Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi wannan mashin sihiri da kake gani duk wanda ya same shi to bazai taba samun damar mallakar sa ba har sai ya karanta wasu dalamisan tsafi kafin ya zama mallakin sa.
ba don komai ba kazo gun boka saljan ba sai don ya baka wannan dalamisan tsafi.
to ina so kasan wani abu nafi boka saljan komai da komai abangaren sihiri.
saboda atafin hannuna nake ganin sa.
muddin kaje kasa mo wannan mashin sihiri to za zan taimake ka da wannan dalamisan tsafi.
ka sani cewa ba ni niyyar cutar da kai ko kadan.
idan har ka bi umarni na zaka cimma bukatar ka wanda karshen ta babu muni ko wata yaudara sai farin ciki.
idan har ka mallaki wannan mashi to asannan ne zaka kawar da aljani bagazas ka karbi aljanin ka.
ya zama dole ka je ka riga aljani bagazas samun wannan mashin sihiri kar ya riga.
za kazo ka same ni mai cika alkawarin dana daukar maka?""

boka hujurul mahas ya dago da kan sa yace.......
Comment and likes
BY ABBAS
WITH:- Shuraih 99%
ρðšтєđ by Shuraih 99%
νįά● Shuraih 99%
Fðя мðяє

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1
By ABBAS
With Shuraih 99%
Part 6
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
to ina so nayi maka wata tambaya.
ko zaka iya fada min ya akayi aljani mardis ya amince da bukatar aljani bagazas har ya tafi birnin sarki maharu domin cika umarnin aljani bagazas.
sannan kuma yanzu idan har na je samo wannan mashi dole mu hadu da aljani mardis tunda shima ya tafi neman mashin ne.
ka na ganin idan mun hadu dashi babu wata matsala..
sarki majarul daufus ya kyalkyale da kafin yace.
yanzu kana tunanin aljani bagazas ya dauke aljani mardis ne haka kawai don ya biya masa bukatar sa ba tare da ya masa wani abu ba. wanda ya danganci juyar masa da kwakwalwa.
to ina mai tabbatar maka da cewa aljani bagazas ya juyar da kwalkwalwar aljani mardis yadda ko kai kayi arba dashi bazai gane ka ba.
domin a yanzu haka ya dauki aljani bagazas amatsayin kai ne.
abinda zai daidaita komai shi ne kawai ka samu mashin sihiri.
saboda dashi zaka dakatar da wannan buri na aljani bagazas.
muddin ka bari aljani bagzas ya samu damar biyan bukatar akan wannan to shike nan taka ta kare ka rabu da wannan aljani baza ka sake samun shi ba.
sannan zalunci da zai gudanar a wannan nahiyar kai kanka baza ka tsira ba don sai ya shafe ka.
abinda zan fada kawai shi ne ka samo wannan mashin sihiri domin cimma bukatar ka"

boka hujurul mahas yace.
na ji duk abinda ka fada kuma ko ta wacce hanya sai na bi don ganin na biya bukata ta.
sannan kuma idan har na hadu da aljani mardis acan wurin neman wannan mashi zan nuna masa. ni ne maigidan sa wanda muke zama tare a kogon dutse.
na tabbata zai gane ko ni wanene.

