Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

arba da ita ba tareda yaji ta burgeshi ba
Tana gama kwalliyar ta fita daga turakar ta ba tareda ta tsaya koda cin abinci ba
Maimakon ta wuce dakin sarki suraif kamar yadda ta saba
Saita canja hanya
Ta nufi wani sashin daban , dakaru na rissinawa tare da mika gaisuwa agareta
Har taje bakin kofar fita daga masarautar kawai sai taji muryar sarki suraif ya kira sunanta
Cikin sauri ta waiga inda ta jiyo muryar tasa alokacin da yake tahowa inda yake
Da karasowar sa yace ke kuwa yau saurin me kike da har kika manta da ziyarar da kika saba kawo mini?
Dajin wannan tambaya cikin zumudi tace
Ya abbana kayi hakuri ina saurin zuwa gurin masoyina farhan ne wannan daliline yasa na manta dakai amma karka damu Idan na dawo yau acikin turakarka zan kwana
Da gama fadin haka sai ta ci gaba da tafiyarta
Koda jin wannan batu sai zuciyar ta buga da karfin gaske, zuciyar sa ta harzuka ainun
Baisan sanda ya daka mata mahaukaciyar tsawa ba

Yace dakata babu inda zakije har abada babu ke babu soyayya da farhan
Matukar ina numfashi adoron kasa dolene ki bi umarnina,
Idan kuwa kika ketare umarnina zan manta da dangartakar dake tsakaninmu
Aikuwa ko sauraronsa bata tsaya yi ba taci gaba da tafiyar ta
A sannan ne yaji kamar ya fada mata dangartakar dake tsakaninta da farhan
Amma sai ya kasa sakamakon tunawa da gargadin da boka hulbaz yayi musu
Cikin fusata sarki suraif ya dakawa dakarun sa tsawa yace me kuke jira ne maza ku dakatar da ita
Karku kuskura ku bari ta fita daga cikin gidan nan ku kama min ita da karfin tsiya
Kodajin wannan umarni sai take dakarun suka zazzare makaman su
Tareda fara kewaye ta ba tareda sun afka matanba ,

Ba komai ne ya janyo hakanba face sanin cewa duk wanda yayi gaggawar tunkararta tofa karshensa yazo
Harsaida sarki suraif ya fusata ya kara daka musu tsawa,
Sannan suka yi kukan kura suka afka mata suka turmusheta suna shirin daura mata sarka
Koda suka lullubeta sai tayi karaji ta yi wulli dasu ta zubar dasu kasa kai kace tayi watsi da tsummokara
Sannan ta zare takobin ta tace nayi rantsuwa da gemun mahaifina duk wanda daga cikin ku ya kara yunkurin dakatar dani saina raba ruhinsa da gangar jikinsa
Tana gama fadin haka sai ta juya ta fice daga cikin gidan alokacin da sarki suraif yabita da kallo
Sai A sannan ne yaji nadamar sanin Boka hulbaz da yayi arayuwarsa sakamakon jefa su da yayi cikin tsaka mai wuya ganin cewa ya haifi 'ya'yan da ba zai iya sarrafasu ba
Har ya kara budar baki da nufin sanar da ita asalinta
Sai zuciyarsa tace kul!!
Karka kuskura ka sanar da ita Domin Idan ka aikata hakan Kamar ka janyo tarwartsewar burinku da kuma nasu ne gaba daya
Haka dai yanaji yana gani huraisa ta fice daga cikin gidan shi kuwa yabita da kallo idanunsa suna neman fito da kwallar nadama
Ba zato ba tsammani sai yaji an dafa kafadarsa ta baya Cikin sauri ya juya Domin ganin wanda ke bayan nasa
Ba kowa ya gani ba face attajiri jawwas
nan fa ya tsaya yana kallonsa cikin mamaki wanda har sau da tsargu yace
Karkayi mamakin zuwana Adaidai wannan lokaci nazo ne da taimakon boka Hushairul hasnal kuma naga dukkan abindaya faru tsakaninka da gimbiya huraisa
Ka sani cewa ahalin yanzu al'amura sun fara kokarin chakudewa
Don haka ya zama dole yanzu mu sami guri mu zauna domin tattaunawa akan al'amuran Domin yanzu na gane cewa duk wahalar da mukayi abaya tana neman ta zama ta banza muddin bamu dauki kwakkwaran mataki ,
Kuma da alama Boka hulbaz ba karamin tuggu ya shirya mana ba wanda ya zarce tunaninmu
Kodajin haka sai zuciyar sarki suraif ta buga da karfi a karon farko na rayuwarsa
Don haka ba tareda gardamar komai ba yajashi gefe daya suka zauna
A sannan ne suka sallami dakarun da suke cikin fadar tareda umartarsu dasu rufe kofofin .

