Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

biyu har mu kara samun damar da muka samu a karon farko?
Dajin wannan tambaya Husnaila tayi shiru na wasu dakiku kamar ba zatace komai ba
Daga can kuma sai tace a halin yanzu bani da tabbacin amsar wannan tambaya taka
Domin a halin yanzu komai ya rikice ba kamar farko ba ,

Amma fa ka sani hanyar kashe makahon kare yawane da ita
Sannan kuma aduk lokacin da kidan ganga ya sauya dole ne rawama ta sauya
Dajin haka sai marna'ul safranbya kasa gane ma'anar maganganunta suka birkita kwakwalwarsa yace
Ke kuwa me kike nufi da wannan magana taki?
Dajin wannan tambaya sai tayi wata 'yar karamar dariya daga bisani kuma tace

Abin da nake nufi shine a halin yanzu hankalin farhan da kuma kowanne mai burin mallakar KARAGAR AJALI
Ya karkata ne zuwa ga neman lasmira
Domin ina tabbatar maka cewa kowanne daga cikinsu a halin yanzu ya dana mugayen tarkunansa a birnin misra domin farautarta

Kada ka manta duk wanda ya iya mallakar wannan yarinya shi kadaine wanda zai iya mallakar TAKOBIN SAIFUL LAIHAM DA KARAGAR AJALI
Duk kuwa wanda ya mallaki wannan karagar shikenan ya zama gagara badau kuma zakin zakuna ko. Kuma ince sarkin sarakai
Wanda zai buwayi duniya da duk abinda ke cikinta domin zai. Dinga sarrafata ne duk yadda yake so

Kamar an zuba hatsi a saman faifai, duk sihiri da yake wannan duniyar a take zai daina aiki da tasiri,
Babu sihirin da zai dinga aiki face na SAIFUL LAIHAM
Kaga kenan idan har muka yi nasarar mallakar yarinya Lasmira
Har mukaje muka dauko karagar ajali nan take sihirin da Sarki Hasnal yayiwa al'ummar birnin ku nan take zai karye
Daga nan ne fa duk zamu cika.
Wasu burika dake cikin zuciyarmu hankali kwance

A yanzu haka idan mukace zamu maida hankalin mu akan Jinin nauwaratul hasnal
to babu shakka zamuyi biyu babu ne gaba daya ma'ana zamu rasa Jinin Nauwaratul hasnal da kuma lasmira gaba daya
Kodajin wannan batu sai marna'ul safran yaji wani farin ciki ya turnunke shi sakamakon bayanin da yaji daga bakinta
Don haka sai ya kara azama cikin gudun nasa fiye da yadda yake a baya

WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GASU GIMBIYA HUSNAILA
++++ +++++++ ++++++

Al'amarin barde Uhaisu kuwa lokacin da ya rarraba dakarunsa acikin birnin misra
domin neman Lasmira shima yaja nasa dakarun suna bin gida gida tareda tozarta talakawan cikin birnin musamman ma marasa karfi
Tareda tozarta su kai har da kwace musu yan abubuwan da suka rage a hannunsu
Suna kan hanyarsu ne sukayi arba da wani dattijon almajiri ya nufo inda suke dauke da kokon abincin daya samo da kyar a gurin bara
Saboda tsabar gigin tsufan da yayi kafafunsa har rawa sukeyi kai kace ba zasu iya daukar nauyin jikinsa ba,

idanunsa kuwa tuni dade da makancewa baya. Gani ko kadan
Duk da ganin irin wannan mawuyacin yanayi da wannan tsoho yake ciki
Baisa su Barde Uhaisu sun dakata sun tsaya domin ya wuce ba
Suna zuwa inda yake Uhaisu yasa dokin sa ya bangaje wannan almajirin ya fadi kasa
Abincin ma da yake hannunsa ya zube sannan ya kara gaba abinsa yana mai murmushin mugunta
Sannan wani daga cikin dakarun dake bayansa ya zaro wata shafadediyar bulala ya tsulawa almajirin sannan ya cakumo wuyan rigarsa ya dagashi sama ya tofa masa yawu akan fuskarsa yana mai cewa
Kai kaskantacce kai wane da har zaka shiga gaban dawakan mu a lokacin da muke gudanar da aikin mai girma sarki shuraim?
Ka sani wannan abu da mukayi ma hukunci ne bisa ga laifin da ka aikata
Sannan ya sakeshi ya fadi kasa jikinsa na kyarma suka ci gaba da tafiya suna masu kyalkyala dariya

