Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hisham ya sanya har dimple ɗinsa na loɓawa yace.
"Yeah meye Kuma abun mamaki just wanted you to impress me, so why should be surprised? or do you want me to tell you I love You."
Zaro idanunta Sosai Jidda tayi tana mamakin anya Hisham ne, kafin tace.
"To ikon Allah gani nayi kamar ba Hisham ɗin da na sani ba, dole nayi mamaki, cewa kayi fa ina burgeki, so Hisham.........
"Ya isa haka Jidda karki ce komai tabbas rashin jituwa ya faru tsakanin mu a baya amma hakan bashi yake nufin bani da hali mai kyau ba, zan ƙara baki haƙuri a karo na biyu Jidda be patient and forget what happened in the past and take that Hisham that you know now is not a new one."
Wani irin sanyi taji jikinta yayi tunda ta ke da Hisham bai taɓa burgeta ba irin na yau lallai yau ta yarda da maganar Nameer Hisham mutumin kirki ne mune bamu fahimce sa yadda ya kamata ba, murmushi Jidda ta saki tace.
"Hisham ko Ubangijin da ya hallice mu muna masa laifi kuma ya yafe mana to meyasa mu bazamu yafewa junanmu ba, Hisham daga yau na manta da abinda ya faru a baya, a yanzu na ɗaukeka sabon abokina, komai ya wuce."
Murmushi Hisham ya saki cikin zuciyarsa ya furta _lallai ko da kin manta abinda ya faru a baya, to tabbas tarihi zai maimaita kansa da kaina zan tuna miki da wannan mantuwar da kikayi yayin da zaki tafi da ciwon zuciya na bakin ciki, wata kila ma hakan ya zamo ajalinki wannan alƙawarin na ne._ kafin yayi murmushi yace.
" Naji daɗi da ya kasance kin manta komai Jidda, tabbas kin samu sabon abokin da zai tare miki wani bangon, zamu ciza kuma zamu hura tare barka da samun sabon aboki."
Dariya Jidda tayi kafin kuma ta ɗan haɗa ranta cikin zolaya tace.
"Amma tsaya Malam na tambayeka, ta yaya zaka iya abota da mai izza, jiji da kai, shegen taurin kai, ta yaya zaka iya answer me idan har kana son nayi aiki a Companyn nan yau."?
Dariya sosai Hisham yayi, kafin yace.
"Yess! Shiyasa nace kina burgeni ai, taken mace kenan izza da ji dakai wannan na mace mai aji ne, taurin kai ɗin ne dai Hisham zai sauya miki shi."
Murmushi Jidda tayi ta girgiza kanta ganin yau wai Hisham ke dariya abun kamar almara, bakinta ta taɓe tare da mikewa tsaye tana cewa.
"Kafin Hisham ya gyara Jidda sau ɗaya na tabbata ita ta gyarasa sau goma, muje ka kaini office ɗina na fara sanin abubuwan da suke gabana."
Murmushi yayi tare da cewa.
"Dole dai sai kin fara shiga office ɗina na gama sanar dake ayyukan ki sannan na haɗaki da wanda zasu nuna miki yadda aikin mu yake tafiya dole sai kin zagaya Kinga yadda muke harkokin mu, dan haka muje office."
"Okay."
Jidda tayi maganar tana tashi, tare suka shiga office ɗin, suna zance kamar abokan da sukayi shekara da sabawa.


