Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani haske ya ratso ta cikin tagar fadar ya dira a gabansa tare da yin sujjada agareshi
Sannan hasken ya rikide ya koma siffar wani dattijon Mutum Cikin siffar rikakkun bokayen nan

Sarki shuraim ya dubi Wannan dattijon Boka Yace yakai abin dogaro na
Me ke tafe dakai a wannan lokaci da baka saba zuwarmin ba ?
Dajin wannan tambaya sai yayiwa sarki nuni da ya sallami 'Yan majalisar dake zaune agurin
Aikuwa nan take sarki ya basu umarnin ficewa daga cikin fadar

Fitarsu keda wuya sai wannan bokan ya tafa hannunsa nan take sai gabaki daya fadar ta rikide ta koma ta gilashi
Cikin girmamawa bokan yace
Ya shugabana kamar yadda ka sani a kowanne karni abu na musamman da yake faruwa acikinsa
To a wannan karni da muka shigo al'amarin dake cikinsa yafi na dukkan karnikan da suka gabata
Dajin wannan batu sai sarki shuraim ya dubeshi yace me kake nufi yi maza ka sanar dani Abinda ke tafe dakai bana son bata lokaci
Cikin ladabi yace shin ka tabajin labarin Wata karagar mulki wacce akewa lakabi da KARAGAR AJALI?
Dajin wannan tambaya sai sarki shurem yace kwarai kuwa na taba jin labarin ta a wajen kakana wanda ya haifi mahaifina
Dajin haka sai bokan yace ya shugabana idan har kasan da wannan karaga to ya zama tilas ka tashi dakaru su shiga cikin wannan birni da kuma kauyukan sa domin farauto maka Wata yarinya karama mai suna lasmira
Bincike ya tabbatar da cewa an haifi Wannan yarinya ne acikin wannan birni namu
Kuma tana rayuwa acikinsa ko. Kuma kauyukan dake kewaye damu
Ita dai wannan yarinyar acikin zuciyarta aka rubuta taswirar hanyar da zata sadaka da inda wannan karaga take
Yanzu haka duk wani ma'abocin ilimin tsafi , manyan sarakuna, da kuma aljanu duk sun kwallafa idanunsu akan wannan yarinya
Yanzu haka ma ina tabbatar maka cewa sun ajiye wakilansu acikin wannan birni domin Neman Wannan yarinya

Don hakane naga ya zama wajibi nazo na sanar dakai wannan abu dake shirin faruwa kafin Lokaci ya kure

Dajin wannan batu sai fuskar Sarki shuraim ta fadada da murmushi daga bisani kuma ya bushe da dariya sannan yace
Ya abin dogaro na hakika Naji dadin wannan labari daka kawo mini
Amma tayayane za'a iya shaida Wannan yarinya da kake magana akanta?
Dajin wannan tambaya sai bokan ya sunkui da kansa yace ai ita wannan yarinya ba kamar Kowa bace
Domin duk wanda ya kalleta da kallo daya zai shaida wacece ita domin a yanxu kaf duniya babu mace mai Kyanta
Kuma shekarunta ba zasu haura biyar zuwa shida ba
Babu Irin binciken da banyi ba acikin alkaluman tsafi na domin gano hakikanin gurin da take amma abu ya gagara sakamakon kariyar da sihirin tsafi yake bata da kansa tun daga lokacin da aka haifeta har zuwa lokacin da zata bayyana
Amma ina mai tabbatar maka cewa idan har ka tura dakarunka suka bazama Cikin birni da kauyuka na cikin wannan gari dole zasu sameta akan tsakanin Yau zuwa gobe
Koda Wannan bokan yazo daidainan a zancensa sai yayi shiru da bakinsa ga barin maganar da yake
Gama fadin hakan keda wuya sai ginin fadar ya koma yadda yake da farko
Ba tareda bata lokaci ba sarki shuraim ya kwallawa sarkin yakinsa barde uhaisu kira
Nantake barde uhaisu ya bude kofar fadar ya shigo ciki Tareda rissinawa yace
Gani gareka ya shugabana me kake bukata, nan da nan sarki shuraim ya kwashe bayanin da wannan boka yayi masa Tareda umartarsa daya hada dakaru masu yawa su fara binciken hanyoyin shigowa Wannan gari gaba dayansu tareda gidajen cikinsa gaba daya
Kuma a tabbata an shiga cikin kowanne gida kuma an caje shi gaba daya
Idan masu Gidan sukayi taurin kai a kashe su gaba daya, dajin wannan umarni take sarkin yaki uhaisu yace an gama ya shugabana
Take ya tashi ya fice daga cikin fadar ya hada dandazon dakaru masu yawa suka shiga cikin gari domin fara bincike
Tun a farkon Fara wannan binciken nasu ne sukaga yanayin garin ya sauya ba kamar yadda suka sanshi abaya ba
Domin a wannan karon bakin fuskoki da yawa sun bayyana acikin garin wasu ma kallo daya zakayi musu ka san cewa ba 'yan nahiyar bane ba baki ne daga Wata nahiyar

