Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga bedroom ɗin ta ba, ya akayi alkawarin mu fa ya kusa Malam kuma har yanzu banji motsinka ba."
Murmushi Hisham ya saki tare da cewa.
"Karka damu da motsina ka jira yau zakaji kyakkyawan labari domin kuwa a yaune zan kiraka kaga matar da zan Aura."
"Serious Hisham."?
Nameer ya tambayesa cike da mamaki.
"Yeah serious kasan dai ban taɓa ɗaukar alƙawari ban cika ba ko, duk da soyayya bata gabana haka kuma har yanzu banga kalar matar da tamin ba, ko wannan da zan fitar manage zanyi da ita."
"Hisham ni fa kana bani mamaki ta yaya zaka auri abinda baka so, wacce Yarinyar ce zatayi gangancin Auren mijin da baya sonta, karka zalunci Yarinyar mutane Hisham, idan baka sonta Please karka yaudareta tukunna ma a ina ka samu yarinyar tell me.?"
Dariya Hisham yayi yace.
"Tell me! Tell me! Hmmm! Nameer koma wacece ka jira zaka ganta, sannan maganar Soyayya ko yaudara da kake, ita ta gani kuma zata iya ɗauka, dan haka babu ruwanka da rayuwata a wannan sabgar kowa ya iya ruwa zai fito ko teku ya faɗa."
Hisham yayi Maganar yana tashi zai bar wajen, magana Nameer yake masa amma Hisham bai ma tsaya ya sauraresa ba ya fice, numfashi Nameer ya saki tare da furta.
"Wacce yarinya ce Hisham ke shirin kai rayuwarta ya baro, mtss! Allah ya rufa asiri, to ni kuma ya zanyi da matsalar Tutu ya zataji idan na fitar da wata a matsayin matar aurena ba ita ba, anya zuciyar ta zata iya ɗaukar wannan ƙaddarar."?
Ya tambayi kansa yana dafe da kansa, ya juma sosai a falon yana saƙar zuci kafin yabar falon.





