Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Jidda.





***********


Sadiq na zaune cikin mota shi da Tunde kiran Hisham ya kuma shigo masa waya daga kiran yayi tare da ce masa ya basa 10minute gashi nan karasowa kafin ya ijiye wayar yana duban Tunde yace.
"Na faɗa maka kayi hankali da gubar nan domin kuwa tana da hadarin gaske, ka tabbatar yarinyar da zakuyi aikin tare mai basira ce, muddun Nameer yasha wannan gubar babu makawa bazai ƙara minti biyar ba a duniya, idan muka kashe Nameer to mun kashe ƙarfin Hisham da hasken sa, domin kuwa cikin duhu da tunani zai fara rayuwa yayin da hankalinsa zai rabu biyu gefe guda na ga ciwon rashin Nameer gefe guda kuma na ga tunanin ɗaukar fansa akan Jidda ina fatan ka fahimta, idan kuma har ka yadda wata matsala ta samu to ka sani babu ruwan Sadiq akanka damuwar zata tsaya domin kuwa na faɗa maka zan iya zillewa."
Kansa Tunde ya kaɗa yace.
"Yes na fahimta, insha Allah gobe komai zai kammala, zanyi aiki cikin basira da kwarewa babu wata matsalar da zata samu."
''okay fatan Nasara."
Sadiq yayi Maganar yana fita daga cikin motar ya shiga nasa tare da jan motar yabar arean wajen.



A parking space na ciki part ɗin su Hisham yayi parking ɗin motarsa tare da fitowa yana kiran Hisham, garden ɗin ya nufa bayan Hisham ya sanar dashi yana garden ɗin, yana zaune a ƙasa kan darduma, fuskarsa cike da fara'a kana ganinsa zaka fahimci yana cikin farin ciki zama Sadiq yayi gefen sa, ganin Hisham na murmushi ya sashi cewa.
"Daga ganinka kana cikin Happy, me ka samo mana, Allah yasa wata hajace mai nauyi."?
Dariya Hisham ya sanya yana cewa.
"Wa ya ce maka samuwa ce, wannan ba samuwa ba ce waken gizo ne dai zaisha wuta harma ya babbake, domin kuwa Allah ya kai damo ga harawa, kaga kuwa ɓarna dole ne, burina ya cika akan wannan bahamagiyar yarinyar domin kuwa ta faɗa tarkona, na kusa biyan bashin gaba, kasan shi bashi tamkar adashe yake muddun kaci to sai ka biya wallahi, ko kafi uwarka kokari, tabbas ta faɗa tarkon da zai zamo tabon baƙin cikin da bazata taɓa mantawa dashi ba har karshen rayuwarta."
Dariya sosai Sadiq ya sanya ko da Hisham bai fayyace masa inda ya nufa ba, kalama ya basa a dunƙule, ya fahimci Jidda ce ta faɗa tarkon sa, Sadiq duban Hisham yayi yace.
"Ni dama nasan dole zata faɗa tarkonka, domin kuwa babu Macen da zata kalleka tace bata so, amma mubar wannan maganar tukunna mu dawo kan lamarin Mamabisola ina son muyi magana akan Tunde."
Dago idanunsa Hisham yayi ya dubi Sadiq cike da mamaki yace.
"Mamabisola kuma Sadiq, meyasa zaka min magana a kansu why SADIQ kana da Alaqa da su ne wanda har zai sa su baka wani saƙo, ko ka fara shiga sabgar su ne."?
A ɗan firgice Sadiq ya ɗago ya kalli Hisham _kar fa nayi wasa Hisham ya gano wani abu na shiga Uku, ko da yake ina bazai taɓa fahimtar komai ba idan kasan wata ai baka san wata ba Hisham na fika iya buga wasa._
Sadiq yayi Maganar zucin yana sakin murmushi kafin ya ɗago ya kalli Hisham yace
"Kana zargina da wata alaqa dasu ne saboda kawai zanyi magana da kai akansu.?"
"Ko ɗaya Sadiq bana zargin ka kuma bazan taɓa zargin ka ba domin kuwa nasan bazaka cutar da ni ba.?"
Numfashi Sadiq ya saki yace.
"Kasan wani abun mamaki kuwa Hisham.?"
Kansa Hisham ya girgiza yace.
"A'a babu abinda zan sani har sai idan ka sanar dani sai dai nayi mamaki sosai da kai da bakinka kace zamuyi magana da kai akan Mamabisola."




