Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsufa zan iyayin abinda matashin jarumi dan shekara ashirin da takwas ma bai zama lallai ya iya ba.
Yanzu dai Badon komai na kiraka ba face na sanar dakai cewa daga yau kabar bauta a karkashi na
Ka koma hannun wadannan yaran
Kawai sai yayi nuni da hannunsa zuwa su farhan sannan yaci gaba da cewa
Daga nan ina so ka daukesu Gaba daya Daga su har iyayensu zuwa birnin romaniya ka sadasu da aminina wato barde Ukairu
Ka sanar dashi cewa wadannan sune yaran da nayi masa alkawarin kawosu domin ya basu kyakykyawan horon yaki
.
Wannan shine umarni na na karshe a gareka sai mun sake saduwa yana gama fadin haka saiya juya musu baya ya kama tafiya,
Juyawarsa keda wuya sai suka ga wani bakin hayaki ya lullubeshi gaba daya sun dena ganinsa, koda daukewar hayakin sai suka nemeshi suka rasa ya bace bat
Da ganin haka ba tareda bata lokaci ba take aljani Amsadur ras ya sa hannunsa guda daya ya shuri su sarki suraif tareda su jawwas ya dora su A gadon bayansa mai kama da katon tsauni
Sannan ya bude manyan fuka fukansa ya tashi sama dasu Cikin azababben gudu
Aikuwa suna fara wannan tafiya ne sarki suraif ya raina karfin gudun da hadimin aljaninsa yake dashi
Domin kuwa Amsadur ras ya ninkashi fiye da sau ashirin, cikin kankanin lokaci yake shafe tafiyar kwanaki
Idan kuwa yazo giftawa ta saman gari ko inuwarsa basa iya gani saidai aji karfin iskar fuka fukansa
Jawwas bai san sanda zancen zuci yazo masa ba yace
Oh! Dama a duniya akwai halitta mai irin wannan karfin gudun adoron kasa
Dajin wannan tambaya sai suraif yace ai idan kana raye a duniya babu abinda b zaka gani ba
Nima kaina nayi mamakin wannan al'amari amma da alama abin al'ajabi yana gaba bamu fara ganinsa ba…..
Kafin ya gama zancen da yakeyi sai suka ga ya rage karfin gudun nasa
A sannan ne suka lura sunzo iyakar birnin romaniya don haka babu shiri Amsadur ras ya saki fuka fukansa ya sauko kasa ya dire su bisa turba
Yace ba Zamu iya ketarewa ta saman wannan gari ba dolene mu ratsa ta kofarsa idan har muna son shiga
Dajin wannan batu sai suraif ya dubeshi cikin mamaki yace ai kuwa kana da ikon shiga cikinsa yadda kake da wannan karfi da kuma girman jiki, ko ta dole zasu barka ka. Shiga

