Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kanta Jidda ta ɗago hawaye na tsiyaya ta kallesa kuka ne yaci ƙarfinta madadin ta masa magana sai ta fashe da kuka, kansa Hisham ya dafe yana cije bakinsa, ya bigi teburin gabanta.
"Oh my god, hmmm! Ya lalata miki rayuwa ko, ki faɗa min gaskiya mana, ya miki fyade ko."?
Ita dai Jidda taƙi magana sai kukanta take ta fama, cike da jin haushi ya daki bango gefensa cikin ɓacin rai ya furta.
"Kuka! Kuka! Kuka! Wannan wanne irin munafurci ne, uban meye ya kaiki office ɗinsa nan aka kiraki ne, kin sani a gaba sai kukan munafurci kike min, bayan ya gama lalata rayuwarki duk macen da ta rasa budurcinta to ki sani ta rasa kimarta da mutuncinta har ma da kimar iyayenta, gashi kema kin shiga wannan jerin waɗannan Mutanen, khabeer ya hallaka miki rayuwa ya cuc.............
"Ya isa haka Hisham! Ka barni da abinda ya dameni, ka barni nayi kukana a duk sanda na haɗa hanya da kai masifa nake gani duk da kayi ƙoƙarin ƙwatata a hannun wannan azzalumin, amma babu alkairi a tarayyata da kai Hisham, bana bukatar aikin na haƙura zanje na riƙe talaucina Allah bazai hanani yadda zan kula da ahalina ba, da kake kiran fyaɗe! Fyaɗe! Waye yace maka ya rabani da darajata, kana ina akayi da zaka yanke hukunci bisa son ranka ko ka yarda ko kar ka yarda ni ban rasa mutunci na ba, babu abinda ya min Allah ya kwace ni a hannunsa, akwai CCTV Camera kaje ka duba ka gani idan yamin fyaɗe, ka daina yanke hukunci da son ranka ka buɗe min ƙofa nabar wannan Companyn."
Iska ya fesar daga bakinsa yace.
"Babu Alkairi a tare da ni kakace, Hmm! Ƙarya kike duk inda na shige alkairi ne ke bin bayana, ki sani babu sharri a tare dani, da kuma akwai sharri a tare dani da banzo na ceceki ba kije ki kwanta kiyi tunani, kije mun ɗaukeki aiki."
Hisham yayi Maganar a zuciye yana ɗaukar takaddun ta ya fita dasu, numfashi Jidda ta saki hawaye na biyo idanunta.


Nameer ganin Hisham ya buɗe ƙofar ya fito a fusace ya sashi shiga da sauri Basmah na biye dashi, Jidda Basmah ta riƙe har yanzu itama ranta na ɓace, Nameer ne yace.
"Kiyi haƙuri Jidda nasan Khabeer bai miki fyaɗe ba, ya dai kuskureki, amma na miki alkawari sai ya gane kuskuren sa, muje na kaiki gida da kaina."
Kanta Jidda ta girgiza tana jan majina tare da sanya hannu ta share hawayen ta, tace.
"Bazan koma gida a haka ba Umma bazata ji daɗi ba, zanje kawai gidan su Basmah na sauya kaya."
"Okay to muje sai na sauƙeki a gidan su Basmah."
Kanta ta girgiza tare da tashi suka fita.


Hisham tunda ya fita daga interview room ɗin motarsa ya shiga tare da wurga takaddun Jidda a bayan motar, darect Joint ya nufa, baiyi wani parking ɗin arziki ba ya fito, ko motar bai rufe ba, sai security ne ya taho da sauri ya rufe masa motar, teburin da babu kowa ya samu ya zauna tare da runtse idanunsa, abubuwan dake faruwa ne suke dawo masa a cikin idanunsa.
_Aduk sanda na haɗa hanya da kai masifa nake gani, babu Alkairi tarayyata da kai_
Da ƙarfi Hisham ya furta.
"Kaga ƴar shegiya, bazaki san tsakanina da ke babu Alkairi ba sai sanda na karya miki zuciya a ranar zaki tabbatar da haɗuwata da ke masifa ce, zan tabbatar miki da wannan furucin naki sai na sanyaki cikin masifar da bakiyi zato ba, tabbas zan ɗaukeki aiki domin shine damata da zan jawoki jikina."
Yayi Maganar yana zarar sigari, leta ya ɗauka a gefen table ya kunna sigarin, zuƙa yayi tare da lumshe idanunsa, sai kuma ya saki murmushi.
"The game is ready, wasan yanzu za'a fara."
Hisham yayi Maganar bakinsa ɗauke da murmushi, Sadiq ya dannawa kira 4 miss Call bai ɗaga ba ya juma sosai yana shan sigarinsa ko ruwa bai sha ba a wajen kafin ya tafi.