Nameer bai shigo office da wuri ba har wajen 12:30 tunda yazo ya shiga office ɗin sa bai fito ba, tare da sanar da sakatariyar sa duk wanda yazo neman sa tace bazai ga kowa ba yau, shuru yayi cike da tunani da zullumin yanda zaiyi ya rabu da Tutu, idanunsa ya runtse tare da miƙewa tsaye kaiwa da komowa yake a office ɗin sa duk damuwa ta ishesa. _meyasa Kan Tutu baya ja ne, meyasa bazata fahimci baya ra'ayinta ba, duk wannan kuskure na ne da na fara sonki Tutu, Hmm Jidda itace muradina, ina sonta fiye da komai a rayuwata, meyasa na kasa sanar da ke soyayyata Jidda ya kamata ki fahimci ina sonki fiye da yadda uwa ta ke son ɗanta, kece alƙibilata Jidda, I love you so much, i love You so much Jidda, Hmmm! Mtsss ya zamo wajibi na bayyana miki soyayyata idan ba haka ba ciwon sonki zai illata zuciyata, yaya zanyi da soyayyar Tutu ya zanyi na rabu da ita cikin sauƙi, Hmm! Lallai ya zamo wajibi ki cire Soyayyata a ranki a baya Tabbas na soki amma a yanzu babu ɗigon sonki a zuciyata, na yadda da kalmar hausawa da suke cewa so tsuntsu ne yakan tashi daga wannan bishiyar ya koma wata._ dafe kansa yayi tare da neman waje ya zauna, wayarsa ce tayi ringing duban wayar yayi yaga Dear murmushi ya saki tare da ɗaukar wayar ya kara a kunnensa.
"Hello Jidda."
Daga can Jidda tace.
"Gani a bakin office ɗin ka, sakatariya ta hanani shigowa, kace mata wai baka bukatar ganin kowa yau meyasa.?"
Numfashi ya saki yace.
"Bawa Sakatariyar wayar."
Miƙa mata wayar Jidda tayi ta amsa umarni ya bata da tabar Jidda ta shigo, bawa Jidda wayar tayi tace zata iya shiga shiga Jidda tayi da sallama, Nameer yana zaune ya dafe kansa kusan bakinta Uku tana sallama baiji ba ya lula duniyar tunani, zama Jidda tayi tare da buga teburin dake gabansa a ɗan razane Nameer ya ɗago kansa ganin Jidda ya sashi sakin numfashi tare da cewa.
"Har kin shigo."?
"Eh tunanin me kake haka ina ta sallama bakaji ba, da alamu Dai yau kana cikin damuwa."?
"No babu wata damuwar da nake da, kawai yau stress ɗina ne haka, ya akayi.?"
"Wannan file ɗin ne Hisham yace na kawo maka ka duba."
Amsa Nameer yayi ya buɗe file ɗin, kafin yace.
"Zanyi aiki a kansa kafin na dawo miki dashi sai ki nemi mai file ɗin idan ya dace da muyi aiki dashi."
"Okay to shikenan bara na koma office."
"Da wuri haka, tun bamuyi hira ba, dama fa neman ki nake akwai Magana mai mahimmanci da nake son mu tattauna, amma yanzu nasan lokacin aiki ne, mayi maganar wani lokacin."
"To shikenan ba damuwa bara naje ni."
Kansa Nameer ya haɗa kafin Jidda ta fita.





**********


Inda suka saba haɗuwa yauma dai nan suka tsaya, Tunde ne ya dubi Sadiq yace.
"Mama tace har yanzu taji shuru babu wani motsi, babu wani harin da ka aikawa Hisham meyasa."?
Murmushi Sadiq ya saki tare da cewa.
"Ka ce mata yaƙin sunƙuru nake bana bukatar kai hari cikin gaggawa, ka sanar da ita cewa ta yadda dani ne yasa ta bani wannan aikin dan haka ta saka ido kawai tayi kallo, ta yaya kuke tunanin na kai masa hari, wato na fargar dashi cewa ana neman rayuwarsu ne, ina bazan taɓa barin ya fahimci hakan ba nafi bukatar na kaisa ƙasa kafin ya ankare."




_____________________________________







_Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._



*0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180*



_Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan auli yasmut siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai._



*Like Share and comments my fan's🥰*






_UMMU NASMAH CE✍🏻_
[7/6, 8:07 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*




