Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aka fara gagarumin shagalin biki
Musamman ma cikin gidan sarautar inda anan ne akafi shagalin bikin
Inda jawwas da suraif suka fito suka caba ado na musamman, suka jero tareda amarensu suna tafiyar kasaita bayan kuwa fadawa ne suketa faman busa kakaki, da take musu baya
Koda jama'ar gari suka hango tahowarsu sai duk suka fara mika musu gaisuwa tareda kirari
Ba tareda bata lokaci ba aka fara gudanar da shagalin biki inda su sarki suraif suka fara rabe raben makudan kudade da tufafi na alfarma ga talakawansu
Inda a gefe guda kuma kuyangi ne suketa yawon raba abinci da abinsha ga mutanen dake
A tsakiyar fadar kuwa Wasu tsala tsalan 'yan mata ne cikin shigarar banza suketa tikar rawa, makada nayi musu busa da kida
Nanfa guri ya rincabe da jama'a kowa na farinciki, wasu kuwa tuni sun bugu sun fara layi saboda buguwar da sukayi da barasa
Su kuwa an gwaye da kansu ne suka dinga raba kyaututtuka ga talakawa nadaga kyautar dirhami da kayan sawa da abinci ga talakawa
Kai saboda farinciki a wannan rana sai ka kasa gane wanene angon
A wannan rana dai anyi gagarumin shagalin bikin da ba'a taba yin kamarsa ba Acikin birnin gaba
Inda aka daura auren attajiri jawwas da wata santaleliyar budurwa mai suna huraisa
Haka Shima sarki suraif aka daura aurensa da masruf 'ya a gurin daya Daga cikin hakimansa
Bayan an gama daurin aurene kowa ya watse saura angwaye kadai
Sannan ne sarki suraif ya shammaci matayen nasu ya dauko wata farar hoda daga aljihunsa ya hura musu ita afuska
Take hodar ta shiga cikin hancinsu ta ratsa ta cikin kwakwalwarsu
Wanda alokaci guda yanayin fuskokinsu suka caccanja cikin murmushi suraif yace ya kai aminina Yanzu lokaci yayi da zaka dauki matata kaje ka tara da ita na iya Wannan dare sannan nima na dauki taka
Kamar yadda boka hulbaz ya shaida mana, dajin wannan batu sai jawwas ya rikice ya kama inda inda ya rasa inda zaisa kansa
Yayinda sarki suraif ya lura da halindaya shiga sai kawai ya bushe da dariya daga can ya murtuke fuska yace
Haba abokina kai har yanzu baka gama sanin tuggun rayuwa ba , Shin kana tunanin zanyi abinda zai tona mana asirine?
Har abada asirin mu bazai taba tonuwa ba, domin a halin yanzu matayenmu duk basa cikin hayyacin su, ba zasu dawo ba har sai zuwa gobe
Kaga kenan Babu ta yadda zasu san da abinda muka aikata musu bare su zame mana matsala.
Don haka domin kawar da zargi yanzu kuyangi tareda dakaru zasu dauki amaren su kaisu gidajensu
Inyaso bayan tafiyar su kai sai ka sanya tufafina ajikinka nima kuma na sanya naka
Kai ka wuce dakin amaryata nima kuma na wuce dakin taka Inyaso idan dare ya raba kafin gari yayi haske sai kowa ya koma gidansa yanzu haka na sa, Yana gama fadin haka saiya tafa tafin hannayen sa
Faruwar hakan keda wuya sai ga wasu kuyangi guda dari sun shigo
Tareda dakaru dari suna shigowa sai suka raba kansu biyu dakaru hamsin, kuyangi hamsin suka Ware daban daban
Kaso daya suka tsaya a bayan masruf dayan kuwa suka koma baya huraisa suka tsaya
Ba tareda bata lokaci ba wasu dakarun suka shigo da kekunan doki guda biyu suka ajiye
Wasu kuyangin suka kama hannun amaren suka sanyasu acikin kekunan dawakan suka fice dasu daga cikin fadar , makada suna ta buga manyan ganguna, har suka kai kowacce daga cikinsu dakinta
Fitarsu keda wuya sai su jawwas suka shiga cikin wasu dakuna sukayi musanyen tufafin dake jikinsu sannan kowanne daga cikinsu yayi badda kama
Bayan tafiyar dakarun da sa'a guda sai suma suka fice daga cikin fadar kama hanyar tafiya ga matayen nasu
Kamar yadda suka tsara, kowa yajewa matar abokinsa
A wannan dare suka kwana adakunansu sannan a karshen dare kafin gari ya soma yin haske suka fice daga cikin dakunan
Kowa ya koma gidansa ba tareda wani ya ankara dasu ba suka koma dakunan