Nan da nan sarkin yaki uhaisu ya rarraba dakarunsa wasu ya umarcesu dasu tsaya a iyakokin wannan gari su dinga bincikar masu shige da fice daga cikinsa
Shi kuma yaja ragowar suka shiga cikin gari suka fara binciken gidaje daya bayan daya Tareda cin zarafin mutanen Gidan musamman 'yan mata
Idan mai gidan yayi taurin kai ko kuma yunkurin hanasu aiwatar da abinda suke aikatawa take suke kasheshi ba tareda wani tausayi ba

Al'amarin almajiri Ruzyal kuwa tun daga lokacin daya dauki lasmira tana jaririya ya fice da ita Daga Cikin birnin misra kuwa sai ya shiga can Cikin wani jeji dake nesa da birnin wanda ya kasance babu mugayen dabbobi acikinsa
Ya nemi wani kogon dutse ya cajeshi sosai ya tabbatar babu wani mugun abu acikinsa
Sannan ya shiga ciki ya gyara shi, Tareda yiwa lasmira shifida ta kara ya kwantar da ita kanta suka ci gaba da rayuwa acikinsa,
A kullum idan zai fita nemo musu Abinda zasu ci sai ya mirgino da wani katon dutse dake kusa da wannan kogo ya rufe kofar shiga cikinsa don kar wani abin cutarwar ya kusance ta
A haka zaije yayi bara duk wuya duk runtsi ba zai dawo gida ba sai ya fara nemo mata Abinda zataci koda kuwa shi bai sa Koda ruwa makurwa daya acikinsa ba
Wasu lokutan ma almajiri ruzyal haka zai kwana tun safe batareda yasa Koda lomar abinci a bakinsa ba
Tsawon shekarun da suka dauka acikin wannan daji bai taba bari wani mahaluki yaga wannan 'ya tasa ba
Domin duk sanda zai fito ma daga cikin wannan kogon sai ya fara kasa kunnensa na tsawon dogon lokaci ya tabbatar da cewa babu motsin abu Mai rai acikinsa Sannan yake fitowa
Aduk sanda ya shafa fuskarta da hannayensa Yaji Irin kyan da take dashi
Sai yaji hankalinsa ya dugunzuma Ganin cewa a duk randa aka sami matsala wani yayi arba da ita tofa karshen rabuwar su da ita yazo
Musamman ma masu sarauta wadanda basu da burin dayafi suga sun tara kyawawan 'yan mata acikin masarautar su
Babban abin bakin cikin ma shine duk sanda aka rabashi da ita babu tabbacin zai sake ganinta a rayuwarsa
Aduk Irin Lokacin dayayi Irin wannan tunani sai yaji kama/ ya kashe kansa ya huta da bakin ciki
Amma da zarar ya tuna da halin da zata iya shiga a wannan lokaci idan ya rasa rayuwarsa sai yaji hankalinsa yayi matukar dugunzuma ya kasa aiwatar da wannan mummunan kuduri nasa don haka kawai sai ya fashe da kuka
A cikin wannan hali har ya xamana lasmira ta fara yin wayo
Wata rana taga mahaifinta ya shiga cikin irin wannan yanayi sai taji itama hankalinta ya tashi don haka ta tambayeshi tace
Ya abbana menene yake faruwa dakai naga ka shiga cikin irin wannan halin na damuwa
Ka sani tun ina jaririya nakan yawan ganina acikin Irin wannan hali Wanda nakan ji rashin dadi da zarar na ganka acikinsa?
Dajin wannan tambaya sai yayi sauri ya sare hawayen daya kwaranyo akan fuskarsa Tareda janyo ta jikinsa yace
Babu komai lasmira kawai dai ina duba Irin yanayin rayuwar da muka taso acikine ta rashin tausayi ga sarakuna ga kuma uwa uba talaucin da muke ciki