************


Tsakiyar dare wajajen 2 na dare idanun Jidda suka buɗe bacci ya gagareta zullumi da tsoron duniya suka shiga zuciyarta rayuwa ta lalace mutane duk sun zamo marassa imani, an maida fyaɗe ruwan dare, ko dan saboda ba'a hukunta masu aikata wannan laifin ne shiyasa laifin ya yawaita an maida mutunci mace ba komai ba, numfashi Jidda ta saki tana tuno abinda ya faru, _yanzu da Hisham baizo ya ceceni ba da yaya kenan da yanzu na rasa mutunci na_ tayi Maganar zucin tana sakin numfashi tare da furta.
"Duk munin halin Hisham ya taimakeni domin kuwa da badan shi ba da yanzu rayuwata tana cikin tasku, lallai ya taimakeni, ashe dama Hisham zai iya taimakon wani, lallai yadda na ɗaukesa ba haka yake ba, meyasa ma na faɗa masa magana marar daɗi bayan shine ya taimake ni, bai dace na kirasa da masifa, wannan kalmar bata dace ga mutumin daya taimaki rayuwar ka ba, nayi kuskuren faɗa masa wannan kalmar ya zamo lallai na basa hakuri, mtsss! To amma Hisham yana da jiji da kai da isa muddun na basa haƙuri to zai rainani ne, amma ai durƙusawa wada ba gajiyawa bane, kai ina anya zan iya bawa Hisham haƙuri kuwa."?
Ta yiwa kanta tambayar tare da yin shuru tana nazari ringing ɗin wayarta ta ji, duban wayar tayi taga bakuwar numbern hannun ta sa ta ɗauki wayar tare da cewa.
"Hello da wa nake magana."?
Daga can taji ance.
"Hisham."
"Hisham kuma."
Jidda ta furta cike da mamakin ina ya samu numbern ta.
"Eh Hisham kinyi mamaki ne.?"
"Ƙwarai kuwa gani nayi babu haɗin danga da garahunu."
Daga can Hisham yayi murmushi tare da cewa.
"Ayya to ai muddun ɓera zai shiga turken mage ki sani dole wannan magen tazo neman wannan ɓeran wataƙila sata ɓeran yayi kinsan ba'a raba ɓera da sata."
"Au ni ce ma ɓerar, amma dai kaci mutunci na, ni zaka kira da ɓera, me na sata a Companyn naku Banda bala'in da na gani."
Dariya sosai Hisham yayi kafin yace.
"Ayya Malama ɓera meye na jin haushi saboda na kiraki ɓera, shifa ɓarawo dole ne ya amsa sunan ɓera."
Cike da hasala JIDDA tace.
"Malam wai me kake nufi da ni ne, ka kirani tsakar dare kana neman faɗa min baƙar magana, idan Mutum ɗan mutunci ne zai kira Mace cikin wannan daren ne."
Dariya ya kuma mata har tana jiyo sautin dariyar tasa yace.
"Haka kuma idan Macen yar mutunci ne ko da an kirata tsakiyar dare bazata ɗaga ba, kinga kuwa marar mutunci ne ya haɗu da ƴar Uwarsa marar mutunci."
Kanta Jidda ta riƙe cike da jin haushi taja doguwar tsuka tare da katse kiran tana furta.
"Banza."





_____________________________________



*Kuyi haƙuri da jina shuru da kukayi kwana biyu, hidima ce tasha min kai, ina muku fatan alheri masoya na ina kuma godiya da ƙaunar da kuke gwada min.*



_Akwai wadanda suka cemin zasu biya kuɗin JALALA amma basa son group na dinga tura musu ta PC to gaskiya idan ta pc kike so 500 zaki biya._



_Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._



*0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180*



_Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan auli yasmut siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai._



*Like Share and comments my fan's🥰*






_UMMU NASMAH CE✍🏻_
[6/8, 9:58 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*




