Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da dama masu ji da
sadaukantaka.
sun mutu acikin wannan dakin.
don haka ku dauke shi ku kai shi can dakin
kasa.
cikin sauri dakarun suka kama hujurul
mahas suka tashe shi tsaye.
suka tasa keyar shi suna tafiya.
awannan lokaci gimbiya salira sai kallon
hujurul mahas take tana tausayin halin da
ya tsinci kan sa har ta kai ga har ga za asa
shi awannan dakin da ba a fita araye idan
har an shige shi.
nan salira taji lokaci guda hujurul mahas ya
kwanta mata taji kamar taje ta dakatar da
wadannan dakaru.
amma babu hali haka ta cigaba da kallon
hujurul mahas.
shi ma hujurul mahas yana kallon ta da
watsiyar ido.
ko da dakarun suka lura da kallon da
hujurul mahas ke yi wa gimbiya salira sai
babban su ya daga wata sanda dake
hannun sa ya bugawa hujurul mahas a
dantsen hannun shi.
sannan yace.
kai 'ban ka!!
mu da muke gidan bamu damu da mu ganta
ba sai kai.
wanda kake matsayin mai laifi..
hujurul mahas ya cije duk da yaji zafin
dukan da wannan shugaban dakarun yayi
masa"
haka suka cigaba da tafiya suna wuce
lunguna da sakuna ba cikin gidan.
duk in da suka wuce sai jama'ar gari suna
kallon su ana mamakin yadda wannan
mutumin tsautsayi yazo masa muraran har
shiga hannun sarki maharu.
lallai muddin idan har ya shiga wannan
dakin na azaba to tashi ta kare don saidai
'uwassa ta haifi wani amma ba shi ba.
haka mutane gari suke ta fada.
ahaka dakarun suka taso hujurul mahas
wanda ke daure cikin sarka.
har suka zo wani babban fili wanda ke share
tas.
babu alamar datti.
ko ina ka duba fes fes.
shi kan sa hujurul yana mamakin yadda
akayi akazo dashi nan kuma aka tsaya
bayan ance kuma dakin azaba za azo dashi.
nan dai hujurul mahas ya tsaya kuma ya
zuba ido yana kallon dakarun.
su kuma dakarun sai suka fara kwance
sarkar dake hannu da kafar sa sannan. har
suka kwance duka.
ko da hujurul mahas yaga sun kwance shi.
sai ya fara zazzare idanu yana kallon gabas
da yamma kudu da arewa.
cikin shammata ya zage karfin dantsen shi.
ya takarkare ya gabzawa wannan shugaban
dakarun naushi akunne.
a take shugaban dakarun ya sandare a
tsaye tamkar gunki.
sannan ya fadi kasa matacce ko shurawa bai
yi ba.
ko da sauran dakarun suka abinda ya faru
ga dan uwan su sai suka kwarara 'uban ihu
suka afakawa hujurul mahas su duka hudun
sai gashi hujurul mahas ya kuntata su nan
take ya shiga gabza musu wawan naushi
suna zubewa kasa matattu kafin wani lokaci
ya bazar dasu duka hudun.
yana gama kashe su sai ya hango wasu
gugun dakaru rike da makamai sun nufo
shi.
nan take hujurul mahas ya juya ya nufi
wannan babban filin da gudu.
kash rashin sani yafi dare duhu.
abin da hujurul mahas bai sani ba shine.
anan wannan dakin azaba yake.
ko da hujurul mahas yaza dai dai tsakiyar
filin sai kasar wurin ta rufza dashi aikuwa
sai gashi ya fada ciki.
nan kasar wurin ta dawo dai dai yanda take.
su kuwa dakaru ko da suka dai dai wurin sai
suka tsatstsaya suna waige waige.
sai daya daga cikin dakarun yace.
ai ya riga fada cikin wannan dakin na
mutuwa.
in da yana nan da mun ganshi.
saboda tanan ya biyo babu yanda za ayi ya
biyo tanan ba tare da ya fada wannan dakin
ba.
don haka mu koma muje mu fada wa sarki
cewa ai wannan jarumi ya fada dakin
mutuwa.
cikin hadin baki dakaru suka ce.
haka ne!!
