Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

guri ya yamutse
kaico hakika idan ajali yayi tilasne bawa ya amsa
sai gashi wannan halittar ta shiga tsakiyarsu tanayi musu cin tsamar nama kafin a dauki wani lokaci mai tsawo tuni filin gasar ya rine da jini
da sassan jikin bil'adama ba tareda sun iya yi mata ko rauni ba
wani lokacin ma tsalle zakaga tanayi duk wanda ta dira akansa sai dai kaga ya talitse naman jikinsa ya makale akan kasa cikin dakikun da basu gaza goma ba
tuni ta karar da jaruman saura mutun uku kacal wadanda suka kasance zakwakwurai masu tsananin juriya gami da naci su dinma kuma tayi musu mugayen raunika
da kyar ma suke iya maida mata da martani a lokacinne filin ya kara cika da ihun 'yan kallo kowa na koda gwaninsa domin kara masa kwarin gwuiwa
wannan ne ya janyo hankalin halittar ta lura da 'yan kallo
don haka take tayi wani gurnani mai ban tsoro ta fito da harshenta lokaci guda ta shuri 'yan kallo ta watsa bakinta sannan ta daka mahaukacin tsalle sai gata ta fito daga cikin ramin ta fada cikin 'yan kallo
ta far musu
wohoho!!!
nanfa guri ya kara yamutsewa yayin da ta hau kan mai uwa da wabi
mutane suka fara guje guje domin ceton ransu
dakaru kuwa suka afka mata domin su dakatar da ita
amma duk abanza domin yunkurin nasu yaki tsanana komai
sai ta hada da dakarun da mutanen gari tana lamushewa manya da yara abin babu kyan gani
mutum kacal wadanda hankalinsu bai tashi ba agurin
daga sadauki farhan wanda ke tsaye aguri daya sai nauwaratul hasnal wacce ke zaune har a sannan akan karagar mulkinta tana dube dube acikin dubunnan mutanen dake gurin
asannan ne idanun ta suka kai kan farhan dake tsaye can gefe guda ba tareda ya kara koda taku guda ba
a wannan lokaci kuwa tuni filin ya gama dadewa babu abinda zaka gani face gawarwaki fululu a zube a kasa

sai wani karamin yaro guda daya daya rage a filin yana ta faman tsala kuka
koda wannan halittar tayi arba da shi take ta ruga da gudu inda yake domin yake don ta talitse shi

SHIN TANA IYA SAMUN DAMAR TALITSE WANNAN YARO?
MENENE SARAUNIYA NAUWARATUL HASNAL TAKE NEMA ACIKIN 'YAN KALLO?
SHIN WA YAKE SAMUN NASARAR LASHE WANNAN GASA?
DON JIN AMSISHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MUN HADU A KASHI NA GABA

LIKE AND COMMENTS

DAGA NAKU HABIBULLAH KBR
09133502477+++++++KARAGAR AJALI 5

++++++++++PART C

-+++++++LBR

HABIBULLAH KBR

loKacin daya rage baifi saura taku guda ba tsakanin wannan muguwar halittar DA wannan karamin yaron ba
sai kwatsam sadauki farhan ya falfalo DA azababben gudu daga inda yake tsaye kamar kiftawar ido ya shure yaron daga wannan guri
sannan ya gabza Mata mahaukacin duka a idonta guda
aikuwa take hannun NASA ya nutse acikin kwarmin idon Nata
nanfa halittar ta kwallara ihu Wanda ya ninka Wanda tayi afarko sautin ihun ya ratsa gaba daya birnin romaniya da makobtansa
ita kuwa sarauniya Nauwaratul hasnal dake tsaye a can gefe guda tana kallo sai fuskarta ta fadada DA murmushi
sai ta kafeshi DA idanu domin gano yanayin kamanninsa amma sai ta kasa sakamakon rufe fuskarsa DA yayi DA rawani
cikin Kumar rai halittar ta fesowa farhan ruwan guba daga cikin bakinta don ta zagwanyar DA naman jikinsa Kafin ruwan ya sauka ajikinsa tuni ya kauce daga wajen
koda gubar ta zuba a kan kasa take gurin ya narke gaba daya Kai kace an narka dalma
cikin zafin nama ta sake kawo masa wafta DA dogon harshenta DA nufin ta hadiyeshi
saidai kash!!!
tuni ya sanya takobinsa ya cake harshen Nata acikin kasa sannan yayi alkafira a sama ya dira a tsakiyar kanta ya caka Mata wasu kananan wukake akan Nata