*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*


*FREE BOOK ONE📚*




*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻




*_Page 43 to 44_*




Dariya Tunde ya saka kafin yace.
"Hakane amma kasan bana bukatar ɓata lokaci, kusan kullum sai na faɗa maka wannan kalmar, kawai ka aika masa makamanka."
"Okay tunda haka kuke bukata kun matsa zan jaraba, amma duk abinda ya biyo baya ku kuka da kanku domin kuwa ni zan iya zillewa, zan saka aiki tunda naji next week ne zaka fara aiki, zan nemo guba, da za'a sawa Nameer a jus ko copee ta kansa zamu fara, zan sanar da kai yadda aikin zai kasance, guba ce mai haɗarin gaske dole sai ka kula."
"Takan Hisham ya kamata mu fara ba Nameer ba domin kuwa nameer bashi da gadon IYABO Hisham shine jininsa dan haka shine zai zamo abin harin mu na farko da jinin Iyabo ya kamata mu fara yaƙi ba ɗan riƙo ba."
Tunde yayi Maganar cikin rashin gamsuwa da maganar Sadiq tsawa Sadiq ya dokawa Tunde tare da cewa.
"Karka kuma bani umarni domin kuwa ba sayata kukayi ba, idan har ka kuma bani umarni to kuwa zan ijiye muku aikin ku sannan kuma na zamo Mutum na farko da zai tarwatsa aniyarku, kunsan waye Sadiq yana da kyau ku kula, da ƙwaƙwalwata zanyi aiki ba da daƙiƙiyar ƙwaƙwalwarka ba, zan kama gabana yanzu idan kaje ka sanar da tsohuwar kakar taka yadda mukayi yanzu, tabbas Nameer shine first target ɗin mu."
Sadiq yayi Maganar yana buɗe murfin motar da sauri ya fice ya tokare fuskarsa da kula posingcap, numfashi Tunde ya saki tare da jan motar ya nufi gida, Wamimo ya tarar a falon nasu babu Mamabisola zama yayi gefen kujera mai biyu cikin harshen yarbanci su gaisa da Wamimo kafin yace.
"Mo ni Mama?"
Ya tambayi Wamimo cikin harshen yaruba, kitchen Wamimo ta nuna masa tace.
"O wa ni ibi idana ounjẹ bayi nduro fun ọ"
"Okay bara naje na sameta kawai."
Tunde yayi Maganar yana tashi ya shiga kitchen ɗin tana wajen gas tana tafasa ruwan Lipton, Tunde ya tsaya gefenta ransa a haɗe.
"Na ga ka haɗa ranka meye Sadiq ɗin ya maka.?"
"Babu abinda yamin Mama sai dai da alamu bamu samu abokin aiki ba, domin kuwa baya amsar umarni daga garemu wanda a wannan tsarin mune muka ɗaukesa aiki kuma ya zamo wajibi ya ɗauki umarninmu."
"Ban tari numfashinka ba Tunde, amma ka sani aikin kai da kai muke da Sadiq bani gishiri na baka Manda ne dan haka nemosa mukayi akan gaɓar da ta dace, ƙwaƙwalwarsa na ja sosai dan haka muje dashi a yadda yake so mu bukatar mu burin mu ya cika, da zarar burinmu ya cika to ƙofar rago zamu masa."
"Okay sai yanzu na fahimci karatun, yace da Nameer ya kamata a fara bansan dalilinsa na hakan ba, amma koma menene ke na fahimce ki."
"Tunda ka fahimce, kaje kawai mu barsa da ƙudirinsa."
"Shikenan Mama ko part ɗina ban shige ba nazo nan bara naje."
Tunde yayi Maganar yana sakin murmushi, itama Mamabisola murmushin tayi kafin Tunde ya bar kitchen ɗin.