" al'amarin hujurul mahas kuwa lokacin da
ya fada wannan dakin sai ya tsinci kan sa a
wani irin duhu matsananci.
al'amarin da ya firgitashi kenan zuciyar shi
tana dukan uku uku.
can sai yaga cikin dakin ya haskake da wani
irin haske.
wanda yasa hankalin ya kwanta.
amma da ya ga abun dake ciki sai hankalin
sa ya tashi.
wani kogon dutse ne ya gani ku sa dashi.
acan gaba ma ga wani shuri babba mai cike
da manyan kofofi.
bayan sauran dakunan dake gaba.
hujurul mahas ya tashi daga zaman da yayi
ya cigaba da kallon wannan kogon dutse.
yana cikin wannan kallon kogon dutsen ne
ya jiyo wani irin gurnani mai matukar tayar
da hankali......
Comment and likes
BY ABBAS
WITH:- Shuraih 99%
ρðšтєđ by Shuraih 99%
νįά● Shuraih 99%
Fðя мðяє

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1
By ABBAS
With Shuraih 99%
Part 13
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
afirgice ya zare takobin sa ya fara ja da baya
yana jiran yaga abinda zai futo.
amma sai gurnanin ya cigaba da karu wa.
nan fa hankalin sa ya dugunzuma.
kamewa yayi awuri daya bisa abinda ya gani
ya futo daga cikin wannan kogo.
wata jibgegiyar macijiya ya gani tana
futowa mai kawuna goma.
ga hakoranta bircik acikin bakinta bare
kuma dogayun fikokin dake bakinta
atsatsaye masu tsinin tsiya.
haka ya cigaba da kallon macijiyar tana
futowa har ta gama futowa.
ko da hujurul mahas yaga girman macijiyar
da tsayin ta.
sai ya tabbatar da cewa rayuwar sa na
tsakanin mutuwa da rayuwa.
awannan lokaci tuni macijiyar ta fara
kewaye shi.
tana gurnani.
ko da hujurul mahas yaga haka sai ya fara
amfani da karfin sihirin sa don ya tsallake
macijiyar da take kewaye shi.
ko da yayi sama sai macijiyar tayi amfani da
jelarta ta bugoshi.
sai gashi ya bugu da jikin dutsen kogon
take kansa ya fashe.
da sauri hujurul mahas ya shafa kansa koda
yaga jini sai ya tashi afirgice ya cigaba da
kallon macijiyar.
sai yanzu ya tabbatar ya shiga tsaka mai
wuya kashe wannan macijiyar sai yayi da
gaske.
dole ne yasan dabarar dazai yi ya kashe ta.
nan take yakara rike takobin sa gam gam ya
fuskanci macijiyar.
kawai sai ya ruga da gudu ya tunkari
macijiyar.
ko da ya iso daf da ita sai ta kawo masa
wawan sara akai.
cikin zafin nama ya goce.
sannan yayi tsalle ya gabzawa macijiyar
sara da takobin sa a tsakiyar kai.
take tartsatsin wuta ya tashi har da hayaki.
al'amarin da ya razana hujurul mahas
kenan.
ya tabbatar tasa ta kare.
haka macijiyar ta cigaba da kai masa
mugayen hare hare yana tsallakewa.
akarshe ta kara buga masa wannan jelarta
ta.
wannan karon sai da yayi sama sannan ya
fado ya bugu da jikin kogon dutsen.
agalabaice ya fara numfarfashi.
kamar ransa zai fita duk da haka sai da
macijyar ta kara kawo mishi sara.
cikin zafin nama ya mirgina ya bar wurin.
macijiyar ta karci kasa.
ta haifar da dogon rami.
hujurul mahas yayi zumbur ya tashi ya rike
takobin sa ya cigaba da kallon macijiyar
yana tunanin dabarar da zai bullo mata ya
kashe ta.
yana cikin wannan tunanin ne bai yi aune
ba sai ji yayi macijiyar ta shammace shi ta
kafta masa sara akai.
take ya fadi kasa yana kakarin mutuwa.
wata farar kumfa tana fita abakin sa.
ita kuma macijiyar sai ta tsaya akan sa tana
gurnani tana shirin karasa shi....
Ahankali ya fara bude idanun sa. Sannan ga
macijiyar tsaye a kanshi tana jiran yayi
wani motsi.
