Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sha domin rage kokwanton da yake cikin zuciyarta
kwanciyarta keda wuya sai barci ya saceta bata sani ba
Tana farkawa saita tashi taje ta watsa ruwa ta wanke fuskarta ta
Kafin ta fito daga wankan tuni kuyangi sun ajiye mata abinci da abin sha kala daban daban akan wani teburi dake tsakiyar turakar tata
Ba tareda bata lokaciba ta zauna ta kai hannunta da nufin cin abincin
Har hannunta yakai bakin kwanon abincin kawai saita tuna da maganar tsohon data gani jiya
Ta tambayi kanta tace shin menene yake shirin faruwa dani?
Kuma me yasa wannan mutumin ya tafi ba tareda ya amsa mini tambayoyi na ba?
Ya zama dole na kara bincike akan wannan bakon jarumi daya bani labari akansa
Kuma nasan hanyar da zan bullo masa domin nima
na samu na biya bukatar dana dade ina burin cikawa
nasan lokaci ya kusa da zan jefi tsuntsu biyu da dutse daya
Tana gama fadin haka saita juya taje ta shafi wani madubin tsafi
Wanda yake makale ajikin bangon turakar tata
Yin hakan keda wuya take sai hoton jarumi rukyan ya bayyana
Lokacin da yake fafata kazamin yaki da wannan dodon acikin daki na biyu
Koda tayi arba da kyakkyawar surar jikinsa da kuma jarumtakar da yake da ita
Sai taji take zuciyarta ta buga da karfi ta tambayi zuciyarta
tace dama aduniya akwai namiji mai irin wannan kyau da jarumtaka kamar mahaifina?
Indai kuwa har yana da wannan karfin damtse dolene Sai mahaifina yayi da gaske sannan zai sami nasara akansa
Ni kuma idan har inaso bukatata ta biya ya zama dole na hada nabi ta kowacce hanya mu fita neman karagar ajali da mahaifina
Sannan na gudu gurin jarumi salyar na yaudare shi da soyayyata
Kuma mu nemo saiful laiham tare
Inyaso ni kuma daga baya sai inci amanarsa na sace wannan takobin
Daga baya naje na hau KARAGAR AJALI
Shikenan daga wannan lokaci na zama sarauniya ta farko wacce zata mallaki duniya
Koda hakan kuwa zai janyo sanadin raba alakar dake tsakanina da mahaifina
Koda gama fadin haka saita tuntsure da dariya sannan ta shafi madubin tsafin hoton komai ya dauke
******* ********* *******
Acan cikin dakin halwar tsafin sarki gulbas kuwa tun a ranar dasu jarumi rukyan suka fara karbar horon sadauki farhan
Shima a wannan ranar ya fara bisa wakilcin wani takadirin aljani mai suna luzzab
Yanzu haka yana matakin farko acikin wata nahiya daban ba wacce ya saba gani ba a rayuwarsa domin duk yawon da yayi bai taba tsintar kansa acikin daji
Makamancin wanda yake ciki ayanzu
Shidai wannan dajin babu komai acikinsa face wata sahara
Mai zafin gaske wacce babu wata halitta mai numfashi asamanta hatta tsirrai babu
Saboda zafin da saharar take dashi har turiri ne yake tasowa ta kasanta
Tun farkon shigowarsa cikin dajin makogaronsa ya bushe
Yaji ya kamu da tsananin kishirwa kuma babu inda zai je ya sami ruwa acikin wannan saharar
Haka dai ya daure yaci gaba da tafiya abinsa ba tareda sanin inda ya dosa ba
Sai da yayi tafiya mai nisa akan saharar alokacin ya fara galabaita sosai
Kawai sai ya hango wata korama daga can nesa kadan daga inda yake
Koda ya hangi wannan koramar sai farin ciki ya kamashi
Ba shiri ya nufi wannan koramar don ya sha ruwan dake cikinta
Sannan ya cika battarsa da ruwan don yayi guzuri dashi ya kara gaba
Cikin sauri ya karasa bakin koramar da isarsa sai ya sunkuya yakai hannunsa
Da nufin ya kwarfo ruwan ciki yasha har hannunsa yakai saman ruwan
Kwatsam sai gani yayi wata bakar kunama tayi fitar burgu daga kasan koramar tasa hannunta guda
Ta zabga masa naushi dashi take yayi sama kamar an ya luluka acikin iska
Tun kafin ya dawo kasa tuni kunamar tayi wani gunji
ta fita da gudu zuwa inda yake ta tsayar da karinta tana jiran dawowarsa ta tsire shi
Koda ya leko da kansa yaga mugun tanajin da kunamar
tayi masa sai ya kara wani tsallen a saman iska ya juya jikinsa ya dira acan nesa da inda kunamar take
Yana bisa digadigansa ya kurawa kunamar ido
Nanfa aka tsaya ana kallon kallo tsakaninsa da kunamar
Shi dai ya rasa wanne zabin zaibi tsakanin ya tari kunamar suyi yaki
Ko kuma su yaje wannan korama ya sha ruwan ruwan dake ciki
Tunda awannan lokaci babu abinda yake damunsa face tsananin kishirwa
Sai dai kuma gashi koda zaije bakin koramar dolene sai ya fafata da wannan kunamar tunda ba wata hanya da zaibi face ya ratsa ta gabanta

