Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

munin halinsa, na sani Umma da mahaifinki yana raye bazaki tagayyara haka ba, Umma nasan zakiji zafin maganganuna domin kuwa uwa ba abar wasa bane sai taki mahaifiyar bata da tausayi."
Idanun Umma cikowa da hawaye sukayi tabbas maganganun ƴarta akan mahaifiyarta gaskiya ne sai dai har cikin ranta tana jin zafi da ciwo idan taji an aibata mata uwa bata taɓa zaton rayuwa na juyawa mutum baya haka ba sai a tsakanin waɗannan shekaru 18 da suka gabata numfashi ta saki kafin ta cewa Jidda.
"Jiddatul kair ki tashi ki bani waje."
"Amma Umma y.......
"Ki tashiii ki bani waje nace miki! Bana son maganar banza babu ruwanki tsakanina da mahaifiyata koma me ta min a rayuwa uwata ce koda mahaukaciya ce ina alfahari da ita, koda kuwa kasheni tayi ta dawo dani ina sonta zuciyata kuma bazata jurewa munanan maganganu akanta ba, ki kiyaye muddun bakya son fushina ya sauka a kanki."





_____________________________________





Share and comment my fan's🥰





*UMMU NASMAH CE✍🏻.*



*_FOR MORE INFORMATIONS_*
*_08147537180_*
[5/11, 7:21 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.



https://chat.whatsapp.com/JdppMXgnPBL1ZTAKjpSrYs



*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*



*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*




*_FREE BOOK ONE_*

*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻





*_Pg 3 to 4_*




"Kiyi haƙuri Umma Allah ya huci zuciyarki, banyi zaton maganar zata ɓata miki rai haka ba, ke uwace gareni fushinki masifa ce a gareni ki yafe min insha Allah bazan kuma wata magana marar daɗi akan Mama ba."
Umma ba tare da ta dubeta ba tace.
"Naji na kuma yafe miki Allah ya muku albarka."
"Ameen Umma na gode."
Tayi Maganar dai-dai Abdu na shigowa gefensu ya zauna, Jidda ce ta dubesa tare da cewa.
"Abdullahi sai yanzu ka dawo daga sallar."
"Na tsaya Liman ya ɗaura min karatu ne shiyasa na juma, ina abinci na."?
"Abincin ka yana madafa."
Ta basa amsar tana miƙewa ta shige ɗakinsu, Abdu Umma ya kalla yace.
"Umma kamar wani abu yana damun Adda naga kamar ranta babu daɗi."?
Numfashi Umma ta saki tace.
"Yanayin rayuwa ne Abdu ba ko wani lokaci bane bawa yake cikin farin ciki, kaje ka ɗauki abincin ka."
"To Umma."
Yayi Maganar yana miƙewa yaje ya ɗauki tuwon nasa kafin ya shiga ɗakin da Jidda ta shiga tana zaune tsakiyar katifa tayi shuru cikin tunani da damuwar rayuwa sallamar sa shine ya dakatar da ita daga tunanin da ta tafi, ta amsa sallamar zama yayi yana sanya hannunsa cikin aljihun sa ya zaro dubu biyar ya miƙa mata.
"Gashi Adda."
Kallon kuɗin tayi ba tare da ta amsa ba tace.
"Gashi kamar yaya kuɗin waye.?"
"Uncle Abdulra'uf ne ya bani yace na kawo miki ko kina da wata buƙata kiyi amfani dasu."
"Abdulra'uf ya baka ka kawo min, na roƙesa kuɗi ne ko kuwa ya ganni cikin tozartacciyar rayuwar da har zan fara roƙo, banyi wannan lalacewar ba Allah ya min ni'ima da har ya bani damar karatu na samu aikin yi, ka mayar masa da kuɗinsa kace bana buƙata."
"Amma Adda gani nayi kamar babu kyau mai da hannun kyauta baya, uncle Abdulra'uf fa sonki yake Adda ba laifi bane idan ya miki kyauta sanin kanki ne yana tausayawa halin da muke ciki, kefa macece komai kece kike mana namiji ma yaya ya ƙare da nauyin gida bare kuma mace dole ne a tausaya miki Adda gashi ni bana da ƙarfin da zan iya neman kuɗi a yanzu bani da lafiyar ɓargon jiki sannan ga ƙafata janta nake hmmm! Adda...........
"Ya isa haka Abdullahi, ka daina min wannan Maganar mace ma mutum ce kamar kowa duk abinda Namiji zaiyi zamu iya dan haka ka daina jin damuwa a kaina, kaje ka mayar masa da kuɗinsa kamar yadda na umarce ka, bana buƙatar abinda zai fito daga garesa na yafe zan iya ɗaukar nauyin rayuwar mu sannan ka sani idan shi Abdulra'uf yace maka yana sona to tabbas yayi kuskure domin kuwa bazanyi kuskuren da mahaifiyata tayi ba, na amincewa Yaruba dukkan su macuta ne basa da imani."
"Amma Adda ya kamata ki duba wann.........
Cikin sauri ta ɗaga masa hannu.
"Ka tashi ka fita min daga ɗaki Abdullahi idan ba so kake na ɓata maka rai ba."
Ganin ranta ya ɓaci yasa Abdullahi tashi ya fice da kwanon tuwonsa yana mai da kuɗin aljihun sa.
Tsuka Jidda taja tare da jawo bargo ta kwanta tana rufe jikinta.