Har sun danyi nisa da inda wannan tsohon kawai sai sukaji wannan tsohon ya kira sunansu daya bayan daya
Cikin sauri suka juyo a fusace domin ganin wanda ya kira sunan nasu
Koda sukaga wannan tsohon ne take zuciyar su ta kama tafarfasa saboda tsananin fusata cikin tsaya uhaisu ya
umarci daya daga cikin dakarun daya kamo masa wannan almajirin yazo dashi gabansa
Ba tareda bata lokaci ba wannan badakaren ya tunkari almajirin da nufin cika umarnin uban gidansa

Saidai koda hannunsa ya sauka ajikin almarin take yaji wani irin zugi gami da radadi irin wanda bai taba jin kamarsa ba a rayuwar sa bai san sanda ya kwarara uban ihu ba

Nan take ya sulale kasa sumamme ba tareda ko ya shura ba
Da ganin abinda ya faru sai gaba daya dakarun sukayi kukan kura lokaci guda suka afka masa
Suna zuwa daidai inda yake take dukkansu jikinsu ya sandare suka kame kyam kamar gumaka,
Da ganin abindaya faru ga wadannan dakaru take uhaisu yayi kukan kura saboda tsananin fusata

Ya dubi wannan tsoho yace hakika ka tafka babban kuskure da kayi jayayya da dakaruna a yau zan nuna maka banbancin dake tsakanin tsohon kashi da kuma sabo

Yana gama fadin haka sai ya runtse idanunsa tareda karanto wasu dalasiman tsafi
sannan ya afkawa wannan almajirin
Ai kuwa suna haduwa sai uhaisu ya dinga kai masa mugun sara a kan dokin wuya domin ya datse masa kansa
Amma wani abin al'ajabi sai kaga wannan almajirin yana iya shanye duk
harin da yake kawo masa cikin zafin nama gami da juriya da bajinta tamkar matashi mai jini ajika
Babu abinda zai kara daure maka kai face tsananin juriyarsa wacce kana gani kasan ya wuce na wanda girma ya kama shi
Kuma duk wannan abu da akeyi ko sau daya baiyi yunkurin mai da martani ba kawai dai kare kansa yake yi tare da wani murmushin mai kama dana mugunta ko kuma raini da yake yiwa uhaisu
Al'amarin daya kara fusata shi kenan ya kara zage damtse wajen kai masa sara da suka babu kakkautawa

Koda suka. Dauki dogon lokaci suna wannan fafatawar sai uhaisu ya sammaci wannan almajirin ya debi kasa ya watsa masa acikin ido tareda gabza masa duka akan karan hancinsa
Saboda karfin dukan sai daya ja da baya taku uku sannan ya cake a gurin
Kafin ya bude idonsa tuni uhaisu ya zame a akasa ya shiga karkashinsa ya shureshi ya daga shi sama ya dankara shi da kasa
Sai dai kafin ya sauka akan kasar tuni kasar gurin ta narke ta zama dan karamin magudanar ruwa
Koda uhaisu ya bugashi take ruwan yayi fallatsi akan jikinsa
Ruwan na sauka ajikinsa take yaji gaba daya jikinsa yayi sanyi kamar an zare masa duk wata laka ta jikinsa

Kawai sai almajirin ya mike tsaye tareda gyara tsayuwarsa yana mai karewa uhaisu kallo sama da kasa
Alokacin da gaba daya jikinsa ya sandare in banda idanunsa babu abinda yake motsi ajikinsa
Sannan ya bushe da mahaukaciyar dariya mai kama da kukan jaki daga bisani kuma ya tsuke bakinsa ga barin dariyar kamar an aiko Masa da sakon mutuwa
Ya tsaya tareda kare masa kallo daga kasa har sama sannan yace
Kai saurayi hakika wannan zafin zuciyar taka da jin kan da kakeyi sunyi yawa kuma ina idan har baka gyara zuciyarka ba sune zasu kaika ga halaka
A halin yanzu ka cancanci mutuwa a hannuna domin kuwa kaima kayi yunkurin kashe ni
Shin kasan dalilin da yasa ba zan kashe ka ba?