**********


Jidda cikin shiri ta fito da la'asar dai-dai lokacin da sukayi alkawarin haɗuwa da Nameer yayin da ya rigata zuwa wajen yana zaman jiranta, tare da Basmah suka fito, cike da mamaki Jidda ke kallon Hisham da ta gansa tsaye a ƙofar gidan su jikin motarsa.
"Hisham kaine kazo babu kira.?"
Hannunsa Hisham ya harɗe tare da cewa.
"Au dama doka ce idan zanzo wajenki sai na kiraki a waya."?
"Ko ɗaya babu wata doka kawai naga ka saba kirana ne idan zakazo."
"Okay yau kuma ban kira ba, Umma tana ciki ne ina son zan sanar da ita zamu fita unguwa da ke.?"
"Unguwa kuma yanzu Hisham baka ga fita zamuyi da Basmah ba ne ko baka ganta bane, ina da alƙawari da Nam.........
Bata kai ƙarshen maganar ba Hisham ya katseta da cewa.
"Listen to me, I told you, we will go out or I will not go out with you tell me."?
Kanta Jidda ta girgiza tare da cewa.
"Ni fa bance baka kai ka fita unguwa dani ba cewa nayi akwai wanda yake jirana yanzu haka.''
Fuskar sa Hisham ya haɗe tamau tare da kallon Basmah yace.
"Ki koma gida Basmah ki cewa Umma na fita tare da Jidda plaza zata tayani sayayya kiyi haƙuri Basmah bazamu daɗe ba yanzu zamu dawo."
Yayi Maganar yana buɗewa Jidda gaban mota kallon Basmah Jidda tayi da ta ke kaɗawa Hisham kai kamar ƙadangare kafin ta buɗe motar ta shiga ita kuma Basmah ta koma cikin gida duk abinda ke faruwa ABDULWASI'U yana ƙofar shagonsa yana kallon su, domin kuwa shi gani yake Jidda irin su Hisham take harin Aure ba irinsa ba talaka shima Hisham motar ya shiga ya ja suka ɗauki hanya, sun ɗanyi nisa da tafiya wayar Jidda tayi ringing hannu tasa cikin jakarta ta ɗauko wayar zata amsa kiran HISHAM yayi saurin kwace wayar daga hannunta ya kashe ba tare da ya duba mai kiran ba cikin aljihun sa ya jefa wayar, Jidda ko da bata ga mai kiran ba tasa Nameer ne yana can yana jiranta yaji shuru.
"Hisham why are you turning off my phone when you are calling me?"
Kansa Hisham ya girgiza.
"I do not need to know, Jidda I want you to give me peace of mind when I need you ."
"Ka fiye rigima Hisham, muje na ga inda zaka kaini."
"Kinyi kyau fa sosai tamkar ɗanyen gold haka kika fito."
Murmushi Jidda ta saki.
"Ka iya tsara zance Hisham, yanzu ina muka nufa."
Murmushi Hisham ya saki yace.
"Karki damu zaki gani yanzu."
Yayi Maganar yana kashe mata ido, kafaɗarta Jidda ta ɗaga alamun to, suna zance jefi jefi har suka shiga babban Mall ɗin Alhassan Ɗan Iya da ke titin Darasawa, parking Hisham yayi tare da fitowa itama Jidda fita tayi tabi bayan Hisham, wani office ya shiga tana tsaye a bakin office ɗin bai juma ba ya fito suka shige ciki tunda Jidda tasa ƙafarta a wannan wajen wani irin sanyi ya ratsata idanunta ta zaro tana kallon abun mamaki yanda aka ƙawata wajen da kyawawan furanni, mai launin ja da kore, ga wasu irin wuta da suke bada hasken ja da kore.
"Wow." Jidda ta furta a fili, murmushi HISHAM yayi Jidda bata ankare ba taga Mutum ya durƙusa a gabanta tare da buɗe akwatin zobe da ke hannunsa zoben azurfa ne mai kyawun gaske an masa ado da zanen love.
"I LOVE YOU JIDDA I WANT YOU TO MARRY ME, I REALLY LOVE YOU, HELP ME RESPOND TO MY LOVE, I LOVE YOU."
Tamkar saukar aradu Jidda taji maganar idanunta ta zaro tana bin Hisham da zoben dake hannunsa kallon mamaki.
"Hisham, are you in love with me?."
"Yeah Jidda i really love you."
"No Hisham you are dreaming, I do not have a position to loving me, bani da wannan matsayin ko wacce kwarya da abokiyar burminta."
Kansa Hisham ya kaɗa cikin nuna tsantsar damuwa yace.
"Ki taimakeni ki amshi soyayyata muddun ba so kike rayuwata ta shiga cikin haɗari ba, babu ruwan so da sani matsayi ko iko Jidda, ki taimakeni ki soni dan Allah."
"No Hisham babu soyayya tsakanin m........
Katseta yayi da cewa.
"Please JIDDA ki taimakeni ki amshi soyayyata wallahi ina sonki na juma da soyayyarki a cikin raina please kiyi seving ɗin rayuwata I love You Jidda."
Runtse idanunta Jidda tayi ta sani babu Macen da Hisham zaice yana so ta ƙisa, itama idan tace bata sonsa a yanzu wallahi tayi ƙarya girgiza Kanta tayi tare da miƙo masa yatsarta zoben Hisham ya sanya mata a yatsar kafin ta ɗago yatsar tana kallon zoben idanunta na runtse ta furta.
"I accept your Love Hisham, I love You too. "
Miƙewa daga tsugunnen da yake Hisham yayi yana sauƙe ijiyar zuciya mai nauyi a fili ya furta.
"Yes! Jidda thank I love you so much."
Ya furta cikin farin ciki tare da zagowa gabanta ya ciro wayarsa selfie ya ɗaukesu dukkan su suna dariya ita dashi suna kallon juna, kana kallon picture ɗin kasan dukkan su suna cikin farin ciki, nuni Hisham ya yiwa Jidda da kujerar dake gaban ƙaramin table ɗin da ke ɗauke da kayan alatu na ci dasha ya mata alamun ta zauna, zuwa Jidda tayi ta zauna har yanzu murmushi ta ke.