Washegari da safe, Tutu da kanta ta musu breakfast ita da Peju kukun gidan su, a daining table suka jera abincin kafin Tutu ta shige bedroom ɗinta tabar Peju tana kimtsa kitchen ɗin Ummi ta turawa saƙon sun kammala breakfast ɗin kafin ta shige tollet wanka.

A hankali ya buɗe idanunsa yana duban agogon bangon dake manne a bangon ɗakin idanunsa ya lumshe tare da duban Nameer da ke bacci har yanzu bashi da niyyar tashi, ƙafafunsa ya ziro ƙasa tare da sanya takalmin dake gefen bed ɗin, ya sauƙa, towel ya ɗauka tare da shigewa tollet, ya juma sosai kafin ya fito ƙugunsa ɗaure da towel ya rataye ɗaya kuma a kafaɗarsa da alamu wanka yayi, a dressing mirror dake gefen bed ɗin ya zauna tare da sanya hannu ya kaɗowa Nameer ruwan gashin sa a fuskarsa yana sanya towel ɗin ya hau tsame ruwan kansa, cikin azama Nameer ya buɗe idanunsa, jin sauƙar abu kamar ruwa a fuskar sa, a kan Hisham ya sauƙe idanunsa kanne masa ido Hisham yayi tare da nuna masa agogo da hannu yace.
"Raise your eyes and look at 11:00 am this weekend Abby is home, breakfast on time is a must."
Numfashi Nameer ya saki tare da jawo ƙaramin filon dake tsakiyar su ya jefi Hisham dashi yana cewa.
"Saboda yau weekend ne shine zaka min irin wannan tashin na razanarwa wai Hisham yaushe zakayi hankali ne, ko sai randa kayi Aure ne.?"
Wani irin kallon off and down Hisham yayiwa Nameer kafin yace.
"Aure! Ni hmmm! Idan mafarki kake ka tashi kayi sadaka, natsani Soyayya, bare kuma Aure da yake ginshikin Soyayya, dan haka ka daina sani a wannan layin."
Murmushi Nameer ya saki yana tashi ya jingina da jikin bed ɗin tare da cewa.
"Ba'a cikawa so baki Hisham, domin kuwa so tamkar iska yake ba'a sanin shigarsa ba'a kuma ganinsa sai dai a jisa a zuciya idan ta ɗauro ma ya taho a makance, sannan baya shawara da zuciya idan zai shiga gareta faɗawa kawai yake, dan haka ba'a cikawa So baki, ta iya yiwa ka faɗa tekun Soyayyar da bazaka taɓa iya fitowa ba komai iya ruwan da kayi."
"Idan har za'a danganta so da iska to tabbas kuwa za'a iya dakatar da shigarta domin kuwa sai ka ja numfashi kafin iska ya samu damar shiga jikinka kaga kuwa za'a iya ɗaukewa So numfashi dan haka zan iya kare kaina daga faɗawa wahalar SO."
"To ai kai Hisham kayi mantuwa, ba'a taɓa iya rayuwa babu numfashi muddun zaka ɗauke numfashinka na awa guda to tabbas zaka rasa rayuwarka ta har abada, ba'a gujewa so kamar yadda ba'a gujewa mutuwa duk tserenka dasu wallahi sai sun cimmaka."
"Musu da kai ai wahala ne Nameer domin kuwa duk inda gaskiya take kauce mata kake muddun a fagen so ne, tamkar malamin Soyayya haka kake, ina tausaya maka domin kana cikin wahala duk da har yanzu bamu ga gwanar taka ba duk wannan lectures ɗin."
Yayi Maganar yana tashi ya je drowar gajeren wando boxer ya sanya tare da farar vest Nameer ne ya mai da masa amsa da cewa.
"A fagen so ba'a kuri na tabbatar maka wata rana sai Soyayya tayi wasa da rayuwar ka a gaɓar da bakayi zato ba."
Kafin Hisham yayi magana Tutu ta turo door ɗin Room ɗin bakinta ɗauke da sallama Hisham amsawa yayi yana cewa.
"Autar Abba, Abba yayo kira ko."?
Dariya Tutu tayi tare da cewa.
"Yeah abinda kuka sani ne ai, yana can yana ta faɗa wai baku fito da wuri ba, yace ku fito yanzun nan daining."
"Kingan ni nan na gama shiryawa ga dai makararren da zaki faɗawa Aku sarkin magana ni kaga fitata sai ka fito."
Yayi Maganar yana zarar wayoyinsa tare da sanya takalmi ya fice, Nameer duban Tutu yayi tare da cewa.
"Ya akayi kika ƙura min ido tamkar kinga baƙo."
"Hmmm! Dole ai na ƙura maka ido ko yaushe kai sai kayi let akan komai kana dai kallon Yaya Hisham akan lokaci yake komai nasa baya wasa da lokaci saɓanin kai."
"Kema fa kinsan dole na makara domin kuwa jiya munja dogon dare, dan haka bai kamata kimin ƙorafi ba, kije kawai ina fitowa nan da 10minute, sannan zamu fita by 12 tunda yau ba ki da school."
Numfashi Tutu ta saki tare da riƙe kunkuminta da kyau tace.
"Bazan fita da kai ba yau Yaya Nameer, gajiyar jiya ma bata gama barin jikina ba bare kuma na kara biyeka, sannan ka dinga ɗaga ƙafa gudun fahimtar wani abu ga ahali, kayi maza ka fito kasan Abba baya jurewa jira."
Tayi Maganar tana fita daga room ɗin numfashi Nameer ya saki tare da tashi ya shiga tollet.



