Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da cewa.
"Haba Hisham babu wani dala daka kinkima, she is gentleman so beautiful, kaga kuwa kana da damar sace zuciyar Jidda cikin sauƙi, sai dai inda gizo yake saƙar babu Auren Jidda cikin mission ɗin ka."
"Wannan ba damuwa ba ne, Sadiq wannan itace damar da Hisham zai gwada ƙarfin sa'ar sa, dan haka ka zuba ido kaga yadda zan ɗauko zuciyar shegiyar a tafin hannuna 3week komai ready insha Allah."
"Okay hakan ma yayi, sai mun haɗu gobe."
"Allah ya kaimu."
Hisham yayi Maganar yana katse kiran murmushi ya sanya tare da furta.
"Ina zan samu phone number ɗinta, hmmm! Okay Idi maye shi zan bawa wannan aikin zuwa gobe zai antayo min numbern nata."
Murmushi ya kuma saki tare da kiran idi maye aikin ya yi basa da adress ɗin Jidda sannan ya katse kiran.


Can kuwa Nameer tunda ya shiga yake kai kawo ya na tunanin ta ina zai fara aika saƙon sa ga Jidda iya nazarin da yayi akan rayuwarta macece mai kafiya da kuma ji da kai, numfashi ya saki tare da zama yayi tagumi, yana jinta a ransa fiye da kima baya jin cewa akwai macen da ya taɓa kaunarta kamarta, tabbas rasa Jidda gareshi tamkar tarwatsa rayuwarsa ne a ko yaushe zuciyar sa tana harbawa ne da sunanta, jigo ce ita a cikin rayuwarsa, a fili ya furta.
"Bazan taɓa yarda na rasaki ba Jidda ko ta halin yaya sai na mallakeki ke tawace zanyi yaƙi da kowa a kanki, komai tsanani komai wahala Jidda bazaki kaucewa rayuwata ba ke tawa ce nima kuma naki ne."
Yayi Maganar yana ɗaukar wayarsa ya kirata bata ɗaga ba, wajen sau biyu, sai kawai ya kira ummanta yana kira kuwa cikin Sa'a Umma ta ɗauka cikin girmamawa Nameer yace.
"Umma Barka da dare, kiyi haƙuri na kira a wannan lokacin."
Daga can Umma tace.
"Ba komai Nameer komai a kamawa take, Allah dai yasa lafiya."
"Lafiya alhamdulillah Umma, dama na kira numbern Jidda ne bata amsa kiran ba, maybe bata san number na bane, dama zance mata ne gobe ta taho da takaddunta na makaranta Companyn mu za'a mata interview, muna saka ran ɗaukarta aiki insha Allah."
Cikin farin ciki umma tace.
"Alhamdulillah! Gaskiya naji daɗin wannan kiran naka Nameer ɗazu kuwa ɗan uwanka ma Hisham yazo ya bamu hkr yace ka nuna masa abinda yayi bai kyauta ba, mun gode da gudumowarka garemu insha zatazo ta Allah ya maka albarka."
"Ameeen Umma na gode sai goben."
"To Allah ya tashe mu lafiya na gode."
Katse kiran Nameer yayi cike da mamaki ya furta.
"Hisham kuma yaje gidan su Jidda, kai anya kuwa Hisham zaije ya basu haƙuri kai mtsss ba Hisham bane gaskiya."
Yayi Maganar Hisham na shigowa.
"Kayi mamaki ne Nameer saboda Hisham yana da ɗagawa ko bazai iya bawa talaka haƙuri ba, to kayi kuskuren fahimta domin kuwa a wannan lokacin Hisham ya yadda yayi kuskure, ni ne naje na basu haƙuri ka daina mamaki."
"But Hisham lallai kuwa idan har da gaske ne Hisham ya fara sauyawa."
"Haka kuke so ku ganni ai shiyasa na sauya saboda kuyi farin ciki."
"Hakane na kira Tunde gobe zaizo interview itama Jidda na kirata zata zo gobe Company."
"Allah ya kaimu goben."
Hisham yayi Maganar a takaice.




