Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsafi tana tofawa agurin bayan ta gama sai tazo ta zauna tana mai fuskantar ruwaisa tace

Yake ruwaisa ki sani cewa yanzu haka duk duniya babu wanda ya iyasa ya san zancen da zamu tattauna dake
Don haka idan har zancen nan ya fita najishi a waje to tabbas kece kika ci amanata
Kuma ki sani sakamakon cin amanata hukuncin kisa ne don ko mahaifina bai iya ya dakatar dani ba idan nayi niya
kuma daga wannan lokaci bazan kara amincewa da kowa ba a rayuwata saboda wacce na fara amincewa tun lokacin kuruciya taci amanata .

Dajin wannan batu sai zuciyarta ta buga da karfi ta dago a razane tace
Me kike nufi ya shugabata shin dama a ranki kinajin cewa akwai lokacin da zanci amanarki?
Nayi miki rantsuwa da abin bauta tunanin haka bai taba zuwa zuciyata ba
Kuma da in furta abinda zamu tattauna dake ga wani gwanda na sa wuka na kashe kaina
Cikin yarda suhaila ta dubeta tace
Shin kina ganin cewa ya halatta mutum yaci amanar wani babba agurinsa domin ceton miliyoyin rayuka da kuma dawo musu da farincikin da suka shafe shekaru rabonsu da samunsa?

Kodajin wannan tambaya sai ruwaisa ta kamu da tsananin mamaki game da wannan tambaya

Don haka sai tace kwarai kuwa wannan maganar taki gaskiyace amma me yasa kikayi mini wannan tambayar?
Bana so ki aikata kuskuren da daga baya zakizo kina nadamar aikata shi
Gimbiya suhaila tayi ajiyar zuciya tace
Yake ruwaisa sanin kanki ne cewa fiye da shekara goma
acikin wannan birni babu abinda ake aikatawa face mulkin kama karya da zalunci
Ta yadda masu mulki ne kadai suke jin dadi acikinsa
Bayan haka kuma kashe mazajen garin nan da akeyi tsawon wannan lokaci babu namiji koda guda daya acikinsa face mutum daya wato mahaifina sarki gulbas
Kuma shine wanda yake silar faruwar duk wannan bala'i
To ki sani cewa yanzu haka yanayin wani gagarumin shiri na mallakar wata karagar mulki wacce akewa lakabi da KARAGAR AJALI
Mallakar wannan karaga daidai take da mallakar duniya da duk abindake cikinta
Domin idan har ya mallaketa hatta Kananun kwari da duwarwatsu sai sunyi masa mubaya'a
Idan har ya sami nasarar mallakar wannan karaga, to ba nan kasar ba duk duniya sai sun shiga tashin hankali da azabarsa
Domin idan ba'ayi sa'a ba sai yayi yunkurin hallaka fiye da rabin mazajen duniya kinga kuwa silar hakan mataye da yawa zasu shiga cikin mawuyacin hali kuma za'a bar marayu wadanda basu da mataimaka
Koguna kuwa mai makon a sami ruwa acikinsu sai dai a dinga diban jinin bil'adama
Idan har ba'ayi yunkurin dakatar dashi ba to tabbas dolene yayiwa kasa ado da jinin bil'adama
Sai anyi mulkin zaluncin da ba'a taba yin kamarsa ba atarihin duniya

Yanzu haka yayi nisa cikin binciken hanyar da zaibi domin tsallake mataki na biyu na mallakar KARAGAR AJALI