Comment and likes
BY ABBAS
WITH:- Shuraih 99%
ρðšтєđ by Shuraih 99%
νįά● Shuraih 99%
Fðя мðяє

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1
By ABBAS
With Shuraih 99%
Part 14
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
tashi yayi zaune daga kwancen da yake.
ya amayar da dafin wannan macijiyar da ta
saka mishi.
cikin zafin nama ya mike zumbur kafin
macijiyar tayi wani yunkurin farmasa tuni
ya daka tsalle sama.
a saman ya zare wasu takubba guda biyu.
sannan.
kawai sai ya caka mata takubban guda biyu
acikin idanun ta biyu.
faruwan hakan kenan sai kan macijiyar
guda biyu ya daina aiki.
ko da hurul mahas ya ga haka sai ya gane
lagon macijiyar a idanun ta yake.
kawai sai ya zage dantse ya cigaba da caka
takubban sa acikin idanun macijiyar...
ita kuwa macijiyar ta fara karaji ta na kawo
masa muggan hare hare amma yana kauce
wa...
wani gagarumar bajinta hujurul mahas ke
nuna wa.
domin cikin kankanin lokaci ya faffasa
idanun macijiyar tare da taimakon
takubban hannun sa.
kawai sai gani yayi macijiyar ta fadi kasa
rikica ko kwakkwaran motsi.
ta riga ta zama gawa.
shi kuwa hujurul mahas sai ya fadi akasa a
sume.
*** al'amarin aljani mardis kuwa tare da
wadannan dakaru .
sai da suka yi kwana uku acikin sararin
sama suna zabga uban gudu tamkar
tauraruwa mai wutsiya sannan suka fara
hango kofar birnin zamar.
awannan lokaci suna iya hango dandazon
muggan dakarun da suke kaikawo awurin.
duk da cewa dare ya fara yi.
kawai sai suka fara rage karfin gudun nasu.
sai da kusa da birnin yanda dakarun baza
su gan suba.
sannan suka fara sauko wa kasa.
sai ga shi sun dira bisa kasa ahankali.
su ka nemi wani wuri abayan wata bishiya
suka buya tare da taimakon ganye bishiyar.
yanda baza agansu ba.
bayan sun nutsu sai aljani mardis ya dubi
wani badakaren aljani wanda shi ne dan
babba acikin su.
sannan yace.
yakai karsas ina so nasa ka
Comment and likes
BY ABBAS
WITH:- Shuraih 99%
ρðšтєđ by Shuraih 99%
νįά● Shuraih 99%
Fðя мðяє

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1
By ABBAS
With Shuraih 99%
Part 15
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
wani aiki.
da zarar dare yayi ina so ka rikida izuwa
siffar bil.adama.
ka yi shiga ta wadannan dakaru mu kuma
sai mu rikida izuwa siffar fursunoni.
sannan sai na saka mana sarka hannu da
kafa yadda ba za su gane mu 'yan harin ba
zato idan har mun shiga cikin birnin ni na
san abin da zan yi.
abin da yasa kaji nace kayi shiga irin ta
wadannan dakaru kuwa.
shi ne.
dakarun suna dayawa.
baza su gane wani ne daban ya shigo cikin
su duk da suna ba da tsaro.
na musamman.
da zarar mun ga dakarun sun fara hango
mu.
sai ka fara ihu kana ikirarin azo ataimaka
maka ga wasu fursunoni.
na tabbata za su zo gare mu domin su
ganewa idanun su.
abu ne mai wuya su gane cewa kai ba acikin
su kake ba.
idan kuwa har suka gane hakan cewa kai ba
daga yankin su ka futo ba. to komai zai iya
faruwa.
yanzu dai bari mu jarraba wannan shawarar
da nazo mana da ita.
na tabbata zamu cimma nufin mu.
ko da aljani mardis yazo nan a jawabin sa.
sai aljani karsas ya gyada kai
alamar ya yarda akwada wannan shawara
da aljani mardis yazo da ita ko za ayi nasara.
suma sauran dakarun aljanun suka amsa
sun yarda da wannan shawara.
