Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce
Ba tareda bata lokaci ba ya kwance ta daga gadon bayansa
Dukkansu suna ta faman haki kamar ransu zai fita tareda kallon juna ba tareda dayansu yayiwa daya magana ba
Bayan sun dan jima ahakane sai ta katse shirun dake tsakaninsu tace
Gaisheka namijin duniya dole na jinjina maka tareda godiya bisa ga ceton rayuwata da kayi domin badon kaiba da yanzu labari na ya shude
Dajin wannan batu sai ya ajiye gwauron numfashi tareda cewa yake ma'abociyar Sani me kika sani dangane da wannan bala'i da muka shiga?
Kodajin wannan tambaya sai tayi shiru Tana tunani tsawon yan dakiku daga bisa ni kuma sai ta dago. Da kanta tace
Lallai mahaifina ya taba bani labarin wani abu mai kama da wannan
Lokacin ina karama amma ban fahimci mai yake nufi ba sai. A yanzu
A Lokacin ya shaidamin cewa duk bayan shekaru dubu dari alkaluman tsafi suna chanja wa kansu salo da tsare tsaren yadda kaddara zata kasance. Agaba
Aduk Lokacin da irin wannan al'amari yazo Hakan na janyo asarar dubunnan rayuka gami da dukiyoyi, sannan kuma sihirin tsafi yana daina aiki gaba daya sai bayan komai ya lafa
Kuma hakan na janyowa mutum Abinda zai faru nan da kwanaki dari uku da sittin da hudu wato shekara guda a tsawon yini guda
Lissafin ranakun zai koma daidai yadda yakene bayan Bayan kawanaki uku
Kaga kuwa indai hakane yanzu kwanaki ukune kacal suka rage lasmira ta bayyana
A halin yanzu duk wani wanda yayi nisa a cikin ilimin bokanci ya ga abinda ya faru kuma ya gane cewa wannan alamace ta bayyanar lasmira
Don haka muma zama bai kama mu ba dolene mu tashi yanzu mu gaggauta Zuwa birnin misra kafin kwanaki uku
Idan har mukayi sakaci abokan gabar mu suka rigamu riskarta shikenan mun rasa ta har abada ko kuma sai mun kara shan wata bakar wahalar kafin mu kwace ta

Tana cikin wannan furuci ne taji wani zafi akan wuyanta Cikin sauri takai hannunta ai kuwa sai taji alamun ciwo
Nan take zuciyarta ta buga da karfi al'amarin daya matukar razana ta kenan
Don haka nan take ta shafi kasa da tafin hannunta nan take tayi arba da Lokacin da boka durgas Yake tarar jininta acikin battarsa ta tsafi har zuwa lokacin daya baci
Amma wani abin mamakin sai ta kasa ganin Lokacin da aka debi jinin, da kuma sanda ya zuba daga jikinta
Al'amarin daya kara razana ta kenan tace da farhan tabbas Akwai mugun abinda yake shirin faruwa a kasa ,
Idan har mukayi ganganci boka durgas ya rigamu mallakar lasmira
To zai iya amfani da jinin jikina domin karanta taswirar dake rubuce acikin zuciyarta
Kodajin wannan batu sai. Shima ya dube. Adimauce yace yake wannan sarauniya Yanzu wacce hanya zamubi domin kawarda Wannan al'amari?
Dajin wannan tambaya Cikin rashin kwarin gwuiwa ta dubeshi tace hanya daya ce Yanzu ta rage mana
Hanyar kuwa itace zan tura masa da tsutsar tsafi wacce zata dinga bibiyar sa a duk inda yake da zarar yayi sakaci da wannan battar zata shiga cikinta zata shiga cikinta ta shanye wannan jinin Sannan ta kone kurmus ba zata kara tashi ba
Hanya ta biyu kuwa itace dolene mu isa birnin misra kafin kwanaki uku kacal
Tana gama fadin haka sai ta karanta wasu dalasiman tsafi guda hudu ta tofa akan kasa
Koda yawun nata ya sauka akan kasa sai ya rikide ya koma wata katuwar bakar tsutsa
Sannan tsutsar ta nutse acikin kasa ta bace musu da gani
Ba tareda bata lokaci ba suka hada hannayen su guri guda tareda karanta dalasiman tsafi
Aikuwa fara karatun nasu keda wuya sai kasar gurin ta dare
Jim kadan sai ga wata dardumar tsafi ta fito daga karkashin kasar ta tsaya akan iska
Take dukkansu suka haye kan dardumar suka zauna, Zamansu keda wuya sai dardumar ta tashi sama dasu ta bace bat acikin gajimare don zuwa birnin misra akan Lokaci