Bai. Tsaya jiran amsar da zai bashi ba saboda sanin cewa ba zai iya bashi amsar tambayar da yayi masa ba
Yaci gaba da cewa
Yakai uhaisu abin da yasa ba zan kashe ka ba shine ina sone ka raini mutuwarka da hannunka saboda zaluncin da ka saba aikatawa
Yana gama fadin haka take ya bace masa da gani kamar bai taba wanzuwa ba

Bacewarsa keda wuya take su uhaisu suka dawo cikin hayyacinsu
Kawai sai uhausu ya kwarara uban ihu saboda bacin rai
Nan da nan ya dauko madubinsa na tsafi ya shafe shi. Domin gano ko wanene wannan almajirin amma al'amarin ya gagara koda ya matsa wajen bincike take madubin yayi bindinga ya tarwatse gaba daya

Bisa dole ya hakura da binciken nasa yaci gaba da tafiya domin gudanar da aikin dake gabansa
Amma abu guda daya da yake masa yawo a zuciyar sa shine tayaya zai rainin dan da zai kashe shi da hannunsa?
Alhalin da guda dayane dashi a duniya

Wata zuciyar tace dashi tabbas maganar wannan almajiri zata iya zama gaskiya domin tuni shi da kansa ya fara fahimtar haka
Saboda yadda suka taso da sabanin ra'ayi da wannan dan nasa
Duk domin lokuta da dama yana yawan yunkurin dakatar dashi akan wannan mummunar dabi'ar tasa
Kai akwai lokacin ma daya taba yunkurin zuba masa guba acikin abincinsa
Wannan dalilin ne ya tabbatar masa da cewa maganar wannan almajiri zata iya zama gaskiya

Nantake ya yanke hukuncin kashe wannan da nasa
Haka dai suka cigaba da tafiya ba tareda sun chanja wannan halayyar tasu ba
Har suka iso wata rumfa suka iske wasu kyawawan yara guda hudu wadanda shekarunsu ba zasu gaza goma ba a zaune acikinta
Amma kuma kana ganinsu kasan sun fito ne daga mabanbantan kabilu
Domin yaren da kowanne daga cikinsu yakeyi ma daban ne dana dan uwansa sannan kuma wani abin mamakin shine yadda suke rayuwa da junansu tareda fuskantar yaren dan uwansa duk da cewa yarukan nasu daban daban ne
uku daga cikinsu dukkansu maza ne
Daya daga cikinsu kuwa macece kuma makauniya saidai duk da wannan makantar tata tana kunshe da wasu abubuwan al'ajabi
Wannan abin al'ajabi kuwa shine baiwar zane zane domin da zarar ta shafa fuskar mutum sau daya nan take zata iya daukar alkalami da takarda ta zana siffarsa babu wani banbanci
A wannan lokaci ta kasance a bakin wannan rumfar tareda daya daga cikin abokan zaman nata tana aikin zanen fuskarsa cikin kwarewa
Ragowar biyun kuwa suna daga cikinta suna wasa tareda yin shewa tsakaninsu

Koda barde uhaisu ya kyallara idonsa yayi arba da wannan yarinya sai ya tambayi daya daga cikin dakarunsa yace

Akwai yaran da suke rayuwa acikin rumfar?
Dajin wannan tambaya sai badakaren yace ya shugabana a sani na da wannan rumfar ta kasance gurine da almjirai suke hutawa idan sun yi bara sun gaji
Duk wanda ka gani a a wannan bukkatar to mutum ne mara galihu acikin al'umma babu wanda ya damu da rayuwarsu

