Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya jurewa rashinsa na kwana goma ba bare kuma na tsawon rayuwa, Abban Hisham mu ɗauke Nameer daga wannan asibitin mu fita dashi waje watakila su zasu iya ceto mana rayuwarsa na shiga Uku idan na rasa Nameer."
Ummi tana kuka take wannan maganar, a wannan lokacin duk wanda ya zo ya wuce yaga wannan ahalin sai ya tausaya musu, kusan gigita Abba sukayi suka kuma tayar masa da hankali, ƙasa yayi tare da Hisham suka zauna cikin sanyin murya Abba yace.
"Ya ya kuke son nayi da rayuwata da wanne zanji da tashin hankalin ku ne ko da ciwon Nameer ko kuwa da fargabar wannan takaddar da tazo gareni, so kuke ku haukata ƙwaƙwalwata, Ramata da girmanki kike abu tamkar yarinya karama madadin ki rarrashi Hisham shine zaki sanya kuka kamar shi kina kin shiga Uku, ku sani babu yadda muka iya da ƙaddara a yau Ubangiji yaga dama zai ɗauki Nameer kuma babu yadda zamuyi dole muyi haƙuri dan Allah ku kwantar da hankalinku mubi komai a sannu ko nima zan samu nutsuwar da zan san Abin yi."
Kanta Ummi ta ɗaga tana cigaba da kukan Abba zame Hisham yayi daga jikinsa ya tashi ya koma wajen Doctor.


Ko da ya shiga sun tattauna sosai akan matsalar NAMEER tare da neman shawarar Doctor ko akwai inda yake ganin idan sunje zasu samu Nasara sai dai ina Doctor ya tabbatarwa da Abba sai dai suyi haƙuri domin kuwa duk inda zasuje wannan result ɗin za'a basu, haka Abba ya fito cikin sanyin jiki daga office ɗin, wajen Nameer ɗin suka koma dukkan su Abba ya zauna gefensa, ya zuba masa idanu cike da tausayin sa, ya taso tun yana yaro a hannunsa bai taɓa ɓata masa rai ba komai cikin ladabi da girmamawa yake masa, ko yaushe tunaninsa da burinsa akan yadda zai kare masa ahalinsa, yadda yake kula dashi ko Hisham ɗan da ya haifa a cikin sa baya masa wannan kulawar, da ace akwai inda za'a bawa Nameer rayuwa tabbas da komai nisan wajen sai yaje ko da dukiyarsa ne gaba daya zai iya kashewa domin ceto rayuwar Nameer, numfashi ya saki shi kaɗai yake zancen zucin Ummi kuwa tana rike da hannunsa.