Yake 'yata har abada ina mai gargadinki da kada ki kuskura ki taba bayyana fuskarki ga kowa daga nan har zuwa sanda zaki. Gama mallakar hankalinki
Matukar kinason dauwamar farin ciki a tattare damu
Daga wannan furuci bai kara ce mata uffan ba Yayi shiru da bakinsa Tareda janyo bargonsa ya kwanta
Ya barta a zaune zuciyarta tanata yi mata sake sake
Domin gaba daya kwakwalwarta bata iya fahimtar maganar daya fada mata ba saboda kankantar shekarunta
Tun daga wannan rana Ruzyal yaci gaba da boyewa lasmira damuwar dake cikin zuciyarsa
Ana Cikin wannan haline Wata rana kwatsam sai aka wayi gari matsanancin ciwo ya kama ruzyal
Lokaci guda zazzabi mai karfi ya kamashi wanda sai da takai jikinsa ya soma sassandarewa idanunsa kuwa suka dinga kakkafewa kamar wanda ya shafe shekaru yana jinya
Koda ganin halin da mahaifinta ya shiga
Take itama hankalinta ya tashi sakamakon ganin irin mawuyacin halin daya shiga
Nanfa ta shiga kokarin nemo masa maganin da zai sha amma sai aka ci gaba da rashin sa'a a wannan lokaci babu Wannan magani acikin kogon
Don haka sai ta yanke hukuncin kawai yau ta fita daga cikin wannan kogo ta shiga cikin gari domin tayi bara ta samo masa wannan magani
Dama tunda take bata taba shiga cikinsa taga yadda mutane suke gudanar da rayuwarsu acikinsa ba

Tana gama wannan tunani saita dauko wani dan karamin rawanin mahaifinta ta rufe fuskarta dashi sannan shima dogon gashin kanta ta tattareshi agadon bayanta ta daureshi
Kasancewarta karamar yarinya mai kananun shekaru sai gashi kamanninta gaba daya sun juye kamar namiji, sannan ta dauki wani dan karamin sanda ta ruke a hannunta ta fice daga wannan kogon ta kama hanyar shiga cikin birnin misra wani abun al'ajabi sai gashi kai tsaye ta nufi wannan birni na misra ba tareda batan hanya ba duk da cewa bata taba shiga cikinsa ba
Kuma akan hanyarta tayita haduwa da mutane wadanda ta dinga kokarin kauce musu don kar su ganta
Saidai abinda bata sani ba shine koda zatazo inda suke ta taba jikinsu babu wanda zai iya ganinta ko kuma yasan da ita agurin komai Karfin sihirinsa
Saboda kariyar da alkaluman tsafi suka bata Wannan ne dalilin dayasa tun tuni aka kasa gano inda take
Idan ka dauke mahaifinta Babu mai iya ganinta har zuwa lokacin da wa'adin sihirin ya diba mata