A can kuwa dakin dasu farhan suke kwance ashe duk abindaya faru jarumi mufran ya gani da idanunsa tun lokacin da gimbiya huraisa ta shigo cikin dakin har zuwa lokacin data fita
Sakamakon rashin wadataccen barci da bai yi ba a daren
Don haka sai ya cika da mamaki akan dalilin zuwanta
Da kuma nuna tsantsar kulawarta da tayi akan farhan kadai
Yasan dole ruwa baya tsami banza akwai abinda take boyewa azuciyarta
Domin da ganin irin kallon da take masa kallone mai nuna tsantsar soyayya da shakuwa
Idan kuwa har haka ne to idan shi baya sonta tofa tabbas tana tareda wahala
Haka dai yayita sake sake azuciyarsa bai sani ba har barci ya sace shi
Kashe gari da sassafe bayan bayan sun tashi daga barci sunyi karin kumallon safe
Sai suka shirya Kamar yadda suka saba suka shiga bargar dawakai suka dauki wadanda suke hawa
Domin fita rangadi cikin dajin da suke farauta acikinsa,
A sannan ne suka lura da cewa mahaifinsu baya Cikin gidan mahaifiyarsu kuwa bata tashi daga barci ba
Don haka ba tareda bata lokaci ba suka fice daga gidan gaba daya
Sannu a hankali har suka fice daga cikin birnin gaba daya suka nausa cikin daji
Suna tafiya suna hira abinsu a sannan ne farhan ya tuna da cewa yau basu fito da gimbiya huraisa ba
Kawai sai yaja linzamin dokin sa yace da 'yan uwansa
Kash!!! Yau mun manta huraisa agida bamu jira ta ba idan har kuwa taje gida ta tarar Bama nan tabbas ba zata ji dadi ba
Kodajin haka sai suma suka ja linzaman dawakan su sukace kwarai kuwa ya kamata mu jirata anan
Ba tareda bata lokaci ba suka sami guri suka zauna
Kwatsam sai mufran ya tuna da al'amarin gimbiya huraisa don
Don haka ya katse shirun dake tsakaninsu tareda duban farhan yace Yakai dan uwana
Anya kuwa tsakaninka da gimbiya huraisa babu soyayya, a iya tsawon rayuwar da mukayi daku na dade ina lura da duk alakarku
Na fuskanci cewa Dukkanku kuna baiwa juna kulawa ta yadda har ba kwa iya jurar zama Tsawon lokaci ba tareda daya ba
Wadannan abubuwa basa faruwa sai ga wadanda suka yi zurfi acikin kogin soyayya
Anya kuwa babu soyayya atsakaninku?
Dajin wannan tambaya sai farhan yayi guntun murmushi sannan ya mike tsaye tareda juya musu baya yace
Tsakanina da huraisa Babu komai sai abota da kuma 'yan uwantaka
Ku sani na dauki huraisa ne Kamar yar uwata wacce muka fito ciki daya da ita
Zuciya kuwa tuni na mikata ga wacce zata zamo sarauniyar mata anan gaba
Wacce sunanta da kyawunta zai ratsa ko'ina cikin duniya kai ba mutane kadai ba har aljanu sai sun razana da kyawunta
Kyanta zai zama silar asarar dubunnan rayuka akarshe duk wanda ya mallaketa shine zai zama gagara badau kuma sarkin sarakai wannan shine kadai burina kuma wacce na mallakawa Zuciya ta
Saidai har yanzu wannan sarauniyar kyau ba'a haifeta ba amma tana daf da zuwa duniya
Kodajin wannan batu sai su safran suka tuntsure da dariya har suna nuna shi da yatsa suka ce
Kai kuwa a ina ka sami wannan tatsuniyar ina mai tabbatar maka Idan har mafarki kake ya kamata ka farka domin ba zai taba zama Gaskiya ba kada ka wahalar da rayuwarka