Koda jin wannan batu sai uhaisu yayi wani guntun murmushi
Sannan ya umarci badakaren daya kamo masa yara biyun dake bakin wannan rumfa nantake kuwa badakaren
Ya nufi bakin rumfar ya kamo mace da namijin tareda daura musu sarkoki nanfa yaran suka fashe da kuka suna ihun neman taimako amma sai wannan badakare ya dinga tsula musu bulala cikin rashin tausayi
Don dole sukayi shiru da bakinsu suka. Daina wannan kukan sannan aka daure su ajikin doki
Ba tareda bata lokaci ba suka sakarwa dawakansu linzami suka ci gaba da tafiya suna fincikar wadannan yara akasa

Suna ji suna gani aka rabasu da 'yan uwansu

SHIN INA BARDE UHAISU ZAIKAI WADANNAN YARA KUMA WANNE IRIN AIKI. ZASUYI MASA?

KUDIN GIMBIYA HUSNAILA YANA CIKA NA GANIN TA MALLAKI KARAGAR AJALI?

SAI. MUN HADU A KASHI NA GABA++++++++++KARAGAR AJALI 8

PART
C

++++++++++LBR

HABIBULLAH KBR

Lokacin da dakarun sarkin yaki uhaisu suka ja wadannan yara guda biyu bisa kafafunsu suka ci gaba da tafiya dasu acikin birnin misra
Kai kace fursunoni suka kamo daga filin yaki tun yaran na kuka har suka saduda babu wanda acikinsu zai baka tausayi face macen data kasance makauniya
Domin haka ta dinga yin tuntube da duwatsu tana dauje kafafunta
Amma haka za'a ci gaba da fincikarta don dole zata mike taci gaba da tafiya
Tun suna kuka haka suka saduda don dole suka daina kukan tareda rungumar kaddara
A sannan ne namijin ya dubi mace yace yake Hilaliya ya zama wajibi a garemu mu daina wannan kukan
Saboda wannan zamanin babu wani sassauci ko kuma tausayi agurin masu karfi da raunana
Dajin wannan batu sai hilaliya ta dubeshi tabbas maganarka gaskiya ce Nargis
Amma fa ka sani babbar damuwata daya ce kada mahaifiyata ta dawo daga aikatan data tafi yi ta iske bana nan
Wanne irin bakin ciki kake tunanin zatayi na rashi na? Kila ma ta iya kashe kanta don bakin ciki
Don haka ni dai ba zan iya zuba ido ina ji ina gani rayuwata ta kare acikin bauta ba duk sanda na sami dama sai na gudu daga hannun wadannan azzalumai
Duk wannan magana da takeyi bata san sarkin yaki uhaisu yayi amfani da sihirin tsafinsa don jin maganar da take fada ba
Saboda nan take yaja linzamin dokinsa tareda daka mata tsawa wacce tasa zuciyarta ta buga da karfin gaske
Kawai sai yasa hannunsa guda daya ya shureta ya daga ta sama kamar ya raga sillen kara kafafunta na yawo akan iska
Nan da nan idanunta suka zazzaro kamar zasu zazzago suyo waje
Sannan yasa hannunsa na dama ya kwada mata mari yana mai cewa
Ke yarinya kinyi kuskure da kike tsammanin zaki iya guduwa daga gareni
Tun wuri ina mai shawartarki daki cire wannan tunanin daga cikin zuciyar ki domin ba zaki taba tserewa daga hannuna ba
Idan. Kuwa kikayi yunkurin guduwa daga gareni hukuncin kisa ne a gareki bayan nasa an gana miki azaba mai radadi yana gama fadin haka sai yayi wulli da ita kanta ya gwaru da kasa ya dare jini yayi tsartuwa daga hancinta
Sannan suka ci gaba da tafiya abinsu, cikin dauriya hilaliya ta mike tareda goge jinin dake goshinta taci gaba da tafiya ahaka
+++++++ +++++++ +++++++

