Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa ba har abada! Da wannan mungun maƙaryacin zaki yadda macijin sari ka noƙe, da kake zancen zaku ɗauke ni aiki a Companyn ku, ce maka akayi mahaukaciya ce ta yayeni da zan yi aiki a ƙarƙashin ku, Allah ya tsari gatari noma ko kwarya ta fashe wallahi akwai sauran zane, kuma ka sani ina nan akan bakata sai ka girbi abinda ka min."
Jidda tayi maganar tana huci, Umma da kallo ta bita shi kansa Hisham dama yasan bazai ci nasara cikin sauƙi ba, miƙewa yayi tare da cewa.
"Umma ranta ne a ɓace har yanzu tana jin haushi na bata gama hucewa, kiyi haƙuri, zan cigaba da baki haƙuri har sai kin haƙura, muje Sadiq Umma na barki lafiya."
"Ba komai na gode Allah yayi muku albarka, ka gaida ɗan uwan naka."
"Zaiji insha Allah."
Hisham ya amsa suna ficewa, Umma kallon Jidda da sai cika take tana batsewa tace.
"Jidda meyasa zuciyar ki bata da kyau ne wani lokacin Jidda idan babu haƙuri duniyar zata zauna ƙalau ne, ita kanta duniyar ma fa ƙalilan ce ko yaushe ina nuna miki mahimmancin haƙuri Jidda, da kike cewa bazaki amshi aikin su ba, so kike mu koma halin da muka shiga a baya ne Kafin ki samu aiki, idan bakiyi danni ba, ko dan Abdu zakiyi saboda kuɗin makarantar sa, kin sani bani da wani yaro Babba Namiji kece jigona dalilin kenan da yasa na dage kikayi karatu, duk rintsi da wahala sai da na tabbatar kin samu ingantaccen ilimi da ingantaccen kwali, kema kin sani babu irin wahalar da bansha ba a rayuwata."
Numfashi Jidda ta saki idanunta na ciko da hawaye tace.
"Na sani Umma kuma bazan taɓa mantawa ba, amma Umma ki sani Hisham yaci mutunci na a rayuwa, Umma mayaudari ne zai iya fakewa da wannan hanyar saboda ya ƙara cutar dani, baki san waye Hisham bane shiyasa kika yarda dashi cikin sauri amma ni bazan taɓa yarda dashi ba, idan har kince dole sai nayi aiki a ƙarƙashin su zan miki biyayya Umma amma sai dai ni nasan dole sai wani mummunan abun ya faru, duk wanda ya haɗa hanyar sa da Hisham dole sai ya taka ƙaya."
Jidda tayi maganar hawayen yana biyo idanunta tare da tashi tabar wajen Umma duban Basmah tayi tace.
"Basmah kinfi kowa sanin waye Jidda dan haka ina son ki bani gudummawa wajen ganin Jidda ta amshi wannan aikin, bamu wata madogara da ta wuce amsar aikin muddun muna son mu cigaba da rayuwa cikin rufin asiri kema shaida ce kan wahalar da muka sha a rayuwa."
"Na sani Umma kuma insha Allah zanyi iya bakin ƙoƙarina domin ganin Jidda ta amshi aikin bara naje na sameta."
"Shikenan Basmah na gode."
Umma tayi Maganar cikin sanyin jiki, kafin Basmah ta tashi tabi bayan Jidda.