"Good morning Abba."
"Morning my soon wannan sarkin makaran yauma dai still ko."?
"Ummm Abba kaima fa kasan Nameer abinda aka saba ne kullum."
Yayi Maganar yana kallon Ummi tare da cewa.
"Good morning Ummina."
"Morning Hisham, da alamu dai yau uba da ɗa sun haɗewa ɗana baki, to kuwa baku isa ba muddun ina zaune anan baku isa kun tsige min yarona ba."
Dariya Tutu tayi kafin tayi Magana, suka jiyo Muryar Nameer daga step yana cewa.
"Yeah! Uwata maganin kukana faɗa musu dai ni ai nasan muddun Ummina na kusa babu wanda ya isa tureni."
"Hmmm! Masu uwa mu kuma ai marayu ne mararsa gatan uwa."
Hisham yayi magana yana murmushi, Abba shima murmushi ya saki yace.
"Chaptern ya isa haka, Tutu kiyi seving ɗin mu."
Miƙewa Tutu tayi tare da jawo plas ɗin abincin ta yi seving ɗin kowa, sanin halin Hisham ba komai yake so ba yasa Tutu dubansa tare da cewa.
"Yaya Hisham me zakaci.?"
"Zuban chief's."
Kanta ta girgiza tare da sanya masa ta tura masa gabansa, kafin tasa nata, breakfast suka fara cikin soyayya da ƙaunar junansu babu wanda yayi magana har suka gama breakfast ɗin, Hisham ya riga kowa tashi, ya koma tsakiyar falon ya zauna, kafin Abba ya biyo bayansa.
"Hisham."
Abba ya kira sunan sa ɗago idanunsa Hisham yayi tare da amsawa.
"Na'am Abba."
"Wannan week ɗin kaje gidan Mamabisola kuwa ka gaishe ta."?
"Banje ba."
"Meyasa."?
"Haka kawai."
"Hisham bana son sakarci da iya shege, Mamabisola uwa ce gareni bana son kana ɗaukarta tamkar wata bare."
"Hmmm! Abba ni fa bazanje inda za'a dinga zagina ana kallona banza ba, kaine take dole a gareka bani ba, dan haka ni babu abinda zanje nayi a gidan ta, kawai ka ƙyaleni."
"Hisham...........
"Dan Allah Abba kabar wannan maganar, please."
Ya katse Abba cikin ɓacin rai fuskarsa a haɗe domin kuwa ya tsani yaji ana zancen Mamabisola.
"Hisham katseni zakayi ina magana saboda iya shege, to bara kaji tunda har Mamabisola ta zamo dolena to kuwa kaima ta zamo dolenka, ni da WALE uba ɗaya muke bani da ɗan uwan da ya shigesa, dan haka ya zamo wajibi ka girmama mahaifiyar sa."
"But Abba........
"Hisham...."
Ummi ta katsesa tana ƙarisowa wajen ta zauna tare da cewa.
"Hisham bana jin daɗin abinda kake yiwa Mamabisola, karka manta su fa jikinka ne dole ne ka girmama su domin kuwa baka da ɗan uwan daya wucesu, baka ganin yadda Tunde ke girmama mahaifinka ko wani weekend sai ya zo ya gaishe sa cikin girmamawa kuma baya taɓa zuwa hannu haka sai yazo masa da abin arziki sai kaine zaka wulaƙanta nasa Iyayen ka kiyaye, jiya ta kirani ai Mamabisolan tana sanar dani rashin mutuncin daka tafka masa, a Company."
"Rashin mutunci kuma Hisham ɗin ya yiwa Tunde, Ramata."?
Abba ya tambayi Ummi cike da mamaki.
