Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiyasa nake son saka cikin lamurana, an gama."
Yayi Maganar yana mikewa tare da ɗiban wayoyinsa yace.
"Bari na shige Company sai mun haɗu da daddare."
"Okay sai mun haɗun."
Har Hisham zai fita Sadiq yace.
"Sorry ya maganar yarinyar nan ne Hajara ya kamata ka bawa Dpo ita fa ta horu ai 5days tana rufe cikin duhu."
"Anjuma insha Allah idan muka haɗu zamuje a fitar da ita wannan ya isheta darasi."
"Okay limamin zamani mai hukunci da zamani."
Sadiq ya masa kirarin yana dariya m
Shima Hisham fita yayi yana dariya yabar Sadiq yana zuƙar shishirsa.



Nameer daga gidan su Jidda gida ya dawo da yaso ya shige Company sai yaji bazai iya zuwa Companyn ba, babu kowa a falon Tutu ta tafi school Ummi kuma sun fita unguwa da drever, bedroom ɗin su ya shige tare da zama bakin bed ɗin ya dafe kansa, tun lokacin da sukaje wani program a Companyn Zeen global concept ya ga jidda tun lokacin hankalin sa ya koma kanta a ko da yaushe tunaninta yake yayi bincike sosai akanta ya tabbatar da a Aminci take, sati biyu da haɗuwar su a Zeen global concept, tazo gidansu da Police akayi arresting ɗin sa, numfashi ya saki tare da furta.
"Wannan lokacin ya kamata na furta mata soyayyata itace macen da ya kamata na aura zuciyata ita take so, ya zamo wajibi na shiga jikin mahaifiyarta hakan zaisa Jidda ta soni."
Ya furta yana lumshe idanunsa, wayarsa ce tayi ringing, Hisham ya gani hannu yasa ya ɗauki wayar.
"Ya akayi."?
Daga can Hisham yace.
"Kana ina ne yazo office ɗin ka sakatariyar ka tace baka shigo ba kuma naga tun safe ka fita."?
"Gani a gida na dawo kaina ke ciwo bazan iya shigowa ba, ɗazun station naje na amso belin jidda."
"Whatt! Belin Jidda kuma, well shikenan ka samu kasha magani sai na dawo."
Hisham yayi Maganar daga can yana taɓe bakinsa tare da katse kiran duban sakatariyar yayi yace.
"Bazai samu shigowa ba, duk wanda yazo ganinsa ki turo sa office ɗina, ina da abu mai muhimmanci da zanje nayi yanzu."
Sakatariyar ce tace.
"Sir akwai wanda ya kawo file ɗin sa yace a bawa Oga Nameer idan ya shigo."
"File kuma okay let me See."
"Okay Sir."
Sakatariya tayi Maganar tana ɗauko file ɗin ta miƙawa Hisham amsa yayi tare da buɗe file ɗin, idanunsa ya ɗago ya kalli sakatariya yace.
"Yaushe aka baki File ɗin, shi Tunde da kansa ya kawo file ɗin ko wani ya aiko."?
"Yes Sir da kansa ya kawo ɗazu kafin ka shigo nace ya kai maka office ɗin ka, yace a'a na riƙe kawai na bawa Oga."
Murmushi Hisham ya saki yace.
"Okay ba damuwa ki cigaba da aikinki zanje da file ɗin."


