Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Wannan wacce irin tambaya ce Hisham da ina da budurwa ai da ka sani bani da ita, amma meyasa kamin wannan tambayar."?
Numfashi Hisham ya saki yana gyara zamansa yace.
"Saboda ina son ka nemi ƙanwata Tutu, amma fa sai idan kaji ta maka babu dole."
Murmushi Sadiq ya saki yace.
"Kai ka isa kamin dole ne Hisham, ka sanni sarai bana ɓoye maita ta, Tutu ba Macen da za'a ce ba'a so bane Hisham sai dai ka gane Soyayya tana buƙatar haɗuwar jini, amma ita ka tuntubeta ne."?
"A'a ban tuntunbeta ba tukunna nafi bukatar na fara ji daga gareka, na tabbata ita bazan samu matsala da ita ba, Sadiq kai Mutum ne na ƙwarai da kowa zaiso haɗa zuri'a da kai shiyasa na yiwa ƙanwata kwaɗayin samun ka a matsayin mijin aurenta."
"Karka damu Hisham kaje ka tuntunbeta idan har ta amince ni bani da matsala, waye zaiki haɗa zuri'a daku Hisham sai dai marar rabo."
Dariya Hisham ya saki yana ɗaukar sigarinsa ya saka a baki tare da kunna mata wuta kafin yace.
"Kai kuma bazaka zamo cikin marassa rabo ba ko, ya labarin wannan shegen ne Dawud."?
"Kai dalla bar zancen ɗan iskan nan ka sanya a kawo min tea ɗin na samu na bawa hanjina hakkinsa, sigari dai ta zamo maka ɗabia Hisham."
Dariya yayi yana ɗaga waya ya kira sakatariya yace tasa a kawo tea da bread kafin ya dubi Sadiq yace.
"Ba ɗabia ta zame min ba rayuwa ta zame min musamman idan ina cikin damuwa nafi jin daɗin ta."
"Kuma kafi kowa sanin illarta ba."
Yayi Maganar dai-dai Sakatariya na shigowa da tea ta ijiye a tebur ɗin kafin ta juyawa, jawo tea ɗin Sadiq yayi tare da bread ɗin a hankali ya fara sha suna hira da Hisham har ya gama shan tea ɗin yana ijiye cup ɗin cikinsa yayi wani irin juyawa idanunsa ne suka firfito waje ya fara wani irin gurnani a ɗan gigice Hisham ya miƙe yana yasar da sigarin hannunsa ya take tare da furta.
"Subahanallah! Sadiq meke faruwa, me yake damunka what kumfa a bakinka Sadiq!''?
Hisham yayi Maganar da ƙarfi yana zagowa ya tallafo Sadiq cikin tashin hankali magana ma ta gagari Sadiq saboda shakewar da wuyansa yayi, idanunsa ya zazzaro numfashin sa sai sama sama yake yana neman daukewa, security Hisham ya dannawa kira cikin gaggawa suka shigo office ɗin kafin kace me zance ya karade Companyn Jidda da Nameer kusan tare suka shigo Nameer shiya kira Police ya sanar dasu, cikin gaggawa kuwa sukazo akayi asibiti da Sadiq yayin da sai shidewa yakeyi kowa da ke cikin Companyn ya shiga cikin tashin hankali, Tunde ma ya shigo sai hankalinsa yayi matukar tashi kar fa ace gubar nan Sadiq yasha, tare suka dunguma zuwa asibitin Nameer da Hisham har Jidda, Take likitocin suka ruhu a kansa, Hisham sosai hankalin sa ya tashi, sai kaiwa da komowa yake ya gagara samun nutsuwa, likitocin sun juma sosai kafin suka fito, doctor yace su Hisham su samesa a office.
Koda sukaje likita ya tabbatar musu guba yasha mai haɗarin gaske kuma shine last abincin da ya ci tare da cewa suna bukatar suga last abinda yaci, a firgice Hisham ya miƙe tare da furta.
"What! Last abinda Sadiq yaci shine tea kuma a office ɗina yasha, ta yaya hakan zata faru, kaga Doctor tukunna a wani hali Sadiq yake ciki.?"
Doctor ne yace.
"Muna bukatar sauran tea ɗin ko cup ɗin da aka sha tea ɗin domin mu gwada muga irin gubar da akayi anfani dashi a yanzu dai haka Sadiq yana halin rayuwa ko mutuwa gaskiya saboda dole sai mun san kalar gubar gubar kafin mu san treatment ɗin da zamu masa na ainihi duk yanzu ma munyi iya bakin ƙoƙarin mu, amma bamu muku alƙawarin zai rayu ba gaskiya."
Numfashi Hisham ya saki tare da dafe kansa Nameer ma sosai hankalinsa ya tashi guba a cikin Companyn su waye yake ƙoƙarin kaiwa rayuwarsu farmaki, wato Hisham aka so kashewa lamarin ya sauƙa akan Sadiq waye ne.
"Hisham ya akayi haka guba kuma a Companyn mu, Hmm! Lamarin ya bani mamaki sosai, ya kamata Police suje suyi bincike."
"Ni kaina mamakin da nake kenan Nameer sakatariya ce ta kawo tea ɗin itace first target ɗin da za'a zarga, Inspector Lawan yana can Companyn zaiyi duk abinda ya dace ni aka so kashewa ba Sadiq ba, doctor muje da nurse ta ɗauko kuma cup ɗin."
Hisham yayi Maganar yana miƙewa jikinsa a sanyaye cike da mamakin yadda hakan ta faru.