sarki majarul daufus yace.
aa kar ka fara kada ka kuskura"
yin hakan babbar matsala ce.
idan har kace za ka tunkari aljani mardis a wannan lokaci.
ka bari sai ka ga ka mallaki wannan mashi kafin ka tunkare shi.
asannan ne komai zai dawo dai dai.
sannan kuma idan ka dawo daga wannan neman mashi.
ina maka albishir da zan aura maka 'yata lushmat.
don ku zamto miji da mata.
boka hujurul mahas ya dago da kansa .
haba! sarki ya ina matsayin boka ita tana matsayin 'yar sarki sannan kace zaka hada ta aure dani.
sarki yayi murmushi yace.
na sani amma nan gaba sai kayi tunanin itace muradin ka.
tun da yanzu nazo maka da batun auren ta tare da kai. kana kokarin janyewa.
ka sani cewa matukar ka auri wannan 'ya tawa ka rabu da harkar bokanci.
zaka yi rayuwar cikin mulki da jin dadi mara misaltuwa.
ko ka manta cewa lokacin da tsinci kanka acikin wannan gida nawa baka kalli wannan yarinyar ta sakar maka murmushi ba.
wannan bai nuna ma ka cewa tana sonka ba.
idan har burin ka ya cika to ka yarda ka zama mijin 'yata domin kuyi rayuwar ku cikin jin dadi.
batun wannan aljani kuwa ba dole sai kayi rayuwa dashi tun da shi ba jinsin ka ba ne.
nasan kun saba dashi sosai da sosai bazan iya cewa ka rabu dashi ba.
saboda biyan bukata yafi dogon buri?
da sannu komai zai dawo dai dai idan har kabi abinda na fada maka.
.
adai dai lokacin ne lushmat ta shigo cikin turakar tasha ado mai rikita zuciyar duk wani namiji da ya kalle ta.
sanye take cikin korayen kaya masu shara shara wanda aka lillika dutse irin na murjani sai sheki da walwali yake yana daukar idanu.
gashin kanta kuwa ya zubo har kwankwasonta shi ma yana sheki da walwali.

hakanne yasa boka hujurul mahas ya tashi tsaye yana kallon lushmat baki abude.
mace sai kace wanda tayi kanta.
ya fada acikin ransa.
sarki majarul daufus yayi murmushi ya dubi boka hujurul mahas yace.
yakai hujurul mahas ina mai umartar ka da kayi gaggawar zuwa neman wannan mashin sihiri kafin aljani mardis ya samu damar raba sarki maharu da mashin.
hujurul ya sunkuyar da kai yace.
angama ya shugaba na zan tafi.
yana gama fadar haka ya juya ya nufi kofar fita yana waigen lumshmat har yana tuntube.
bayan ya fita sarki majarul daufus ya tashi daga kan kujerar da yake zaune ya kyalkyale da dariya. kamar bazai dai na ba.
sannan yayi tsit da barin dariya yace.
wannan shi ake kira kura da shan bugu gardi da kwashe kudi.
tsuntsu ya fado mana daga sama gashashe.
Comment and likes
BY ABBAS
WITH:- Shuraih 99%
ρðšтєđ by Shuraih 99%
νįά● Shuraih 99%
Fðя мðяє

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1
By ABBAS
With Shuraih 99%
Part 7
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
na tabbata hujurul mahas sai ya sami nasara akan mashin sihiri. kinga kuwa buri na daf da cika.
nan gaba sauran bokaye da sarakuna su dawo biyayya agareni.
lushmat dai na tsaye tana kallon mahaifin nata.
sai da ya gama maganar tasa sannan tace.
yakai abba na ya kamata ka janye wannan nufin naka ga wannan jarumi.
kasani cewa idan har ya tafi neman wannan mashin sihiri zai sha bakar wuya wanda zai gwammace gara mutuwa da rayuwa.
don me zai hana baza ka fasa raba shi da wannan ba.
tun shi ma burin sa yake so ya cika dashi.
idan har ya mallaki mashin.
taimako daya za kayi masa shi ne ka basa dalamisan tsafin da zai karanta ga mashin sihirin nan"
majarul daufus yayi murmushi sannan yace.
kin ga 'yata ki kwantar da hankalin ki kada wannan abun da ya fara ya zamma matsala agareki.
samar da wannan mashi agateni babban farin ciki ne wanda ke kanki sai kin yi alfahari da haka.
kada ki yi tunanin wata matsala game da aikata wannan abu da nayi ga jarumin nan wato hujurul mahas.
saboda shima idan har ya samu ya ga ya mallaki wannan mashi to babu makawa sai kaddamar da zalunci ako ina akasashen nan.
ya zama dole nima na zamo mai kare kaina"
! ni da shi! kowa ya kwaci kansa aranar daya zo da mashin sihiri?
ko da majarul daufus yazo nan azancen sa.
sai lishmat ta dago da kanta ba tace komai ba. ta cigaba da kallon mahaifin na ta.
maharul daufus yace.
ya naji kinyi shi baki ce komai ba.
lushmat tayi murmushi tace.
babu komai abbana!!!!