+++++++ +++++++++ ++++++++

Adaidai wannan gurine aljani rafkana ya katse karatun Labarin da lardisa take yiwa rukyan tareda cewa
Ka gafarce ni ya shugaba na sai ku fara shirye shiryen ku domin daf muke da isa tsuburin makabur inda anan ne zamu shiga duniyar hallaka
Amma ya shugabana koda ace ni na rasa rayuwata a wannan tafarki kai kuma ka sami nasara ina rokon ka dauki gawata ka kaiwa mahaifiyata Sannan ka nuna mata Saiful laiham ka sanar da ita cewa tare dani aka dauko ta
Idan kuwa bakayi nasara ba komai daren dadewa Inaso ka dawo ka kona gawata
Da hannayenka kuma kada ka bari mahaifiyata tasan Labarin mutuwa ta a wannan tafarki
Domin nasan dole zuciyarta ta buga ta mutu gaba daya
Kodajin wannan bukata ta aljani rafkana sai jikin rukyan dana lardisa yayi saboda tsananin tausayinsa
Bata san Lokacin da hawaye ya zubo daga cikin idanun ta ba
Amma sai tayi sauri ta goge hawayen don kar su lura da hakan
Acikin zuciyarta tace
Lallai buri shi yake makantar da dan adam har ga kai kanshi ga hallaka
Tabbas ruwa baya tsami banza dole akwai wani gagarumin bala'in acikin wannan duniya wanda mu bamu Sani b
Tunda duk abinda zai razana aljanu ba karamin bala'i bane
Tana cikin wannan zancen zuci ne ta fara hango tsuburin makabur anesa dasu kadan a tsakiyar wani katon teku wanda basa iya bango karshensa
Shi kansa wannan teku jiragen ruwa ma basa ratsawa ta cikinsa saboda yadda igiyarsa take kadawa da karfin gaske
Sannan a kullum ruwan tafasa yake kamar an dora takobina akan wuta
Suna fara hango wannan tsuburi take dukkansu suka fara gyara damararsu
Adaidai lokacin da suka isa gaban tsuburin sai aljani rafkana ya saki fuka fukansa ya sauka agaban tsuburin
Ba tareda bata lokaciba suma suka sauka daga gadon bayansa
Suka nufi kofar tsuburin Wacce ta kasance katuwar gaske saidai kuma cikinsa akwai duhun gaske
Nan take suka nemi itace suka kunna wuta ajikinsa , tareda kutsawa cikin tsuburin suna laluben kofar duniyar hallaka
Rukyan ne a gaba sai lardisa Wacce take take masa baya sai kuma rafkana
Suna tafiya suna dube dube tareda share yanar dake cikin kogon don neman wannan kofa
Yawan yanar dake cikin tsuburin ce ta tabbatar musu da cewa an shafe shekaru daruruwa ba tareda an shiga cikinsa ba
Sai da suka shafe yinin Wannan ranar suna laluben wannan kofa amma suka rasa kofar da suke nema
Har sun sami guri sun zauna sai suka hango wani tsuntsu ya shigo cikin tsuburin maimakon yayo inda suke sai ya kauce hanya yabi wata Hanyar daban take bangon ya bude kansa ya shige ciki
Koda ganin abindaya faru take suka fahimci akwai wani abu a Hanyar sa wannan tsuntsu yabi
Don haka sai suma suka tashi suka ga bayan sa, suna Shiga gurin take katangar ta mai da kamta ta rufe
Kawai sai wani haske ya fito daga idanun tsuntsun ya daki kirjin rukyan
Yayin da hasken ya daki kirjinsa take hasken ya kara karfi kamar zai kashewa su rafkana idanu
Har sai da suka sa hannu suka rufe idanunsu
Nan Take hasken ya gauraye kogon Gaba daya sannan kasar gurin ta rufta sai ga wata kofa ta jan haske ta bayyana tareda bude kanta
A saman kofar kuwa anyi rubutu cikin alkaluman tsafi da manyana baki an rubuta
BARKANKU DA ZUWA DUNIYAR BALA'I DA MASIFA
YAKAI BAKON WANNAN DUNIYA KA SANI CEWA ACIKINTA BABU ABINDA ZAI KWACEKA
FACE TSANANIN JURIYA , NACI, KARFIN BASIRA DA KUMA JARUMTAKA DON HAKA DUK ABINDA YA SAME KA ACIKINTA KANKA ZAKA ZARGA
Suna gama karanta wannan rubutu ne sukaga wata katuwar halitta mai kama da babba da jaka tayi fitar burgu daga cikin. Kofar ta shuresu gaba dayansu harda aljani rafkana Sannan ta shige cikin kofar dasu
Al'amarin daya matukar baiwa gimbiya lardisa mamaki kenan musamman data ganshi a takure a gefe daya cikin wannan jakar duk da irin girman jikin da yake dashi
Shima kuma irin tunanin da yake kenan acikin zuciyarsa yace
Lallai idan da kwadayi babu irin wulakancin da ba zaka gani ba a rayuwarka
Suna cikin wannan tunani ne sukaji an watsar dasu a kasa kamar tsummokara sannan babba da jakar ta ruburbushe ta zama kasa