Kodajin haka sai shima ya mayar masu da martanin murmushi yace tabbas maganata gaskiya ce
Domin tun ina jariri acikin kwalbar sihiri naka mafarki da wannan yarinya bara na fara nuna muku fuskarta azahiri ku gani
Da gama fadin haka sai bude tafin hannunsa tareda karanta dalasiman tsafi
Faruwar hakan keda wuya take saiga hoton fuskar lasmira ta bayyana akan tafin hannun nasa
Koda ganin irin tsananin kyan da take dashi take duk su biyun suka kidime basu san sanda suka sunkuyar da kawunansu kasa ba suna kallon wannan kyakykyawar fuska tata
Alokacin ne suka ji kishi ya kama su tareda hassada sakamakon fuskantar da sukayi tabbas farhan akwai abinda ya fisu Sukaji Idan har basuyi da gaske ba nan gaba zai iya cika wannan buri nasa
Basu san lokacin da hankalinsu ya fita daga jikinsu Tareda sunkui da kawunansu kasa ba suna kallon ta
Suna cikin wannan haline wani rikakken sihirtaccen zaki ya lallabo ta bayansu kai tsaye ya kawowa farhan farmaki ta baya da nufin ya datse masa wuya
Girman zakin kadai yakai girman rikakken bujimin sa
Koda ya rage saura baifi kamu guda ba tsakaninsu
Kwatsam sai ga gimbiya huraisa ta falfalo da azababben gudu
Tana zuwa ta daka tsalle ta dira a gadon bayansa ta kama kansa da karfin tsiya ta matseshi a hammatarta
Aikuwa take kan zakin ya dagargaje ji kake rukukus kai an tauna kuli
Kwakwalwarsa gami da jini sukayi fallatsi ta wullar da mushensa a gefe guda
Cikin sauri suka jiyo bayansu kawai sai sukayi arba da gimbiya huraisa fuskarta cike da kwalla ashe duk hirar data wakana atsakaninsu taji
Har farhan ya bude baki da nufin yi mata magana saita dakatar dashi da hannu tace
Naji duk abinda ka fada
a halin yanzu na fahimci bani da gurbi acikin zuciyarka kuma na yarda tabbas Wannan yarinya zata bayyana anan gaba Wacce indai tana raye ba zan taba samun soyayyar ka

Ni kuma bazan bari wani ya shiga tsakaninmu ba saboda haka nima yanzu zan shiga duniya farautar ta a duk inda take
Daga yanzu ba zaku sake gani ba har sai na cika burina akanta
Amma ka sani har karshen rayuwata zuciyata ba zata taba rabuwa da soyayyar ka ba
Tana gama fadin haka take ta rikide ta zama haske shima hasken ya tarwatse cikin iska
Bacewarta keda wuya mufran sukaji alokaci guda sun kamu da soyayyar yarinyar da farhan ya nuna musu hotonta
Sukaga idan har suka riga farhan da huraisa mallakarta tabbas sune zasu zama gagara badau
Kuma a halin yanzu farhan shine kadai matsalar su ya zama dole suga bayansa da wuri
Da gama wannan zancen zuci take duk su biyun suka zare makamansu su kasa farhan a tsakiya da nufin hallakashi

SHIN SUNA SAMUN DAMAR HALLAKA FARHAN?
SHIN HURAISA TANA SAMUN NASA4AR RISKAR LASMIRA
YAYA HALIN DA ALJANI AMSADUR RAS YAKE CIKI?