Kodajin wannan tambaya sai ya tuntsure da dariya daga bisani yace
Lallai baka san mutanen birnin romaniya ba ka sani Wannan birni shi akewa kirari da kodame kazo an fika, ma'ana duk jarumtaka, tsafi ko kuma dukiyar da kake takama da ita idan har ka shigo birnin nan
Sai ka sami wanda ya dame ka ya shanye duk girman nan nawa da kuke gani idan har nace zan ratsa da karfin tsiya na shiga cikin sa to saidai wani bani ba,
Abayama da nake shiga ina shigane albarkacin boka Hushairul hasnal
Yanzu kuwa na koma karkashinku don haka kune zaku shigar dani cikinsa
Yana gama fadin haka saiya rikide ya koma siffar bakin bawa janye da keken doki cike da tarin dukiya aciki
Sannan wasu dawakai guda shida shida suka bayyana agabansu
Tareda wasu dakaru kimanin su dari uku abayansu
Ba tareda bata lokaci ba suka haye kan dawakan Sannan suka nufi birnin romaniya
Da isarsu kofar garin sai suka kwankwasa kofa,
Wani badakare ya leko ta cikin taga Tareda tambayarsu su waye ku kuma meke tafe daku?
Dajin wannan tambaya sai sarki suraif ya tari bakinsa yace
Nine sarki suraif na birnin sin kuma ina tareda attajiri jawwas ba Komai ne ya biyo damu ta birnin nan ba face kasuwanci
Kodajin wannan batu sai badakaren ya fito da kansa ya duba kayayyakin da suka zo dasu
Ya tabbatar da cewa babu wani abin cutarwa aciki
Kawai sai ya yiwa dakarun nuni dasu bude musu kofa ,
Ba tareda bata lokaci suka kutsa kansu cikin garin
Suna shiga Cikin birnin suka cika da mamaki sakamakon ganin yanayin mutanen garin
Gabza gabza masu kirar mutanen farko kuma Dukkansu jikinsu a mummurde yake mazansu da matansu
Ko'ina ka kewaya acikinsa babu abinda mutane sukeyi face baiwa kansu horon yaki
Yayinda zakaga yaro karami yana ta faman naushin katon dutse da hannunsa
Ba taredaya gaji ba har sai dutsen ya dagargaje ya zama gari
Wani kuwa sai Kaga ya shuri katuwar giwa ya dagata sama yayi hajijiya da ita sannan ya wullar da ita
Basu farga har suka isa kofar gidan barde Ukairu inda nan ne babban gurin horar da jarumai
Tun daga nesa barde Ukairu ya kura musu idanu yana nazarinsu
Har suka karaso cikin rumfar da yake zaune, da isowarsu kafin aljani Amsadur ras yayi bayani tuni ya tari numfashinsa da cewa
Barka da zuwa Amsadur ras Tareda manyan baki ai tuni boka Hushairul hasnal ya sanar dani zuwanku
Amma kafin nan inaso ka debe min wadannan dakarun iskar dake bayanku
Dajin haka sai ya juya ya kalle su da idanunsa take dukkaninsu har da keken dokin da yake kai suka ruburbushe suka zama kasa
Ba tareda bata lokaci ba barde Ukairu ya umarci wata kuyangarsa data je ta kawowa su jawwas abinci
Nan da nan kuwa ta tafi Bayan dakiku kadan ta dawo dauke da abinci na alfarma ta ajiye agabansu. Sannan ta juya ta tafi ta basu
Barde Ukairu ya nuna musu abincin tare da yi musu bismillah
Aikuwa take suka zauna suka bude cikinsu sukayita dankarar abinci
Bayan sunci sun sha ne barde Ukairu yace yanzu zamu fara abinda ya kawo ku
Tun daga wannan rana aka fara baiwa su safran horon yaki tun daga matakin farko
Wanda al'amarinsu saida ya baiwa iyayensu mamaki sakamakon ganin yadda komai aka koya musu take yake zama acikin kwakwalwarsu
Arana ta biyune su jawwas suka koma gidajensu suka bar su farhan a wannan makaranta
Dare da rana babu abinda suke yi face karbar horo mai tsanani
Wani babban abin mamakin ma daga garesu shine yadda suke iya karbar horon da cikakken gardi ne yake iya dauka a matsayinsu na yara
Duk karfin dukan da akayi musu take suke shanye shi kamar ba jikinsu aka daka ba
Tun suna dukan duwatsu da hannayensu suna ruburbushewa sai ya zamana sun daina amfani dashi an koma ajiye musu dunkulallen bakin karfe agabansu da zarar kuwa sun dakeshi saidai Kaga ya lotse da kansa kamar sun daki busashshen ganye

Afannin gudu kuwa Ana daukar sune akai su can wani daji wanda gaba dayansa babu komai aciki face dankararren tabo wanda sai mutum yayi tafiyar wata guda sannan zai kure shi
Acan za'a ajiyesu adora musu buhun duwatsu akansu suyita gudu acikinsa
Tun safe har dare ba tareda tsayawa hutawa ko cin abinci ba tun sunayi suna faduwa sai daya zamana suna iya shafe wannan tafiyar acikin yini uku kacal kuma su dawo gida

Wannan al'amari nasu ba karamin baiwa Ukairu mamaki yake ba domin bai taba ganin yara masu juriyar wahala kamarsu ba
Wani lokacin kuwa katti za'a samu suyita dukan su da manyan itatuwa har sai sun kakkarye ajikinsu
Shi kansa uzairu da farko saidaya dinga tausaya musu amma daga baya daya fuskanci kashinsu ba irin na kowa bane sai ya daina tausayin nasu
Ya zamana har yana basu horon da shi kansa ba'a bashi mai wahalar sa , acikin gwagwarmayar rayuwa ya koyesu

