Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

C

+++++++LBR

HABIBULLAH KBR

Lokacin da wannan shirgegiyar halittar ta doka su aljani farsad bin bardas da kasa
Kamar tayi jifa da sillen kara suka fadi can gefe daya
Cikin tsananin juriya aljani farsad ya mike tsaye tareda gyara tsayuwarsa
Yayinda itama bhajaht ta gyara tata tsayuwar tareda zare sharbebiyar takobi tana mai fuskantar halittar
Koda Wannan halittar taga tsananin tsaurin ido Irin na jaruma bhajaht sai mamaki ya kamata bata san sanda dariya ta kwace mata ba daga bisani kuma ta tsuke bakinta ga barin dariyar
Tace Lallai bil'adama bashi da kunya Yanzu ke Wannan 'yar karamar halittar idan banda tsaurin ido da rashin kunya taki tayaya zakiyi tunanin zaki iya gabza yaki dani
Har ki sami nasara?
Ki sani. Atsawon rayuwata a wannan duniyar na gabza yaki da manyan mazaje da sarakuna marasa adadi
Gaba dayansu babu wanda ya iya ketare Wannan daji a raye ko kuma shafe dakiku dari uku da sittin muna yaki dashi ba tareda na tura shi barzahu ba
Ke kuwa wacece acikinsu da har kike da tsaurin idon tsayawa a agabana?
Dajin wannan tambaya sai jaruma bhajaht ta daka masa Tareda cewa
Ai kuwa wannan karon Kayi gamon da baka isa ka tsira daga kaifin takobina ba
Ina mai tabbatar maka cewa duk tsawon shekarun da suka shude kananun jarumai kake haduwa dasu Yanzu kuwa tarihinka na daf da shudewa
Ina mai rantsuwa a da abin bautata Wannan karon duk abindaya shiga gabana sai na shafe tarihinsa komeneneshi
Sannan na wuce wuce kan narkakken dutsen wuta na dauko takobin saiful laiham kota wanne Irin hali

Koda jin wannan batu sai halittar ta kara bushewa da dariya a karo na biyu Wacce tafi ta farkon

Daga can kuma sai ta shammaci su bhajaht ta kawo musu wani mahaukacin duka da hannunta
Cikin zafin nama aljani hursad bin zafran ya shuri bhajaht daga gurin
Halittar ta sami kasa saboda karfin dukan saida kasa ta danyi girgiza

Kafin ta sake juyowa inda suke tuni suma sun afka mata
Nanfa suka ruguntsume da azababben yaki mai matukar muni guri ya rincabe
Tun ba'a dauki dogon lokaci da fara fafatawar tasu ba suka hargitsa dajin gaba daya kai kace yakin duniya
Kura ta turnuke dudufniyar kafafu da gunjin halittar ya cika dajin
Sai ga halittar ta fito da wasu zakwa zakwan farata daga jikin hannunta masu matukar kaifi da tsini wadanda suka kasance makamai a gurinta tana kai. Musu sara dasu
Da zarar makaman dake hannun su bhajaht sun hadu da farcen wannan halittar sai dai kaga tartsatsin wuta mai karfi ya tashi tamkar ana hura wuta a makera
Idan kuwa ta karci bishiya da wadannan faratan nata saidai kaga ta jijjigogota daga karkashin kasa har jijiyoyin jikinta