DAGA NAKU
HABIBULLAH KBR

LIKE AND COMMENTSKARAGAR AJALI
5
++++++PART B

LBR
HABIBULLAH KBR

Ai kuwa kodayin wannan tunanin take cikin shammace mufran ya kaiwa farhan mahaukacin sara a dokin wuya da nufin ya tsinke masa wuya
saidai kai kafin ya kara wani yunkurin tuni safran ya gabza masa mahaukacin duka akan ruwan cikinsa da hannayensa guda biyu
wanda sabod karfin dukan sai dayayi baya taga taga yana layi kamar zai fadi
amma saboda juyiya sai ya zaro takobinsa ya cake ta akasa ba tareda ya yarda ya fadi ba a
lokaci guda duk su biyun suka afko masa suna kawo mai munanan hare hare ta ko ina da nufin su hallakashi yana karewa
da fari ya dauka abin nasu wasa ne amma koda ya lura da yanayin fuskokinsu da kuma irin harin da suke kawo masa sai ya tabbatar da cewa
wannan karon ransa suke bukata ya zama dole ya kare kansa
ai kuwa nan take ya kara kaime wajen fadan nasa
nanfa guri ya rincabe kura ta tashi ta turnuke sararin samaniya ta yadda daga nesa idan ka jiyo zaka dauka wasu manyan kasashen ne suke yaki
take suka hargitsa dajin gaba daya bishiyoyi suka dinga kakkaryewa suna faduwa kasa
WOHOHO HAKIKA JARUMTAKA DA KUMA JURIYA BAIWA CE
duk da kasancewar su safran sun saka farhan a tsakiya tareda hada karfi da karfe akansa
sai gashi sun kasa samun nasara ba don komai ba sai don tsananin juriya da kuma zafin naman da yake dasu
domin alokaci guda yake iya tare duk harin da suke kawo masa harma ya mayar da martani
al'amarin daya kara fusata su kenan don haka suka kara zage damtse akansa
wannan karon kuwa sai fada yasha banban
domin sai gashi a wannan karon har sun fara samun damar gabza masa naushi a kan fuskarsa
ta yadda har sai da idanuwansa suka rufe ya fara gani dishi dishi amma saboda bakin naci bai yarda ya yarda takobinsa kasa ba a haka yaci gaba da yakin dasu

acan kuwa al'amarin gimbiya huraisa lokacin data bace tabar su farhan a wannan daji
bayan tafiyarta sai taji zuciyarta tanata bugawa da karfin gaske
taji ajikinta dole akwai abinda zai iya faruwa ga farhan din
don haka ba shiri ta kara bacewa acikin iska
bata bayyana ba sai a inda tabar su farhan tana bayyana taga abinda yake faruwa
take zuciyarta ta fara tafarfasa kamar zata kone
nantake kuwa itama ta zare takobinta ta afka musu domin taimakon farhan
WOHOHO hakika idan kaga ana rabon fada na yara ne
idan manya ne kuwa sai dai a tsaya kallo daga nesa
domin kuwa ana fara wannan yaki take guri ya kara yamutsewa fiye da farko sautin karafkiyar makamai ya cika dodon kunne

kAICO HAKIKA IDAN SADAUKANTAKA TA HADU DA SADAUKANTAKA ABIN BAYA DADIN KALLO
kai saboda bala'in yadda suka dinga jifan junansu da sihiri kala daban daban saida takai dajin gaba daya ya fara girgiza tamkar kasa zata dare su rufta ciki

suna cikin wannan fafatawane kwatsam sai sukaji an daka musu tsawa alokaci guda wani haske ya fito ya daki kirazansu

nantake sukaji jikinsu yayi sanyi kamar an zare musu lakar jikinsu
suka kasa daga koda dan yatsansu bisa dole suka dakata da fadan da sukeyi

ba kowa bane yayi wannan aikinba face boka hushairul hasnal abayansa kuwa sarki suraif ne tareda attajiri zawwas fuskokinsu amurtuke babu alamar annuri

suka tsaya tsawon lokaci mai tsawo suna kallonsu ba tareda dayansu yace uffan ba

daga can sai hushairul hasnal ya dubesu cikin karayar zuciya kamar wanda zaiyi kuka daga bisani yace
hakika yau kun bani kun bamu kunya kuma kun karya babban shirin da muka jima munayi akanku

ku sani maganar da farhan ya fada akan lasmira gaskiyace
kuma duk wanda ya mallaketa shine zai iya mallakar KARAGAR AJALI
saidai kuma ba anan gizo yake sakar ba
domin neman karagar ajali daidai yake da mutum ya fita farautar mutuwarsa
kuma kafin takaika ga mallakarta dole sai anyi asarar dubunnan rayuka
saidai a halin yanzu ita kanta wannan yarinya ba'a haifeta ba
amma a cikin binciken da nayi na gano cewa tabbas a wannan rana za'a haifeta saidai kuma alkaluman tsafi zasu dinga bata kariya ta yadda babu wanda zai gano inda take
sai dai da zarar ta bayyana a take kowa zai sani