Kai a takaice dai Cikin 'yan satittika suka gama karbar horon yaki
Anan ne aka soma jarraba horon nasu da manyan dakarun Ukairu
Su ashirin wadanda suka kasance gabza gabzan mazaje masu dakawa maza gumba a hannu
Anyi ittifakin a gaba daya birnin babu manyan mayaka kamarsu
Bayan anyi gasarne su farhan suka sami nasara akan dakarun
Saboda Hakane Ukairu ya kira aljani Amsadur ras gefe yace
Yakai wannan hadimi ka sani a halin yanzu wadannan yaran sun karbi gagarumin horon da koda duniya sukayi nufin yaka ina da tabbacin zasu sami nasara
Ba don komai ba sai Domin juriyar da nacin da suke da su
Kuma babu irin masifar da zasu shiga su kasa kubuta
Amma kuma hakan ba zata taba yiwuwa ba face sun hade kansu guri daya kuma bisa jagorancin karamin cikinsu wato farhan
Domin duk da kasancewarsa karami amma na fuskanci dukkansu ya fisu juriyar wahala, zafin nama, sa'a da kuma kaifin kwakwalwa
Wadannan kuwa sune matakan nasara arayuwa, abinda nake guje musu kuwa shine rabuwar kai idan har kawunansu suka rabu to duk wannan horon da suka karba zai iya zama na banza
Ba don komai nake fada maka haka ba face don kasan lokacin sallamar su yayi su koma gurin iyayensu da zama

, ka sanar dasu Jawwas cewa ya zama dole subi shawarar da aminina Hushairul hasnal ya basu idan har sunaso 'ya yansu su yi nasara a rayuwar su
Kodajin haka saiya tashi ya je inda su farhan suke ya dan yi musu bayani daga baya yayi musu sallama
Sannan aljani Amsadur ras ya daukesu ya mai dasu birnin sin
Daga ranar da suka koma birnin sin suka fara rayuwa cikin jin dadi, kuma suka kara zamewa birnin garkuwa daga abokan Gaba
Sai da ya zamana cewa gaba daya biranen dake cikin nahiyar sun dawo karkashin masarautar sin
Komai yawan dakarun da abokan Gaba suka fito dasu su farhan kawai ake tura musu su fatattake su da karfin tsiya
Su jijjige kofar birnin su fito da sarkinsu
Idan kuwa suna gudu kai kace ba akan kasa suke tafiya ba domin gani zakiyi har tashi sama sukeyi saboda karfin gudun
Haka kuma suna iya shafe kwanaki suna yaki ba tareda sun gaji ko kuma sun bukaci abinci ba
Komai yawan dakarun dake gabansu sai sun fatattakasu ,
Cikin kankanin lokaci sunansu ya karade duniya
Ya zamana kowanne sarki yana fargabar ranar da zasu sauka agarinsa
Don haka a duk karshen wata suke yin hawa da kansu su zo birnin sin su kawowa sarki suraif da jawwas dukiya mai tarin yawa tare kuma dayi musu biyayya ba don komai ba sai don su tsira da mutuncin su
Kai Bama mutane kadai ba hatta manyan dabbobin daji da aljanu sunyi matukar razana da bayyanar wadannan jarumai domin har lakabi sukeyi musu da TAWAGAR AJALI

Duk wani hatsabibin dan fashi ko kuma aljani bisa dole suka dinga yin kaura daga nahiyar sin zuwa wasu nahiyoyin daban
A kwana a tashi sai da suka shafe shekaru uku ba tareda an bar su sunyi abokai mata ba
Domin kaucewa tuggun boka hulbaz kai ko inda suke ma mata basa zuwa
Tsawon wadannan shekaru sai shakuwa ta shiga Tsakanin su ya zamana akafi yaushe suna tare
Musamman ma farhan da Husnaila sune abotarsu ta fi karfi fiye da sauran
Harma ta bangaren Husnaila ta fara kokarin juyewa zuwa soyayya azuciyarta
Ba tareda wani ya lura da hakan ba hatta mahaifan nasu
Akullum idan suka fito motsa jiki babu abinda takeyi face satar kallonsa
Akwai Wani lokaci da farhan tare dasu safran ke kwance acikin turakarsu suna barci
A wannan dare Husnaila taji ba zata iya kwanciya barci ba tareda ta kara kallon fuskarsa ba
Don haka a wannan daren ta tashi ta fita daga gidan sarautar ta kama hanyar zuwa gidan Jawwas inda anan ne dakin su mufran yake
Duk inda tazo ta gifta a wannan dare babu badakaren da yake kokarin tsaida ita
Domin babu wanda Baisan dokin da take hawaba cikin kankanin lokaci ta fara hango katangar gidan attajiri jawwas
Don haka saita sauka daga kan dokin ta barshi a tsaye. A gurin sannan ita ta falfala da gudu ta bayan gidan a wannan lokaci hankalin dakarun dake tsaron gidan gaba daya ya tattara a kofar gidan
Tana isa daf da katangar gidan saita daka tsallebdaga Inda take sai gata ta tashi sama kamar tsuntsuwa ta sauka a saman katangar
Duk da cewa Tsawon katangar yakai taku dari da hamsin da doriya
Taci gaba da tafiya cikin azababben gudu akan katangar ba tareda wani ya ankara da ita ba
Kasancewar ta san kan gidan kai tsaye ta wuce Cikin dakin dasu farhan suke kwance
Da isarta sai ta ratsa ta cikin ginin katangar dakin ta shige ciki
Kai tsaye ta wuce inda farhan ke kwance ta tsaya akansa tana kallon fuskarsa tana yin murmushi afuskarta
Bata san sanda ta fara yi masa baitocin soyayya ba tareda ta sani ba
Harta kai hannunta da nufin shafa kan fuskarsa
Sai zuciyarta ta buga da karfi
Tace kul karki kuskura ki fara nuna masa abinda ke cikin zuciyarki ki bari shi ya fito ya furta miki Domin tabbas yana sonki kuma yana kaunarki kawai dai ki jira lokaci
Haka dai ta zauna tana kallonsa bata sani ba har dare ya raba
Kodata ankara sai tayi wuf ta mike zumbur ta fice daga dakin domin komawa gida tana tafiya tana waiwayensa