Nanfa ya rasa zabin daya kamata yabi. Yana cikin wannan tunanin ne kawai yaga kunamar ta sake tahowa
inda yake gadan gadan cikin mugun nufi tana gudun kasar gurin tana amsawa saboda tsananin girmanta
Arayuwar sarki gulbas tunda yazo duniya bai taba ganin kunama mai girma da muni kamar wannan kunamar ba
Domin kana ganinta kasan ba halittune wanda ka saba gani ba
Dole an samar da itane cikin ilimin bokanci domin biyan wata bukatar

SHIN SARKI GULBAS, BOKA SURKAIS DA JARUMI RUKYAN SUNA KUBUTA DAGA CIKIN TARKUNAN MUTUWAR DA SUKA FADA KUWA ?
TAYA GIMBIYA SUHAILA ZATA IYA RISKAR JARUMI RUKYAN HAR TA YAUDARESHI TACI AMANARSA?
SHIN ACIKINSU WANENE YAKE DA SA'AR DA ZAI MALLAKI KARAGAR AJALI?

DON JIN AMSOAHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA DAGA NAKU
HABIBULLAH KBR
WHATSAPP NO 09081494322
LIKE AND COMMENTS ARE OUR************KARAGAR AJALI

********-----*2 PART A

LBR

***********HABIBULLAH KBR

Whatsapp no
09133502477

Lokacin da sarki gulbas da wannan kunamar suka tsaya sukayi cirko cirko suna kallon juna
Sai kawai sarki gulbas yayi kukan kura yayi fitar burgu ya afkawa mata
Suka kachame da bakin artabu mai matukar muni shi da ita
Ya zamana cewa kowannensu yana kaiwa abokin gwaminsa mugayen hare hare
Saidai kunamar ta ninka sarki gulbas sau biyar a karfin damtse da kuma kuzari
Aduk sanda ta kawo masa sara da karin dake jikinta da zarar ya kauce
Saidai kaga bakin ruwa mai yauki yana feshi daga jikin karin nata
Nanfa guri ya yamutse kura ta tashi ta turnuke a sararin samaniya
Inbadon yana da tsawon rai ba da kuma matukar zafin nama da tuni kunamar tayi kacha kacha dashi
Itadai wannan kunamar ta dage sosai wajen ganin ta hallaka shi
Shi kuwa burinsa kawai yaga ya tsira yaje ya sha ruwan wannan koramar don gusar da kishirwar data addabeshi
Amma babban tashin hankalin shine har tsawon wannan lokacin da suka diba suna
Wannan fafatawa shi ya kasa samun nasara ko kadan akanta
Saboda yadda take kawo mai mugayen hare hare yana kaucewa
Saida suka shafe dakiku masu yawa suna fafatawa ba tareda daya ya sami nasara akan daya ba
Kuma duk. Sanda sarki gulbas ya sami nasarar sara ko kuma ya soki jikin kunamar da tsinin takobinsa
mai makon takobin ta huda jikin saidai kaga tartsatsin wuta ya tashi kamar haduwar karfe da karfe
Saidai kaga kunamar tayi jijjiga kamar ma kara mata kuzari yake kara mata
Ma'ana dai bata da wata makasa ajikinta
Abinda bai sani ba shine ba zata taba mutuwa ba face yasha ruwan wannan koramar domin shine kadai makashinta