Haka dai lasmira taci gaba da tunkarar Hanyar da zata sadata da birnin misra bisa kafafunta
Tundaga nesa data fara hango kofar shiga wannan birni sai taji farinciki ya turnuke ta Ganin cewa yau Zata shiga a salin mahaifar iyayenta taga yadda suke rayuwa aciki
Koda ta fara hango kofar shiga birnin sai taganta cike da dakaru sun tareta suna binciken masu shiga cikinsa daya bayan daya wasu ma akan idonta aka dinga tozarta su amma babu yadda zasu iya, nanfa taji tsoro ya kama zuciyarta taji Kamar ta koma da baya don gudun kar irin abindaya same su ya sameta amma data tuna halinda mahaifinta yake ciki sai taji ba zata iya komawa da baya ba dolene ta ratsa koda kuwa zata rasa rayuwarta
******** ********
Al'amarin boka hulbaz kuwa lokacin daya tare jinin nauwaratul hasnal acikin battar tsafinsa
Bai zarce ko ina ba sai Cikin kogon tsafinsa, da shigarsa sai ya bude Wata 'yar karamar jaka ya sanya battar aciki,
Sannan ya dauko wata kwalbar giya ya kwankwada yayi nakit saboda huce gajiyar dake tattare dashi
Har yaje ya sami guri zai kwanta kawai sai ya tuna da aljani Amsadurraz wanda ya kulle acikin kwalbar tsafi
Nan Take yayi nuni da Hannunsa zuwa inda kwalbar take
Tsulum sai kwalbar ta taso da kanta ta sauka akan teburin dake gabansa
Boka hulbaz ya kare masa kallo acikin wannan kwalbar yana nazarinsa
Daga bisani sai ya tuntsure da dariya yace ya kai Amsadurraz ka sani a yau na gama duk wani shiri da nakeyi domin mallakar KARAGAR AJALI
Abu daya kachal nake jira shine bayyanar wannan takadiriyar yarinya lasmira
Domin tun a matakin farko na sami nasarar tarwatsa kan su farhan don haka babu abinda zai hana ni mallakar LASMIRA

Nasan da cewa har yanzu kana mamakin dalilin daya sa na barka a raye tun farkon kamoka har Zuwa Yanzu ba taredana hallaka ba
To ka sani ba don komai kake raye ba sai don kai nakeso ka dauke ni ka kaini can fadar MUGTARUL BARZAK
Mu ratsa ta cikinta har mu isa daki na karshe mu dauko TAKOBIN SAIFUL LAIHAM da KARAGAR AJALI
Daga wannan lokaci shikenan amfaninka ya kare a gurina nan take zan hallaka ka tunda baka da sauran amfani agurina
Yana zuwa daidai nan a zancensa sai aljani Marwanulhas ya tuntsure da dariya daga bisani kuma ya tsuke bakinsa
Al'amarin daya matukar baiwa Boka hulbaz mamaki kenan acikin zuciyarsa yace
Shin Wannan aljani menene Abin takamarsa da har Yake iya tsayawa yayi jayayya dani ?
Marwanulhas yace tabbas ni idan ka kama ni na yarda Kayi galaba akaina amma abune mawuyaci ka Iya samun nasara akansu farhan duk da cewa kuwa kansu arabe Yake
Shin idan har ka mallaki lasmira tayaya kake Ganin zaka sami taswirar dake jikinta bayan itama bata san da maganar ta ba?
Dajin wannan tambayar sai yayi karamin murmushi yace Wannan kuma aikina ne tuni na gama dashi
Domin yanzu haka ina Tareda jinin sarauniya nauwaratul hasnal atare dani
Zan iya amfani dashi domin karanta wannan taswirar……..
Suna cikin wannan tattaunawa ne
Kogon da suke ciki ya soma girgiza madubin tsafinsa ya fara tangal tangal kamar zai babbako daga jikin bango ya fado kasa
Komai na tsafinsa ya tsaya cak ya daina aiki
Ita kuwa wannan kwalba da aljani marwanulhas Yake ciki take tayi bindiga ta tarwatse
Ya fito daga cikinta , nantake girman jikinsa da manyan fuka fukansa suka dawo yadda suke abaya
Shi kuwa boka hulbaz hankalinsa ne ya dugunzuma ya manta da maganar aljani marwanulhas
Wanda saboda ganin ya sami wannan damar tuni ya bude fuka fukansa ya sulale ya fice daga cikin wannan kogo
Jim kadan sai komai ya lafa kawai sai yaga
Anyi wani rubutu akan allon tsafinsa da launin ja Cikin manyan baki kamar haka

LOKACI YAYI DA ZAKA NEMO LASMIRA

Yana gama karanta wannan rubutu take hoton komai ya dauke
Nantake ya tuntsure da mahaukaciyar dariya wacce tasa kogon dinga amsa kuwwa
Kasa kuwa ta dinga fantsama tareda tsawa , sai dayayi dariyar ta isheshi sannan ya tsuke bakinsa ga barin yinta

Sannan yayi girgiza faruwar hakan keda wuya take ya rikide zuwa siffar mikiya ya tashi sama tareda ratsawa ta cikin gajimare ya nufi hanyar shiga birnin misra

SHIN YANA SAMUN DAMAR MALLAKAR LASMIRA?