Saidai kash duk wannan abu daya faru ya farune akan idanun aljani Amsadur ras
Yaganta tun daga lokacin data shigo cikin dakin da duk abubuwanda suka faru
Aikuwa koda gama ganin wannan al'amari sai yaji zuciyarsa ta buga kamar zata faso kirjinsa ta fito waje
Ya tuna da maganar boka Hushairul hasnal da kuma barde Ukairu cewa macece zata iya tarwatsa musu rayuwa da kuma burinsu
Idan kuwa har Hakane to tabbas hanasu tarayya da mata da akayi kamar an kashe maciji ne ba'a sare kansa ba
Tabbas Husnaila ce Wannan mace da ake gudun tarayyarsu da ita
Ya zama dole kafin lamari ya baci yayi gaggawar zuwa ya sanar da boka Hushairul hasnal domin a dauki kyakykyawan mataki akan hakan
Aikuwa da gama wannan tunani sai take ya bude fuka fukansa da nufin yaje ya sanar da Hushairul hasnal halin da ake ciki

SHIN YANA SAMUN DAMAR SANAR SANAR DA BOKA HUSHAIRUL HASNAL?
YAYA SOYAYYAR FARHAN DA HUSNAILA ZATA KASANCE ?

KUMA WANNE IRIN SHIRI BOKA HULBAZ YAKEYI AKANSU?

DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI. MU HADU A KASHI NA GABA
DAGA NAKU HABIBULLAH KBR

LIKE AND COMMENTS

KARAGAR AJALI

5 PART
A

LBR

HABIBULLAH KBR

Lokacin da aljani Amsadur ras ya bude manyan fuka fukansa ya tashi sama da nufin yaje ya sanar da boka Hushairul hasnal halin da ake ciki sai yayi ta tsala gudu a saman iska kai kace duniyar zai bari gaba daya
Yana cikin wannan azababben gudu ne kwatsam akan hanyar sa
Sai yayi kicibus da hadimin boka hulbaz wato aljani Ragazalu
A tsaye a saman iska tareda wasu dakarun aljanu masu dumbin yawa abayansa sun tare hanyar sa ta zuwa kogon boka Hushairul hasnal
Tsakanin aljani Amsadur ras da ragazalu akwai gaba mai tsanani tun suna yara
Wannan ne yasa a duk lokacin da suka hadu sai sun fafata kazamin yaki atsakaninsu
Koda yin arba da wadannan dakaru sai yayi turjiya a sama tareda gyara tsayuwarsa
Alokacin ne Ragazalu ya ratso ta cikin dakarun ya fito gaba yana fuskantar Hushairul hasnal yace
Yakai abokin gaba a wannan ranar baka isa ka kubuta daga hannuna ba, don haka yanzu kana da zabi guda uku