Shi kuwa Hisham picture ɗin ya turawa Nameer ta Whatsapp tare da rubuta masa.
_surprise she is my wife to be, My first Love JIDDA._
Yayi sending yana sakin murmushi, tare da tura masa text ta message yace ka buɗe Whatsapp ɗinka na aiko maka da saƙo mai mahimmanci.


Nameer dake can yana zaman jiran JIDDA a cikin inter room garden, sai duba agogo yake har 5:30pm babu Jidda wayarta kuma ya kira yafi sau goma switch off ya kira Basmah ma wayarta baya tafiya, jin shigar text cikin wayarsa ya sashi duba sakon Hisham ya gani, data ya buɗe cikin minti goma sai sakon nasa na Whatsapp ɗin ya shiga, Nameer kansa tsaye ya shiga kan saƙon picture ya gani rubutun ƙasan ya fara karantawa kafin ya buɗe picture ɗin.
_Surprise She is my wife to be, My first Love Jidda._
Murmushi Nameer ya saki ko a zuciyarsa bai kawo Jiddar sa bace ya furta.
"Wai dama da gaske Hisham yake ya fitar da matar aure, cap waye ce tayi gangancin shiga rayuwar Hisham."
Yayi Maganar yana saka hannu ya buɗe picture ɗin, a wani irin firgice ya miƙe tsaye ganin Hisham tsaye da Jiddar sa da yake zaman jira yanzu cikin nishaɗi suna dariya.
"Whatt! Jidda no impossible ba Jiddana bace."
Nameer yayi Maganar cikin tashin hankali yana goge idanunsa wai ko sune suke masa karya.




_____________________________________





*_ALHAMDULILLAH NA GODE SOSAI DA ADDU'OIN KU MASOYA DA KUMA UZURIN DA KUKA MIN NA DAKATAR DA WANNAN LABARIN DA NAYI NA WASU KWANAKI HAR ALLAH YASA YAU NA DAWO, ALHAMDULILLAH! JIKIN MAMA YAYI SAUƘI SOSAI ADDU'A TA KARƁU NA GODE SOSAI JALALA POSTING BA KAMA HANUN YARO INSHA ALLAH I LOVE YOU MY FAN'S🥰_*




*MUSAMMAN JALALA GROUP DA ƳAN UWANA SHAƘIƘAINA ƳAN ƘUNGIYATA KAINUWA WRITER'S INA GODIYA TA MUSAMMAN GAREKU, NA GODE NA GODE DA KULAWARKU GARENI MASU KIRANA DA MASU TURO MIN SAƘO NAJI DAƊI SOSAI ALLAH YABAR ZUMUNCI.*






_Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._



*0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180*



_Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan auli yasmut siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai._



*Like Share and comments my fan's🥰*






_UMMU NASMAH CE✍🏻_
[7/7, 8:22 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.



https://chat.whatsapp.com/KoKE4o7opsRG4PfMLrKO2J


Mutane sai tambayata LINK ƊIN group ɗin JALALA suke to yau dai gashi na sake muku link ɗin amma group ɗina yana da doka, sannan ina haɗa namiji da Allah da yayi haƙuri karya shiga min group dan Allah na haɗaka da Allah🙏🏼