suna cikin wannan tattaunawa ne sukayi wo wata iska mai karfi tana kadawa asararin samaniya saboda karfin kadawarta sai da gashin kansu ya kwance ya fara yawo a cikin iska
take gaba daya suka daga kawunansu sama domin ganin meke faruwa
kawai sai sukayi arba da aljani amsadur ras a sama yana kokarin saukowa kasa amma bishiyoyin dake dajin sun hanashi sauka kasa saboda girman jikinsa
har saida boka hushairul hasnal ya tofa masa wasu dalasiman tsafi sannan jikinsa ya zama kamar haske ya iya sauka kasa
yana mai sujjada ga hushairul hasnal alokacinda ya kafe shi da idanu kamar yana nazari akansa
ta yadda sai da yaji zuciyarsa ta fara hugawa da sauri
kamar ace kyat ya saki fitsari a wando ya dauka asirinsa ne zai tonu

daga can kuma sai hushairul hasnal yace
ya kai amintaccen hadima
kai kuwa menene ya faru dakai kwana biyu banji motsinka ba ?
dajin wannan tambaya sai yayi caraf yace
ya shugabana dalili shine
awadannan kwanakin nayi tafiya ne zuwa can birnin mu na aljanu
wanda ke can bangon duniya domin kaiwa iyalina ziyara sakamakon haifa mini jariri da tayi amma ka gafarceni ya shugabana
irin haka ba zata kara kasancewa ba
koda yaji haka sai yayi murmushi yace
ba komai ina tayaka farincikin samun karuwa da kayi
da gama fadin haka ya sake juyawa inda su farhan suke yace anan ne zamu rabu daku
daga yanzu dagani har su zai yi wuya ku kara ganin daya daga cikin mu sai bayan mai rabo ya mallaki karagar ajali daga cikin ku
kuma a wannan lokaci bai zama lallai dukkanku ku dawo ku riske mu a raye ba
a sannan ne idanun mahaifansu suka fara zubda kwalla sakamakon tunawa da wasiyyar da boka surkais ya bar musu
al'amarin daya matukar karyar da zukatansu farhan kenan
suna cikin wannan hali ne kawai sai boka hushairul hasnal ya nunasu da sandar tsafinsa
aikuwa nan take wata iska mai karfi ta fito daga cikin sandar ta shuresu sama sannan ta tarwatsa su gabas, yamma, kudu da arewa

WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GASU FARHAN BAYAN AN TARWATSA SU CIKIN DUNIYA
++++++ +++++++ ++
can dakin tsafin boka surkais kuwa yaga duk abindaya faru tsakanin su sadauki farhan da 'yan uwansa tareda aljani amsadur ras ta cikin madubin tsafinsa
har zuwa sanda boka hushairul hasnal ya tarwatsasu duniya
koda ganin wannan al'amari take ya takarkare ya bushe da dariya mai kama da kukan jaki
wanda saboda rashin dadin dariyar saida amsadur ras ya sanya hannunsa ya toshe hancinsa
sai da yayi dariyar ta isheshi sannan ya tsuke bakinsa ga barin dariyar ya sunkuyar da kansa daidai fuskar amsadur ras yace
kagani da idonka yadda tarkona ya fara aiki akan iyayen gidanka?
tun daga yanzu matakin nasara ta zai fara gaba domin komai nasanya agabana sai na sami nasara
a kan karagar ajali zan iya hallaka kowa hatta mahaifina kuwa muddin zai tsaya agabana
dalili dayane ya hanani kasheshi tun a baya
wannan dalili kuwa shine ta hanyar jininsa dake gudana ajikina ne kadai zan iya riskar karagar ajali
da zarar kuwa ya mutu kafin na mallaketa take nima jinin jikina zai kone gaba daya na mutu
har sai na mallaketa sannan zan iya ganin bayansa kuma nima na rayuwa
farin cikina dayane da har yanzu babu wanda ya iya gane dan leken asiri na wanda yake tare dasu cikin siffarka