_____________________________________






*ANAN ZAMU DASA AYA HAR SAI ALLAH YA KAIMU BAYAN SALLAH INDA ZAMU DAWO SALLAH DA SATI ƊAYA NASAN ZUWA WANNAN LOKACIN AN GAMA HIDIMAR AIKIN NAMA MA'ANA DAI MUN TAFI HUTUN SALLAH BANSO ACE NA TSAYA BA SABODA RASHIN TYPING DA NAYI KWANA BIYUN NAN, TO SAI DAI BABU YADDA NA IYA DOLE NE MU TAFI HUTUN SALLAH SABODA AYYUKA INSHA ALLAH ANA GAMA HIDIMAR SALLAH ZAMU DAWO POSTING BA KAMA HANNUN YARO HAR SAI MUN DASA AYA A KARSHEN LABARIN.*




_Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._



*0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180*



_Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan aul yasmut siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai._



*Like Share and comments my fan's🥰*






_UMMU NASMAH CE✍🏻_
[7/18, 7:20 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*



*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*





*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻



*FREE BOOK ONE 📚*




*_PAGE 47 TO 48_*



"Ba fa wata magana ba ce ta ɗaga hankali Hisham mamaki na ke yadda Mamabisola ta lalata rayuwar Tunde ta barsa ya ke abinda ya ga dama a rayuwarsa, ina wannan yaron A'lameen ɗan gidan Alhaji Dage yaron da ya kashe wannan almajirin har aka kaisa prison na Abuja kafin mahaifinsa ya shiga ya fita aka fito dashi."?
Shuru Hisham yayi yana tunani kafin yace.
"Okay na gane Dagash zaka cemin sai nafi ganewa na ganesa meya faru.?"
Numfashi Sadiq ya sauƙe kafin yace.
"Tare na gansa shi da Tunde wajen sau uku ina ganinsu tare nan a ShopRite na gansu nan kuma a Sudan Markey sai kuma yau na gansu tare a mota kasan abokin ɓarawo ɓarawo ne Hisham, ni fa wannan lamari ya fara bani tsoro kuma tashin hankali na yanzu Tunde ya shigo Companyn ku."
Tsuka Hisham yaja yace.
"Mtsss ni nayi zaton wani abun zaka faɗan to Sadiq ni ina ruwana dashi idan yaga dama yaje ya shiga cikin Yan shan jini ma dan Allah mubar wannan maganar mu dawo kan maganar wannan jakar yarinyar."
"Jakar yarinya kuma Hisham JIDDA itace jakar."?
"Kwarai kuwa Jaka ma ta bugawa a jarida yo idan Banda mahaukaciya yanzu ita idan akace zanso yar matsiyata irinta sai ta yarda, ban taɓa raina basirarta ba sai yau wallahi."
Dariya sosai Sadiq ya saki tare da cewa.
"Shege abokina wato dai yanzu kai murna kake ka samu karenka ya tsotsi ƙashi karfa reshe yayi ƙoƙarin juyewa da mujiya dan itama yarinyar naga so beautiful, ka dai taka sannu Hisham."
Tsuka Hisham yaja yace.
"Mtsss! Tsiyata da kai kenan wani sa'in ba'a tadin arziki da kai wallahi, yo ni ko baki Ammi tamin zanso wannan Yar talakawa ne, da dai nayi rayuwa da wannan Yarinyar ta aure na gwammaci na mutu gauro yanzu dai ba wannan ba, ta faɗa tarkona meye next takun da zanyi mata kasan fa wani sa'in kaine madubina a wannan harkar saboda ba wai shiga sabgar mata nake ba ka sani."
"To naji abinda ya kamata kayi yanzu shine ka ƙare dagewa wajen ganin ka kama zuciyar ta ma'ana ya zamana cewa bata jin ko wanne ɗa namiji a ranta sama da kai taji bazata taɓa iya rayuwar Aure da wani ba idan ba kai ba, ka ƙara kwantar da kanka gareta da nuna mata kulawa Hisham zakaga yadda zata mace a akanka idan har ta kai wannan matakin a Soyayyar ka to da shine zaka iya yiwa rayuwarta illa."
Duban Sadiq Hisham yayi tare da cewa.
"Kana nufin kenan har yanzu ban gama samun makaman da zan yaki JIDDA dasu ba."?
"Kwarai kuwa Hisham makami ɗaya kawai ka riƙe da sauran rina a kaba tukunna yanzu ta fara sonki yana da kyau ka riƙe zuciyar ta."
"Na fahimta Sadiq insha Allah kuma sai na baka mamaki domin kuwa bazan taɓa daina jin ciwon tozarta Nameer da JIDDA tayi ba har sai na wulaƙanta rayuwarta sannan ne zan huce zuciyata taji cewa da gaske Hisham bazai taɓa bari a wulaƙanta Nameer ba."
"Hakan ma yayi domin kuwa ana tauna ƙasa ne saboda aya taji tsoro."
Sadiq yayi Maganar yana kallon Hisham sun juma sosai a wajen da Hisham kafin Sadiq ya tafi.