Shigowar Tutu gidan babu kowa hakan ya sata haurawa sama har zata buɗe bedroom ɗin Ummi taji motsin mutum a bedroom ɗin su yaya NAMEER, fasa shiga bedroom ɗin Ummin tayi ta nufi na su Nameer nocking tayi Nameer dake kwance yana aiki da system ɗinsa yace.
"Yes come."
Shigowa Tutu tayi ganin Nameer ne kawai ya sata zama bakin bed ɗin..
"Ina yaya Hisham ɗin na ganka kai ɗaya.?"
"Yana Company ya akayi har kun tashi daga school ɗin kenan."?
"Eh, Yaya Nameer am.......
Katseta yayi da cewa.
"Um um, kinga I love you, kinsan Nameer bashi da wata mata bayan Tutu, wai ma na tambayeki naga sai ƙara kyau kike meye sirrin ne."
Murmushi Tutu ta saki cike da ƙaunar Nameer tace.
"Waye sirrina bayan kai, Yaya Nameer ji nake nafi ko wacce mace Sa'a domin kuwa babu wanda ya kaini dacen samun jarumin saurayi."
Murmushi kawai Nameer ya saki yace.
"To naji sarauniyata, time ɗin dawowar Hisham yayi zamu fita da yamma ki shirya."
"Okay I love you."
Ta furta tana murmushi.
"I love You too."
Shima Nameer ya furta yana kanne mata ido, fita Tutu tayi cike da farin ciki domin kuwa a duk sanda ta kalli Nameer farin ciki ne yake gauraye zuciyar ta, bata juma da fita ba kuwa Hisham ya shigo ko takalmin sa ba cire ba ya zauna tare da miƙawa Nameer file ɗin Tunde.
Amsa Nameer yayi tare da buɗe file ɗin sanda ya karanta tukunna kafin ya dubi Hisham.
"Amma ai ko kai zaka iya Sumit ɗin file ɗin idan kasa hannu ai shikenan ka basa office ɗin da ya kamata yayi aiki ba sai ni ba."
"Okay na fahimta, kuma nasan hakan sai dai karka manta ni ya fara kawowa file ɗin office ɗina, kuma na yanke hukuncin bazamu ɗauki ɓarawo aiki ba, dan haka baza'a ɗaukesa ba."
Murmushi Nameer yayi yace.
"Amma karka manta Abba ne ya bada umarnin mu ɗaukesa dan haka ya zamo wajibi Tunde yayi aiki a Companyn mu, bayan shima zan ɗauki Jidda itama aiki a cikin Companyn saboda kaine ka mata asarar aikinta dan haka ya zamo wajibi ni kuma na biya bashin da ka ɗauka rigimar ta ƙare."
Murmushi Hisham ya saki yana sunkuyawa ya zare takalmin ƙafarsa bai cewa Nameer komai ba, ganin yayi murmushi yayi shuru yasa Nameer cewa.
"Nayi magana kamin shuru baka faɗa min ra'ayinka akan hakan ba.?"





_____________________________________







_Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._



*0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180*



_Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan auli yasmut siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai._



*Like Share and comments my fan's🥰*






_UMMU NASMAH CE✍🏻_
[5/26, 8:10 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*