Sunyi nisa da tafiya HISHAM yace.
"Sadiq meka fahimta a zuwan mu gidan nan shin ka hango nasara kuwa.?"
"Eh to kusan haka amma dai akwai ƙura, kaima tunda muka fito naga kamar ka sare, ko da zakayi nasara akanta to zata baka wahala da alamu tana da taurin kai yarinyar sannan ƙwaƙwalwarta yana ja sosai sai ka taka a hankali."
Iska Hisham ya fesar daga bakinsa kafin yace.
"Naga alamar haka, Sadiq kasan kuwa yadda nake jin zuciyata kamar ta fashe tsabar baƙin ciki sanda na ƙasƙantar da kaina a gabansu, matsiyacita wadanda basu wuce bayina ba, Sadiq lallai duk wani baƙin ciki da zuciyata ta ƙunsa ya zamo BASHIN GABA tabbas zansa Jidda cikin JALALAR da sai ta gwammaci mutuwa fiye da rayuwa, sai tace meyasa ma tazo duniya, ban taɓa tsanar mutum irin yadda na tsani Jidda ba, kamar yadda tace da ganina gara ganin baƙin maciji da ni a gareta to kuwa na gwammaci ganin mutuwata sama da ita, hmmm! Sadiq wannan yarinyar ta ɓallo ruwan da bazata iya taresa ba, kuma nayi alƙawarin sai ta soni sai nayi wasa da zuciyar ta kamar yadda sarakuna suke wasa da Doki sai ni tsalle a cikin zuciyarta ina tafe ina zaneta kamar yadda ake yiwa bayi, zan kunna mata wutar da bazata iya kasheta ba a zuciyarta, na rantse sai na koya mata soyayyata, ko da kuwa zansha wahala kafin hakan ta kasance."
Numfashi Sadiq ya saki yana sakin murmushi yace.
"Na godewa Allah da yasa abinda ta maka baisa ka zuciya ba, ka sani sai ansha wahala ake samun nasara ba'a taɓa cin galba akan masoyi cikin sauƙi ka sauƙe ni anan zanje unguwa."
"Unguwa kuma to na kaika mana sai na shige, nima gidan Aunty Halima zanje."
"Karka damu Hisham, ka sauƙe ni kawai."
Kansa Hisham ya kaɗa tare da yin parking Sadiq ya sauƙa, yana fita yaja motar yabar wajen murmushi Sadiq ya saki yana bin motar da kallo sanda yayi nisa wata farar mota tayi parking a gaban sa, buɗe motar yayi ya shiga, yana shiga ya ɗaga kai ya kalli Tunde sai suka saki murmushi Tunde ya ɗagawa Sadiq babbar yatsa alamun jinjina👍🏼
"Banyi zaton zaka iya buga wannan wasan haka ba, sanda Mama ta kiraka baka wannan kogilar cikin tsoro da tunanin kai Aboki ne a wajen Hisham wanda ya yadda da kai, sai gashi ga baro ƙasar da kake saboda amsar wannan kogilar, a yayin da kasa Hisham wasa da zuciyar wata kai kuma bai san wasa kake da rayuwar sa ba, da alamu dai zamu ci Nasara akan ahalin Iyabo ta dalilinka, hmm tabbas zamu kauda hankalinsa da wannan yarinyar akan mu, Hisham wawa ne na ajin farko marar lissafi."








_____________________________________






_Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._



*0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180*



_Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan auli yasmut siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai._



*Like Share and comments my fan's🥰*






_UMMU NASMAH CE✍🏻_
[5/31, 9:01 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*