***********

Jidda ganin ta tashi aiki da wuri ya sata biyawa gidan su Basmah, dan ta sanar da ita ranar zata koma gida, ta samu kuwa ta koma, Abban Basmah ta shiga ta gaisar kafin ta shige ɗakin Basmah tana zaune tayi shuru da alamu tunani take ga wayarta kuma a gefe ana kira bata lura ba zama Jidda tayi tare da dafa kafaɗar ta tace.
"Ke tunanin me kike haka ga wayarki kuma majnunun naki yana kira."?
Tsuka Basmah taja tana kallon wayar tata tare da jan doguwar tsuka cike da mamaki Jidda tace.
"Basmah Ahmad ne fa yake kiranki kika ja tsuka lafiya ko kunyi faɗa ne."?
Kanta Basmah ta girgiza tare da cewa.
"Faɗa kuma kema ai kin san bamu taɓa faɗa da Ahmad ba, kawai dai wayar ce yau bana son yi har kun tashi daga wajen aikin ne."?
Kanta Jidda ta ɗagawa Basmah tace.
"Eh na dawo 5:00pm suke tashi daga aiki ga ko wanne ma'aikaci."
"Jidda ina son na ijiye aikina na jarida nazo na nemi aiki a Companyn ku nima, saboda bana jin daɗin aikin babu ke."
Ɗan zaro idanunta Jidda tayi tace.
"Basmah kinyi shaye-shaye ne da kike faɗar wannan maganar."
"Jidda sai nayi shaye-shaye ne zanbar aiki a Aminci, just ce miki nayi na gaji bana son aiki dasu, ina bukatar sauyi, fine babu wani laifi tunda ba Companyn ubana bane da zan tabbata anan ke ko Companyn ubanane idan na gaji zan iya sauya waje bare wannan da bani da alaka ta kusa ko ta nesa dashi."
"Amma ai komai yaya ne bai kamata ki bar aiki a ƙarƙashin Aminci ba, aikin jarida yana da matukar muhimmanci, ko nima ba'a son raina nabar aiki dasu ba, amma idan kina ganin hakan yafi miki shikenan sai ki fara tuntubar Nameer kiji."
Numfashi Basmah ta saki tare da cewa.
"Ba Nameer zan tuntuba ba, Hisham zan tuntuba saboda shi mutumin kirki ne, infact ma hankalina yafi kwanciya dashi."
Dariya Jidda ta saki tace.
"Au har Hisham ne yafi Nameer kirki, impossible kawai dai son ranki kike faɗa Malama."
"Ke nifa Hisham burgeni yake wallahi, gayen yayi arayuwa kina ganin handsome guy, kinga kamar fa yadda Nameer ɗin ya faɗa ne a baya HISHAM mutumin kirki ne kawai rashin fahimta yasa muke masa kallon wani bahagon mutum amma ni yanzu na fahimci waye Hisham."
Taɓe bakinta Jidda tayi tace.
"Hmmm! Hakane nima na fahimci hakan amma duk da Hisham bazai kai Nameer kirki ba, ke Kinga ni wannan chapter ta isheni haka dama jikin Abba nazo gani, kuma tunda jikin da sauƙi tashi ki rakani nayi gida."
Jidda tayi maganar tana tashi, tashi itama Basmah tayi Jidda ta shiga ta yiwa Mama sai da safe kafin Basmah ta rakata har waje.