" hakan kuwa suka yi ba yan dare ya yi sai
aljani karsas ya rikida izuwa irin wadannan
dakaru masu gadi.
su kuwa su aljani mardis suka rikida izuwa
fursunoni.
aljani karsas ya sa musu sarka hannu da
kafa.
aljani yasan dalilin da yasa shi bai zama
shugaba da zai jagoranci dakarun da suke
tare dashi.
shiyasa yasa aljani karsas.
bayan aljani karsas ya daddaure su da
sarka sai kama sauran sarkar da ta rage ya
fara jan su.
haka suka ta tafiya har suka fara isowa in
da wadannan dakaru suke.
da yake cikin dare ne.
sai ya fara jan su aljani mardis da karfi suna
cijewa.
ya shiga kwalawa dakarun kira azo taimaka
masa.
aikuwa sai dakarun suka ankara dashi...
saura suka tsaya abakin kofar shiga garin
saura suka nufo in da su aljani mardis suke.
cikin kankanin lokaci sai ga dakaru sun
kewaye su aljani mardis.
nan take wani badakare mai kirar
samudawa.
ya ratso ta cikin dakarun.
ya bayyana atsakiyar filin.
nan take ya cafke sarkar dake hannun aljani
karsas "
da wata irin babbar murya yake magana.
zan tafi dasu wurin shugaban mu sarkin
kofa.
domin shi zai yanke hukunci.
don haka ka biyoni abaya.
yana gama fadar haka.
ya dakawa fursononin tsawa yace.
kai kananan kwari.
ku na tunanin mugun nufin ku zai sauka
akan mu ne?
ko kadan ba ku isa kuyi mana komai ba.
domin ka ta wacce siiiiga ku ka zo sai an
tona muku asiri.
yanzu gashi kun shiga hannu.
daya daga cikin dakarun mu ne shi ya tona
asirin ku.
dama kuna so ku kawo mana mamayar ba
zato?
ko haka ba ne?
ya wankawa daya daga cikin fursunonin
mari.
yace.
"ba tambayar ku nake ba.
dukan su fursunonin suka ce.
eh.
shugaban dakarun ya finciki sarkar dake
daure ajikin
fursunonin.
ya fara jansu.
aka buda masa hanya ya wuce.
saurana dakarun suka bi shi abaya duuuu?
kamar dokuna.
suka tunkari wurin sarkin kofa.
sauran dakarun dake bakin kofa suka ba da
hanya.
kai tsaye aka tura su aljani mardis gaban
wannan sarkin kofa mai kirar manyan
samudawa.
jikin sa gabadaya acike jijiyoyi.
ga damatsan hannayen sa burdin burdin".
sarkin kofan ya tashi tsaye.
ya kyalkyale da dariya kamar bazai daina
ba.
daga ya murtuke fuska.
yace.
wadannan su ne fursunonin.
aka ce eh"
ina wanda ya kawo su."
aljani karsas ya ratso ta cikin dakarun cikin
siffa irinta dakarun.
aka ba shi hanya.
ya tsaya a gaban sarkin kofa.
ko da sarkin kofa yaga wanda ya kawo su.
sai yayi murmushi. ya fara zagaye aljani
karsas.
shi kansa ya fara tsorata da al'amarin sarkin
kofa"
kada fa asirin su ya tonu fa"
sarkin kofa ya kyalkyale da dariya sannan
yayi tsit.
ya dakawa su aljani mardis tsawo yace.
karya kuke ku ba mutane ba ne.
nasan me kuke nufi.
kun shirya wani makircin ku ne daban.
sai gashi hakan ku bai cimma ruwa ba?
sarkin maharu. wato sarkin birnin ya fada
mana akwai wasu bakin aljanu za su zo nan
birnin a cikin siffa ta bil'adama.
abinda ya fada mana.
mu kama ku mu sakaku acikin sarka mu
gurfanar daku gareshi.
ko ku bimu acikin ruwan Sanyi.
mu tafi daku amutunce.
idan kuma ko kace da tsiya zaku bimu.
zamu kai kune a wahalce."
ko da su aljani mardis suka wannan batu.
sai suka fara zazzare idanu.
suka tabbatar da cewa asirin su ya
tonu.........
