Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

HIKAYAR SARAUNIYAR KYAU LASMIRA

Sannan littafin ya bude da kansa shafi na farko
Take lardisa ta gyara zamanta sannan ta fara karatu kamar haka

+++++++ +++++++++ +++++++

A wani zamani can baya mai tsawo kimanin shekaru dubu uku da doriya da suka gabata alokacin da karfin dantse dana sihiri suka zama jari
Awannan zamani tun kafin KARAGAR AJALI ta bayyana acikin wannan duniyar tamu
Anyi wata hamshakiyar sarauniya wacce tun farkon kafuwar duniya ba'a taba samun wacce ta kama koda kwatankwacin kafarta a bangaren kyau ba
Masana da masu bincike sun bayyana cewa kyawunta ba iya mutane kadai yake rudawa ba harda ma jinsin aljanu
Domin akullum jayayya ake kowanne bangare nacewa tasu ce
Wanda hakan ya jawo kullum cikin farautar juna suke babu dare bare rana don mallakarta
Mayaka, jarumai, matsafa da sarakuna da yawa sun rasa rayukansu adalilin burin mallakar wannan kyakykyawar sarauniya
Kai Bama maza kadai ba hatta 'yan uwanta mata kishi suke da ita har fata suke da ace sun kasance mazaje to tabbas zasu iya sadaukar da rayuwarsu Domin mallakarta
Matan da suka kasance kyawawa kuwa sai kyawun nasu ya dinga zama gori da yiwa dariya gami da tsokana agaresu badon komai ba sai don basu kama koda kafar lasmira ba a bangaren kyau, Kai har wadanda ba kyawawanba sai suka dinga finsu kwanciyar hankali da walwala acikin mutane
Bisa dole suka dinga boye fuskokinsu da kyalle Domin kare martabarsu
Kai a takaice dai akazo Ana maganar kyau to da zarar an ambaci sunan lasmira tofa zance ya kare,
Duk irin wannan daukaka data samu ita a gareta basu kara mata komai ba face tashin hankali da nadamar kasancewarta a matsayin da take kai,
Ba don komai ba sai don yadda kullum dare da rana babu abinda akeyi face farautar ranta tun tana jaririya har zuwa sanda ta tsinci kanta acikin wata kebantacciyar masarauta wacce a wannan karni babu wani guri mai tsaro kamarta

Itadai wannan masarauta Ana kiranta ne da RUGTARUL BARZAK
Masana bincike akan duniyoyi na wannan zamani sunyi ittifakin cewa kaf cikin duniyoyin da ake dasu babu duniya da take da guri mafi tsaro face masarautar RUGTARUL BARZAK
Ita dai wannan masarauta ba akan doron kasa take ba kuma tana da manya manyan fadoji masu girma da tsananin guda goma sha biyu
Wanda ba'a taba samun mahalukin daya taba koda ketare mataki na farko ba bare ya isa na biyun
Ba don komai ba face tsananin dakarun tsaron da aka zuba aciki
Na jinsin sihirtattun bakaken aljanu, maridai da dodanni na musamman masu hatsarin gaske
Ko ina an zubasu burjik tareda manyan tarkuna masu yawan gaske akan hanyar zuwanta
Tsakanin kowacce Fada zuwa 'yar uwarta akwai matattakalu guda dari biyar
Kuma kowacce matattakala dakaru dubu ne suke gadinta wasu akan kasa wasu a saman iska wasu kuwa ta karkashin kasa
Ta yadda ko sauro bai isa ya gifta ta gaban su ba tareda sun ankara dashi ba
Kuma kullum sai an debesu an zurasu acikin wasu kwalaben tsafi an kara tsamasu da sirrikan tsafi wanda zai dinga kara musu karfi da kuzari