Ta fadi kasa rikica, idan kuwa dutse ne sai kaga ya dare biyu kamar an yanka tufa
Duk da cewa su biyu ne sai gashi sun kasa samun damar koda lakatar jikinta
In badon suna da matukar zafin nama ba da tuni halittar ta mitstsikesu da kafafunta saboda mugun takun da take kawo musu
Sai da suka shafe lokaci mai tsawo suna fafata yaki da wannan halittar ba tareda sun sami Koda karamar nasara akanta ba
Kai ko. Kadan ma sun kasa samun damar koda kusantar jikinta bare su tabuka wani abin
Nanfa suka fara tunanin hanyar daya kamata su bullo mata Domin sun tabbatar da cewa a wannan karon Karfin damtsensu ba zai taba cetonsu ba
Dole sai dai su hada da dabarun yaki, suna cikin wannan haline
Halittar ta shammacesu ta cafki kafafun aljani hursad da hannunta guda daya
Sai gashi duk girmansa yana reto acikin Hannun nata ba tareda ya iya kwacewa ba
Wannan ce damar da bahjhat ta samu ta shammaci Wannan halittar ta daka tsalle daga kan aljani hursad ta dira akan wannan halittar
Wohoho sai gashi tana tafiya ajikin wannan halita kamar kadangare ajikin bango Cikin azababben gudu
Tana kai mata sara da takobin hannunta,
Koda halittar ta lura da akwai mutum akanta sai ta saki aljani hursad ta wullashi can gefe ta dinga kai mata duka da lafcecen hannunta
Cikin zafin nama bahjhat ta dinga tsalle tana tsallake dukan da take kawo mata Cikin azababben zafin nama
Ahankali har ta isa doron wuyan ta daga takobinta iya karfinta ta caka mata ita a tsakiyar wuyanta
Nantake halittar ta kwallara wani ihu mai karfin Gaske wanda ya karade dajin gaba daya alokacin da jini yayi feshi daga kan wuyanta kamar an bude magudanar ruwa
Kafin bhajaht ta zare takobin daga jikin wuyanta
Tuni ta gabza mata duka da hannunta guda daya
Saboda karfin dukan saida ta luluka sama , sai gashi tana yawo a saman iska daga bisani ta fado Cikin wani dajin a tsakiyar wasu dogayen Bishiyoyi
Nanfa jikinta ya dinga buguwa da rassan bishiyun ta fara Neman fita daga hayyacin ta koda ganin haka take aljani hursad ya yunkuro da karfin gaske daga inda yake kwance Cikin azababben gudu Kafin ta isa kasa ya shureta ta hannayensa suka luluka Cikin gajimare suka bar wannan halittar tanata faman birgima akasa har saida ta sandare ta zama gawa

Nanfa suka bar wannan daji suka nufi daji na gaba , saida sukayi tafiyar sa'o'i masu yawa basu hadu da wani abin cutarwar b

Sai bayan sunyi nisa da fita daga cikin wannan daji ne suka isa Cikin daji
na gaba wanda hannayensa gaba daya ya banbanta da wanda da wanda suka baro domin shi babu komai acikinsa face dusar kankara wanda saboda matukar sanyinta basu san lokacin da suka fara kyarmar sanyi ba kasancewar babu kaya masu dumi ba

Cikin wannan daji kuwa gaba dayansa babu wata halitta ko guda daya da take rayuwa acikinsa saboda matukar sanyin da ake
Haka dai suka ci gaba da kutsa kai cikin wannan daji ba tareda fargabar komaiba kai kace suna tafiyane acikin gidansu

Daga can sai aljani hursad yace da ita ya shugabata Hakika tun da nake rayuwa ban taba ganin guri mai matukar sanyin Wannan daji ba
Ki duba fa saboda bala'in sanyinsa ko halittu masu rayuwa babu acikinsa

Dajin wannan batu saita yi wani guntun murmushi wanda ya kasa gane dalilin yinsa
Daga bisani kuma tace, dadi na dakai shine saurin mantuwa shin ka manta sunan duniyar da muka kawo kan mu ne?
Idan ka manta sunanta DUNIYAR HALLAKA
Fiye da daruruwan shekaru duk wanda ya shigo cikinsa baya fita a raye saboda bala'in da ke cikinsa
Nima kaina bani da tabbacin zan iya fita daga cikinsa bare kuma kai
Abin da kawai nake so shine mu hada kamu wajen taimakon juna ta Hakane kadai zamu sami nasarar mallakar Abinda muka fito nema
Daga wannan furuci bata kara magana ba suka ci gaba da tafiya a hakan ba tareda sun tsaya yada zango ba

Yayinda sukayi nisa a cikin dajin ne suka iso saman wani teku wanda tuni kankara ta gama lullube kansa har wani tururi ne yake tashi daga jikinsa saboda tsananin sanyinsa