aikuwa nan take wukaken suka huda man Nata jini yayi tsartuwa kamar an buds magudanar ruwa
nanfa ta fara murgin murgin akasa saboda zafin fitar rai
kafin cikar wasu dakiku ta daina motsi ta zama matacciy
a sannan ne farhan yayi duba inda nauwaratul hasnal take
bisa mamaki sai ya ganta har yanzu a wannan guri kuma bata daina kura masa idanu ba
daga bisani sai yaga ta Dan ajiye masa guntun murmushi Wanda ya kasa gane dalilinsa
kawai sai ya jiyo sahun sukuwar doki daga bayansa an nufo inda yake tsaye
koda mahayin ya karaso inda yake sai ya sauka daga kan dokin cikin rissinawa ya mika masa wata guntuwar wasika
yana karba sai mahayin ya haye kan dokinsa yaci gaba DA tafiya abinsa

ba tareda bata lokaci ba farhan ya bude wasikar tareda Fara karantawa kamar haka

lale marhaban DA zuwan sadauki farhan na birnin sin

ya Kai wannan bakon jarumi ka Sani tuni nasan DA zuwanka wannan birni DA kuma dalilin zuwan naka
a halin yanzu kana kan hanyarka ne ta zuwa birnin misra domin Neman sarauniyar kyau wato lasmira don ta zamo maka hanyar DA zaka mallaki karagar KARAGAR AJALI
don ka zama gagara badau kuma sarkin sarakai Wanda duniya ba zata manta DA tarihinka ba

yakai farhan a halin yanzu akwai gagarumin aiki agabanka
bayan haka akwai wash sirrika da har yanzu baka sansu ba game DA lasmira Wanda ni kadaice nasansu
idan har kanason sani saikazo fadata domin tattaunawa akansu
koda yazo daidai nan akaratun wasikar DA take sake maida dubansa zuwa inda nauwaratul hasnal take tsaye
a wannan Karon sai yaga ta juya masa baya taci gaba DA tafiya abinta yayinda farin hayaki ya rufe Mata baya ya daina hangota
nanfa zuciyarsa ta kamu DA mamakin yadda akayi tasan tarihinsa DA kuma dalilin barinsa DA gida
duk yadda akayi dole tana DA kykkyawar masaniya game da karagar ajali
don' haka yabi bayanta
yana gama wannan tunani sai ya shafi madubi tsafinsa ya duba taswirar hanyar DA zata kaishi gidan sarautar rumaniya
sannan ya mayar DA shi ya nufi hanyar
tafiyar dakiku kadan yayi sannan ya isa kofar masarautar Wanda dakaru sama DA dubu ashirin suka kewayeshi don tabbatar DA tsaro
amma koda suka hango tahowar as sai suka buds masa hanya yayinda guda kuma daga cikinsu yayi masa rakiya har tsakiyar fadar fadar
DA zuwa saiya iske sarauniya Nauwaratul hasnal a zaune ta chaba ado Wanda ya ninka Wanda tayi afilin gasar Neman aurenta
agabanta kuwa katon teburin abinci ne an zube nau'in abinci Kala daban daban
tun daga bakin kofa badakaren yaja tunga ya tsaya farhan ya karasa ciki
cikin tattausar murya nauwaratul hasnal tace
barka DA zuwa babban jarumi farhan Dan gidan attajiri jawwas

