Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kasa suka kama yawo akan iska amma wani abin mamaki babu ko burbushen kasa da take zubowa
Lokaci guda kuma sai ga rufin gidan ya bude kansa kamar an bude littafi hasken rana ya dallare ko ina acikin gidan
Sai ga wani shirgegen aljani mai matukar girma da kirar sadaukai ya ratso ta saman rufin ya shigo cikin gidan
Kai da ganin wannan aljani kasan dolene ya kasance jarumin gaske wanda yasha gwagwarmaya arayuwarsa
Tunda gimbiya lardisa take bata taba ganin aljani mai girma da kwarjininsa ba a rayuwarta
Sai dai tasha jin labarin ire irensu acikin labaranta
Koda bayyanar wannan aljani take ya rissina ga rukyan Cikin girmamawa yace
Gani ya shigabana mai kake bukata na biya maka nan take komai wahalarsa koda kuwa zan rasa rayuwa ta?
Koda aljani rafkana yazo daidai nan a zancensa sai sadauki rukyan yayi masa wani murmushi mai kama dana mugunta daga bisani yace
Yakai rafkana ayaune nakeso kayi mini aiki na karshe don haka Inaso ka dauke ni
Tareda abokiyar tafiyata ka kaimu can tsuburin makabur ka shigar damu cikin duniyar da take kasan wannan duniyar tamu
Wacce akewa lakabi duniyar hallaka domin dauko TAKOBIN SAIFUL LAIHAN
wacce ake ajiyeta a tsakiyar ita wannan duniyar Bisa kan narkakken dutsen wuta…… .
Kafin ya gama rufe bakinsa tuni aljani rafkana ya fashe da kuka har yana birgima akasa tareda cewa
Ya shugabana kayi mini rai hakika wannan Aiki haka yafi karfina bazan iya ba
Domin na dade inajin labarin wannan duniya a bakin mahaifiyata tun ina karami ta fada min cewa
Inda ace za'a debo watar Wannan narkakken dutse cikin mudu daya ta isa ta narkar da wannan duniyar gaba daya
Iyayena da kakannina duk sun mutu ne akan tafarkin duniyar hallaka don dauko ita wannan takobi
Acikin kofofin duniyar hallaka guda dubu babu kofar da basu jarraba shiga ta cikinta ba
Amma ko daya daga cikinsu bai. Dawo a raye ba
Ina mai tabbatar maka da cewa mutuwa tafi tunkarar wannan duniyar sauki
Don haka ina rokon daka gaggauta kashe ni yanzu akan na tunkari wannan duniyar
Koda yazo daidai nan azancensa sai rukyan ya bushe da dariya daga nan kuma yace
Haba namijin duniya kada ka manta da gwagwarmayar da kasha abaya
Ka tuna da fafatawar da mukayi a cikin duniyar fatalwa wacce saida muka shafe sati guda muna yaki da mugayen fatalwu babu hutu
Kuma babu ci babu sha kamar ba zamu tsira ba
Amma saboda dagiya da kuma kwarin gwuiwar da muka sa a zuciyar mu sai da muka sami nasara akansu
Ina tabbatar maka da cewa muddin muka kwarin gwuiwa azuciyar mu tabbas a wannan karon ma zamu sami nasarar tarwatsa duniyar hallaka mun dauko saiful laihan daga cikinta
Kuma mun karya alkadarinta munyi abinda iyaye da kakanni suka kasa yi
Hakadai yaci gaba da karfafa masa gwuiwa har saida yaji dukkan tsoro ya kau daga zuciyarsa

Yaji wani kwarin gwuiwa ya shige shi don haka take ya rankwafar da gadon akasa suka haye suka zauna a sannan ne wani aljani ya kawo musu kayan guzuri suka karba
Zamansu keda wiya sai rafkana ya bude fuka fukansa ya tashi sama
Yana fita daga harabar gidan sai gidan ya koma kamar yadda yake abaya
Nanfa aljanin ya dinga tsala a zababben gudu a sararin samaniya kai kace duniyar gaba daya zai bari saboda tsananin karfin gudunsa
Saida suka shafe lokaci mai tsawo suna tafiya ba tareda dayansu yake uffan ba
Kowa yana tunanin wani abin daban
Don haka sai rukyan ya katse shirun dake tsakaninsu yace
Yake ma'abociyar hikayoyin mazan jiya tun dazu zuciyata a kage take dason jin cigaban hikayar da kike bani don haka zanso ki karasa bani ita
Don naji yadda zata kasance tsakanin wadannan tagwayen 'yan uwa masu abin al'ajabi
Dajin haka sai ta gyada kanta tareda yi. Masa tattausan murmushi sannan ta zaro littafin taci gaba dakaratun afili kamar haka