Koda isa tsakiyar wannan teku kwatsam ba zato ba tsammani sai ga wata lafceciyar macijiya mai matukar girma gami da kauri Wacce basu taba gani ko jin labarin macijiya Mai Irin girmanta ba
Ta faso ta kasan tekun ta taso sama kai kace daga cikin baka aka harbota ta
Kafin suyi wani yunkuri saboda matukar zafin naman macijiyar tuni ta nannade su duk su biyun ta koma kasan ruwan dasu
Nantake kuwa ruwan ya hade kansa Tareda komawa yadda yake abaya
Saboda tsananin matsar da wannan macijiyar tayi musu sai suka kasa Koda daga hannayensu Tareda yunkurin kwatar kansu
Koda suka nutse a kasan tekun take jikinsu ya fara sandarewa
Idanunsu suka fara kakkafewa saboda bala'in sanyin dake kasan sa
Tumi suka fara fita daga cikin hayyacinsa gaba daya suka saki jikinsu
Domin sun tabbatar da cewa wannan karon babu abinda zasu iyayi. Domin kwatar ransu

WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GA JARUMA BHAJAHT DA ALJANI HURSAD ACIKIN DUNIYAR HALLAKA

********* ********** ******

Acan kuwa Al'amarin SARKI GULBAS DA GIMBIYA Suhaila kuwa lokacin da wannan tsuntsun tsafin dake dauke dasu ya kama hanyar tafiya kogon hallaka
A wannan lokaci sai da suka shafe kwana guda da wasu sa'o'i suna tafiya a sararin samaniya sannan da tsakar rana suka isa bakin tekun bahar JURRAS
Wanda a wannan lokaci babu wata teku mai girmansa a kaf fadin duniya
Sai ambaliya igiyar tekun takeyi kai kace zai kwace ya dulmiyar da duniya baki dayanta
Koda isowarsu bakin wannan teku take tsuntsun ya saki fukafukansa ya sauka bisa turba abakin gabar tekun
Ba tareda yayi. Yunkurin shiga cikinsa ba
Nantake sarki gulbas ya runtse idanunsa tareda karanto. Wasu dalasiman tsafi acikin zuciyarsa Tareda tofawa a kan tekun
Aikuwa yin hakan keda wuya take tekun ta fara kadawa da karfin gaske fiye da farko ruwan ya dinga fallatsi da tsiri Kamar zai hade da sararin samaniya