***********



Washegari bayan sunyi breakfast suka raka Abba har airport sanda jirgin su ya tashi tukunna suka shige Company, da misalin sha ɗaya da rabi, Tunde ya shigo, a office ɗin Nameer ya zauna kasancewar yasan halin Hisham, bai wani juma da zuwa ba Jidda ta kira Nameer cewa ta shigo Companyn, security ya kira yace ya shigo masa da Jidda office ɗin sa, tare suka shigo da Basmah Jidda tasha doguwar riga marun color tayi rolling ɗin gyalen a kanta duk da Jidda ba gwanar makeup bane sosai tayi kyau, da sallama suka shigo tunda suka shigo Nameer ya tsurawa JIDDA ido tamkar zai cinyeta sosai ta masa kyau kujera ya nuna mata tare da cewa.
"Basmah sannunku da zuwa Bismillah ku zauna."
Zama sukayi, Jidda ba tare da ta kalli Nameer ba tace.
"Sannu aiki, jiya Umma ta isar min da saƙon ka, ga takaddun nawa."
"A'a bani zan amshi takaddun ba Hisham ne, wannan bangaren sa ne shike tace ma'aikata."
"Hisham kuma, to amma namee........
Hannu Nameer ya ɗagawa Jidda tare da cewa.
"Hisham ya sauya ba yadda kika sanshi a baya bane, karki yanke hukunci ki jira har yazo tukunna."
Nameer yayi Maganar yana ɗaga waya ya kira Hisham yace yazo office ya samesa su jidda sunzo, kafin ya ijiye wayar, jefa jifa Nameer suna taɗi da Basmah ita dai Jidda tayi shuru, kusan 30minute babu Hisham baizo ba, har aka doshi awa ɗaya, Jidda sosai ranta ya sosu domin kuwa ita a rayuwarta babu abinda ta tsana sama da jira cike da hasala ta miƙe tace.
"Tashi mu tafi Basmah."
"Ta tashi ku tafi kuma meyasa."
Kallon Nameer tayi kai tsaye tace.
"Saboda banzo dan a wulaƙanta ni ba."
"Haka zalika kuma babu mai wulaƙanta ki."
Sukaji muryar Hisham ta doki kunnen su gaba daya juyowa sukayi suka kallesa murmushi ya saki ya ƙariso yana cewa.
"Sorry kun gaji da jirana ko, akwai waɗanda suka juma kafin ku su na tsaya na sallama amma har kin ƙosa da yawa."
Shuru Jidda tayi tare da komawa ta zauna dariya Hisham yayi tare da dafa dest ɗin da take zaune ya kanne mata ido yace.
"Kamar dai har yanzu haushina kikeji ko, we'll da ma kinyi murmushi domin ko yaya kika juya yanayinki kyau kike ƙarawa, zan iya ganin takaddun naki."
Yayi Maganar yana ɗaga mata gira, idanunta jidda ta runtse cike da jin haushin sa tace.
"Bani na fara zuwa ba, sai ka fara sallamarsa tukunna."
Murmushi Hisham yayi tare da juyawa ya kalli Tunde.
"Au wai dama wannan shagiri girbau ɗin yana nan ne shima, hmm! Wai Tunde baka da zuciya a ƙirjinka ne, da ace ni ne kai ko inda Companyn nan yake bazan kalla sai dai ina kare ya cinye zuciyar, sai dai fa mu anan bama ƙyale ɓarawo muddun ya saci abummu, hannu muke cire masa, miƙo min takaddun naka ɗan uwana Tunde."
Yayi Maganar yana sakin murmushi wani irin ɗaci Tunde yaji a zuciyarsa sosai ransa ya ɓaci ji yake tamkar ya tashi ya cakwamo Hisham, idanunsa ya runtse.





_____________________________________





_Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._



*0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180*



_Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan auli yasmut siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai._



*Like Share and comments my fan's🥰*






_UMMU NASMAH CE✍🏻_
[6/2, 8:20 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*