Acan kuwa al'amarin Yarinya Lasmira kuwa lokacin data tunkari kofar shiga birnin misra sai ta dinga sauri sauri tareda rufe fuskarta don kada wani ya ganta
A sannan ne kawai ta jiyo sautin bugun tambari yana tasowa daga can bayanta tareda busar algaitu gami da sarewa inda aka samar da kida mai matukar dadin sauraro
Cikin sauri ta juya bayanta don ganin me tahowa , kawai sai tayi arba da wasu ayarin fatake cikin shiga ta alfarma irin ta mutanen birnin misra
A gaban ayarin kuwa wani dattijo ne wanda shekarunsa ba zasu haura shekaru arba'in da tara ba
Fuskarsa cike da tarin kasimba yaci ado irin na manyan attajirai sai murmushi yakeyi shi kadai
Da ganin sa kasan irin mutanen nan ne masu matukar fara'a abayansa kuwa dakaru ne kimanin su dari ruke da makaman yaki sai kuma wasu tarin kuyangi 'yan mata masu jini ajika da kuma masu kananun shekaru
Kowacce daga cikinsu ta daure fuskarta da farin mayafi sai kuma wasu bayi dauke da tarin akwatuna wadanda aka cika su da tarin dukiya abayansu kuwa wani rukunin dakarun suma guda dari cif suna take musu baya
Kodayin arba da wadannan ayari take Lasmira tayi sauri ta sami duhuwar ciyayi ta buya acikinta
Sai da ta tabbata ayarin fataken ya matso kusa da ita saita wuf ta fito daga maboyar tata ta shiga cikin wannan ayarin
Saidai kash sai aka sami akasi ta gifta ta gaban dakarun dake tsaron ayarin
Kawai sai taga wani daga cikin dakarun ya nufo inda take gada gadan fuskarsa babu annuri hannunsa guda daya akan kuffen takobinsa

Koda taga wannan badakare cikin wannan yanayin take taji zuciyarta ta buga da karfi
Jikinta ya fara rawa tareda kyarma kamar kace kyat ta ruga da gudu , kyawawan idanuwanta kuwa suka zazzaro , zuciyarta ta dinga bugawa da karfin gaske domin tsoron hukuncin da wannan badakare zaiyi mata
Nanfa ta tsaya a inda take ta zubawa sarautar allah ido tareda jiran karasowar wannan badakare
Koda badakaren ya karaso inda take kawai sai taga ya zarce gurin kuyangar dake kusa da ita yana mai ce da ita
Yake Dabira kada fa ki manta da alkawarin dake tsakanin mu na raba duk abinda kika samu a gurin mai girma hubair kaso biyu ki bani kaso daya daga ciki
Idan kuwa har kika karya alkawari ina mai tabbatar miki cewa zan tona asirinki a gurinsa na shaida masa cewa kece wacce kika kashe matar sa ta hanyar sanya mata guba acikin abinci domin ki samu kusanci agurinsa
Dajin wannan batu sai idanun Dabira suka zazzaro ta kama kame kame sannan tace kayi mini rai yakai Hukairu
Idan har ka sanar dashi wannan ina mai tabbatar maka cewa nima kashe ni zai yi
Nayi maka alkawarin zanyi ma duk abinda kake bukata komene shi matukar zaka rufa mini asiri
Kodajin haka sai wannan badakare yayi wani dan karamin murmushi mai kama da kukan jaki yace
Ai shikenan
Yana gama fadin haka sai ya wuce gaba yana wata 'yar karamar dariya

Haka dai wannan ayarin fatake yaci gaba da tunkarar kofar birnin misra suna isa bakin wannan kofar take suka ja linzaman dawakansu suka tsaya cak

A sannan ne fa wani daga cikin dakarun dake tsaron kofar wani matashin saurayi, kuma shirgegen kato mai kirar mutanen farko ya ratso ta tsakiyar dakarun sa yazo gaban wannan bafataken ya tsaya tared cewa

Barka da dawowa mai girma hubair bin ru'ais ya hanya ? Yau kusan shekaru biyu kenan da barinka wannan birni ina fatan dai ka sami nasarar samo abinda ka fita nema ?
Dajin wannan tambaya sai hubair ya tuntsure da dariya daga bisani kuma yace kwarai kuwa tafiya tayi kyau domin kuwa a yau na dawo da tarin dukiya wannan birni namu
Kuma babu wanda zan fara nunawa su face mai girma sarki shurais
Don haka sai ka bude min kofa na wuce da ayari na cikin gari

