Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai a hanuna."
Numfashi Mamana ta saki ta dubi Baban mu tace.
"Kaga Baban Nameer kayi haƙuri INSHA ALLAH komai zai wuce rayuwar taƙaitacciya ce, kuma kaga ai ita kasuwa dama Sa'a ce idan ba'a samu ba yau gobe za'a samu, idan ruwan ya tsagaita, sai ka fita ka sayowa Nameer garin Hamsin Suger na ashirin, ya samu yasha yunwar ta damesa mu zamu iya haƙuri shi kuma yarone bai san babu ba."
Kansa Baban mu ya kaɗa yace.
"To Allah ya iyar mana."
Ni dai ina zaune ina kallon su, shi kansa Baba kana kallon sa zaka fahimci shima yunwar yakeji amma haka ya danne tasa, kayan jikin nasa ya sauya yazo ya zauna kusa dani yana lallashi na, ko kafin a gama ruwan tuni har bacci ya ɗaukeni, sai ji kawai nayi Mama na tashi na nasha garin ashe har an gama ruwan Baba yaje ya sayo min, haka na tashi nasha garin da Mama ta jiƙa min ita kuwa da Baba haka suka kwana da yunwa.



Washegari da safe ma da zan tafi makaranta Mama da kanta ta fita taje ta amso min bashin Taliya a wajen iya mai Taliya da Ɗanwake dake bayan layin mu ta samin a plast na tafi dashi makaranta.
Ko da na dawo daga makaranta na samu Mama ta mana buragandu shi naci nasha ruwa, na fita wasa na, da la'asar lis Hajja Anti ta shigo gidan mu makwabciyar mu ce suna shiri sosai da Mama duk da ƙarancin shekaru na a wannan lokacin ina iya fahimtar wasu abubuwan, tazo ne tana sanar da Mama cewa akwai wanda take musu aiki ta mata magana ta cikiya musu ƴar aiki wanda zata dinga musu wanke wanke da shara kawai, shine taga halin da muke ciki tace ko Mama zataje ta dinga yi sosai hakan ya yiwa Mama daɗi sai dai bata amince mata ba tace sai ta sanar da Babana, akan wannan maganar sukayi sallama da Hajja Anti akan tana sauraran Mama.

Ko da Baba ya dawo Mama ta sanar dashi ransa bai so ba, sai dai yadda Mama ta kafe da kuma hujjojin ta na amfanin da aikin zai mana yasa Baba amincewa, da wayar Baba Mama ta kira Hajja Anti take sanar da ita Baba ya amince, tace washegari zata zo suje wajen da Uwar ɗakin nata.






____________________________________



_Wannan littafin Book one Free, Book two ba Free bane Paid ne, to akwai Costomers ɗina da suka saba sayen Book ɗina sunce abasu account number zasu fara payment, so da 300 nace so amma duba da yadda ake ciki na tsadar rayuwa yasa na barsa a 200 ba ga Costomers ɗina ba har ga all fan's ɗina ga account number wanda yaga zaiyi payment_



*0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180*



_Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike, falyakum khairan auli yasmut._





*Share and comments my fan's🥰*





_UMMU NASMAH CE✍🏻_





*_For More Information 08147537180_*
[5/24, 7:56 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.



https://chat.whatsapp.com/JwLvHkW5qmbBQd6JEgDjMV


Gashi masu cewa a saka su a group ɗin JALALA sai suyi joining mata zallah dan Allah Banda maza please kar namiji ya shigo dan Allah



*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*



*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*



_Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, sannan sorry akwai abinda na manta ban sanar da ku ba cewa akwai wacce ta bada rabin kuɗin Mutum shabiyar tace sadaka, an samu Mutum 8 sun ciko kuɗin dan haka kema ƴar uwata idan kina son shiga cikin wadanda zasu samu wannan sauƙi akwai sauran dama na Mutum 7 zaki iya cika Naira 100 kacal ki ganki a Paid group amma damar Mutum bakwai ne kawai ya rage idan kin samu kin shiga cikin wadannan Mutum bakwai ɗin to fine_