Itama Tutu a gigice ta shigo asibitin ko da Ummi ta sanar da ita abinda ke faruwa da Nameer ihu Tutu ta sanya sosai hankalinta ya tashi Abba ne ya mata nasiha sosai kafin ta risina tabar kukan amma har yanzu tana ijiyar zuciya, Nameer bai farfaɗo ba har wajen karfe biyar na yamma, tunda ya buɗe idanunsa yake ƙarewa ɗakin kallo, akan Hisham da ya takure a gefe yayi shuru Nameer ya sauƙe Idanunsa.
"Hisham."
Ya kira sunansa ɗago idanunsa Hisham yayi tare da tashi da sauri ya nufesa kusa dashi ya zauna sai kuma yaji kuka yazo masa sai yanzu Hisham ya samu damar sakin kuka mai sauti yana kifa kansa a jikin Nameer idanunsa Nameer ya runtse cikin sanyin jiki yayi Magana.
"Tabbas kukan ɗan uwana gareni ya tabbatar da cewa mummunan abu na faruwa ga rayuwata, Abbana ka faɗa min me likita yace yake damuna karka ɓoye min Abba ka faɗa min zan rungumi kaddara tunda ni musulmi ne nasan bazan kaucewa kaddarata ba."
Wani irin tausayinsa ne ya kuma shiga zuciyar Abba shima hawayen ne ya ciko a idanunsa saurin mayar dasu Abba yayi gudun karya karyawa Nameer zuciya, Abba cikin tashin hankali da yanayin damuwa yace.
"Ba wata matsala bace fa Nameer likita yace zaka samu lafiya......
Saurin ɗago kansa Hisham yayi tare da katse Abba da cewa.
"A'a Abba karka ɓoye masa cutarsa kasa ya sanya rai ga abinda ba lallai bane ya tabbata, yana da kyau yasan cutarsa, domin ko ba komai zai san tanadin da zai yiwa goben sa, Nameer ba kai kake cikin damuwa ba mune, cutar a jikinka take amma mune muke jin zafin ciwon, mune muke cikin tashin hankali da masifa domin kuwa rasaka garemu masifa ce Nameer babbar masifa ma, zan shiga cikin kuncin rayuwa komai zai ƙwace min muddun na rasaka, kaine fitilar rayuwata ta yaya zan koyi rayuwa ba tare da kai ba, likita yace kana ɗauke da *KANSAR ƘWAƘWALWA* yace bazaka wuce wata biyu ba a duniya zaka mutu, amma nasan karya yake zaka rayu, zamu cigaba da rayuwa tare bazaka mutu ka barni ba sai dai ni na mutu na barka."
Yayi Maganar yana kuka har da majina idanunsa sunyi jajur, idanunsa Nameer ya runtse madadin ya shiga cikin tashin hankali sai murmushi ya saki tare da kamo hannun Hisham, gaba ɗaya da mamaki suka kallesa ganin murmushi a fuskar sa madadin tashin hankali.
"Wai kuka kake Hisham saboda Yar wannan maganar, ni fa mai rai ne dole ne wata rana zan mutu Meyasa zaku damu akan abinda yake kan kowa, dukkan mu zaman jiran mutuwar muke, dan haka ku daina damuwa, idan na mutu ba ga ka nan ba Hisham, zaka kula mana da Abba da Ummi da Tutu bazaka bari suyi kukan rashina ba, ku daina damuwa Ubangiji ya gama tsara lamarinsa a kaina karkuyi fushi da ikon Ubangiji muyi haƙuri sai mu ci jarabawar mu, ummina Abbana ku daina kuka muddun kuna son na cigaba da dariya kafin lokacin mutuwata."
Hawayen fuskarta Ummi ta goge tare da kamo hannunsa tace.
"Hakane Nameer insha Allah ma zaka rayu, zamu cigaba da nema maka inda zaka samu lafiya."
Abba shima nasiha ya dinga yiwa Nameer yayin da sai murmushi yake yana jansu da tadi har Hisham ya ɗan sake, Tutu ma duk kukan da take sai da Nameer yasa tayi dariya.
Ranar Hisham ne ya kwana tare da shi a asibiti, washegari da safe Ummi ta taho da breakfast ita da Tutu, wajen sha biyu na rana Mamabisola tazo asibitin, bata samu Abba ba sai Ummi da Hisham, cikin girmamawa Ummi ta bata waje.