++++++++ ++++++++ +++++++
Lokacin da wannan batoyi ta shuri su sadauki farhan daga wannan kogon dutse
Sai gashi tana tsala mahaukacin gudu dasu kamar walkiya tana ratsawa ta karkashin kasa da kuma tekuna kamar yadda haske yake ratsawa ta cikin gilashi ba tareda wani abu ya tare shi ba
Basu sauka ako'ina ba sai Cikin wata masarauta mai dumbin tarihi Wacce ta shafe dubunnan shekaru da shudewa
Suna sauka bisa turba sai wannan batoyin ta rikide ta koma nauwaratul hasnal
Nantake ta share dattin dake kasa itakuma huraisa ta kwance rawanin dake kanta aka shimfidar dashi a kasa
Cikin tashin hankali nauwaratul hasnal ta durfafeshi da nufin saka masu magani don rage masa zugin da yake ji
Kawai sai ganin Husnaila tayi ta zare takobi ta kawo mata mahaukacin sara a dokin wuya da kaifin takobin ta

Maimakon takobin ta yanka jikinta sai gashi ta ratsa ta ta wuce tamkar ta sari iska
Cikin murmushi nauwaratul hasnal ta dubeta tace ba fada dani ne abindaya kamata ki fara yi ba
A binda yafi a halin yanxu shine ceton rayuwarsa daga halin da yake ciki
Idan har bamuyi da gaske ba zai iya rasa rayuwarsa akowanne lokaci
Dajin wannan batu sai jikin huraisa yayi sanyi ta mayarda takobi ta cikin kufe
Duk su biyun suka dukufa akansa suna kokarin tsayar da jinin dake zuba ajikinsa
Don har a sannan bai farfado daga doguwar suman da yayi ba
Cikin sauri huraisa ta dauko wani garin magani takai hannunta da nufin zuba masa akan raunin
Kafin Hannun ta yakai jikinsa tuni nauwaratul hasnal ta rike hannunta tareda cewa
Wannan ba shine makarin dafin dake jikinsa ba
Da zarar kin kuskura kin zuba masa wannan garin magani take jikinsa zai fara zagwanyewa har ya rasa rayuwarsa
Idan har muna son samun makarin wannan gubar dolene mu koma inda aka fafata wannan kazamin yaki
Mun kwato kuttun kibiyoyin sadauki safran domin acikine kadai makarin wannan dafi yake
Kafin sannan dolene daya daga cikin mu ya arawa farhan rayuwarsa ma'ana ruhinsa
Domin ya sami karfin da zai iya wannan Aiki acikin Abinda ba zai wuce sa'o'i uku da rabi ba
Daga ke har shi babu wanda zai iya zama da wannan dafi ajikinsa na tsawon wadannan sa'o'i face ya zama gawa
Ni kuwa zan iya zama dashi har na tsawon sa'o'i biyar