*0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180*



_Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan auli yasmut, siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai da kuma a baka labari gara ka bayar._




*FREE BOOK ONE 📚*



*_Page 23 to 24_*



*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻




Kamar yadda Hajja Anti tace Washegari da safe tazo ta ɗauki Mama da yake ranar weekend ne bamu da makaranta hakan yasa Mama kama hannuna muka tafi tare, bana mantawa a lokacin ina da shekara goma sha ɗaya ne a duniya aji na biyar a primary school dake nan unguwar Ora, duk da ƙarancin shekaru na ganin gidan da muka shiga sai da ya burgeni, sosai yamin kyau tunda muka shiga na fara tsalle ina cirar flower ɗin da sukayi ado dashi a gidan, Mama ce ta kamo hannuna tana zaro min ido tace.
"Kul ka ƙara cira musu flower Babana sojaji zasu kamaka su maka bulala ka gansu can suna kallon mu ka bari kaji Babana ba kyau yiwa mutane ɓarna."
Dubana na kai ga sojojin dake zaune bakin get ɗin, dama kuwa ni gwanine wajen tsoron soja, cikin sauri na ƙanƙame Mama har muka shiga part ɗin nasu muka shige babban falon gidan ban kuma taɓa wani abun ba, a falon muka zauna har lokacin ina maƙale jikin Mama, bamu juma da zama ba Ummi ta sauƙo daga sama, kana kallon matar zaka fahimci matar mutunci ne domin kuwa fuskarta a sake take, a kujera ta zauna tare da duban Hajja Anti tace.
"Hajja Anti yau kece a gidan nawa, wata sabon gani, sannu baiwar Allah."
Ummi tayi Maganar tana kallon Mama, cikin girmamawa Mama ta gaishe ta kafin Hajja Anti tayi dariya tana cewa.
"Aunty Ramata kwana biyu sai a hankali, amma wallahi ina da niyyar zuwa na gaishe ki, ranan munyi magana da Aunty Luba take cemin kina son ƙarin ƴar aiki, to shine na samo miki wannan baiwar Allah, nasan zata iya abinda kike buƙata, na kira Aunty Luba take cemin na kawota kawai darect wajen ki idan ta miki sai a ɗauketa."
Murmushi Ummi ta saki tace.
"Eh tabbas munyi magana da ita ina bukatar mai goge goge da sharan falon nan, idan har kun yaba da halinta da tsaftar ta, to ai ni bani da matsala sai ta fara aiki kawai."
"Ehh gaskiya bata da matsala ko kaɗan tana da tsafta sosai."
Duban Mama Ummi tayi tace.
"Baiwar Allah na ɗauke ki aiki dan Allah ki riƙe min amana, menene sunan ki."?
Kanta Mama ta ɗago tace.
"Insha Allah zaki sameni mai riƙe amana sunana Fatima amma ana kirana da Maman Nameer."
Murmushi Ummi tayi ta kalleni hannu ta miƙo min tace.
"Ayya wannan shine Nameer ɗin ko, zo kaji yarona."
Sakin Ummi nayi na tashi naje wajenta akan cinyar ta ta ijiye ni da gudu na hango wani ƙaramin yaro ya fito daga wani room ya faɗa a jikin Ummi ko da ganin yaron nasan zan girmesa da wajen shekara biyu Ummi ne ta dubesa tace.
"Kai HISHAM ina ka shige tun ɗazu lami na jiranka zata sauƙe ka a gidan Mamabisola."?
Ransa Hisham ya haɗa cikin ƙunƙuni yana tura baki yace.
"Ummi ni bazani ba babu inda zanje ni ball zanyi."
Yayi Maganar yana kama hannuna yace.
"Kazo muje muyi Ball, Abbana ya kawo min sabuwar Ball daga Indonesiya zo muje mu buga."
Murmushi Ummi tayi cikin mamaki tace.
"Ikon Allah lallai Nameer da Sa'a ka shigo gidan nan yau har Hisham ne zaiga baƙo bai masa hali ba yace suzo suyi wasa, to kaga Nameer kuje kuyi wasan kaji banda faɗa, kai kuma karka kuskura ka masa wani abun nasan halinka kaga ɗan uwanka ne, sunan sa Nameer."
Dariya Hisham yasa yana tsalle yace.
"Ummi ina sonsa bazan dakesa ba Ball zamuyi, mu tafi Nameer."
Yayi Maganar yana jan hannun Nameer suka fita, da kallo Ummi ta bisu tana murmushi kafin tace.
"To Maman Nameer zaki fara aiki yau falon nan da can ɗakin baƙi zaki dinga mopping sai wanke wanke kina iya farawa zamu baki dubu goma a wata 10k."
Cike da farin ciki Mama tayi dariya tace.
"Na gode sosai Hajiya kin taimakeni na gode."
Murmushi Ummi tayi tare da tashi ta haura sama bata juma ba ta fito hannunta riƙe da kuɗi ta bawa Hajja Anti, anan Hajja Anti tabar mu ta tafi.
Ƙarfe shabiyu na rana Mama ta gama aikin, a ɗan wannan wuni har sabo ya shiga tsakanina da Hisham tunda nazo bamu rabu ba, har sai da Mama tazo tafiya, sosai Hisham ya haɗa ransa yace sai ya bimu, da ƙyar da lallashi Ummi ta rarrashesa kafin muka koma gida.