"Sannu da zuwa Mama."
Ummi tayi Maganar cikin girmamawa, da yauwa Mamabisola ta amsa tare da cewa.
"Yanzu nake jin labarin abinda ke faruwa da Nameer, Iyabo ya kiran yake sanar dani, Allah ya basa lafiya."
Da ameeen Ummi ta amsa kafin Mamabisola ta kuma cewa.
"Ramata garin yaya wannan mahaukacin ɗan naki yayi gangancin sakewa ma'aikata har akayi kisan kai a cikin ma'aikata, hmm! Iyabo yace min mahaifin yaron da aka kashe ya shigar da Companyn ku ƙara kuma wannan duk gangancin y'ay'anki ne, zaku samin Iyabo cikin masifa dan yanzu ma gashi hankalin sa ya tashi."
Nameer dake kwance ne ya ɗan zaro idanunsa yana kallon Hisham, kansa Hisham ya girgizawa Nameer yana hucin maganganun Mamabisola, Ummi ce mata tayi.
"Bamu da hakkinsu insha Allah babu abinda zai faru, gaskiya zatayi halinta."
Murmushi Mamabisola ta saki tare da cewa.
"Abinda zai ceci wannan Company hujja ce kawai kuma ance babu ita ku dai kun jawowa IYABO masifa, to dama Ramata ya ya za'ayi abinda kika haifa yayi albarka shima Iyabo ai yasan abinda ya debowa kansa, ni kinga tafiyata."
Tayi Maganar tana tashi ta fita daga room ɗin, numfashi Ummi ta saki tare da kallon Hisham da ke famar huci, zaiyi magana ta ɗaga masa hannu.
"Duk abinda yake cikinka ka mayar dashi, Mamabisola Tana da ikon da zata dakeni ma bare duka, uwa na ɗauketa dan haka bana son naji kayi wata maganar a kanta."
Shuru yayi tare da mayar da kansa gefe Nameer ne yace.
"Alhaji Sagir ne ya shigar da Company ƙara.?"
"Eh Nameer nayi mamaki kwarai domin kuwa shi da bakinsa yace ya yafe."
Shuru Nameer yayi ya kasa magana domin kuwa maganar ta ɗaga masa hankali.
Hisham ne ya tashi ganin kiran Jidda yasan ta jisa shuru ne shiyasa ta nemesa bata san abinda ke faruwa da Nameer ba, fita waje yayi ya amsa wayarsa, Abba bai dawo asibitin ba har wajen la'asar lis ko da Ummi ta tambayesa inda yaje yake sanar da ita yaje sun gana da Chief judge ne akan karar da Alhaji Sagir ya shigar ya ce har Alhaji Sagir yaje ya samesa amma yana nan kafe akan lallai sai an shiga kotu, kanta Ummi ta jinjina tare da tambayar Abba yaya za'ayi.
"Hmmm! Wallahi ban sani ba Ramata sai an shiga kotun dai musan abinda zai faru wadannan yaran ne suka min shirme da tun fari sun sanar dani da na yiwa tufkar hanci tun wuri, kai Nameer yaya jikin naka.?"
"Da sauƙi Abba, kayi haƙuri Abba ba laifin Hisham ba ne, ni ne na hana a sanar da kai abinda ke faruwa gudun kar mu ɗaga maka hankali bamuyi zaton lamarin zai rincabe haka ba, dan har munyi magana da Alhaji Sagir ɗin ya tabbatar mana da ya yafe, yaushe sukace za'a shiga kotun."?
"Akan Monday sukace amma na samu Chief judge na roki alfarmar a daga shari'ar zuwa ka samu lafiya, yanzu sai last this month zamu shiga kotun, maybe shawara ya sauya gani yake bazai iya haƙuri ba, Doctor ya bamu sallama zamu iya komawa gida yanzu."
"To Abba maganar Hisham da Jidda fa."?
"Yau da daddare Alhaji Bawa zai kawo sakamakon binciken da yayi, mu jira sa tukunna."
Kansa NAMEER ya kaɗa shi dai Hisham yana ji baiyi magana ba Ummi kuwa haɗa ranta tayi cike da haushi basu fi minti sha biyar ba, suka haɗa komai suka taho gida.
Hisham bayan ya sauƙe su ne ya juya da kan motarsa zuwa gidan su Jidda a ƙofar gida ya tsaya ya kirata a waya kusan minti goma da kiranta ta fito sanye da Hijab har ƙasa motar ta bude ta shiga tana duban Hisham.
"Zuciyata har ta fara dukan Uku Uku ɗazu da naji shurun yayi yawa, gashi weekend ba aiki bare nasan halin da kake ciki, ya jikin yaya Nameer ɗin, meke damunsa.?"
Numfashi Hisham ya saki yana jingina kansa da site ɗin motar kafin cikin damuwa yace.
"Ina cikin tashin hankali Jidda makiya sun sako rayuwata a gaba, ga tashin hankalin Nameer na fara saduda da rayuwa Jidda, babu makawa makiya sunci galba a kanmu, domin kuwa ina ji a jikina za'a rufe Companyn mu, ga kuma Nameer yana tsakiyar rayuwa da mutuwa, bashi da lafiya Doctor ya tabbatar mana da cewa KANSAR ƘWAƘWALWA ke damunsa yace Nameer bazai haura wata biyu ba a duniya zai mutu, rayuwar nan babu komai a cikin ta Jidda sai tarin bakin ciki."
Wani irin razana Jidda tayi tare da furta.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Hisham me kake faɗa min, Yaya Nameer ɗin ne yake cikin wannan halin, kai ina faɗar likita ai ba faɗar Ubangiji bane, a dai sauya wani asibitin aji su kuma me zasu ce.?"
"Hmmm! JIDDA kenan lokacin da likita yace Sadiq yana halin rayuwa ko mutuwa ai haka kikace kuma yazo ya mutun, kawai dai Jidda ina cikin tashin hankali, mtsss Hmm! Nazo na ganki ne kawai na tafi kije kawai kaina yana ciwo zanje na kwanta."
"Amma Hisham ina bukatar lokacinka fa, daga zuwa sai tafiya."
"Please JIDDA ki barni na tafi, wallahi jiri nakeji na juma anan bazan iya kai kaina gida ba, nazo ne na ganki ko zan samu sukuni."
Kanta Jidda ta kaɗa tace.
"Shikenan ka gaishe da yaya Nameer ɗin insha Allah gobe zanzo na gaishe sa."
Da zaiji Hisham ya amsa sanda Jidda ta shiga gida kafin ya tafi.