DON SANIN YADDA ZATA KASAN CE MU HADU A KASHI NA GABA
DAGA NAKU HABIBULLAH KBRKARAGAR AJALI 8

++++++++PART B

LBR

+++++++HABIBULLAH KBR

SADAUKARWA GA UMMU JAWAHEER
AND
AHMAD ZIZA JR DAN ZAKI

Al'amarin gimbiya Husnaila kuwa lokacin da suka fito Neman su farhan a karo na biyu Tareda aljani marna'ul safran
sai suka wanzu suna masu keta hazo Tareda kara azama domin
ganin sun riske su da wuri Kafin lokaci ya kure musu
Tunda suka fito a wannan karon babu abinda husanaila take face tunani
da mamakin yadda akayi ta rasa Wannan jini da yake cikin battar ta dole akwai dalilin faruwar hakan
Sannan abu na biyu da yake mata yawo acikin zuciya shine Tayaya
zata iya fuskantar su farhan alhalin ta tafi ba tareda tayi musu sallama ba
Sannan idan har suka gano cewa ta debi jinin nauwaratul hasnal zasu kara yarda da ita a karo na biyu?

Amsar data kasa baiwa kanta kenan, suka ci gaba da tafiya abinsu har rana ta fadi a sannan ne sukazo giftawa ta saman wani daji mai tarin ni'ima

Komai na cikin wannan daji kuwa a tsabtace yake duk da cewa a kwai tarin dogayen bishiyu acikin amma ba zaka ga ko ganye guda daya a cikinsa ba
Akoda yaushe Wannan daji a tsabtace yake kamar share shi akayi
Sannan ga tarin wasu kyawawan tsuntsaye acikinsa masu rera wani daddadan kuka Mai dan karen dadi

Sannan a gefen Wannan daji wata 'yar karamar korama ce wacce ruwa garai garai mai haske Tareda gardi yake gudana acikinta
Koda zuwansu daidai wannan daji take husanaila taji ta kamu da matukar sha'awar yada zango acikinsa

Don haka ba tareda bata lokaci ba ta umarci marna'ul safran dayayi kasa kasa domin tana son yin rangadi acikin wannan daji
Ba tare da bata Lokacin komai ba ya saki fuka fukan nasa ya sauka akan turba

Take aljani marna'ul safran ya rikide zuwa siffar matashin saurayi
Husnaila ta shige gaba shi kuwa yabita abaya a sannan nefa ta karajin sha'awar wannan daji ta shiga ranta saboda
daddadar iskar dake kadawa acikinsa wacce har saida ta kwance gashin kanta ya zuba kasan mazaunanta
Sannu a hankali ta durfafi inda wannan koramar take wacce gefenta
ke cike da tarin wasu gajerun bishiyu masu kyau na 'ya'yan itatuwa nunannu masu dan karen zaki tana zuwa ta mika hannunta ta tsinki wani anibi nunanne ta sanya a bakinta ta fara ci
Daga nan saita cire doguwar rigar dake jikinta ya zamana daga ita sai wata gajeriyar riga da karamin wando ajikinta sannan ta daka tsalle ta fada cikin wannan koramar ta fara wanke jikinta
Shi kuwa aljani marna'ul safran sai ya tsaya a bakin koramar yana gadinta domin tabbatar da tsaro
Nanfa husanaila ta ci gaba da ninkaya acikin wannan ruwa tana wanke jikinta dashi
Tana cikin wannan wanka ne ta hango wani dan karamin kifi mai matukar ban sha'awa shi kadai acikin wannan korama yana ninkaya acikinta
Shi dai wannan kifi ba irin wanda aka saba gani bane domin haske ne kamar farar fitila
Sannan kana iya ganin komai na jikin wannan kifi hatta giftawar jininsa
Tunda husnaila take bata taba yin arba da kyakkyawar halitta mai kyawun wannan kifi ba
Don haka take taji ta kamu da tsananin sha'awar ta kama shi ta kiwata shi a tare da ita
Koda yin wannan tunani take tayi nutso a kasan wannan korama tabi bayan wannan kifi
Koda kifin yayi arba da ita take shima yayi nutso a kasan koramar domin tsira da rayuwarsa