Ko da muka koma bayan Baba ya dawo Mama ta ke sanar dashi yadda sukayi a gidan aikin da albashin da za'a dinga bata sosai hakan ya yiwa Baba daɗi yasan komai yaya wata wahalar zata ragu.




************



Haka rayuwa ta dinga tafiya kullum sai Mama taje gidan aikinta yayin da shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanina da Hisham, duk kuɗi da ikon su Hisham hakan baya hana wata rana ya biyo Mama ya kwana a gidan mu, haka duk weekend dani Mama take zuwa, sai ya zama Mama da Ummi suma suka shaƙu sosai, Ummi tana kyautatawa Mama dai-dai gwargwado, bana mantawa akwai ranar da mai gadin su Ummi na part ɗin su ya ijiye aikin, hakan yasa Mama neman alfarmar Ummi akan a ɗauki Baba ya maye gurbin mai gadin, babu musu Ummi ta sanar da Abba yace a kira Baba yazo suyi magana, ko da saƙon ya isawa Baba baiyi ƙasa a gwiwwa ba yazo a ranar da yazo shima Baba a ranar ya fara aiki, hakan tasa Abba bawa Baba wani ƙaramin part dake cikin gidan yace mu dawo da zama tunda aikin Baba na kwana ne, baiyi musu ba Baba duba ga Irin kyautatawar da suke mana.


Numfashi Nameer ya saki tare da juyowa ya kalli jidda yace.
"wannan shine dalilin da yasa muka baro wannan gidan muka komo gidan ALHAJI IYABO da rayuwa, ba iya nan labarin ya tsaya ba Ahmad.

Ni sawa Ahmad yayi cike da mamaki yace.
"Na matsu naji ƙarshen labarin ahalinka Nameer."
Kanta Jidda ta kaɗa itama tace.
"Tabbas rayuwar ka abar tausayi ce Nameer dole ka sakawa Alhaji IYABO da alkairi menene ya faru bayan dawowarku gidan Alhaji Iyabo.?"