Matayensu na ainihi, har zuwa wannan lokaci Matan nasu basu dawo hayyacin su ba
Tun daga wannan rana sukaci gaba da rayuwa da matan nasu cikin kwanciyar hankali kuma a kullum babu abinda suke face tunani da nazari akan yadda zasu kare rayuwar 'ya'yansu daga sharrin boka hulbaz

Bayan auren nasu ne da wata guda alamomin samun juna biyu suka fara bayyana ga matayen nasu
Nanfa suka kamu da tsananin farinciki mara misaltuwa, don haka da kansa sarki suraif ya tako ya kawowa jawwas ziyarar bazata
Yana zuwa kuwa ya iskeshi an zube masa tarin abinci tarin abinci da abubuwan sha yana ci tare da matar sa cikin nishadi
Koda ya hango sarki suraif sai fuskarsa ta fadada da murmushi ya taso da sauri ya tareshi
Yace lale marhaban da zuwan babban abokina , na sani abindake tafe dakai shine irin yanayin da nima nake ciki yanzu,
Zoka zauna mu taya juna barka ba tareda bata lokaci ba ya sami guri ya zauna
Suka cigaba da cin abincin tare suna cin abincin suna hira cikin nishadi
Suna cikin cin abincin ne jawwas ya dubi huraisa yayi mata nuni da ta basu guri zasu tattauna
Ba tareda bata lokaci ba ta tashi ta fice daga turakar
Kawai ya dubi sarki suraif yace
Ya kai suraif kayi sani cewa daga yanzu zama agaremu ya kare dolene mu mike tsaye mu zage damtse da kyakykyawan tanadi tun kafin zuwan wadannan jarirai
Mu don haka ni yanzu na shirya shiga duniya domin haduwa da
Wasu manyan bokayen da suke nahiyoyi daban daban, kodajin wannan batu sai suraif ya tuna da maganganun da boka hulbaz ya fada
Kodayin wannan tunani sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi cikin sauri yace
Gaskiya mun tafka kuskure kuma munyi ganganci da sakaci akan wannan lamari
Maganarka gaskiyace ya zama dole mu tashi ayanzu mu tafi cika wannan aiki.
Ba tareda bata lokaci ba suka tashi duk su biyun sukayi sallama da matayensu , suraif kuwa ya bada ajiyar karagarsa a gurin matarsa
Sannan suka fice daga cikin garin,
Tundaga ranar da suka fita suka fara ziyartar manyan bokaye daban daban suna neman sirrikan tsafi daga nahiyoyin dake makobtaka har saida
Suka shafe wata takwas suna zagaye kasashen duniya da duk inda suka sami labarin wani babban bokan
Yayinda akan hanyar su kuwa suka dinga haduwa da manyan dabbobin daji, 'yan fashi da sauransu
Amma da karfin tsiya suraif da hadiminsa suke tarwatsasu
Su budawa kansu hanya
A sannan ne jawwas yayi nadamar kasancewarsa ba mayaki ba domin dashi kadai ne babu makawa ba zai iya tseratar da rayuwarsa ba
Acikin wata na tara ne suka dawo daga tafiyar tasu cikin sululalun dare alokacin garin yayi tsit babu sautin da kakeji face na karnuka sai kuma dakarun da suke gadi
Basu sauka ako'ina ba sai tsakiyar birnin, sautin kada fuka fukan aljanin saida ta haddasa wata 'yar karamar guguwa
Wacce karfintane ya fargar da dakaru zuwansu
Cikin sauri dakaru sukazo cikin girmamawa suka tarbesu suka rakasu har gidajensu ba tareda sauran jama'a sun ankara ba
Yayinda jawwas ya isa gida acikin wannan dare kwatsam saiya iske matarsa tana nakuda
Koda ganin haka sai hankalinsa ya tashi cikin sauri ya tura dakaru suka kirawo masa wata babbar ungozoma Domin tarbar haihuwar
Da zuwan ungozoman cikin sauri ta sanya aka kawo mata kayan aiki sannan taja dakin ta rufe
Kafin cikar sa'o'i biyu tuni ta haifi santala santalan jarirai guda biyu
Koda akazo aka sanar dashi wannan haihuwar take ya kamu da tsananin farinciki ba shiri yaja ungozoman cikin baitul malinsa
Yace daga yanzu zuwa wayewar gari na baki duk dukiyar da kika diba acikin dakin nan Domin yau burina ya gama ciki
Yana gama fadin haka saiya koma inda huraisa take wacce tuni angyarata cikin koshin lafiya
Su kuwa jariran tuni anyi musu wanka Sannan an yanke musu cibiya, har an sanya musu tufafi na alfarma
Take ya debi jariran guda biyu yana kwallar farinciki wacce bata taba zuba daga idanunsa ba.