Da daddare bayan sunyi deaner Ummi ta koma tsakiyar falo shi kuwa Hisham bedroom ɗin su ya shige saboda yana da aikin da zaiyi ya rage daga Nameer sai Tutu a daining ɗin, idanunta Tutu ta ɗaga ta kalli NAMEER da take lura dashi tunda aka fara cin abincin shi bai wani ci ba yafi mai da hankalinsa ga tunani da alamu yana cikin matukar damuwa.
"Kayi haƙuri yaya Nameer dazo nazo na takuraka da tambaya kana cikin yanayin da baka bukatata a lokacin kayi haƙuri zuciyata ce ta gaza samun nutsuwa da halin da na ganka a ciki a zatona ni abokiyar shawararka ce babu abinda zaka iya ɓoye min a matsayina na matar da zaka Aura."
Kallonta yayi sai kuma tausayinta ya kamasa sosai _tabbas da tasan abinda yake zuciyata bazata so na furta mata shi ba, tabbas RASHIN SANI YAFI DARE DUHU_ Nameer yayi Maganar zucin har zuwa lokacin idanunsa na kanta, numfashi ya saki tare da cewa.
"Ba ɓoye miki damuwata nake ba, kawai ina cikin yanayi marar daɗi ne yau shi yasa bana so kowa ya kasance kusa dani nafi bukatar kadaici a wannan lokacin karki damu ba wata damuwa ce ta ɗaga hankali ba infact ma komai ya shige."
"Amma yaya Nameer zaman mu cin abinci fa ina lura da kai baka wani ci abinci ba, sai ma tunani da kake yi wannan kaɗai ya isa ya nuna damuwar da kake ciki mai girma ce, Please farin ciki na tell me."
Kansa ya girgiza yace.
"Tunda na ce miki kibar maganar nan ta wuce to ki barta ba gashi ba yanzu kallonki ya san yani cikin nishaɗi, ke ta musamman ce Tutu i love You so much."
Murmushi Tutu ta saki sosai taji daɗin maganganun NAMEER a gareta kafin tace.
"Shikenan na bari amma ka sani bana son sake ganinka cikin damuwar nan, domin farin cikin ka shine nawa, kasan dai irin matukar Soyayyar da nake maka numfashi ma wuya zai bani muddun babu kai cikin rayuwata domin kuwa rayuwar duhu zata min irin duhun da ko tafin hannu baza'a iya kallo ba, yau idan na tuna cewa gobe ne alkawarin ku na neman matar Aure da kuka yiwa Ammi zai cika sai naji wani irin farin ciki domin kuwa gobe ne kowa zai ji labarin Soyayyar mu harta Abba da baya ƙasar nan sai mun kirasa mun sanar masa."
Dariya Nameer ya saka tare da cewa.
"Saboda baki da kunya Jidda sai ki sanar da Abba Soyayyar ki."
Nameer yayi Maganar cikin dariya Tutu idanunta ta zaro cike da mamaki tace.
"What JIDDA kuma yaya Nameer wacece kuma JIDDA da har zakayi sha'afan da zaka kirani da sunanta wani irin mahimmanci ta ke dashi a rayuwarka."?
Tayi Maganar tana haɗa ranta tamau.
Kansa Nameer ya dafe bai san ma ya ambaci Tutu da sunan Jidda ba, tsabar Jidda ce kaɗai take yawo a cikin ransa numfashi ya ɗan saki tare da cewa.
"Sorry Farin ciki na, babu wani mahimmanci da take dashi a rayuwata kawai dai sunan ne yazo bakina, Kinga mubar wannan maganar yanzu ina son zan haura akwai aikin da zanyi."
Kanta Tutu ta kaɗa tare da cewa.
"Okay shikenan amma dai hankalina bai kwanta da wannan Jiddar ba dan harma naji na tsaneta tun kafin nasan waye ita."
Murmushi kawai Nameer ya saki tare da tashi yace.
"I love You."
Yayi Maganar yana haurawa sama murmushi Tutu ta saki ta bisa da kallo cike da so da kauna kafin ta tashi tayi wajen Ummi.