_____________________________________







_Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._



*0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180*



_Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan auli yasmut siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai._



*Like Share and comments my fan's🥰*






_UMMU NASMAH CE✍🏻_
[7/20, 8:35 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*




*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*





*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻




*FREE BOOK ONE 📚*



_Wannan littafin ba free bane na kuɗi ne Book one shine Free kuma mun kusa zuwa karshen Free zamu shiga Book two inda zaku cigaba da karatun wannan littafin akan 200 kacal ban tsawwala ba farashin da zaku iya biya na sanya dan Allah idan har kina son wannan littafin kina bibiyar sa kizo ki biya kudin ki, ki cigaba da karatun sa akan farashi ƙalilan, karki yadda ki kasance cikin ɗaya daga cikin masu cin hakkin wani 08147537180._




*_Page 51 to 52_*




Numfashi Nameer ya saki cike da tunani gabaki ɗaya Companyn suka koma sun sami Police suna ta famar bincike, inspector Lawan da kansa ya dage wajen binciken, Zainab sosai ta shiga cikin tashin hankali domin kuwa ta rasa ya akayi akayi sauyin cup ɗin har Sadiq yasha gubar duk da bata san akwai alaqa tsakanin Tunde da Sadiq ba, cikin tashin hankali Tunde ya nufi Zainab ganin an tsawaita bincike tana nan tsaye itama cikin tashin hankali ya iske ta.
"Bana faɗa miki cewa kar a samu kuskure ba, meyasa zaki min wannan shirmen kinsan rayuwar waye kuwa kika sanya cikin hadari, yana da matukar muhimmanci a rayuwata, kin riga kin aikata kuskure amma ki sani karki kuskura a san cewa kece kika sanya wannan gubar idan har akayi ƙoƙarin ganoki babu shakka kafin a iso gareki zan ɗauke numfashin ki."
Yayi Maganar yana nuna mata yatsa tare da barin wajen cikin hanzari, numfashi Zainab ta sauƙe tana huci ta furta.
"Babu wanda ya ganni da zan aikata haka kuma babu wanda ya isa ya gano ni ko shatin yatsata bai taɓa cup ɗin ba bare nayi tunanin tashin hankalin rayuwa."
Tayi Maganar tana sakin murmushi, can kuwa nurse da police ɗaya suka koma da cup ɗin tea ɗin asibiti inda darect sukayi lap da shi domin gwada launin gubar, Duk binciken Police ɗin ya ta'allaka ne akan sakatariya da Esther wacce itace ta haɗa tea ɗin.
Sosai sakatariya ta shiga tashin hankali, Inspector Lawan ne ya sasu su biyun a gaba sukayi asibitin za'a gwada zanen yatsunsu, shi kansa Hisham lamarin ba ƙaramin ɗaga masa hankali yayi ba wunin ranar haka sukayi shi cikin bincike da tashin hankali sai Nameer bai yadda an sanar da Abba abinda ke faruwa ba.