Wasu daga cikinsu kuwa an kirkiresu ne da garwashin wuta, wasu kuma kankara haske da sauransu
Da ace za dauko jinsi hudu daga cikinsu a zurosu cikin wannan duniyar zasu iya gamawa da ita cikin abinda bai wuce yini guda ba
Komai hatsabibancin mutum ko aljan da karfin sihirinsa bai isa ya iya ratsawa koda kofa guda daya ba
Ba tareda sun san da zuwansa ba
Manyan jarumai, sarakuna da bokaye da dama sun rasa rayukansu adalilin kokarin shiga wannan masarauta amma sun kasa hatta gawarwakinsu ma basu dawo ba
Gaba daya wannan duniyar tana karkashin sarrafawar wani takadirin aljani ne wanda ake wa lakabi da Hubbas bin mufras
Wanda agaba daya bokayen wannan zamani ba'a sami wanda yake da rabin karfin sihirinsa
Kuma ba don komai ya kirkiri wannan masarauta ba sai Domin ta zama babbar ma'adanar kayan tarihi wacce ba'a taba samun kamarta
Masana sun tabbatar da cewa duk wanda ya sami nasarar shiga wannan masarauta kuma har ya fito araye tabbas zai sami daukakar da babu wanda ya taba samun kamarta
Kuma tarihi ba zai taba mantawa dashi ba har zuwa karshen duniya
Babu komai acikin wannan masarauta face tarin kayan yaki kala daban daban wanda mazan jiya suka yi amfani dashi haka kuma ga tarin dukiya wacce inda za'a tara gaba daya mutanen duniya ba zasu iya karar da ita ba tsawon shekaru goma
Bayan haka duk wani kalar sihirin tsafin da mutum yake takama dashi Idan ya shiga wannan guri sai ya zama jahili Domin hatta littafin farko da aka fara rubuta kundun tsatsuba ajiki yana
yana boyene acikin wannan masarauta

Acikin Fada ta goma sha daya ne boka Hubbas ya boye sarauniya lasmira Bisa acikin wata kebantacciyar Fada wacce akewa lakabi da aljannar duniya
Bisa tsaron dakarun sa wadanda suka fita daban da saura wajen karbar horo
Sai kuma wasu kuyanginta na musamman da suke kula da duk wasu bukatunta
Tun lasmira tana karama 'yar shekaru shida boka Hubbas ya tura aka sato masa ita
Kuma tun a ranar da aka kawo masa itane ya dauketa da kansa ya tsomata acikin wani tsumin tsafi
Domin yasa ta tayi tsawon shekaru kamar yadda jinsin aljanu sukeyi
matukar tana cikin wannan Fada zata iyayin shekaru dubunnai ba tareda ta mutu ba
Tare kuma mantawa da duk wani Abu wanda ya faru da ita a baya
Tun daga wannan lokaci ne ta manta da duk abubuwanda suka faru da ita abaya harda iyayenta da sauran danginta
Wannan daliline yasa gaba daya bata San meye soyayya ba
Haka Kuma bata San meye da namiji ba
Har ta cika cikakkiyar budurwa a wannan lokacine kyawunta ya gama bayyana fiye da baya
Wanda su kansu hadiman da suke kula da ita har rikicewa suke yayin kallon ta
Shi kansa boka Hubbas yakanji wani lokacin kamar ya kusanceta amma da zarar ya tuna da wani sirri
Bisa dole yake janye mummunan kudurinsa akanta

A kullum sai boka Hubbas yasa wasu likitoci sun binciki lafiyarta don kar ta kamu da wani ciwon da zai illata ta

Acikin daki Na karshe kuwa anan ne aka adana KARAGAR AJALI tare da takobin SAIFUL LAIHAM

Wadanda aka kerasu da dutsen lu'u lu'u da zinare
Andora ita saiful laiham din Akanta sai kyalli da walwali suke wanda kan iya kashewa mai kallo idanu
agaba daya wannan fadar babu badakare ko guda daya saboda shi da kansa boka Hubbas ke gadinsu saboda mahimmancinsu
Tsawon shekaru dubunnai ko kura bata taba sauka akansu ba saboda karfin sihirin dake tattare dasu
A duk bayan mako guda sai duk hadiman da suke cikin wannan masarauta sun tattare kansu acikin wannan daki Na karshe Domin yin bauta ga karagar AJALI bisa jagorancin boka Hubbas
Dukkansu sunyi Imani cewa itace ke kula da duk duniyoyin sama da kasa da kuma basu kariya
Don haka a duk bayan shekara guda boka Hubbas yana tura wakilansa sauran duniyoyin Domin su kawo masa fursinoni guda dari uku Domin shayar da jininsu ga karagar AJALI.