Koda aka shafe wasu sa'o'i uku ana wannan hali sai ya zamana gaba daya sarki gulbas ya fita daga hayyacinsa
Saboda tsananin kishirwar dake addabarsa ya zamana hatta yawun bakinsa ma ya bushe

Don haka babu sauran kuzari ajikinsa da kyar ma yake iya kare hare haren da take kawo masa
Nanfa ya fara tunanin hanyar daya kamata yabi don tsira daga sharrin wannan sihirtacciyar kunamar
Don ya tabbata muddun aka cigaba da wannan fadan
acikin wannan hali sai ya zamana cewa
Kare harin nata ma ba zai iya ba daga nan shikenan ta sami nasara akansa kuma za'a rufe tarihin gwagwarmayar da yayi abaya
Muddin bai mallaki karagar ajali ba
Don haka dole ya samarwa kansa mafita kota halin kaka ya samu ya sha wannan ruwan
Kafin lokaci ya kure masa
Koda gama wannan tunanin sai yaja da baya kamar taku goma
Sannan ya kara falfalowa da gudu kamar zai yi gaba da gaba da ita
Koda yazo daidai inda take sai ya zame ya kwanta ya wuce ta karkashinta
Sannan ya mike ya nufi koramar da gudun gaske
Wohoho nanfa aka kasa tsere atsakaninsu
Ya dage iya karfinsa yana gudun ceton ransa itama kuwa ta biyoshi da dukkan karfinta tana domin ceton tata rayuwar
Duk wannan gudu da sukeyi tazararsu bata wuce taku goma ba
Don haka sai dada kawo masa sara take da karin nata
Kafin ya shiga cikin koramar da zarar ta kawo masa harbi saidai kaga
Ya zame masa ko kuma yayi tsalle ya kaucewa karin nata
Cikin kankanin lokaci ya isa bakin koramar yana zuwa
Ya daka tsalle ya afka cikinta yayi nutso akasanta ya bude
bakinsa ya fara kwankwadar ruwan
Aikuwa ruwan yana shiga cikin bakinsa take kunamar ta kama da wuta
Ta kone kurmus koda sarki gulbas ya gama shan ruwan koramar
Sai yayi ninkaya a saman koramar da nufin ya fito daga cikin ta
Kwatsam sai yaji kasan koramar ta dare wata iska mai karfi ta fito daga ciki ta jashi can kasanta
sannan komai ya koma daidai kamar yadda yake abaya
Koda iskar ta zukeshi zuwa kasan koramar sai ya tsinci kansa acikin wani tafkeken gida
Wanda akayi masa gini irin na tsofaffin gidajen tarihi na birnin farisa
Saboda yadda ginin gidan yakeda matukar tsawo da dogayen dirkoki
Saidai kuma ko ina acikinsa cike yake da yanar gizo gizo ta yadda baka isa ka matsa gaba ba face ka share wannan yanar da hannayenka
Shi dai wannan daki babu alamun akwai wata halitta mai rai acikinsa saboda yadda gidan yayi tsit
Ajikin bangon gidan kuwa an cikashi da zanikan halittu masu firgitarwa
Wadanda kallon su kadai ya isa ya kawarwa da mutum kwanciyar hankali da nutsuwa har iya tsawon rayuwarsa
Koda sarki gulbas yayi arba da wadannan kalar zanika
Saiya girgiza kansa yace lallai wannan karaga taci sunanta KARAGAR AJALI
Kuma duk wanda baiyi yawon duniyaba bazai san wahalar dake cikinta da kuma dadinta ba
Tabbas duk yadda akayi akwai halittu masu matukar hatsari acikin wannan daki kafin na shiga na gaba na tarar da abinda yake cikinsa