Itakuwa ungozoma ba shiri ta fita acikin murna ta samo hayar rakuma ta dawo ta dinga jidar darhami har zuwa wayewar gari bata debi Koda kaso daya bisa goma ba
Kashe gari kuwa da sassafe haka ya fito da tarin dukiya ya dinga yana rabawa sadaka ga mabukata
Tun suna zuwa karba har saida Suka gaji suka daina zuwa , bayan fitowar ranane ya dauki jariran ya hau keken doki
Ya tafi gidan sarauta domin yayiwa sarki albishir
Koda isarsa saiya iske shima sarki suraif masruf ta haifi 'ya mace
Ba tareda bata lokaci ba suka hadu su biyun suna taya juna murna
'Yan majalisu da dakaru sai zuwa suke suna kawo gaisuwa da taya murna, suna cikin wannan yanayi ne
kwatsam sai suka ga gaba daya fadar tayi duhu kai kace dare ne ya raba
Nanfa guri yayi tsit kai kace babu wata halitta mai numfashi a gurin
Da ganin wannan bakon yanayi take kowa ya shiga taitayinsa dakaru suka fara zare makamai
Jim kadan sai duhun gaba daya ya yaye komai ya koma yadda yake a baya
Adaidai lokacinne wani bakon boka ya bayyana wanda akalla shekarunsa sun haura casa'in da doriya
Saboda tsananin tsufan da yayi har doron bayansa ya fara durkufawa, gashin kansa kuwa gaba daya fari ne babu digon baki ajikinsa
Hannunsa na hagu yana ruke da wata sandar tsafi wacce yake dogarawa da ita
Kai da ganinsa kasan irin boyayyun bokayen nan ne wadanda suka jima sunayiwa kansu tanadi
Koda dakaru sukayi arba da wannan bakon bokan sai gaba dayansu sukayi kukan kura suka afka masa da nufin suyi gunduwa da sassan jikinsa
Ba tareda bokan yayi wani yunkuri ba koda ya rage baifi saura taku daya ba a tsakaninsu
Sai kawai wata iskar tsafi mai karfi tazo ta zukesu ta watsa su wajen fadar sannan kofofin gaba daya suka rufe kansu
Da ganin abindaya faru ga wadannan dakaru sai zuciyar sarki suraif ta fara tafarfasa take yayi kukan kura
Tare da zare takobin sa ya afka kan sa da nufin yayi masa zuwa daya
Yana zuwa daidai inda yake sai Yakai masa mummunan sara a dokin wuya da nufin ya tsarge wuyan Daga jikinsa
Koda takobin ta sauka ajikinsa take ta ratsa shi ta wuce kai kace haske ya sara ba tareda ya sami ko kwarzane ba a jikinsa
Cikin zafin nama ya dunkule Hannunsa taredav kara kai masa wani dukan a gefen muka mukinsa
Koda Hannunsa ya sauka ajikinsa sai yaji kamar an kwarara masa tafasasshen karfe akan hannun nasa
Don haka Baisan sanda yaja da baya ba, ya koma amfani da sihirin tsafin sa
Amma sai shima sihirin yaki yayi tasiri akan wannan bakon bokan
Bisa mamaki sai yaji bokan ya tuntsure da dariya cikin wani irin sauti mai amsa amo
Sannan ya fara bayani kamar haka
Haba Yakai wannan jarumin sarki ni banzo gareku da zummar yaki bane kawai nazo ne
Da nufin taimakonku akan kudurin daya fitar daku daga birnin
Nasan da cewa kun fita kun zagaye duniya inda kuka ziyarci bokaye dari da sittin da biyu
Da nufin baiwa jariran ku kariya da kuma sa'a abisa abokin hamayyarsu wanda kuma shine silar zuwansu duniya wato boka hulbaz
Har su rigashi mallakar KARAGAR AJALI da kuma SAIFUL LAIHAM
Ku sani cewa hakika a halin yanzu yayi mummunan tanadi akan wadannan jarirai wanda idan har ba'a dauki kyakykyawan mataki ba
To da zuwansu duniya da kuma wahalar da kuma kukasha akansu duk zasu zama na banza
Dajin wannan batu sai jikin suraif yayi sanyi ya mayar da takobin sa cikin kube
Yayiwa bokan nuni da wata kujera daya zauna akanta
Maimakon bokan yaje inda kujerar take sai suka kujerar ta babbako daga mazauninta ta dawo inda yake tsaye ya zauna akanta
Zamansa keda wuya sai suma suma sami guri suka zauna , jawwas yayi gyaran murya daga bisani yace dashi Yakai wannan boka
Shin wanene kai kuma menene ke tafe dakai?