Kuma kamar yadda shima yake da wannan mugun kuduri haka duk wani mai yunkurin mallakar karagar ajali yake
Saidai bincike ya nuna cewa idan har na hada kai da daya daga cikinsu wato jarumi rukyan kuma
. Har soyayya ta kullu a tsakaninmu to tabbas zamu sami nasarar dauko takobin saiful laiham ni kuma zanyi amfani da wannan damar na sace takobin daga gurinsa
Daga nan Boka farraz zai hada ni da daya daga cikin hadiman Aljanun sa
Ya kaini can darul maut
Na ruga su hawa kan karagar ajali domin hana su aiwatar da mugun shirin da sukeyi
Koda gimbiya suhaila tazo daidai nan a zancenta sai kuyanga ramsiya tayi shiru
Hankalin ta a tashe tana nazarin maganar acikin zuciyarta Daga can sai ta dago ta dube ta tace
Haba ya shugabata akan wanne dalili kike son saka kanki acikin tarkon mutuwa
Ki sani koda ace kin sami nasara akan mahaifinki bai zama dole ki samu akan shi jarumi rukyan ba
Domin kamar yadda kike matashiyar budurwa mai tashen kuruciya to shima haka yake
Haka kuma yadda kike da tunani irin na matasa haka shima tunaninsa yake
Bayan haka inaso ki sani ita soyayya muguwar abace wacce tafi guba zafi
Kuma aduniya babu wasan dayafi na soyayya hadari musamman ma shi da
Akace mutum ne mai kyawun gaske da kuma farin jini wanda 'yan mata da yawa suke burin mallaka
Kinga idan ba'ayi sa'a ba mai makon ke ki sami nasara akansa sai reshe ya juye da mujiya shi ya sami galaba akan ki
Kinga kuwa kinyi biyu babu
Kai kodama kin sami nasarar sace takobin saiful laiham daga Hannunsa Tayaya kike ganin zaki iya zuwa can darul maut har ki hau kan KARAGAR AJALI ?
Bayan haka ta yaya kike tsammanin shi boka farraz ba zaici amanarki ba?
Domin duk wani mashahuri burinsa shine ya mallaki wannan karaga
Kodajin wannan tambayar sai zuciyar gimbiya suhaila ta buga da karfi
Ta rasa abinda yake mata dadi daga can kuma sai tayi dariya tace yanzu dai bansan amsar da zan baki akan wannan tambayar taki ba
Amma lokaci ne zai warware komai yanzu na sallame ki sai anjima
Tana gama fadin haka sai kuyanga ruwaisa ta mike tsaye ta fice daga turakar tabar gimbiya suhaila cikin kogin tunani
WANNAN SHINE ABINDAYA FARU A BANGAREN GIMBIYA SUHAILA BAYAN TATTAUNAWAR SIRRIN DA TAYI DA KUYANGA RAMSIYA
*****************************
Al'amarin jarumi rukyan kuwa lokacin da wadannan aljanu suka ciccibeshi kamar gawa suka nufi can harabar da suke rataye fursunoni dashi
Su kansu a matukar razane suke dashi domin basu taba ganin mutum mai taurin kansa da kuma nacinsa ba
Gani sukeyi kamar koda yaushe zai iya dawowa cikin hayyacinsa ya far musu da yaki
Suna cikin tafiyar ne daya daga cikinsu mai matukar surutu ya kalleshi ya kare masa kallo sannan yace
Oh! Ku duba wannan 'yar karamar halittar da muke rainawa wai yau itace ta bamu wahala sosai har sai da maigidan mu ya tunkareshi da kansa sannan ya sami galaba akansa
Dajin haka sai abokan tafiyar tasa sukace kwarai kuwa bakaga a karon farko shi kansa mai gidan namu saida wannan mutumin yayi masa dukan da yasa shi ganin taurarin wuya a idanunsa ba?