**********


Da daddare Jidda tana zaune suna hira da Umma taji wayarta tayi ringing dubanta ta kai ga wayar taga Hisham, murmushi ta saki tare tashi ta koma ɗaki tana ɗaga kiran.
"Hello."
Jidda tayi maganar tare da yin shuru daga can Hisham yace.
"Hi ƙawata ya akayi kin koma gida lafiya."?
Murmushi Jidda tayi tace.
"Na koma lafiya, ya naka gajiyar aikin."?
Murmushi Hisham yayi yace.
"Gajiya kuma sai kace mace, no ni ban gaji ba, amma ina fatan kinji daɗin aiki da Companyn mu ko.?"
"Eh to da dai da ne sai nace aiki da Hisham babu daɗi amma da Hisham ya sauya lokaci guda aiki dashi yafi komai daɗi, naji daɗin fara aiki a ƙarƙashin ka.''
Ɗan dariya Hisham ya saki yace.
"Masha Allah kice Hisham ya ciri tuta, kin san meye Jidda.?"
"A'a sai ka faɗa."
Gauron Numfashi ya saki tare da ɗan hura iska a Speaker wayar, yace.
"Ke macece ta musamman, kina abubuwa da yawa wanda ba ko wacce mace ta ke dashi ba, ke ta dabance da sauran mata, kina burgeni sosai Jidda, gaki da kyau ga ado ga diri ga kyawun sura ga ilimin addini dana zamani, bakina yayi kaɗan ya lissafo ingancinki shiyasa nace ke macece ta musamman Jidda."
Murmushi Jidda ta saki sosai taji daɗin maganganun Hisham.
"Duka wannan yabon ni na cancanci amin sai na ke ga kamar bani da wannan abubuwan da ka lissafo."
"Bazaki fahimci hakan bane ke, amma ni na hango abinda ke baki hango ba, bara na barki haka dama na kira naji kin isa lafiya ne, ki gaishe da Umma."
"Shikenan zataji na gode."
"Okay bye."
Hisham yayi Maganar yana katse kiran murmushi Jidda ta saki tare da lumshe idanunta ta furta..
_Hmmm! Hisham kai mutum ne na musamman wanda ya zauna da kai shine kawai zai fahimci hakan._
Tayi Maganar tana sakin numfashi tare da tashi ta dawo wajen Umma.
"Ke dawa kike waya ne.?"
Cewar Umma Jidda zatayi Magana yaro ya shigo yace.
"Wai Jidda tazo inji Abdulra'uf."
"Abdulra'uf kuma na masa meye jeka ce ina aiki bazan samu fitowa ba."?
Umma ne tace.
"Kai yaro kace tana zuwa."
Da sauri Jidda ta kalli Umma cikin mamaki, Umma cewa tayi.
"Kalleni da kyau ja'ira yo meye laifin Abdulra'uf da zaki dinga nuna masa ƙiyayya gani nayi wanda yace yana sonka ya fi maƙiyinka komai lalacewarsa, maza kije ki sauraresa baki san inda alkairinki yake ba, yaron arziki da yake mutunta naki ke kice zaki nuna masa ƙiyayya, wannan ba tarbiyya ta bace."
Bakinta Jidda ta tura tace.
"Ni fa Umma bana sonsa, dan haka banga dalilin da zaisa na dinga tsayuwa dashi ba muna ɓatawa juna lokaci, kawai Umma ke babu ruwanki a tsakanin mu."
Abdu ne yace.
"Amma fa Adda gani nayi Abdulra'uf bashi da laifi yana da sana'ar sa, kuma mutumin kirki ne, yana da cikakken ahali, ina ga wannan ake bukata a neman Aure."
Harara Jidda ta watsawa Abdu tace.
"Kai kuma wa ya saka bakinka a cikin wannan maganar, ko Maganar ne.?"
"Ya fiki gaskiya ki daina masa tsawa, ki tashi kije kiransa maza."
Miƙewa Jidda tayi ranta a ɓace ta yayiɓi Hijab ɗinta zata fita taji Umma tace.
"Au saboda zaki wajen maƙiyinki shiyasa bazaki kimtsa ba, zaki fita haka to maza ki dawo ko ɗan powder ki goga a fuskar ki."
"Kanta Jidda tasa ta fice ba tare da ta juyawa ba kanta Umma ta girgiza ta cewa Abdu.
"Rabu da ita sai dai ta fita ko bata so, ni banga laifin yaron nan ba da tabi ta ɗaura masa tsana, yaron da tun yana ƙanƙaninsa ubansa ke tahowa dashi a hannu ƙofar gidan ga, nasabar sa duk an sani amma tsabar iya shege irin na jiddatul kair tabi ta ɗaura masa karan tsana, na rasa dalilin da yasa bata sauraron samari duk wanda yazo zance wajenta sai tasan yadda tayi ta koresa, ni wannan lamari harya fara bani tsoro, shuru kawai nayi ina kallonta ta mai sheni shasha bansan sonta shi Abdulra'uf yake ba."
"Hmmm! Umma ni fa na rasa me yake damun Adda, ko fa zancen Aure bata so a mata."
Abdu yayi Maganar yana kallon Umma.
"Barni da ita zan daidaita ta ne, ka tashi kaje ka karɓo min kamu a wajen Iya."
Amsawa da to Abdu yayi yana tashi ya fita.