Dajin wannan tambaya sai yayi murmushi yace da farko dai sunana
Hushairul hasnal kuma ni mahaifine ga boka hulbaz,
Yaku wadannan manyan mutane ku sani cewa
Inbanda na fito daga inda nake zaune nazo nan inda kuke Yanzu haka shekarata hamsin da biyar acikin kogon tsafina ba tareda na fito waje ko kuma mutane su san ina rayeba

Tsawon wadannan shekaru babu abinda nakeyi face bincike akan wata karaga wacce akewa lakabi da KARAGAR AJALI tare da lokacin bayyanar ta, Kai harma da wanda zai iya mallakarta kuma yayi amfani da karfin sihirinta
Amma har kawo yanzu babu wanda yasan inda take kai a wannan lokacin ma kaf duniya Babu wanda yasan labarin ta face ni kadai
Sai aranar dana sanar da dana wato boka hulbaz a wannan lokaci bai wuce shekara bakwai ba
Sai bayan na sanar dashi labarinsu ne nadama tazo min domin Nasan dolene yayi kokarin mallakarsu kota wanne hali
Idan kuwa har ya mallakesu to babu makawa sai yayi amfani dasu wajen bautar da duk wasu halittu na duniya Saboda zallan rashin imaninsa
Tun daga ranar dayasan labarin wadannan abubuwa shima saiya dukufa kan tanadin hanyoyin da zaibi domin mallakarsu
Ana zaune wata rana sai na wayi gari hulbaz ya gudu yabar gida
Tun daga wannan lokaci ban sake haduwa dashi ba, saidai bincike ya nuna min cewa yanzu haka ya mallaki sihirin tsafi mai karfin gaske
Kuma har yaje inda ake tsammanin za'a haifi jaririyar da zata zama silar bayyanar karagar AJALI
,
Kuyi sani cewa yanzu haka duniya bata Farga da wadannan abubuwa ba
Domin babu wanda yasan da batun su face ni sai hulbaz da kuma ku dinnan
Bayan haka inaso ku sani yanzu haka hulbaz yayi gagarumin shiri akan jariranku
Saidai shirin ba zai fara tasiri ba sai nan da Wasu 'yan shekaru masu zuwa,
Kuma ba komai ne zai fara tashinsa ba face mace, babu irin binciken da banyiba Domin in gano wacece ita ba amma na kasa
A wannan lokaci gaba dayansu kawunansu zasu rarrabu ya zamana kullum suna farautar juna kamar rana da wata
Dare da rana
Kowanne kuma daga cikinsu zai dinga fada da dan uwansa ne akan yakinin cewa shine mai gaskiya
Kai hatta ku ba zaku iya banbance waye mai gaskiyaba acikinsu daga karshe dai idan har da rabo dole daya Daga cikin sune zai iya mallakar KARAGAR AJALI
Kuma a sannan ne daya Daga cikin su zai rasa rayuwarsa,
To a wannan lokacin zasu gane kuskuren da suke aikatawa har ma suyi nadama
Babu kalar binciken da banyiba Domin gano wanda zai yi nasara , da kuma wanda zai mutu acikin su amma Abu ya gagara
Don haka ya zama tilas mu tsaresu daga hulda da mata har zuwa sanda zasu gama mallakar hankalin kansu
Idan kuwa har anaso su taso da gagarumin tsaro da karfin sihiri
Dolene daga wannan rana a sanyasu acikin kwalaben sihiri na tsawon shekaru shida da wata tara
A sannan ne zasu fito da gagarumin sihirin tsafi na ban al'ajabi kuma zasu fito da kwarin jiki kamar 'yan shekara sha hudu
Daga ranar da suka fito kuma sai a mikasu inda zasu koyi dabarun yaki na musamman
Kodajin wannan batu sai sukayi shiru suka fara kallon juna ba tareda sanin hukuncin daya kamata su yanke ba.