Wata rana sarauniya lasmira na kwance acikin turakarta tana sharara barci sai kawai tayi mafarki da wani kyakykyawan saurayi sanye da kayan yaki masu kwarjini ya bayyana acikin wannan duniyar
Kuma har ya shigo cikin gidan sarautar yana ratsawa ta cikin matakan tsaron gidan da karfin tsiya
Ya iso har cikin turakar tata ya dauketa sannan ya wuce inda KARAGAR AJALI DA SAIFUL LAIHAM SUKE
Ya daukesu sun gudu
Koda tazo daidainan amafarkinta saita farka a firgice tana mai gyara zamanta
Nanfa ta fara tunani acikin zuciyarta cewa
Shin dama akwai wata halitta mai shigen irin yanayin jikina?
Idan kuwa akwaisu to a wacce duniyar suke?
Amsar data kasa baiwa kanta kenan,
Kawai sai tayi gyaran murya take wasu kuyanginta suka bayyana
Cikin izza ta dubesu tace inaso yanzu yanzu ku kawo min allon zane tareda tauwada da alkalami
Dajin wannan tambaya duk sai sukayi jugum suna kallon ta cike da mamaki tareda cewa ya shugabar mu ke kuwa yau me zakiyi da wadannan abubuwa?
Kodajin wannan tambaya sai ta daka musu tsawa tace umarni na baku ba taimako na nema ba
Idan kuwa kukaki yanzu fushina zai sauka akanku
Cikin rawar jiki sukace kiyi hakuri ya shugabar mu take suka bace daga turakar tata
Jim kadan sai gasu sun dawo da abubuwan data bukata sun ajiye agabanta sannan suka kara bacewa
Ba tareda bata lokaci ba ta dauki wannan alkalamin tareda dangwalar wannan tauwadar ta fara zana siffar wannan matashin saurayi data gani acikin mafarkinta
A hankali har sai data gama zanashi gaba daya kai kace shine a tsaye a gabanta
Koda ta gama zana wannan bakon Sadauki sai taji zuciyarta ta buga da karfi
Atake taji kwakwalwarta ta fara juyawa tareda wasu irin tunane tunane kamar mai shirin haukacewa
Abu na farko daya fara zuwar mata shine anya kuwa bata taba haduwa da wannan saurayi ba abaya ?
Idan kuwa harta taba haduwa dashi to hakan yana nufin ta taba rayuwa a wata duniyar daban cikin jinsin halittu irinta
Daga bayane aka kawota wannan guri,
Duk yadda akayi kuma akwai alaka mai karfi Tsakanin ta dashi
Abu na biyu kuwa shine ina iyayenta suke a halin yanzu wanne irin hali suke ciki na rashinta?

Koda gama wannan tunani sai ta kwarara uban ihu wanda ya ratsa Gaba daya turakar tata
Ba shiri dakaru suka dinga rugowa a guje Domin ganin me yake faruwa
Suna zuwa suka iske ta zaune kalau tasa hoto agaba tana rusa kuka
Adaidai lokacinne wani sautin kyalkyala dariya ya ratsa turakar Gaba daya wanda yasa ta dinga girgiza tare da tambal tambal
Kamar kwale kwalen da iska take kokarin tuntsurar dashi
Daga can sai ga kokon kan boka Hubbas ya ratso ta jikin rufin turakar ba tareda gangar jikiba, kan yana yawo a saman iskaA lokacin daya dakata da dariyar da yake fuskarsa a murtuke kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa
Nanfa hankalin kowa daga wajen ya tashi jikinsu ya fara karkarwa kai kace Acikin tekun kankara aka ciro su
Cikin wata kakkausar murya ya dubeta yace
Yarinya kinyi kuskure da har kike tunanin akwai lokacin da wani zaizo daga wata duniyar Domin karbar ki daga hannun mu
Ki sani cewa babu mahalukin daya isa ya iya zuwa har nan Domin karbarki
Anan zaki karasa rayuwar ki kuma ba zan bari ki mutu ba daga nan har karshen duniya
Saboda ke babbar kadara ce agurina wacce bazan taba yin sake da itaba
Idan kuwa baki daina irin wannan tunanin ba ni da kaina zan dauki mataki akanki.
Yana gama fadin haka saiya tuntsure da dariya mai kama da saukar aradu
Sannan fuskar tasa ta face daga cikin dakin..