hujurul mahas kuwa yana fita agidan sarki najarul daufus.
ya tsaya yana tunani.
ashe akwai mata kyawawa aduniya kamar lushmat. mace sai kace ita tayi kanta.
idan har na cika burina sai na mallaki gimbiya lushmat na aure ta' tunda har mahaifi ya yarda na auri 'yarsa mu kasance tare da ita.
wai akan wannan dalili sarki majarul daufus zai taimake ni haka.
ban san shi ba bai sanni ba.
ko dai akwai abinda ya shirya game da mashin sihirin nan?
nan dai ya cire zargi acikin zuciyar sa.
yayi shiru na tsawon lokaci sannan ya bace bat!!!!!

**** al'amarin aljani mardis kuwa lokacin da ya luluka acikin gajimare. shi da sauran dakarun da suke biye dashi.
sai ya zamana cewa suna zabga gudu babu kakkautawa.
babu ko hutawa. gudu kawai suke.
sai da suka yi kwana biyar suna gudu acikin sararin sama.
sannan aljani mardis ya fara sake fukakan shi yana sauka kasa .
suma sauran dakarun suka fara sauka kasa.
cikin kankanin lokaci sai gashi sun dira bisa turba.
acikin wani irin daji mai yawan sarkakiya.
ko ina ka duba acikin daji bishiyoyi ne masu tsayin gaske.
wanda ya karawa dajin duhu.
aduk lokacin da suka taka ganyayen bishiyoyin da suka zuba akasa.
sai suji karan rugurguwar ganyayen ya cika dodon kunne'
hakanne ya sa suka fara tafiya ahankali.
har suka fita a wajen dajin sannan suka tsinci kan su awani fili babba wanda ashare yake babu bishiyoyi irin wanda suka gani abaya.
aljani mardis ya juyo ya dubi sauran dakarun yace.
anan zamu yada zango kafin muci gaba da tafiya.
saboda bai wuce kwana 'uku ba mu riski birnin zamar ba in da zamu hadu da mummunan bala'i. wanda ba musan karshenta ya zai kasance ba.
sauran dakarun suka amsa da wannan umarni na aljani mardis.
su duka suka je bakin kogi suka sha ruwa sosai sanda suka ko shi sannan suka nemi wani wuri suka kishingida suna hutawa.
suna cikin hutawar ne.
sai suka ji dirar wani abu tamkar an sako katon tsauni daga sama don har sai da kasar wajen ta yi girgiza.
afirgice su aljani mardis suka.
wani mummunan aljani suka yi arba dashi.
yana kwala kwala idanu jajaye babu kyan gani.
faratan hannayen sa kuwa duk girman dutse idan ya sara sai ya raba shi biyu.
gabadaya jinkin amurde yake.
sai kace da karfe aka yishi.
zumbur su aljani mardis suka tashi tsaye.
shikuwa aljani sai bushe da wata irin mahaukaciyar dariya wadda ta cika dajin da amsa kuwwa.
Fyayi ta dariya kamar bazai daina ba.
daga can kuma sai ya murtuke fuska.
Yysannan ya dakawa su aljani mardis tsawa yace.
kai kananan kwari
mai yasa ku kayi ganganci zuwa birnin zamar domin ku raba sarki maharu da mashin sihiri.
ba ku da labarin sarki maharu ne?
......
Comment and likes
BY ABBAS
WITH:- Shuraih 99%
ρðšтєđ by Shuraih 99%
νįά● Shuraih 99%
Fðя мðяє