*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*


*FREE BOOK ONE 📚*





*_Page 35 to 36_*





*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻


Murmushi Hisham ya kuma saki ganin ran Tunde yayi mungun ɓaci nauyin jiki ya sa ya kasa miƙo masa takaddun nasa.
"Hannunka yayi nauyi ne bazaka iya miƙo min takaddun ba, au ko nazo na ɗauka da kaina ne."
Teburin gabanta Jidda ta daka da ƙarfi tare da miƙewa a hasale, gaba ɗaya juyawa sukayi suna kallonta har Hisham ɗin, gaban Tunde ta ƙarisa ta ɗauki takaddun nasa ta matso kusa da Hisham.
"A rayuwata na juma banga mutum irinka ba, nayi tsammanin cewa ni ne kaɗai kake wa wannan wulaƙancin ashe kowa baifi ƙarfin wulaƙanci a wajen ka ba, ta yaya zai iya miƙo maka bayan ka ci masa mutunci, ka gyara rayuwarka Hisham domin kuwa baka kan turba mai kyau, saboda yazo neman aiki wajenka bashi zai baka lasisin wulaƙanta sa ba, ga takaddar ni na miƙo maka idan ma hannu ɗaya bazai baka sau biyu ni na haƙura da nawa shi dai ya samu."
Murmushi Hisham ya saki yana kallon Jidda.
"Haka zalika ke ma ɗaukar damuwar wani ki ɗaura a kanki baya baki wahala, shi wannan ɗin da zaki ari faɗansa to ɗan uwana wannan faɗan cikin gida ne yana da kyau ki kawar da kanki, amm me ma kikace idan ma hannu biyu bazai bani na karɓa ba ke kin haƙura da naki, Hmm! Ko sau dubu hannunki ya miƙo min ni mai amsa ne a gareki saboda ina neman afuwarki, gaskiya ke macece ta musamman ƙwarin zuciyar ki na burgeni."
Yayi Maganar yana amsar takaddun Tunde yace masa.
"Interview room idan na gama dashi zan kiraki.''
Yayi Maganar yana fita NAMEER ne ya dubi Tunde yace.
"Ka tashi kaje kayi haƙuri kasan halin Hisham muma haƙuri muke dashi."
Kansa Tunde ya haɗa yana dariya zuci domin kuwa shi a yanzu kallon biri yake yiwa Hisham, tarkon da suka ɗana masa zaiyi wuya ya tsallake sa tashi yayi yabi bayansa Jidda ne tace wa Nameer.
"Nameer wai shi Hisham haka rayuwarsa take, ya kamata ku dinga masa burki bai kamata ku barsa ya tafi a haka ba, da zan samu dama wallahi da zan saisaita rayuwarsa."
Numfashi Nameer ya saki, yana kallon Jidda yayin da yakejin ƙaunarta na nunkuwa a zuciyarsa, kafin yace.
"Zaiyi wahala ki iya gyara Hisham tunda har muka gagara sanyaya masa zuciyar sa to babu wanda zai iya, kuma baku fahimci Hisham bane, shifa baya taɓa shiga harkar wani, idan kinga Hisham ya shiga harkarki to tabbas kece kika taka masa gonarsa baki san waye Tunde bane da bazakiyi gaggawan shiga faɗansu ba, su ɗin ƴan uwane na kusa iyayensu gindinsu ɗaya."
"Kai ai kullum a cikin kare Hisham kake, Nameer halin ka mai kyau ne da ace Hisham kamarka yake to da tabbas sai yafi kowa jin daɗin rayuwarsa, kasan meye ina tausayawa matar da zata auri Hisham domin kuwa zata sha wahala kafin ta fuskanci waye shi."
Murmushi Nameer ya saki yace.
"To ni kuma tawa matar wani irin tausaya mata akeyi."?
Murmushi itama Jidda tayi tace.
"Ai kai Nameer duk matar da ta aureka to tabbas tayi sa'ar miji na gari, za kuma taji daɗin rayuwarta."
Dariya Nameer yayi yace.
"Gashi kuma wacce nake so ita bata san ina yi ba, ina sonta sosai soyayya ta haƙiƙa Soyayyar gaskiya ji nake tamkar bazan iya rayuwa ba tare da ita ba, ita ɗin rayuwata ne."
"To amma meyasa bazaka sanar da ita Soyayyar da kake mata ba, kana da kyawawan halin da Mace bazata ƙika ba, ko wacce Mace ka furtawa kalmar so na tabbata bazata furta maka kalmar ƙiyayya ba."
"Shikenan lokaci shine alƙali, Allah yasa maganar ki ta tabbata, ta soni Kamar yadda nake sonta."
Jidda batayi magana ba Hisham ya kira waya yace Jidda ta ƙariso, kallonta Nameer yayi yace.
"Hisham yace ki ƙarisa, kije sakatariya zata saka a kaiki."
"Okay to shikenan Basmah ki jirani ina zuwa."
Tayi Maganar tana tashi ta fita, kafin ta fita ma Nameer ya kira sakatariya tana fita ta samu security ya nuna mata, inda zatayi, tana zuwa ta shiga room ɗin babban room ne ma'aikata ta samu sosai a wajen, hakan ya nuna mata ba room ɗaya bane a ciki, wani ɗan korido ta bi, kanta ta ɗaga taga wani room an rubuta BUA INTERVIEW ROOM, rasa inda zata samu Hisham ya sakata sakin numfashi ta tura room ɗin wani mutumi ta samu zaune cikin office ɗin sallama tayi ya amsa.
"I'm sorry, Hisham nake nema."
Murmushi ya saki tare da tashi yaje ya rufe room ɗin yana murmushi ya juyo tare da doso Jidda yana cewa.
"Wow she is beautiful, ƴan ba sai kin sayarwa Hisham ba, idan aiki kike nema kawai ki bani hadin kai kin samu just 11minute ma is okay.''
Yayi Maganar yana matsota Jidda ganin da gaske neman rungumeta yake ya sata yin baya cikin tashin hankali, take baya tana cewa.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Auzubillah! Allah ya tsare ni daga sharrinka Hisham fa nake nema dan Allah ka buɗe min ƙofa na fita ni ba Yar iska bane ka matsa min na shige."
Dariya ya sanya yace.
"Gaki kamar Mace mai wayo ashe wawiya ce, just 11minute fa kawai ya isa."