******


Ko da daddare Nameer yana kwance a gefen Abba Shi kuma Hisham yana zaune kan kujera Alhaji Bawa ya shigo shida Alhaji Ahmed, tashi Nameer yayi ya zauna Abba duban Hisham yayi yace yaje ya kira Ummi tashi yayi yaje ya kirata suka dawo tare itama gefen Abban ta zauna tana cewa su Alhaji Bawa.
"Barkan ku da zuwa Alhaji Bawa Alhaji Ahmed Barka."
Cikin fara'a suka amsawa Ummi Nameer da Hisham ma gaishe su sukayi har suna tambayar NAMEER jikinsa, Abba ne yace.
"Alhaji Bawa tun dazu na ke sauraron zuwan ka, Allah dai yasa binciken da kukayi akan Yarinyar an samu sakamako mai kyau."
Shuru Alhaji Bawa yayi sai Alhaji Ahmed ne ya nisa yace.
"To Alhaji maganar gaskiya dai anje anyi bincike da farko yaron wajena Kabiru na aika unguwar su Yarinyar ya min bincike, sanda ya kawo min sakamakon ban daddara ba na koma da kaina na sake bincike shima Alhaji Bawa da kansa yaje yayi binciken abun mamaki gabaki ɗaya sakamako ɗaya muka samu babu wani sauyi, da farko dai ita Yarinyar bata da wani aibu kowa Alkairi yake faɗa a kanta tana da riƙon addini ga girmama manya, mahaifin yarinyar bahaushe ne haka kuma mahaifiyarta bahaushiya ce mahaifiyarta ne yaruba, Alhaji IYABO, akwai babbar matsala gaskiya, dangin mahaifiyar Yarinyar duk mijin da ya auresu farko sai ya rasa rayuwarsa, gaba daya haka suke, ita na mahaifiyar Yarinyar yafi tsananta domin kuwa maza huɗu ta aura duk basa wuce sati da Auren suke mutuwa, shine dalilin da yasa aka kyamace ta tabar cikin Yan uwanta ta dawo gefe ta zauna, wannan itace matsalar Alhaji Iyabo, duk wanda ya auresu da fari mutuwa yake, sannan kakar Yarinyar uwar mahaifiyarta kenan ance cikakkiyar ƴar bariki ce, amma ita yarinyar bata da matsala, wannan shine abinda muka binciko kuma mun tabbatar da gaskiyar lamarin haka yake."
Kansa Nameer ya dafe, Abba numfashi ya saki kafin ya kalli Hisham da yake kallonsu hankali tashe domin kuwa a yanzu yana jin Soyayyar Jidda sama da komai a rayuwarsa yana jin cewa zai iya rayuwa da ita a ko wani hali, ya ijiye duk wata ɗaukar fansa da yayi niyya a gefe, a yanzu da gaske yake jin Soyayyar ta, ƙirjinsa ya dafe dake dukan Uku Uku Muryar Abba yaji yana cewa.
"Subahanallah! Alhaji Ahmed, gaskiya wannan ba irin da za'a aura ba ne, bazai yiwu Hisham ya auri wannan Yarinyar ba, menene amfanin auren da babu jin daɗin rayuwa, sati ɗaya miji ya mutu, no Hisham kayi haƙuri da wannan Yarinyar ka nemi wata ka dai ji da kunnen ka, Nameer ka basa shawara ya nemi wata, Ramata kema ki faɗawa danki babu Aure tsakanin sa da wannan Yarinyar, Alhaji Bawa na gode sosai."