A halin yanxu abin da ya rage masa a rayuwa ba zai haura rabin sa'a ba
Don haka ni yanzu zan bashi aron rayuwata in yaso ke ku tafi tare dashi ku samo kokarin
Amma fa ki sani rayuta ta dogara da taku idan kukayi nasarar dawowa kafin sa'o'i biyar na tsira
Idan kuwa kuka haura zan mutune da farincikin mika rayuwata ga masoyina
Dajin wannan furuci dai huraisa taji Kamar an watsa mata tafasasshen ruwa amma sai ta danne kishin nata
Ba tareda bata lokaci ba nauwaratul hasnal ta fara karanta wadansu dalasiman tsafi tana tofawa akan raunin dake jikinsa
Nantake saiga wani bakin Abu mai kama tsutsa ya fito daga cikin kirjinsa ya shiga nata kirjin
Faruwar hakan keda wuya take ta sulale ta fadi kasa tana shure shure dafara ta fara fita daga bakinta
Kafin 'yan dakiku tuni ta zama sumammiya
Adaidai wannan lokaci ne farhan ya farfado daga mawuyacin halin da yake ciki
Kodaya kyallara ido yaga huraisa agabansa agefensa kuma yaga sarauniya nauwaratul hasnal ce akwance
Saiya mike zumbur kamar babu abindaya same shi ya dubeta cikin rashin yarda yace wanene ya kawo ni wannan guri kuma me ya faru ga abokiyar tafiyata?
Dajin wannan tambaya ba tareda bata lokaci ba ta zayyane masa duk abindaya faru
Kodajin wannan bayani take yaji tausayinta ya kamashi a karon farko
Yaji dolene yayi mata halacci don haka nan take ya mike tsaye tareda gyara damararsa
Take yayi girgiza ya fuka fukai suka fito daga kafadunsa ya budesu ya tashi sama
Ganin haka yasa itama Husnaila ta falfala da azababben gudu n gaske
Tana fita daga masarautar ta iske aljani marna'ul safran a tsaye a bakin kofa sai kada fuka fukansa yake
Ba tareda bata lokaciba itama ta dane bayansa ya luluka da ita cikin gajimare
Yabi bayan sadauki farhan iya karfin gudun sa domin su isa wannan kogo kafin su mufran su fice daga cikin sa
Sai a sannan ne ta gane cewa tabbas Akwai banbancin karfin sihiri tsakanin ta da farhan
Kasancewar a wannan karon suna gudun tareda amfani da karfin sihirinsu domin takaice tafiyar dake gabansu
Domin da kyar da sidin goshi marna'ul safran Yake iya bin sawun farhan
Abinda basu sani ba shine shi kansa farhan a wannan lokaci mamakin da yakeyi kenan domin baisan inda ya sami wannan gagarumin karfin sihiri ba
Ba komai ne ya janyo haka ba face aron ruhin da nauwaratul hasnal ta bashi
Cikin kankanin lokaci suka bayyana acikin wannan kogo da suka fafata yaki aciki Adaidai lokacin da su safran ke shirin fita daga cikinsa
Kawai sai gani sukayi farhan ya faso ta saman rufin kogon Kamar saukar aradu ya bayyana acikinsa
Sumul mul kamar babu abindaya sameshi
Al'amarin daya matukar razana su kenan har suka dan ja da baya arazane saboda mamaki domin suna san cewa matukar aka sanyawa mutun wannan dafi dake jikin kibiyar mufran bai isa ya iya wuce sa'a guda a raye ba

Adaidai. Nan ne farhan tayi musu wani murmushi mai kama dana mugunta yace
Kunyi mamakin ganina a raye ko ?
Duk da mugun tanadin da kuka jima kunayi akaina wanda baiyi tasiri ba to a yanzu sai ku shirya tarba ta
Koda gama fadin haka sai ya afka musu yana mai karaji da kururwa ba tareda bata lokaciba
Suma suka afka masa koda ya rage baifi saura taku uku ba a tsakaninsu sai gimbiya huraisa ts faso ta karkashin kasa bisa kafafunta
Suna haduwa gaba dayansu sau suka kara kachamewa da wani sabon bakin artabun mai tsananin firgitarwa da kuma ban sha'awa ga 'yan Kallo
Domin fada suke mai matukar ban al'ajabi sakamakon ganin yadda karfinsu tareda iya yakinsu sukazo daya

Husnaila da safran suka ware guri daya Yayinda shi kuma farhan suka ja tunga da mufran
Fara wannan fada keda wuya sai kogon ya kara birkicewa fiye da farko
sawayensu suka dinga dudufniya wanda ya nemi ya haddasa girgizar kasa a cikin kogon
Babu abinda zai kara baka tsoro face ganin yadda suke kaiwa junansu mugayen hare hare domin ganin bayan juna
Duk sanda wani daga cikin su. Yakaiwa abokin gwaminsa hari da zarar ya kauce duk abinda ya samu take yake tarwatsewa
Koda kuwa dirkar gini ce take take karyewa ta fadi kasa
Idan junansu suka samu sai kaga sun shanye kamar babu abindaya same su duk da cewa sunaji ajikinsu
Saida suka shafe kusan sa'a guda suna wannan fafatawa ba tareda dayansu ya sami akan daya ba
Sakamakon yadda karfinsu da iya yakinsu suka zama daya