Comment and likes
BY ABBAS
WITH:- Shuraih 99%
ρðšтєđ by Shuraih 99%
νįά● Shuraih 99%
Fðя мðяє

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1
By ABBAS
With Shuraih 99%
Part 16
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
sarkin kofa ya dakawa wasu dakaru tsawa.
wanda su kasance karatan samudawa.
yace.
Ku kama su ku kara daure cikin sarka.
a tafi dasu gurin sarki""
! dakata !!!
aljani mardis ya dakawa wadannan dakaru
tsawa.
kada dayan ku ya matsa kusa damu"
lokaci guda aljani mardis ya rikida izuwa
ainihin halittar sa.
suma sauran aljanun suka dawo ainihin
halittar su"
ko da sarkin kofa yaga haka sai dakawa
dakarun tsawa.
yace.
me kuke jira dasu ku kamasu ku daure su
cikin sarka"
awannan lokaci sarkar da ta daure su aljani
mardis ta tsinke.
ko dakarun suka zo wurin su aljani mardis
domin su daure su.
cikin zafin nama aljani mardis.
yayi amfani da hannun sa.
ya daki badakaren mai rike da sarkar akai.
take badakaren ya fadi kasa matacce.
sauran dakarun kuwa suma ya gaggasa
musu naushi daddaya suka bace awurin.
ko da ganin wannan abun sai gabakidaya
dakarun suka afakawa su aljani mardis. aka
ruguntsume da azababben yaki.
shi kuwa sarkin kofa gefe daya ya koma ya
cigaba da kallon wannan gumurzu.
wohoho!!
nan fa su aljani mardis suka zamewa
wadannan dakarun masifa. sun kuntata su.
ban da Sara da sukar dakarun babu abinda
su aljani mardis suke.
cikin kankanin lokaci sai jikin ya rine da jini.
domin sai gididdibar dakarun suke ba ji ba
gani.
sai dai kaga lokaci guda aljani mardis ya
fillewa dakaru ashirin kai alokaci guda.
shima aljani karsas sai gagarumar bajinta
yake nunawa.
domin shima ragargazar dakarun yake.
haka suma sauran aljanun.
sai karkashe dakarun suke"
ko da sarkin kofa yaga za'a karar da
wadannan dakarun nasa.
sai kwarara uban ihu.
Wanda yayi amsakuuwa afilin gabadaya"
babu shiri dakarun suka janye yakin dukan
su.
aka budawa sarkin kofa hanya ya shigo.
tsakiyar filin ya tsaya.
sannan ya zare takobin sa ya daga sama ya
kwarara wani ihu daban.
Wanda yasa dakarun wajen suka toshe
kunnuwan su.
har sai da ya tsaya da dariyar sannan aka
samu sauki.
sannan ya fuskanci aljani mardis ya daka
masa tsawa.
kai shu'uman aljanu karyar ku tasha Karya.
kun kashe mun dakaruna gabada ya.
Wanda suka rage ba su fi guda arba'in ba .
duba kasa duka gawarwakin dakaruna ne.
Wanda suke tayani gadi"
ba dan dalili kwaya daya ba da sai nayi
muku mugun kisan gillah.
sarkin mu yana bukatar ku a raye.
yanzu zan kama Ku na daure ku acikin
sarka...
aljani mardis ya dakawa sarkin kofa tsawa
yace..
karya kake kace zaka kama mu ka samu
cikin sarka.
ba ka isa ba wanene kai.
idan har kaga an kama mu anan to tabbas
bama numfashi.
sarkin kofa.
yayi murmushi yace.
kada ka wahalar da kanka abanza.
da kai da wadannan abokan tafiyar taka.
domin daure Ku acikin sarkar nan ya zama
dole.
aljani mardis. yace.
to bari na fada maka ko sarkin ku ne yazo
nan yace zai saka mu a sarka to ba zai Iya
bare kai karamin alhaki.
mafita daya ce ka bamu hanya kawai mu
wuce har can cikin wannan birni domin mu
sarki maharu da mashin sihiri...
kafin aljani mardis ya rufe bakin tuni sarkin
kofa ya tunkaro shi kai tsaye.
aljani mardis ya tsaya awurin da yake.
yana jiran karasowar sarkin kofa.
sarkin kofa yana zuwa ya kawowa aljani
mardis cafka..