SHIN SUNA IYA SAMUN DAMAR FITA DAGA WANNAN SABUWAR DUNIYAR A RAYE KUMA CIKIN KOSHIN LAFIYA?

SHIN WANENE YAKE FARA MALLAKAR YARINYA LASMIRA?
SHIN GIMBIYA SUHAILA TANA RISKAR SU FARHAN HAR TA KARA DIBAR JININ NAUWRATUL HASNAL BA TAREDA TA SANI BA?
SHIN TSUTSAR TSAFIN NAUWARATUL HASNAL TANA RISAKAR BOKA DURGAS?
DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MUN HADU A LITTAFI NA GABA DAGA NAKU HABIBULLAH KBRKARAGAR AJALI
7
++++++PART
++++++A
LBR
**********
HABIBULLAH KBR

Lokacinda wannan babba da jakar ta watsar dasu Farhan kasa sannan ta bace
Duk sai sukayi sauri suka mimmike tsaye tareda share kurar jikinsu, suna masu karewa dajin da suke ciki kallo sai ganin su sukayi acikin wani tafkeken daji wanda ya fita daban da dazuzzukan da suka saba gani a rayuwarsu
Shidai wannan daji cike yake da manya Manyan duwatsu masu girman gaske wanda kowanne daya daga cikinsu zaka ganshi kamar ya hade da sararin samaniya saboda tsabar tsawonsa
A kasa kuwa sawayen kafafune masu kama dana giwa saidai girmansu ya ninka na giwa sau biyar kai da gani kadan cewa halittar dake da wadannan sawu dole ta kasance mai. Girma gami da karfin gaske
Lokacinda suka gama karewa wannan dajin Kallo sai rukyan yace
Yaku 'yan uwana tofa ku sani daga aikin dake gaban mu sai fara don haka sai mun hada karfi da karfe Sannan zamu sake nasarar mallakar Abinda muka fito nema
Da gama fadin haka saiya kama hannun lardisa suka haye gadon bayan aljani rafkana sannan ya umarceshi daya tashi dasu ya ketarar dasu Wannan daji
Aikuwa take ya bude fuka fukansa ya luluka acikin gajimare da karfin gaske domin ketare wannan daji
Koda sukayi nisa acikin sararin samaniya sai suka cika da mamaki sakamakon jiyo wani sauti gami da gurnani mai ban tsoro da sukayi acikin duwatsun wani dutsenma gani zakayi har turirir ne ma yake tasowa ta cikinsa
Koda sukazo giftawa ta gaban daya daga cikin duwatsun sai sukaga babu komai acikinsa face jinsin mutane da aljanu
Da mutane fiye da guda dubu uku da doriya a daddaure cikin murtuka murtukan sarkokin tsafi sai gana musu azaba ake
Kowanne daya daga cikin fusunonin aljanun ya ninka aljani rafkana a girma fiye da sau goma
Amma sai gashi saboda radadin azabar da suke sha sai kukan neman dauki sukeyi sai dai duk a banza domin babu mai sauraronsu
Haka dai suka ci gaba da tafiya suna gifta ababan al'ajabi da kuma razanarwa
Kwatsam suna cikin tafiya sai suka jiyo sautin wani gurnani mai firgitarwa
Wanda saboda sautinsa sai da jikinsu ya fara kakkarwa Tareda rawar dari
Har sai da suka sa hannayensu suka toshe kunnuwan nasu amma duk a banza
Basu san lokacin da jikinsu ya fara rawa ba zufa ta fara kwaranyo musu kamar wadanda aka tsoma acikin rijiya
Idanunsu suka kumbura kamar zasu fito daga jikinsu
Saboda bala'i aljani rafkana bai san lokacin da ya saki fuka fukansa ya sulalo kasa ba
Koda saukar su akan kasa sai sukayi kicibus da wani murgujejen tsohon zaki mai tsananin girma da kwarjini
Girmansa kuwa ya isa abin razanarwa musamman idan kayi la'akari da fadin kirjinsa gami da zaftara zaftaran hakoransa
Da Yake dasu
Aduk sanda wannan zakin yayi gurnani sai komai na cikin wannan dajin ya shiga taitayinsa
Domin sun san shi sarki ne da gidansa kuma kukansa kadai yana ishara ne da take nunawa halittun duniyar cewa tabbas bakin halittu sun shigo