Koda gama ayyana haka sai ya dora hannunsa guda akan kufen takobinsa
Kuma ya kara gyara damararsa yaci gaba da kutsa kansa acikin gidan
Har ya wuce ta cikin dakuna guda goma bai hadu da wani abin cutarwa ba
Sai a daki na sha dayan ne ya fara jin wani sauti yana giftawa ta cikin kunnensa
Kamar sautin giftawar iska, nanfa ya fara waige waige da dube dube
Ko zaiga abinda yake giftawa amma sai yaga babu komai
Amma duk da haka yana jin sautin acikin sautin har wata dariya ake kyakyatawa
Shi kansa wannan ihun ya isa abin firgitarwa da razana mai sauraro
Yana cikin wannan hali ne kwatsam sai yaga kasa ta tsage wasu irin fatalwoyi suka dinga tasowa daga cikin kasar
Adadin wadannan fatalwun kuwa ya zarce guda dari biyar da doriya
Kowanne daga yana ruke da wasu gajerun adduna guda biyu
Bakinsu kuwa cike yake da zakwa zakwan hakora masu kaco kaco birjik abakinsa masu tsini ba kyan gani
Idanunsu kuwa sun rine sunyi jawur kamar an gasa dan buda a wuta
Kai da kagansu kasan fatalwu ne masu shan jinin dan adam
Koda gama fitowar wadannan halittu duk sai sukayiwa sarki gulbas kawanya suka soma kewaye shi
Ta gaba da baya suna zagaya shi taredayin wani gurnani mai firgitarwa
Daga can kuma sai suka afko masa da dukkan karfinsu
Suna masu karaji da kururuwa take shima ya zare takobinsa daga cikin kufenta ya afka musu da dukkan karfinsa
Suna haduwa suka kachame da azababben yaki a tsakaninsu
Ya zama shi kadaine a tsakiyar wadannan fatalwu suna masu kawo masa sara da suka
Tako wanne bangare domin suyi gunduwa gunduwa dashi
Nanfa guri ya yamutse in banda karar karafkiyar karafa babu abinda kunne keji
Inda acewa mutum zai tsaya kallo alokacin da suke wannan bakin artabu sai yayi zaton sarki gulbas ba mutum bane
Saboda yadda yake da matukar bakin zafin nama kamar
Shaidani dukda yawan wadannan fatalwu sai gashi yana
kare duk harin da suke kawo masa kuma alokaci guda ba tareda Wani ya sami nasarar lakutar koda gefen rigarsa ba
Saidai babbar matsalar daya fuskanta guda daya ce
Takobinsa ko kadan bata lakutar jikinsu da zarar ya kai musu sara ko suka sai dai kaga takobin ta ratsasu ta wuce ba tareda ta illata su ba Ma'ana dai kamar ya sari haske ko kuna inci iska
Gaba ki daya dakin ya cika da sautin karafkiyar karafa
Ya zamana duk inda ka waiga babu abinda zaka gani face dakarun fululu kuma duk yawansu mutum daya suka tararwa