Koda sarkin kasuwa Hubair yazo daidai nan a zancensa sai mai tsaron kofar ya dan girgiza kai sannan yace kayi hakuri ya shugabana
A wannan lokaci muna cikin tsananin bincike ne bisa ga umarnin sarki
Ya umarce mu cewa duk. Wanda zai shiga wannan gari dole ne mu bincike shi sosai kuma komai kusancin dake tsakaninsu
Saboda haka kayi hakuri mu gudanar da aikin mu kamar yadda aka umarce mu ka wuce salin alin
Dajin haka sai sarkin kasuwa ya dan jinjina kansa daga bisani yace babu damuwa zaka iya gudanar da aikinka domin bani da matsala akan hakan saboda haka zaka sameni a matsayin mai biyayya ga dukkan umarnin ka
Yana gama fadin haka sai ya umarci bayin da yake tafe dasu da su gurfanar da kekunan dokunan da aka zubo dukiyar aciki sannan su fito da dukkan akwatunan dake cikin su
Kafin cikar wasu dakiku tuni bayin sun aikata abinda aka umarce su
Sannan suka hau dogon layi suka tsatstsaya
Sannan suma kuyangi mata wadanda Lasmira take cikinsu suka kafa nasu layin
Sai kuma dakaru wadanda suka kasan ce a bayansu sukayi nasu sahun daban

Nan take mai tsaron kofar da yaransa suka fara bude akwatunan tare da bincikar su daya bayan daya sai da suka tabbatar ba'a boye wani abin a ciki ba
Sannan suka koma bangaren bayin suna kare musu kallo
A bangaren Lasmira kuwa hankalinta ne yayi matukar tashi. Fiye da farko domin ta tabbata a wannan karon idan akace za'ayi wannan bincike to tabbas idan aka ganta abin da mahaifinta yake gudu shine zai faru ma'ana za'a raba ta dashi rabuwa ta har abada
Amma dataga cewa a wannan lokaci babu abinda zata iya yi domin kauce musu sai ta rungumi kaddara ta
Koda wadannan dakaru suka gama da bangaren wadannan bayi sai suka dawo kan kuyangin
Sannan suka umarci kowacce wadda tasan wani abun ya rufe mata fuska data gaggauta bude fuskar tata

Daga nan ne fa dakarun sukazo suka fara bunciken nasu daya bayan daya suna bin kowacce daga cikinsu suna caje ta sannan su wareta gefe daya har layi yazo kan Lasmira
Ya zamana itace a akan layi
Nanfa ta fara dawurwura a gurin tana kokarin neman hanyar da zata bi ta gudu
Kawai sai taga shugaban dakarun ya dakawa wacce take bayanta tsawa ba tareda ita ya kalleta ba
Yace me kike jirane maza kizo kece akan layi, take kuyangar ta matsa gaba jikinta yana kakkarwa badakaren ya gama binciken da zaiyi akanta sannan ta wuce haka dai wadannan kuyangi suka dinga zuwa daya bayan daya ana bincikarsu
Har akazo kan wadannan dakaru suma aka yi musu binciken da za'ai musu ba tareda daya yayiwa Lasmira magana ba

Al'amarin daya matukar bata mamaki a karon farko kenan tace a ranta shin me yasa wadannan dakaru suka rabu dani ne ba tare da sunyi min abin da suke yiwa sauran mutane ba?
Take zuciyarta ta bata amsa da cewa wata kila ke abinda yasa suke kyale ki saboda kankantar shekarunki ne yasa suka rabu dake
Wata zuciyar tata kuma tace kai ba haka bane domin akan idona naga an binciki wadanda basu kaini shekaru da kuma girma ba
Haka dai tayi ta sake sake a cikin zuciyarta ba tareda ta iya gano dalilin hakan ba

ABINDA BATA SANI BA KUWA SHINE DUK WANNAN BINCIKE DA AKEYI ANA YINSA NE KAWAI DON FARAUTAR RAYUWARTA IDANUNSU NE KAWAI BASA IYA GANINTA
WANNAN DALILI NE YASA BASA KUSANTAR INDA TAKE