Bayan sun karewa wannan zakin kallo sai suka tabbatar da cewa yaufa sun gamu da gamonsu sai sun zage damtse sannan zasu kubuta daga cikinsa
Yayinda Zakin ya kyallara ido yaga su aljani rafkana sai yayi wani gunji sannan ya falfalo da gudu kansu
Saboda karfin takun nasa kasa har girgiza take kura kuwa ta turnuke sararin samaniya
Ba tareda bata lokaciba shima aljani rafkana ya afka masa yana mai karaji da kururuwa
Suna zuwa kusa da juna sai ya kai hannunsa da nufin ya kama zakin da karfin tsiya ya karya masa kashin wuya
Take zakin yayi tsalle ya gabza masa duka a kirjinsa
Saboda karfin dukan sai da aljani rafkana Tareda su rukyan dake gadon bayansa
Sukayi sama kamar an harba majajjawa suka fadi a can gefe inda nan take rafkana ya sume
Inbadon Allah ya taimaki su lardisa ba da akan su zai fado ya turmushe su
Ba tareda bata lokaciba sukayi sauri suka mike zumbur. Suka afka masa
Ruke da makaman su gadan gadan cike da dakakkiyar zuciya
Suna zuwa kusa da juna suka daka tsalle a Lokaci guda Tareda kai masa sara Lokaci daya
Koda zakin ya kula da nufin su sai yayi turjiya wacce ta janyo tashin kura
Sannan shima yabi su saman Tareda gabza musu duka sai gashi duk su biyun sunyi sama kamar an jefa dutse
Suka Fada a can gefe guda
Ita kuwa lardisa tuni kanta ya gwaru da wani dutse wanda ya janyo darewar goshinta jini yayi tsartuwa
Alokaci guda wani jiri ya debe ta ta sulale ta fadi kasa ta fita daga hayyacinta
Kawai sai zakin ya nufo kanta da gudun gaske domin ya hallaka ta
Wohoho!!!
Koda rukyan yaga abinda ke shirin faruwa daga inda yake kwance
Baisan sanda yayi kukan kura ba ya taho da azababben gudu Koda ya rage baifi saura taku guda ba tsakanin zakin da ba
A sannan har zakin ya daga murgujejen kansa da nufin ya kama kanta ya taune
Saiga rukyan ta shiga ta karkashin zakin yayi sufa cikin zafin nama ya janye lardisa daga inda take kwance
Yayin da hakoran zakin suka sauka akan wannan dutsen take ya marmashe abakinsa tamkar ya tauna alawa
Karfin zakin ya juyo inda yake tuni ya ajiye lardisa acan gefe guda sannan ya kara juyowa Tareda fuskantar zakingaba da gaba
Shi kansa zakin ba karamin mamaki yayi ba saboda ganin tsananin tsaurin idon rukyan