Sannan aka dinga tsawa da walkiya daga sararin samaniya mai karfin gaske wacce kan iya zautar dame sauraronta
Nanfa ruwan ya cigaba da hautsinewa yana tumbotso da kugi mai karfin gaske har wata kumfa mai kauri ta dinga tasowa daga kasansa
Jim kadan saiga wani dan karamin kwale kwale ya taso daga kasan tekun wanda girmansa ba zai iya daukar Mutum fiye da biyu ba
Sannu a hankali kwale kwalen ya karaso inda suke sannan ya tsaya a saman ruwan
Ba tareda bata lokaciba su sarki gulbas suka shige Cikin wannan kwale kwalen shi kuwa wannan tsuntsun tsafin take ya dinga kankancewa har sai daya koma baifi kamar girman kurciya ba Sannan ya kada fuka fukansa ya sauka akan kafadar sarki gulbas
Nantake kuwa kwale kwalen ya fara tafiya da kansa dauke dasu a saman ruwan ba taredaya nutse kasa ba
Su. Kuwa duk sun zauna sosai acikinsa sun nutsu domin ganin yadda zata kasance Tareda dora hannayensu akan takubbansu suna jiran tsammani
Sai. Da suka jima suna tafiya a saman Wannan teku ba tareda sun hadu da wani abin cutarwar ba
Sannan kuma har tsawon wannan lokaci ruwan bai daina tambal tambal dasu ba
Suna cikin wannan hali ne sukayi arba da wani katon kifi mai matukar girman gaske wanda tunda suke basu taba ganin kifi mai girmansa ba
Ya taho daga nesa da inda suke cikin a zababben gudu
Nanfa suka fara amfani da karfin sihirinsu domin su dakatar da karasowar Wannan kifi amma abu ya gagaresu
Sannan sukaji. Kamar an daure kafafunsu da manyan sarkoki suka kasa koda motsa jikinsu daga inda suke tsaye
Babu Irin kokarin da basuyi ba domin ganin sun tabuka wani abin amma abu ya gagara bisa dole suka saduda tareda zubawa sarautar Allah ido
Koda Wannan kaifi ya karaso inda suke take ya bude wangamemen bakinsa ya hadiye su gaba daya su biyun
Sannan ya nutse a kasan tekun Tareda ci gaba da tafiya abinsa yana kutsawa ta kasan tekun Cikin azababben gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya
Haka dai wannan kifi ya dinga ratsawa har ta kasan duwatsu Cikin azababben gudu
Bai tsaya ba sai daya fasa kasa ya sauka Cikin wani kasurgumin daji wanda babu koda bishiya kwaya daya acikinsa face tarin wasu dogayen tutoci masu launin ja da kuma zanen kwarangwal din fuskar bil'adama ajikinsu
Sai kadawa suke acikin iska
Nan Take Wannan kifi ya amayar dasu sarki gulbas da gimbiya suhaila a wannan dajin
Sannan jikin kifin ya rubushe agurin ya zama gari shima garin ya tashi yabi iska
Koda su sarki gulbas suka tsinci kansu acikin wannan daji wanda babu gida gaba ba gida baya sannan basu ga alamar akwai wani abu mai numfashi ba a cikinsa sai wadannan jajayen tutoci
Take suka mimmike tsaye tareda gyara damararsu, anan nefa sarki gulbas ya dubi suhaila yace yake
'yata tofa ki sani yau mun shigo guri mafi hadari a duniya don haka ina mai gargadin ki da kada ki kuskura ki aikata wani abun ba tareda izini na ba
Dajin wannan umarni na sarki gulbas sai ta girgiza masa kanta alamar ta gamsu da bayanansa b Tareda tace uffan ba
Ba tareda bata lokaciba suka durfafi inda daya daga cikin tutocin take
Suka kura mata ido sai sukaga anyi Wasu kananan rubutu akasan tutar cikin yaren tsafi
Wanda a iluminsu basu taba ganin wannan yaren ba , nanfa suka fara kokarin karanta abindake rubuce ajikin tutocin amma sai Abu ya gagaresu saboda matukar sarkakiyar da take cikin rubutun
A sannan ne sukaji an bushe da mahaukaciyar dariya wacce ta karade dajin baki daya suka kasa gane daga inda sautin dariyar Yake tahowa.
Don haka sai suka nutsu Tareda kasa kunnuwansu sai da aka dauki dogon lokaci ana kyakyata wannan dariyar sannan komai ya lafa
Sukaji wata kakkausar murya tana cewa
BARKANKU DA ZUWA DUNIYAR MUSIBA , YAKU BAKI ACIKIN WANNAN DUNIYAR TOFA KU SANI DAGA YANZU BAKU DA SAURAN IKO DA KANKU DA KUMA RAYUWARKU ACIKIN WANNAN DUNIYAR BAYAN HAKA KU SANI ACIKIN WANNAN DUNIYAR BABU WANDA YAKE DA IKON FITA DAGA CIKINTA A RAYE DUKKANKU SAI KUN ZAMA MATATTU GAWARKU MA A NAN ZATA BUSHE TA ZAGWANYE…… .
Koda jin wannan batu take zuciyar sarki gulbas ta fara tafarfasa kamar zata kone
Nantake ya dakawa mai maganar tsawa yace karyarka tasha karya ka sani baku isa ku. Iya cutar da koda Mutum daya daga cikin mu
Nayi rantsuwa da allon tsafi na wannan karon sai na karya alkadarin wannan duniyar gaba dayanta na dauki abinda ke cikinta kamar yadda nayi alkawari tun farko

Idan har ka isa kai namiji ne ka fito fili mu fafata ba ka buya a wani gurin kana cika baki ba