*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*



*FREE BOOK ONE 📚*



*_Page 39 to 40_*




*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻



Tunda Hisham ya amshi takaddun Jidda kusan 14days babu wani sako sai dai abinda ya bawa Jidda mamaki yadda lokaci ɗaya shaƙuwa ta shiga tsakanin Umma da Hisham domin kuwa a kai akai yake zuwa gidan nasu ko Nameer bai shaƙu da Umma ba yadda Hisham ya shaƙu da ita kayan Abinci da wasu abubuwan buƙata na gida haka Hisham ke kawo wa su Umma, harta Basmah yanzu mutunci ne sosai ke tsakanin ta da Hisham yanda Hisham ke yiwa Umma biyayya kamar mutumin kirki ke kyace itace ta haifesa, maganar Khabeer kuwa tuni su Nameer suka Kaisa kotu, zama ɗaya aka yankewa Khabeer shekara bakwai a gidan yari na yunkurin fyaɗe da ya yiwa Jidda da taran Naira dubu ɗari wannan abu ba ƙaramin daɗi ya yiwa Jidda ba, sai dai har yanzu akwai guntun faɗa tsakanin Jidda da Hisham, Soyayyar Jidda kuwa ko yaushe ninkuwa yake a zuciyar Nameer yayin da ya kasa sanar da ita ko nuna mata alamun yana sonta.



Yau Jidda tana zaune ita da Basmah tace wa Basmah.
"Basmah wai yaushe ne zaki koma gidan ku, kinga tunda aka yiwa Abba aiki suka dawo gida ya kamata ace kin koma, nasan Mama idanu kawai ta zuba miki taga gudun ruwanki bazata ji daɗi ba."
"Au korata kike wai Jidda."
"Ko ɗaya Basmah gidanku gidan mu ne kamar yadda kike kallon gidan mu a naku, nasan dai Mama bazata ji daɗi bane da zamanki anan dole zata buƙace ki."
"To gobe INSHA ALLAH sai na koma."
Da Allah ya kaimu Jidda ta amsa dai-dai Nameer na sallama a cikin gidan nasu fuskarta a sake Jidda ta amsa kafin ya shigo, kujera ƴar tsugunne Jidda ta basa ya zauna.
"Sannu da zuwa Yaya Nameer."
Cewar Jidda murmushi Nameer ya saki tare da cewa.
"Yauwa sannu Jidda ke da Basmah ne.?"
"Eh wallahi yaya Nameer, ya aikin jiya da daddare ai na kiraka sai Hisham ya ɗaga wayar yace baka kusa."
"Eh tabbas bana kusa Basmah, ya akayi da wani labarin ne."
Murmushi Basmah tayi tace.
"A'a ba komai kawai dama gaisuwa ce, kuma na jika shuru kwana biyu shine Umma tace na kiraka naji ko lafiya."
"Ayya Allah sarki Umma na, bana gari kwana biyu naje Abuja."
Jidda ne tace.
"Gashi kuma Umman bata nan taje unguwa."
"Ba wajenta dama nazo ba, takaddun ki na dawo miki dasu, gobe zaki fara aiki, a ƙarƙashin Hisham, office ɗin Khabeer da ya bari wannan gurbin muka baki kece zaki tace ma'aikata na fannin goge shinkafa, ina fatan zaki iya aikin."?
Numfashi Jidda ta saki tare da cewa.
"Zan iya mana sai dai banso ace an ajeni a ƙarƙashin Hisham ba."
"Shine yake da alhakin tace ma'aikata, kuma shine ya baki wannan gurbin bani da ikon da zance masa meyasa domin aikinsa da ya juma yana yi."
Basmah cewa tayi.
"Ke dai kawai Jidda kice Allah yasa hakan shi yafi alkairi."
"Wannan shine gaskiya Basmah."
Cewar Nameer, kanta Jidda ta girgiza tace.
"To Allah yasa hakan yafi alkairi, jiya Abdu ya dawo yace yaje zai biya kudin makaranta sai suka ce masa, ai an biya masa wani yaje last week ya biya, nasan kaine ka biya kudin."
Cike da mamaki Nameer yace.
"A'a gaskiya bani bane infact ma bansan lokacin biyan school payment ɗin nasu yayi ba, to amma waye ne zai biya masa har 39k.?"
Cikin mamaki sosai Jidda tace.
"Ba kai bane to waye ne ikon Allah."
"Sai Allah amma dai ko waye ne wata rana zai bayyana, ni bara naje muna da meeting yanzu."
"To shikenan mun gode yaya Nameer gobe insha Allah zan fito da wuri."
"To Allah ya kaimu kya gaishe da Umman idan ta dawo."
Yayi Maganar yana fita, Jidda cike da mamaki ta dubi Basmah tace.
"To waye ya biyawa Abdu kuɗin makaranta.?"
Shuru Basmah tayi tana tunani kafin tace.
"Anya ba Hisham bane, kin fa san yanzu ya sauya, daga yadda kika sanshi."
"Gaskiya ne ya sauya tun sanda ya taimake ni lokacin da khabeer yaso keta min mutunci na, daga ƙwayar idanunsa yadda ransa ya ɓaci na tabbatar da ya sauya, da Hisham yazo har gidan nan yace nayi haƙuri da abinda yamin na yarda ya sauya sai dai ba'a yabon ɗan kuturu sai ya shekara goma da yatsa."
"Hakane yanzu ni bara naje nayi wanka sai nazo muje gidan ko."
"To shikenan sai kin fito."
Tayi Maganar tana jingina da jikin bango.