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1
By ABBAS
With Shuraih 99%
Part 8
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
ko kuma kun gaji da rayuwa ne kuka zabi ku
mutu.
ban da abinku ya za ayi kare yayi fada da
zaki.
kun tafka babban kuskure da har kuka
tunkari birnin zamar domin ku raba sarki
maharu da mashin sihiri.
gashi kuma duk wanda yayi yunkurin raba
sarki maharu da wannan mashin sihiri
sakamakon sa mutuwa.
don haka ba ku da mafita.
ko ku kubuta daga hannu na .
don haka ya zama dole sai na kashe ku.
aljani mardis yayi murmushi na nuna
dakakkiyar zuciya duk da cewa ya tsorata
da ganin wannan aljani.
amma hakan bai hana shi.
magana ba yace.
baka isa ka yi mana ko mai ba domin mun fi
karfin ka.
saboda ba dan mu rasa rayuwar mu ba mu
ka tunkari birnin zamar ba.
munzo birnin zamar ne domin mu raba sarki
maharu da mashin sihiri.
ko da aljani mardis yazo nan azancen sa sai
wannan basamuden aljanin ya kara
bushewa da dariya. wanda ta haddasa
bishiyoyi suka kama girgiza suna kokarin
kakkaryewa.
daga sai ya murtuke fuska yace.
lalle wannan mafarki naka bazai taba zama
gaskiya ba.
domin abinda ka fada dai dai yake da
mafarkin karya.
ina shawartarka.
da ka hakura da cewa nafi karfin ka.
domin idan nace zan kashe ka da karfi na
duka gawar kama baza ta ganu.
domin sarki maharu ya umarce ni da na kai
masa gawar ka.
yadda zai gane ka.
aljani mardis ya daka wa aljanin tsawa yace.
karya kake babu abinda da za ka iya mana
saboda ni kadai ma na fi karfin ka nesa ba
kusa ba.
idan har ka naso ka cigaba da rayuwa to ka
koma in da ka futo.
don ahalin yanzu ko wanda ya turo ka yazo
nan baza mu firgita bare har ta kai ga mun
yi saranda agaresa....."
kafin aljani mardis ya gama rufe bakin tuni
wannan aljani ya shammace sa ya mangare
sa ya da wannan katon hannun nashi.
duk da girma irin na aljani mardis sai da
yayi tsalle ya gwara kansa ajikin wata
bishiya.
ita kanta bishiyar tana kokarin karyewa.
da sauri aljani mardis ya shafa kansa ko da
yaga jini sai ransa ya baci.
kawai sai ya mike zumbur ya zare takobin
sa.
sannan ya dubi sauran dakarun aljanun
yace.
ku koma da baya na wannan fadan ba naku
ba ne.
shi kuwa wannan basamuden aljani sai ya
kara bushewa da dariya.
sannan yace.
ai na fada maka cewa nafi karfin ka baza ka
iya dani ba.
idan ka lura tun yanzu za ka gane nafi karfin
ka tun da gashi tun yanzu na fara kaika
kasa.
aljani mardis ya dakawa aljanin tsawa yace.
kai tafi can kayi amfani da dabara domin
kaga ka kai abokin gabar ka kasa.
ba wai karfin dantse ba.
ina so ka sani ni zan kashe ka da hannu na
duk girman nan naka.
idan kuma ka musanta bari ka gani!
kawai sai aljani mardis ya zare takobin sa.
ya falfala da gudu ya tunkari aljanin.
shi kuwa aljanin ya tsaya a in da yake yana
kallon aljani mardis yana jiran ya karaso.
adai dai lokacin ne aljani mardis yazo daf da
aljanin.
ko da aljanin yaga haka sai ya kara kawo
masa duka da wannan hannu nasa da nufin
ya karya masa kafadar sa.
cikin zafin nama aljani mardis ya sunkuya
ya kaucewa harin wannan aljani.
kafin aljani yayi yunkurin juyowa tuni aljani
mardis yayi sufa tare da zare takobin sa.
sai da ya iso dai dai kunnen aljanin.
sannan ya soka masa takobi akunnen shi na
hagu ya futo ta dama.
sannan ya zare takobin sa.
aljanin kuwa kamewa yayi tamkar gunki.
daga can kuma sai ya fadi kasa rikica kamar
katon tsauni har kura ta tashi.
ko motsi bai yi ba.
shi kuwa aljani mardis ya maida takobin sa
cikin kufe.
sannan yayi murmushi.
yace yanzu waye yaje kasa......