Ana cikin wannan fafatawa ne wani daga cikinsu ya shammaceshi ya daga addarsa ya kafta masa sara agadon baya
Take gadon baya nasa ya dare jini yayi tsartuwa daga gurin raunin
Take sarki gulbas ya kwallara ihu saboda zafi da zugin da yaji
Cikin karaji yayi kukan kura atsakiyarsu irin wanda ke firgita mazan fama a filin daga
Saboda karajin da yayi saida sukaja da baya suna kallonsa
Take ya yagi rigarsa ya daure raunin da sukayi masa
Suka sake dawowa suka ci gaba da bakin artabu babban abinda ya baiwa sarki gulbas mamaki game da wadannan fatalwoyi shine
Yadda takobinsa
Take iya haduwa da makaman hannunsu amma kuma bata iya ratsa jikinsu
Wani lokacin ma makaman hannun nasu har subucewa suke su fadi kasa amma kuma sai yaga sunyi zumbur sun sunkuya sun dauki makamin
An cigaba da yakin
Nanfa ya tabbatarwa da kansa dole akwai wani sirrin dangane da wadannan makamai
Ba tareda bata lokaci ba ya canja salon fada ya zamana
Babu abinda yake yi face yunkurin yaga ya buge makamansu daga hannayen nasu
Saboda ko kadan ya daina mai da hankalinsa akan sukar jikinsu
Gaba daya ya tattara karfinsane wajen kaiwa makaman nasu duka
Ai kuwa cikin sa'a daya daga cikinsu ya kawo masa sara da addarsa
Take sarki gulbas ya kauce yasa kafarsa ya daki kotar addar
Take addar ta kwace daga hannun nasa tayi sama
Cikin zafin nama sarki gulbas ya daka tsalle yabi takobin sama ya cafketa
Tun kafin ya diro kasan ya kaiwa mai addar sara da ita
Nan Take kansa ya tsinke daga jikin gangar jikin ya fadi kasa
Koda fatalwun suka ga haka suka kara yunkurowa da karfinsu
Suka kara kachamewa da wani sabon yakin wanda yafi na farko
A wannan lokaci sai ya zamana cewa yaki yasha banban
Sarki gulbas inbanda muguwar barna babu abinda yake yi musu
Duk inda ya ratsa acikinsu saidai kaga yana zaftare kawunan su
Da hannayensu yana gididdiba su kamar ana sassabe agona
Nanfa guri ya rinchabe ya hautsine inbanda ihun Wadannan fatalwu babu abinda kunne keji
Su kuwa kara danno kai suke ba tareda suna tsoron mutuwar ba
awannan lokaci sunga bala'in da basu taba gani ba 🙂🤣domin tun suna turo kansu sai daya zamana sun fara ja da baya saboda ganin mutuwa muraran da sukayi da idanunsa
Kafin a kara daukar wani lokaci mai tsawo tuni sarki gulbas ya gama karar dasu duk sun dagargaje sun baje akan kasa tamkar ba'a taba tashinsu ba
Don haka sai sarki gulbas ya sunkuya ya dauki takobinsa ya maidai ita acikin kufenta yaci gaba da kutsawa ta cikin dakunan wannan gida

WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GA SARKI GULBAS BAYAN YA KUBUTA DAGA TARKO NA FARKO DA KUMA NA BIYU
********* ************* ****
Al'amarin boka surkais kuwa lokacin da suka kasa tseren gudu da wannan wutar sihirin
Saida suka shafe sa'o'i masu yawa suna gudu ba tareda ya tsaya da gudunba
Kuma yana gudun yana nazarin yadda zai koma da baya domin bude kofar shiga
Cikin wannan gida don tsallake matakin farko da kuma ragowar matakan
Yana cikin gudun ne kawai yajiyo kugin wutar daga bayansa
Cikin sauri ya waiwaya bisa mamaki sai yaga wata murtukekiyar bulalar haske tana dukan wutar tana korata baya
Koda ganin wannan al'amari sai boka surkais ya cika da tsananin mamaki yace aransa
Duk yadda akayi wannan wuta bata shiri da haske Domin
yanzu rana ta fadi idan har inaso na gano kofar shiga wannan gidan wutar dolene nayi hakuri zuwa gobe da safe idan rana ta bude yana gama fadin haka saiya sami guri ya zauna ya kishingida da wani
Dutse dake bayansa aikuwa yin hakan keda wuya sai barci ya dauke shi ba tare daya sani ba
Bai farka ba sai washe gari da rana lokacin da hasken rana ta kwalle hasken yazo ya bugi idanuwansa
Firgigit boka surkais ya farka daga barcin daya sha
Yana mikewa ya bude jakarsa ya fiddo abinci yayi loma uku sannan ya gyara damararsa ya cigaba da gudu amma a wannan karan wutar yake tunkara
Saida yayi gudu kamar wanda yayi abaya
Sannan ya isa inda wutar take
Yana zuwa ya sami guri ya tsaya cak yayi cirko cirko yana mai kallonta
A sannan ne ya lura wutar tana da wasu dogayen harshuna guda biyu
Wadanda suka kalli sama atsaye kamar bishiyu atsakiyarsu kuma wata katuwar kofa ce mai maganadisu ajikinta wanda kan iya janyo duk wani karfe dake kusa da ita
Amma ita kanta kofar tayi jawur saboda hucin hutar
Atsakiyar kofar kuwa wata hudace ta zura makulli acikinta
Amma fa kafin ya riski wannan kofar dole sai ya ratsa ta cikin wutar
Nanfa ya tsaya yana tunanin yadda zaifi ya riski wannan kofar
Daga can sai dabara ta fado masa
Take ya falfala da gudun gaske ya tunkari wutar duk da yanajin hucin wutar yana ratsa jikinsa kamar zai zagwanyar da jikinsa
Koda yazo daidai bakin wutar sai ya daka tsalle ya dunkule jikinsa aguri guda
Yayi fitar burgu zuwa cikin wutar kamar an harba kibiya daga cikin baka
Yana zuwa daidai inda kofar take saiya zura wannan makulli a gurinsa
Ai kuwa yin hakan keda wuya sai kofar ta bude kanta
Ya fada ciki sannan kofar ta maida kanta ta rufe koda shigarsa cikin wannan gida sai ganinsa yayi acikin wani kogon dutse
Wanda babu komai acikinsa face duwatsu da wasu koguna wanda kowanne kogo daga cikinsu shima ya kasance babba kuma mai fadi da tsawo da kuma tsananin duhu
Ta yadda baya iya ganin abinda ke cikin kogunan a saman dakin kuwa wata jijiyar bishiya ce
Wacce a samanta anyi rubutu cikin babban baki kamar haka
BARKA DA ZUWA KOGON UWAR MACIZAI
YAKAI BAKON WANNAN KOGO KA SANI ACIKINSA AKWAI MACIZAI MASU MATUKAR YAWA DA KUMA TSANANIN DAFI
WANDA IDAN HAR DAYA DAGA CIKINSU YA SARI JIKINKA IDAN HAR BAKA CI WANNAN JIJIYAR BA CIKIN DAKIKU GOMA KACHAL JIKINKA ZAI KAMA ZAGWANYEWA KAMAR NARKAKKIYAR DALMA