_____________________________________







_Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to insha Allah Book One ya kusa zuwa karshe, alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._



*0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180*




*Like Share and comments my fan's🥰*






_UMMU NASMAH CE✍🏻_
[7/25, 9:13 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*




*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*





*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻




*FREE BOOK ONE 📚*



_Wannan littafin ba free bane na kuɗi ne Book one shine Free kuma mun kusa zuwa karshen Free zamu shiga Book two inda zaku cigaba da karatun wannan littafin akan 200 kacal ban tsawwala ba farashin da zaku iya biya na sanya dan Allah idan har kina son wannan littafin kina bibiyar sa kizo ki biya kudin ki, ki cigaba da karatun sa akan farashi ƙalilan, karki yadda ki kasance cikin ɗaya daga cikin masu cin hakkin wani 08147537180._




*_Page 57 to 58_*



Idanunsa Hisham ya kuma runtsewa tare da cije lebensa yana jin maganar Abba tamkar yana zuba masa ruwan zafi a jikinsa, Muryar Ummi ne ya kuma dukan kunnen Hisham.
"Dama ni ai Abban Hisham da ka saurareni tun fari baza'a kai zuwa wannan lokacin ba zamu rabasa da yarinyar amma tunda yanzu yaji da bakinsa zai haƙura dole ai."
Numfashi Alhaji Ahmed ya saki tare da tashi suka yiwa Abba sallama, shima Abba tashi yayi ya rakasu har ya dawo Hisham bai ce komai ba, Abba ne yace masa.
"Muna magana Hisham kayi shuru tamkar baka wajen, bakaji abinda ake magana bane.?"
Abba ya jefa masa tambayar sai yanzu Hisham ya ɗago idanunsa da sukayi jajur ya kallesu tare da cewa.
"Ina jin ku Abba, to me zance muku, ni na amince ko wacce irin mummunar kaddara Jidda ta ke ɗauke dashi ni na amince zanyi rayuwa da ita a haka, Abba Ƙaddara rayuwa bata nufin karshen mafarkin Rayuwa, Jidda kaddarata ce ko iya soyayyar ta da nakeji a raina ya nuna min cewa Jidda kaddarata ce, da farko ba son gaskiya nake yiwa Jidda ba Abba a nufina na kona zuciyarta da soyayya domin ɗaukar fansar abinda ta yiwa ɗan uwana Nameer sai Ubangiji ya juya lamarin sa ya sanya min Soyayyata na haƙiƙa a raina bazan iya jagorantar rayuwata ba dole sai da ita Abba, ba dole ace kaddararta da ta ahalinta ɗaya ba ne, kayi haƙuri bazan iya bin umarninka ba akan rabuwa da Jidda, ina son Jidda na amince idan na aureta na mutu ko ba komai zan mutu cikin farin ciki da cikar muradina, *KO BAKU AURA MIN ITA BA DOLE SAI NA AURE TA, BA ZAN TAƁA RABUWA DA ITA BA KO MAI ZAI FARU KO DA HAKAN YANA NUFIN KARSHEN NUMFASHI NA NE.*
Yayi Maganar a zuciye yana tashi ba tare da tsayawa sauraren abinda Abba zaice ba zai bar wajen, Muryar Nameer ya dakatar da shi.
"Tabbas ƙaddarar rayuwa bata nufin karshen mafarkin rayuwa Hisham na yarda da wannan maganar taka, sai yanzu na fahimci ƙaddarar ciwo na, da alamu Ubangiji yana nufin ni ne zan fanshi rayuwar ɗan uwana, bani da doguwar rayuwa a wannan duniyar, wata biyu ne ya rage min zanyi amfani da wannan kwanakin domin ceto Soyayyar ɗan uwana, zan kasance mijin Jidda na farko domin bawa Hisham farin ciki na tsawon rayuwa, zan auri Jidda idan na mutu ka samu damar kasancewa da ita a matsayin mata ba tare da wani tsoron mutuwa ba, Abba ni zan auri Jidda idan na mutu Hisham ya kasance da ita na har abada."