koda yazo daidai nan a zancensa sai amsadur ras yayi guntun murmushi mai kama dana mugunta daga bisani yace
indai kuwa haka ne kana yaudarar kanka
domin ina da yakinin baka san mahaifinka ba kamar yadda nasan shi kaidai kawai ka zuba ido kaga yadda zata kasance
da gama fadin haka sai ya sami guri a cikin kwalbar da yake kulle ya kishin gida
al'amarin daya matukar bata wa boka surkais rai kenan yaji kamar ya mitstsikeshi amma sai ya fasa ya mayar masa da martani da cewa

ni kuwa yanzu zan baka mamaki kuma ayanzu duk motsin da zasuyi zasuyi shine tamkar a tsafin hannu na
yana gama fadin haka saiya sai ya nuna bangon dakinsa da tafin hannunsa

take hoton sadauki farhan ya baiyana lokacin da wannan iskar ta shureshi bata sauke shi A ko ina ba sai cikin birnin farisa
a wannan lokaci safiyace rana bata take ba
amma sai ya iske garin ya cika makil da mutane sai hada hada sukeyi daga sassa daban daban
kuma mafi yawa daga mutanen da yake gani baki ne ba asalin 'yan birnin ba
dakaru kuwa an baje su a ko'ina sai tare baki suke suna bincikarsu don tabbatar da tsaro
amma wani abin mamaki kaf cikin dakarun babu wanda yayi yunkurin tunkararsa da sunan bincike
ba komai ne yasa hakan ba face yanayin kirar jikinsa da kuma tufafi masu tsadar da suke jikinsa
wanda suke nuna cewa dolene ya kasance dan kasaitaccen gida ko dai na sarauta ko kuma na attajirai
sannan kuma mafi yawa daga mutane suna dauka cewa shima yana daga cikin manema auren Sarauniya nauwaratul hasnal
su kuwa 'yan mata binsa sukeyi da kallo tamkar zasu hadiyeshi
wasunsu ma har faduwa sukeyi ba tareda sun sani ba
wannan cikowa daya gani ce ta tabbatar masa da cewa akwai wani abu da yake faruwa
don haka babu shiri ya janyo rawaninsa ya rufe fuskarsa idanunsa kadai ake iya gani
agadon bayansa kuwa takobinsa ce a rataye
yaci gaba da tafiya abinsa kamar dama can ya taba zuwa garin
ya nufi bangaren da yaga mutane sunfi durfafa don ganewa idonsa abinda yake faruwa
duk da kasancewar fuskarsa a rufe take hakan Bai Hana mutane binsa da kallo ba
a haka har ya isa tsakiyar garin inda ya iske dubunnan mutane sunyi cincirindo a wani katon fili
mazansu da matansu yara da manya Babu masaka tsinke
gurin ya cika da hayaniya Kai kace ba iya mutane bane kadai a gurin harda aljanu
kuma har a sannan mutane basu gama hallara ba
ba tareda bata lokaci ba ya dinga ratsawa ta cikin mutane yana dada kutsawa har ya isa karshen filin
anan ne ya isa bakin wani katon rami mai matukar fadi wanda agefunansa akayi masa ganuwa da katangun karfe daga karshen ramin kuwa a gefe guda wata katuwar koface mai matukar kauri wacce aka sana'anta ta da zallan bakin karfe
daga daya hannun kuwa wasu matasa ne majiya karfi guda ashirin wadanda suka fito daga sassa daban daban na nahiyar sun tsaya a tsaye sai hura hanci suke hannayensu ruke da muggan makamai kamar zasu ci babu
acan saman wannan fili kuwa Sarauniya Nauwaratul hasnal ce a zaune bisa karagar mulkinta wacce aka kerata da zallan zinare sannan akai mata ado da lu'u lu'u
ta caba kwalliya mai matukar kyau wacce kan iya zautar da mai kallonta
bayan ta danyi shiru na wasu dakiku tana mai karewa al'ummar filin kallo daya bayan daya duk da tsananin yawansu sai gashi tana iya kallonsu daya bayan daya saboda karfin sihirinta
kai harma tana iya karanta abinda dake zuciyar kowanne daga cikin su
farhan ne kadai ta kasa ganeshi da kuma abindake tafe dashi
bayan ta gama nazari akan su ta mike tsaye ta fara jawabi kamar haka