A wannan lokaci sunyi rushe rushe da yawa acikin kogon harya soma kokarin rugujewa
Sannan ne fa hankalin farhan ya dugunzuma sakamakon tunawa da yayi da halin da nauwaratul hasnal take ciki
Mai kama da rayuwa da mutuwa
Idan har basuyi da gaske ba tabbas tabbas zata iya rasa rayuwarta
Koda gama wannan tunani sai. Ya kara zage damtse
A can bangaren Husnaila da safran ma haka al'amarin yaci gaba da kasance wa
Domin kuwa kaiwa junansu kyawawan hare hare suke wanda da zarar takubban su sun hadu da juna sai dai kaga tartsatsin wuta gami da turiri suna tashi sama
Saidai kuma. Ita tanayin fadan badon ta ceci nauwaratul hasnal bane
Tana fadan ne domin taga ta riga farhan kwatar kuttun safran domin ta sace shi ta gudu gaba daya
Haka dai suka dinga kaiwa junansu sara babu kakkautawa har takai kogon ya fars marmsowa yana neman danne su
Ana Cikin Wannan fafatawa ne huraisa ta shammaci safran ta dankara masa duka a agadon baya wanda saboda karfin dukan saidaya dukushe kasa
Ai. Kuwa nan take cikin zafin nama tasa hannu ta tsinke kuttun daga kafadarsa
Ta ruga da gudu ta dare bayan aljani marna'ul safran ya bude fuka fukansa ya tashi da nufin guduwa
Koda safran yaga abindake shirin faruwa take ya nuna aljanin da yatsunsa
Nantake wata murtukekiyar sarkar tsafi tayi fitar burgu daga hannunsa ta harde fukai fukan marna'ul safran dai gashi yana reto akan iska
Kawai sai safran ya daka tsalle daga inda yake ya dira agadon bayan sa suka ci gaba da fafatawa a haka
Karfin dudufniyar kafafunsu ce ta rikits aljani marna'ul safran ya fara layi da tangal tangal a sama yana neman fadowa kasa

Tsananin tangal tangal din da yakeyi ne yasa kuttun dake kafadar huraisa ya subuce ya fado kasa
Tun kafin ya iso kasa saiga wani shudin ruwa ya kwaranyo daga cikinsa zai zube akasa
Koda ganin haka take sai farhan ya taho da mahaukacin gudu
Kafin ruwan ya sauka. A kasa tuni ya tara bakinsa ruwan ya zuba acikinsa
Sannan ya daka tsalle shima ya haye gadon bayan marna'ul safran
Ya tsinke sarkar data daureshi da takobinsa tareda jefo safran kasa
Kafin su mufran su kara wani yunkuri tuni wasu sarkokin tsafi sunyi fitar burgu daga karkashin kasa sun daure su tamau
Nantake wannan kofar hasken ta sake bayyana suka shige ciki sannan ta kara bacewa kamar farko
Basu bayyana ako'ina ba sai Cikin sai masarautar da gangar jikin nauwaratul hasnal ke kwance
Suna bayyana sai marna'ul safran ya fice daga cikin ta
Gimbiya Husnaila ce ta fara rugawa da gudu inda nauwaratul hasnal take kwance ta tallafo kanta ta dora akan cinyarta
A wannan lokaci baifi saura dakiku uku suka rage sa'a biyu su cika ba
Koda Farhan ya iso inda take sai ya sunkuya ya kafa bakinsa akan nata ya dura mata wannan ruwan magani
Wannan ce damar da Husnaila ta samu ta zaro wata karamar allura da mazubi ta zuki jinin nauwaratul hasnal
Kafin farhan ya dago da kansa tuni ta sulale ta bace daga masarautar

SHIN NAUWARATUL HASNAL TANA FARFADOWA DAGA WANNAN HALI MAI KAMA DA RAYUWA DA MUTUWA ?

SHIN HUSNAILA TANA KAIWA ALJANI MARNA'UL SAFRAN WANNAN JINI
KUMA YANA. AMINCEWA DA ZAMA HADIMINTA ?

SHIN WANNE KALUBALE JARUMI RUKYAN ZAI FUSKANTA AKARON FARKO NA NEMAN SAIFUL LAIHAM?

DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MUN HADU A KASHI NA GABA
DAGA NAKU HABIBULLAH KBR
WHATSAPP
09133502477

LIKE, COMMENT AND SHARE PLSKARAGAR AJALI
+++++++++++6 PART C

++++++++++++LBR

HABIBULLAH KBR

Lokacin da gimbiya huraisa ta sulale ta gudu bayan ta debi jinin nauwaratul hasnal
Farhan bai dago da kansa ba sai bayan fitar ta
Bayan ya dago dinne ya lura babu Huraisa a gurin don haka nan take yaji zuciyarsa ta buga da karfi ya tabbatar da cewa tabbas Akwai mugun abindaya kawo Huraisa
Nauwaratul hasnal bata motsa daga dogon suman da tayi ba
Sai bayan wasu dakiku kadan a sannan ne idanunta suka fara budewa ahankali
Daga baya tayi kwakwkwaran tari guda uku gami da aboyene zuciya
Koda tayi arba da farhan daidai da saitin fuskarta sai taji Kamar ta rungumeshi a kirjinta
Amma tsananin kunya da jinkai suka hanata aikata hakan , kawai sai tayi murmushi tace
Ina mai Godiya bisa ga ceton rayuwata da kayi sannan ta mike daga kwancen
Haka shima sai ya bita da kallo bisa jin cewa da tayi ya ceci rayuwarta alhalin itace ta ceci tasa rayuwar
Har ya budi baki zaiyi magana sai ta fara numfashinsa da cees ina kuma huraisa ta tafi?
Dajin wannan tambaya sai yayi shiru ya rasa amsar wannan tambaya da tayi masa
Daga can kuma sai yace yanzu muka rabu da ita domin ta koma can nahiyar data baro
A sannan ne farhan ya karanta wasu dalasiman tsafi sannan ya tofa akan raunikan dake jikinsa
Ai kuwa nan take raunikan suka hade kansu kamar an shekara dajinsu
Bayan nan suka fara shirye shiryen cigaba da tafiya
WANNAN SHINE ABINDAYA FARU A BANGAREN SU JARUMI FARHAN DA SARAUNIYA NAUWARATUL HASNAL
BAYAN GIMBIYA HURAISA TA SSKI NASARAR DIBAN JININTA WANDA ZATA BAIWA ALJANI MARNA'UL SAFRAN
+++++++ ++++++++
Acan kuwa bangaren gimbiya huraisa kuwa lokacin data debi Wannan jini ta sulale ta gudu
Tana fita daga gidan sarautar saita iske aljani marna'ul safran yana ta zaman jiranta
Cikin sauri huraisa ta nuna masa wannan battar jinin tace wannan shine jinin da kake bukata don haka sai muyi don haka sai muyi sauri mu bar wannan yanki gaba daya
Tana gama fadin haka sai ta haye gadon bayansa shi kuma ya bude fuka fukansa ya
Nufi hanyar da zata mai dashi can birninsu cikin azababben gudu domin cika burin mahaifinsa na son dawo da kabilar su. Ta bakaken aljanu doron kasa
Saida suka shafe yini guda suna tafiya a sararin samaniya sannan suka fara hango nahiyar bakaken aljanu
Suna shiga cikin garin kuwa sai ta cika da tsananin mamaki
Badon komai ba sai don ganin yadda birnin ya kawatu ainun fiye da yadda mutane suke kawata nasu
Kai harma ya ninka na mutane fiye da sau dari
Ko ina acikin birnin gashi ban cike da jinsin aljanu manya da yara mazansu da mata atsaitsaye birjik Kamar Kayi musu magana su amsa