"Ƙwarai kuwa wai yaje Company da takaddunsa zai nemi aiki saboda inda yake aikin babu salary mai kyau, amma yaron nan Hisham sai cewa sakatariya yayi bazai gansa ba, hakan yaɓatawa Mamabisola rai shi kansa Tunde cewa yayi bazai koma ba."
"Yo ina zai koma yaje ɗan uwansa ya wulaƙanta sa, HISHAM anya kana son farin ciki na kuwa, Nameer!."
Abba yayi Maganar yana kwaɗawa Nameer kira, Nameer dake zaune a daining shida Tutu ne ya juyo tare da amsawa yana miƙewa ya taho garesu gefen Abba ya zauna yace.
"Lafiya Abba naga ɓacin rai a fuskar ka.?"
"Dole ai kaga ɓacin rai a fuskata tunda ku baku da mutunci."
"Abba me kuma mukayi.?"
"Dole ai ka tambaye ni wato saboda Tunde yaje Company neman aiki shine bari a wulaƙanta sa ko aƙi ganinsa bare aji meke tafe dashi."
Numfashi Nameer ya saki tare da cewa.
"Tunde kuma yaushe yaje Company, wallahi ban sani ba bani da labari."?
Kallon Hisham daya haɗa rai Abba yayi tare da cewa.
"Oh ashe kai ɗaya kayi tsiyar ya maka kyau, Nameer zan kira Tunde Monday zaizo company lallai ku gansa kuma ku amshi takaddunsa, ku tabbatar kun basa aiki a gurbin daya kamata wannan umarnina ne."
"Shikenan Abba insha Allah abinda kace haka za'ayi Allah ya huci zuciyarka."
Nameer ya yiwa Abba maganar cikin sanyin kalami tare da girmamawa, duban Hisham dake kumbura Abba yayi yace.
"Ba kumbura zakayi ba, ka fashe, sannan duk uzurin dake gabanka tsakanin yau da gobe ka ijiye sa kaje ka gaishe da Mamabisola idan ba haka ba ni da kaine."
Hisham shuru yayi ba tare da yace wa Abba komai ba, saima tashi da yayi yabar wajen, Da kallo Nameer ya bisa ganin ransa a ɓace yasa Nameer bin bayansa, kanta Ummi ta girgiza dai-dai Tutu na ƙarisowa ta zauna jikin Ummi.
"Hmmm! Abban Hisham, ni fa lamarin Hisham da Mamabisola yana bani tsoro, domin kuwa Hisham da gaske baya sonsu a shekaru irin na Hisham ya wuce ace sai an turasa yaje ya gaishe da Mamabisola, amma Abban Hisham menene duk hakan anya kuwa rayuwa zata yiwu a haka babu fahimtar juna tsakanin su, sune fa gatansa bashi da jinin daya wuce su a yau muka mutu dole sune zasu zame masa katanga."
"Ramata ni kaina wannan lamari na Hisham yana bani tsoro duk da Mamabisola ta taka muhimmiyar rawa wajen cusawa zuciyar Hisham tsanar su, a duk lokacin da zaka nunawa yaro ƙiyayya tun yana ƙaraminsa to tabbas zai tashi da haushinka, Ni da ɗan uwana Wale mun kasance cikin ƙaunar junanmu sai dai ita Mamabisola sam bata son hakan bata ƙaunar shaƙuwa dake tsakanina da Wale dalilin kenan daya sanya tabar gidan mu na gado ta koma gefe, tunda Baba ya mutu Mamabisola ta ɗaura min tsana har yau na kasa fahimtar laifin dana mata sai dai bana fatan hakan ya faru dasu Hisham shida Tunde, wato rashin zumunci da gaba."
"To Allah ya kyauta ya gyara lamarin, bara naje na gyara Room ɗin ka, ke kuma ki tashi ki tattara daining ɗin."
Ummi tayi Maganar tana tashi ta haura Room ɗin Abba.
Abba hannu yasa ya ɗauki jarida.