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*



*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*




*FREE BOOK ONE 📚*




*_Page 45 to 46_*





*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻



"Ta yaya hakan zata faru soyayya tsakanin wuta da auduga, no bazai taba yiwuwa ba domin kuwa babu ta yadda wuta zata jitu da Auduga a waje guda, na tabbata dole sai wannan wutar ta ƙoneta, ya akayi haka Hisham da Jidda soyayya."
Ya furta maganar a kiɗime cikin munguwar mamaki.
_yeah serious kasan dai ban taɓa ɗaukar alƙawari ban cika ba ko, duk da soyayya bata gabana haka kuma har yanzu banga kalar matar da tamin ba, ko wannan da zan fitar manage zanyi da ita_
Ya maimaita maganar Hisham ta ɗazu a cikin zuciyarsa yana neman warware kalaman nasa amma ƙwaƙwalwarsa ta gaza fassara kalaman Hisham, ko cikin mafarki kai ko a zahiri aka ce masa yau HISHAM da Jidda zasuyi jituwar da soyayya zata shiga tsakanin su wallahi sai ya ƙaryata, runtse idanunsa da suka kaɗa sukayi jawur yayi tare da buɗesu ya dafe kansa dake sara masa ji yake tamkar ya kurma ihu da ƙarfi ko nauyin da zuciyar sa ta masa zata ragu.
"Meyasa ƙaddara zaki min haka, meyasa kika haɗa soyayyar mace ɗaya a zukatan ƴan uwa masu ƙaunar junan su, wannan wacce irin mummunar ƙaddara ce, I love Jidda, bazan iya rayuwa ba tare da ita ba, why Hisham zaka rabani da farin cikin rayuwata why, bazan iya jure rayuwa ba tare da ita ba, HISHAM! Why.!?"
Yayi Maganar cikin ƙaraji yana dunƙule hannunsa ya daki teburin gabansa idanunsa ya runtse tare da cije lebensa idanunsa sun dawo tamkar gauta wato Jidda shanyasa tayi ta tafi wajen Hisham ta ma manta da yana jiranta, yayi Maganar zucin zuciyar sa tamkar zata fashe, sakon Hisham ya ƙara dubawa bai san sanda hawaye ya biyo idanunsa ba, hannunsa na karkarwa zuciyar sa na ƙuna ya yiwa Nameer reply da
_congratulation Bro na tayaka murnar samun Mace ta gari, ko cikin mafarki ban taɓa zaton soyayya zata shiga tsakanin Hisham da abokiyar faɗansa JIDDA ba, ashe Alkairi ne tsakanin ku, naji daɗin haɗuwar ku Allah ya sanya muku alkairi._
Ya tura saƙon zuciyar sa na harbawa da ƙarfi hannunsa ke tura saƙon amma zuciyar sa tamkar zata fashe haka yakeji, numfashi ya saki tare da kifa kansa jikin kujerar da yake zaune hawaye ya cigaba da zirarowa daga idanun sa, ga wani kwallon da ya tsaya masa na baƙin ciki ya tokare masa ƙirji ya juma sosai kansa yana kife kafin ya ɗago ya share hawayen sa miƙewa tsaye yayi tare da kwasan wayoyinsa ya fito daga wajen motarsa ya shiga yaja da ƙarfi cikin matsanancin tashin hankali ga kansa dake mungun sara masa.




********

Zama yayi a gabanta ya fuskance ta tare da dafe kumatunsa ya zuba mata idanu yana lumshe idanunsa.
"Kallon yayi yawa idan dai ba haɗiye ni zakayi ba."
Jidda tayi maganar tana sakin murmushi, murmushi shima Hisham ya saki yace.
"Kinsan meye kuwa."?
"Ban sani ba har sai ka faɗa."
Numfashi Hisham ya saki tare da cewa.
"Banyi zaton zaki amshi soyayyata cikin sauƙi ba Jidda, hmm! Jidda tun sanda na fahimci cewa ke macece mai adalci da riƙon amana da kuma tallafo damuwar wani daga ranar na fara jin Soyayyar ki a raina da farko banyi zaton cewa soyayya bace na ɗauka cewa kawai burgeni kike, sai da zuciyata ta fara matsa min da tunaninki da kuma yawan kallonki a cikin idanuna da kuma mafarkin ki da nakeyi ko yaushe yasa na fara gaskata zuciyata sonki take, Soyayya kuma ba ta wasa ba, i love You so much Jidda, hmmm! Na miki abubuwa da yawa na rashin kyautawa hakan yasa nake jin zaiyi wahala ki amince da soyayyata, meyasa kikayi saurin amincewa dani Jidda?."
Tunda ya fara Maganar ta tsura masa idanu tana kallon sa har sai da ya kai ƙarshe kafin tayi murmushi tace.
"Hisham babu ruwan so da ɗabia dan haka ka daina tambayata dalilin Soyayyarka a gareni abinda dai na sani ina sonka a koma yaya kake ni zan iya rayuwa da kai a haka."
"Hmmn! Hakane Jidda na sani babu ruwan so da ɗabia amma kuma ki sani akwai ɗabiar da so ke gujewa, musamman ni da............
Saurin dakatar da Hisham Jidda tayi da cewa.
"A'a Hisham karka tuna baya mu kalli gaban mu da kuma tunanin yaya zamu tafiyar da goben mu, ina sonka Hisham soyayya ta gaskiya."
Murmushi Hisham ya saki sun juma sosai a wajen suna fira cikin nishaɗi har sai 5:59 sannan Hisham ya dawo da Jidda gida bayan ya gama mata sayayya.