nasan zakayi mamakin dalilin dayasa na Sanka harma na gayyaceka zuwa man,kuma nasan zakaso sanin daliln hakan
kafin sannan ga guri nan ka Fara zama tayi masa nuni DA kujerar DA take fuskantar tata
sannan ta tashi ta Fara karanta wasu dalasiman tsafi tana tofawa a kowacce kusurwa ta fadar
duk inda ta tofa wadannan dalasimai saidai kaga tururin hayaki yana tashi tareda wani sauti Kai kace Ana zuba ruwa acikin tafasashshen mai
bayan ta kammala tsubbace tsubbacenta sai ta dawo ta sami guru ta zauna ta Sanya hannunta cikin farantin abincin ta Fara ci sannan tayi masa tayi
ba tareda bata lokaci ba kuwa ya Fara cin abincin
tsawon lokaci ba tareda dayansu yace DA daya uffan ba
sai bayan sun kammala ne ta katse shirun dake tsakaninsu DA cewa

yakai farhan ka Sani cewa ba komaine yasana gayyaceka izuwa wannan guri ba sai
domin na sanar dakai wadansu abubuwa wandanda a halin yanzu daga kai
har' yan uwanka babu Wanda yasan dash

DA farko dai inaso ka Sani ba Kaine ka kawo kanka wannan birni nawa ba
nice DA kaina na sarrafa alkaluman tsafinka suka kawo ka yankin birnina
nasan DA cewa zakazo nan tun shekaru uku baya ,Abu dayane abin cikena na kasa ganewa
shine DA wacce irin siffa zakazo kuma a Ina zaka bayyana?
daga bayane na gane cewa zaka bayyana a gareni
wannan hanyar kuwa itace dolene na had a gagarumar gasar mutuwa ta manema aurena
duk Wanda yayi nasara shine xai aureni duk DA nasan cikin jaruman gasar babu Wanda zai tsira daga sharrin wannan muguwar halittar
Abu na gaba DA make son ka Sani shine dani DA Kai an haliccemune domin juna kuma DA sihiri guda
ma'ana kamar yadda boka hushairul hasnal ya kyankyasheka ta cikin kwalbar sihiri haka nima akayi ni
atakaicedai ba macece ta haifeni ba a salima mahaifinane ya kirkiro wannan sihirin tsafin
a lokacin DA yake Raye babu irin kokarin DA baiyi ba domin yaga ya kare karagar ajali daga fadawa hannun azzalumai
wannan daliline yasa ya kirkironi ta hangar zuba kwayoyin haihuwarsa acikin kwalbar sihiri domin baiwa KARAGAR AJALI kariya
saidai hakan ba zata yiwuba sai mun hada karfi DA karfe ni dakai
banbancin dake tsakanina dakai shine Kai kana tsafi sannan kuma kana DA karfin damtse.
n kuwa ban kasance mayakiya ba amma daga nan inda nake zaune ina IyA ganin duk abinda yake faruwa a duniya DA kuma sarrafashi Kai hardama abin DA zai faru nanda shekaru dubu masu zuwa DA kuma dalilin afkuwar su
Abu dayane yake min cikas acikin sha'anina shine aljani rabtarul has Wanda karagar ajali DA saiful laiham ke karkashin tsaronsa
acikin bincikena na gano cewa nan gaba duniya zata hargitse DA kashe kashe jini zai gauraye DA tekunan duniya gawarwakin mutane zasu zama taki agurin tsirrai DA duwarwatsu
kasa zata rine da jinin bil'adama sakamakon barin saiful laiham adoron duniya
dole sai mun hadu ni dai sannan zamu iya dakatar da wannan bala'i
kodajin wannan batu sai farhan ya tuntsure da dariya daga bisani kuma yace
yake wannan sarauniya
hakika na yarda Kinsan tarihina sosai shi yasa kika kirkiri kalaman da zaki fada min tun kafin nazo nan wanda yin hakan bazai sa na gasgata maganarki ba
yana gama fadin haka saiya mike tsaye da nufin fita daga fadar
sai tace dashi saurin me kakeyi ne ?
yanzu zan nunamaka zahiri
harda hadimin aljaninku da boka SURKAS
ya kama dannan ya turo muku dan leken asirinsa da yayi domin kara zafafa gaba tsakaninka da 'yan uwanka
tana gama fadin haka saita tafa hannayenta
take sai ga hoton aljani SHAMZAN daure cikin kurkuku ana gana masa azaba
daga can kuma sai ga hoton tafiyar sa duniyar hallaka cikin tsaka mai wuya .sannan hoton ya dauke wani hoton daban ya bayyana inda yaga karshen duniya yadda zata rikice bayan shudewarsa daga doron kasa sanadiyar Saiful laiham