Saidai duk jikinsu babu inda yake motsi ko kuma numfashi
A sannan ma har kura da Gama lullube jikinsu Gaba daya Wacce idan zaka kankarewa daya daga cikinsu kurar jikinsa
Sai ka shafe fiye da wata guda
A gefe guda kuma dakarunsu ne cikin shirin yaki ruke da garkuwa cikin shirin yaki
Kai da gani kasan cewa alokacin da wannan annoba ta same su suna fafata kazamin yaki ne da wani abokin gabar nasu
Lokacin da huraisa ta gama karewa sai ta kara cika da mamakin yadda wannan ibtila'i ya same su duk da irin kirar karfin da suke da Ita
Bata san Lokacinda ta tunkari inda wadannan dakaru suke ba ta kai hannu da nufin taba jikin daya daga cikinsu
Kwatsam sai taji an daka mata tsawa Wacce a karon farko a rayuwarta ta buga da karfi
Bata san lokacin data janye hannunta ba
Ta juyo da sauri don ganin daga inda tsawar ta tawo
Kawai sai tayi arba da wani dattijon aljani sanye da hular karfe hannunsa kuwa yana ruke da kwagirin tsafi
Kallo daya zakayiwa wannan aljani kasan cewa ya jima a duniya Domin a Kallo zai shafe sama da shekaru dubu uku da doriya
Cikin murmushin aljanin ya dube ta yace lale marhaban da gimbiya huraisa 'yar sarki suraif mai mulkin birnin sin
Yake wannan Gimbiya badon komai na hanaki taba wannan badakare sai domin cetonki
Saboda da kin kuskura kin taba jikinsa take kema zaki Shiga cikin halinda suka ciki saboda karfin sihirin da yake jikinsa
Kodajin wannan batu sai tace nagode da ceton rayuwata da kayi amma menene ya sanya jama'arka cikin wannan mugun yanayi?
Dajin wannan tambaya sai dattijon aljanin yayi shiru Kamar ba zaice komai. Ba daga can kuma sai yace
Ba zan iya baki. Amsar wannan tambayar ba domin abune wanda ya shafi rayuwata saidai in sanar dake wanda ya aikata hakan
Ba kowa bane face sarki hasnal mahaifin sarauniya nauwaratul hasnal wacce a halin yanxu take tareda dan uwanki
Yamzu dai sai ku biyo ni zuwa dakin bokanci na
Yana gama fadin haka sai. Ya wuce gaba suka bishi a baya Tafiyar 'yan dakiku sukayi sannan suka isa tsakiyar wani katon daki
wanda babu komai acikinsa face kayan aikin bokanci, da tarkace iri daban daban
A tsakiyar dakin kuwa an ajiye wata babbar kwatarniyar tsafi wacce aka gauraya nau'in jinin halittu sama da dubu dari uku da doriya acikinta
Sai faman zabalbala suke kamar zasu fasa tukunyar su fito waje
Koda isarsu gaban wannan kwatarniyar sai yaja tunga ya tsaya
Sannan ya miko mata hannunsa tareda umartar ta data miko masa wannan battar da jinin Yake ciki
Nan take kuwa ta kwanto battar daga jikin mugunta ta mika masa
Take ya bude battar ya dagata sama da nufin juye wannan jinin acikin kwatarniyar
Kwatsam sai yaga babu komai acikin don haka cikin tashin hankali ya dubi huraisa yace
Ina kika saka jinin ai babu komai acikin battar nan