Daga can sai kuma ya rugo kan zakin da gudun gaske, nanfa shima zakin ya kai masa muguwar raruma
Cikjn zafin nama ya kaucewa harin Tareda yin turjiya gaba dayansu
Wacce ta janyo tashin kura a inda suke
Nanfa suka kachame da masifaffen yaki mai. Matukar muni
Ana fara wannan fada rukyan ya fara raina jarumtakar da yake da ita
Badon komai ba sai don yadda Zakin Yake kawo masa hari da matukar karfin gaske
Wanda badon ya dage wajen kauce masa ba da tuni ya dade da shudewa
Nanfa suka ci gaba da da kwarmatsuwa suna tada kura
Kafin a dau Lokaci mai tsawo tuni sun tashi hankali dajin gaba daya,
Tsuntsaye da dabbobi suka dinga guje guje domin neman ceton rayuwarsu
Saida suka shafe fiye da sa'a uku suna wannan fafatawa ba tareda daya ya sami nasara akan daya ba
Al'amarin daya matukar razana rukyan kenan musamman daya tuna cewa jiki da jini dole ne idan aka cigaba da fadan a haka zai gaji Zakin ya sami nasara akansa
Domin har yanzu shi Zakin babu alamun gajiya a Tareda shi

Yana cikin wannan tunani ne ya jiyo sautin lardisa tanayi masa umarnin ya kauce daga can nesa
Ba tareda gardamar komai ba kuwa ya kauce daga gurin, kawai sai ta dinga zaro wasu kibiyoyi tana harbawa zakin Cikin tsananin zafin nama
Koda kibban suka sauka ajikinsa sai ya juyo da sauri inda take sannan yayi girgiza duk kibban suka zube

Nantake ta ruga da gudu ta shiga cikin daji aikuwa shima Zakin sai ya bita da gudun gaske Domin ya kure mata gudu

Koda ganin haka sai shima rukyan yabisu abaya
Kaico !!!!!!
Nanfa aka kasa azababben gudu atsakaninsu kamar zasu tashi sama
Duk da girma da kuma karfin gudu Irin na wannan zakin sai gashi sun zama na banza domin ya kasa cimmata
Saboda wani irin gudu ta dinga yi na ban al'ajabi tana giftawa ta zaman duwatsu da bishiyoyi tamkar tauraruwa mai wutsiya
Kai kace ba mutun bace ita tsuntsuwa ce mai fuka fukai
Idan kuwa tazo giftawa ta guri mai kayoyi kai tsaye take takawa ta samansu taci gaba da tafiya
Al'amarin daya matukar baiwa rukyan mamaki kenan Ganin yadda take abubuwan al'ajabi
Wani lokacin ma sai yaga har gizo takeyi masa
Abinda bai sani ba shine ta dade tana baiwa kanta Irin wannan horo
Tun rana karama saboda gudun zuwan Irin wannan rana kuma acikin karance karancen da tayi ta dade da sanin cewa akwai Irin wadannan zakuna da kuma hanyoyin samun lagon su
Tana cikin wannan gudun ne ta zaro wasu layun tsafi guda biyu ta damkesu a hannayenta
Sannan ta fara karanta wadansu dalasiman tsafi tana tofawa akan kasa
Faruwar hakan keda wuya take Karfin gudunta ya karu fiye dana farko
Sannan fa dinga bacewa Tareda bayyana agurare daban daban
Kwatsam tana Cikin wannan gudun sai ta shammaci Zakin ta bayyana agabansa Tareda dunkule duka hannayenta ta gabza masa duka a tsakiyar kansa
Saboda karfin dukan saida zakin ya fadi kasa yayi birgima sau uku
Sannan ya kara mikewa tsaye kamar babu abinda ya sameshi
Tareda karkade jikinsa
Cike da mamakin inda ta sami wannan gagarumin karfi haka
Koda ya kyallara idonsa yayi arba da layun dake hannunta
Take yayi wani gurnani wanda ya amsa kuwwa acikin dajin da nan ya ruga da gudu cikin daji don tsira da rayuwarsa
duk wannan abu daya faru jarumi rukyan yana gefe yana kallo
Don haka sai yaji kamar an zare masa lakar jikinsa ya tabbatar da cewa tabbas lardisa akwai abindata boye masa da wata manufar a zuciyarta
Wacce bai santa ba a yanzu
Sai a sannan ne nadama tazo masa akaron farko na amincewa da ita
Amma dai koma menene lokacine zai bayyana masa komai
Yana cikin wannan zancen zucin ne ta karaso inda yake ba tareda ya Sani ba sai data dura masa iska acikin kunne sannan ya dawo hayyacinsa
Ya dubeta ba tareda nuna Wasu alamu ba yace
Barka kinyi kokari sosai a wannan karon duk da cewa cewa kin bani matukar mamaki yadda kika iya gano lagon wannan sihirtaccen zaki
Dajin wannan batu sai tayi murmushi daga bisani kuma tayi ajiyar zuciya tace
Wannan ai cigaban mai hakan rijiya ne domin Iya lagon Wannan zaki kadai na sani ragowar kuwa kaine zaka samo su ta hanyar Karfin damtse dana sihirinka
Sai kuma uwa uba wato kaifin. Basira
Yanzu Abinda yafi mana kawai shine mu tashi aljani rafkana domin isa daji. Na gaba
Suna cikin wannan tattaunawa ne suka hango tahowar aljani rafkana ya durfafo inda suke
Yana zuwa inda suke sai ya saki fukafukansa akasa tareda duban su Cikin kakkausar murya yace
Ya shugabana tabbas ba karamin kokari kukayi ba agurin Ganin Bayan Wannan zaki
Amma idan ba zaka damu ba zanso nasan wanda ya iya hallakashi acikinku