**********



"Wai Hisham ya kuke ciki ne da Jidda har yanzu zuciyarta bata fara yarda da kai bane, ya kamata zuwa yanzu ta fara yarda da kai, ka sani alƙawarin ku da Nameer na fitar da matar Aure sati biyu ya rage karka yadda ka kasa cika alkawari."?
"Sadiq komai taurin zuciyar ta na tabbata zuwa yanzu tana jina a ranta kasan meye dalilina."?
Kansa Sadiq ya girgiza yace.
"No sai ka faɗa."
"Dalilina shine komai bushewar zuciyar ta, tunda har na sunkuya a gabanta da mahaifiyarta na bata hakuri dole jikinta yayi sanyi, domin kuwa tasan abune mawuyaci wanda zaisa ni Hisham na bata hakuri, sai kuma Khabeer da ya saukaka min aiki, domin kuwa cetonta da nayi a hannunsa wannan kaɗai ya isa ta yarda da ni, uwa uba kuma tallafawa uwarta da nakeyi da wannan nakasasshen ƙanin nata, abu ɗaya ya rage min kuma shima sa ido kayi kallo, na tabbata nan da sati ɗaya zan bijiro mata da soyayyata kuma ina tabbatar maka ko shawarar wani bazata nema ba zata amince sani, ina tabbatar maka sai nasa rayuwarta a cikin taskun masifar da bata taɓa zato ba."
"Shege abokina gaskiya ƙwaƙwalwarka naja, kayi aiki mai kyau wasa yazo tsakiya."
Cewar Sadiq, sai kuma yace.
"Hisham ni wai Company nawa kuke dashi ne."?
Ɗago idanunsa Hisham yayi cikin mamaki domin kuwa ta yaya Sadiq zai masa wannan tambayar akan kadarorinsu kafin yace.
"Meyasa kamin wannan tambayar Sadiq, me hakan zai amfanar dakai."
Murmushi Sadiq ya saki _wato Hisham ya zargi wani abu a ransa kenan, ina bazaka taɓa gane santsin da nake ƙoƙarin yarfawa ƙafarka ba sai randa ka buɗi idanunka ka ganka a ƙasa warwas a ranar zaka fahimci kai mahaukacin kare ne_ Sadiq yayi Maganar cikin zuciyarsa kafin yace.
"Me kuwa zai amfaneni dashi Hisham, jiya ne ina zaune a wani Joint ni da Abba naji wani yana cewa, kuna da Company biyar a ƙasar Rasha, to shine abin ya bani mamaki domin ni bansan kuna da Company a Rasha ba, yadda nake da kusanci da kai ya kamata ace na sani, amma kuma sai naga kamar tambayar bata maka daɗi ba."
Murmushi Hisham yayi yace.
"Bawai banji daɗi bane abunne ya bani mamaki da ka min wannan tambayar domin kuwa a sanina bamu da Company a rasha, infact ma idan muna dashi,ai bai zamo lallai sai na sanar da kai ba komai kusancin dake tsakanin mu, Sadiq asirin ciki sai hanji sanin sirrin dukiyar mu, wannan tsakani na da ahalina ne, dan haka babu wannan layin tsakanina da kai Sadiq mu tsaya iya abotar mu."
Numfashi Sadiq ya saki domin kuwa ba haka yaso ba, yaso ace ya bigi cikin Hisham amma ba komai lallai wata rana sai na sani kafin na aika ka lahira murmushi ya saki tare da cewa.
"To shikenan Allah ya baka haƙuri, yanzu ya za'ayi ina son zan shige Abuja gobe."
"Okay kana buƙatar kuɗi kenan, muje POS sai na baka, nima zan shige ne muna da meeting."
Tashi sukayi suka shiga mota, a POS ɗin suka tsaya Hisham ya cire 50k ya bawa Sadiq kafin ya saukesa a ƙofar gidan su ya shige Companyn nasu .