Hisham jin Jidda shuru bata shigo ba ya sashi kiran Nameer yana tambayar sa ina jidda cike da mamaki Nameer yace ai tun ɗazu security ta kawo ta, ijiye wayar Hisham yayi cike da mamaki ya fito, room ɗin da yake cikin yana kallon wanda Jidda ta shiga, har zai shige sai ya jiyo tamkar Muryar mace tana kuka cikin room ɗin khabeer alkanawi, bakin room ɗin yaje ya tsaya tare da sanya hannu yayi nocking jin nocking yasa khabeer saurin juyawa sai kuma ya juyo ya kalli Jidda da har ya ɓarka mata rigarta, a zatonsa security ne daga inda yake tsaye yace.
"Waye ne.?"
"Hisham."
Amon Muryar Hisham ta doki kunnen sa, cikin ɗaga murya a gigice Jidda tana kuka tace.
"Hisham! Ka taimake ni! Zai keta min mutunci na."
Cike da mamaki HISHAM ya toshe bakinsa tare da furta.
"What Jidda, khabeer buɗe ƙofar nan."
Bakinsa khabeer ya toshe tare da ɗaura hannunsa a ka, cikin mungun tsoro, da gudu Jidda ta buɗe ƙofar, har tana bige Hisham wajen fitowa ta ƙanƙame jikinta sakamakon yagewar da rigarta yayi, kallon Jidda Hisham yayi tare da juyawa ya kalli khabeer, ƙafarsa yasa zai shiga room ɗin sai kuma ya tsaya cikin zuciyarsa ya furta.
_me zaisa na taimaka mata, to wai ma meya aikata mata anya kuwa ba fyaɗe ya mata ba._
Yayi Maganar yana juyawa ya kalli Jidda rigarta daya yayyage ya ke kallo rabin ƙirjinta duk a waje idanunsa ya runtse tare da mai da kansa gefe, Rigarsa ta sama ya cire tare da miƙa mata ta amsa cikin sauri, da wani irin mungun kallo yake bin khabeer idan akwai abinda ya tsana a rayuwarsa shine yaga ana ketawa mace haddi.............




_____________________________________







_Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._



*0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180*



_Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan auli yasmut siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai._



*Like Share and comments my fan's🥰*






_UMMU NASMAH CE✍🏻_
[6/7, 7:22 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*