Dajin wannan tambaya sai dukkansu sukayi shiru suna masu kallon junansu aka rasa wanda zaice uffan Daga cikinsu
Koda rafkana yaga babu mai. Niyar bashi amsa daga cikinsu

Sai yace to ai shikenan Yanzu sai kuzo muci gaba da tafiya Domin aiwatar da aikin dake gaban mu
Yana gama fadin haka suka haye gadon bayansa
Shi kuma ya bude fuka fukansa ya a luluka sararin samaniya

WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GASU JARUMI RUKYAN BAYAN SUN FITA NEMAN SAIFUL LAIHAM

A can birnin ikarul uzbar kuwa lokacin da gimbiya suhaila ta bar kebantaccen gidan gonarta
Ta kama hanyar ta ta komawa Gidan sarautar saita dinga bin hanyoyi daban daban don kada dakarun mahaifinta su san daga inda ta taho
Bata isa gidan sarautar ba saida yamma ci sakaliya a wannan lokaci rana tana daf da faduwa
Kai tsaye ta kutsa kai cikin gidan saidai a wannan karon duk inda ta gifta saidai kaga dakaru
Sun bita da kallo, dukkan su fuskokinsu cike da alamun tambaya
Saidai basu da damar tuhumarta saboda darajar da take da Ita bisa dole Sukayi shiru
Haka dai ta ci gaba da tafiya har ta isa bargar dawakai ta ajiye dokinta sannan ta juya ta nufi hanyar turakarta
Tun daga farkon Hanyar ne taga tarin mutane fiye da yadda ta tafi ta bar gidan
Al'amarin daya matukar karyar mata da gwuiwa kenan jikinta yayi sanyi ta fara tunanin mahaifinta ne ya mutu
Haka dai taci gaba da kutsawa ta cikinsu
Koda yazo giftawa ta bakin turakar sarki gulbas sai ta tsaya cak cike da mamaki
Ba komai ta gani ba face sarki gulbas a tsaye cak bisa kafafunsa
Kamar babu abindaya taba samunsa a wannan lokaci ya tara gaba daya Manyan hadimansa yana yi musu jawabi
Akan yadda ya sami wannan gagarumar lafiya alokaci guda Tareda gagarumin aikin dake gabansa
Na zuwa duniyar hallaka domin dauko TAKOBIN SAIFUL LAIHAM
yana cikin yi. Musu bayanin ne ya hango tahowar gimbiya suhaila daga can nesa
Koda ya kyallara ido yayi arba da ita take ya sallami duk wadanda suke gurin suka tafi
Sannan ya buda hannayensa
Nantake ta ruga da gudu inda yake yake suka rungume juna na tsawon dakiku daga can ta janye jikinta daga jikin nasa tace
Ya abbana kaikuwa ya akayi ka sami wannan gagarumar lafiya alokaci guda haka mai ban al'ajabi?
Dajin wannan tambaya sai shima ya saki jikinta yana mai dubanta tareda cewa
Yake lasmira ki kwantar da hankalinki ki sani ba komai ne ya bai wannan lafiya ba face saiful laiham da kanta domin na fita nemanta akan Lokaci
Kuma a yanzu na yanke hukuncin tafiya tare dake
Saidai fa idan har muna son zuwa akan Lokaci dolene sai mun sami aljani mai matukar karfin gudu da juriyar wahala gami da karfin damtse
Bincike ya tabbatar da cewa irin wadannan aljanu guda biyu ne kadai suka rage
Nafarko ana kiransa da suna rafkana
Kuma a halin yanzu yana tare da jarumi rukyan
Na biyun kuwa harsad bin zaffar
Shidai wannan aljani shu'umin gaske ne kuma annoba ne barinsa a doron kasa
Domin a Lokacin da yake kan samartakarsa yakan iya zagaye duniya gaba dayanta Cikin abinda bai wuce sa'o'i biyar ba
Saidai. Inda matsalar take shine duk. Nahiyar daya gifta ta cikinta sai Karfin iskar kadawar fuka fukansa ta rushe da yawa daga gidajen nahiyar
A wannan lokaci ya kasance yana bauta ne a gurin kakana na dari biyu da ashirin
Wanda shine asalin wanda ya gina wannan birni Mai suna zaffar bin shasam
Wanda ya kasance jika na goma sha hudu ga boka durgas wanda ya fito daga tsatsonsa ta ta silar wata tsohuwar karuwarsa