Numfashi Nameer ya saki ya cigaba da cewa.
"Bayan mun dawo gabaki ɗaya Hisham sai ya tare a Wajen mu babu abinda yake mayar dashi part ɗin su sai har idan tare dani zamu shiga, Abba hakan sosai ya masa daɗi domin kuwa a yanda suka san Hisham bai taɓa aboki ba, asali ma duk yaron da yazo gidan korarsa yake amma sai gashi lokaci ɗaya Hisham yayi sabo dani, wannan dalilin yasa Abba yamin transfer daga Makarantar gomnati da nake ciki zuwa privet inda Hisham ke karatun aka ijiye mu waje guda, duk abinda zai taɓani Hisham baya so haka nima bana yadda wani ya ɗaga masu hannu, a haka rayuwar mu ta tafi har muka girma muka shiga jami'a komai namu tare yake tafiya duk wanda yasan Hisham to yasan ni, haka kuma ake min kallon ɗan Alhaji Iyabo domin kuwa ya maidani ɗansa komai tare yake mana haka Ummi duk abinda zata yiwa Hisham sai ta min wani lokacin takan hana Hisham ni ta bani amma hakan bazai sa Hisham yaji haushi na, ranar da bazan taɓa mantawa da ita ba a tarihin rayuwata itace ranar da muka wayi gari da mummunan tashin hankali ranar talata, ni da Hisham bamu kwana a part ɗin mu ba kasancewar Abba yace mu kuma wajen su, cikin dare wuta ta tashi a part ɗin su Mamana, wajen misalin ƙarfe 2 na dare, kwalala da ihun sojojin gidan shine ya tashi kowa dake cikin gidan, yayin da ake ta watsawa part ɗin ruwa sai dai ina tamkar ƙara hura wutar ake, har abin kashe gobara da Abba ya ijiye anyi amfani dashi amma a banza, hankalina sosai ya tashi bansan sanda hawaye ke zubowa daga idanuna ba, fire service aka kira ko da sukazo sukayi nasarar kashe wutar da sauri aka shiga part ɗin sai dai kash ƙaddara ta riga fata domin kuwa su Mama sun ƙone rai yayi halinsa nayi kuka tamkar zan bisu haka shima Hisham yaji mutuwar, ko wanka ba'a samu an musu ba kasancewar sun ƙone sai ruwa kawai aka yayyafa musu aka musu sallah, ranar babu wanda hankalin sa bai tashi ba da mutuwar su Baba, bayan anyi sadakar Uku, ne Abba da Ummi suka ijiye ni suka min nasiha sosai da nuna min mahimmancin haƙuri inda Abba yace min.
(Baka rasa iyaye ba NAMEER kai mai iyaye biyu ne, muma iyayenka ne baka da banbanci da Hisham a wajen mu, bazamu bari kayi maraici ba duk gatan da uba zai nunawa ɗan da ya haifa zan nuna maka shi NAMEER ka cigaba da yiwa iyayenka addu'a Allah ya musu rahama.)
Wannan Maganar ta Abba sosai tamin daɗi domin a lokacin da iyayena suka rasu ina da shekara ashirin ne a aduniya tun daga wannan ranar kuwa na cigaba da rayuwata a wajen Abba da Ummi da zuri'arsu domin kuwa dangin mahaifina babu wanda ya kuma nemana har sai da sukaga na kawo ƙarfi sannan suke nemana saboda ina da abinda zan basu, wannan shine tarihina.


Kallon Jidda yayi ya cigaba da cewa.
"Ki faɗa min Jidda ta yaya za'ace dukkan masu kuɗi azzalumai ne, Abba Mutum ne na gari kuma na kwarai."
Numfashi Jidda ta saki.
"Ƙwarai kuwa na yadda da maganar ka Nameer, kayi haƙuri bansan cewa Hajara sharri ta maka ba sai jiya da daddare Dpo ya faɗa min."
"Ba komai Jidda nasan yanzu haka Umma tana can hankalin ta a tashe muje na sauƙe ku."
"Nameer ina tsoron komawa Umma a wannan lokacin da wani baki zan faɗa mata cewa na rasa aikina, dashi muka dogara nasan dole hankalinta zai tashi."
Murmushi Nameer yayi tare da cewa.
"Karki damu Jidda Umma mutum ce mai tawakkali a kallo ɗaya da na mata, na kuma gama hukunci tunda Hisham yasa kikayi asarar aikinki ni zan baki babban matsayi a COMPANYN MU *_HISHAM RICE MILL LIMITED_* zaki samu salary sama da wanda kike ɗauka a aikinki na baya."
Zaro idanunta Jidda tayi a firgice tace.
"Whattttttt! Hisham rice mill limited, hmmm! Sorry Nameer bazan taɓa iya haɗa inuwa ɗaya da Hisham ba domin kuwa nayi rantsuwa da Allah sai na masa rashin mutuncin da bai taɓa cin karo dashi ba a rayuwarsa alkawari na ɗauka."