cikin zafin nama aljani mardis ya sunkuya
ya goce ya bi ta tsakanin kafofin sarkin kofa.
nan ya zare takobin sa ya sari bayan sarkin
kofa.
nan take yaji kamar ya sarin karfe.
al'amarin da bashi mamaki kenan .
lalle sai yayi da gaske.
afusace sarkin ya juyo. ya kara kawo masa
cafka.
nan ma ya kara kaucewa.
haka rinka kawowa aljani mardis cafka yana
gocewa.
daga karshe ya samu nasarar bige aljani
mardis.
sai da yayi sannan ya bugu kasa agalabaice.
kamar ransa zai fita.
nan fa sarkin kofa ya tunkaro aljani mardis
kai tsaye.
shi kuwa aljani mardis ya fara mika hannu
don ya dauko. takobin sa. amma hannun sa
yaki ya tarar.
gashi sarkin kofa saura kadan ya zo in yake .
cikin sauri aljani karsas ya harbo masa wata
karamar wuka mai tsananin kaifi.
ya cafe wukar.
nan take ya kamu da tsananin farin ciki
domin wannan dole tayi tasiri ajikin sarkin
kofa.
adai dai lokacin sarkin kofa ya iso ya tsaya
akan aljani mardis.
nan take ya futo da wata murtukekiyar
sarka.
sannan ya juya da kansa domin ya kira
wasu dakaru.
kafin ya juyo tuni aljani ya tashi zumbur
yayi tsalle.
yayi amfani da wukar hannun sa. kawai sai
ya farke masa ciki .
nan take wukar ta kamashi.
sai ga tumbin sa ya zazzago waje.
nan take sarkin kofa ya fadi kasa yana
shure shuren mutuwa.
su kuwa sauran dakarun sai suka tarwatse.
suka kama gudu acikin daji ba tare da sanin
in da za suje ba"
shi kuwa aljani mardis sai yayi murmushi.
yana duban wukar.
sannan ya juya ya dubi sauran aljanun
yace.
muyi sauri mu shiga cikin birnin nan ba mu
da lokacin tsayawa.
cikin sauri dukan suka dunguma suka shiga
cikin birinin kai tsaye.."
**** cikin dare ne sosai sarkin maharu yana
kwance acikin daki.
a wannan lokaci idanun sa biyu bai yi bacci
ba.
Kawai sai yaji takun sawu.
acikin dakin da yake.
zumbur ya tashi zaune ya fara waige waige.
amma bai ga komai ba.
da sauri ya tashi yaje ya bude kofa.
ya lelleka waje bai kalli komai ba.
nan take ya tuna da mashin sihiri.
cikin sauri ya koma cikin dakin.
ya nufi in da ya aje wannan mashin.
yana zuwa ya tarar babu komai an dauke
mashi.
kawai sai ya sa hannu ya fara bincika wurin.
amma babu mashi.
nan take hankalin yayi mugun dugunzuma.
yace .
shi kenan ta faru ta kare.........

Comment and likes
BY ABBAS
WITH:- Shuraih 99%
ρðšтєđ by Shuraih 99%
νįά● Shuraih 99%
Fðя мðяє

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1
By ABBAS
With Shuraih 99%
Part 17
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
da sauri ya dauki takobin sa.
yana fadin aikuwa yau garin nan babu
zaman lafiya.
cikin daren nan kowa hankalin sa ya tashi"
"an dauke wannan mashin"
ya kara fada tare da cije leben bakin sa"
da sauri ya fita waje yana fadin ina masu
gadin gidan nan.
yana fada yana kara fada.
cikin kankanin lokaci sai ga kowa ya furfuto.
sun sussunkuyar da kai.
ya daka musu tsawa yace.
karya kuke munafukai ku futo min da
wannan mashin.
idan kuma ba haka zan yanke mummunan
hukunci akanku.
kun sanni ba ni da sassauci"
dukan su dakarun suka dago da kan su
afirgice.
suka ce.
bamu dauki wannan mashin ba.
sannan kuma bamu kalli wanda ya dauka
ba.
babu wanda ya shigo domin ko ta ina acikin
gidan nan mun tabbatar da tsaro."
sarki maharu ya kwara uban ihu.
kawai sai ya dakarun da sara da suka.