Sarki zafran da aljani hursad bin zaffar sun jima suna tanadin yadda zasu mallaki KARAGAR AJALI tare
Sai dai basu kai ga biyan Wannan bukatar tasu ba wata rana sai sarki zafran ya kama aljani hursad bin zafran da laifin cin amanarsa
Ta Hanyar zuwar wa matarsa Cikin siffarsa ya sadu da ita akan gadon mulkinsa
Tun daga wannan rana sarki zafran ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai ta hanyar daure shi da wasu murtuka murtukan sarkokin tsafi
Wadanda a kullum kara daure kansu suna, sannan ya sanya shi acikin babbar kurkukun wadannan birni Wacce take cikin karkashin kasa
Ita kuwa wannan kurkuku tun daga randa aka kulle aljani hursad bin zafran
Ba'a sake budeta ba , kuma wannan kurkuku an gina tane a a kasan turkarki
Duk duniya babu abinda zai iya budeta face sarkar dake wuyanki
Itakuwa Wannan sarkar mahadinta yana cikin turakarki
Da zarar an sanya ta a muhallin nata take kofar zata bude kanta
Yake 'yata ina mai umartarki daki gaggauta miko min Wannan sarkar domin mu tafi aikin dake gaban mu
Kodajin wannan batu ba tareda gardamar komai ba ta sanys hannunta a wuyanta
Ta zaro Wannan sarka tana kokarin mika masa sarkar ne
Kawai sai ta jiyo sautin muryar sarki gulbas yana mai daka mata tsawa
Alokacin daya daki kofar turakarta da karfi, Wanda saboda karfin dukan sai da kofar ta fadi kasa
Fuskarsa a murtuke babu annuri Cikin kakkausar murya yana mai cewa kada ki kuskura ki mika masa wannan sarkar
Domin ba Kowa bane a gabanki ba face boka surkais
Yi maza ki miko min Wannan sarkar a hannuna

Nanfa ta fara duru duru ta rasa wanda zata baiwa Wannan sarkar a tsakaninsu
Yayin dana farkon ya daka mata tsawa Yace me kike jira ne maza ki mikomin wannan sarkar!!!!

Ita kuwa kodata rasa wanda zata baiwa Wannan sarkar saita janye hannunta ta mayarda sarkar jikin wuyanta, ba tareda ta mikawa daya daga cikinsu ba
Kafin hannunta ya karasa jikin wuyanta tuni sarki gulbas na farkon

Please Login or Register in order to submit comment