*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*





*FREE BOOK ONE 📚*




*_Page 27 to 28_*



*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻








"Au wai Hisham banza kayi dani nayi maganar kayi min shuru."
Agogon hanunsa da ya cire ya ijiye tare da juyowa yace.
"Meyasa zaka damu dole sai kaji ra'ayina ba dai kai ka gama yanke naka hukuncin ba to meye nawa a ciki."
Tashi Nameer yayi ya zauna tare da cewa.
"Ina son jin ra'ayinka ne saboda bana son rigima bana son su fara aiki ka dinga ɗaga mana hankali a Company, nasan halinka sarai Hisham."
Dariya maganar ta bawa Hisham tare da juyowa yace.
"Oh saboda ni ne masifaffe zan ɗaga muku hankali ko, to ai abinda baka sani ba Nameer saboda ka ɗauki Jidda aiki ni wannan ba matsala ta bace abu ɗaya ne dai bazan yadda ba dole sai anyi kafin a ɗauke ta aiki shine cike dukkan wani doka na Company dole sai an tantance ta, bayan duba takaddunta ana bukatar sai an mata interview kasan wannan wajibi ne a cikin Company, sannan shi Tunde da kake magana a kansa kamar yadda ka faɗa bazanyi jayayya da maganar Abba ba, to shima sai ya cike ƙa'idojin Company idan har sun cancanta za'a gani."
"Hmmm! Haba Hisham nifa ba yaro bane, kawai kace zaka koresu a wajen interview tunda kaine mai interview a cikin Company kaga kace sun faɗi ai ba wani abu mai wahala bane a wajenka, musamman Jidda da kake jin kamar ka kasheta."
Sosai Hisham yayi dariya cikin zuciyarsa ya furta.
_Nameer baka san shirina akan Jidda bane shiyasa kake kallon kamar bazan bari tayi aiki a Companyn mu ba, wannan dama ce mai kyau ka kawo wanda burina zai cika cikin sauƙi muddun Jidda tayi aiki a Companyn mu._
Numfashi ya saki har yanzu dariyar yake yace.
"Nameer ka fahimce ni, ni fa yanzu bani da matsala tsakanina da Jidda, bashin gaba ce kuma an fanshe, babu bashi tsakanin mu yanzu, ta kulleka na kulleta Final, karka damu ka shigo ayi interview tare da kai tunda kana min kallon maƙaryaci."
"Ba kallon maƙaryaci nake maka ba Hisham sanin hali ne yafi sanin kai nafi kowa sanin waye kai."
"Okay shikenan babu kuma abinda zance maka yanzu."
Hisham yayi Maganar yana ɗaukar towel ya shige tollet, tashi Nameer yayi ya fita falo, Ummi ya gani yanzu, murmushi ya saki yace.
"Ummi yaushe kika dawo."
"Kuna ƙuryar ɗaki Nameer yaushe zaku san dawowata."
Zama yayi yana murmushi yace.
"Shigowa ta babu kowa shiyasa ma na shige bedroom."
"Nameer wai ya Maganar Aure ne, na fara gajiya fa da ganinku haka just 35yrs ai ya kamata ace zuwa yanzu kunyi haihuwar fari."?
Dariya Nameer ya saki tare da cewa.
"Kai Ummi nawa shekara 35 take da har za'a gaji damu, insha Allah Ummi Auren nan yana zuwa nan kusa kusa amma fa nawa bansan na Hisham ba, dan shi ko zancen Soyayyar ma baya so."
"Ƙyaleni da ɗan ƙwal uba, Auren nan dai sai yayisa ko na masa Auren dole."
"Haba dai Auren dole ai yanzu an shige wannan zamanin da ake yiwa mata Auren dole bare kuma maza."
"Naji to kai surukar tawa a ina take.?"
Murmushi Nameer yayi yana jin Jidda cikin ransa yace.
"Ummi na dai ganota amma ban furta mata ra'ayina ba, amma Ummi ina sonta sosai so beautiful ce yarinyar."
"To marar kunya ko kunyata baka ji, to dai kayi gaggawar sanar da ita karka tsaya kallon ruwa ƙaton kwaɗo ya maka ƙafa, amma dan Allah Nameer ku nemi Aure a gidan mutunci saboda mace ta gari itace ƙashin bayan al'umma daga gareta ake samun ƴaƴa na gari, yana da kyau ku kula."
Numfashi Nameer ya saki yana jinjina kansa yace.
"Hmmm! Hakane Ummi insha Allah bazamu ɗauko macen da za'a kuka da ita ba."
"To Allah yayi jagora ya muku albarka."
Tayi Maganar dai-dai Hisham na sauƙowa, kusa da ita ya zauna yana cewa.
"Ummi jiya Abba yake cemin zai tafi Istanbul by tomorrow, kuma zai kwana biyu it's true."?
"Eh insha Allah gobe zai tafi suna da meeting da zasuyi acan so shima tafiyar ta taso masa ne kawai lokaci guda, bayan haka ai ya juma baije Istanbul ba."
"To Allah ya kaimu, maganar wannan Yarinyar Hajara da na rufe a gidan gonar Abba ya za'ayi da ita na miƙawa hukuma itane ko kawai na ƙyaleta tayi tafiyar ta.?"
"Subahanallah! Hisham dama baka saki yarinyar nan ba, ni Hisham mai yake damunka ne, kana da hankali kuwa ka ɗauki yarinya mace ka je ka ɓoyeta saboda ubanka ya ɗaure maka gindi, bana fa jin daɗin abinda kake Hisham ka dinga kiyayan ɓacin raina, yanzu dan ubanka idan Tutu aka yiwa abinda ka yiwa wannan yarinyar zakaji daɗi, tashi ka tashi kaje ka ɗauki ƴar mutane ka mayar da ita gidan ubanta."
Idanunsa Hisham ya runtse yana jin faɗan Ummi, a rayuwarsa ya tsani faɗa da tsawa.
"But Ummi........
"Kul kamin wata magana cewa nayi ka tashi kaje ka saki ƴar mutane."
Nameer ne ya miƙe tsaye tare da cewa.
"Allah ya huci zuciyarki Ummi kiyi haƙuri ni bara naje da kaina na maida ta gidan su, a wani room ka rufeta.?"
Ɗago idanunsa Hisham yayi ya kalli Nameer kafin cikin ɓacin rai yace.
"Ka tambayi mai gadi zai nuna maka key ɗin room ɗin yana hannunsa."
Yayi Maganar yana tashi yabar wajen, harara Ummi ta watsa masa tana cewa.
"Kai dai Allah ya shiryeka, ina sane da baka daina shan sigarin nan ba ai dan uwarka shasha wanda baisan ciwon kansa ba, kana ganin ɗan uwanka yanda yake tafiyar da rayuwar sa cikin nutsuwa da albarkar kowa amma kai Banda kai sai zafin ran tsiya da bazai amfanar da kai komai ba ga shegen taurin kai."
Shi dai Hisham baiyi magana ba ya shige a zuciye.
"Ummi dan Allah kiyi haƙuri ki daina masa faɗa haka, kinsani Hisham haka Allah ya hallice sa a haka ya taso bazai sauya ba, dan Allah Ummi ki daina wallahi raina suya yake min idan kina zaginsa."
"Umhum ai kune masu ƙara tunzura sa dole ya cigaba da ganin abinda yakeyi dai-dai ne, zaka shige ne ko kaima sai na ɓata maka rai."
"Allah ya huci zuciyarki Ummi."
Yayi Maganar cikin girmamawa yana fita, tsuka Ummi taja cikin ɓacin rai, tana jin haushi da takaicin wannan sigari da Hisham ke sha tayi faɗan tayi zagin amma abu ya gagara, ga sigari illace ga kayan cikin Mutum musamman Huhu tana saurin lalata sa.
_Allah ka shirya min Hisham, Allah ka fitar masa da wannan sigarin a ransa._
Tayi zancen cikin zuciyarta tana sakin ijiyar zuciya.