Nanfa aka kasa mahaukacin tsere tsakanin su domin duk da kankantar wannan kifi sai gashi yana da karfin gudu tamkar babban kifi
Saboda haka saita kara kaimin gudunta abu kamar wasa sai gashi wankin hula yana neman kaita dare
Ta tabbatar da cewa idan tayi sakaci wannan kifin zai iya kubce mata gaba daya
Dayin wannan tunani take ta karanta wasu dalasiman tsafi ta kara dulmiya kanta acikin ruwa
Sai gashi a wannan karon ta kurewa wannan kifin gudu cikin kankanin lokaci ta riski karamin kifin
Cikin zafin nama ta kai hannunta da nufin cafke wannan karamin kifin
Koda hannunta ya sauka ajikin wannan kifi take wata irin tsawa mai karfi gami da walkiya suka tashi

Kawai sai ji tayi wata iska mai karfi ta shure ta tayi sama da ita sannan ta watsar da ita acan gefe daya
Nan take launin ruwan koramar ya canja daga fari zuwa launin jini
Komai na dajin shima ya chanja daga ainihin launinsa zuwa mummunan launi
Shi kuwa wannan kifi take wannan hasken na jikinsa ya fita daga jikinsa ya tashi sama launin sa kuwa ya chanja zuwa bakikkirin
Gimbiya husnaila bata san lokacin data saki wannan kifin ba ya fada cikin koramar
Sannu a hankali wannan hasken na jikin kifin ya dinga tashi sama kamar turiri
Daga bisani kuma. Ya cure a guri daya sai gashi ya rikide zuwa siffar wani dattijon aljani mai matukar kamala

Wanda gaba daya jikinsa babu bakin gashi koda guda girman wannan aljani ya ninka aljani marna'ul safran sau biyu
Idanunsa kuwa dara dara ne masu matukar haske hannunsa na dama yana ruke da ruhin wannan karamin kifi

Na hagu kuwa yana ruke da wani karamin akwati wanda cikinsa babu komai sai wasu kwalabe guda bakwai cike da rayukan halittu
wadanda suka hada jinsin farar fata, bakar fata da dai sauran nahiyoyi
har guda bakwai acikin kowacce daya daga cikin su suna ta yakar
junansu da zubar da jini domin ganin daya daga cikinsu ya hau saman daya daga cikin kwalaben amma an rasa wanda ya iya zuwa zuwa saman nata
Take wannan aljanin ya sunkuyo da kansa kasa ya karewa su husanaila kallo sama da kasa cikin alamun damuwa kamar kace kyat ya fashe da kuka saboda tausayinsu

Daga bisani kuma sai fuskarsa ta juye zuwa wani yanayin daban na rashin imani kawai sai ya bushe da dariya
Wacce tasa dajin amsa kuwwa har zuwa sauran dajijjikan dake makobtaka dasu
Saida yayi wannan dariyar ta ishe shi sannan ya tsuke bakinsa kamar aiko masa da sakon mutuwa
Al'amarin daya baiwa su husnaila matukar mamaki kenan taji ba zata iya shiru ba
Ta dubi wannan aljani tace yakai wannnan aljani wanene kai kuma meke tafe da kai? Sannan mene dalilin sauyawar kamalarka agaremu?
Dajin wannan tambaya sai bakon aljanin ya kara dubansu a karo na biyu a lokacin da fuskarsa ta sake juyewa irin ta mutanen kirki daga bisa ni yace
Yake wannan bil'adama ni sunana Aina'ul zaljas kuma an halicceni ne domin wanzar da zaman lafiya da kuma fitina a cikin wannan duniyar taku
Yake husnaila ki sani an haliccine tun shekaru dubu dari biyu da doriya
Tun daga randa aka samar dani ne aka sanya ni ajikin wannan kifi domin wanzar da zaman lafiya acikin wannan duniyar taku
Zamana ajikin wannan kifin shine abinda zai zaunar da zaman lafiya a wannan duniya
Kuma wannan kifi muddin ina zaune ajikinsa zai iya rayuwa har zuwa karshen duniya ba tareda ya mutu ba