Dafe kansa Hisham yayi sosai ransa ya ɓaci, da faɗan da iyayensa suka masa, drowa ya buɗe tare da ɗauko sigari zai kunna, Nameer daya shigo ne yayi saurin sanya hannu ya fisge karan sigarin yana cewa.
"Wai da gaske bazaka daina shan sigari ba Hisham.?"
Idanunsa da suka kaɗa sukayi jajur Hisham ya ɗago ya kalli Nameer tare miƙa masa hannu cikin ɓacin rai da kaushin murya yace.
"Bazan daina ba, miƙon Abina!."
"Bazan bayar ba, ka ƙwace da ƙarfi."
"Nameeeer!"
"Hishammmm! Bazan bada ba, ka zauna muyi magana."
Shima Nameer ya masa maganar cikin tsawa dafe kansa Hisham yayi tare da zama yana kallon Nameer, kafaɗarsa Nameer ya dafa cikin taushin murya da alamun kwantar da hankali ya ce masa.
"Cool down Hisham, ka nutsu, ba komai ake ɗauka da zafi ba, ka fahimci Abba mana gaskiya yake faɗ.........
"Nameer! Ya isa bana son jin komai akan wadannan mutanen, ni ba ƴan uwana bane bana ƙaunarsu Nameer, ko dasu ko babu su zan iya rayuwata, meyasa dole sai nayi mu'amala da mutanen da basa ƙaunata Abba ya kasa gane hakan, Nameer ni kai ne ɗan uwana kaine rayuwata ka ishine rayuwa a matsayin jigo, idan kana kusa dani bazan nemi agajin kowa ba, ina jinka tamkar numfashina, akwai ka ƙyaleni bana buƙatar su."
"Hmmm! Hisham jigo baifi jini ba, ko ka manta da karin maganar Hausawa, jini yafi ruwa kauri, duk yadda zan kai ga ƙaunarka bazan maye gurbin jininka ba, ka yiwa Abba biyayya, dan Allah, kasan Abba bazai cutar da kai ba, ka shirya anjuma muje gidan Mamabisolan."
"Nameer Meyasa zaka tursasa zuciyata yin abinda bana so, ka sani bana iya musu da kai, tamkar Yayana na gaba dani haka nake kallonka."
Numfashi Nameer ya saki yace.
"Na sani Hisham, shiyasa nake son kayiwa Abba biyayya, meyasa baka sanar dani zuwan Tunde Company ba.?"
"Saboda nasan zaka sauraresa har ka basa aiki shiyasa ban sanar da kai ba, sannan ka sani ina kan bakata baza'a bawa Tunda Tunde aiki a Companyn mu ba, maganar zuwa gidan Mamabisolan kuma tunda ka matsa zanje."
Yayi Maganar yana saka kai ya kwanta saman bed ɗin, numfashi Nameer ya saki, domin kuwa har cikin ransa baya jin daɗin yadda Hisham ke jin tsanar Mamabisola, tollet ya tashi ya shige yabar Hisham kwance.