Comment and likes
BY ABBAS
WITH:- Shuraih 99%
ρðšтєđ by Shuraih 99%
νįά● Shuraih 99%
Fðя мðяє

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1
By ABBAS
With Shuraih 99%
Part 9
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
ya juyo ya dubi sauran dakarun aljanun
yace.
mu yi sauri mu bar wannan daji domin
zaman mu anan ba zai yiwu ba.
saboda sarki maharu zai din ga tura mana
mugayen aljanu wanda za su zama sanadin
ajalin mu ya zama dole muyi gaggawar
barin?
hakan kuwa suka yi cikin kadan suka bude
fukafukan su suka tashi sama suka luluka
acikin gajimare.
aljani mardis ne agaba suna zabga uban
gudu?
**al'amarin hujurul mahas kuwa.
lokacin da ya bace daga gidan majarul
daufus bai bayyana ako ina ba.
sai awani kyakkyawan daji mai cike da
ni'ima na kyawawa ciyayi masu dauke da
korayen ganye wanda ya karawa dajin kyau
sosai.
sa'annan kuma ga bishiyoyi gajeru masu
kyawawan launi wanda ka iya sa mutum
yaji tamkar ya kwanta asaman bishiyar.
hujurul mahas ya cigaba da karewa dajin
kallo yana murmushi.
yana cikin wannan kalle kallen ne ya hangi
wasu mutane guda biyu zaune agefen wata
bishiya.
cikin mamaki hujurul mahas ya kame awuri
daya.
ya cigaba kallon wadannan mutane.
to su wadannan halittu mutane ne kuwa.
saboda me za su zo wannan daji mai
matsanancin nisa da kuma wahalar hanya.
bisa ga dukkan alamu dai ko da kafa suka zo
saboda babu wani aljani agurin su wanda ya
dauko su don ya gajarce musu tafiya!
anya kuwa wadannan mutane ko dai wani
tarko suka dana saboda ni. bari dai in je
garesu don nasan ko su wanene.
ko da ya aiyana haka sai hujurul mahas ya
durfafi inda wadannan mutane suke.
ko da ya fara isowa daf dasu sai ya ga ashe
wadansu kyawawan mata ne guda biyu
suna cin tuffa.
suna hira.
hujurul mahas ya karasa kusa dasu duk da
haka basu san yazo ba.
sai da yayi magana yace.
barkanku dai!
firgigit suka dago da kai tare da dafa kirji.
suka fada a tare!
mutun ne kai ko aljan!
hujurul mahas yace.
ai ku ya kamata nayi wa wannan tambayar.
saboda ban kalla wanda zai shi cikin dajin
nan ba idan har bai cika hatsabibin jarumi
ba kuma sadaukin gaske.
ya ku wadannan kyawawan mata ina so ku
fada ko ku su wanene sannan kuma mai ya
kawo ku cikin wannan daji kuma ina zaku
tunkara?
ko da jin wannan tambayar sai wadannan
mata suka dubi junan su cikin mamaki
sannan dayar tace akan me za ka yi mana
wannan tambayar bayan bamu san ko kai
wanene ba.
hujurul mahas yace.
kun ga ni bani da niyyar cutar da ku ko
kadan don haka ku kwantar da hankalin ku
ku fada min ko ku su wanene.
ko da matan suka ji wannan maganar sai
suka kara duban junan su.
sannan suka fashe da kuka atare.
hujurul ya fara lallashin su yace.
ku dai na kuka mu shiru ku fada min
menene matsalar ko zan iya magance muku