Kodajin wannan batu sai aka sake bushewa da dariya a karo na biyu sannan akace
Ka kwantar da hankalinka dan samari a sannu zan bayyana gareka
Da gama fadin haka sai sautin komai ya dauke suka daina jinsa
aikuwa daukewar sautin keda wuya sai suka fara tafiya acikin dajin suka kutsa cikinsa ba tareda sanin inda suka dosa ba
Sai da suka shafe Tsawon Lokaci suna tafiya ba tareda daya daga cikinsu yayi magana da daya ba
A sannan ne sarki gulbas yayiwa gimbiya suhaila wani kallo wanda bai saba yi mata irinsa ba
Wanda sai dayasa taji zuciyarta ta buga da karfi ta dubeshi tace
Yakai abbana shin menene dalilin Wannan Irin Kallo da kayi min
Kodajin wannan tambaya sai yayi murmushi yace menene amfanin boye mini ainihin siffar ki?
Inaso ki sani naga dukkanin abubuwanda kika aikata acikin birnina tun daga lokacin dana kwanta rashin lafiya
Har zuwa dawowarki daga gidan gonarki na bayan gari
Naga tsananin jarumtakar da kike da ita wannan daliline yasa na amince da zuwa wannan guri tare dake
Ina da tabbacin cewa koda ni ban sami damar daukar Saiful laiham ba ke zaki iya daukarta
Kuma a kowanne irin lokaci zaki iya taimakon kanki
Abu daya da zan gargade ki Yanzu shine ki chanja tunanin cin amanata dake zuciyar ki
Domin da zarar na kamaki to zan yanke duk a lakar dake tsakanina dake kuma na yake ki da dukkanin makamai na na hallaka ki
Nasan zakiyi mamakin yadda na iya gano wadannan sirrika naki wadanda kika boye su acikin zuciyarki kuma bayan kin dakatar da duk wasu alkaluman tsafi na a wannan lokacin?

To Yanzu zan tuna miki cewar
Duk wanda ya riga ka kwana dole ya rigaka tashi, kuma komai sammakonka to ka sani wani a tafe ya kwana,
Yanzu zan gaya miki Abinda baki sani ba
Tundaga Lokacin danaga hargitsewar alkaluman tsafi na naji ajikina cewar dole akwai makusancinci na acikin wannan lamari
Don haka kai tsaye na shiga turakarki nayi amfani da madubin tsafinki
Ta cikinsa na. Gano duk wadannan al'amura, amma hakan baisa naji na tsaneki a zuciyata ba saboda kaunar da nake miki

Kodajin wannan batu take Gimbiya suhaila taji nadama tazo mata a karon farko
Nantake ta fadi a gabansa tana mai neman gafararsa saboda Yanzu ne ta tabbatar da matukar kaunar da mahaifinta yake mata
Sannan suka ci gaba da tafiya abinsu, saida suka yini suna tafiya ba tareda sun hadu da wani mugun abin ba har rana ta fadi
Don haka suka sami guri suka kafa tanti sukaci abinci sannan suka raba kwanciya kowa ya kwanta tsawon rabin dare sannan suka tashi suka ci gaba da tafiya
Basu jima da tafiya ba suka isa wani daji mai cike da tarin ni'ima wadanda suka hada 'ya'yan itatuwa kamar su rufta, fasadabur, inibi da dai sauransu koraye nunannu
Sannan ga tarin ciyawa mai laushin gaske ga tarin tsuntsaye masu kyawun gaske
A gefen dajin kuwa korama ce wacce ruwa garai garai ke gudana acikinta
Da isarsu wannan daji sai suka cigaba da tafiya acikin sa hankalinsu akwance
A nan nefa husanaila ta hango wani jan tsuntsu kyakykyawa akan Wata itaciya Yana rera kuka mai dan karen dadi wanda yayi matukar bata sha'awa
Koda ganin wannan tsuntsu sai ta zaro kibiya ta dana a kan bakanta da nufin harbin wannan tsuntsun
Da ganin abinda take shirin yi charaf sai gulbas ya ruke hannunta yace
Karki kuskura ki taba wannan tsuntsun da duk wani abu daya danganci ni'ima ko kuma sha'awa dake wannan guri domin suna iya zama tarko a gare mu
Ba tareda gardamar komai ba kuwa ta mayar da kibiyar tata, suka ci gaba da tafiya a hakan
Haka dai suka dinga wuce kayan alatu iri iri agabansu ba tareda sun tsaya daukar komai na daga cikinsu ba
Koda suka zo giftawa ta gaban wani lambu sai sukaji wani irin daddadan kamshi ya bugi hancinsu
Wanda ya ratsa kwakwalwarsu gaba , Ai kuwa shakar wannan turare keda wuya take sukaji Wata kasala ta kama su idanunsu suka fara lumshewa