*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*




*FREE BOOK ONE📚*





*_Page 31 to 32_*





*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻




Murmushi Sadiq ya saki yana duban Tunde kafin ya girgiza kansa yace.
"Idan har Hisham wawa ne to kuwa tabbas kowa ma dake wannan duniyar wawa ne, Hisham fa ba gaɓo bane kamar yadda kake tunani komai da lissafi yake yi, tabbas ni zan iya wofintar da tunaninsa saboda yadda bazai taɓa ankara zan cutar dashi ba, yarda ce zata sa na iya kai Hisham ƙasa ba wauta ko rashin lissafi ba, idan wayo ne da kuma lissafi Hisham ya fini nesa ba kusa ba dan haka ko yanzu karka ɗauka cewa Hisham ba'a ankare yake ba, takun mu ya kamata mu iya."
"Hakane na fahimta, Mama tana son zatayi Magana da kai."
Kansa Sadiq ya girgiza.
"No Bazanyi Magana da ita ba ba kuma zan haɗu da ita ba, ina yin komai cikin tsaro ne, bana bukatar wani ya fara fahimtar akwai alaqa tsakanina da ku, kaima kanka ina haɗuwa ne kawai da kai ba tare da motar gidan ku ba, dan haka duk abinda take son tattaunawa da ni ta sanar dakai kai ka zamo ɗan saƙo."
"But ko waya bazaku iya kuyi ba, ko da baku haɗun ba.?"
"A wannan lokacin hanyar sadarwa ma ba cikakken tsaro bane da ita saboda abu mai sauƙi ne a bibiyi da wadanda kake waya dan haka bazanyi waya da ita ba, sannan ka jaddada mata cewa muddun muka kammala wannan mission ɗin ta cire HISHAM RICE MILL LIMITED a cikin lissafin ta domin nine wanda zai mallakesa kamar yadda na faɗa muku zamu kawo ƙarshen gaba ɗaya wadannan mutum huɗun, Hisham Ummi Abba da kuma Tutu saboda sune suke da gadon IYABO, to tabbas zan iya tsayar da numfashin su, ka tabbatar mata Company nawa ne, idan kuma aka ci amanata to tabbas kuma bazan barku ba sai na kawo ƙarshen ku, da lissafi nake komai cikin nazari nasan tunda kukaci amanar Alhaji Iyabo to abu ne mai sauƙi a wajen ku kuce zakuci amanata, to ina ankare cin amanata gareku tamkar kun ɗebi tafasasshen ruwa ne kun watsa a jikin ku, magana ta da kai a yanzu tazo ƙarshe."
Sadiq yayi Maganar yana buɗe motar ya fita numfashi Tunde ya saki tare da jan motar yabar wajen, ko da ya koma gida yadda sukayi da Sadiq ya sanarwa Mamabisola, murmushi ta saki Tunde ne yace.
"Mama wannan mutumin bashi da hankali idan har muka basa Companyn ai shikenan mu mun tashi famfam saboda Company shine fa ƙarfin arzikin su, shiya kawo musu dukkan kuɗin da suke alfahari dashi yanzu gaskiya Mama bazai yiwu mu basa wannan Companyn ba."
"Tunde kenan kai yaro ne shiyasa ba komai zaka fahimta ba, Tabbas HISHAM RICE MILL LIMITED shine babban Companyn su amma ka sani suna da ƙananun Company a jahohi daban-daban, sannan akwai wani babban Companyn nasu a Indonesiya NAMEER COTTON LIMITED ana ji dashi Company ne na AUDUGA suna kuma sarrafashi ta hanyoyi daban daban, suna yin atampopi da sauransu, dan haka mu barsa da wannan Companyn domin kuwa Sadiq shine garkuwar da zai iya kai Hisham ƙasa mu kuma dama Hisham shine matsalar mu domin kuwa idanunsa suna kammu."
"Okay to shikenan Mama, yace bazaiyi magana da ke ba kuma bazaiyi waya da ke ba, saboda tsaro duk saƙon da kike son isar masa yace ki faɗa min ni na isar masa idan muka haɗu."
Dariya Mamabisola tayi sosai kafin tace.
"Tabbas kansa yana ja, yana tafiya da lissafi na fahimci karatun nasa da alamu kuma zai kawo hadda, ba damuwa ka zamo ɗan saƙo."
"Okay ya maganar zuwa ƙauyen da zasuyi da Wamimo."?
"Tunde zan tsagaita tukunna naga takun Sadiq idan akwai nasara Bama bukatar tsafi, mu jira muga iya tseren sa tukunna itama Wamimo na sanar da ita hakan."
"Shikenan Allah yasa tseren yayi gudu dan ina bukatar ganin ƙarshen su cikin gaggawa."
Yana rufe bakinsa wayarsa tayi ringing dubansa ya kai ga wayar Nameer, Mamabisola ya kalla.
"Nameer ke kira."
"Ka ɗauka kaji abinda zai ce maka."
Wayar ya ɗauka yayi sallama sun ɗan juma suna waya kafin Tunde ya katse yana kallon Mamabisola yace.
"Kinji wai na kawo takadduna gobe za'a min interview."
"Okay ba damuwa kaje ɗin, bara na je na kwanta."
Mamabisola tayi Maganar tana tashi tabar falon.




***********


Dariya Aunty Halima tasa tana duban Hisham tace.
"Wai da gaske kake Hisham."
"Allah kuwa Aunty Halima, da gaske nake ina son haɗa Sadiq da Tutu Aure, saboda amanarsa da kuma hankalinsa, Sadiq yana bani gudummawa sosai a cikin al'amari na, amma ke ya kika gani."
Numfashi Aunty Halima ta saki tace.
"To wani hanzari ba gudu ba, Kamar Tutu tana da wanda take so domin kuwa ni ta taɓa cemin tana da wanda take so, kaga kuwa bazamu mata Auren dole ba, wanda take so shi zamu ɗauka mu bata."
Cike da mamaki Hisham yace.
"What Aunty akwai wanda Tutu take so ya akayi mu bamu sani ba daga ni har Nameer babu wanda ta sanar hakan kuma bana tunanin ta sanar da Ummi dan da Ummi ta sani zata sanar damu, amma Aunty waye tace miki wanda take so ɗin."?
"No bata sanar dani waye bane gaskiya ta dai cemin tana da wanda take so, amma kafin kayi magana da Sadiq ka fara zama da Tutu tukunna."
"Okay shikenan hakan zanyi zan samu lokaci nayi magana da ita, dare yayi zan koma gida Aunty sai da safe."
"Allah ya tashe mu lafiya ka gaishe da Ummin naku, ka cewa Nameer ina neman sa."