ita.
daya daga cikin matan tayi shiru sannan ta
nutsu ta fara bayani...
mu matafiya ne mun futo daga birnin
zansar zuwa wani kauye domin ziyarar wasu
yan uwan mu acan kauyen.
bayan mun futo daga birnin zansar domin
muje wannan kauyen.
sai muka taka da kafar mu har zuwa bayan
gari in da zamu samu kwale kwale wanda zai
haurar da mu daga babban kogin dake
birnin zansar.
munsha wahala saboda nisa dake birnin
zansar zuwa tsallaken kogin.
ga abincin mu ya kare sannan kuma ga
yunwa ta addabe mu.
bayan mun tsallake wannan kogi sai muka
futo agalabaice.
muna haki.
ashe wadannan matuka jirgin barayi ne
bamu sani ba.
duk da cewa muna halin yunwa da gajiya.
sai da wadannan 'yan suka mana dukan
tsiya.
suka kwashe mana sauran kayan da muka
zo dasu suka tafi suka bar mu cikin
matsanan cin hali na rayuwa ko mutuwa.
kamar ba za mu rayu ba.
haka muka yi ta zama awannan wuri har
muka fara samun sauki.
ahaka ne mukayi ta yawo acikin daji har
mukazo wannan daji.
shi ne kazo ka same mu anan wurin....
lokacin da wannan kyakkyawar wannan
budurwa tazo nan alabarin ta.
sai hujurul mahas yaji tausayin su ya kama
shi.
ya dube su yace.
kar kudamu zan taimakeku na na saku
ahanyar da zaku je kauyen da kuke son
zuwa.
amma zan zauna daku anan har sai kun
samu hutu na tsawon kwana biyu.
yanda zaku je kauyen naku cikin kuzari da
kuma kuna jin kafin jikin ku.
ina fatan babu matsala
wannan shawara da nazo muku da ita.
'yan matan suka yi murmushi sannan suka
ce.
ai babu wata matsala don taimakon mu
kayi.
mun tabbata kaima kana jin yunwa.
kana bukatar kaci abinci.
don haka ga tuffa nan kaci don ka magance
yunwa.
hujurul mahas yayi murmushi yace.
ah da wuri haka.
to bari dai na ci.
kada kuce ban kyauta muku rashin cin abin
cin ku da nayi.
dayar budurwar tayi murmushi wanda ya
kara rikirkitar da hujurul mahas.
ai tuni ya manta da batun wata lushmat.
saboda daya kalli wadannan 'yan mata sai
ga ashe lusbmat mummuna ce.
budurwa ta dauko tuffa guda biyu tace.
gashi kaci don kayi maganin yunwa.
ta bashi tana murmushi.
shi ma yana mata murmushi.
zai kai tuffar bakin sa sai ya tsaya.
yana nazarin tuffar.
ko da 'yan mata suka ga haka sai dayar
tace.
ya naga ka tsaya.
kana tunanin ko zamu cutar da kai ne.
ai kawai kaci mu ba muda wata mummunar
manufa akanka.
hakanne yasa hujurul mahas ya manta da
komai .
ya kai tuffar bakin sa ya gutsura ya fara
taunawa.
sannan ya hadiye .
ya kara gutsura ya tauna ya hadiye.
sai da ya gama cinye tuffar duka sannan.
wadannan 'yan suka dubi junan su kawai
sai suka bushe da wata irin dariya.
al'amarin da razana hujurul mahas.
kawai sai yaji cikin shi ya murda ya fara yi
mishi ciwo.
Comment and likes
BY ABBAS
WITH:- Shuraih 99%
ρðšтєđ by Shuraih 99%
νįά● Shuraih 99%
Fðя мðяє