Kafin a dauki dogon lokaci tuni barci Mai nauyi ya dauke su duk su biyun
Sai farkawa sukayi suka tsinci kansu acikin wani kogon dutse wanda babu komai acikinsa face tarin yana kamar ta gizo gizo ta wani yawu mai santsi da ya malale ko ina a cikin kogon dutsen duk jikinsu kuwa a daddaure yake da sarka mai matukar kaurin gaske wacce saboda kaurinta sai suka kasa motsa jikinsu gaba daya
Sannan ko ina acikin kogon dutsen babu komai face kwarangunan mutane da aljanu fululu
Baka jin sautin komai acikin wannan dutse face wani sautin kuka Mai kama da kukan gyare wanda ya karade kogon gaba daya suka rasa daga inda sautin yake tasowa
Koda ganin su acikin wannan guri take hankalinsu ya dugunzuma ya tashi
Suka Fara kokarin tsinka Wannan sarkar da karfin damtsensu amma abu ya gagara
Daga nan suka fara amfani da karfin sihirinsu amma sai sukaga kamar kara tamke kansu suke
Har wani zafi da radadi sukaji yana ratsa kashushuwansu don dole suka hakura Tareda zubawa sarautar Allah ido
Bayan Wasu 'yan dakiku sai sukaji Wannan sauti yana karuwa Tareda gurnani yana kara tashi fiye da ko yaushe wanda ya kara karade kogon gaba dayansa
Daga can kuma sai suka. Fara jin wani ruwa mai matukar yauki yana kwaranyowa ta saman kansu
Cikin sauri suka daga kansu sama domin ganin abinda yake faruwa
Take sukayi arba da wata shirgiyar halitta mai kama da gizo gizo tana saukowa daga saman
Saidai shi wannan gizo gizon kowacce kafarsa guda daya ta kasance tana da matukar kaifi da tsini kamar karshen takobi

Sannan yana da kawuna guda goma a gangar jikinsa kuma a jikin kowanne kai a kwai idanuwa goma wandanda Yake Ganin duk abinda yake gabansa dasu
Bayan haka yana da sharbebiyar jela mai matukar tsayi da kauri
Lokacin dasu sarki gulbas sukayi arba da wannan gizo gizo take hankalinsu. Ya dugunzuma ainun suka fara yunkurin ceton ransu domin sun tabbatar da cewa idan har basu tabuka wani abu ba tofa a nan gurin dukkansu zasu rasa rayuwarsu

WANNAN SHINE ABINDAYA. FARU GASU SARKI GULBAS BAYAN SUN FADA TARKON MUTUWA TUN A FARKON SHIGARSU DUNIYAR HALAKA

+++++++ ++++++++
SHIN SU SARKI GULBAS SUNA SAMUN DAMAR KUBUTA DAG WANNAN TARKON MUTUWAR DA SUKA FADA?
SHIN SU JARUMA BHAJAHT NA KUBUTA DAGA WANNAN KOGIN KANKARA?

INA LABARIN JARUMI RUKYAN DA BOKA SURKAIS?
DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MUN HADU A KASHI NA GABA
DAGA NAKU HABIBULLAH KBR