SHIN SUNA AMINCEWA DA SHAWARAR BOKA HUSHAIRUL HASNAL?
TAYAYA MACE ZATA IYA SHIGA TSAKANINSU KUMA WACECE ITA?
SANNAN DAGA INA TAKE?
WANENE ZAI SAMI NASARAR MALLAKAR KARAGAR AJALI ACIKIN SU?

DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MUN HADU A KASHI NA GABA DAGA NAKU
HABIBULLAH KBRKARAGAR AJALI
4***********
PART ********C

LBR

***********HABIBULLAH KBR

Daga can sai sarki suraif yace Yakai wannan boka to kai menene ribarka idan har ka taimaka mana?
Dajin wannan tambaya sai ya ajiye gwauron numfashi sannan yace ni acikin wannan abu babu abinda zai amfaneni
Saidai ina da burin ganin mamallakin wannan karaga da saiful laiham da idanuna kafin ajali ya riske ni
Idan kuwa har kukayi sakaci ina tabbatar muku da cewa duk wahalar da kukasha ta zama ta banza, don haka ina sauraron hukuncin da zaku yanke
Koda yazo daidai nan azancensa sai ya dakata da maganar da yakeyi ya zuba musu idanu
Ba tareda bata lokaci ba jawwas ya janyo suraif gefe yace Yakai abokina ka sani a halin yanzu bamu da zabin daya wuce amincewa da wannan boka domin a bokayen da muka ziyarta babu wanda yayi mana irin cikakken bayanin da shi yayi mana , don haka nidai na amince dashi dari bisa dari,
Dajin wannan batu sai shima ya gyada kansa yace ainima babu abinda zanyi a yanzu sai yadda kayi don haka na amince
Suna gama wannan tattaunawar sai suka dawo inda boka Hushairul hasnal yake sukace sun amince
Koda jin amincewarsu sai ya ya kama hannayensu tareda karanta wasu dalasiman tsafi
Faruwar hakan keda wuya take sai dukkaninsu suka bace bat daga cikin fadar
Basu bayyana ako'ina ba sai cikin kogon tsafin boka Hushairul hasnal wanda ke can kusa da birnin Hindu
Da bayyanarsu sai su jawwas suka yi arba da wasu manyan kwalabe guda hudu acikin fadar wacce wani shudin ruwa yake sauka akansu duk bayan dakika goma da zarar ruwan ya sauka akansu sai kwalaben suyi wani irin kara mai kama da an zuba ruwa acikin tafasasshen mai
Kodaya lura da irin kallon da suke yiwa kwalaben sai ya dafa kafadunsu yace ku kwantar da hankalinku
Wannan ruwa ba mai cutarwa bane agaresu, Bane komai bane face mai amfani agaresu
Yana gama fadin haka saiya nuna kwalaben da Hannunsa take duk kwalaben guda uku suka bude kansu,
Sannan jariran suka fice daga hannunsu da kansu suka shiga cikin kwalaben Faruwar hakan keda wuya sai akwatunan suka sake rufe kansu ruf tamkar basu taba wanzuwa ba
Boka Hushairul hasnal ya sake duban sarki suraif yace Yakai wannan sarki ina bakin cikin sanar dakai cewa daga yanzu ba zaka sake samun haihuwa ba har abada ,
Kai kuwa jauwas nan da wata uku matarka zata sake samun wani juna biyun wanda zata haifi da namiji
Wanda daga shi ba zata sake haihuwa ba
Don haka a daidai wannan lokaci kafin ta fara da samun cikin zan tura daya Daga cikin hadimai na
Ya sato min dan tayin dake cikinta a sanyashi. Acikin waccan kwalbar da tayi ragowa
Ta yadda za'a kyankyashe shi tareda 'yan uwansa kuma su fito duniya tare
Don haka a halin yanzu zamu rabu daku ku koma gidajenku ina mai umartarku daku rarrashi matayenku
Domin Nasan irin ciwon da zasu ji na rashin 'ya'yansu, amma karku sanar dasu inda suke domin hankalinsu ba zai kwanta ba
Ku kuwa na baku dama a duk lokacin da kuke son ganin su zaku iya zuwa nan da zarar kun kira sunana
Amma kafin ku tafi ku fara radawa 'ya 'yanku suna wanda zasu tashi dashi yayin girmansu
Dajin wannan batu sai fuskokinsu suka kama murmushi
Sukaji damuwarsu da fargabarsu sun ragu acikin zukatansu
Don haka caraf sai suraif yace ni na sanyawa 'yata suna HUSNAILA
nan take shima jauwas ya sanya wa nasa suna SAFRAN da MUFRAN
Sannan yayi shiru Yana tunanin sunan da zai sanyawa na karshen …
Kafin ya bude baki ya fadi sunansa take suka ga wata walkiya ta haska cikin kogon wacce saboda karfin ta saida suka rufe idanuwansu
Koda budewarsu sai suka ga Ajikin kwalbar Da babu komai acikinta anyi rubutu kamar haka FARHAN !!