**********



Washegari da safe Nameer da Tutu ne kawai suke breakfast Ummi tana azumi bata fito daining ɗin ba, shima Hisham da azumi ya tashi, yana can bedroom ɗin su bai fito ba.
"Yaya Nameer kullum ji nake tamkar na jawo sati huɗin da kuka yi alkawarin fitar da mata kai da yaya Hisham, gashi har mun cinye sati biyu."
Spoon ɗin da ke hannun Nameer ya ijiye tare da xubawa Tutu ido yace.
"Ban fahimta ba, meyasa kikeji tamkar ki jawo wannan watan yazo da wuri.?"
"Hmmm! Saboda a wannan lokacin ne zaka fitar dani a matsayin matar da zaka Aura, duniya zata san Soyayyar dake tsakanina da kai, ina kwadayin wannan ranar shiyasa nake gaggawar tazo ta, i love You so much Yaya Nameer, bansan Irin Soyayyar da nake maka ba, ina burin ganina a ƙarƙashin inuwar aurenka."
Numfashi Nameer ya saki, tare da runtse idanunsa.
_Ta kasa fahimtar bata ra'ayina, ta kasa gane bana jinta a raina yanzu, ya kamata zuwa yanzu ta fahimci haka ba sai na faɗa mata da bakina ba, Jidda itace zaɓina itace muradina, kuma ya zamo wajibi na aureta komai rintsi komai wahala sai na mallaketa kiyi haƙuri Tutu bazan iya aurenki ba, bazan yiwa Soyayyar Jidda kishiya ba, itace muradina ba ke ba._
Nameer yayi Maganar zucin idanunsa na runtse, plat ɗin abincin ya ture daga gabansa tare da miƙewa zai bar wajen ba tare da ya yiwa Tutu magana ba, kallon sa tayi tace.
"Ya ka tashi baka ce komai ba, ko akwai wata matsala ne.?"
Murmushi Nameer yayi yace.
"Matsala kuma Tutu, Allah ya rabamu da ita, lokacin aiki ne yayi, Allah ya nuna mana lokacin."
Yayi Maganar a takaice yana barin wajen numfashi Tutu ta saki tana sakin murmushi, ko kaɗan bata fahimci Nameer baya sonta ba.






_____________________________________







_Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._



*0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180*



_Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan auli yasmut siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai._



*Like Share and comments my fan's🥰*






_UMMU NASMAH CE✍🏻_
[6/10, 4:54 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*




*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*




*FREE BOOK ONE 📚*




*_Page 41 to 42_*




*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻






Hisham ya riga Nameer fita Company, ko da yaje ya samu tuni har Jidda ta isa, a bakin office ɗinsa ya tarar da ita zaune murmushi Hisham ya saki ko kaɗan Jidda bata kula da shigowar sa wajen ba, sai ji tayi mutum ya sunkuyo kanta har tana jiyo hucin numfashin sa idanunta ta runtse tsikar jikinta ya zuba, ƙamshin turarensa ne ya tabbatar mata da Hisham ne, ganin ta runtse idanunta yasa Hisham sakin murmushi yana ƙarewa ƙaramin bakinta kallo, murmushi ya saki tare da cewa.
"ke meye na runtse idon ko ance miki sunbatarki zanyi dallah Malama buɗe idanunki."
Jidda da idanunta ke runtse ne tace.
"Ka matsa kusa dani malam akan me to zaka ranƙwafo kaina kamar wanda zai bani magani."
Kansa Hisham ya ɗaga har yanzu fuskarsa ɗauke da murmushi ya zauna a gefen ta, mutane tsirarun da suke wajen ne suka bi Hisham da kallon mamaki domin kuwa tunda suke dashi basu taba ganin yayiwa wata murmushi ba ko ya tsaya kusa da wata sai yau Hisham duban Jidda yayi yana dariya yace.
"Kinsan me kuwa Jidda, gaskiya ke kyakkyawa ce babu ƙarya duk wanda yace miki mummuna sai dai maƙiyi, matsalar ki ɗaya."
Hisham yayi Maganar yana taɓe bakinsa, dubansa Jidda tayi tare da sakin murmushi domin kuwa maganar tasa dariya ta bata."
"Hmmm! Ikon Allah to meye kuma matsalar tawa yanzu ni ɗin har na fika matsala.?"
"Ƙwarai kuwa kin fiye izza da ji da kai ga shegen taurin kai, sai dai fa ahakan ma kina burgeni."
Ɗan zaro idanunta Jidda tayi cike da mamaki ta kalli Hisham.
"Ni ce nake burgeka Hisham ni ɗin."?
Jidda ta masa maganar cike da mamaki, dariya

Please Login or Register in order to submit comment