Kodajin wannan batu sai tayi wuf ta karbi battar daga hannunsa Cikin sauri tasa idonta ta leka cikin ta

Koda idanun ta suka sauka acikin battar sai. Taga babu komai acikinta face tarin yashi
Al'amarin daya matukar bata mamaki kenan don haka ba shiri ya kwanto madubin tsafinta ta shafeshi don taga Abin daya faru ga jinin
Shafar madubin keda wuya sai ga hotonta lokacin da take nuna wa aljani marna'ul safran wannan jinin
Ashe ta manta bata rufe murfin battar daidai ba
Don haka lokacin da marna'ul safran yake tashi da Ita sama sai wannan battar ta tuntsure jinsin jinin ya tsiyaye akasa
Saidai kafin jinin ya sauka akasa saiga boka durgas ya bayyana dauke da tasa battar ya tare jinin da ita sannan ya bace
Koda gama Ganin abindaya faru sai gaba dayansu suka kwarara uban ihu wanda saboda karfin sa sai da kasa ta fara girgiza daga bisani kuma suka turbune fuska
Mahaifin marna'ul safran ya dubi huraisa yace
Yake wannan jaruma ki sani cewa a halin yanzu zama bai kamaku ba
Dolene ku tashi ku kara samo wannan kafin lokaci ya kure domin yana daf da kurewa
A halin yanzu sun canja salo a gaba dayan duniya , ma'ana sarauniyar kyau wato lasmira tana daf da bayyana
Idan kuwa har ta bayyana ba zamu taba mallakar jinin nauwaratul hasnal ba
Kai koda ma mun samu babu amfanin da zaiyi mana
Yake huraisa ki sani a halin yanzu ba lasmira ce abokiyar gabar ki. Ba
Nauwaratul hasnal itace babbar matsalar ki domin idan har tana tare da farhan wata rana sai tace amanarsa ko kuma tayi sanadiyar rushewar duk farincikinsa
Ko kuma ta janyo ya rasa rayuwarsa gaba daya
Nauwaratul hasnal shu'umar mace ce wacce tasan yaudara gami da cin amana,
Sannan kuma tana da karfin basira sosai fiye da yadda kike tsammani
Abu daya kachal ta rasa a rayuwarta, wannan abu kuwa ba komai bane face karfin damtse
Inda ace ta gado mahaifinta sarki hasnal da sai shuhura a duniya fiye da yadda yayi a zamaninsa
Domin da a zamaninsa ne lasmira ta bayyana ina mai tabbatar miki cewa babu abinda zai hanashi mallakar KARAGAR AJALI
Yanzu sai ku gaggauta tashi ku tafi neman wannan kafin nan da cikar kwana uku kacal
Idan a wannan karon kike iso nan da wannan jinin muka karasa wannan sihiri da nake hadawa kabilar mu suka dawo
Nayi alkawarin da kaina zan taimake ki muga bayanta
Yana gama fadin haka saiya juya musu baya
Nan take aljani marna'ul safran ya shuri huraisa ya dorata a gadon bayansa sannan ya bude fuka fukansa suka tashi sama gaba daya

WANNAN SHINE ABINDAYA FARU TSAKANIN GIMBIYA HURAISA DA SARKIN BAKAKEN ALJANU

******** ******** *******
Al'amarin sadauki Farhan da sarauniya nauwaratul hasnal kuwa
Lokacinda suka baro wannan tsohuwar masarautar da nufin ci gaba da tafiya
Kwatsam lokaci guda sai suka ga bakin hadari ya tare da guguwa mai karfi alokaci guda sun turnuke duniyar
Aka dinga wata. Mahaukaciyar tsawa mai karfin Gaske tamkar zata farka kirajensu ta fito da zuciyoyinsu
Gami da walkiya Wacce ta dinga tarwatsa duwarwatsu da tsaunika
Saboda karfin iskar dake kadawa saida ta kwance rawanin da suka rufe fusokokinsu
Kasa kuwa ta dinga girgiza tana tsagewa , bishiyoyi da duwarwatsu suna fadawa ciki
Su din ma sai mafaka suka samu suka samarwa kansu mafaka
Suna cikin wannan haline Kawai wani katon tsauni yayi bindiga gami da tsawa
Wata mahaukaciyar bakar wuta mai matukar zafi ta kwaranya daga cikinsa
Ta nufo inda suke da gudun gaske duk. Inda wutar ta gifta take yake komawa kurmus
Abinda Yake garin kuwa sai ya daskare ya koma dutse
Koda sukayi arba da wannan wutar take farhan ya kama hannun Nauwaratul hasnal suka falfala da azababben gudu domin ceton ransu
Suna gudun ne Iya karfin su tamkar kafafunsu zasu tabo keyarsu
Amma Wani Abin tsoro shine duk gudun da suke da zarar sun juyo bayansu
Sai suga tsakaninsu da wutar bai wuce taku uku Zuwa hudu ba
Nanfa suka kara zage damtse tareda amfani da karfin sihirinsu domin su dakatar da wutar amma sihirin yaki yayi. Tasiri

Al'amarin daya matukar kara razanasu kenansuna Cikin wannan haline kafar nauwaratul hasnal ta zame ta fada cikin wani rami da kasa ta rufta

Cikin zafin nama kafin ta karasa ciki tuni farhan yasa hannu ya cafo sannan ya fito daga ramin
Duk Cikin Abinda bai wuce rabin dakika ba ya goyata agadon bayansa yaci gaba da gudun a haka dauke da ita ba tareda ya tsaya ba
A haka yaci gaba da gudu dauke da ita tun safe har rana ta fadi adaidai wannan lokaci ne
Wutar ta dauke dif komai ya koma. Yadda yake abaya
Haske farin wata mai karfi ya dallare duniya kai kace tsakar rana

Please Login or Register in order to submit comment