Ragowar kwalaben kuwa an rubuta sunaye kamar yadda suka fada
Da ganin wannan rubutu sai boka Hushairul hasnal ya dubeshi cikin al'ajabi yace
To ka gani da idonka Tunda kai ka kasa zabar masa suna to abin bauta ya zabar masa
Anan zamu rabu daku sai mun sake haduwa agaba
Yana gama fadin haka take su sarki suraif suka bace daga cikin kogon nasa basu bayyana ako'ina ba sai cikin fada
Har zuwa lokacin da suka dawo dakaru basu iya bude kofar fadar ba bare su shigo ciki
Tun daga wannan rana akaci gaba da renonsu Husnaila acikin kwalaben sihiri Ana kara tsamasu da sirrikan tsafi har zuwa wata uku sannan kamar yadda Hushairul hasnal ya fada
Saidaya aika da hadiminsa yaje ya ciro dan tayin dake cikin huraisa
Aka ajiyeshi acikin wannan ragowar kwalba, tare da renonsa tareda sauran 'yan uwansa
Sannan akai akai mahaifansu suna zuwa ziyartarsu
Kwanci tashi saida suka shekara shida da watanni tara Acikin wadannan kwalabe
Aranar da suka cika wata tarane tun da duku dukun safiya su sarki suraif suka bayyana acikin kogon tsafin nasa

Saidai a wannan rana Basu ga boka Hushairul hasnal ba amma kuma ga kwalaben nan a jiye kamar yadda suke

Saidai acikin kwalaben cike suke da wani hayaki wanda ya hana idanuwansu kallon abinda yake ciki
Nanfa zuciyarsu ta buga da karfi suka fara tunanin anya kuwa boka Hushairul hasnal ba amanarsu yaci ba ?
Cikin tsoro da fargaba jawwas yaje kusa da kwalaben ya mika hannunsa da nufin tabawa

Kwatsam sai yaji boka Hushairul hasnal ya daka musu tsawa
Wacce saboda karfin ta saida yaji zuciyarsa ta buga da karfi bai san sanda yaja da baya ba da sauri
Kawai sai suka hangi boka Hushairul hasnal hasnal ya taho inda suke fuskarsa cike da damuwa kamar wanda akayiwa albishir da ranar mutuwarsa
Yana dogarawa da sandar tsafinsa, koda ya iso inda suke sai yace lale marhaban da zuwan
Kuyi hakuri Nasan kunyi jirana kuma harkun kosa da jirana
Ba komai ne yasa kukaga bana nan ba face halwar tsafin dana shiga akansu farhan
Wannan kuma hayaki da kuka gani bana komai bane face sirrikan tsafina wanda na zuba ajikinsu gaba daya
A halin yanzu babu wani sihiri da yayi saura ajikina duk na mai dashi jikinsu
Ba don komai ba sai don ina da tabbacin anan gaba zasu baiwa tsafi kariya daga azzalumai masu burin tarwatsa duniya dashi
A halin yanzu akwai wani hadimin aljanina da zai dauke su ya wuce dasu makarantar da zasu Kuyi yaki
Ina mai tabbatar muku da cewa Koda basu mallaki karagar AJALI ba sunansu zai bazu a duniya yadda baza'a manta dasu ba
Saidai alokacin da zasu sami wannan nasarar bai zama lallai ina raye ba
Abu daya Kawai nake shakka, wannan abu kuwa ba Komai bane face tuggun da dana hulbaz yake shiryawa a yanzu
Domin ni kaina ina shakkarsa duk da cewa ni na haifeshi amma ance mai laya ya kiyayi mai zamani
Da gama fadin haka ya takarkare cikin daga murya ya karanto wasu dalasiman tsafi
Faruwar hakan keda wuya sai kwalaben suka fara tsatstsagewa tare da kumbura wani sauti Yana fita daga jikinsu