KUMA DUKKANSU BA ZASU TABA MUTUWA BA FACE KA GANO MAHAIFIYARSU KA KASHETA
DON HAKA SAI KAYI AIKI DA LURA

Koda gama karanta wannan rubutu sai rubutun komai ya dauke
Lokacin da boka surkais ya gama ganin wannan sanarwa
Sai kawai ya sami guri ya tsaya cak yana jiran ganin daga wanne bangare ne macizan zasu fara fitowa
Jim kadan sai ya fara jiyo wani sautin kukan macizai yana fitowa daga cikin wadannan kogunan tako ina
Kafin cikar wasu dakiku tuni kogon ya cika da wasu irin macizai
wadanda kawunansu suka kasance jajaye jelarsu kuwa bakake ne sidik tako'ina babu banbancin komai
babu wanda yafi wani daga cikinsu , Kai komai ruwan idon mutum bai isa ya iya tantance waccece ta haife su ba
Koda gama fitowar wadannan macizai duk sai suka fara wani kuka mara dadin ji
Kuma dukkansu suka nufo inda boka surkais yake suna masu kewayeshi
Daga can sai dukkansu sukayi tsalle alokaci guda suka fado kansa da nufin duk suyi masa rubudugu su dura masa dafin dake bakunansu

WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GA BOKA SURKAIS BAYAN YA SAMI NASARAR RATSAWA TA CIKIN KATANGAR WUTA
******* ********* **********

Al'amarin jarumi rukyan kuwa lokacin da yaki yayi tsanani tsakaninsa da wannan maridi
Saiya fuskanci cewa tabbas karfin damtsensa bazai kwaceshi ba daga hannunsa
Don haka sai ya canja salon fada ya zamana yana ta faman zullewa maridin yaki yarda ya rutsa shi a guri daya
Wani lokacin ma sai kaga har tashi sama yake yana gudu ajikin katangar dakin tamkar yana gudu akan doron kasa
Kuma yana gudun yana cigaba da kaiwa maridin dodon hari
Nan fa hankalin dodon ya birkice ganin yadda karamar halittar daya raina tana kokarin bata masa lokaci
Don haka saiya dinga kaiwa rukyan duka ba kakkautawa
Cikin kankanin lokaci suka birkita dakin ya fara kokarin ruftowa kansu gaba daya saboda karfin dukan da dodon yake yiwa dirkar ginin
Koda jarumi rukyan yaga abinda ke shirin faruwa ga dakin ya shammaci dodon
Lokaci guda ya tsaya da guje gujen da yakeyi sannan yayi tsalle ya kama hawa jikin dodon cikin sauri kamar yana hawa kan bishiya
Nanfa dodon ya fara buge buge don ya kado daga jikin sa
Amma saboda zafin namansa kafin hannun yazo inda yake
Tuni yayi tsalle ya sauka daga gurin ya koma wani gun daban
Koda ya isa kan wuyan dodon sai yasa takobi ya datse shi
Take jini yayi feshi kamar an bude idaniyar ruwa kan dodon kuma ya fadi kasa ya gangara can gefe guda
Cikin zafin nama rukyan ya dira daga jikin gangar jikin nasa
Alokacin ne gangar jikin ta sulale ta fadi kasa rikica jini na zuba daga jikinsa

Sai a sannan ne ya lura da cewa rana ta fadi kuma dare har ya fara
Don haka dolene ya kwana a wannan daki kafin gari ya waye yaci gaba da tafiya

KARAGAR AJALI 2

********PART B

LBR

***********---------HABIBULLAH KBR

Lokacin da jarumi rukyan ya sami guri ya kwanta bayan ya sami nasarar kashe wannan maridin dodon
Sai kawai ya tsinci kansa cikin tunani kala daban daban game da abubuwan da suka faru da shi a baya
Da kuma irin gwagwarmayar daya sha a rayuwarsa tun yana yaro karami
Da irin kyawawan 'yan matan da suka kamu da soyayyarsa abaya yaki amincewa dasu
Yace bazai taba yin aure ba sai ya sami daukakar datafi ta kowa a wannan zamanin

Sai nadama tazo masa yace lallai dan adam akwai shi da buri
Da ace ya amince dasu da yanzu ya sami macen da zata zama abokiyar rayuwarsa
Kuma wacce zata kula masa da dan da zasu haifa koda bayan ransa
Amma yanzu Gashi ya shigo tafarkin da bashi da tabbacin fita daga cikinsa
Tsananin sa'ace kawai zata fitar dashi Daga wannan gida
Har yakai ga cika babban burin da yake tanadi akansa
Yana cikin wannan tunanine yaji cikinsa ya fara murdawa alamar yunwa tana addabarsa ba tare daya sani ba
Cikin sauri ya kwance jakar guzurinsa ya fito da wani busashshen gasashshen nama daga ciki ya fara ci
Sai dayaci ya cika cikinsa sannan ya daure bakin jakar ya maida ita jikin kugunsa ya daure
Koda gama cin wannan abinci sai take yaji barci ya kama idanunsa
Nan da nan kuwa cikin kankanin lokaci ya buge da barci ba tare daya sani ba