Ko da Jidda ta fita ta samu Abdulra'uf tsaye jikin gidan Alhaji Barau da ke manne jikin gidan nasu, tsayawa Jidda tayi tare da sallama ta kawar da kanta gefe fuskarta a haɗe daga wannan sallamar Jidda bata kuma magana ba, ko arzikin gaisuwa bai samu ba, numfashi ya saki ganin Jidda bata da niyyar magana yasa shi nisawa yace.
"Da ganin fuskar ki baki so kika fito, kiyi haƙuri idan na takuraki ba laifina bane laifin zuciyata ne, na kasa cireki a cikin zuciyata, ina sonki, amma na rasa dalilin da yasa kike nuna min ƙiyayya, Meyasa haka Jidda.?"
Sai yanzu Jidda ta ɗago kanta ta kalli Abdulra'uf tace.
"Naji daɗi da kamin wannan tambayar, ba ƙiyayya nake nuna maka ba, bana son na yaudareka saboda bana jin zan iya Auren ka, kayi haƙuri ba wai ina faɗa maka wannan maganar ba ne saboda kaji zafi a ranka bane, a'a ina faɗa maka gaskiyar abinda yake raina ne, bana jin sonka na Aure a cikin zuciyata karmu yaudari juna dan Allah kayi haƙuri ka nemi wata Please."
"Hakane na juma da fahimtar bakya sona sai dai idan na zauna ina yawaita tunanin cewa ko wani mungun hali nake dashi wanda bazaki iya aurena ba saboda shi, kokuwa saboda ni talaka ne shiyasa, ki amsa min wannan tambayar abinda ya kawo ni ƙofar gidan ku kenan yanzu."?
"A'a ko ɗaya Abdulra'uf baka da wani mungun halin da za'a ƙika saboda shi halinka mai kyau ne, haka kuma ni ba yar kowa bace dan haka bazan ce sai mai arziki zan aura ba, sonka ne kawai banayi ka fahimta kayi haƙuri kaje ka nemi wata zaka samu wacce ta fini idan har bakaji daɗin maganata ba, dan Allah kayi haƙuri."
"Ba sai kin bani hakuri ba Jidda ba komai Allah ya haɗa kowa da rabonsa, amma ki sani ina jinki a cikin zuciyata bazan taɓa daina sonki ba Jidda Allah ya baki miji na gari wanda zai riƙeki bisa gaskiya da amana, ni zan tafi ki gaishe da Umma."
"Na gode da ka fahimce ni kaima Allah ya baka wacce ta fini."
Jidda tayi maganar tana komawa ciki.



**************


Bayan sati guda


Damuwa da soyayyar Jidda ta hana Nameer sakat duk sanda ya kasance shi ɗaya babu abinda yake sai tunaninta, zuciyarsa ta gaza samun nutsuwa, sai yayi yunkurin sanar da ita Soyayyar sa sai yaji ya kasa hakan, yayin da tsananin shaƙuwa ta shiga tsakanin JIDDA da HISHAM ya zamo tamkar abokinta na yarinta, zuciyarta ɗaya take jin Hisham sai dai shi kuwa har yanzu cikin zuciyarsa tsanar JIDDA ce a cikin ta, yana sake mata ne kawai saboda burin samun cikar ƙudirinsa akanta.



Yau takama asabar ranar weekend yana zaune shi kaɗai a falo ya kira JIDDA, da sanar da ita zasu haɗu ya fitar da abinda ke ransa ko zai samu sukuni, ringing ɗaya ta dauka, daga can tace.
"Barka da safiya Nameer."
"Barka Jidda ina fatan yau kina free ina son zamu haɗu ne da ke a inter room garden."
Numfashi Jidda ta saki kafin tace.
"Okay ba damuwa amma lafiya kuwa sannan zan iya zuwa da Basmah."?
Murmushi NAMEER ya saki tare da cewa.
"Zaki iya zuwa da Basmah, wannan kiran alkairi ne Jidda fatana dai mu haɗu yau ɗin."
"Okay da misalin ƙarfe nawa zamu haɗu."?
"By 4:30pm."
Nameer ya faɗa a takaice, murmushi Jidda tayi tace.
"To shikenan sai mun haɗun ka gaishe da ummin ku."
Da zataji Nameer ya amsa kafin ya katse kiran dai-dai Hisham na sauƙowa ya zauna gefensa yana cewa.
"Ya kake zaune kai ɗaya, ina Ummi da Tutun suke.?"
"Tutu ai tana da school yau, Ummi kuma bata juma da

Please Login or Register in order to submit comment