Daga can sai sukayi bindiga suka tarwatse gaba daya, sai ga su farhan sun fito daga cikinsu tsirara ko tufafi babu ajikinsu
Sannan Hushairul hasnal ya mika musu tufafi suka sanya ajikinsu
Abin wani abin mamakin ma shine safran da mufran kai harma da Husnaila duk yanayin jikinsu daya
Ma'ana girda girdane masu girman kirar jiki, saidai kuma farhan siffarsa ta fita daban da tasu
Bai karasa su a girma da kaurin jiki ba amma kuma gabaki dayansu babu sa'ansa a fagen kyau
Sannan yana da kirar jarumai kamar su
Suna fitowa sai suka raba idanu suka rasa gurin wanda ya kamata suje Tsakanin boka Hushairul hasnal da iyayensu
Da ganin haka sai Hushairul hasnal yace dasu me kuke jira ne ai sai kuje gurin iyayenku
Dajin haka sai suka ruga da gudu gun iyayen nasu kuma kowa sai yaje gurin mahaifinsa na zahiri ba tareda kuskure ba
Nanfa su jawwas suka rungumesu tareda hawayen farin ciki sakamakon ganin 'ya'yansu lafiyayyu
Kafin ajali ya riske su bayan sun dan tattauna sai suraif yace da Hushairul hasnal
Yakai wannan boka muna godiya da duk taimakon da kayi mana
Amma ka sani na dade da yiwa kaina alkawarin nine mutum na farko da zan fara baiwa su safran horon yaki
Zanso ka bani damar zama dasu domin na cika alkawarin dana daukarwa kaina ko kuma na kasance taredasu a inda zasu karbi horon yaki
Dajin wannan batu sai Hushairul hasnal yayi guntun murmushi daga bisani yace ai Wannan ba matsala bace daga wannan aiki ni zan fita daga sabgar su Domin na gama aikina
Don haka kaima zaka iya kasancewa taredasu har ma ka basu horon yakin da kake dashi yayinda kuka isa can,
Idan kun shirya yanzu hadimin aljanina zaizo ya daukeku gaba daya zuwa can
Da gama fadin haka saiya karanta wasu dalasiman tsafi ya tofa a kan kasa
Faruwar hakan keda wuya sai kasa ta fara girgiza wani bakin hadari ya tokare sararin samaniya kafin cikar dakika goma take suka ga wani shirgegen aljani ya ratso saman rufin kogon ya shigo ciki
A ka'ida girman kogon yayiwa Koda fuka fukin aljanin guda daya kankantar da ba zai iya sakewa acikinsa ba
Amma Koda saukar sa aciki sai suka ga kogon ya kara girma da fadi ninkin ba ninkin din nada har saida aljanin ya zamo dan mitsitsi acikinsa
Koda bayyanarsa sai yayi sujjada ga Hushairul hasnal sannan dube shi cikin kakkausar murya yace ya shugabana kai kuwa yau wacce irin bukatace dakai wacce har tasa ka nemeni alhalin rabonka da nema na yau shekara hamsin da biyar kenan lokacin da mukaje yaki duniyar fatalwa?
Yanzu kuwa har girma ya kamaka kuma karfinka ya ragu fiye dana
baya na tabbata ba zaka iya jarumtakar da kayi ba a lokacin
Dajin wannan batu sai ya tuntsure da dariya dariya sannan ya dubi aljanin yace
Yakai AMSADUS RAS ka sani cewa ko kura ta fadi tafi karfin wasan yara , kuma komai lalacewar tsohon zaki yafi saurayin kare
Ka sani cewa duk da na

Please Login or Register in order to submit comment