nantake yaji hankalinsa ya dugunzuma ya tashi baisan lokacin daya koma ya zauna ba
Nauwaratul hasnal ta dora hannunta kusa da nasa tace
yakai farhan ka sani kaddara tunda har ka baiwa 'yan uwanka labarin karagar ajali har ma hakan ya janyo sanadin rabuwar kanku to dolene ka fita nemanta kafinsu
kuma ina tabbatar maka da cewa koda kai. ko 'yan uwanka kun mallaki lasmira baku isa ku san inda taswirar duniyar hallaka take ba
domin an rubutatane da alkalamin tsafi kuma a tsakiyar zuciyarta wanda ni kadai ce zan iya karanta taswirar
idan kuwa aka tilasta mata da bincike take zuciyar zata kone kurmus
kaga kenan babu mai mallakar lasmira dasu karagar aajal acikinku

ni kuwa bazan taimaka maka ba har saibkayi min alkawarin zakayi zaman aurene koda kuwa na tsawon sa'a tunda nasan a yanzu lasmira ta gama shiga zuciyarka
koda tazo daidai nan a zancenta sai tayi shiru ta zuba masa idanu tana jirantaji hukuncin daya yanke
saidaya jima yana tunani ya tabbatar da cewa
bashida wata mafita data wuce ya karbi tayin data yi masa
sannan yace da ita ya amince da bukatarta
nanfa ta kamu da tsananin farinciki ba tareda bata lokaci ba ta rubuta wasikar bada ajiyar karagar mulkinta ga wazirinta
ta aika wani amintaccen hadiminta a sirrance domin ya kai masa
sannan suka fito daga gidan sarautar domin fita neman lasmira

da fitar su suka iske tsuntsun tsafinta a harabar gidan sarautar sai shawagi yake a sama
amma koda ya sunkuyo da kansa kasa ya hango fiyowarta take ya saki fukafukansa ya sauko kasa
ba tareda bata lokaci ba suka haye gadon bayansa ya luluka da su cikin gajimare kai tsaye ya nufi hanyar da zata kaisu birnin misra don neman lasmira wacc take daf da bayyana
tazarar dake tsakanin birnin rumaniya da birnin misra nisan tafiyar shekara uku da rabi ce komai karfin gudun aljani ko jarumtakarsa
badon komai ba sai domin mugayen hatsarurrukan dake kan hanyar dajijjikan

wanda kuma ya zama dole mutum ya ratsa ta cikinsu kafin ya isa birnin misra
wannan daliline yasa al'ummar wadannan kasashe suka yanke zumunci a tsakaninsu bayan sunyi iya kokarinsu don ganin sun kawo karshen wannan masifa amma sun kasa

karfin iskar dake kadawa a samace ta janyo kwancewar rawanin da farhan ya rufe fuskarsa dashi
koda ganin wannan kyakykyawar fuskar tasa sai nan take nauwaratul hasnal ta kara rikicewa fiye da farko taji kamar an share mata duk wata damuwa ta kasa dauke idanunta daga kan fuskarsa
har saida shima ya ankara da halin data shiga
don haka sai yasa hannunsa a karon farko ya jijjiga kafadarta tareda cewa
yake wannan sarauniya mai daraja bai kamata ki zubar da kimarki kamar yadda sauran mata suke aikatawa ba

dajin wannan batu sai tayi murmushi tace
akan me?
sabodani ba mace bace kamarsu?
sai yanxu ne na gane dalilin dayasa 'yar uwarka gimbiya lardisa ta makance acikin soyayyarka
kuma ina tabbatar maka cewa a halin yanzu bata daga cikin masu neman lasmira don mallakar saiful laiham da karagar ajali
Ita burinta shine ta hallaka ta kowa ya rasa
sannan ta dawo domin mallakar ka
damar da muke da ita yanzu itace muyi kokarin riskar lasmira kafin ts rugamu
wannan yarinya ba zata bayyana ba sai nan da shekaru uku da rabi cif cif
kaga kenan yayi daidai da lokacin da zamu isa birnin misra
daga wannan furuci tayi shiru da bakinta bata kara cewa uffan ba
sukaci gaba da tafiya abinsu babu wanda ya kara c da wani uffan
saida suka shafe kwanaki uku cur suna tafiya ba tareda yada zango ba ko kuma sun hadu da wani abin cutarwar ba
acikin kwana na hudun ne suna cikin tafiya kwatsam ba zato ba tsammani sai sukaji wata irin gagarumar iska mai karfin gaske ta taso daga kowacce kusurwa ta dajin ta cure aguri guda sannan ta juyo kansu
nantake guguwar ta rikita tsuntsun tsafin da suke kai ya kasa gaba ko baya sai kada fuka fukansa yake
lokaci guda kuma ta tsitstsinka shi a saman
take su sadauki farhan suka sulalo kasa saidai kafin su isa kan turba tuni
wasu manyan fuka fukai sun faso ta cikin kafadunsa sun fara kadawa cikin iska

sannan ya ruke nauwaratul hasnal da hannunsa na hagu na damar kuwa ruke da zabgegiyar takobinsa
kallo daya zakayi masa a wannan lokaci kasan cewa lallai ya cika namijin gaske kuma mai taurin zuciya
badon komai ba sai domin yadda yaki nuna alamun tsoro akan idanunsa
sannu a hankali suka sauka kan turba cikin wani kasurgumin daji mai matukar ban tsoro da razanarwa
dirarsu keda sai fukafukan suka bace daga jikinsa
sannan ya cewa nauwaratul hasnal ai kece zaki shiga gaba tunda kinfini sanin hanya
ba tareda gardamar komai ba kuwa ta shige gaba shikuwa yana biye da ita tare da lura da duk wani sauti ko motsi na dajin
suna cikin tafiya ne kwatsam sukaga kasa ta fara girgiza tana tsatstagewa
daga can saiga wata katuwar macijiya tayi fitar burgu daga cciki ta
ita dai wannan macijiya tsawon ta kadai yafi tsawon dogayen bishiyoyin dabino biyu
kaurinta kuwa yayi na rikakkun bishiyoyin kuka guda uku
fatarta kuwa mai matukar santsice , tauri da kuma walwali
a duk sa'addata daga kanta sama sai kaga kamar kan Nata zai hade da sararin samaniya
a tsakiyar kanta kuwa tana DA wasu dogaen kahun huna guda hudu
masu matukar kauri da kuma tsini
ita kanta nauwaratul hasnal tayi matukar mamakin bayyanar wannan macijiya domin asalinta ba'a wannan nahiyar take ba
dole wasune suka turota ta hanyar amfani da alkaluman tsafi
nanfa su farhan suka ja tunga tareda fuskantar wannan macijiya har zuwa sanda ta gama fitowa daga cikin ramin
cikin rada nauwaratul hasnal tace da farhan
kayi iya kokarinka domin ceton ranka nima zan kula da rayuwata
maganar data bashi mamaki kenan
yace a cikin zuciyarsa
tayaya mutumin da bai iya koda ruke takobi ba zai kare kansa kansa daga wannan macijiya

aikuwa kafin ya gama wannan zancen zucin da yake tuni macijiyar ta shammaceshi ta kawo masa mahaukacin farmaki da jelarta
cikin tsananin zafin nama kafin jelar ta eauka ajikinsa tuni ya daka tsalle kamar wanda aka harba da sifirin ya kaucewa harin nata
ita kuwa nauwaratul hasnal tuni ta narke ta zama ruwa
shima ruwan kasa ta tsotse shi ko danshi babu
koda jelar ta sami wani katon dutse dake bayansu take dutsen ya tarwatse
saboda karfin dukan nata
nantake farhan ya ruga da azababben gudu kan macijiyar yana mai karaji da kururuwa irin ta masu dakakkiyar
suna haduwa yakai mata mahaukacin sara a tsakiyar kanta
koda kaifin takobin ya sauka ajikinta take wata kara ta tashi
kai kace karfe da karfe ne suka hadu sannan itama ta gabza masa duka da kahonta
saboda karfin dukan saidaya tashi sama kamar an harbashi daga cikin baka
ya gwaru da wata katuwar bishiya dake bayansa
har saida bishiyar ta jijjigo daga karkashin kasa suka fadi tare gudan jini ya fito daga bakinsa da hancinsa
take yasa hannunsa ya share Jinin da hannunsa
sannan ya kara falfalawa da gudu kanta
haduwarsu keda wuya sai suka kachame da azababben yaki mai Matukar muni
a wannan karon sai yaki yarda ya fuskanceta gaba da gaba ya dings hadawa da zulle zulle da kauce kauce
aikuwa cikin kankanin lokaci suka hargitsa dajin gaba daya bishiyoyi suka dinga kakkaryewa tareda duwarwatsu
guri Ya yamutse babu abinda kakeji face karafkiyarsu
aduk sa'adda takai masa hari ya kauce saidai kaga duk abindata samu ya dagargaje
shi kuwa babu abinda yake face kauce kauce gami da zulle zulle tamkar ya kasance ifiritin aljani
saida suka shafe sa'o'i masu yawa suna wannan fafatawa ba tareda dayansu ya sami nasara akan daya ba
suna cikin wannan hali ne kwatsam sai ga nauwaratul hasnal ta taho da gudu kan macijiyar cikin siffar mulmulen karfe
koda karfen da macijiyar suka hadu take wata kara ta tashi wacce ta gauraye dajin gaba daya
take mulmulen karfen yayi tsalle ya fadi gefe guda ya rikide ya koma ainihin siffar nauwaratul hasnal cikin mawuyacin hali mai kama da rayuwa ko mutuwa
koda ganin abindaya faru ga nauwaratul hasnal take yaji zuciyarsa ta fara tafarfasa kamar zata kone
take ya mai da takobinsa cikin kufe tareda karanta wwas dalasiman tsafi ai kuwa nan take ya rikide ya koma dunkulen wuta
itama wutar tayi fitar burgu tamkar an harba majaujawa ta fara kama dajin cikin kankanin lokaci wutar ta gauraye dajin gaba daya
kaico!!!!!!!

hakika wuya abar gudu ce, kuma idan kaji ana maganar ki gudu tofa sa gudu ne baizo ba
domin kuwa koda wannan macijiya taji wannan ruwan bala'i ba shiri ta fara neman hanyar tsira da kafafunta
saidai kash!!!
damar data kasa samu kenan a wannan lokaci saboda yadda ya kuntatata tareda toshe mata kofofin tsira
tana cikin wannan mawuyacin haline wuta r ta fasa bakinta ta shiga cikinta sannan tayi bindiga ta tarwatse

faruwar hakan keda wuya sai wutar ta dunkule guri guda ta cure ta koma ainihin siffar farhan
cikin sauri ya ruga da gudu inda nauwaratul hasnal take kwance magashiyan kamar bata numfashi
take ya sanya hannunsa ya ciccibota ya fara duba lafiyar jikinta
bisa mamaki sai yaga ta bude tana yi masa tattausan murmushi daga bisani tace
sannu da kokari jarumin jarumai hakika yau ka nuna min bajintarka a fili kuma na kara gamsuwa cewa nan gaba zaka iya mallakar KARAGAR AJALI
Duk da cewa ba karamin aiki bane agabanmu
da gama fadin haka sai ta mike tsaye kamar babu abindaya sameta tace me kake jira ai sai ka tashi muci gaba da tafiyar da ke gaban mu kafin lokaci ya kure
batare da bata lokaciba ya mike tsaye tareda gyara damararsa suka ci gaba da tafiya abinsu suna hira
kai kace ba'a guri mai hatsari sukeba idan ka gansu saika dauka cewa sunyi shekaru DA sanin juna
a wannan karon sai suka koma amfani DA sihirin tsafinsu wajen takaice Nisan tafiyar
saboda haka cikin kankanin lokaci suka dinga shafe tafiya mai nisan gaske bisa kafafunsu
saida suka shade sa'o'i goma suna tafiya ba tareda yada zango ba ko kuma sunci wani abinba har zuwa yammaci
da yammaci sakaliya ne suka isa iyakar wannan dajin da suke cikibdafvda faduwar rana
anan ne suke iske wani katon teku wanda igiyarsa take kadawa da karfin gaske
kamar akowanne lokaci zata iya kwacewa ta malale duniya gaba daya
a wannan guri babu sautin da kunnuwa sukeji face kadawar wannan ruwa
kai da gani kasan dole baza'a rasa mugayen halittu ba
da isarsu wannan guri duk sai sukaja tunga suka tsaya domin tunanin hanyar da zasu bi domin ketare wannan teku
nanfa sukayi cirko cirko suna nazari ba tareda dayansu yace uffan ba
daga nan ne fa dabara ta fadowa farhan kawai sai ya ruga da gudu zuwa dajin da suka baro domin samo itatuwan da zasu sassaka jirgin da zasu ketare ruwan dashi
ya barta a tsaye ita kadai tana mai kiran sunansa amma ko waigowa baiyi ba
bayan dakiku masu yawa sai ta hangoshi daga nesa ya taho dauke da murtuka murtukan bishiyoyi biyu a kafadarsa
bata san sanda ta wangame baki ba ta bishi da kallo
sakamakon yadda zallar kirar sadaukantakarsa ta fito a fili tareda kyawunsa
jijiyoyinsa da damatsansa sukayi burdin burdin kamar zasu fasa rigarsa su fito waje
akugunsa kuwa yana janye da murtuka murtukan jijiyoyin bishiyu
duk da kasancewar yana dauke da kayan. nauyi amma tafiya yake kamar bai dauki komai ba
yana zuwa daf da ita ya wullar da bishiyun yace ki jirani na kammala sassaka jirgin da zamu ketare wannan teku dashi
domin komai dare sai mun ratsa ta cikinsa ba zamu kwana acikinsa ba
dajin wannan batu sai ta maida masa da martanin murmushi ba tareda tace uffan ba
azuciyarta tace inda kasan abindana sani game da wannan teku da baka fadi haka b