______________________________________




Like comments and share my fan's.



_Jalala fan's kun rage comments ya dai ban fa gane ba wai shin bacci kukayi ne to dan Allah ku farka_




*UMMU NASMAH CE✍🏻*






_for more information 08147537180_
[5/25, 7:55 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


💑 *_JALALA_* 💑


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*



*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*




*FREE BOOK ONE📚*




*_Page 25 to 26_*




*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻





"Ashsha haba Jidda banji daɗin wannan maganar taki ba, wannan faɗan naku ya kamata ya tsaya haka meye amfanin rigimar, fitina fa a kwance take meyasa zaku ta da ta, halinku yazo ɗaya da Hisham shiyasa bazaku taɓa daidaitawa ba, muje na sauƙeki."
Ba tare da jidda tayi Magana ba ta shige gaba, bayanta sukabi motar Nameer ɗin suka shiga, a hanya Ahmad ya sauƙa shi kuma Nameer ya shige da Jidda har ƙofar gidan su yayi parking tare suka shiga cikin gidan da Nameer, Basmah ce kawai a tsakar gidan tana shara, ganin Jidda yasa Basmah tahowa da gudu ta rungumeta.
"Alhamdulillah! Sannu Jidda."
Murmushi Jidda ta saki tana kama hannun Basmah tace.
"Ina Umman take.?"
"Umma ta fita makwabta can gidan su Indo."
Numfashi Jidda ta saki ta dubi NAMEER.
"Umman bata nan, na gode Nameer, ka fitar dani daga cikin cell bazan manta da hakan ba."
"Bakomai idan ta dawo kwa gaishe ta."
Basmah ce tace.
"Zataji insha Allah Nameer mun gode."
Kansa Nameer yasa ya fice zama Jidda tayi bakin ƙofa Basmah ta ijiye tsintsiyar ta taho kusa da jidda ta zauna."
"Har kunyar kallon idanunki nake, na miki laifi nine sanadiyyar faɗawa halin da kika shiga gashi kin rasa aikin ki, wallahi banyi da nufi ba, nayi ne saboda neman mafita na ciwon Abba da nasan tarko Hisham ya ɗana miki wallahi da bazan fara kuskuren saki ki amshi kuɗin ba."
Murmushi jidda ta saki tace.
"Karki damu Basmah ni nasan bazaki taɓa cutar da rayuwata ba, hmm! Abba mahaifi nima nake kallon sa zan iya komai domin ganin ya samu lafiya dan haka karki saka a ranki naji haushinki, ko ɗaya sai ma sonki da na ƙara ji a raina ƙawata ki kalli idona ki cigaba da faɗa min abinda ya dace dani a rayuwata, Basmah da Jidda abu ɗaya ne. Jidda bazata taɓa jin kunyar Basmah ba dan haka Basmah ma karta kuskura taji kunyar Jidda."
Dariya Basmah tasa tare da rungume Jidda, tace.
"Dama na sani Jidda bazata taɓa jin haushin Basmah ba, za'a yiwa Abba aiki."
Cike da farin ciki Jidda.
"Kai haba a ina aka samu kuɗin.?"
"Nameer jiya da yazo wajen Umma ya bata 50k ni kuma 30k shine Umma ta cika kuɗin aikin tun jiya da daddare na kai kuɗin yanzu su muke jira su saka ranar da zasuyi aikin, Jidda gaskiya da alamu wannan Nameer ɗin yana da kirki yafi wannan Hisham ɗin."
"Hmmm! Haka naga alamu amma har yanzu zuciyata bata amince dashi ba saboda mayaudara ne, dan haka karki kuskura kiyi saurin sakin jiki dashi, aikina kuma dana rasa karki damu haka Allah ya hukunta, shi kuma Hisham dani yake zancen zan bambance masa tsakanin aya da tsakuwa."
"A'a Jidda dan Allah ki fita a harkarsa babu ruwanki dashi wannan fa ɗan tasha ne bazaiji kunyar wulaƙanta ki ba."
"Mubar maganar Basmah domin kuwa bazan hanu ba, bari naje na watsa ruwa kafin Umma ta dawo."
"Shikenan nima idan kin fito zanje asibiti na dubo Abba."
"Shikenan bara na fito ɗin.''