Jidda na shiga gida Hisham ya saki numfashi tare da sakin murmushi wayarsa ya ɗauka ya kira Sadiq yana ɗagawa yace su haɗu a gida kafin ya katse kiran ya ja motar.



***********


Tutu tana zaune a falo taga shigewar Nameer kamar mai tangaɗi yana riƙe da kansa da sauri Tutu ta miƙe tsaye tare da cewa.
"Subahanallah! Yaya Nameer meya sameka.?"
Bai ko kulata ba ya haura sama da ƙyar bayansa Tutu tabi da sauri, kusan tare suka shiga bedroom ɗin nasa, a saman bed ya zube yana runtse idanunsa har yanzu ƙirjinsa zafi yake masa ga ɗaci da yakejin zuciyar tasa na masa, idan ya runtse idanunsa sai ya ga hoton Hisham da Jidda da sauri ya buɗe idanun nasa a firgice tare da furta "Ni!." Da ƙarfi cikin ƙaraji har sai da tutu ta tsorata da sauri tace.
"Yaya Nameer meya sameka, hankalina ya tashi Yaya Nameer please meke faruwa."?
Idanunsa da suka gama rinewa ya ɗago ya kalli Tutu wani irin haushinta yaji bakinsa ya cije bai kulata ba ya juyar da kansa gefe, cikin tashin hankali Tutu ta kuma fuskantar Nameer ta sunkuya a gabansa tace.
"Yaya Nameer please meyake damunka, dan ka faɗa min hankalina ya na tashe."?
Cike da jin haushin ta Nameer ya daka mata tsawa yace.
"Get out Tutu."
"Yaya Nameer na fita kace, kana cikin damuwa zaka ce na fita na baka waje, ta yaya zan iya barinka cikin wannan damuwar, idan kana cikin damuwa zuciyata bazata taɓa samun sukuni ba, bazan bar nan ba har sai ka faɗa min abinda ya sameka."
Cikin tsawa ya kuma ce mata.
"I told you to get out of this room! And don't make me worry more, Get out."
"Nameer...........
"Please! I say get out."
Yayi Maganar cikin tsawa yana yunƙurowa tamkar zai kai mata duka, a firgice Tutu tayi baya tare da tashi ta fice da sauri tana kuka, Nameer kansa ya dafe.
"I love you so much Jidda, how can I own you? why Hisham you will come between me and my happiness, why."?
Ya furta hawayen na kuma biyo idanunsa.

Tutu tana fita falo ta zauna a saman kujera tana rera kukanta, cikin munguwar damuwa da tashin hankali ta furta.
"Why are you expelling me from you Yaya Nameer, what is happening to you? Your concern lifts my spirits, I love You so much Yaya Nameer, i love You."
Ta furta cikin tashin hankali tana cigaba da kukanta, tana cikin kukan Hisham ya shigo tsayawa yayi cak yana kallon Tutu tare da furta.
"Ke kukan uban me kike yi me aka miki.?"
Jin muryar Hisham yasa Tutu miƙewa da sauri ta faɗa jikinsa tare da kuma sakin kuka mai sauti.
"Tutu tambayar ki fa nake wht happening.?"
Cikin kukan tace.
"Yaya Nameer yaya Nameer ne yaya Hisham yana can."
"Nameer kuma meye Nameer ɗin ya miki dukanki yayi."?
Hisham ya mata tambayar a takaice.
Hawayen ta ta share tana sauke ijiyar zuciya tace.
"A'a ni ba dukana yayi ba, shine dai yana can ya shigo cikin damuwa har hawaye yake idanunsa kuma sunyi jajur da na bisa bedroom ɗinku ina tambayar sa meya samesa shine yamin tsawa wai na fita na basa waje, hankalina ya tashi Yaya Hisham saboda ban taɓa ganinsa a cikin irin wannan mummunan yanayin ba."
Numfashi Hisham ya saki cike da mamaki yace.
"Nameer kuma yake cikin damuwar da har zata sanya sa kuka, kuma ban sani ba kai mtsss bara dai na je na gani."
Yayi Maganar yana cire Tutu daga jikinsa ya haura bedroom ɗin da sauri, Tutu numfashi ta saki har yanzu tana cikin tashin hankali wayarta ta ɗauka ta kira kawarta Samira tace tazo zasuyi magana kafin ta katse kiran tana zama ta zuba tagumi.