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1
By ABBAS
With Shuraih 99%
Part 10
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
sai yanzu ya tabbatar da cewa wadannan
'yan yaudarar shi suka.
domin yaci wannan abinci.
nan wadannan 'yan suka rikida izuwa wata
halitta.
sai gashi sun zama jibgan jibgan samudawa
masu girman jiki.
wanda idan suka kama mutum da hannun
take zai suburbushe komai jarumtakar shi.
nan samudawan suka kara bushewa dariya.
sannan suka murtuke fuskar su.
daya daga cikin samudawan ya dakawa
hujurul mahas tsawa wanda yake kwance
cikin shi yana murdawa.
yace.
kai yaro mun samu labari kana so kayi
kokarin raba sarki maharu da mashin sihiri.
tare da taimakon wani sarki da ake kira
majarul daufus.
to ina so kusani wannan buri dai dai yake
da tafiya neman jaki mai kaho.
sa'annan kuma gashi kayi biyu babu.
ba kada tsuntsu ba kada tarko.
saboda ayanzu take zamu mika ga sarkin
mu.
wato sarki maharu wanda yake so mu kaima
kashi araye.
kasani cewa ba kada mafita ko dabara.
idan mun kaiwa sarkin mu kai.
za mu je har gidan sarki majarul daufus shi
ma mu kamo shi mu gabatar dashi agaban
sarkin mu.
kuma ina mai tabbatar maka da cewa
matukar mu ka gurfanar da kai agaban
sarki.
to hukuncin kisa ya tabbata akanka.
saboda diyawa mutane ire iren ku sun
halaka bisa wannan buri nason suga sun
mallaki mashin sihiri......
hujurul mahas ya katsewa wannan
basamuden magana da cewa.
karya kake!
kawai sai yaji cikin sa ya kara yi masa ciwo
sosai.
nan da nan ya sume a wurin.
*** fada ce kasaitacciya mai cike da kayan
kawa iri iri gwanin ban sha'awa.
ga kilisai na alfarma shinfide acikin fadar.
ko ina ka duba acikin fadar lu'u lu'u ne
azube sai sheki da walwali yake.
ga kuma wasu kujeru masu laushi da
taushin gaske.
wanda saboda tsananin laushin su duk
wanda ya zauna akan kujerun take zai ji
barci yazo masa.
zaune akan daya kujerar sarki maharu ne.
ya sha ado irin nasu na sarakai.
sannan ya saka wata riga mai rintsin baki.
asaman bakin rigar ya sanya wata alkyabba
mai kyalkyali da daukar ido.
ahannun sa na dama ya rike mashin sihiri
wanda shima sai kyalkyali yake.
mashi ne wanda idan ka kalle shi take za
kaji ya burge ka saboda tsananin kyansa
kaji kamar ka dauke shi kayi tafiyar ka
dashi.
kayi amfani dashi wajen adon cikin gida.
awannan lokaci sarki maharu fuskarsa
amurtukr yana jiran zuwa wannan
samudawan da ya tura su kawo mishi
hajurul mahas wanda yake yunkurin raba
shi da mashin sihiri.
sannan kuma yasan matakin da zai dauka
akan aljani mardis"
agefe daya kuwa gimbiya salira itama tasha
ado na gaban kwatance da daukar ido"
gimbiya salira yarinya ce mai kaifin tunani
da basira da hangen nesa.
ba tada girman kai ko kadan ba ta damu da
abin duniya ba.
burin ta kawai shi ne.
taga ta faranta ran talakawa amma hakan
bazai yiwu ba.
domin mahaifin ta bazai daga yaga ta dauko
wata hanya wadda zata farantawa talakawa.
nan da nan sai ya taka mata birki.
hakan ne yake bakanta mata rai.
saboda babu yanda ta iya.
don haka mahaifinta ya zame mata ciwon
ido sai hakuri.
ahaka take nuna fara'arta agareshi.
suna zaman lumana.
domin duk da ta rasa mahaifiyar ta sai gashi
ya maye mata gurbin mahaifiya.
kuma tana alfahari da hakan saboda sarki
maharu yana nuna so da kauna agareta.
duk da bata son zalunci da yake gudanarwa
ga talakawa"
A daya gefen na kuwa fadawa ne sun kewa
shi ko wanne kan sa asunkuye ko wanne
yana dar dar don kada sarki ya fusata.
ya huce haushi akansu.
domin idan aka mata masa baya ji baya
gani.
don irin rashin mutuncin da zai kowa sai ya
shafe shi.
anan cikin wannan zaman ne afada sai
kwatsam aka ga fadawa suna budawa ana
ba da hanya.
sai ga wasu dakaru sun taso hujurul mahas
agaba.
an daure hannayen shi da kafafun sa acikin
sarka.
har sai da suka zo kusa da sarki sannan
suka tsaya
Comment and likes
BY ABBAS
WITH:- Shuraih 99%
ρðšтєđ by Shuraih 99%
νįά● Shuraih 99%
Fðя мðяє