Tunda Hisham ya dawo gida har yayi wanka ya kwanta tare da jawo system ɗinsa ya hau aiki, ƙarfe 10:30 har zuwa wannan lokacin Nameer bai dawo ba, ture system ɗin Hisham yayi tare da miƙewa ya fito falo Ummi da mai aikinta kawai Hisham ya gani suna kallo zama yayi yana Zama mai aikin ta tashi tabar wajen.
"Ummi ina Tutu.?"
"Tutu kuma ba sun fita da Nameer ba wai sunje zatayi shopping."
Shuru Hisham yayi tare da kallon agogo yace.
"Amma ya kamata ace zuwa yanzu sun dawo 10:35 fa Ummi, Hmm mtsss bai dace Nameer ya kai har wannan lokacin da Tutu ba."
"Hisham meye damuwarka ba dai da ɗan uwanta ta fita ba, bana son shirmen banza."
"Allah ya huci zuciyarki Ummi, bawai wata fassara dabam nayi ba, yauwa Ummi wai nikam Tutu ta sanar da ke akwai wanda take so ne ma'ana zata aura.?
"Tutu kuma to ai bamma taɓa jin tace min ta fita zance ba, bani da labari gaskiya amma me ka gani."?
"No Ummi ba komai kawai na tambaya ne."
"Hisham."
"Na'am Ummi."
"Hisham kana ɓata min raina abinda kake min Hisham bana jin daɗinsa."
"Ummi ni kuma me nake miki ummi.''
Yayi Maganar cikin tashin hankali, numfasawa Ummi tayi tace.
"Sigari, sigari da kake sha Hisham shine yake ƙona min raina na ce maka bana so amma Hisham kaƙi bari kafi so ko yaushe raina ya dinga ɓaci ko.?"
"Kai Ummi kin razana ni, nifa sigarin nan idan ban shata ba ji nake tamkar bani da lafiya musamman ma idan raina yana ɓace sai nasha nake samun sukuni, kawai ki cigaba da min addu'a idan da rabon zan daina sha is okay, kuma idan banda ke ma Ummi bafa sigarin da zata fito a jikina na matsiyacita nake sha ba, babu wanda ya isa yace ina shan sigari sai wanda ya sani,sigarin ma ai kala-kala ce."
"Hmmm! Ikon Allah ina nuna maka gabar kana kai yamma zakayi, yanzu Hisham idan bata fito a jikinka ba ai dai bazata fasa cutar da lafiyar ka ba ko, Hisham ka sani ina maka tsananin ƙaunar da bazan iya jure rashinka ba, dan Hisham ka daina shan sigarin nan she is dangerous to why zaka nace da shan abinda kasan cutarwa ce ga rayuwarka, ka bari bana so."
"Shikenan Ummi kiyi haƙuri insha Allah zanyi ƙoƙarin naga na rage, idan bansha bane Ummi bana jin daɗi, musamman idan ina cikin damuwa amma insha Allah zan rage."
"Allahu yasha Hisham."
"Ameeen Ummi Abba fa ya kwanta ne.?"
"Ehh ya kwanta tun ɗazu kasan gobe sammako zaiyi zuwa Indonesiya, na Companyn Nameer."
"Eh ya faɗa min, Ummi dai kina ji da Nameer baki cewa Companyn mu sai Company Nameer."
"Ya za'ayi bazanji dashi ba, shi da baya ɓata min rai duk abinda na hanasa hanuwa yake, amma kai fa Hisham ba ka jin maganata."
Tayi Maganar dai-dai Tutu na shigowa da sallama kusa da Hisham ta zauna tana cewa.
"Ummi mun dawo."
"Ta ganki ai, nayi zaton ai kwana zakuyi acan."
"Kai yaya Hisham daɗinta ma dai da Yayana na fita, ba da wani ba."
"Ki fita da wani mana dan ubanki idan ban karya miki ƙafa ba."
Daga nesa Nameer yace.
"Umhum ai nasan za'a rina, kai dai a duniya babu wanda kake sauƙe fushinka a kansa sai Tutu."
Dariya Hisham yayi yace.
"Au dama haka kake ɗauka, na ma kusa na aurar da ita na huta."
Ummi dariya tasa tana kallon Hisham tace.
"Ikon Allah mutumin da bai aurar da kansa bane yake tunanin aurar da wata yo Hisham gaka ƙaton tuzuru bakayi Aure ba sai auta na zaka takurawa ai kuwa baka isa ba, ka fara auren tukunna kafin ka saka wani yayi."
Dariya Nameer tare da ƙarisowa ya zauna yace.
"Yauwa Ummi faɗa masa dai, Malam ka fara fito da mata tukunna."
"Au wai taron dangi zaku min akan nace wannan ƙaramar alhakin tayi Aure, to kai mai bakin banga taka matar ba."
"To idan ba tsoro ba, nan da wata biyu kowa ya fito da tashi matar da zai aura mana."
Cewar Nameer, dariya Hisham yayi yace.
"Na kuwa yarda Ummi ki zamo shaida, alƙawari kuma mukayi, da dai bani da niyyar Aure amma tunda yanzu ka hasala ni zan kuma baka mamaki."
"Wannan alƙawarin kuwa zan kasance mai tuna muku."
Itama Ummi tayi Maganar, dukkan su dariya sukayi, Hisham ya juya ya kalli Tutu yace.
"Naje gidan Aunty Halima ɗazu muke tattauna magana akanki take cemin kince mata akwai wanda kike so zaki aura, waye ne.?"
Da sauri Nameer ya juya ya kalli Tutu, itama shi ta kalla tare da sakin murmushi ta juya ga Hisham.