KARAGAR AJALI 8

+++++++++++

PART A

LBR

+++++++++++HABIBULLAH KBR

Lokacinda aljani rafkana ya shuri su jarumi rukyan suka luluka acikin gajimare domin zuwa cikin daji na biyu a cikin duniyar hallaka
Sai ya kara azama yana mai saurin tafiya duk da cewa yasan Wannan fa Tafiyar mutuwa yakeyi
Sai yaji cewa gwanda ya tunkareta gadan gadan kuma ya cire tsoro daga cikin zuciyarsa sannan ya kara dage damtse
Domin idan yayi hakan acikin biyu dole ayi daya
Kodai su sami nasara ko kuma akasin hakan
Amma idan ya sanya tsoro acikin zuciyarsa ya tabbata bazai sami zabin farko ba
Sai tabbacin zabi na biyu Wato mutuwa gaba daya wannan daliline yasa yaji dukkan tsoro ya fita daga zuciyarsa
Yaji aransa cewa duk wuya duk rintsi sai ya tabbata yakai matakin karshe yaga SAIFUL LAIHAM da idanunsa koda kuwa bai taba ba domin hakan ya zamarwa mahaifiyarsaa abin alfahari koda kuwa ya rasa rayuwarsa bashi da nadama
Ita kuwa lardisa sai ta koma gefe daya ta zauna ta dauko littafin kundin hikayoyin ta fara rubuta Abinda ta gani da idanunta acikin daji na farko tun daga farkon shigowarsu cikin wannan duniyar har zuwa yanzu
Shi kuwa jarumi rukyan yana can gefe daya Yana kallon yanayin sararin samaniyar dajin
Kawai sai ya kyallara ido ya hango Wannan kundun hikayoyi a gaban lardisa
Ai kuwa take ya taso daga inda yake ya matso daf da ita yadda har suna jin numfashin juna yace
Mai zai hana Yanzu ki ci gaba da karanto mana hikayar farhan muji yadda take kasancewa dashi bayan juyawar alkaluman tsafi?
Shin lasmira tana bayyana acikin kwanaki biyun da aka ambata?
Dajin wannan tambaya sai ta rungume littafin akirjinta tace mai kake ci ne na baka zuba?
Kada ka manta da halin da muke cikine yanzu ?ai ka bari mu sami gurin yada zango daga nan sai mu dora daga inda muka tsaya
Koda tazo nan a maganarta sai ya dora hannunsa akan cinyarta yace
Nifa matukar zan dinga sauraron Wannan daddadar hikayar babu abinda zai tsorata ni a rayuwa
Ni a yanzu ji nake ma kamar wannan hikayar tafi abindake gabana daraja
Don haka ina mai rokonki da darajar abin bautarki daki ci gaba da karantamana wannan hikayar don samun kwarin gwuiwar tunkarar abin dake gaban mu

Kodajin wannan batu sai ta ruke hannayen nasa da tafin hannunta tare da sauke masa tattausan murmushi tace karka damu tunda kai ka bukata ni kuma ya zama tilas na sanar dakai
Take ta kara gyara zamanta shi kuwa aljani rafkana sai ya fara sassauta karfin gudunsa domin ya sami nutsuwar sauraron Wannan hikayar

Ba tareda bata lokaciba ba lardisa ta budo shafikan baya sannan tayi gyaran murya domin janyo hankulansu daga bisani ta dora daga inda ta tsaya abaya
+++++ ++++++ +++++++

Lokacin da su sadauki Farhan Da sarauniya Nauwaratul hasnal suka tashi sama a kan Wannan dardumar tsafin
Sai ga dardumar tana tsula wani gawurtaccen gudu dasu acikin gajimare fiye da yadda aljanu sukeyi
Domin Karfin gudun da takeyi dauke dasu ya wuce tunanin mai tunani suna ketawa ta cikin hazo da kuma saman tsaunika kamar kiftawar ido
Basa taba yada zango face matsananciyar bukata ta kama dayansu kamar bawwali da makamancinsa
Sai. Su sami daji su yada zango acikinsa

WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GASU SADAUKI FARHAN BAYAN SUN TAFI BIRNIN MISRA AKAN DARDUMAR TSAFI

+++++ ++++++ ++++++

Acan birnin misra kuwa a wannan lokaci mulkin Wannan birni yana karkashin mulkin wani azzalumin matashin saurayi Mai suna shuraim bin mursan
Sarki shurais a tarihin birnin misra ba'a taba samun azzalumin sarki ba kamarsa
Kai a takaice dai tsayawa kwatanta zaluncinsa ma bata lokaci ne
Wannan daliline yasa talakawa ke matukar shakkarsa kai bama su kadai ba
Har manyan masu fada aji a birnin basa iya ketarewa maganarsa domin tsira da mutuncinsu

Wata rana sarki shuraim ya zauna zaman fada kamar yadda aka saba ya harde kafafunsa akan karagar mulki
Kawai sai

Please Login or Register in order to submit comment