Ko da Nameer ya shiga ya samu Hisham zaune a saman kujera mai biyu dake tsakiyar bedroom ɗin, tollet Nameer ya shige yayi wanka ya fito tare da sanya boxer da vest ya zauna yana ƙoƙarin jawo system ɗinsa yaji muryar Hisham.
"Nameer wai bakaga sakon da na turo maka bane ta Whatsapp."?
Kansa Nameer ya ɗago ya kalli Hisham tare da cewa.
"Bakaga sakon da na maido maka ba kenan halan baka buɗe data bane."
"Eh ban buɗe ba gaskiya, kayi mamaki ko da kaga Jidda na fitar a matsayin matar da zan aura."?
Numfashi NAMEER ya saki yana jin wani ɗaci na taso masa a zuciyarsa kafin yayi murmushin ƙarfin hali yace.
"Babu abun mamaki ai Hisham shi Allah ba yadda baya lamarinsa naji daɗi da ya kasance Jidda ka fitar domin kuwa ko shakka bana yi kayi dacen mace ta gari, amma Hisham Soyayyar gaskiya kuwa kake yiwa Jidda anya babu wani manufa a ƙasan ranka karfa ka zalunci Yarinyar mutane."?
Murmushi Hisham ya saki kafin yace.
"Nameer kana ganin zan cutar da Jidda ne meyasa zakayi wannan tunanin, hmm! Nameer har cikin zuciyata nake jin Soyayyar Jidda ina sonta sosai."
"Ban yarda ba Hisham ko ka manta abinda ka faɗa min ko matar da zaka fitar bawai kana sonta bane manage kawai zakayi da ita ko ba haka ka faɗa min ba."
Dariya sosai Hisham yayi yana ture system ɗin sa gefe yace.
"Malam ni fa wasa nake maka wai dama serious ka ɗauki maganar gaskiya she is funny."
Numfashi Nameer ya saki yace.
"Okay Allah ya sanya alkairi nima insha zakaga tawa."
"Allahu yasha" Hisham ya furta yana maida kansa ga system ɗin sa.






**********


Cike da farin ciki Jidda ta shiga gidan nasu babu kowa tsakar gidan hakan ne ya bata damar faɗawa ɗakin ta domin kuwa tasan Basmah na ciki tana zaune tana ninke kaya Jidda ta faɗa jikinta tare da rungumeta ta baya tana dariya juyowa Basmah tayi tare da cewa.
"Lallai yau da alama ta samu wannan farin ciki haka."
Dariya Jidda ta kuma saki tare da sakin Basmah ta zauna a tsakiyar katifar tace.
"Basmah yau dai nima nayi tsuntuwa domin kuwa burina ya cika na samu irin namijin da nake burin aura, zancen da nake miki harma ya furta min kalmar I love You."
"Ban fahimta ba naga da Hisham kuka fita a can ɗin kika gamu da saurayin."?
Kanta Jidda ta girgiza tare da cewa.
"A'a shi ɗin dai Hisham."
Da ƙarfi zuciyar Basmah ta buga tare da dafe ƙirjinta idanunta suka firfito waje da karfi ta furta.
"What! JIDDA Hisham shine yace yana sonki.?"
Ta jefa mata tambayar ƙirjinta na harbawa da ƙarfi, dariya Jidda tayi tace.
"Ƙwarai kuwa Hisham ɗin, Basmah bazan ɓoye miki ba nima fa na kwana biyu ina jin sonsa a raina kawai ina dannewa ne saboda ban san me gobe zata haifar ba, nayi mamaki da baki fahimci hakan ba keda kikafi kowa sanin waye ni."
Gumine ya ketowa Basmah tamkar zata danna ihu haka taji zuciyar ta, jikinta duk ya mata nauyi hankalinta ya tashi.




_____________________________________







_Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._



*0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180*



_Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan auli yasmut siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai._



*Like Share and comments my fan's🥰*






_UMMU NASMAH CE✍🏻_[7/19, 8:18 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*