yana fadin karya kuke yi ku futo min da
wannan mashin.
ba ku isa ba.
kafin a jima ya karkashe wadannan dakaru"
adai dai lokacin gimbiya salira ta futo tana
fadin.
lafiya abbana me ya faru...
agigice ya ce.
an sace wannan mashin sihiri.
an sace"
zama bai kamani ba .
dole ne na tunkari gidan aljani bagazas.
domin ina tunanin shi zai dauke wannan
mashin"
yana gama fadar haka sai suka ga an jeho
wata farar takarda.
basu ga Wanda ya jeho ba.
cikin tsananin mamaki suka dubi junan su.
salira tace bari na je na dauko..
sarki maharu yace.
dakata"
kawai sai ya nufi in da wannan farar takarda
take.
yana zuwa yasa hannun ya dauka.
sai yaga ashe wasika ce ajiki.
ko da ganin haka sai ya warware takardar
ya fara karanta wasikar kamar haka..............
ni ne boka saljan wanda nake zaune acan
dajin jahur.
to kasani yanzu na kaura a dajin jahur.
na canja wurin zama baza ka taba sanin in
da nake ba""
ni ne na sace maka wannan mashin sihiri
saboda baka isa ka mallake shi ba.
yanzu kam babu kai babu samun mashin
sihiri.
ka rabu dashi kenan baza ka same shi.
ko kadan babu sa hannun aljani bagazas
awannan
tabargazar da akayi .
shi ma nasan za a labarta masa cewa ni na
dauke wannan mashin.
nasan dole shi ma zai ce zai shiga farautata.
to inaso ka sani dakai da aljani bagazas ba
ku isa kuje in da baza ma kusan in da nake
ba.
har sai na gama mallakar wannan mashin
sihiri.
ina fatan zaka yi hakuri ka rungumi wannan
kaddarar da tazo maka ba kayi zato ba.
bari na barka haka kada ka hadiyi zuciya ka
mutu?
ko da sarki maharu yazo nan akaranta
wannan wasikar sai ya yayyaga ya watsar.
sannan yace.
idan na ya isa na bar shi shege nake.
duk in da yake sai na nemo shi.
idan yana ji da shu'umanci to nasa wasa ne?
mu zuba mu gani?
salira tace.
me kuma ya faru daka karanta wasikar?
sarkin maharu yace.
kinga barni kawai yau din nan?
yana gama fadar haka ya fara tattara
gurayen tsafin sa yana sawa ajikin sa.
ita kuma gimbiya salira sai ta tsaya tana
kallon sa.
sai da ya gama shirin tsaf sannan ya dubi
salira yace zan sa dakaru wasu daban za
suyi gadin ki.
yana gama fadar haka ya fice acikin gidan
gabada ya.
ya hau kan dokin sa ya zabure shi da gudu"
****ita Kuma salira sai ta tsaya ta bishi da kallo
tana sake sake.
akan lamarin da hujurul mahas ya shiga.
ya zama dole tasan yadda za tayi ta ceci
rayuwar sa kafin mahaifin ta ya dawo.
babbar matsalar yanzu cikin dare ne.
ga kuma hanyar da za'abi a shi ga gidan
azabar nan guda biyu ne.
daya tana can waje.
in da hujurul ya shiga.
dayar kuma tana cikin gidan sarautar ta su.
ta yaya za ta wuce wadannan dakaru ba
tare da an tambaye ta ina zata ba.
domin an basu gadin ta kada subar ta ta
fita acikin wannan gida.
dole za suce zasu dakatar da ita yanzu me
ne abinyi.
ta tsaya tana nazari.
tun lokacin da tayi arba da hujurul mahas
ta ji kamu da kaunar sa.
taimakon sa agareta ya zama dole.
za ta taimake sa ko da yace baya son ta.
idan ko yace baya son ta.
baza ta daina bibiyar sa.
har sai ta koya masa sonta acikin zuciyar sa.
ta hanyar nuna masa dabara irin tasu ta
mata.