A firgice ya tura bedroom ɗin nasu ko sallama baiyi ba turus ya tsaya ganin Nameer cikin yanayin da Tutu ta sanar dashi.
_Da gasken kuwa hawayen yake_
Hisham ya furta cikin zuciyarsa kafin ya ƙaraso kusa dashi da sauri ya zauna yana dafa kafadarsa jin an da fa kafadarsa yasa Nameer saurin ɗago rinannun idanunsa ya zuba a cikin na Hisham da baisan ma shigowarsa ba.
"Nameer dama ashe zaka shiga damuwa ka shigo ɗaki kayi kuka kai ɗaya, ni bazaka sanar dani ba yaushe ka fara ɗaukar damuwarka taka kai ɗaya, ba raba damuwar junan mu muke ba why zaka ɓoye min why Nameer.?"
Hawayen dake fuskarsa Nameer ya sa hannu ya goge tare da girgizawa Hisham kai yace.
"No Hisham babu wata damuwa da take damuna, kawai kaina ke ciwo sosai jin kan nake tamkar zai rabe gida biyu, sai kuma tsinkewar zuciya da ke damuna jima nake kamar na tattara kayana na gudu."
Numfashi Hisham ya saki tare da cewa.
"A'a Nameer wannan damuwar taka ba ta ciwon kai ba ne, tsinkewar zuciya kuma meye ma'anar sa, amma ka tashi muje asibiti a maka gwajin bp."
"Gwajin BP kuma Hisham me zai haɗani da Bp ni da ba wata damuwa bace gareni, please Hisham ka ƙyaleni da wannan maganar na samu nutsuwa tukunna idan kaina na ciwo kafi kowa sanin bana son damuwa please dan Allah."
"Nameer ni fa nace maka wannan damuwar ba ta ciwon kai bane akwai dai abinda yake damunka wanda ni kake ɓoye min, ciwon kai bazai saka tsinkewar zuciya ba Nameer, kuma ɗazu munyi waya da Hassan abokinka yace min ya shigo gari ya nemi layinka baya tafiya sai ka taɓa sa."
Cike da fara gajiya da maganganun Hisham ga shi haushin sa yakeji yau yace.
"Hisham na ce maka kaina ne yake ciwo Final babu abinda zan ɓoye maka a wannan duniyar, Please kabar ni haka."
"Okay shikenan amma dai kasha magani, ni fita ma zanyi na bar maka bedroom ɗin, zanje garden zamuyi magana da Sadiq gacan ƙanwarka a falo ka sanyata kuka."
Hisham yayi Maganar yana tashi ya fita, da kallo Nameer ya bisa zuciyarsa na masa ƙunci komawa yayi ya kwanta tare da runtse idanunsa da ƙarfi.
_Hassan ya dawo tabbas ya dawo akan gabar da nake buƙatar sa, shine zai warware min wannan matsalar da na ke ciki na MAHAUKACIN SO, ita kuma Tutun kuka ta ke hmm! Ya zataji kenan idan ta fahimci cewa bazan iya Auren ta ba, me zai faru idan har su Abba suka fahimci akwai alaqar Soyayya tsakanina da Tutu kuma suji cewa bazan aureta ba, wanne irin hukunci Abba zai yanke min?._
Nameer ya furta cikin zuciyarsa yana jin jikinsa duk babu daɗi shi kansa bai so ace ya rabu da Tutu ba sai dai babu yadda ya iya da zuciyar sa JIDDA itace kaddararsa da ke biye dashi tamkar Inuwa bayajin zai iya haƙura da

Please Login or Register in order to submit comment