Kodajin wannan tambayar sai wanda ya fara maganar yayi dariya sannan yace
Tab da ace yasan cewa makasar mu a tsakiyar cibiyoyin mu take da tabbas daya daga cikin mu ba zai tsira b..
Kafin ya gama fadin abinda yake bakinsa tuni wani daga cikin su ya kwada masa mari don ya dakatar dashi ga barin maganar da yake furtawa
Aikuwa cikin rashin sa'a sai iska ta kwashi maganar da sukeyi kai tsaye sai cikin kunnuwan jarumi rukyan
Ai kuwa yanajin wannan furuci sai yaji wani azababben karfi ya shiga jikinsa
Take yayi kukan kura wanda ya razana aljanun da suke kusa dashi
Suka ja da baya kamar zasu gudu, kawai sai ya kama sarkokin da suke jikinsa ya tsitstsinka su suka zube kasa
Cikin zafin nama ya zaro gajerun wukake a kugunsa
Ya falfala da gudu ya nufi inda aljanun nan suke
Yana zuwa tsakiyarsu kawai sai yayi katantanwa atsakiyarsu ya wuce gaba
Giftawarsa keda wuya sai ga jini ya barke daga cibiyoyin su kamar an bude magudanar ruwa dukkansu suka zube kasa matattu
Cikin kankanin lokaci ya isa tsakiyar fadar inda ragowar aljanun suke
Koda suka hango tahowarsa daga nesa sai duk sai suka shiga taitayinsu
Suka saki baki suna mamakin yadda ya iya Kwacewa daga daurin sarkokin da akayi masa
Take wasu daga cikin aljanun suka ruga da gudu inda yake domin su tareshi kafin ya karaso
Aikuwa suna haduwa dashi sai suka ruguntsume da masifaffen yaki
Wannan lokacin sai labari yasha banban domin duk inda ya kutsa kansa acikin su sai dai kaga jini yana feshi da fallatsi
Kafin a dauki wani lokaci tuni fadar ta cika da jinin wadannan aljanu
Nanfa fadar ta cika da kakarin mutuwar aljanun, duk inda ka waiga babu abinda zaka gani face gawarwakinsu faca faca cikin jini
Koda shugaban aljanun yaga irin barnar da jarumi rukyan yake yiwa dakarunsa
Sai ransa ya baci zuciyarsa ta harzuka ta fara ta fasa kamar zata kone
Cikin shammace ya falfalo da gudun tsiya da nufin yayi masa fashin albasa
Saidai kash tuni rukyan ya ankara dashi, koda isowarsa sai ya kawo masa mahaukacin duka da gudumar hannunsa
Aikuwa cikin tsananin zafin nama rukyan ya daka tsalle ya kaucewa harin
Kafin aljanin yayi wani yunkuri tuni ya juya jikinsa a saman ya caka wukaken biyu a tsakiyar cikibiyarsa
Take wukaken suka lume acikin cibiyar tasa ya fadi kasa yana kakarin mutuwa
Koda sauran aljanun sukaga abindaya sami shugabansu
Sai suka kara rudewa da firgicewa mai makon su ci gaba da yaki
Sai gashi sun fara kokarin kare kansu suna guje guje don tsira da rayuwarsu saboda yadda sukaga ruwan bala'i
Sai dai kash babu damar yin hakan domin kure musu gudu ya dinga yi yana kashe su
A wannan rana sunga masifar da basu taba ganin irinta ba Arayuwa, domin ko guda daya daga cikinsu bai sami damar tsira ba, sai daya kashe su gaba daya
Yana gama wa dasu shima ya zube kasa yana haki da numfarfashi saboda tsabar wahalar daya sh,
bayan ya huta sai ya shafa magani ajikin raunikansa da suke masa zugi Sannan ya mike ya debi makamansa ya gyara su
ya nufi hanyar daki na gaba.

KUYI HAKURI BISA JINKIRIN DA AKA SAMU INA FATAN HAKA BAZATA SAKE FARUWA BA

YAUSHENE ZASU KAMMALA KARBAR WANNAN HORO?
SHIN KUYANGA RAMSIYA ZATACI AMANAR GIMBIYA SUHAILA?
WANNE IRIN MASIFU NE ACIKIN DAKUNAN DA ZASU FUSKANTA NAN GABA?
SHIN BOKA FARRAZ YASAN CEWA GIMBIYA SUHAILA NA DAF DA GANO SHIRIN DA YAKE AKANTA?

SAI MUN HADU A KASHI NA GABA
HABIBULLAH KBR

LIKE AND COMMENTS************ KARAGAR AJALI 3

PART
****************A

LBR

************HABIBULLAH KBR

Kamar yadda aka tsara wannan karbar horo haka su sarki gulbas
Suka dinga ratsawa ta cikin dakuna mabanbanta wanda masifar daki na gaba tafi wacce ke cikin daki na baya
Sai da suka kwana goma cur suna cikin wannan gida suna fafatawa, da kuma fadawa cikin tarkuna masu mugun hatsari kamar zasu rasa rayukansu gaba daya wani lokacin ma sai sun fitar da rai ga tsira da rayukansu
Amma bisa sa'a da kuma jajircewa sai kaga sun kubuta
Kai a wadannan ranaku sunga bala'in da tunda suka zo duniya basu taba ganin irinsu ba
Sai da takai ga cewa abincinsu da ruwan shansu sun kare
Saidai idan yunwa ta dame su sai su sami mushe suci ba tareda sun gasa namansa ba
Sannan su shanye jinin jikinsa,
Kai wani lokacinma itace suke samu su dinga ci har sai sun gusar da yunwar su
Tsawon wadannan ranaku sai da takai ga cewa sun raina jarumtakar da suke takama da ita, domin kuwa sunzo matakin da bata da amfani saidai sa'a da rabo
Saida ta kai ga cewa dukkansu sun kasa daga koda hannayensu saboda wahalar da suka fuskanta acikin daki na karshe
Su da kansu suka tabbatarwa da kansu cewa lallai SADAUKI FARHAN ya cika sadauki kuma dodon maza ,kuma shu'umin gaske wanda idan da akwai duniyar datafi wannan ya cancanci ya mulke ta
Acikin daki na karshe ne suka sami duk bayanin da suke bukata
dan gane da takobin saiful laiham da sirrikan da suke tattare da ita
Kuma kowanne daga cikinsu saida aka zana masa taswirar zuwa inda take acikin kwayar idonsa
Ta yadda da zarar ya mutu agarin neman ta babu wanda zai sake mallakar wannan taswirar face shima ya karbi tasa jarrabawar horon
Aranar da suka kammala karbar horon ne wata iriyar iska mai karfi tazo ta zukesu gaba dayansu ta duk ta watsa su cikin dakunan da suke kafin fara horon cikin mawuyacin hali wanda ka iya cewa suna tsakanin mutuwa da rayuwa

Boka surkais ne ya fara bayyana acikin kogonsa na tsafi idanunsa a rufe saboda yadda fuskarsa tayi caba caba da jini
Koda bayyanarsa acikin dakin halwar tsafinsa sai ga wasu aljanu sun ratso saman rufin dakin sun shigo ciki
Cikin gaggawa suka fito da kayan magunguna suka dukufa akansa domin yi masa magani
Wasu kalar magunguna suka fito dasu daga cikin wata jakar fatar damisa
Suka dinga shafawa ajikin ciwukan jikinsa domin yi masa magani
Saboda irin mugayen dafin da suka shiga jikinsa
Su kansu sunyi matukar mamakin yadda akayi ya tsira da ransa ba tareda ya mutu ba
Saida suka yini guda suna hidima akansa sannan hankalinsa ya fara dawowa jikinsa
A hankali ya bude idanuwansa koda ya ganshi acikin kogon tsafinsa sai ya kamu da farinciki har ya yunkura da nufin ya zauna sai yaji kamar jijiyoyin jikinsa zasu tsitstsinke
Cikin sauri aljanun suka maidashi kan. Gadonsa sukace kayi hakuri ya shugaban mu
Ba zaka iya yin aikin komai ba har sai nan da sati guda
Saboda mugayen raunikan da suke jikinka ya zama tilas kayi hakurin jiran wannan lokaci
Kodajin haka sai zuciyarsa ta fusata, ya dakawa hadiman nasa tsawa yace
Kuna nufin naci gaba da zama a wannan guri har sai abokan gabata sun rigani isa inda wannan takobi take?
Cikin rawar jiki shugabansu yace ba haka muke nufi ba ya shugaban mu
Ba zasu taba rigaka isa inda take ba domin muna da tabbacin cewa alokaci guda kuka fara karbar wannan horo
Don haka alokaci daya zaku kammala kaga kenan dolene suma yanzu su kasance acikin irin yanayin da kake ciki
Idan baka yardaba kuwa sai ka duba Cikin madubin tsafinka zaka gasgata maganarmu
Ba tareda bata lokaci ba surkais ya dubi madubin tsafinsa
Take wani haske yayi fitar burgu daga cikin idanun nasa ya daki madubin
Ai kuwa faruwar hakan keda wuya sai madubin yayi baki kirin ya soma kokarin tsagewa
Nanfa gumi ya dinga tsiyaya daga jikin boka surkais kamar wanda yayi wanka acikin ruwan sama
Bisa dole ya hakura da binciken yana mai kwarara uban ihu
Wanda ya razana gaba daya hadiman da suke cikin kogon suka fara guje guje domin ceton rayukansu.

Tirkashi!!! Inda ace hadiman sun san halin daya shiga lokacin da yake karbar wannan horon
Da dolene suyi masa dariya domin duk sanda kaji ance ga ko gudu
To sa gudu ne baizo gurin ba.
Suna cikin wannan hali sai kawai aka bude kofar dakin aka shigo
Cikin sauri hadiman suka waiwaya domin ganin mai shigowar
Ba kowa bane face wani matashin yaro dan kimanin shekaru goma sha biyar
Sanye da kaya masu tsada ajikinsa fuskar yaron amurtuke babu alamar fara'a
Koda ganin sa sai dukkansu suka kara rudewa saboda sanin rashin tausayinsa da zalincinsa ya ninka mahaifinsa sau goma
A rayuwar boka surkais babu abinda yake kauna sama da wannan da nasa
Kuma bashi d burin dayafi yaga ya gaji sirrikan tsafinsa
Sai dai kash!!
Wannan yaro yana da matsalar kwakwalwa azahiri idan ka ganshi ba zaka taba fahimtar haka ba

Saidai idan yana wasu ayyukan ne zaka fuskanci cewa yana da matsalar kwakwalwa
Domin shi a rayuwarsa komai yana kallonsa ne a baibai
babu kokarin da boka surkais baiyi ba don yaga wannan da nasa kishbaru ya sami lafiya amma abu yaci tura
Daga karshene ya gane cewa dole sai ya mallaki sirrikan tsafin abokan takararsa sannan zai sami damar baiwa wannan yaro nasa lafiya
Kai tsaye kishbaru ya wuce zuwa inda nahaifinsa yake
Yana zuwa yayi tsalle ya fada kan rauninsa saboda murna
Nanfa boka surkais yaji kamar ya kwarara uban ihu saboda tsananin zafi
Amma sai ya jure zafin don kar ya nuna gazawarsa afili
Kawai sai boka surkais ya janye shi da sihirin tsafinsa ya mai dashi gefe
Kishbaru yace ya abbana ina ka tafi ba kwana biyu banganka ba?
Kuma menene ya sameka naga ciwuka ajikinka? Dajin wadannan tambayoyi sai yayi dan guntun murmushi sannan ya tofar da wani gudan jini daga bakinsa yace
Ka kwantar da hankalinka kishbaru yanzu haka ina kan wani tafarki ne
Wanda babu mai iya riskar matakin da zan hau da zarar bukatata ta biya
Zaka zama babban. Shararren matsafi kuma ina mai tabbatar maka da cewa kaine zaka gajeni ka dinga sarrafa duniya kamar a tafin hannunka
Ta yadda dana zaluncinka ba zasu taba shudewa ba har abada
Don haka n yanke cewa tare dakai zamu shiga duniya neman takobin saiful laiham
Amma ya zama tilas na zauna nayi jinya ta kankanin lokaci kafin tafiyar mu

Dajin wannan batu sai fuskarsa ta fadada da murmushi yana kyalkyala dariya
Daga can kuma sai ya juya kan hadiman mahaifinsa
Wadanda tuni jikinsu ya fara kyar ma saboda su kansu basa samun nutsuwa Idan yana gurin
Aikuwa yana juyawa sai ya wata iska ta fito daga idanunsa
Ta shuri aljanun ta dinga wujijjiga su a sama tana maka su da jikin garu
Nanfa suka fara ihu a saman suna rokon yayi musu afuwa amma sai yayi buris dasu kamar baisan sunayi ba
Ya cigaba da kyakyacewa da dariyar sabida farinciki
Shi kuwa boka surkais sai ya bishi da kallo fuskarsa cike da fara'a
Sai daya gama jigata wadannan aljanun sannan ya sakesu
Suka fado sharaf, sannan ya wuce ya barsu akwance
**********************
Alamarin jarumi rukyan kuwa sai farkawa yayi ya ganshi acikin turakarsa kwance akan wani luntsumemen gado
Ga wasu kuyangi da likitoci sun dukufa akansa suna ta faman sa masa magunguna ajikin raunikansa ba ji b Gani don ceton lafiyarsa
Duk cikinsu babu wanda yasan da cewa ya farfado daga doguwar suman da yayi
Saida sukaji yayi gyaran murya sannan suka lura dashi
Cikin biyayya shugabarsu wacce ta kasance matashiyar budurwa 'yar kimanin shekaru sha tara tace
Barka da dawowa jarumin jarumai kuma namijin mazaje mai shirin hawa KARAGAR AJALI
Nan da dan kankanin lokaci wanda sunanka zai shiga cikin kundun mazajen jiya,
Ya shugabana tabbas jikinka akwai mugayen raunika wadanda dole sai kayi jinyar kwanakin da basu gaza bakwai b sannan zaka sami lafiya
Ka tafi cika sharadi na biyu dake gaba wanda yafi na baya hatsari

Dajin wannan batu sai rukyan ya juyo inda take cikin tsananin mamakin ganinta acikin wannan kebantaccen gida nasa
Ba kowa bace wannan kyakkyawar budurwarba face gimbiya lardisa 'ya agurin sarki kussaru na birnin sin
Ita dai lardisa ta kasance ita kadaice 'ya agurin mahaifinta wacce yake matukar kauna kuma yanzu haka itace wacce yake sa ran zata gaji sarautarsa bayan ya mutu
A rayuwar gimbiya lardisa babu abinda take kauna sama da rubuce rubucen labaran tarihin manyan mayaka, jarumai, sarakai da kuma bokaye
Wannan daliline yasa kullum acikin yawo take aduniya
Tana bin tsofaffin mayaka da kuma wadanda suke tashe ,aljanu, kai hardama sarakuna tana samun labarai agurin su tana rubutawa acikin wani babban KUNDIN TARIHI da yake jakarta domin itama tabar tarihin da za'a dinga tunawa da ita bayan mutuwar ta
Kuma tanayin rubutun ne da alkaluman tsafi ta yadda ba zasu taba goguwa daga jikin littafin ba

Gimbiya lardisa tana daya daga cikin matan da suka nuna soyayyarsu ga jarumi rukyan a baya amma ya watsar da soyayyar tasu
Cikin mamaki rukyan ya dubeta yace
Yake gimbiya lardisa ke kuwa menene ya kawoki nan kuma tayaya kika shigo nan kika saje da hadimai na ba tareda sun ankara dake ba?
Dajin wannan tambayar sai ta kara sakin wani murmushi
wanda ya fito da kyawunta afili tace
Kada ka damu yakai wannan gwarzon mazaje kuma tarwatsa maza
Ba komai ne ya raboni da masarautata da kuma karagar mahaifina ba face dalilai guda biyu
Dalili na farko shine soyayyarka……..

Cikin sauri rukyan ya dakatar da ita sannan ya umarci ragowar hadiman dasu fice daga dakin su bashI guri
Nan da nan kuwa suka fice suka barsu su biyu rak
Ka sani tun farkon haduwata dakaI acikin yankin mu zuciyata ta kamu da matukar kaunarka
Duk da kasancewar baka amshi soyayyata ba amma ni na gwammace na dawo karkashinka

koda kuwa zan zama daya daga cikin bayinka masu yi maka hidima
Dalili na biyu kuwa shine inaso ka taimaka mini ka bani labarin abubuwan al'ajabi da kuma irin gwagwarmayar dakasha alokacin da kake karbar horon sadauki farhan don na rubutashi
Acikin littafina na kundun tarihi don a halin yanzu daf nake da gama rubuta shi
Da zarar na rubuta gwagwarmayar da kuka sha acikin kwanaki goman da suka wuce da kuma wadanda zaku fuskanta anan gaba shikenan na kammala rubutun littafin
Sai naje Na adanashi acikin babban dakin ajiye kayan tarihi dake cikin birnin sin dakin da yafi kowanne dakin kayan tarihi tsaro a duniya
Don haka nake neman alfarmar ka amince dani mu jera mu tafi neman saiful laiham tare
Domin naga abubuwan da zasu da idanuna kuma na rubuta su da hannayena
Dajin wannan batu sai jarumi rukyan ya bushe da dariya kamar zai fado daga gadon da yake
Al'amarin daya matukar bata mamaki kuma ya daure mata kai kenan
Sannan ya kura mata ido cikin alamun rashin yarda daga bisani yace
Aikuwa wannan aiki da kike ba zai taba kammala ba
Domin koda kin san abubuwan da suka faru dani to bai zama lallai ki san abubuwan dasu sarki gulbas suka tarar ba
Bayan haka tayaya kike ganin zan amince dake cewa ba zaki ci amanata ba
Har na tafi dake neman saiful laiham?
Dajin wadannan tambayoyi sai itama ta yi murmushin nuna yadda da kanta, daga baya kuma wata kwallar takaici ta zubo daga idanunta
Wacce bai san dalilin zubar ta ba
Tace masa
dan gane da tambayar da kayi mini ta farko itace inaso ka sani
, samun labaran abubuwan da suka faru gasu sarki gulbas ba abune mai wahala ba
Domin yin hakan shi yafi komai sauki a gareni, kada manta dukkansu babu wanda bai haihuba daga cikinsu
Duk da cewa sun rabu da iyayen 'ya'yan nasu, amma kuma suna matukar kaunar 'ya'yan
Don haka dolene su labartawa 'ya'yayen nasu labarin gwagwarmayar da suka sha
Ni kuma ina daga nan inda nake zanyi amfani sihirin tsafina na sarrafa iska ta dauko min duk irin labaran da zasu tattauna akan wannan tafiya da sukayi na rubuce su acikin littafina, amma bayan wannan ba zan Iya jin komai ba
Domin wannan sihiri yana aiki ne lokaci zuwa lokaci, kuma yana iya dauko zance koda kuwa daga bangon duniya ne
Idan ina da bukatar hakan,…… .
Har rukyan ya bude bakinsa da nufin ya sake yi mata wata tambayar sai ta dakatar dashi tace
Nasan kana mamaki bisa wannan magana dana fada maka.
Amma a guri na wannan ba abin mamaki bane domin kowa a bangaren iliminsa sarki ne
Ni ban isa na shiga sabgar ilimin da kuke dashi na tsafi da kuma jarumta ba
Haka kuma ba zaku iya sanin dabarun da nake dasu domin tattara labarai ba
Koda kuwa zaku tattara hankalinku da ilimin tsafinku guri daya
Don haka kowa ya tsaya iya matsayinsa,

Sanin sirrinkane kadai yafi karfina tunda babu wanda kake dashi da zaka fadawa
Wannan dalilin ne yasa nazo da kaina domin ka fada min
Game da tambayarka ta biyu itace
Duk da matakan dana taka abaya da kuma wanda nake kai yanzu
Ina rantsuwa da abin bautata ban taba haduwa da namijin da zuciyata ta kamu da soyayyarsa ba sai kai
Kuma akanka zan iya salwantar da duk abinda nake dashi
Don haka tayaya kake ganin zanci amanarka?
Koda ba zaka karbi soyayyata ba ina neman alfarmar ka amince min mu tafi neman saiful laiham tare,
idan kuwa har baka amince ba shi kenan rayuwata bata da amfani
duk wahalar dana sha a baya ta zama ta banza gwanda ma na kashe kaina tunda baka amince dani ba
Na tabbata ko bayan raina zaka dinga tunawa dani kuma alhakina sai ya bika koda kuwa ka mallaki karagar ajali
Amma fa ina mai tabbatar maka da cewa dukkan mu muna da bukatar juna acikin wannan tafiyar
Tana gama fadin haka hawaye yana zuba daga idanunta
kawai saita zaro wuka daga jikin kugunta ta dora a wuyanta ta dadira da nufin ta kashe kanta
Koda dirar wukar akan wuyan nata take sai wukar narke ta zama ruwa
Ba tareda tayi koda kwarzane ba, Al'amarin daya matukar bata mamaki kenan
Ta saki baki tana kallon hannunta,
Rukyan yace waya fada miki kina da ikon kashe kanki acikin farajiya ta,
Kije ki sami guri ki zauna zanyi tunani akan al'amarin da kika zo min da shi daga baya zan fada miki hukuncin dana yanke,
Amma har yanzu baki sanar dani hanyar da kika bi kika shigo cikin wannan gidan nawa ba
Dajin haka sai tace
Ai kaine ya kamata ka duba madubin tsafinka ka gani da idanuwanka
Aikuwa cikin sauri ya bude tafin hannunsa
Take yaga lokacin da gimbiya lardisa ta ta rikide ta koma siffar gizo gizo
Ta makale ajikinsa lokacin da yake yawon shakatawa acikin wani daji dake yankin birnin sin lokacinda ya kaiwa mahaifinta ziyara
Har zuwa sanda ya kama hanyar dawowa wannan gidan nasa akan matashin aljaninsa
Duk tsawon lokacindaya dauka kafin yazo wannan gida nasa ba tareda tasha koda ruwan sha ba
WANNAN SHINE ABINDAYA FARU A CAN BANGAREN JARUMI RUKYAN BAYAN KADDARA TANA KOKARIN HADASHI DA WATA ABOKIYAR TAFIYAR
***** ********* ******************KARAGA­R AJALI
3 PART

****************** B

LBR
********************­ HABIBULLAH KBR

Acan gidan sarauta kuwa lokacin da sarki gulbas ya bayyana acikin turakarsa
Babu kowa acikin turakar sai shi kadai adaidai lokacin
ne wata kuyanga wacce take aikin share share acikin turakar ta bude kofa ta shigo domin yin aikinta
Shigarta cikin turakar keda wuya ta wuce can ciki da kayan aikinta
Kawai sai tayi arba da sarki gulbas, cikin razana ta kwarara
ihun neman taimako don a zatonta wani aljanin ke ya bayyanar mata cikin siffarsa
Cikin kankanin lokaci dakaru suka rugo da gudu cikin
turakar don ganin abinda yake faruwa
Koda sukayi arba da sarki gulbas sai dukkaninsu tsaya cak
Bisa rashin tabbacin sanin shine ko kuma bashi bane
Saida sarki gulbas ya daka musu tsawa sannan suka tabbatar da shine
Cikin sauri shugaban dakarun ta ruga da gudu cikin turakar gimbiya suhaila ta sanar da ita cewa ga sarki ya dawo
Take kuwa tabar abinda takeyi ta tafi cikin turakar tasa
Tana ganin halinda yake ciki saita umarci wata badakariya
dataje

Please Login or Register in order to submit comment