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
MASHIN SIHIRI 1
By ABBAS
With Shuraih 99%
Part 11
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
su kuwa dakarun sai suka danna kafadar
hujurul mahas don ya durkusa bai yi
gardama ya durkusa ya sunkuyar da kan sa.
shi sarki maharu tashi yayi daga kan
kujerar ya fara kaikawo.
alokacin fadar tayi tsit ana sauraron
hukuncin da sarki zai yanke ga wannan mai
laifi.
lokaci guda.
sarki maharu ya tsaya da kaikawon da yake.
ya juyawa hujurul mahas baya fuskar sa
amurtuke"
affusace ya juyo.
ya dakawa hujurul mahas tsawa tare da
nuna shi da yatsa yace.
kai ragon maza.
kayi kuskure da har kayi gangancin
tunkarata don ka rabani da mashi sihiri.
sai kayi nadamar da baka taba yi ba
arayuwar ka.
da kai da wanda ya aiko ka.
sai kun shiga mummunar 'ukuba.
wanda zaku gwammace gara mutuwa da
rayuwa.
na yi alwashin duk wani mahalukin da yayin
yunkurin raba ni da wannan mashin sihiri.
to hukuncin kisa ya tabbata akan sa.
ko mutun ko aljani.
raba ni da wannan mashin sihiri.
ko sadaukan duniyar ne baza su iya ba.
ba shakkar duk wanda yayi kokarin raba ni
dashi.
zan halakashi ko shi wanene.
gashi yanzu kayi yunkurin zuwa har fada ta
domin kara ba ni mashin sihiri.
sannan akarshe ba ka cimma burin ka ba.
ba ka da mafita ka shigo hannuna.
zan sa akai ka dakin azaba.
in da na tanadi.
muggan aljanu.
da mugga dabbobin daji masu matukar
hadari.
da ma sauran abubuwa da za kayi karo dasu
idan har ka shiga wannan dakin azaba.
wanda idan an shige shi ba a fita araye.
shekara da shekaru duk wanda ya shigo
wannan dakin gawar sa baza ta futo ba.
sannan kuma zan sa ataho min da aljani
mardis shi ma ya bi bayan ka.
sai kuma mai baka shawarar kazo in da nake
wato majarul daufus.
shi ma sai na sa an kamo shi an saka shi
adakin da ba a fita araye......
Comment and likes
BY ABBAS
WITH:- Shuraih 99%
ρðšтєđ by Shuraih 99%
νįά● Shuraih 99%
Fðя мðяє

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%

ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99% MASHIN SIHIRI 1
By ABBAS
With Shuraih 99%
Part 12
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
sarki maharu yana gama fadar haka ya juyo
ya dubi sauran dakarun dake tsaye sun
sunkuyar da kan su.
yace.
kai ku dauke shi ku kai shi dakin azaba na
karkashin kasa.
sannan ku kwance sarkar dake hannun shi
da kafar shi.
kuma ku kwace takobin dake wurin sa.
ko dama ko kun bar shi da takobin babu
abinda zai iya yi a wannan dakin.
saboda jarumai

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment