Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hadiye mutun goma alokaci guda suji kamar basu hadiyi komai ba
Yayinda wadannan halittu suka kyallara idanunsu sukayi arba dasu Farhan take suka falfalo da gudu kansu da nufin su dasa musu wawa
Nantake shima Farhan yayi kukan kura ya afka musu ita kuwa nauwaratul hasnal har zuwa wannan lokacin bata bude idanunta ba kuma bata daina karanta dalasiman tsafin da take karantawa ba
Koda Farhan ya hadu da wadannan halittu take suka kacame da azababben yaki mai matukar muni da razanarwa mai ban tsoro
Saboda tsananin mugun yawan da suke dashi sai gashi sun lullubeshi kamar an ajiye kwayar gero atsakiyar gidan tururuwa tako ina sai faman kawo masa hsri suke yana karewa tareda mayarda martani
Yana cikin wannan haline ya tuna da nauwaratul hasnal wacce a wannan lokaci take cikin nazari ahallarar tsafi bata ma San abinda yake faruwa ba
Kuma a wannan lokaci har wasu daga cikin dodannin sun nufi inda take gadan gadan
Take Farhan yayi kukan kura wanda saidaya razana halittun suka danja da baya
Cikin tsananin zafin nama ya dinga tarwatsasu da kaifin takobinsa domin zuwa inda nauwaratul hasnal take
Koda ya rage saura kiris tsakanin nauwaratul hasnal da wadannan halittu take Sai ta rikide wasu nauwaratul hasnal din guda biyu masu matukar kama da ita suka fito daga tsagin jikinta na dama Dana hagu
Saidai su wadannan guda biyun suna dauke da makaman yaki a hannayensu
Komai Kellen kurillar mutum bai isa ya iya banbance tsananin ta gaskiyar ba da wadannan guda biyun

Da bayyanarsu Sai suka sanya nauwaratul hasnal a tsakiya suka fara kare farmakin da ake shirin kai mata
Nanfa guri ya Kara hargitsewa da karafkiyar karafa da rurin halittun duk inda ta durfafa saidai kaga wadannan masu kama da itan sun juya wajen sunata ragargazar halittun tareda bata kariya
Acan gefe daya kuwa Farhan ne a tsakiyar su kamar iblishi yana kai musu sara da suka cikin zafin nama juriya da bajinta
Hakanan duk inda yasa gaba saidaya kaga yana zubar da halittun kasa kamar Ana sassabe a gona
Aduk sanda yakai musu sara saidai kaga kaifin takobinsa ta tafi da kawunan diya da guda goma
Kuma yana fadan ne cikin kuzari babu alamun gajiya a tare dashi
Har aka shafe sa'o'i sama da bakwai batareda an tsayar da wannan fada ba
A sannan ne hankalin halittun ya tashi sakamakon ganin yadda yake musu muguwar barna
Ba Tareda sun sami damar yi masa Koda kwarzane ba shi kuma bai Dakata da shayar dasu gidauniyar mutuwa ba

Don haka Sai lokaci guda suka guys daga bangarensa suka koma inda nauwaratul hasnal take sukayi mata kawanya da nufin dasa mata wawa tareda mataimakanta
Tunda shi sun tabbatar da babu yadda zasuyi dashi

WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GA SADAUKI FARHAN BAYAN GUGUWAR TSAFI TA RABA SHI DA 'YAN UWANSA
++++++ ++++++ +++++

Al'amarin gimbiya Husnaila lokacin da wannan guguwar ta shureta bata sauketa a ko'ina ba
Sai a birnin farisa da yammaci tsakaliya alokacin kowa yana gudanar da harkokinsa kamar yadda aka saba
Yayinda mutane sukayi arba da ita sai suka fara gudu azatonsu yar harin sumame ce sakamakon ganin ta bakuwar fuska agunsu
Cikin kankanin lokaci guri ya rikice da guje guje
Kodata lura Koda ta lura halinda suka Shiga sai tayi sauri ta janyo rawani ta rufe fuskarta dashi
Sannan ta dauko madubin tsafinta ta shafeshi domin ta nemi inda zata samu makwanci
Acikin madubin ne ta gano Manyan gidajen kwanan garin masu tsadar gaske
Batareda bata lokaci ba ta mayarda madubin tsafin nata ta nufi hanyar da zata kaita babban gidan kawunan garin wanda yake kusa da masarautar birnin
Bata jima tana tafiyaba ta isa gidan wanda ya kasance babban gida kuma kerarre wanda babu kamar sa a kaf fadin birnin inka dauke gidan sarauta
Ko ina acikin birnin kewaye yake da dakaru masu yawan gaske dauke Manyan makaman yaki
Yayinda suka hango tahowar gimbiya huraisa cikin wannan Shiga da tayi sai suka gyara rukon makaman su suka tsaya jiran isowarta azatonsu 'yar fashi ce
Ba tareda fargabar komaiba kuwa taci gaba da tunkararsu Koda ya rage baifi saura taku goma ba Sai taja tunga ta tsaya
Sannan daya daga cikin masu tsaron ya karaso gaban kofar. Ya dubeta yace
Yake wannan bakuwa wacece ke kuma meke tafe dake ?
Dajin wannan tambaya sai ta basu amsa cikin irin yarensu tace
Nice gimbiya Husnaila 'ya agurin sarki lasmar na birnin sin kuma nazo ne domin na kama dakin da zan kwana idan gari ya waye naci gaba da tafiya
Kodajin wannan batu sai badakaren yayi murmushin mugunta sannan yace
Idan har kinson Shiga wannan gida dolene ki bude fuskarki sannan ki biya ninki biyu na abinda mutanen wannan gari suke biya
Batareda gardamar komai ba kuwa ta kwance nadin dake kan fuskarta sannan ta dauki curin kamar kudi ta jefa masa
Cikin sauri badakaren ya dauki jakar kudin hannunsa na kakkarwa ya fara lissafawa sakamakon ganin da yayi adadin yawan kudin yakai kudin da suke samu a akwana hudu na duk bakin da suke kama hayar gidan
Cikin rawar jiki yasa yasa yaransa suka bude mata kofa ta wuce ciki
Tana Shiga ta iske gidan ta iske 'ya'yan sarakai tare dana masu fada aji acikin birnin sai sharholiyarsu suke
Cikin gidan kuwa an kawata shi ainun da kayan alatu nau'i daban daban irin na sarakai
Acan gefe guda kuwa 'yan mata ne kyawawa sai tikar rawa sukeyi agaban wasu katti don sanya musu nishadi
Mafi yawan mutanen dake wannan guri attajiraine, sarakai da kuma kasurguman 'yan fashi wadanda suka Shahara anahiyar
Yayinda suka hango tahowarta take suka fara yafuto junansu suna nuna gimbiya Husnaila
Ita kuwa sai ta kau Dakanta kamar bata gansu ba Kuma ta koma gefe tayi zamanta
Zamanta keda wuya sai wata ma'aikaciya tazo ta ajiye mata nau'ikan abinci da abinsa iri daban daban domin gusar da yunwar dake addabarta

Har Husnaila takai hannu da nufin fara cin abincin don tana matukar jin yunwa
Sai ta tuna da wanda take matukar kauna wato sadauki Farhan
Lokaci guda hannunta ya fara kakkarwa ta kasa cin abincin sakamakon tunawa da abin daya faru tsakaninta dashi
Ta kuma tuna cewa a halin yanzu dolene 'yan uwansa suci gaba da yunkurin hallaka dashi

Don haka ya zama dole itama tayi kokarin bashi kariya Koda kuwa aboyene
Amma Koda ta tuna cewa ayanzu shi zuciyarsa bata tareda ita ta karkata ne akan lasmira
Sai taji bakin ciki ya turnuke ta kuma taji ya zama wajibi tayi iya kokarinta don ganin bai hadu da lasmira ba
Nanfa taji ta kasa samun nutsuwa dole saita duba halinda yake ciki
Don haka sai ta karanta wadansu dalasiman tsafi ta tofa akan teburin abincin dake gabanta
Take teburin yayi haske sai dai kuma maimakon fuskar farhan ta bayyana ajiki sai taga nauwaratul hasnal acikin madubin shi kuma ta kasa ganinsa
Nantake taji zuciyarta ta buga da karfi Nanfa ta Kara zage damtse
Domin janye ta daga madubin tsafin nata amma sai Abu ya gagara
Saboda bakin ciki bata san lokacin bata rafka uban ihu ba wanda ya janyo hankalin mutanen dake gurin ya dawo kanta
Kawai saita sunkuyarda kanta akan teburin ta fashe da kuka tareda rera dadadan baitocin yabo ga masoyin nata
Tana cikin wannan haline saiga yarima ramsin ya shigo cikin gidan abincin tareda dakaru fiye da dari abayansa masu bashi kariya
Agabaki daya birnin farisa babu azzalumi wanda yake takurawa mata kamarsa
Saboda tsananin tsoron da suke masa saida ta kai 'yan mata sun daina fitowa daga gidajensu domin da zarar yayi ido biyu da mace tofa ta karfi da yaji zai sa dakaru sa kamo masa ita don yayi lalata da ita
Idan kuwa tayi taurin kai tofa zaiyi mata fyade ne abainar jama'a ko kunya baya ji
Idan kuwa mace ta sami juna biyu dashi tofa zai turo dakaru ne a sirrance su kasheta
Yayindaya lura gaba daya mata sun koma buya agidajensu sai ya koma binsu har cikin gidan agaban iyayensu ya aikata mugun nufinsa akansu
Lokacin da yarima ramsin ya shigo wannan gidan abinci sai guri yayi tsit kai kace mutuwa ce ta gifta
Kowa ya mike tsaye domin girmamawa shi kuwa sai ya kurawa kowa ido yanayi musu wani kallon banza
A wannan lokaci ne yayi arba da gimbiya huraisa wacce har a wannan lokaci bata dago da kanta ba
Wannan ne ya tabbatar masa da cewa lallai ita bakuwa ce a wannan nahiya
Don haka dolene ya koya mata hankali kuma yaci mata mutunci kamar yadda ya saba yadda ko agaba zataji tsoron haduwa dashi
Ba tareda bata lokaci ba kuwa ya wuce inda take sunkuye fuskarsa cike da murmushin mugunta
Yana zuwa daidai kanta sai ya kai hannunsa da nufin ya taba ta
Ba zato ba tsammani sai yaji tayi caraf ta kama kansa ta buga da teburin dake gabanta
Take kan basa yayi kwatsa kwatsa kamar an buga kwai akan dutse ya fadi kasa matacce
Koda dakarun sukaga abinda ya faru ga shugabansu take suka zazzare makamansu suka afka mata da nufin su hallaka ta

Kash!!!!! Hakika rashin sani yafi dare duhu inda ace sun san abinda zai faru da basuyi gangancin tunkararta ba
Domin Koda suka tunkareta sai itama ta Shiga cikinsu ta dinga budasu da karfin tsiya

Nanfa guri ya rincabe jini ya dinga fallatsi yana kwaranya akan kasa
Sautin karafkiyar karafa ta cika dodon kunne cikin abinda bai wuce dakiku goma ba ta Bazar da dakarun
Adaidai wannan lokaci ne sarki farsad ya iso gurin tareda dubban dakarunsa
Domin tuni labari ya riske shi kan babban laifin data tafka masa
Da zuwansa Sai ya umarci dakarun dasu afka mata
Aikuwa take sukayi kukan kura suka afka mata gaba daya
Koda ya rage baifi saura taku uku ba a tsakaninsu sai sukaji an daka musu tsawa daga gefe guda sannan wata iska mai karfi ta shuresu ta watsar dasu
Ba kowane ya aikata wannan Aiki ba face boka shuraim wanda ya kasance dan uwa na jini ga sarki farsad
A ka'idar sarautar garin shine wanda za'a baiws sarautar birnin amma saboda baya ra'ayi sai yaki karba ya gwammace abarshi ya cikagaba da aikin bokancinsa
Cikin kakkausar murya sarki farsad ya dubeshi yace yakai dan uwana akan wanne dalili zaka hanani daukar fansa akan abinda wannan yarinya ta aikata min?
Dajin wannan tambaya sai yayi murmushin karfin hali sannan ya matsa kusa dashi Cikin karamar murya yace

Kayi hakuri yakai dan uwana ka sani cewa yaki a wannan lokaci bashida amfani
Domin koda zaka tara gaba daya dakarun sannan ka nemo aron wasu daga kasashen makobtaka ba zamu iya samun galaba akan wannan yarinya ba
Badon komai ba sai don irin sadaukantakar da take da ita
Bama dakarun mu kadai ba hatta n din nan babu yadda zan iya da ita domin an renetane acikin kwalbar tsafi mai karfin Gaske
Amma kamar yadda ka sani Komai na duniya Yana da nasa lagon
To itama tana da nata lagon shine abokinta Farhan wanda take matukar sonsa fiye da kowa a rayuwarta
Mu kuwa dashine zamu kafa mata tarkon da zata fada mu binne ta
Da goma fadin haka take suka umarci dakarun dasu koma da baya
Ba tareda bata lokaci ba suka fice daga gidan suka barta ita kadai acikinsa sai ragowar dakarun da suka rage
A sannan ne ta iya samun damar cin abincin dake gabanta amma ko kadan batajin dadinsa jinsa take kamar madaci abakinta
Badon komai ba sai don abinda ta gani acikin madubin tsafinta
Tana cikin wannan haline Kawai saita ga gidan ya fara girgiza kai kace kasa ce zata tsage ya nutse a karkashinta Nanfa hadiman suka rikice suka fara gujeguje don ceton rayuwarsu
Daga can saiga wani shirgegen bakin aljani ya ratso rufin dakin ya shigo ciki mai matukar muni
Saboda matukar girman da aljanin yake dashi saida gidan ya ruguje gaba daya
Nanfa aka fara kallon Kallo tsakaninta da aljanin daga can sai ya zube kasa cikin girmamawa yace
Barkanki da hutawa gimbiya Husnaila ya agurin sarki suraif
Dajin wannan batu saita dubeshi tace kai kuma wanene kuma meke tafe da kai ?
Koda jin wadannan tambayoyi sai ya dago da kansa yace ni sunana marna'ul safran kuma na fito daga jinsin bakaken aljanu na bangon duniya tsagin gabas
Badon komai nazo nan sai domin mu hada kai duk mu biyun mu biya bukatun dake gaban mu
Bukatarki ta farko itace ki riski dan uwanki ki rabashi da macen dake tare dashi Sannan ki rigashi mallakar sarauniyar kyau wato lasmira
To a halin yanzu ni kadai ne zan iya biya miki wannan bukata
Domin babu wani aljani da yake da karfin guduna duk duniya. Saboda ina iya zagaye duniya cikin abinda bai wuce yini guda ba kachal
Ni kuwa Abu daya Kawai nake nema a wajenki
Wannan Abu kuwa ba komai bane face digon jinin nauwaratul hasnal wacce ke tareda dan uwanki
Domin gama hada wani sihiri da mahaifina yake aikatawa don farfado da kabilar mu daga doguwar suman shekaru ashirin da mahaifinta ya jefasu aciki
Idan kuwa har bamu iya karya wannan shiri to. Nan da wasu shekaru kabilarmu zata shafe daga doron kasa

Dani da mahaifina bamu da ikon tunkararta Domin da zarar mun yi hakan zamu kone kurmus
Amma ke ina da tabbacin zaki iya wannan Aiki
Idan har kin amince zamu yimin wannan Aiki tofa nima a shirye nake n zama bawanki har zuwa sanda zaki mallaki lasmira
Kodajin wannan batu sai tayi shiru tana nazari acikin zuciyarta
Anan jefa taga bata da wani zabi face tabi bayansa idan kuwa karya yake mata da zarar ta gane take zata yake shi ta hallaka shi
Da gama wannan tunani take tace masa ta amince
Nantake kuwa ya rankwafar da bayansa ta haye ta zauna
Zamanta keda wuya sai shima ya bude manya Manyan fuka fukansa guda dari hudu da doriya ya tashi sama da ita cikin azababben gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya

Tunda huraisa take bata tabajin labarin aljani mai karfin karfin gudu kwatan kwacin marna'ul safran ba
Saboda yadda yake kada fuka fukansa da karfin gaske, ta yadda acikin dakiku kadan yake shafe tafiyar watanni

WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GA GIMBIYA HUSNAILA BAYAN TA HADU DA ALJANI MARNA'UL SAFRAN
++++++++ +++++++++ +++++++

Acan kuwa Al'amarin sadauki Farhan lokacin da wadannan dodanni suka juya inda nauwaratul hasnal take da nufin yi mata taron dangi domin sanin ba zasu sami nasara akan farhan ba
Koda ya lura da nufin su sai ya dinga kure musu gudu yana rafkesu da takobinsa
Kan ajima ya tuni yayi musu gagarumar barna wacce tafi ta farko
A wannan lokaci tuni kogon ya gama malalewa da jinin dodannin tareda gawarwaki
Saida gaba daya fuskarsa da jikinsa suka yi caba caba da jini
Yana cikin wannan haline kwatsam sai yaji an harbo masa kibiyoyi guda biyu daga nesa
Take kibiyoyin suka fasa kirjinsa suka fito ta gadon bayansa
Jini yayi feshi daga kirjin nasa
Kafin yayi wani yunkuri sai ya sake jin an jefo masa mashi wanda saidaya faso ta kwuibin cikinsa
Bai san lokacin daya kwallara ihu ba Saboda tsananin zafi da zugin dayaji
Yayin da yayi baya gaba taga taga kamar zai fadi amma koda yaje daf da kasa
Sai cake takobinsa ya tokare da ita bai yadda ya fadi kasa ba
A sannan ne ya hango sadauki safran daga can nesa ruke da baka a hannunsa yana mai kyalkyala dariyar mugunta
Koda ganin haka take sai ya daina jin duk wani zugi da radadi
Nantake ya gyara tsayuwarsa tareda zare wuka daga kugunsa ya jefa masa
Kafin yayi wani yunkuri tuni wukar ta datse hannun da yake ruke da bakar jini yayi tsartuwa
Daga dungulmin hannun nasa
Sannan yasa takobinsa ya karye kibiyoyin dake jikinsa da kuma mashin
Sannan ya yagi rigarsa ya daure raunikan dake jikinsa don tsayar da jini

Ya ci gaba da yakin a haka ba tareda ya nuna alamun gajiya atare dashi ba
Kai sai ka dauka ma kara masa kuzari ake Domin a wannan lokaci yana yaki ne da dukkan karfin sa tareda zafin nama, juriya da bajinta
Ya hana dodannin kuntatawa nauwaratul hasnal itama acan gefe daya dakarunta sunata kokarin bata kariya
Kodata lura da halinda yake ciki sai hankalin ta ya tashi sakamakon sanin cewa tabbas idan aka ci gaba da yakin a haka komai juriyarsa dole ya sare sakamakon jinin dake zuba ajikinsa
dayin wannan tunanin saita kara zage damtse wajen sarrafa dakarun nata da alkaluman tsafi
A sannan ne jiri ya fara dibarsa ya dinga layi sakamakon dafin kibiyoyin da ke jikinsa
Idanunsa suka lumshewa amma duk da haka bai yadda ya yarda takobinsa ba
A daidai wannan lokaci ne safran bayyana da dungulmin hannunsa wanda har yanzu ke digar da jini
Hannun damansa kuwa ruke da takobi tsirara, fuskarsa amurtuke babu annuri
Daga days gefen kuwa mufran shima da takobi tsirara sai murmushin mugunta Yake
Yayinda farhan ya kyallara ido yayi arba dasu sai ya gyara rukon takobinsa
Domin ya tabbatar da cewa wannan karon dolene ayi dauki ba dadin da yafi na farko
Acikinsu wajibi ne daya ya rasa rayuwarsa ko shi ko kuma su
Kafin ya gama tunanin da yake tuni duk su biyun sun falfalo da gudu kansa suna masu karaji da kururuwa
Take shima ya afka musu sunasuna haduwa suka kai masa mahaukacin sara a dokin wuyansa
Cikin zafin nama ya kaucewa saran nasu suka sari iska
Koda takubban nasu suka hadu sai wani tartsatsin wuta ya tashi tareda karar haduwar karfe karfe
Nanfa suka kacame da azababben yaki mai matukar muni
Hakika sadauki Farhan ya cika namijin gaske mai matukar juriyar wahala duk da cewa akwai dafi mai karfi ajikinsa ga kuma jiri na dibarsa kamar zai fadi
Sai gashi a hakan ya zame musu alakakai sun kasa samun nasarar lakutar jikinsa al'amarin daya matukar daure musu kai kenan

Kaico koda aka fara wannan bakin artabun sai wadannan dodannin suka dakata da yakar nauwaratul hasnal suka kewaye suka zama 'yan Kallo
Don haka cikin tsawa ta umarci dakarun dake bata kariya dasu kai masa dauki
Take suka falfala da azababben gudu inda su farhan ke fadan
Tun daga nesa farhan ya dinga yi musu nuni dasu dakata karsu karaso amma sukaki
Koda zuwansu sai suka kaiwa safran suka akan ruwan cikinsa
Cikin zafin nama yasa takobinsa ya kare hare haren nasu
Cikin fushi yasa kafa ya gabzawa daga daga cikinsu duka akan ruwan cikinta
Saboda karfin dukan saida tayi sama sannan ta gwaru da jikin dirkar gini
Dayar kuwa sai yasa hannunsa ya shekaru tareda dagata sama kafafunta sai wutsil wutsil da reto suke a sama
Don kare kanta amma abu ya gagara
Ita kuwa nauwaratul hasnal ta gaskiyar sai ta fara shure shure daga inda take har tana kakarin mutuwa saboda azabar da take ji sakamakon shakar da akayiwa mai bata kariya

WANENE YAKE RASA RAYUWARSA TSAKANIN FARHAN DA KUMA. 'YAN UWANSA?
SHIN NAUWARATUL HASNAL TANA TSIRA DAGA WANNAN SHAKAR DA AKAYI MATA?
SHIN GIMBIYA HUSNAILA TANA BIYAWA ALJANI MARNA'UL SAFRAN BUKATARSA ?
WANE IRIN MATAKI SARKI FARSAD YAKE DAUKA AKAN GIMBIYA HUSNAILA ?

DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MUN HADU A KASHI NA GABA
DAGA NAKU
HABIBULLAH KBR
WHATSAPP NO
09133502477

LIKE, COMMENT AND SHAREKARAGAR AJALI

+++++++6

PART B

++++LBR

HABIBULLAH KBR

Koda ganin abinda yake faruwa ga sarauniya nauwaratul hasnal sai nan take farhan ya daka tsalle ya gabza safran mahaukacin duka a gadon bayansa
Saboda karfin dukan baisan lokacin daya saki wuyanta ba tayi gaba taga taga yana neman faduwa amma sai ya cake bai yarda yaje kasa ba
Cikin rashin sa'a koda farhan ya je kasa sai kafarsa ta zame sakamakon jirin dake dadinsa kansa ya gwaru da kasa ya fadi kasa sumamme
Koda ganin wannan gagarumar nasara da suka samu take sai su mufran suka daga makamansu alokaci guda suka kai masa mahaukatan hare hare da nufin suyi gunduwa gunduwa dashi

Ba zato ba tsammani Kawai saiga gimbiya Husnaila ta bayyana kamar walkiya bisa gadon bayan aljani marna'ul safran amma bai yarda yaje kusa da nauwaratul hasnal ba
Take ta daka tsalle daga inda take tana mai yin karaji gami da kururuwa ta dira a tsakiyar su
Ta kare dukka hare haren da suka kawo masa
Koda takubban su suka hadu da tata sai tartsatsin wuta ya tashi kamar Ana aza wuta a makera tareda Sautin haduwar karfe da karfe
Sannan ta gaba musu duka a kan fuskokinsu wanda saboda karfin dukan saida sukaga taurarin wuya a idanunsu
Suka dan jajja da baya taga taga taku uku saboda mamakin ganin ta
Itakuwa nauwaratul hasnal bata san lokacin da zancen zuci ya kamata tace
Lallai wannan shi ake kira da turnuku fadan iblisai wanda wani daga waje bai isa ya shiga ciki ba"
Tana cikin wannan zancen zuci ne Kawai taga su safran sun kara tasowa gimbiya Husnaila zasu saka ta atsakiya suyi mata taron dangi
Kuma ta tabbatar da cewa indai sukayi haka tabbas zasu sami nasara akanta
Koda ganin haka take ta rikide ta koma soffar rikakken batoyi
Ta tashi sama ta feshe su mufran da wuta mai karfin Gaske sannan ta shuri su farhan da gimbiya Husnaila a gadon bayanta
Kawai sai wata farar kofa ta haske ta bayyana suka shige cikinta
Take itama kofar ta bace bat kamar bata taba wanzuwa ba
Koda ganin wannan abu daya mufran da safran suka kwallara ihu saboda tsananin takaici Suka bi daidai inda kofar hasken ta bayyana da Kallo
Suna kokarin dawo da ita da sihirin tsafinsu amma sai yakiyin tasiri don dole suka hakura

++++++++ ++++++++ +++++++
Yayinda gimbiya lardisa tazo daidai nan a karatunta sai ta dakata Sakamakon ganin da tayi
Wani mahaukacin gumi yana tsatatsafowa daga jikin jarumi rukyan
Kamar wanda aka tsomashi acikin ruwa jikinsa yanata kakkarwa kai kace zai fado daga kan gadon da yake kwance
Cikin tsananin tashin hankali ta ajiye littafin dake hannunta ta tashi
Da nufin nemo mai kula da lafiyarsa
Kwatsam sai taji yasa hannunsa ya riko hannunta tareda yaye mayafin dake rufe dashi
Koda juyowarta sai taga taga ciwukan dake jikinsa suna warkewa gaba dayansu
Kafin cikar wasu dakiku masu yawa tuni sun gama wakewa kamar basu taba wanzuwa ba
Al'amarin daya matukar daure mata kai kenan ta saki baki tana kallonsa
Koda ya lura da kallon da take masa sai ya tuntsure da dariya sannan yace nasan kinyi mamakin ganin samun kafiyata alokaci guda
Ba komai ne ya janyo hakan ba face karfin sihirin da muka samu a yayin da muke karbar wannan horon
A halin yanxu inajin karfin da ban tabajin kamarsa ba kamar zan iya daukar duniya gaba dayanta
Don haka a yau zan fita neman SAIFUL LAIHAN kafin su boka surkais su riga mu
Yana gama fadin haka sai ya sauka daga kan gadon da yake kwance
Ya shiga cikin wani daki daban ya kullo kofa
Jim kadan sai gashi ya fito cikin gagarumar shigar yaki mai matukar ban tsoro
Hannayensa kuwa cike da gurayen tsafi a damatsansa
Yana fitowa sai ya dubeta tareda cewa yake ma'abociyar hikayoyi
Nayi rantsuwa da kabarin kakana nan gaba kadan sai nayi jarumtakar da baki taba rubuta irinta ba acikin wannan kundi naki
Don haka nan gaba kadan zanso ki karasa bani labarin hikayar yadda gabar wadannan 'yan uwa take karewa da wanda yake nasara
Sai kuma wanda yake mutuwa daga cikinsu, Kai hardama lokacin da boyayyen sirrin dake tsakaninsu yake tonuwa
Nangaba kadan idan mun sami lokaci zaki ci gaba da bani wannan daddadar hikayar mai cike da rudani acikinta da abubuwan al'ajabi
Yanzu kema sai ki tashi ki shirya mu fita neman abinda ke gaban mu
Ba tare da bata lokaci ba itama ta mike ta shiga cikin masaukinta jim kadan sai gata ta fito sanya da nata kayan yakin
Wadanda akayiwa ado da zaren zinare ba karamin kyau kayan sukayi mata ba kasancewar anyi su ne da zaren zinare
Sannan ta daukar karamar akwatin da take sanya kundun hikayoyi aciki ta mai dashi ciki ta rufe
Sannan ta daureshi agadon bayanta daga nan ta fito daga cikin dakin ta iske rukyan a tsaye Yana jiranta
Kodaya ga irin shigar da tayi sai ya tuntsure da dariya yace
Ai wannan shigar da kikayi kadai ta isa ta nunawa duniya cewa ke kadai zaki iya yakar duk abinda ke cikinsa kuma kiyi nasara akansa
Dajin wannan batu saita girgiza kanta tareda maida masa da martanin murmushi tareda cewa
Ka iya bakinka domin akoda yaushe hakkin daka raina shine yake tsone maka ido
Daga wannan furuci babu wanda ya kara magana daga cikinsu
Sannan rukyan ya runtse idanunsa tareda karanta wadansu dalasiman tsafi azuciyarsa
Fara karatun keda wuya sai gidan da suke ciki ya fara girgiza kamar zai dilmiye a karkashin kasa
Komai na gidan kuwa sai ya bar kan doron

Please Login or Register in order to submit comment