Tunda suka fara Maganar Abba ke bin Hisham da kallon mamaki duk da yasan zuciyar Hisham amma bai taɓa tsammanin zai iya kallon idanunsa ya ce zai juya masa baya akan mace ba, kafin Abba yayi Magana Ummi tace.
"Akan wannan matsiyaciyar Yarinyar zaka sadaukar da rayuwarka Nameer wa ya ce maka bazaka rayu ba, zaka samu lafiya Nameer a wannan asibitin kawai mukaji furucin su bamu ji na wasu asibitin ba, zamu je asibitin Doctor Barde shima zai ƙara gwadawa bazamu tsaya ba har sai ka samu lafiya, kai kuma Hisham a wannan karon bazan ɗauki iskancinka ba, tabbas zan koya maka hankali, dole ka rabu da ita dan ubanka ai ba tsoronka mukeji ba bare ka juya mu yadda ranka yake so shasha."
Ummi tayi Maganar cikin ɓacin rai, shi dai Hisham bai ce komai ba bayan wannan maganar da yayi, Nameer zaiyi magana Abba ya ɗaga masa hannu tare da cewa.
"Ya isa haka, duk ku tafi ku bani waje, ya maka kyau Hisham na gode iyakata ka nuna min kaje kayi abinda kake so kaje maza ka nemi wasu iyayen da kake dasu bayan mu su nema maka Auren mu ai bamu isa da kai ba ."
Wani irin sanyi jikin Hisham yayi, kansa ya girgizawa Abba tare da cewa.
"Kayi haƙuri Abba wallahi kun isa dani, ka fahimce ni Abba ina son Jidda wallahi bazan iya rabuwa da ita ba Please Abba ka taimakeni ka Aura min ita ko da ita ko babu ita bazan taɓa tsallake wa'adin da Ubangiji ya min ba a duniya mu yarda da ƙaddara nas...............
"Ka shige ka bani waje Hisham!."
Abba ya dakatar dashi a zafafe cikin tsawa, idanunsa Hisham ya runtse tare da barin wajen cikin kunar rai, bayansa Nameer yabi da sauri Ummi Abba ta duba tare da cewa.
"Nasha faɗa maka cewa mu daina biyewa Hisham muna masa duk abinda yake so amma kaƙi saurarana, duk abinda Hisham yayi a wajen ka daidai ne yau ga irinta nan ya nuna maka bazai yadda ya rasa abinda yake so ba, saboda ka saba masa da samun duk abinda ya nema."
"Ramata karki ɓata min rai da maganar banza, ko yanzu ma ba hanasa abinda yake so nayi ba, rayuwarsa nake son karewa da ace Yarinyar nan bata da wannan tabon mutuwar to da tabbas zan aura masa ita, sannan ko yanzu idan har aka samu ƙaddarar da zata sauya wannan tabon mutuwar to tabbas zan aura masa yarinyar."
Cike da mamaki Ummi ta ke kallon Abba.
"Abban Hisham har akwai wata kaddarar da zata sauya mutuwa, oh na fahimta saboda muradin danka ya cika ka yarda ya aureta ko da zai rasa rayuwarsa, hakan Soyayya ce, kai fa kace ya haƙura da yarinyar yanzu kuma ka sauya maganar me yaja hankalinka haka.?"
"Ni ne Ummi ni ne naja hankalinsa, da ku rasa mu gabaki ɗaya gwara a rasa ɗaya dole dai ni mutuwa zanyi, ki yarda da ƙaddara Ummi, Doctor Sabo bazai faɗi result ɗin karya ba akan ciwo na, ko da asibiti ɗari zamuje amsar dai ɗaya ce waye kika ga mai KANSAR ƘWAƘWALWA ya yi doguwar rayuwa ya kamata mu yiwa kanmu hisabi idan rai ya ɓaci mu kai zuciya nesa Ummi Hisham yana son Yarinyar nan ya kamata ki barsa ya aureta, Ummi auran Jidda da zanyi shine kawai zai ceto Hisham daga mutuwa, ban taɓa neman alfarma a wajenki ba Ummi, amma yau zan nema, idan har kika min haka Ummi shine zai tabbatar min da kinfi kowa ƙaunata a duniya, kuma zan mutu ina farin cikin wannan alfarmar da kika min dan Allah Ummi."
Hawaye ne ya zubo daga idanun Ummi, tare da takawa taje gaban Nameer ta tsaya.
"nasan alfarmar da zaka nema a wajena Nameer bazan iya ba, bazan iya kallo kasa rayuwarka a cikin haɗari ba, duk da yanzun ma Rayuwar taka acikin haɗari take, Nameer

Please Login or Register in order to submit comment