*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*




*FREE BOOK ONE 📚*



*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻





*_Page 37 to 38_*





Idanunsa ya kuma runtsewa tare da ware su akan khabeer da yayi tsuru_tsuru yana kallon sa a mungun fusace Hisham yayi kan khabeer tare da shaƙo wuyansa wani irin naushi ya kaimasa a cikinsa tare da jidesa da ƙafarsa ya faɗi warwas a ƙasa, ƙara kai masa naushi yayi a bakinsa, wani irin ƙara khabeer ya danna tare da yunƙurowa zai tashi Hisham yasa ƙafa ya kwashesa, yayin da Jidda ta ke gefe takure hawaye na cigaba da biyo idanunta tabbas tayi danasanin zuwa wannan ma'aikatar da ace tasan haka zata faru da ita da babu abinda zai kawota, shi kuwa HISHAM ya dage sai dukan khabeer yake, ya gagara ramawa domin kuwa yasan yana wani yunkuri zaiyi asarar aikinsa, jin ihunsa yasa ma'aikatan wajen zuwa suka taru a kansa, ƙoƙarin ƙwacesa suke amma sun gagara, da ƙyar suka kwacesa daga hannun Hisham, wani irin huci Hisham yake tamkar mayunwacin zaki, Nameer da Basmah a gigice suka taho wajen sanda security suka sanar dashi, Gaban Hisham ya tsaya tare da cewa.
"Hisham meyake faruwa, da girman ka Hisham kasa hannu a jikin ma'aikacin ka why.?"
Idanunsa da suka kaɗa sukayi jawur Hisham ya ɗaga tare da nuna masa JIDDA da hannun sa gabaki ɗaya juyawa sukayi suka kalli Jidda itama idanunta sunyi jajur da sauri Basmah taje ta riketa tana cewa.
"Innalillahi! Jidda meya sameki, ke da..........
Bata ƙarisa maganar ba idanunta suka sauƙa akan rigarta da ya yage sai yanzu ta kula da rigar Hisham dake jikinta, a fusace Basmah tazo ta tsaya a gaban Hisham.
"Me kuka aikata mata, me ka mata Hisham, dama kun kirata da sunan bata aiki ne saboda ku wulaƙanta ta, macece fa ita, Meyasa baka yafiya ne Hisham."
"Ya isheki haka, ba dai Hisham ya aikata wannan mungun aikin ba, duk tsiyata ban taɓa tunanin ketawa Mace haddinta ba, ki juya ki yiwa wannan ɗan bunsurun wannan tambayar da kike min."
Hisham yayi Maganar cikin tsawa yana ɗaukar wayarsa Police ya kira yace suzo su tafi da khabeer Idanunsa shima Nameer ya runtse wani irin ɗaci da baƙin kishi ne yaji ya sarƙafe masa wuya, a fusace idanunsa a rufe yasa hannu ya finciko khabeer da ƙarfi tare da haɗasa da jikin bango, take goshin khabeer ya fashe jini ya biyo fuskarsa, wuyansa ya kuma shaƙowa wani irin gurnani khabeer keyi idanunsa duk sun firfito waje alamun wahala, shi kuwa Hisham kansa ya dafe tare da neman waje ya zauna yana jin zuciyarsa na hura, yama kasa yiwa NAMEER magana, Basmah tana ƙanƙame da Jidda duk hankalinsu na tashe, ƙarar motar Police da sukaji shiya ƙara ɗagawa Khabeer hankali, duk alokacin yana jin a ransa cewa kashesa Nameer zaiyi, jin motar Police yasa Hisham tashi da sauri ya wani irin kwashe khabeer rigib yayi a ƙasa, ƙafarsa Hisham yasa ya taka ƙafar khabeer da ƙarfin gaske ji kake ƙafar tayi ƙas, ya ɗaga ƙafarsa zai kuma takesa Police ya yi saurin rike Hisham ƙoƙarin ɗaga khabeer sukayi ya tsaya da ƙafarsa abu ya gagara, hakan ya tabbatar da cewa Hisham ya karya khabeer, Police ɗin ne yace.
"What Hisham ka karyasa fa, duba kaga wannan ƙafar tasa bata tsayuwa."
"karaya huɗu naso yayi ba ɗaya ba, duka hannayensa da ƙafofin naso su karye, ɗan matsiyaciya bunsurun banza! Wannan tsinanne ne la'anannen Ubangiji, ku fice da shege daga wajen nan, dan uwarsa an faɗa maka cewa nan Companyn tsinannune irinka kwarton banza kaji kunya kuma kayi asara, ɗan shegiya, tauren banza."
Hisham yayi Maganar cikin tsawa, dubansa Police ɗin yayi yace.
"Kabi a hankali mana Hisham meyasa kai ka fiye zafin zuciya ne, komai sannu muke binsa dole sai mun san abinda ke faruwa kafin mu tafi dashi."
"Ba zafin rai kawai nake da shi ba harda zafin hannu, bayan zafin hannu ma harda na ƙashi na rantse da Allah idan baku fita dashi ba zan illata sa yadda ko likitocin duniyar nan zasu taro a kansa bazasu iya gyarasa ba, dan haka ku fice da tsinanne, tunda ba Companyn ubansa bane."
Hisham ya kuma maganar yana huci, Nameer ne ya girgiza kansa yace.
"Sargent Bala ku shige dashi can office ɗin naku zan biyo bayan ku, sannan karku sassauta masa fyaɗe yaso aikata mana a cikin Company juya kaga yadda yaci zarafinta."
Kansa Sargent Bala ya kaɗa tare da juyawa ya kalli Jidda keyar khabeer ya kaɗa sukayi gaba, Police ɗin suna fita Hisham ya dubi ma'aikatan dake tsaye a wajen da yawa idanunsu yana kan Jidda baiyi magana ba yaja hannun Jidda ya shige da ita room ɗin daya fito yana huci, tunda Hisham ya riƙe mata hannu Jidda taji tsikar jikinta ya zuba wani abu ya taso mata daga ƙafarta har cikin ƙwaƙwalwarta, bai jira su Nameer sun shigo ba ya rufe ƙofar da ƙarfi idanunsa sunyi wani irin kaɗawa har abun tsoro idan ya ɗago ya kalleki.
"Ki faɗa min, ya miki fyaɗe ne karki ɓoye min meya miki."?


Please Login or Register in order to submit comment