Ba zan taba juyewa izuwa siffata ta biyu ba har sai lokacin da wannan kifi ya mutu
Shi kuma ba zai taba mutuwa har sai lokacin da wani bil'adama
ya taba jikinsa to anan take zai kamu da cutar ajali domin an lalata duk garkuwar dake jikinsa
Yake husnaila ki sani ajikin wannan kifi ne aka ajiye sinadarin dake baiwa Sarauniyar kyau lasmira kariya wacce ita kuma ke dauke taswirar zuwa fadar Rugtarul barzak

Muddin wannan kifi yana raye babu wanda ya isa ya iya ganeta

Yana zuwa daidainan a zancensa sai yayi musu nuni da ruhin wannan kifi dake hannunsa yaci gaba da cewa

Nan da ko. Wanne lokaci wannan ruhi zai iya kamawa da wuta ya kone kurmus
Don haka da zarar ya gama konewa to asannan ne fuskata ta biyu zata bayyana acikin
Duniya, ma'ana mutane da aljanu zasu fara yakar junansu dare da rana
tekuna su rine da jini, gawarwaki suyiwa kasa ado ta yadda idan gumu ya kai gumu sai ka rasa tsabtataccen gurin takawa face ya rine da jini
Duk wadannan abubuwa zasu faru ne sanadiyar bayyanar lasmira
Yayinda kowa zai kwallafa rayuwarsa domin mallakar ta inda dubunnan rayuka zasu yi ta salwanta a kowacce rana

Wannan akwati ta hannun haguna kuwa ba komai bane face rayukan da zasu yita fafutukar ganin sun hau kan karagar ajali daga nan har zuwa kashen duniya

A kullum kuma a duk lokacin da wani ya mutu a lokacin ne za'a kara haifar wani
Haka zasuyita salwantar da rayukan su a banza,

Duniya ba zata gyaru ba harsai. Zuwa kashen zamani inda wasu masu bakin addini zasu bayyana

Su ma'abota wannan bakon addini basa tsafi amma kuma addininsu yana da matukar karfi
Su kadaine zasu kawo karshen zubar da jini a duniya,

Amma duk da haka akwai hanya guda daya ta rage afkuwar zubar da jini acikin duniya
Wannan hanyar kuwa itace dolene duk wanda ya sami damar mallakar KARAGAR AJALI
wajibi ne a gareshi daya sadaukar da rayuwarsa ga KARAGAR AJALI
Wannan ce kadai hanyar da za'a iya rage ZUBAR DA JINI adoron kasa
Koda aljani aina'ul zaljas yazo daidai nan zancensa sai ya tsuke bakinsa bai kara yin magana ba
Har husnaila ta bude bakinta da nufin yi masa tambaya kawai sai taga ya rikide ya sake komawa hayaki ya bace cikin iska

Bacewar aljanin keda wuya husnaila ta ruga da gudu inda marna'ul safran ke tsaye cikin siffar matashin saurayi tace

Ya kai abokin tafiyata ya zama tilas mu kara azama domin zaman hutu bai kama mu ba
Kar muyi sakaci a wannan karon su farhan su subuce mana
A halin yanzu nasan duk inda suke ba zai wuce hanyar zuwa birnin misra ba
Dolene mu bisu can mu riskesu tun kafin Lasmira ta bayyana a idon duniya kar muyi sakaci a wannan karon
Dajin wannan batu take aljani marna'ul safran ya koma ainihin siffarsa
Sannan ya shureta ya dora agadon bayansa take ya bude fuka fukansa ya sake nutsewa acikin gajimare tareda kusantar hanyar birnin misra
Nanfa suka ci gaba da kutsa kai acikin iska cikin wani irin gudu na ban al'ajabi ba tareda dayansu yayiwa daya magana ba
Har suka shafe dakiku masu yawa ba tareda dayansu yacewa abokinsa uffan ba

A sannan ne aljani marna'ul safran ya katse shirun dake tsakaninsu yace
Yake husnaila idan har muka riski su farhan anya kuwa kina ganin
a wannan karon su Nauwaratul hasnal zasu yarda damu a karo na

Please Login or Register in order to submit comment