yaku jama'ar birnin farisa da makobtaka kamar yadda kuka sani
wannan itace ranar da aka warewa masu neman aurena domin gudanar da gagarumar gasar aurena wacce ba'a taba yin kwatankwacinta ba
acikin wannan gari
domin a wannan karon kofa a bude take ga duk wanda yake da burin aurena ko a ina yake kuma komai talaucinsa idan har yayi nasarar wannan gasa
a take a nan gurin za'a daura mana aure dashi kuma shine wanda zai ci gaba da mulkin wannan birni har bayan mutuwa ta
don haka yanzu duk wanda yake da sha'awar aurena zai iya fitowa cikin wadannan jaruman gasa domin gwada sa'ar sa
amma fa kusani bayan wuya sai dadi kuma faduwar gaba a sarar namiji ne
sannan har abada matsoraci baya taba zama gwani
koda tazo daidai nan a zancenta take gurin ya kara cika da hayaniya fiye da ffark kowa yana fadin albarkacin bakinsa
anan ne fa hankalin mazaje ya tashi zukatansu suka kufulo sakamakon daular da sukaji an ambata
ba shiri masu mafarkin tara dukiya a dare daya suka fara fitowa daga inda suke suna shiga cikin jaruman gasa wasun suma basu taba fita koda filin yaki ba amma saboda yaudarar kai suka dinga shiga cikin filin
mata kuwa suka dinga nadamar kasancewar su mata da basu zo a mazaje ba
bayan kowa ya iya wadanda zasu shiga gasar sun gama shiga filin
anan ne dakaru suka janye matattakalar shiga filin gasar da wata katuwar kugiya
sannan nauwaratul hasnal tayiwa wani badakare inkiya da idanunta
aikuwa take ya kada wata katuwar kararrawa wacce sautinta ya ratsa birnin gaba daya harda ma dajijjikan dake iyaka dashi
ba tareda bata lokaci ba wasu karatan dakaru suka fara aikin zare wasu
manyan sakatu wadanda suke jikin wannan kofar da take rufe acikin ramin
saboda nauyin sakatun sai da suka jike sharkaf da Gumi kamar wadanda aka tsoma acikin kogi

sakatun na zarewa ne wannan katuwar kofa ta bude wani irin tururi da hayaki suka fara dannowa daga cikin ta
kai kace ana aza wuta a makera
ahankali turrurin yaci gaba da fitowa daga ciki har ya zamana babu shi amma babu wani abu daya fito

har aka shafe wasu dakiku masu yawa wannan ne yasa mutane suka kagu da jira
don haka wani mai xafin zuciya daga cikin jaruman gasar ya zare takobinsa tareda durfafar dakin
da nufin fito da abinda yake cikinsa koda ya danna kansa cikin dakin take aka feshi da wani ruwa mai yauki
nantake naman jikinsa ya zagwanye kashushuwansa suka zube a kasa
wani gurnani ya fito daga dakin
sannu a hankali sai ga wata katuwar halitta mai matukar muni ta fito daga cikin kogon
koda mutane sukayi arba da wannan shirgegiyar halittar take suka rikice suka hau kace nace akan wannan halittar sakamakon ganin tsananin munin da take dashi
itadai wannan halittar ta kasance mai matukar muni
da kuma karfin gaske fatar kamar dutse sannan hakoranta suna da matukar tsini kai kace kibiyoyi aka jera

har shenta kuwa yana da matukar tsawo kuma
akoda yaushe yakan karawa kansa tsayi domin farautar abinda yake hari
da zarar ta wangame bakinta sai dai kaga wani ruwa mai matukar dafi yana tsartuwa daga bakinta

ai kuwa yayinda jaruman gasar sukayi arba da wannan halitta take wasu daga cikin su suka fara nadamar shiga cikinta saboda tabbacin ba zasu fita a raye ba

wadanda kuwa basu shiga ba murna ta kamasu da farinciki
yayinda wannan halitta ta kyallara ido taga mutanen dake gabanta
take ta mika dogon harshenta sai gashi ta damko mutum sha biyar daga jaruman gasar alokaci guda ta taunesu
koda ganin wannan abu take ragowar jaruman gasar sukayi kukan kura alokaci guda suna masu karaji da kururuwa suka afka mata
aka ruguntsume da a zababben yaki take kura ta turnuke

Please Login or Register in order to submit comment