++++++++ +++++++++
Asalin sarauniya lasmira an haifeta ne acikin yankin birnin misra cikin wani kauye mai suna kamisur basad
Gaba daya mutanen wannan kauye talakawa ne wadanda basu da tabbacin samun abincin da zasuci a rana
Wasu ma daga cikinsu sai sun fita sunyi bara sannan suke samun abinda zasu ci
Wannan daliline yasa dakarun sumame basu fiya kawo musu hari ba saboda kaurin sunan da sukayi akan talauci
Mahaifinta wato ruzyal da mahaifiyarta sun kasance mafiya talauci daga cikin kabilar kuma Dukkansu sun kasance makafi
Lokacin da suka sami cikin ta sunyi matukar farinciki mara misaltuwa
Amma duk lokacin da suka tuna irin rayuwar da suke ciki kuma abinda zasu haifa zai taso aciki sai su fashe da kuka
A ranar da suka haifetane hankalin su yafi tashi fiye da ko yaushe
Sakamakon shafa fuskarta da sukayi suka ga irin kyawun da allah ya bata
Ba komai ne ya daga musu hankali ba face sanin cewa da zarar mutane sun lura da kyawun ta
Dolene a rabasu da ita da karfin tsiya irin rabuwar da bazasu sake haduwa
Kuma rayuwarta zata shiga tsaka mai wuya sakamakon farautar ta da za'a dingayi
Wannan daliline yasa hankalinsu ya dugunzuma suka rasa me ke musu dadi
Saboda tsananin tashin hankali take zuciyar mahaifiyarta ta buga da karfi ta fadi ta mutu
Koda ruzyal ya shafa fuskarta ya tabbatar da cewa ta mutu sai ya fashe da kuka ya rasa meke masa dadi kawai sai ya fashe da kuka kamar bazai daina ba
Daga can saiya tashi ya haka kabari ya binne matar tasa acikin dakin nasu
Shima har ya dauki wuka zai kashe kan nasa sai ya tuna da jaririyarsu wacce take bukatar kulawa
Dayin wannan tunani sai ya yanke shawarar ya dauketa daga cikin mutane ya su koma can wajen gari inda babu mutane su ci gaba da rayuwa a can
A Wannan rana ya dauketa suka sulale suka bar garin suka koma cikin jeji inda yaci gaba da rainon jaririyarsa kuma ya sanya mata sunan mahaifiyarta lasmira
Haka dai yaci gaba da rainonta cikin kauna da shakuwa, duk wani Abu wanda uwa da uba suke yiwa 'ya'ya shine yake yi mata harta fara tasawa
Wanda akullum kyawunta kara bayyana yake fiye dana baya , ta yadda akullum Wannan kyawun nata kara dagawa ruzyal hankali yake
Ta yadda kullum idan ya kebance ya fara tunanin halinda zata shiga Bayan ransa saiyayita kuka
Kuma Tsawon wannan lokaci bai taba bari wani mutum ya ganta ba
Haka Kuma baya bari ta fita daga kogon dutsen da suke Koda kuwa ya tashi zai fita nemo musu abinci sai ya barta Acikin dutsen sannan ya mirgina wani dutsen ya rufe kogon dashi ta yadda ba zata iya fita da ciki ba
Kuma wani abun ba zai iya shiga ciki ba

WANNAN SHINE TAKAITACCEN TARIHIN SARAUNIYA LASMIRA
****** ******** *********

A can yankin birnin sin kuwa kafin haihuwar lasmira da shekara goma
Anyi wani hamshakin attajiri mai suna jawwas bin Taiwan a wannan zamani kaf yankin birnin sin babu attajirin daya mallaki koda rabin dukiyar daya tara
Domin saboda tsabar dukiyar daya tara sai daya zamana an rasa guraren da za'a dinga zuba su
Bisa dole aka dinga haka rijiyoyi Ana zubawa aciki bisa tsaron dakarun aljanu
Jawwas ya kasance mutumin kirkine mai tsananin tausayin talakawa wannan daliline yasa kullum kofar gidansa cike yake da masu neman taimako
Yayinda zai fito da kansa yana raba musu abincin da zasuci da kuma kudade masu yawa kamar baya tsoron su kare
Hakane yasa yake da matukar farinjini a gurin talakawa da mutanen gari
A rayuwar jawwas bashi da wani aboki wanda ya wuce sarkin sin na wannan zamani kasancewar tare suka taso tun suna kanana
Don haka shakuwa mai karfi ta shiga Tsakanin su har ya zamana idan suna zaune aguri idan bako yazo bai isa ya iya banbance waye sarki ba Acikin su
Saboda yadda komai nasu ya zama daya babu banbanci,
A inda kawai zaka gane banbancin su shine a gurin zaman Fada ko kuma yayinda aka fita filin daga
Badon komai ba sai don banbancin sadaukantaka, attajiri jawwas bai kasance mayaki ba tun yana karami,
Shi kuwa sarki suraif ya kasance hamshakin Sadauki mai dakawa maza gumba a hannu
Wanda baya tsoron ratsawa ta tsakiyar abokan Gaba Komai yawansu ya fatattake su da karfin tsiya har sai sun gudu da kafafunsu
Shi kuwa attajiri jawwas ko ruke takobi bai iya ba
Duk irin wannan daukaka da allah ya basu sai suka zama kamar na banza Domin duk su biyun babu wanda ya taba haihuwa acikinsu
Kuma babu irin kokarin da basuyiba Domin su sami haihuwa amma Abu ya faskara
Duk da cewa sun auri mataye fiye da dari don samun haihuwa
Suna zaune wata rana sai suka sami labarin bayyanar wani hatsabibin bakon boka a can kusa da birnin misra
Wanda labarin hatsabibancin sa ya bazu a ko'ina cikin duniya
Saboda yadda yake aikata abubuwanda duk bokaye suka kasa
Aikuwa suna samun labarin bayyanar sa sai sukayi shiri su biyun suka
wani hadiman aljanin sarki suraif tareda da dukiya mai uban yawa suka tafi gurinsa Domin neman haihuwa
Tsakanin birnin sin da misra tafiyar shekara guda ce amma saboda karfin gudun aljanin da suke kansa sai suka shafeta acikin mako biyu kacal
Koda suka sauka abakin kogon dutsen da yake zaune sai sukayi arba da boka hulbaz a tsaye kyam a bakin kogon tsafin nasa fuskarsa cike da murmushi kamar wanda yaga 'yanuwansa na jini
Nanfa mamaki ya kamasu sakamakon ganinsa da sukayi matashi wanda shekarunsa ba zasu Gaza sha biyu ba zuwa sha uku
Suka fara kokwanton anya kuwa shine bokan da ake basu labari
Kawai sai suka ji yace lale marhaban da sarki suraif tare da babban attajiri jawwas
Hakika kunzo inda bukatar ku zata biya, don haka kawai ku biyo bayana
Yana gama fadin haka ya juya ya shige cikin kogon dutsen nasa suna biye dashi a baya
Aikuws suna shiga ciki duk sai suka zama cikakkun 'yankauye Domin ganin yadda aka kawata cikinsa fiye da yadda aka kawata masarautarsa
Da. Shigarsu cikin gidan sai take wasu kujeru guda uku suka bayyana a turakar
Cikin murmushi ya dubesu yace ga guri nan ku zauna kuci abinci
In yaso Daga baya sai mu tattauna akan abindake gaban mu
Zamansu keda wuya sai wasu kuyangi suka kawo abinci kala daban daban suka ajiye a gabansu
Ba tareda bata lokaci ba suka ci abinci suka sha lemo sannan suka gyara zamansu
Har sun bude bakinsu da nufin yi masa bayani sai ya dakatar dasu da hannu tareda cewa
Nasan da bukatar dake tafe daku
Dukkanku kunzo ne Domin neman haihuwa wacce kuka shafe shekaru kuna nemanta kuka rasa
Kuma kun auri mataye da yawa saboda bukatar ku ta biya amma kuka rasa
To yau kunzo inda bukatar ku zata biya kuma a share muku hawaye matukar zaku aikata abinda na umarceku
Dajin wannan batu sai attajiri jawwas cikin zumudi yace wane abune zamu aikata ina mai tabbatar maka da cewa zamu aikata shi komai wahalar sa
Kodajin haka sai yayi murmushi yace me kake ci na baka na zuba bayan yanzu zan fada muku
Da farko dai idan har kunason samun haihuwar wadanda zasu gaji bayan ku
Ku sani ba zaku taba samun haihuwa ba da saduwar farko ba da matayenku na aure ba muddin baku yi musanyensu ba
Abin nufi kuwa shine Dolene ku sake sabon aure a ranar da zaku tare kai sarki suraif sai ka tare da matar da Jawwas ya aura haka Shima kuma ya tare da taka
Kunga kenan kai jawwas matarka zata haifi dan suraif haka Shima matarsa zata haifi danka
Muddin kukayi haka to Awannan ranar zasu sami juna biyu, shikenan sai kowa ya koma amfani da matarsa
Wannan ce kadai hanyar da zaku bi Domin samun biyan bukatar ku
Koda yazo daidai nan a zancensa sai ya dakata yana mai sauraron yaji hukuncin da zasu yanke

Alokacin da dukkansu Sukayi zuru zuru suna masu kallon juna suka rasa hukuncin da zasu yanke

SHIN SUNA YARDA DA SHARADIN DA BOKA HULBAZ YA SHARDANTA MUSU?
SHIN LASMIRA TANA KUBUTA DAGA DAKIN DA TAKE CIKI?

DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMVAYOYI SAI MUN HADU A KASHI NA GABA**********KARAGAR AJALI

*********4 PART B

LBR

******** HABIBULLAH KBR

Lokacin dasu sarki suraif suka fara zazzare idanu sakamakon jin umarnin boka hulbaz tsawon lokaci mai tsawo ba tareda dayansu ya kasa yanke hukunci ba
Sai kawai yayi wani guntun murmushi yace
Haba kada ku bani kunya mana ku tuna fa kufa manya ne wadanda suka tara ababan more rayuwa kala daban daban idan har baku karbi shawarata ba to ina mai rantse muku ba zaku taba samun haihuwa ba
Kuma da zarar kun mutu wani ne a banza zai gaje duk duniyoyin da kuka shafe shekaru kuna tarawa
Yanzu baku da isashshen lokaci ya zama dole ku yanke hukunci yanzu kafin lokaci ya wuce
Cikin sanyin jiki jawwas yaja sarki suraif gefe sukayi kus kus sannan suka dawo sukace mun amince
Dajin haka sai boka hulbaz ya tuntsure da dariya daga. Can kuma sai ya tsuke bakinsa alokacin da fuskarsa ta nuna tsantsar damuwa
Wanda suka rasa dalilin hakan har jawwas yaji bazai iya jurewa ba ya tambayeshi yace
Yakai wannan boka kai kuwa menene dalilin wannan yanayi daka shiga guda biyu alokaci guda
Kodajin wannan tambaya sai ya gyada kai cikin alamun damuwa da kuma kwarin gwiwa
Yaci gaba da cewa ba komai ne yasa ni shiga wannan yanayi ba face
Wannan karo na farko da zan zama silar cikar farincikin manyan mutane guda biyu
Kuma shine karo na farko da zan zama silar haihuwar wadanda zasu zamo abokan hamayyata a bayan girmansu,.
Ku sani cewa bayan haihuwar wadannan jarirai naku zasu taso da tsananin jarumtakar da har karshen duniya za'a dinga tunawa da tarihinsu Saboda yadda labarin jarumtakarsu zai bazu ako'ina acikin duniya
A Wannan lokaci ne zasu bazama neman abinda nima nazo wannan nahiya dominsa
Ba don komai nazo wannan nahiya ba sai don jiran bayyanar wata Yarinya wacce zata zama silar bayyanar bayani akan wata karaga wacce akewa lakabi da KARAGAR AJALI
Idan har na mallaki wannan karaga da mahadinta wato takobin SAIFUL LAIHAM kamar na mallaki wannan duniyar da sauran duniyoyine
Wadanda a halin yanzu babu wanda yasan inda wadannan abubuwa suke
Itakuwa wannan Yarinya a halin yanzu ma ba'a haifeta ba

Idan har muka hadu da wadannan yara naku zamu fafata kazamin yaki dasu
Wanda bani da tabbacin samun nasara ko kuma faduwa akansu.
Amma ina mai baku shawara dakuyi iya kokarin ku wajen ganin kun horar dasu ilimin bokanci dana dabarun yaki iya iyawarku domin kare kansu Daga sharrina idan mun hadu
, kamar yadda nima zan zauna na fara shirye shirye akan su tun gabanin haihuwarsu
Don in kare kimata a wajensu , kuma zan yake su da dukkan karfina a duk lokacin da muka yi arangama dasu

Shawara ta karshe da zan baku itace ya zama dole kowanne daga cikinku ya rike 'ya'yan da matanku suka kamar dan cikinsa ba tareda banbanci ba
Bayan haka komenene zai faru bayan haihuwar wadannan 'ya'ya naku kada ku kuskura ku sanar dasu yadda aka haifesu Domin hakan babu abinda zai janyo a gareku face nadamar haihuwar tasu kuma suma burinsu ba zai taba cika ba
Da wannan furuci nake sallamar ku daga yanzu ba zamu sake haduwa daku ba Koda kuwa zaku dawo nan,
Yana gama fadin haka take ya bace musu da gani suka nemeshi sama da kasa suka rasa
Ba tareda bata lokaci ba suka mike suka bar kogon nasa suka hau aljanin daya kawo su suka kama hanyar komawa birnin sin
Tunda suka bar kogon boka hulbaz dayansu bai cewa kowa uffan ba
Saboda tunanin maganar daya fada musu wanda ya birkita kwakwalwarsu
Har saida suka fada dogon tunani mai tsawo ,
Jawwas yayi dogon numfashi sannan ya dubi sarki suraif yace Yakai abokina kaji bayanin da wannan takadirin bokan yayi kai kuwa me kake ganin zamuyi
Shin zamu hakura da haihuwar ne ko kuwa zamu haifa masa 'ya'yan da nan gaba shi zai zamo ajalinsu?
Dajin wannan tambaya sai suraif ya tuntsure da dariya al'amarin daya daure masa kai kenan
Daga bisani kuma ya turbune fuska kamar an aiko masa da sakon mutuwa yace
Ai wannan ba wani Abu bane, Tunda har munsan abinda zai faru dole agaba muma dole mu dauki namu matakin kuma muyi mugayen shirye shirye akan zuwansa

Zamu koyar dasu dabarun yaki daga hannun kwararrun mayaka wadanda babu kamarsu a wannan karni,
Haka bayan haihuwar ba zamu taba shayar dasu nono ba saidai tsumin tsafi daga ranar da aka haifesu har zuwa yayesu
Kamar yadda Shima yayi ikirarin cewa tun daga wannan rana zai fara tanadin zuwansu
To muma haka zamu fara tun yanzu wajen ganin bai sami biyan bukatar sa ba
Zamu horar dasu fannoni daban daban na kowanne ilimi, sannan mu basu tsaro na musamman ta yadda zasu iya karawa da kowa a duniya
Ka sani boka hulbaz ya fito ne ya gaya mana gaskiyar abinda zai faru a gaba dan haka bamu San irin shirin da Shima zai yi akai ba,
Haka dai suka ci gaba da hirar su har suka isa birnin sin ba tareda sun ankara ba
Har sai da sukaji aljanin dake dauke dasu ya daina kada fuka fukansa tareda yin gyaran murya sannan suka lura da isowarsu
Ba tareda bata lokaci ba suka sauka daga kansa suka nufi kofar garin wacce dakaru ke tsatstsaye suna gadinta ruke da makamai a hannunsu
Shi kuma aljanin ya kada fuka fukansa yayi tafiyarsa abinsa
Da isarsu bakin kofar birnin take dakaru suka wangame musu kofa cikin girmamawa
Wasu daga cikinsu suka bisu a baya suka dakaru har gidajensu
A Wannan rana sarki suraif da attajiri jawwas suka saki matayensu
Suka nemo kyakykyawan ''yan mata wadanda babu kamarsu acikin birnin da kewaye aka fara shagalin aurensu
Kuma aka aika da wasikun gayyata ga manyan sarakuna da attajiran da suke nahiyar
Aikuwa kashe gari tun da duku dukun safiya baki suka fara ciccidowa garin daga sassa daban daban na nahiyar
Don halartar Wannan bikin, kafin a jima tuni gari ya cika ya batse da jama'a babu masaka tsinke

Nanfa gari ya cika ya batse da jama'a

Please Login or Register in order to submit comment