ba tareda bata lokaci ba ya fara sassara bishiyun da wani gatari bai kammala ba sai bayan da dare ya raba bakajin komai face na kadawar iska da kuma kukan tsuntsayen dake bayansu
yana gamawa ne ya lura nauwaratul hasnal ta fara jin yunwa amma don kada ta nuna gajiyawarta taki ta fada masa
don haka take ya fiddo da wani gasahsshen kilishi daga cikin jakar guzurinsa ya mika mata taci shima yadau wani ya fara ci
bayan sun kammala cin abincin ne suka tashi suka tura jirgin cikin ruwa sannan suka shiga suka kama tafiya
farhan ya zauna a tsakiyar jirgin yayindaya ruke matukan jirgin da hannayensa biyu yana tuka shi
Ita kuwa ta tsaya abayansa
ahankali jirgin ya fara tafiya a saman ruwan yana kara gudu har ya ratsa cikin tekun ba tareda sun fuskanci wata matsala ba
kuma suna tafiyar suna lura da ko ina na cikin ruwan har dare ya gama rabawa ya zamana in banda hasken farin wata babu abinda kake gani
a wannan lokaci ne barci ya fara kama nauwaratul hasnal bata sani ba
kwatsam sai igiyar ruwan ta kara hautsinewa jirgin ya soma tambal tambal kamar zai kife dasu
koda ganin wannan al'amari sai farhan ya mike tsaye tareda sakin matukan jirgin don ganin abinda yake shirin faruwa

ba zato ba tsammani sai suka ji. wata mahaukaciyar tsawa da walkiya wanda sukayi sanadin darewar ruwan gida biyu kamar an yanka lemo suka rufta cikin sa sannan ruwan ya koma ya hade..

ME ZAI FARU GASU SADAUKI FARHAN DA NAUWARATUL HASNAL?

SHIN SUNA IYA KUBUTA DAGA WANNAN TEKU HAR SU ISA BIRNIN MISRA AKAN LOKACI?

DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MUN HADU A KASHI NA GABA
NAKU. HABIBULLAH kbr

KARAGAR AJALI
+++++++++6
PART A

+++++++++++LBR

++++HABIBULLAH KBR

TYPING

HABIBULLAH KBR

Kawai sai ganinsu sukayi acikin wani katon kogon dutse mai tsananin duhu wanda ko tafin hannunsu basa iya gani aciki

Da bayyanarsu acikin wannan guri take nauwaratul hasnal ta samar musu da hasken tsafi wanda ya haske kogon baaba daya
Nanfa suka cika da mamaki sakamakon ganin yadda aka cika kogon da zanikan halittu masu hauwa wadanda babu su a awannan zamani don tuni sun jima da shudewa
Kallo daya zakayiwa wadannan halittu kasan cewa a zamaninsu ba karamar barazana suka zamarwa duniya ba

Farhan ya dubeta yace take ma'abociyar ilimin sani me kika sani dangane da wadannan halittu arayuwarsu ta baya?
Dajin wannan tambaya sai tace aini a ka'idar sihirina bana iya ganin abinda ya ride ya wuce tsawon shekaru dari baya sai dai wanda zai faru don sanin hanyar magance shi
Amma abinda zaifi mana daga yanzu har zuwa lokacin da same mallaki karagar ajali kar mudinga bincike akansu my tunkareshi gadan gadan
Koda kuwa duk my biyun zamu rasa rayukan domin tsawaita bincike babu abinda zai haifar mana face karayar zuciya
Tana game fadin haka Sai ta wuce gaba idanunta arufe tana karanta wadansu dalasiman tsafi azuciyarta
Yin hakan keda wuta take Sai kogon ya faru girgiza yana rangaji kamar zai rufta cikin kasa
Manyan duwatsu suka fara ruftowa kafin cikar dakiku goma tuni wadannan halittu sun fara faso jikin ginin kogon suna fitowa fili azahiri cikin siffofi dajin daban daban
Wasu zaka gansu da siffofin bil'adama amma kawunansu na batoyine
Sai feshin wuta suke ta bakunansu, wasu kuwa dodanni ne amma wadanda kawunansu sun ninka gangar jikin a girma sau uku ta yadda zasu iya

Please Login or Register in order to submit comment