_____________________________________





*Masu min VTU Please ku daina bana son vtu ga account number na saka a jikin page ku ɗauka ku turo kuɗin ku ta ciki, idan baki da account ban tsananta ba nace kiyi snap ɗin katin mtn ki turo, to meye na yin VTU, duk wanda ta sake min VTU transfer ɗin katinta zanyi na mayar mata, dan haka dan Allah ku daina idan kin turo kuɗi kuma ki tabbatar da kin turo min shaidar biya bana so muzo muna wallahi tallahi da ke, yau kwana uku Mutum biyu sukace sun turo na ce ni ban gani ba su kawo shaidar biya sunce wai yayi delete a wayarsu, ni kuwa har yau banga alart ɗin su ba, ta yaya alart zaiyi delete a wayar Mutum idan bashi ya goge ba dan Allah idan kun tura ku turo shaidar biya.*




_Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._



*0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180*



_Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan auli yasmut siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai._



*Like Share and comments my fan's🥰*






_UMMU NASMAH CE✍🏻_
[6/1, 8:25 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*




*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*




*FREE BOOK ONE 📚*



*Page 33 to 34*



*_WRITING ON 01/03/2022_*





"Yaya Hisham Yaushe Aunty Halima ta faɗa maka hakan.?"
Tayi Maganar tana kallon Nameer girgiza mata kai Nameer yayi alamun karta sanar da Hisham, girarta ta ɗaga masa alamun meyesa, Muryar Hisham taji yace.
"Malama ina ruwanki da ranar da ta faɗa min tambayar ki kawai nayi sai ki bani amsa."
"Okay sorry, amma yaya Hisham nifa cikin wasa na yiwa aunty Halima wannan maganar, bansan ta ɗaukesa serious ba, ni bani da wani saurayi, da kuma da Ummi ta sani."
Murmushi Hisham ya saki tare da cewa.
"Wa yaga sarkin baƙin jini yarinya mai shekara ashirin wai bata da manemi, to ai shikenan ni hakan ma yamin daɗi domin kuwa zan sadakar da ke cikin sauƙi."
"Yaya Nameer kana jinsa ko wai ni zai sadakar, wallahi nafi ƙarfin ayi sadaka dani ina nan Allah zai kawo min miji na gari.''
Dariya Nameer yayi tare da miƙewa yana cewa.
"Wannan faɗan ni yafi ƙarfina, kunga ma shigewata dan wallahi bacci nakeji."
Ummi ne tace.
"Kana da gaskiya Nameer nima tashi zanyi naje na kwanta kwa ƙarita ku biyu."
Ummi tayi Magana itama tana tashi tayi bedroom ɗin ta shima Nameer shigewa yayi Tutu tana tura bakinta itama ta tashi bakinsa Hisham ya taɓe tare da jawo wayarsa ya kira Sadiq Ringing ɗaya ya ɗaga.
"Ya akayi Hisham.?"
"Mtsss! Kai dai Sadiq barni, kasan wata cacar da muka sanya da Nameer.?"
"A'a sai ka faɗa min."
Numfasawa Hisham yayi yace.
"Musu muke akan maganar Aure cikin haka har mukayi muƙabalar fitar da matar Aure cikin wata biyu, Ummi itace alƙali, anya kuwa ban ɗauko dala babu gammo ba."
Daga can Sadiq yasa dariya tare

Please Login or Register in order to submit comment