lamarin ba, cikin jimami suka rabu da Jidda.



**********


Acikin kwana shida da maganar Abba da Hisham da kuma Nameer sunje asibiti huɗu da Nameer manyan asibitin da suka fi dukkan asibitin da ke cikin garin har result ɗin sa aka tura India suka ƙara bincike amsar dai ɗaya ce bazai rayu ba bazai gaza wata biyu a duniya ba, Hisham da Umma sosai suka kuma shiga cikin tashin hankali sai dai babu yadda suka iya da kaddara dole suka haƙura, sai a wannan lokacin Abba da Ummi suka amince da Nameer ya auri Jidda duba da yadda Hisham ya shiga tashin hankali akan Jiddar, shima Hisham da kyar ya amince Nameer ya auri Jidda dan har cikin ransa yake jin kishin hakan duk da Nameer ɗan uwansa ne, Abba yace gara ayi auren cikin gaggawa kafin wata biyun ta cika.

A cikin wannan satin Abba ya tura su Alhaji Bawa sukaje har gida suka samu Umma ta musu kwatancen inda zasuje su sami Baffan Jidda Malam Aminu da ke zaune cikin jihar Gombe tare da basu numbern wayarsa, ko da suka dawo Abba da kansa ya kira Malam Aminu ya masa bayanin abinda ke faruwa, cikin mutuntawa da kulawa Malam Aminu yace Allah ya kawo su lafiya, Abba Nameer yasa yaje ya yankawa su Alhaji Bawa ticket ɗin jirgin Gombe washegari su tafi.
Haka kuma akayi washegari suka tafi Gombe harda Nameer, wuni guda suka gama abinda ya kaisu suka dawo, inda Malam Aminu ya bawa Nameer Auren Jidda sai dai shi baya da masaniya akan neman Jidda da Hisham dan Abba yace kar a sanar da Malam Aminu a nuna masa kawai Nameer shine yake neman auren nata, ansa ranar auren wata ɗaya tal, inda Malam Aminu yace shima zaizo Kwaran a ɗaura Auren kawai anan, ko da suka dawo suka sanar da Abba yace hakan yayi sai dai Umma ita bata ƙaunar shigowar Jidda cikin ahalinta a haka aka ijiye maganar auren.



**********


Sosai Basmah ta ke dariya ita kaɗai a cikin daki, shuru tayi na wasu mintinan sai kuma ta kuma sakin dariya tare da furta.
"Allah mai iko rana ɗaya sai ya baka dama tabbas Hisham zai zamo nawa."
Tayi Maganar tana dariya text ne ya shigo wayarta hakanne yasa Basmah Daga wayar ta buɗe sakon zama tayi ta fara karanta sakon.
_Bana son kusan ko ni waye shiyasa na ɓoye number ta na turo miki wannan text ɗin, nasan kece aminiyar Jidda ta haƙiƙa, wacce kike ɗaukar damuwarta amatsayin naki, to shawara zan baki ki bawa Jidda akan Auren da take niyyar yi da Nameer nan ba da jumawa ba babban kuskure ta ke kokarin tafkawa rayuwarta, Nameer ƙarya yake bashi da wata cutar KANSAR ƘWAƘWALWA, wannan shirinsa shi da likitotin daya saya saboda bukatar ya mallaki Jidda, bashi da wannan cutar dan haka idan har ta auresa to ta tabbatar ta rasa Hisham na har abada NAMEER MUNGUN MACIJI NE WANDA BASHI DA ALKIBILA, dan Allah ki sanar da Jidda ku san yadda zaku dakatar da wannan Auren ni musulmi ne wallahi na miki rantsuwa da Allah Nameer bashi da wata cuta ƙarya ne, idan kuma wannan maganar da na faɗa miki ƙarya ne to na yadda bala'in Ubangiji ya sauƙa a kaina, shida abokinsa Doctor Hassan suka kulla wannan makircin saboda cikar ƙudirinsa na mallakar Jidda ya gama bincike akan Mahaifiyar Jidda shiyasa ya ɓullo da wannan makircin saboda yasan ta nan ne kawai burinsa zai cika._
Miƙewa tsaye Basmah tayi a firgice da ƙarfi ta furta.
"What!!! Nameer ɗin."