*********

Da shirinta ta fito bayan ta gamawa Umma duk wasu ayyukan ta, a baranda ta samu Umma zaune, kallonta Umma tayi tace.
"Ina zuwa kika fito cikin shiri bayan yau baki da aiki weekend ne.?"
Sunkuyawa tayi tare da cewa.
"Umma zamuje asibiti ne mu dubo wacce na ce miki moto ya bigeta mun kaita asibiti, ni da Basmah zamuje."
Kanta Umma ta girgiza tace.
"Ai na manta da zancen ma shaɗaf, to Allah ya tsare hanya ina mata sannu da jiki, amma ki dawo da wuri karki juma."
"To shikenan Umma."
Tayi Maganar tana miƙewa ta fice a ƙofar gidan nasu ta ga Abdullahi shida ABDULWASI'U suna zaune wajen shagonsa, kanta ta kawar tare da tsayawa ganin ta tsaya yasa Abdu tashi ya nufota.
"Ina zakije Adda.?"
"Zanje asibiti ina fatan ka mayarwa da wannan mutumin kuɗinsa.?"
"Ehh na maida masa kin bawa Umma kuɗin cefene ne.?"
Dafe kanta Jidda tayi tace.
"Kash kaga wallahi na manta ita kuma Umma bata tuna min ba."
Tayi Maganar tana sanya hannu taja zif ɗin jakarta dubu da dari biyar ta bawa Abdu tace ya kaiwa Umma na cefene amsa Abdu yayi tare da mata a dawo lafiya kafin ya shiga cikin gidan ABDULWASI'U cike da so da ƙauna yake kallon Jidda sai dai bata basa fuskar da zai mata magana ba, tunda yace yana sonta ta daina koda gaishesa, yana kallonta Basmah ta ƙariso da mai adaidaita ta shiga suka bar wajen.
"Dama nayi hasashen yanzu zaki ƙariso shiyasa ma na fito, jiya na kwana da tunanin halin da wannan yarinyar ta ke Allah dai yasa ta dawo hankalinta."
Jidda tayi maganar tana duban Basmah, numfashi Basmah ta saki tare da cewa.
"Ai kuwa mun kwana da damuwa ɗaya, domin nima da ita na kwana a raina."
Basmah tayi Maganar cike da tausayawa Yarinyar daidai sun iso harabar asibitin IBUNKU OLU CLINIC fita sukayi Jidda ta biya kuɗin kafin suka shiga basu sha wata wahala ba suka hango Aisha ƙanwar Ahmad zaune a bakin room ɗin da aka kwantar da Yarinyar, bayan sunyi sallama Aisha ta amsa Jidda ce tace.
"Aisha sannu, ya mai jikin dai, ta farfaɗo kuwa, wai ma ya kike zaune a waje."?
"Jikin nata da sauƙi sosai tama farfaɗo, likita ne a ciki shiyasa na fito waje, Aunty Basmah ina wuni."?
"Lafiya Aisha sannu da ƙoƙari, Allah ya saka da alheri, amma jikin babu wata matsala tana gane mutane.?"
"Ba matsalar komai tana gane mutane dan sanda ta farfaɗo naji tana kiran Abioye dana tambayeta waye ita sai tace Auntyn ta ne."
Girgiza kanta Basmah tayi tace.
"Okay to alhamdulillah."
Tayi Maganar dai-dai likita na fitowa, shiga sukayi suka sameta zaune jingine jikin gadon asibitin.
"Sannu baiwar Allah, ya jiki."
Sukayi maganar kusan a tare da kallon rashin sani take binsu kafin cikin raunanniyar murya ta amsa da.
"Jiki da sauƙi."
"Hmmm! Allah ya ƙara afuwa."
Cewar Jidda kafin Basmah tace.
"Baki gane mu ba ko, mune waɗanda muka kawo ki asibitin nan sanda moto ya bigeki, sannu ya jikin dai."?
Kafin tayi Magana Aisha tace.
"Sune suka ceci rayuwarki, sai ki gode musu."
Kanta ta girgiza tare da cewa.
"Na gode sosai tabbas da badan ku ba da wataƙila labarin mutuwa ake yanzu na gode ƙwarya da kuka ceceni daga hannun wannan azzalumin, da yanzu rayuwata ta lalace, wayyo! Abioye kizo ki koma dani imo state bazan iya rayuwar wannan garin ba."
Tayi Maganar cikin matsanancin kuka, cike da tausayin ta, Jidda ta zauna a bakin bed ɗin cikin tausayawa ta fara rarrashinta.
"Ya Isa haka ki daina kukan ba lafiya gareki ba nutsuwa da hotu kike bukata naga duk kina firgice har yanzu, waye azzalumin kin sansa ne sannan su waye iyayenki da alamu kinsan wanda ya bigeki.?"
Kafin tayi Magana Basmah tayi saurin cewa.
"Haba Jidda meye haka na jera mata wannan tambayoyin Yarinyar da take gadon asibiti, kwance babu ƙwarin jiki kike aikin jarida akanta, kya bari ai ta samu sauƙi a sallamata kafin ki jero mata wadannan tambayoyin."
Tsuka Jidda taja tare da cewa.
"Ƙanwata rabu da ita, naga jikin naki da ƙwari, wanda ya miki wannan aikin yana bukatar a

Please Login or Register in order to submit comment