Dukkan su babu wanda ya samu damar barin cikin Companyn har sai da suka kai 6:30pm kusan kiran magaruba dan har sai da Police suka dawo da sakatariya da Esther tukunna, Hisham Jidda ya ɗauka ya Kaita gida.





********



Ƙafafuwan sa ya tankwashe a gabanta yayi shuru, yayin da ranta ke ɓace cikin hasala tace.
"Wace shegiya daƙiƙiyar ka bawa wannan aikin, idan har Sadiq ya rayu ba lallai ya ƙyale mu ba, domin kuwa cewa zaiyi gangancin mu ne, koma yace da gangan muka aikata masa hakan saboda ya nemi wani abu daga cikin dukiyar da muke hari, ya kamata yarinyar nan ta fuskanci hukunci, a wannan karon idan har Hisham ya gano akwai hannun mu cikin sanya wannan gubar wallahi sai ya tarwatsa rayuwarmu."
Kansa Tunde ya girgiza tare da cewa.
"Mtsss! Mama ban taɓa zaton cewa Zainab zata min ganganci ba, sai dai ki sani bazata taɓa bari a gane itace ta aikata ba, asirin mu bazai tonu ba, baƙin ciki na ɗaya ne Mama na tarwatsewar mission ɗin nan banso ace Nameer ya tsallake wannan tarkon ba, naji baƙin ciki sosai, Mama karki damu wannan gubar bazata bar Sadiq ya rayu ba bare ya zamo barazana a rayuwar mu shine ya tabbatar min da ƙarfin gubar duk wanda yasha yace bazai rayu ba dan haka karki damu Sadiq tasa yazo karshe."
"Amma Sadiq yana da mahimmanci a aikin mu rashin sa wata matsalar ce fa, waye zamu samu na jikin Hisham wanda zai iya mana wannan aikin shine babban tashin hankali na, domin Sadiq shine jigon aikin mu."
"Hmmm! Na sani Mama amma ki sani bazamu rasa ba, gari da yawa maye bazai ci kansa ba, ke dai ki cigaba da addu'a, sannan Mama dole fa sai kunje kauyen nan da Wamimo domin kuwa bazamu iya kaisu ƙasa ba dole sai mun haɗa da asiri."
Shuru Mamabisola tayi tana tunani kafin ta ɗaga kanta tace.
"Shikenan, zan nemi Wamimo zamu san yadda za'ayi kaje ka ci abincin ka."
Kansa Tunde ya girgiza tare da tashi yabar wajen, bayan ya fita ne Mamabisola ta miƙe tsaye cike da tunanin yadda zata bullowa lamarin domin kuwa taga lamarin yana shirin fin ƙarfinta muddun tayi wasa kwabarta zata mata ruwa.
"Lallai dole Wamimo tazo muje ƙauyen nan na Agunjin."
Tayi Maganar tana sakin numfashi cike da damuwa wayarta ta ɗauka ta kira Wamimo sukayi magana akan tafiyar sun juma suna waya kafin sukayi sallama.




**********


"Meyasa zaka sawa kanka damuwa haka bayan Police suna nan suna bincike, dole kasan zasu gano wanda ya aikata wannan aikin bazai tsira ba tunda akwai CCTV Camera."?
Kansa Hisham ya girgiza yana kallon Jidda cike da damuwa yace.
"Har yanzu baki fahimci damuwata ba Jidda, damuwata rayuwar Sadiq ne idan Sadiq ya mutu ta wannan dalilin bazan yafewa kaina ba domin silata hakan ta faru dashi, Sadiq wani tsagi ne na rayuwata Jidda, mutumin kirki ne da babu ruwansa bashi kyashi ko mugunta bare kuma hassada, gashi can a tsakanin rayuwa ko mutuwa babu tabbacin zai tashi, da ace zansan wanda yayi wannan aikin babu makawa sai na kashe sa kafin aje ga hukuma, ina jin zafin halin da Sadiq ya shiga da wani ido zan kalli mahaifinsa tun ɗazu na gagara komawa asibitin da akace Alhaji Sagir mahaifinsa yaje."
"Insha Allah ina da yakinin babu abinda zai samu Rayuwar Sadiq insha Allah zai tashi, rayuwarsa tana hannun Ubangiji ne ba na likita ba faɗa ne kawai nasu, amma ainihin sanin gaibun yana hannun Ubangiji, ka daina ɗagawa kanka hankali insha Allah komai zai tafi normal."
Bakinsa Hisham ya cije tare da cewa.
"Hmmm! Jidda rayuwata aka nema bata Sadiq ba domin kuwa ni nace akawo min tea ba tare da sanin waye zai sha ba kinga kuwa ni aka so kashewa ya faɗa kan Sadiq."
"Karka ce haka waye kake dashi maƙiyi a wannan Companyn da zai nemi rayuwarka naga zaman lafiya kuke da kowa cikin mutuntawa da ƙaunar juna tunda na fara aiki ban taɓa ganin Company mai haɗin kai daya burgeni irin Companyn ku ba."
Murmushin takaici Hisham yayi yace.
"Kin manta kenan da fyaden da Khabeer yaso miki kuma a cikin Companyn namu, a hakan ne kike yabon mutanen cikin ta, ɗan adam ba abin yadda ba ne Jidda, ina da makiyin da zai iya neman rayuwata."
"Ban fahimta ba waye wanda zai iya neman rayuwar ka a cikin Companyn.?"
"Tunde.?"
"What!?"
Jidda ta furta tana zaro idanunta cike da mamaki.
"Ƙwarai kuwa, meyasa zakiyi mamaki ko kin manta abinda ya faru ne a baya na Case ɗin Hajara ko kin manta da shine ya sanya Hajara ta yiwa NAMEER sharrin fyade duk wanda zai maka sharrin fyaɗe to tabbas zai iya kasheka."
"A'a ban manta ba, amma wannan bashi zai baka hujjar cewa Tunde zai nemi rayuwarka ba, zato zunubi ne ko da ya kasance gaskiya, idan baya ta wuce babu amfanin a tuno sa, amma naga kai kamar baka manta ba, alkairin baya ake tunawa ba sharrinsa ba."
"Kina da saurin manta maƙiyi Jidda da wannan zuciyar taki wata rana za'a cutar da ke, ki shiga gida ana kiran sallah nima zan shige."
Yayi Maganar yana buɗe mata murfin motar, kanta Jidda ta girgiza tace.
"Dan Allah ka samu nutsuwa insha Allah babu abinda zai faru sai Alkairi."
Tayi Maganar itama tana fita daga cikin Motar da kallo Hisham ya bita ba tare da yace komai ba har ta shiga gida, kafin yaja motar sa yabar wajen ransa cunkushe da damuwa.


Ko da Hisham ya koma gida ma ya samu Nameer dasu Ummi a falo a zaune suna ta jajanta maganar, inda Nameer ya hana Ummi sanar da Abba maganar gudun kar a ɗaga masa hankali baya ƙasar, ranar haka suka kwana cikin yanayin rashin jin daɗi musamman Hisham da yakejin zafin abinda ya faru da Sadiq shi Nameer tashin hankalin ma biyu ya zame masa ga na zullumin rashin Jidda ga kuma na abinda ya faru a Companyn nasu, haka dai suka kwana ba daɗi washegari sammako Hisham yayi zuwa asibitin sai dai zuwan sa yayi bala'in ɗaga masa hankali domin kuwa ya tarar da mahaifiyar Sadiq da ƙanwarsa sai ihu suke Allah ya yiwa Sadiq rasuwa Hisham jingina bayansa yayi da jikin bango ya runtse idanunsa bai san sanda hawaye ya biyo fuskarsa ba, gagara magana yayi idanunsa na lumshe hawaye na cigaba da biyo idanunsa, Nameer a haka ya ƙariso ya samu Hisham gaban Safiya ƙanwar Sadiq ya ƙarisa tare da cewa.
"Me yake faruwa karki cemin Sadiq ya rasu.?"
Kanta safiya ta ɗaga tana kara sakin kuka cikin rawar murya tace.
"Yaya Sadiq ya rasu, mun shiga Uku."
Tayi Maganar cikin matsanancin kuka kansa Nameer ya dafe tare da furta.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Baku shiga Uku ba safiya akwai Allah ki daina kukan."
Yayi Maganar yana tashi yaje ya tsugunna a gaban Alhaji Sagir, yace.
"Alhaji.........
Hannu Alhaji Sagir ya ɗaga wa Nameer tare da tashi yabar wajen, shuru Nameer yayi tare da tashi ya nufi Hisham.
"Hisham ka yi haƙuri Please ga police sun shigo."
Idanunsa Hisham ya ɗago ya kalli Nameer tare da juyawa ya kalli Police ɗin, room ɗin da gawar Sadiq yake suka nufa ganin Alhaji Sagir yana huci yasa Hisham bai tunkari inda yake ba.
Inspector Lawan sun juma sosai cikin ROOM kafin suka fito da umarnin za'a iya ɗaukar gawar Sadiq, Hisham inspector Lawan ya nufa tare da dafa kafadarsa yace.
"Munyi duk wani binciken da zamuyi bamu samu wata hujjar da ta nuna wanda yayi amfani da gubar nan ba, guba ce mai haɗarin gaske wanda duk wanda ya shata rayuwarsa bazata tsira ba, sakatariya da Esther babu hannunsu cikin aikata wannan masha'ar, sannan mun koma Companyn naku da daddare mun ƙara bincike har CCTV Camera dake Companyn sai da muka duba amma bamu ga komai ba, bamu da wata hujjar da zamu kama wani da laifi amma zamu cigaba da binciken ma'aikatan ku ɗaya bayan ɗaya.''
Kansa HISHAM ya girgiza yace.
"Na gode Inspector Lawan, tabbas duk wanda yayi wannan aikin babu shakka ya juma yana harin mu yayi komai ne cikin dabarar da baza'a iya gano sa ba, kuyi kokarin gano wanene zan baku duk wani haɗin kan da kuke bukata."
Hannu inspector Lawan ya bawa Sadiq kafin yabar wajen, gawar Sadiq aka fito da ita a motar asibitin akayi gida dashi, shima Hisham yabi bayansu tare dashi akayi sallar jana'izar Sadiq bayan sun dawo ne daga makabarta Hisham ya sunkuyawa gaban Alhaji Sagir yana basa hakurin abinda ya faru, a wannan lokacin ya saurari Hisham harma suka zauna waje daya aka cigaba da karɓar gaisuwa.
Tun da Tunde yaji labarin mutuwar Sadiq hankalinsa ya tashi sai dai ko da wasa baije wajen amsar gaisuwar ba gudun kar Hisham ya zargesa.




***********


Dariya ta sanya da jin labarin mutuwar Sadiq madadin tayi jimami, cike da mamaki Wamimo take kallonta ita da Tunde kafin Wamimo ta nisa tace.
"Mamabisola meyasa kike dariya madadin kiyi alhinin rasa abokin aiki, wannan kisar fa kune kuka yisa."?
Dariyar ta kuma saki tace.
"Ba dai mu ba, shi dai ya kashe kansa waye ya kawo gubar idan ba shi ba, shine ya bada ajalinsa da hannunsa, dan ni tunda nazo duniya ban taɓa sanin akwai wannan gubar ba, duk makirci na."
"To amma Mama meyasa kike dariya.?"
Tunde ya jefa mata tambayar, Zama tayi tare da kallon sa tace.
"Ina dariya ne saboda na samu hanyar durƙusar da IYABO, da wannan mutuwar da Sadiq yayi a Companyn su zanyi amfani wajen ganin na durkusar da Companyn su, duk wani bincike sunyi basu samu hujjar wanda yayi wannan kisan ba, da Wannan zan tunzura Alhaji Sagir ya shigar da Companyn ƙara kotu domin bin kadun jinin ɗansa, zan nuna meyasa meyasa aka rasa duk wata hujja, hakan na nuna kenan anyi shirin kashe masa dane shiyasa aka goge hujjar da zata nuna wanda ya aikata kisan ni nasan yadda zan tunzura zuciyarsa harya hasala ya maka *Hisham rice mill limited* a kotu, yayin da su kuma basu da wata hujjar da zasu kare kansu."
Tayi Maganar tana sakin murmushi, gabaki ɗayansu dariya suka sanya tare da kallon juna suna jinjinawa Mamabisola.







_____________________________________







_Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to insha Allah Book One ya kusa zuwa karshe, alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._



*0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180*




*Like Share and comments my fan's🥰*






_UMMU NASMAH CE✍🏻_
[7/22, 7:56 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*




*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*





*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻




*FREE BOOK ONE 📚*



_Wannan littafin ba free bane na kuɗi ne Book one shine Free kuma mun kusa zuwa karshen Free zamu shiga Book two inda zaku cigaba da karatun wannan littafin akan 200 kacal ban tsawwala ba farashin da zaku iya biya na sanya dan Allah idan har kina son wannan littafin kina bibiyar sa kizo ki biya kudin ki, ki cigaba da karatun sa akan farashi ƙalilan, karki yadda ki kasance cikin ɗaya daga cikin masu cin hakkin wani 08147537180._




*_Page 55 to 56_*




Kallon Hisham Abba yayi ya kalli takaddar sammacin kansa ya girgiza tare da cewa ɗan sakon.
"Okay kana iya tafiya Allah ya kaimu Monday."
Kafin ya dubi HISHAM da yayi Matukar kaduwa yana gigice har yanzu hawayen yake.
"Hisham baka da hankali, yanzu Hisham ayi kisan kai a cikin Companyn mu baku sanar da ni ba saboda rashin hankali, yanzu wannan gangancin da kukayi kasan irin asarar da zai haifarwa Company kuwa.?"
Kansa Hisham ya kaɗa sai yanzu ya samu damar fashewa da kuka cikin kukan yace.
"Bashi bane damuwata Abba, na amince nayi asarar komai a rayuwata muddun ɗan uwana zai kasance tare dani har abada, Abba lafiyar Nameer shine damuwata Abba mu nema masa lafiya kana jin abinda likita yace ɗan uwana bazai wuce wata biyu ba a duniya, bazan iya kirga wannan kwanakin ba Abba kace min mafarki ne, kace kunnena karya yake min Abba."
Yayi Maganar cikin wani irin kuka mai ɗagawa mai sauraro hankali.
Tausayin sa ne ya kama Abba, ya jawo sa jikinsa tare da rungumesa Ummi ma kukan ta kuma sanyawa tana neman waje ta zauna.
"Rayuwa zata mana tsanani Hisham rashin Nameer a rayuwar mu tamkar rasa jigon jikin mu ne, bazan

Please Login or Register in order to submit comment