_____________________________________







_Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to insha Allah Book One ya kusa zuwa karshe, alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._



*0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180*




*Like Share and comments my fan's🥰*






_UMMU NASMAH CE✍🏻_💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*




*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*





*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻




*END OF BOOK ONE LAST FREE PAGE 📚*




_Wannan littafin ba free bane na kuɗi ne Book one shine Free kuma wannan page ɗin shine last free page zamu shiga Book two inda zaku cigaba da karatun wannan littafin akan 200 kacal ban tsawwala ba farashin da zaku iya biya na sanya dan Allah idan har kina son wannan littafin kina bibiyar sa kizo ki biya kudin ki, ki cigaba da karatun sa akan farashi ƙalilan, karki yadda ki kasance cikin ɗaya daga cikin masu cin hakkin wani 08147537180 Ummu Nasmah na maraba da masoyanta, wannan shine damar da zaku nuna min soyayya ta hanyar sayen wannan littafin._






*_Page 61 to 62_*





Cike da tsantsar mamaki Basmah ta nemi waje ta zauna _ta yaya za'ace NAMEER zai ci amanar Hisham wannan ba maganar da hankali zai ɗauka bane, amma kuma ai ana iya komai akan Soyayya, to tunda nima zan iya cin amanar Jidda meyasa shi Nameer zan kasa yarda da zai ci amanar Hisham, ko da yake kusancin dake tsakanin Hisham da Nameer yafi ƙarfin kusancin dake tsakanina da Jidda_ numfashi Basmah ta saki a fili ta furta.
"Hmmm! To ma wai waye ne ya turo min wannan sakon a idan gaskiya ne a ina ya samu wannan sirrin waye Hassan ya kamata nasan waye shi Hassan domin sanin dabiun sa shine zai tabbatar min da waye Nameer a zahiri dai Nameer mutumin kirki ne to amma ta yaya cikin sa zai kasance baƙi, to ma meyasa zan faɗawa Jidda wannan saƙon ni ai wannan babbar dama na samu bazan taɓa bari Jidda tasan wannan maganar ba, domin kuwa Auren Nameer da JIDDA shine zai bani damar samun Hisham a matsayin mijin aurena, lallai wannan babbar dama ce gareni."
Tayi Maganar tana sakin murmushi tare da jingina kanta a jikin bango.