A zama yayi tare da dafe kai cikin matsanancin ɓacin rai, tebur ya buga tare da cewa.
"Rabon da Ummi ta zageni ko ta min faɗa harna manta a rayuwata, amma yau Ummi ke zagina, kuma duk wannan matsiyaciyar yarinyar ce sanadi, JIDDA na tsaneki na tsaneki I hate you!."
Yayi Maganar da ƙarfi yana runtse idanunsa.
Ya juma sosai yana huci har Nameer ya dawo sai kusan isha kafin ya ɗan saki har suka ci abinci, Hisham fuskarsa tana ɗaure ita dai Ummi bata kulasa ba, ko Nameer bai yiwa sallama ba ya yi ficewarsa, shima Nameer wanka yayi ya ɗauki Tutu suka fita.




************


A bakin railway ya ɗauki Sadiq sunyi nisa da tafiya Sadiq yace.
"Ina zamuje ne, can gidan gonar Abba ne.?"
Girgiza kansa Hisham yayi Yace.
"No ba can zamuje ba Nameer yaje yayi handling ɗin wannan Case ɗin."
"To ina kenan zamuje."?
"Kai Sadiq ka cika yawan tambaya kasan dai duk iskancina bazan je na sayar da kai ba ko, Ora zamuje, gani nayi ya kamata mu fara buga Game ɗin nan yau."
Dariya Sadiq ya saka tare da cewa.
"Au har ka gama playing ɗin yadda game ɗin zai kasance kenan, to menene tsarin."?
Kansa Hisham ya girgiza tare da sakin murmushi yace.
"Ka zuba idanunka zaka gani, Hisham ne fa ko ka manta ne.?"
"Ina kuwa zan manta Hisham, ai nasan saƙar ka shiyasa wani lokacin nake tsoron ka, amma dai ka taka a hankali gudun zamewa kasan wani sa'in bama fahimtar akwai santsi a waje har sai mun jimu a ƙasa, ya kamata mu dinga tafiya da waiwaye."
"Karka damu Sadiq duk santsi wajen akwai takalmin da ya fi ƙarfinsa muje zuwa zakaga ƙarshen wasan."
Dariya Sadiq yayi basu kuma magana ba har sai da suka yi parking a ƙofar gidan su Jidda, duban Hisham Sadiq yayi yace.
"Hisham wai kiranta za'ayi ne.?"
"No shiga gidan zamuyi da kanmu."
"Shiga kuma Hisham ba tare da neman izini ba."
"Karka damu biyoni kawai."
Kansa Sadiq ya kaɗa tare da fitowa daga motar key Hisham ya yiwa motar kafin suka nufi gidan su Jidda kansa tsaye Hisham ya shiga da sallama Umma ne ta amsa Jidda kanta na sunkuye tana ɗaurawa Abdu karatu, Basmah ma tana gefe, Umma cike da mamakin su sun shigo musu gida kai tsaye duk da Umma bata san Hisham ba, kamar wanda akace Basmah ta ɗago kanta taga Hisham na doso su a zabure Basmah tace.
"Hisham."
Ai Jidda saurin ɗago kanta tayi cikin mungun mamaki taga Hisham miƙewa tayi tsaye tayi tace .
"Hisham meya shigo da kai gidan mu.?"