*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*





*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻




*FREE BOOK ONE 📚*





*_Page 49 to 50_*





Jidda ganin Basmah ta kwabe fuska har tana haɗa gumi ya sata cewa.
"Basmah meye haka kin wani haɗa rai sai kace wanda na faɗa miki ranar mutuwarki, har kina haɗa gumi akwai matsala ne."?
Saurin girgiza kanta Basmah tayi tace.
"Yo Jidda ba dole na haɗa gumi ba naji kinzo min da wata magana tamkar almara, meye zai haɗaki soyayya da Hisham, har kin manta halinsa kin manta waye Hisham kin manta kalar rashin mutuncin sa, da zakiyi gangancin shiga rayuwar sa."?
Murmushi Jidda ta saki tare da cewa.
"Hmmm! Basmah kenan meye aibun Hisham, ke fa da bakinki kike cemin ashe Hisham mutumin kirki ne mune bamu fahimce sa ba, yanzu kuma kice zaki tuno da baya, we'll munin halinsa ba abun gudu bane domin kuwa irinsu suna bukatar macen da zata nuna masu rayuwa shiyasa banji tsoron shiga rayuwar sa ba, ina son Hisham Basmah bazan iya rabuwa dashi ba kiyi haƙuri mace ma tana gyara miji ki fahimta, ina da yakinin Hisham bazai juyawa rayuwata baya ba, na kawo miki labari mai daɗi shine zaki sa gwiwwata ta sare madadin ki karfafa min gwiwwa akan abinda nake muradi."
Numfashi Basmah ta saki zuciyarta na hura har yanzu hankalinta a tashe yake _Wannan wacce irin masifa ce yaya Hisham zai min haka ni da nafi kowa muradinsa ni da nake da shirin shiga Companyn su domin samun kusanci dashi, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Jidda meyasa zaki min haka_ Basmah tayi Maganar zucin cikin matsanancin tashin hankali kanta ta girgiza tace.
"Shikenan Jidda Allah yasa haka yafi Zama Alkairi, yanzu ya kukayi dashi kin tabbatar Soyayyar gaskiya yake gwada miki.?"
"Ƙwarai kuwa Basmah na tabbatar ɗari bisa dari, ina labarin Ahmad ne kwana biyu bamu haɗu ba."
Bakinta Basmah ta taɓe
"Yana nan lafiya jiya ma sai da ya tambayeki."
"Ayya dan Allah idan kunyi waya kice masa na gode da mantawa da yayi dani, bara naje wajen Umma bata san na dawo ba."
Kanta Basmah ta girgiza kafin Jidda ta fita tana fita Basmah ta mike tsaye.
"Na shiga Uku ni Basmah duk adana soyayyar Hisham da nake amma sai da aka min ƙofar rago, Hmm why Jidda, mtsss bazan iya haƙura da Hisham ba kiyi haƙuri Jidda dole sai na kwaci soyayyata."
Tayi Maganar cikin huci tana riƙe kunkuminta.





**********


After two days


Companyn cike yake da ma'aikata kasancewar yau take ranar aiki Monday kowa yana harkokin gabansa, Yau lokaci a kure Hisham ya shigo Companyn, darect office ɗin Jidda ya nufa yaga ko tazo, ya samu ta shigo amma tayi office ɗin mr John hakan ya sashi juyawa ya koma nasa office ɗin, Tunde kuwa tun shigowarsa ya nufi Wajen Zainab ya sameta zaune ita ɗaya a wajen da suke goge shinkafa, gefenta Tunde ya zauna.
"Ya akayi Tunde ka shiryawa aikin ne."?
"Kwarai kuwa na shirya shiyasa ma kika ganni anan Zainab bana son matsala a aikin nan duk yadda za'ayi ki samu ki zuba wannan gubar a tea ɗin da Nameer zaisha bana son kuskure."
"Kuskure Hmm kaima fa Tunde idan har baka yarda dani ba bazaka bani wannan aikin ba dan haka karka damu aiki zai tafi yadda kake bukata."
"Shikenan ga nan gubar ki kiyaye."
Tunde yayi Maganar yana miƙa mata kwalbar gubar amsa Zainab tayi kafin tace.
"Nan da 30 minute ina jiran alart ɗina yana shigowa zan aiwatar da aikin."
"Karki damu zakiji" Tunde yayi Maganar yana tashi yabar wajen murmushi Zainab ta saki tare da furta "akan kuɗi ba abinda bazan iya aikatawa ba, kayi haƙuri Nameer kuɗi yafi min komai a rayuwa."


Kansa tsaye Sadiq ya shigo office ɗin dubansa Hisham yayi yana sakin murmushi yace.
"Nayi zaton bazaka zo ba ai Bismillah ka zauna."
Zama Sadiq yayi yace
"Ai kasan muddun ka kirani zanzo, Allah dai yasa lafiya ka kirani da sanyin safiya kasan ko breakfast banyi ba."
"Mtsss! Kiran dole ya kama Sadiq, bara na kira sakatariya tasa a kawo maka tea ko da bread ne ka fara kafin muyi maganar ko."
Kansa Sadiq ya girgiza yace.
"Bar tea ɗin tukunna sai mun gama tattaunawa."
"Okay Sadiq ni har yanzu akwai Yarinyar da ka fitar a matsayin zaka Aura.?"


Please Login or Register in order to submit comment