haka salira ta tsaya tana sake sake daga
karshe ta yanke shawarar bari gari ya waye
ta kaddamar da wannan kudirin nata da
tasa

Comment and likes
BY ABBAS
WITH:- Shuraih 99%
ρðšтєđ by Shuraih 99%
νįά● Shuraih 99%
Fðя мðяє

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1
By ABBAS
With Shuraih 99%
Part 18
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
a zuciyarta"
ta koma Daki kuyanginta na biye da ita"
**
al'amarin su aljani mardis kuwa tun lokacin
da suka shigo cikin birnin tun kafin su
karasa cikin garin wani shu'umin badakare
ya tsayar dasu yana labarta musu cewa ai
an sace wannan mashin sihiri.
a cewar su aljani mardis basu yarda ba.
sai sun je sun tabbatar da gaskiyar lamarin.
kawai suka ji jama'ar gari suna ta fadan an
sace mashin sihiri na sarki.
nan da nan zance ya cika gari.
acikin daren.
jin wannan maganar daga bakin jama'ar
gari ya tabbatar musu da cewa gaskiya ne
an sace mashin sihiri don haka basu yi kasa
aguiwa ba. nan da nan suka juya da baya
suka bude fukan fukan su suka tashi sama
suka luluka acikin gajimare suka bace bat.
don ko ta yaya sai sun nemo wanda ya sace
mashin sihiri?
*** kwance yake cikin halin galabaita don
bai dade da farfadowa ba daga suman da
yayi ba.
cikin karfin hali ya tashi duk da cewa jiri
yana daukar sa bai karayah ba.
ahakan yaje ya dauko wata jakar sa wanda
zuba maganunkan sa aciki.
don faduwar da yayi ne yasa jakar ta fadi
can gefe.
zama ya shiga manna maganin ajikin raunin
da wannan macijiya tayi masa.
ya na manna maganin kamar zai rusa ihu
amma dage yana cije laben bakin sa"
don kada sauran muggan abubuwan dage
cikin kogon su jiyo shi.
yanzu yanzu sai su farmasa bai shirya ba.
bayan ya gama sa maganin acikin raunikan
dake jikin sa.
sai yaji wata irin matsananciyar yunwa tazo
masa bai yi zato ba.
nan fa hankalin sa ya tashi.
don saboda babu in da zai samu abinci
acikin wannan kogon.
shiru yayi yana nazari.
can sai ya tuna akwai sauran guzurin
abincin sa acikin wannan jakar.
nan take ya duba jakar da ya futo da
maganin.
sai gashi yaga sauran guzurin nasa.
nama ne gasasshe wanda yaci ya rage tun
kafin ya fado hannu sarki maharu.
haka yaci naman sosai har rage da yake
nama yana da yawa.
sai aje sauran don bai san me zai faru ba
nan gaba ba.
haka ya zauna awurin tsawo lokaci.
sai gashi ya ji saukin jikin sa ba kamar dazu
ba.
awannan lokaci tamkar babu abinda ya
same shi a gumurzun da yayi abaya.
kawai sai ya mike tsaye.
ya dauki takobin ya mayar da ita cikin
kufenta.
sannan ya dauki jakarsa ya rataya.
kawai sai yaga an yi rubutu ajikin bangon
kogon.
kamar haka.....
sai kayi bakin artabu da muggan halittun
dake cikin wannan kogon guda goma kafin
ka samu hanyar fita daga wannan taskar
wahalar.
hujurul mahas ya tsaya yana tunani..
to shi sarki maharu shi wanne irin azzalumi
ne.
ta yaya ma ya samar da wannan gida mai
cike da munanan hadarurruka"
amma babu komai.
duk abinda yayi farko zai yi karshe.
tunda har yana rike da wannan mashin
sihiri dole sai an samu Wanda zai halaka shi.
ya raba shi da mashin sihiri shi kenan tashi
ta kare.
hujurul ya jima atsaye yana tunani.
daga karshe sai ya tunkari wannan kogo
dake gaban sa.
kawai sai ya shige kai tsaye.
ba tare da fargabar komai ba.
yana shiga yaji an rufe kogon ruf.
babu ta in da zai bi ya fita.
waigowa yayi ya duba kofar kogon sai yaga
ai arufe take.
to waye ya rufe bayan babu kofa.
kuma shi ne kadai acikin kogon.
tow.
ya fada acikin zuciyar sa.
kawai sai juya ya cigaba da tafiya.
yana taka kwarangwal din mutane.
wanda sun dade

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment