Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daukarsa ba
Kwakwalwarsa ta fara juyawa kamar wanda yasha giya ya bugu har yana neman tuntsurewa ya fadi kasa
Kawai sai aljanun suka jefo masa wata murtukekiyar sarka
Take sarkar ta kanannadeshi hannu da kafa
su kuwa sai suka kama sarkar suka jashi wani bangaren na gidan
Suna tafiya suna rera wata waka irin tasu ta aljanu kai tsaye suka wuce dashi cikin wata tangamemiyar fada wacce tafi dakin da suka baro girma da kuma fadi
Gaba daya fadar acike take da jinsin wadannan aljanu maza da mata a karshen fadar kuwa wata karagar mulki ce
Zaune akanta wani aljani ne ya murtuke fuskarsa sai kallon jarumi rukyan yake
Aljanun suna isowa sai suka wullar da shi kasa
Shugaban aljanun ya karewa rukyan kallo wanda aka wullar dashi kamar jikakken tsumma a gabansa
Sai kawai ya bushe da dariya daga can sai yamurtuke fuskarsa yace
Aikuwa wannan bil'adama ni da kaina ne ya kamata nayi watandarsa
Na tsotse jinin jikinsa sannan na baku gangar jikin nasa ku kachacchala ta da kanku
Yana gama fadin haka sai ya kai hannunsa ya shako wuyan rukyan
Ya dagashi sama take kafafuwansa suka fara reto asama yayin daya fara ganin taurarin wuya idanuwansa suka bubbulo sukayi jawur kai tsaye aljanin ya kai bakinsa kan wuyan rukyan da nufin ya gatsa shi
Koda jarumi rukyan yaga abinda ke shirin faruwa
Kawai sai yaji wani irin karfi yazo masa
Take yayi kwallara ihu ya tsitstsinka sarkokin da suke jikinsa
Kuma yasa kafafu ya jerawa aljanin duka dasu
Saboda
karfin dukan saida aljanin yayi baya taga taga kamar zai fadi amma sai gashi ya cake
Su kuwa aljanun duk sai suka zare idanu suna kallon abindake faruwa cikin mamaki
Cikin tsawa shugaban aljanun ya dubesu yace me kuke jirane maza ku kamashi ku aikata masa. kamar yadda muka saba yiwa duk wani bako daya shigo hannunmu
Dajin haka sai dukkaninsu sukayi kukan kura suka afka masa da. Nufin kowa ya yagi rabonsa
Aikuwa ba shiri shima ya zare takobinsa yayi karaji da kururuwa ya afkawa aljanun
Suna haduwa sai suka ruguntsume da azababben yaki
sai gashi aljanun su lullubeshi ta sama da kasa kamar kudajen zuma sunaso suyi masa taron dangi
Shi kuwa shi kadai atsakiyarsu sai ragargazarsu yake yi
Ya hana su samun damar abinda suke shirin aikatawa
Koda sun lullubeshi da zarar yayi katantanwa atsakiyarsu
Sai kaga sun tarwatse kamar anyi watsi da sillen Kara
Nan fa guri ya yamutse in banda sautin haduwar karafa babu abinda kunne keji
Kafin kace wani abu tuni dakin ya hautsine ya cika da iface iface

Sai gashi rukyan shi kadai a tsakiyar wadannan aljanu
Sun dabaibaye shi sun hana shi yin gaba ko baya saboda wasu mugayen hari da suke kawo masa
Kuma babban tashin hankalin shine
Da zarar takobinsa ta hadu da hannunsu saidai kaga tartsatsin wuta ya tashi
Idan kuwa ya sari jikinsu sai yaji kamar ya sari dutse ba tareda takobin ta ratsa jikinsu ba

WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GA JARUMI RUKYAN ACIKIN DAKI NA UKU

******* *********** ********
Al'amarin gimbiya suhaila kuwa lokacin da ta yanke shawarar cin amanar mahaifinta
Sai ta sake yin wani tunanin fara shirinta akan yadda zata yaudari jarumi rukyan
Don haka sai ta yanke shawarar ziyartar wani boyayyen bokanta acan bayan gari mai suna farraz bin sulkas
Boka farraz takadirin bokane na gani na fada wanda tsakaninsa da sarki gulbas
Kar ta san kar ne a fannin ilimin bokanci abindasu sarki gulbas suka fishi kawai shine karfin damtse
Da iya yaki domin ko kadan bai iya koda ruke takobi ba
Bare yayi yaki da ita wannan ne yasa ko kadan baiyi yunkurin shiga sawun masu takarar mallakar KARAGAR AJALI ba
amma kuma idan aka juya bangaren yaudara da cin amana babu kamarsa acikinsu
Don haka shima kiris yake jira da zarar sunje sun dauko TAKOBIN SAIFUL LAIHAM zai salallabo ya saceta ba tareda
Shi ya rigasu mallakar karagar ajali

Ba tareda bata lokaci ba suhaila ta fito daga cikin turakarta sanye da wata doguwar riga wacce ta matse jikinta gam ta kama hanyar fita daga gidan sarautar
Duk inda ta gifta ta gidan sarautar dakaru mata ne da kuyangi suke rissinawa suna gaisheta
Ita kuwa tana amsawa cikin fara'a da murmushi akan fuskarta
Tamkar wacce taga 'yan uwanta na jini
yana daga cikin dalilan da suka sa take son mallakar karagar ajali
Domin taga ta kwatowa mazaje 'yanci acikin birninsu
Tana matukar tausayin yadda mahaifinta yake muzguna musu har takai ga cewa
Babu sauran mazaje agarin face baki da suke shigowa
Idan kaga mace da juna biyu kuwa a garin to a cikin biranen makobtaka ta samo shi
Wannan rayuwa da suke ba karamin tausaya musu take ba
Tasan babu ta yadda zata cecesu daga wannan kuncin face ta riga mahaifinta hawa karagar ajali ta haka ne kadai zata ceci duniya daga azabarsa
Lokacin data fito wajen gidan sarautar sai kawai taga mutane sai gudanar da rayuwarsu suke kamar kullum
Koda sukayi arba da ita a wannan lokaci sai dukkansu suka bar abinda suke taho gurin ta suna gaisheta
Itama ta amsa musu gaisuwar tasu sannan ta zura hannunta cikin aljihun rigarta ta kwaso zinare mai yawa ta fara raba musu saida kowa ya samu
Sannan tayi musu sallama ta rikide ta koma siffar shaho ta tashi sama Cikin gajimare
Cikin azababben gudu kamar ba bil'adama ba su kuwa sai suka daga kansu suka bita da kallo har saida ta kure musu da gani
Sannan suka cigaba da harkokinsu, ita kuwa saita yi ta wannan gudun a saman iska
Don haka nan da nan ta fita daga cikin birnin gaba daya ta nausa cikin daji
Tafiya kadan tayi daga cikin birnin ta isa bakin kofar gidan boka farraz koda zuwanta sai ta sauka kasa ta koma zuwa ainihin siffarta
Kawai sai tayi arba da boka farraz a tsaye a kofar gidan fuskarsa cike da murmushi
Ahannunsa kuwa yana ruke da wata izgar tsafinsa da sanda
Cikin fara'a yazo ya tareta yace barka da zuwan gimbiya suhaila dirkar birnin ikarul izbar sannan yaja hannunta suka shige cikin gidan nasa

Wanda ya kasance madaidaicin gida ba mai girma sosai ba amma kuma an kawata shi sosai kamar gidan wani mashahurin attajirin
Da shigarsu cikin
Gidan kai tsaye sai suka wuce cikin wani daki wanda babu komai acikinsa face kayan tsubbace tsubbace
Suka sami guri suka zauna cikin fara'a boka farraz ya dube ta yace yake wannan 'yar sarki
Hakika nayi farin cikin zuwanki a yanzu kuma ki sani nasan duk abindake tafe dake da kuma dalilin zuwanki
Na san cewa kinzo ne domin sanin kowanene tsohon da kika hadu dashi jiya acikin birninku da kuma dalilin zuwansa
Sai kuma sanin hanyar da zakibi ki yaudari jarumi rukyan ko ba haka bane?
Dajin wannan tambaya sai suhaila ta gyada kai tace kwarai kuwa
Kawai sai Boka farraz runtse idanunsa yana nazari acikin ilimin
bokanci daga can kuma
yaci gaba da cewa ki sani shidai wannan tsoho da kika gani
idan duk matsafan duniya zasu hadu basu isa su iya sanin
kowaye shi ba saboda karfin sihirinsa sai dai idan sarki gulbas, boka surkais da jarumi rukyan sun ajiye gabar dake tsakaninsu sun hada sihirin tsafin su guri guda shine zasu iya saninsa
Kinsan kuwa wannan ba abune mai yiwuwa ba kamar yadda wuta da ruwa basa taba haduwa aguri daya
Saidai kuma binciken da nayi ya tabbatar min da cewa duk abindaya fada miki gaskiyane dole sai ya faru
Sai dai ni kuma zanyi miki kashedi guda daya karki kuskura da zarar kun hadu da jarumi rukyan karki bari soyayya ta shiga tsakaninki dashi
Domin shi namiji ne mai saurin jan hankalin 'yan mata
Idan kuwa har kikayi kuskuren yarda dashi to shikenan
bukatarki ba zata taba cika ba har abada
Hanyar kuwa da zaki bi ki yaudareshi itace da zarar kun sami nasarar dauko TAKOBIN SAIFUL LAIHAM saiki dauko wannan hodar ki hura masa ita afuskarsa da zarar kinyi haka shikenan a take zai rasa tunaninsa har abada ba zai kara dawowa daidai ba face
Saiful laiham ta dawo hannunsa mu kuma ba zamu taba barin hakan ta faru ba
Dazarar kin dauko wannan takobi sai ki garzayo wannan kogon nawa
ni ina da aljanin da zai iya daukar ki daga nan har zuwa darul maut
Kinga daga wannan lokaci kin zama sarauniyar sarakai wacce ba'a taba yin kamarta ba a tarihin duniya
Idan kika sami wannan matsayi bukatar da nake da ita agareki kawai itace
Inason ki bani karagar mulkin mahaifinki domin itace kadai bukatata
In yaso ke sai ki cigaba da mulkinki cikin kwanciyar hankali
Dajin haka sai fuskar ta ta fadada da murmushi ta mika hannu ta karbi wannan hodar
Tace hakika naji dadin wannan gudummawa daka bani ni kuma nayi alkawarin zan cika maka wannan burin naka duk wuya duk tsanani
Tana
gama fadin haka saita dauko wata jaka cike da lu'u lu'u ta mika
masa sannan ta juya ta sake komawa siffar shaho ta kama hanyar komawa cikin gari

Fitarta keda wuya sai boka farraz ya bushe da dariya yace
Hakika yaro yaro ne in banda hauka da kuma kuruciya irin nata
Tayaya inaji ina gani zata sami daukakar da babu wanda ya taba samunta kuma na zuba ido ina kallo harma na dinga yi miki bauta?
Ai wannan abune da bazan taba bari ya faru ba,
Da zarar
kin sami nasarar sato wannan takobi
Ni kuma anan zanyi amfani da dabarata karbe takobin
daga hannunki kuma na kasheki da ita
Ta yadda zai zama kura da shan bugu kato da kwashe kudi

Kamar yadda gimbiya suhaila tayi a fitowarta wannan karan bata dawo ainihin siffarta ba saidata shiga har cikin masarautarsu
Tun daga nesa da dakaru suka ga wannan shaho yana shirin giftawa ta saman
Gidan sarautar sai dukkansu suka zaro kibbau suka dana ajikin baka suka harba da nufin jefo shi saboda rashin yarda
Aikuwa koda kibiyoyin suka isa jikinta sai dukkaninsu suka kama da wuya suka kone kurmus
Tokar tasu ma ta tashi tabi iska
Koda dakarun sukaga wannan al'amari sai duk suka zare makamansu
Da nufin subi tsuntsun suyi masa kisan gilla ba zato ba tsammani sai kawai sukaga tsuntsun ya rikide ya koma gimbiya suhaila
Cikin biyayya dukkansu sukace barka da zuwa ya shugabar mu
Kiyi hakuri bamu san cewa ke bace,
dajin haka sai ta gyada kai tace ai wannan ba laifin ku bane
Kunyi ne acikin rashin sani da kuma kokarin kare wannan masarauta daga harin abokan gaba
Tana gama fadin haka sai ta wuce kai tsaye izuwa can tsakiyar gidan sarautar inda turakarta data sarki gulbas suke
Koda sai ta dauko wani hodar tsafi sannan ta kunna wuta
Ta zuba hodar acikin wutar yin hakan keda wuya sai wani irin hayaki ya tashi sama ya gauraye acikin iska
Cikin kankanin lokaci hayakin ya gama gauraye ko ina acikin birnin duk wanda yaga gimbiya suhaila a wannan rana
Da zarar ta shaki wannan iskar a take take mantawa da cewa ya ganta
Don haka take kowa ya manta da fitarta ko kuma shigowar ta garin kamar dai acikin mafarki suka ga wadannan abubuwa
Bayan ta gama da mutanen birnin saita wuce kai tsaye izuwa dakin tsafin sarki gulbas
Shima ta sihirce kayan tsafinsa gaba daya ta yadda ba zai taba sanin sirrinta ba tako wanne hali
Sannan ta fito ta kama hanyar komawa tata turakar
Kamar bata shirya komai ba

SHIN SARKI GULBAS YANA GANO SHIRIN DA GIMBIYA SUHAILA TAKE AKANSA?
SHIN GIMBIYA SUHAILA TANA GANE NUFIN BOKA FARRAZ?
TAYA JARUMI RUKYAN ZAI KUBUTA DAGA HANNUN WADANNAN MAYUN ALJANU?

SHIN BINCIKEN DA SU GIMBIYA SUHAILA SUKAYI YANA ZAMA GASKIYA CEWA IDAN TA HADA KAI DA JARUMI RUKYAN ZASU SAMI NASARAR MALLAKAR SAIFUL LAIHAM?

YAUSHENE SU BOKA SURKAIS ZASU GAMA KARBAR HORON SADAUKI FARHAN?

DON JIN AMSAR WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA
NAKU
HABIBULLAH KBRKARAGAR AJALI

*********2 PART C

LBR

HABIBULLAH KBR

Lokacinda wadannan macizan suka yi tsalle sukayo kan boka surkais da nufin su dura masa dafin dake bakunansu
Sai yayi sauri ya kwanto garkuwarsa daga gadon bayansa ya tare harin nasu
Sannan yayi watsi dasu suka fadi can gefe guda kamar busassun karare
Aikuwa dukkansu sai suka juyo inda yake suna wani ruri
Sannan sukayi masa rubdugu cuna kawo masa harbi nan da nan shima ya fito da takobinsa ya fada cikinsu
Suka ruguntsume da azababben yaki tsakaninsa da macizan
Duk inda ka kalla saidai kaga macizan suna yawo ta samansa kamar kamar iska don ganin bayansa
Shima kuwa sai ya dage yaki bari damar Hakan ta samu a garesu
Kuma wani babban abin mamaki game da wadannan macizai shine karfin su
Da kuma zafin namansu wanda yasha banban da irin macizan daya saba gani a duniya
Domin duk da kankantarsu idan suka kawo masa sara ya tare da garkuwarsa
Sai yaji duk jikinsa ya amsa saboda karfin da suke da shi
Kuma babu wani abu da zai daure maka kai game dasu face yadda kamar su tazo daya
Babu wani banbanci ajikinsu kamar sune sukayi kansu
Ta yadda komai ruwan idon ka baka isa ka gane banbancin dake tsakaninsu ba
Nanfa guri ya yamutse saboda suke kawo masa hari
Duk inda boka surkais ya waiga babu abinda yake gani face wadannan mayatattun macizai
Shi kansa boka surkais ya tabbatar da cewa bai isa ya iya ratsawa ta cikin wadannan macizai ba
Ya wuce face basa numfashi amma babban abin tambayar shine
Tayaya ne zasu mutu alhalin duk abinda yake musu basa ji?
Kai saida suka shafe sa'a bakwai suna wannan fafatawa ba tareda dayansu
Ya sami nasara akan daya ba kuma har a sannan ya gaza gane asalin mahaifiyar macizan
Suna cikin wannan hali ne cikin rashin sani kafarsa ta dama ta zame ya fada cikin wani kwazazzabo dake cikin kogon
Ai kuwa take ya sulale ya fada ciki gaba daya, koda ganin haka sai suma macizan suka bishi cikin kwazazzabon sukayi masa kawanya
Ai kuwa acikin wannan haline wani daga cikinsu ya sami nasarar saransa a gadon bayansa
Take boka surkais ya kwarara uban ihu saboda tsananin zafi da zugin da yaji
Cikin dakika daya yaji kamar jijiyoyin jikinsa sun tsinke
Kawai saiya tuna da bayanin daya karanta a farkon shogowarsa wannan kogo game da karfin dafin da suke dashi
Kawai sai yayi kukan kura ya tarwatsa macizan da karfin tsiya
sannan yayi tsalle daga cikin ramin kamar daga cikin baka aka harba shi
Ya fice daga cikin kwazazzabon sannan ya sake yin wani tsallen guda daya ya cizgi wannan jijiyar bishiyar da bakinsa ya tauneta
Aikuwa yin hakan keda wuya sai yaji ya daina jin wannan zafi da radadin da yakeji
Sannan yaji wani sabon kuzari ya shigeshi kamar ma yanzu suka fara fadan

Kuma. Adaidai wannan lokacin ne yaga yanayin launin macizan yana sauyawa Ma'ana suna banbanta da juna
Kwatsam sai ya hangi wata guda daya daga cikin su wacce kanta yafi na kowanne kankanta
Koda yayi arba da wannan guda dayar sai yayi maza yasa takobinsa ya datse mata kai da ita
Take kuwa kan nata ya tsinke daga jikin gangar jikin nata
Suma kuma ragowar macizan a take kawunansu suka tumbuke daga jikinsu suka fadi kasa matattu kamar basu taba wanzuwa ba
Koda boka surkais yaga wannan nasarar daya samu
Sai ya kamu da tsananin farin ciki ya sami guri ya zauna ya huta tsawon wani gajeren lokaci
Ya tashi ya nufi kofar shiga daki na gaba

WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GA BOKA SURKAIS
***** ****** ******
Al'amarin sarki gulbas kuwa lokacin daya sami nasarar ketare dakin fatalwu sai ya cigaba da tafiya acikin wajnan gida har ya isa bakin kofar daki na gaba
Tun kafin ya karaso bakin kofar sai kofar ta bude da kanta wanwar
Tun a bakin wannan kofar ya fara hango abubuwan da suke cikin dakin
Ba komai ya gani ba face gumaka wadanda aka sassakasu da zallan duwatsun wuta cikin wata irin siffa mai ban tsoro
Kuma kowanne daga cikinsu siffarsa ta banbanta data dan uwansa wajen girman jini da kuma kirar halitta
Da ganinsu an samo su ne daga mabanbantan kabilu
Kuma daga nahiyoyi daban daban kowanne daya daga cikinsu kirar jikinsa a murde take
Kuma yana ruke da almudi na bakin karfe a hannunsa
Kai tsaye sarki gulbas ya danna kansa cikin dakin ba tareda shakkar Komai ba
Duk da cewa yasan ruwa baya tsami banza dole akwai tuggun da aka shirya ajikinsu
Haka dai ya kutsa kansa Cikin dakin ya fara ratsawa ta tsakiyar gumakan ba tareda dayansu ya motsaba
Kai saboda tsabar dadewar da sukayi a wannan yanayin har gizo gizo yazo ya gama nadesu da yana kura kuma ta lullube su
Amma kuma kasan dakin babu komai face kashushuwan mutane wadanda saboda dadewa har ruburbushewa suke yi
Da ganin wadannan kashushuwa sai yace
Oh ! Hakika duniya daban tsoro take yanzu suma wadannan azamaninsu jarumai ne na gaske
Amma saboda neman daukakar duniya, suna da kuma sarautar da babu wanda ya taba samun kamarta a zamaninsu
Amma yanzu gashi duk. Sunyi babu ba tareda sun sami cikar burinsu ba
Koda yin wannan tunani sai yaji zuciyarsa ta buga da karfin gaske
Kamar zata fasa kirjinsa ta fito waje
Ya tambayi kansa yace yanzu nima idan nayi kuskure kadan shi kenan nima anan tarihin rayuwata zai tsaya duk wahalar danasha a baya ta tashi a banza kenan tunda nan da wani lokaci za'a manta da tarihina?
Koda yin wannan tambayar sai yaji hankalinsa ya tashi ya kuma dugunzuma
Yace aikuwa karyane ta kowanne irin hali sai nabi na fita daga wannan gida lafiya
Koda kuwa zan rasa sassan jikina gaba daya bazan bari su jarumi rukyan su rigani mallakar karagar ajali ba
Ai. Kuwa yana gama wannan tunanin sai yaji zuciyarsa ta kekashe ga barin tunanin mutuwa yaji kamar shi kadai zai iya zare makami ya yaki duniya gaba ki dayanta kuma ya sami nasara cikin kankanin lokaci
don haka sai ya ci gaba da kutsa kansa cikinsu kamar yana tafiya acikin gidansa
Amma kuma ya kasa kunnensa yana sauraron duk wani sauti na cikin dakin domin yasan koda yaushe za'a iya kawo masa hari
Haka dai yaci gaba da tafiyarsa ba tareda wata fargaba ba
Yana cikin tafiyar ne kawai yaga wata walkiya gami da tsawa sun ratsa dakin wanda sautinta kadai ya isa ya razana mutum
Faruwar hakan keda wuya sai dukkansu cikin abinda bai wuce dakika guda ruhi y shiga jikinsu gaba daya
Aikuwa ruhin yana shiga sai daya daga cikinsu ya daga takobinsa
ya kaiwa sarki gulbas mahaukacin sara da nufin ya zaftare masa kai
Cikin bakin zafin nama sarki gulbas ya sunkuya ya ya kaucewa takobin
Amma duk da haka sai da kaifin takobin ya zaftare masa saman gashin kansa
Kafin ya dago wani ma ya sake kawo masa wani saran
Kafin kaifin takobin ya sauka ajikinsa tuni ya gangara ya kauce daga gurin ya mirgina can gefe daya
Tun kan ya karasa mikewa tsaye tuni alokaci guda dodannin suka kawo masa wasu sara da suka da makaman su
Cikin zafin ya daga takobinsa ya tare makaman nasu da ita ba tareda makami guda ya sauka ajikinsa ba
Wani tartsatsin. Wuta ya harda turirin hayaki daya daga cikin dodannin kawai ya shammace shi ta baya ya gabza masa naushi da dunkulallen hannunsa wanda saboda tsabar murdewarsa kace manyan duwatsu aka cuccure
Saboda karfin dukan saida sarki gulbas yayi sama yana layi
Kafin ya diro kan kasa sai wani ma daga cikinsu ya gabza masa naushi akan fuska
Take hancinsa da bakinsa suka fashe jini yayi tsartuwa daga cikinsu takobinsa kuwa saidata subuce daga hannunsa ta fadi gefe guda
Ai kuwa sai suka sami damar saka shi a tsakiya suna ta ragargazarsa da kafafunsu da kuma hannaye tako'ina
Ai kuwa cikin kankanin lokaci suka hada masa jini majina saboda karfin dukan nasu
Domin sai da yaji kamar kashushuwan jikinsa zasu karye
Nan da nan ya fara fita daga hayyacinsa idanunsa suka fara gani dishi dishi
Nanfa ya tuna da wahalar daya sha a baya tun farkon shigowarsa cikin wannan
Da kuma sa'ar daya samu ta wuce sauran matakan tsaron gidan, kuma idan har baiyi da gaske ba duk wahalar baya ta zama ta banza kenan
Koda yin wannan tunani sai yayi karaji yasa hannunsa ya goge jinin da yake zuba daga hancinsa
Cikin bacin rai da fusata ya daka tsalle ya kama hannun daya daga cikinsu
Ya saka gwuiwar kafarsa ya dake shi da ita aikuwa take hannun nasa ya karye baras
Dodon ya kwallara wani irin azababben ihu wanda sautin sa yasa
Sauran dodannin suka tsaya cak da kawo masa hari don ganin abinda ya sami dan uwansu
Damar da ya samu kenan ya sunkuya ya dauki takobinsa daga kasa
Ya kutsa cikinsu Suka kaure da yaki mai matukar razanarwa
Duk inda ka duba babu abinda zaka gani face tartsatsin wutar haduwar makaman su
Guri yayi matukar yamutsewa saboda kwarmatsuwar da suke yi sai da suka shafe sa'o'i bakwai suna wannan bakin gumurzu sannan sarki gulbas ya sami nasarar kubuta daga hannunsu

WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GA SARKI GULBAS
***************************************

Al'amarin jarumi rukyan kuwa lokacin da suka ruguntsume da masifaffen yaki da wadannan aljanu
Sai ya fuskanci cewa ta cikin kwayar idonsu suke zuba masa arwa muddun kuwa zai bar idonsa abude yana kallon nasu to bai isa ya iya daukar lokaci mai tsawo yana yaki dasu ba
Don haka ba shiri ya yage hannun rigarsa ya daure idanunsa tamau da shi
Kuma ya cigaba da yaki dasu din kamar idanuwansa basu kasance a rufe ba, amma a wannan karon babu abinda yake amfani dashi face sautin motsinsu ta yadda ko numfashi sukayi yana iya sauraronsu kamar idanunsa abude suke
Nanfa yaki yayi matukar tsamari guri ya hautsine kamar ana yakin duniya
Sai dai kuma duk wannan abu da akeyi ya kasa samun damar koda yankan daya daga cikinsu haka suma sun kasa lakutar jikinsa saboda yadda yake da zafin nama kamar maciji
Wohoho!! Hakika idan kaji ana ga ki gudu to sa gudu ne bai zoba
Kuma inda babu kasa nan ake gardamar kokawa duk wannan yawa da aljanun suke dashi sai ya zama na banza domin bil'adama guda daya yana nema ya zame musu alakakai
Su kansu basu taba ganin bil'adama ko aljani mai matukar taurin rai da zafin nama kamarsa ba
Domin sunyi iya yinsu don ganin sun kamashi da hannayensu amma sun kasa samun damar hakan ,

Koda sarkin aljanun yaga abinda yake faruwa sai ransa
ya baci zuciyarsa ta fara harzuka kai kace ana Aza wuta ne acikinta
Kawai sai ya dakawa dakarun nasa tsawa wacce sautinta ya cika fadar gaba daya
Take duk ragowar aljanun suka ja da baya a mataukar razane
Take ya sauko daga kan karagar mulkin sa yana tafiya kasa na amsawa
Shidai wannan aljani ya kasance gabjejen gaske wanda siffarsa ta banbanta data ragowar domin Komai nasa ukun nasu ne
Ma'ana tsawo, kauri, hannaye, fuka fukai da dai sauransu
Sai a sannan ne rukyan yasan irin kirar da aljanin yake da ita
Domin dazu bai kula da hakanba kasancewa baya cikin hayyacinsa
Amma yanzu da kunnuwansa yana iya jin motsin motsawar kafafuwansa da kuma fuka fukansa
A hankali aljanin ya zura hannauyensa guda hudu ya zaro makaman yakinsa
Hannu daya gatari ya ruko daya Kuma adda ce daya kuma takobi dayan kuwa mashi
Ragowar hannayen kuwa babu komai ajikinsu yazo ya tsaya agaban rukyan yana mai fuskantar sa
Ai kuwa take rukyan y falfala da gudu ya fuskanci aljanin
yana zuwa daidai inda yake sai ya daka tsalle sama da nufin yayi masa fashin albasa
Take aljanin ya sunkuya takobin ta wuce sannan yasa hannunsa guda daya ya bugo jarumi rukyan dashi
Nantake ya wuntsila ya fadi kasa kan fuskarsa, saboda karfin faduwar da yayi saida goshinsa da bakinsa suka fashe
Koda ganin wannan nasara sai aljanin ya bushe da dariyar mugunta wacce ta ratsa ko ina acikin fadar tareda amsa kuwwa
Daga can kuma sai ya murtuke fuska kamar an aiko masa da sakon mutuwa
Sannan ya sunkuya ya kama Gashin kan jarumi rukyan ya daga shi sama yadinga gwara fuskarsa da jikin dirkar gini
Har saida yayi masa jina jina sannan yayi wulli dashi yaje ya bugu da gini saboda karfin dukan sai da yaji kamar duk kashushuwan jikinsa sun kakkarye
A wannan lokaci ko hannunsa ma da kyar yake iya dagashi
Take aljanin ya juya da baya ya kyaleshi a gurin ya dubi
wasu dakaru yace kuyi maza ku daureshi ku daukeshi ku kaishi can marataya ku rataye shi
Kuma kada ku kuskura ku bari ya kwace daga hannunku
Ni da kaina zanyi gunduwa gunduwa da namansa kuma da ransa harsai ya mutu sannan nayi farfesunsa tunda ku kun kasa koda kamashi
Dajin haka sai dakarun suka russina gaba dayansu tareda cewa an gama ya shugaban tawagar mayu
Da gama fadin haka sai suka sunkuya suka azamasa sarkoki ajikinsa
Sannan suka ciccibeshi acikin mawuyacin hali mai kama da rayuwa ko mutuwa suka wuce dashi can dakin rataya.
WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GA JARUMI RUKYAN LOKACIN DAYA FADA TARKON JINSIN MAYUN ALJANU
************ *************
Acan gidan sarauta kuwa lokacin da gimbiya suhaila ta shige cikin dakin ta shiga sai ta aika wata badakariya domin ta kirawo mata Wata kuyanga mai suna ruwaisa
Take kuwa badakariyar ta cika umarni cikin kankanin lokaci sai ga kuyanga ruwaisa ta hallara acikin turakar
Arayuwar gimbiya suhaila babu wacce ta yarda da ita kamar kuyanga ramsiya domin tun suna yara suka taso atare acikin gidan sarautar don haka akwai amana mai karfi a tsakaninsu
Cikin biyayya ruwaisa tace me kike da bukata ya shugabata?
Dajin wannan tambayar sai gimbiya suhaila tayi mata nuni data zauna akan kujerar data ke fuskantar tata
Ba tareda bata lokaci ba ta sami guri ta zauna
Zamanta
keda wuya sai gimbiya suhaila ta mike tsaye ta dinga bin kowacce kusurwa ta dakin tana karanta wasu
dalasiman

Please Login or Register in order to submit comment