_____________________________________







_Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._



*0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180*



_Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan auli yasmut siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai._



*Like Share and comments my fan's🥰*






_UMMU NASMAH CE✍🏻_[5/27, 7:59 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*




*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko Please._*



*FREE BOOK ONE📚*





*_Page 29 to 30_*




*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻


Murmushi kawai Hisham yayi bai kuma tsaya ba ya cigaba da tahowa, cikin azama Jidda ta taho zata tare gabansa Umma ta daka mata tsawa.
"Karki kuskura! ki dawo ki zauna a inda kike.''
"Hisham ne fa Umma ta yaya zan barsa ya shigo mana gida ya cima mutunci, kinsan kuwa yanda na tsani ganin wannan mutumin, wallahi Umma da ganin wannan gara nayi karo da mungun maciji, shine fa mutumin daya tozarta ni shine mutumin da baya ƙaunar yaga asirin mu ya ruhu shiya rabani da aikina Umma saboda kawai yaga mun tozarta, wannan maƙiyin Allah ne."
Kanta Umma ta jinjina domin kuwa ta fahimci yadda Jidda take jin zafin Hisham a cikin ranta.
"Na sani Jidda, dan haka ki koma ki zauna haka na ce miki."
Shuru Jidda tayi tana cije bakinta zuciyarta na tafasa ta koma ta zauna, Basmah ma daga inda take ta zauna Umma kuwa nuni ta yiwa Hisham da tabarma tace.
"Ga waje ku zauna."
Zama sukayi Hisham ya dubi umma tare da cewa.
"Barka da dare."
"Barka yaro kaine Hisham ko, Allah yasa ba wani kuskuren muka sake maka ba."?
"Ko ɗaya Umma babu wani kuskure da kuka min ni ne ma na muku kuskure, Umma ba tashin hankali bane ya kawo ni, nazo ne na baki haƙuri a matsayin ki na uwa na tabbata zaki fahimce ni, nasan ba lallai Jidda ta yadda dani ba, saboda tana kallon na yaudareta a baya da nufin na saduda wanda hakan yasa ta faɗa tarkona har na samu hujjar da na rufeta a police station, Umma a yanzu ba yaudara ba ce ta kuma kawoni gidan ku ke uwace kuma kin girme mu idan har yaudara ce ta kuma kawoni na tabbata ke zaki fahimci hakan, Umma jiya mun zauna da Nameer munyi magana ya nuna kuskurena akan abinda na yiwa Jidda, kuma na fahimta na gane cewa ita bata da laifi gashi kuma na cutar da ita da yawa, jiya banyi bacci ba tunani da damuwar zaluncin da na mata su suka dameni da tunanin anya kuwa Jidda zata yafe min, ban tunkaro Jidda nazo gareki saboda ke uwace zaki gane zafin da nakeji a raina ita Jidda ba lallai ta fahimce ni ba, dan Allah ku yafe min, maganar aikinta kuma da ta rasa munyi magana da Nameer zata kawo takaddunta mu duba insha Allah zamu ɗauketa aiki, Umma zafi da ciwon abinda Jidda tasa aka yiwa ɗan uwana shine yasa idanuna rufewa harna mata haka, bana iya riƙe kaina muddun aka taɓa Nameer, amma yanzu na fahimci kuskure na aikata ga Jidda kuyi haƙuri, wannan shi ya kawo ni."
Shuru Umma tayi tana sauraren Hisham sosai Maganar sa ta shiga jikinta kuma bata hango yaudara ko rashin gaskiya a tattare dashi ba, tsantsar gaskiya da nadama ta hango a idanunsa, numfashi ta saki kafin tace.
"Na saurari maganganun ka Hisham, ni kaina bazan ɓoye maka da farko naji zafin ka, amma tun sanda ɗan uwanka yazo gidan nan yake bani haƙuri ya kuma tabbatar min kai ba mutumin banza ba ne na yarda dashi, saboda Mutum ne na ƙwarai shi, sai kuma yanzu da kazo na tabbatar da hakan wannan akasi ne daya faru kuma Allah ya ƙaddara sai anyi hakan ni na fahimce ka, ita kanta Jidda tun farko da nace ta janye jikinta a cikin Case ɗin da taji maganata dama hakan bata faru ba, ni na yafe maka kuma ita ma jidda ta yafe maka."
"Wallahi ban yafe masa ba Umma kuma bazan yafe

Please Login or Register in order to submit comment