Kwanciya barcinsa keda wuya sai yayi wani mafarki
Da Wata bakar inuwa mai canja siffofi tana biye dashi
a kan hanyarsa ta dauko takobin saiful laiham duk inda
yayi wannan inuwar tana makale dashi daga karshe
kuma daga shi har inuwar sai su fada cikin wani mahaukacin tarkon mutuwa
Haka dai a cikin wannan barci yayita mafarkai iri iri masu abubuwan al'ajabi acikinsa
Har zuwa safiya lokacin da gari ya waye yayi haske rana ta gama takewa
Yana farkawa daga barcin take ya mike tsaye saboda ganin yadda rana ta take cikin hanzari ya gyara damararsa ya daure
Ya gyara jikinsa sosai domin tunkarar daki na gaba yana gama shiryawa sai ya nufi hanyar da zata kaishi daki na gaba kai tsaye ba tareda shakkar mai zai tarar acikinsa ba
Bai jima yana tafiya ba ya iso bakin wata katuwar murtukekiyar kofa wacce aka kerata da zallan bakin karfe mai matukar kauri da fadi
Wacce kaifi da tsini ba zasu taba tasiri ba jikinta ba tsawonta kuwa ya wuce tsawon doguwar bishiyar dabino
Yana zuwa daf da wannan kofa take yaji sautin zare wasu mahaukatan sakatu
Wanda sautin zarewarsu ya cika dakin da yake ciki tareda amsa kuwwa
Sai da aka dau dakiku dari biyu da tamanin ana zare sakatun sannan kofar ta bude kanta
Ya shige cikin dakin yana shiga cikin dakin sai kofar ta maida kanta ta rufe
Sakatun suka sake maida kansu suka rufe bam ta yadda babu wanda ya isa ya iya zaresu saboda yanayin shirin da akayi musu
Yana shiga cikin sai ya iske babu komai acikinsa face sassan jikin bil'adama da aljanu asakale ajikin garu jini yana tsiyaya daga jikinsu
Wasu kuwa an daure su ne da hanjin cikinsu suna reto a saman dakin
gaba daya dakin ya cika da jini hatta shafen dakin anyi shi ne da jini
Komai rashin imanin mutum idan yaga yadda akayi wa wadannan fursunoni kacha kacha da jikinsu dolene ya tausaya musu
Koda ganin wannan bakar kisan gilla da akayiwa wadannan fursunoni sai
Yayi sauri ya kauda fuskarsa ga barin kallonsu ya cigaba da tafiya acikin dakin
Dakika dari da ashirin kadai yayi acikin wannan daki kwatsam sai gani yayi wasu irin aljanu masu munin gaske kuma suna matukar kama da bil'adama ta bangaren fuskokinsu da kirar jikinsu saidai kuma suna da hakora zako zako masu matukar tsini
Idanunsu kuwa 'yan mini mini ne kai kace basa gani da idanun
Hannayensu kuma gaba dayansu na karfuna ne wadanda ajikinsu akwai farata masu kaifi da tsini
Agadon bayansu kuma wasu Kananun fuka fukaine guda hudu
Wani irin jini mai maiko aai dalale yake daga cikin bakin nasu
Adadin wadannan aljanu kuwa sun wuce guda dubu da doriya
Kai da ganin wadannan aljanu kasan suna daga cikin jinsin mayun aljanu wadanda basu da abinci sai zallan jini
Duk wanda yayi arba da wadannan aljanu dolene y shiga taitayinsa saboda irin munin halittar da suke da ita
Koda gama bayyanarsu duk sai suka kura masa idanu suka zuba masa arwa
Nanfa yaji jikinsa na kakkarwa kamar kafafuwansa ba zasu iya

Please Login or Register in order to submit comment