Da ganan ne sarkin kofa ya umarci yaransa dasu budewa hubair da mutanensa kofa
Nantake kuwa wadannan dakaru suka bude katuwar kofar birnin su hubair da jama'arsa suka shige cikin birnin
Da shigar su cikin birnin misra sai suka iske cikin birnin cike da tsatstsauran tsaro fiye da wanda suka tarar a bakin kofar shigowa birnin
Saboda yadda suka dinga ganin rukuni rukuni na dakaru wadanda suke ta shawagi ako'ina acikin garin suna ta faman bincike
Al'amarin daya matukar baiwa hubair mamaki kenan ya rasa wannan dalilin wannan tsatstsauran tsaron
Don haka koda suka zo giftawa ta gaban wani rukuni na dakarun
Sai hubair yaja linzamin dokinsa ya kira daya daga cikinsu ya tambayeshi dalilin wannan bincike nasu
Nan take wannan badakaren ya shaida masa cewa sunayi ne domin kama wata yarinya guda daya bisa ga umarnin sarki kuma ya sanya kyauta mai tsoka ga duk wanda yazo masa da ita araye
Dajin wannan batu sai hubair yayi wani dan karamin murmushi sannan ya ja linzamin dokinsa yaci gaba da tafiyarsa

Bai zarce ko'ina ba sai hanyar da zata sadashi da gidan sarauta
Duk inda zai gifta sai dai kaga mutane suna daga masa hannu tared girmamawa kai kace shine ke mulkin birnin gaba daya
Ba don komai ba sai don saboda kyawun halayyar da yake da ita gami da kyautatawa talakawa

Duk da kasancewar sa dan uwa na jini ga sarki shurais amma sai halayyarsu ta banbanta
Shi sarki shurais ya kasance azzalumi mai matukar takama da izzar mulki wanda bashi da rangwami akan talakawansa
Wanda tsananin zaluncinsa al'umma suke yi masa biyayyar dole

Amma shi Hubair sai ya zamanto mai matukar saukin kai da jin kai ga talakawansa
Ko kadan baya kaunar yaga waji abu ya sami talakansa musamman ma raunana
Saboda sai yayi iya karfinsa domin yaga yaga ya taimaka musu
Wannan halayya tasa sai ta sanya mutane suke matukar kaunarsa tareda girmama shi kai kace shine ke mulkin birnin misra
Basu jima suna tafiya ba suka iso kofar gidan sarauta don haka ba tareda bata lokaci ba dakaru suka gama yin binciken da zasuyi akan jama'ar da yake tafe dasu
Sannan suka basu hanya suka shige cikin gidan sarautar tun kafin su isa harabar gidan sarautar tuni wani badakare ya garzaya ya sanar da sarki shuras dawowar hubair.

Don haka cikin. Farinciki. Sarki shurais ya fito harabar gidan sarautar ya tsaya domin tarar dan uwansa
Lokacin da su shurais suka iso harabar gidan sarautar sai suka iske sarki hubair a tsaye fuskarsa cike da mumushi

Koda isowarsu take dakaru sukaja tunda da gaba dayan mutanen dake tare dasu
Attajiri hubair ne kadai ya karasa inda sarki shurais yake suna haduwa take suka rungume junansu cike da farin cikin sake haduwa
Daga nan ne fa wasu dakaru suka kawo musu kujeru tareda abubuwan ci da kuma sha suka ajiye musu
Ba tareda bata lokaci ba attajiri hubair yaci abincin ya cika cikinsa
Sannan ya umarci wadannan dakarun dasu kaiwa jama'ar da yake tafe dasu. Nasu abincin domin suma suna cikin yunwa
Daga nan ne attajiri hubair da sarki shurais
Suka tashi suka shige cikin gidan sarautar suka tattauna akan bayan rabuwarsu
Da dukkanin abubuwan da suka faru akan hanyarsa ta tafiya kasuwanci zuwa manyan kasashen duniya da irin gwagwarmayar da suka sha
sannan ya sanar dashi mutuwar matarsa ta wacce ta mutu sanadiyar zazzafan. Ciwon ciki
Inda sarki shurais ya tausaya masa bisa ga rashin da yayi na matarsa
Bayan sun jima suna tattaunawa ne suka taso domin nunawa sarki

Please Login or Register in order to submit comment