Tun ɗazu ta ke kuka tamkar ranta zai fita taki tayi shuru idanunta yayi jajur, Ummi tayi tambayar duniya ta faɗa mata abinda yake damunta amma taƙi sai kuka kawai take tayi rarrashin duniya kuma taki tayi shuru, Hisham ne ya shigo yana waya shima duk fuskar sa ta faɗa dan tunda aka saka ranar auren Nameer da Jidda zuciyar sa take tsinkewa ga fargar mutuwar da aka Nameer zaiyi nan da wata biyu, ganin Tutu nata kuka ya sashi katse wayar tare da nufar su yana cewa.
"Ummi meke faruwa kuma, meya sameta."?
Numfashi Ummi ta saki dai-dai Abba na shigowa shi da Hisham tace.
"Umm ka ganta tun ɗazu take wannan kukan nayi tambayar duniya ta faɗa min abinda ke faruwa taƙi, nayi rarrashin ma kuma taƙi tayi shuru bansan meke damunta ba."
Zama gefenta Hisham yayi tare da dafa kafadarta.
"Tutu kalli idona ki faɗa min meke damunki ko Allah zaisa na iya share miki hawayenki, faɗa min."?
Kuka ta kuma fashewa dashi jikinta na rawa daƙyar ta buɗe bakinta tace.
"Yaya Hisham da gaske zaka share min hawayena."?
"Eh zanyi maganin damuwarki idan har bata fi ƙarfi na ba, faɗa min menene matsalar."?
Idanunta ta ɗaga ta kalli Abba kafin ta sunkuyar da kanta.
"Yaya Hisham idan har ana son na cigaba da farin ciki a cikin gidan nan to a fasa Auren Yaya Nameer da Jidda, ni ya Aure Ni."
A firgice Hisham ya ɗago kansa ya kalli Ummi ya kalli Abba da Nameer da suma suka zaro idanunsu suna kallon Tutu.
"Tir ƙashi."
Hisham ya furta yana mai da kallonsa ga Tutu kafin ya miƙe tsaye yace.
"Tutu kinsan abinda kike faɗi kuwa, kin haukace ne, Nameer ba matsayin uwa ɗaya uba ɗaya ya kamata ki ɗaukesa ba, ya fasa auren Jidda ya aureki ke gaki uwarsa kin basa umarni ko, to yaƙi bin umarnin naki uwarsa tsine masa albarka ya shiga duniya, dan Allah Ummi kiji wani rashin hankali wai bazata ƙara farin ciki ba muddun bai aureta ba, to sai ki mutu da baƙin ciki wawiya."
Hisham yayi Maganar a fusace tamkar zai kai mata duka, Nameer kuwa wani irin tsinkewa zuciyar sa yayi ko da wasa baiyi zaton Tutu zata birkice haka ba, numfashi ya saki tare da jinginuwa da bango ya kasa magana Ummi ce tace.
"Wai dama wannan uban kukan da kike duk na wannan shashancin ne Tutu, kin manta da lalular da Nameer yake ɗauke dashi ne bai kai wata biyu ba ya rage masa a wannan duniyar bama da wani kwanciyar hankalin farin ciki daga mu harshi Nameer ko wani wayewar gari da fargabar mutuwar sa muke tashi, ita kanta Jiddar da zai Aura kin sani Tutu ba wai da san ransa zaiyi Auren ba, kinsan dalilin aurenta da zaiyi, amma kuma ke yanzu sai ki ɓullo mana da wannan shashancin, karna kuma jin kinyi wannan Maganar."
Kukan Tutu ta kuma fashewa dashi cikin tashin hankali ta hau cewa.
"Ni fa Ummi na yarda na auresa a haka ko da kwana ɗaya nayi tare dashi, zanyi farin cikin ganin wannan ranar na tsawon rayuwata, Ummi wallahi ina son yaya Nameer, shima fa Ummi yana sona ku tambayesa mana kuji, mun fa juma muna soyayya Ummi karku hana mu farin ciki Ummi wallahi muna son junan mu."
Kansa Nameer ya dafe jin ta fasa masa taya amma da ke namijin duniya ne sai yayi fuska tamkar baiji zancen ba, Hisham da Abba ido suka Daga suka kalli Nameer.
"Nameer kana jin abinda Tutu ta ke faɗa, da gaske ta ke kuna son junanku kai da ita.?"
Ɗago kansa yayi ya kalli Hisham shima tare da nuna kansa da yatsa cikin yanayin mamaki yace.
"Wai ni ɗin ne nake soyayya da Tutu, wannan wacce irin magana ce kike haka, nifa kallon ƙanwar da muka fito ciki ɗaya na ke miki Tutu, anya kuwa yau kina cikin hankalin ki, Hisham da ace ina soyayya da Tutu kaine mutum na farko da zan fara sanarwa ko da ban sanar dasu Abba ba, kaima ka sani, ina ga yau dai Tutu bata cikin hankalin ta akwai abinda ke damunta."
Kansa Hisham ya gyada tare da cewa.
"Tabbas haka ne Nameer da bazaka ɓoye min ba, barni da ita idan kin haukace ne to ni kuma zan kaiki asibitin mahaukata ko tausayin halin da yake ciki bakya yi, yanzu na taka miki wuya."
Da wani irin mungun mamaki Tutu ta ke bin Nameer da kallo tana matsowa garesa hawaye na daɗa gudu a fuskarta tamkar saukar aradu taji maganar tasa, sanda tazo daf dashi cikin kuka da wani irin sautin Muryar da ya fara dashewa itama ta nuna kanta da yatsa sai kuma ta fashe da kuka.
"Yaya Nameer ƙarya nake! Karya nake kace meyasa meyasa zaka min

Please Login or Register in order to submit comment