************



Lumshe idanunsa Hisham yayi yana zugar sigarin sa hankali kwance, shi kuwa Sadiq shisha ma yake zuƙa, yasar da karan sigarin yayi ya takesa, tare da sanya hannu ya ɗauki coffee ɗin dake gabansa a hankali yake kurɓar coffee ɗin.
"Hisham da zan baka shawara da kaci nasara a yaƙinka tsakaninka da wannan yarinyar nasan maganar da ta faɗa maka a police station har yanzu shine yake damunka a ranka, duk nasan babu abinda ta isa ta maka, amma yana da kyau ka koyawa rayuwarta darasi."
Ijiye coffee ɗin Hisham yayi tare da mai da kallonsa ga Sadiq yace.
"Wacce irin shawara zaka bani ina jinka."
"Hanya ce mai sauƙi Hisham, shi yaƙi ɗan zamba ne ba ɗan fito na fito ba, ba'a taɓa cin nasara ga maƙiyi ɓaro ɓaro, yaƙin sunƙuru yafi aika saƙo ga maƙiyi, yanzu fa zamani ya sanda a da ana yaƙi ne da takwabi amma yanzu zamani ya kawo bindiga idan har bindigar ma ta gagara, sai kawai a tashi bom."
"Kasan bana fahimtar irin wadannan murɗaɗɗun kalmomin tafi kawai kai tsaye ka faɗa min abinda yake ranka."
"Hisham ka yaudari yarinyar nan da zummar Soyayya ka tusa mata sonka a cikin ranta ta yadda zataji bazata iya rayuwa ba tare da kai ba, ina son Soyayyar ta kusa kaiku ga Aure ma'ana har rana asaka randa za'a ɗaura Auren kace ka fasa aurenta ka fito ka nunawa duniya cewa tana da cutar da ke karya garkuwar jiki, sannan ka saye dukkan likitocin garin nan ta yadda Maganar ka zata Tabbata, idan ka mata haka to ba dukan zuciyar ta kayi ba kasheta kayi, domin kuwa ba ita ba hatta ƴan uwanta sai baƙin ciki ya kusa kashe su."
Waro idanunsa Hisham yayi tare da saki dariya har yana dukan teburin gabansa
"Nice idea Sadiq tabbas wannan ce kaɗai hanyar da zan gama mata wulaƙancin duniya, bansan meye Soyayya ba amma wannan karon zan buga wasa da ita domin kuwa idan wasa akan maƙiyi ne ba ƙaramin daɗi yake min ba, ka zuba idanunka ka kalli yadda wasan zai fara."
"Nasan zaka iya shiyasa na kawo maka wannan shawarar amma karka yadda kowa yasan Game kake bugawa a Soyayyar ta, ka nuna musu Soyayyar gaskiya ne, hatta Nameer dasu Ummi su ɗauka son na gaskiya ne, amma karka sanar da kowa har sai ta amshi tayinka."
"Kana da basira Sadiq

Please Login or Register in order to submit comment