Na farko Ina mai umartarka daka mika wuya agaremu cikin sauki mu mika ka ga mai girma boka hulbaz kamar yadda ya umarce mu
ko kuma ka koma da baya tareda alkawarin ba zaka sanar da Hushairul hasnal abinda ka gani ba
Na karshe kuwa shine kana da damar da zaka yake mu Idan har kayi nasara shikenan zaka iya tafiya kaje ka yi abinda kaga dama ,
Ammafa ka sani idan har muka sami nasara Zamu kamaka ne da karfin tsiya mu mika ka gurinsa
Dajin wannan batu sai ya tuntsure da dariya yayi ta kyalkyalawa kamar ba zai daina ba
Daga can sai ya murtuke fuska kai kace an aiko masa da sakon mutuwa
Kawai sai ya nuna Ragazalu da yatsa yace karyarka tasha karya
Daga kai har kananan dakarunka baku isa ku iya dakatar dani daga abinda na sa agabana ba
Kuma daga kai har mai gidan naka karshen ku yana nan zuwa a kusa
Kaidai ina mai bakin cikin sanar dakai cewa yanzu karshenka yazo ba zaka taba iya kaucewa daga hannuna ba Idan kaga ka bar nan to gawarkace
Don haka ka shirya maza bisa kanka Koda gama fadin haka saiya zare shafceciyar takobin sa Yana mai karaji da kururuwa ya afka izuwa kan dakarun
Koda ganin haka take sai suma dakarun suka falfala da gudu kansa
Suna haduwa a saman iska suka kachame da azababben yaki
Nanfa suka yi masa rubdugu ta ko'ina suka yanyameshi suna wani karaji da gurnani mara dadin sauraro tareda kai masa sara da suka tako ina da nufin suyi masa kwaf daya
Ai kuwa yana shiga tsakiyar su sai ya dinga karaji Yana kai musu sara da suka tako'ina
Duk inda ya mika hannunsa saidai Kaga kawunan dakarun suna zubewa kasa
Nanfa kasuwar rayuka ta bude sassan jiki suka soma yawo a sararin samaniya tareda kwaranyar jini
Jini ya dinga fallatsi yana yawo a sararin sama sannan ya kwaranya akan kasa
Sai gashi shi kadai ya zame masu alakakai sun kasa koda taba shi kuwa duk inda ya durfafa saidai Kaga sassan jikinsu suna barin gangar jikinsu
Tareda feshin jini kamar an bude magudanar ruwa, inda ace akwai mutum a tsaye akasan inda suke wannan bakin artabun sai yayi zaton ruwan jini akeyi a Maimakon ruwan sama sai dai idan ya soma ganin sassan jiki suna zubowa kasan
Sai gashi shi kadai ya zame masu alakakai duk da yawan nasu ya zamo na banza, cikin kankanin lokaci ya zubar dasu kasa ya zamana babu saura face Ragazalu
Koda aljani ragazalu yaga abindaya faru saiya takarkare ya kwarara uban ihu
Wanda saboda tsananin fusatar da yayi sai ga tartsatsin wuta yana fita ta tsakankanin hakoransa
Jikinsa ya fara kyarma idanunsa suka kada sukayi jawur kai kace garwashin wuta ne acikin kwayar idon nasa
Kawai sai ya falfalo da gudu zuwa kan aljani Amsadur ras yana zuwa daidai inda yake sai ya kawo masa wani mummunan sara da nufin ya datse masa kansa
Nantake cikin bakin zafin nama ya sunkuya takobin ta sari iska sannan shima ya kai masa wani saran domin maida martani
Koda takubban nasu suka hadu take wani tartsatsin wuta ya tashi sama sannan wutar ta dunkule ta sauko kasa
Tana sauka akan wata katuwar bishiya take bishiyar ta kama da wuta ta kone kurmus duka bai wuce Cikin dakiku biyu ba
Lokacin dasu ragazalu da Amsadur ras suka kachame da azababben yaki sai gashi suna kaiwa junansu
Mugayen hare hare Cikin tsananin juriya da bajinta kai kace jikinsu bana jini da tsoka bane da duwatsu aka sassaka su
Nanfa sarararin samaniya ta rikice sakamakon gumurzun da suke aka dinga dinga wata karamar walkiya saboda haduwar makaman dake guri
Saiga fadan nasu ya zama abin sha'awa kuma abin tsoro sakamakon yadda ya kazanta
Nanfa suka hargitsa gaba daya dajijjikan da suke kasansu bishiyoyi suka dinga konewa kurmus dabbobi kuwa suka kama guje Domin neman tsira saidai kash!!
Agarin gudun nasu ne suka dinga fadawa cikin wutar da kuma ramuka marasa mafaka suna mutuwa aciki
Saida suka shafe sa'o'i masu yawa suna wannan bakin artabun an rasa wanda zai sami nasara atsakaninsu domin alamu sun nuna cewa karfi yazo daya
Kuma ba tareda wani ya sami nasarar koda lakutar jikin daya ba
A sannan ne wata dabara ta fadowa Amsadur ras don haka take ya canja salon yaki
Ya koma zulle zulle tareda kai masa farmaki ta sama da kasa cikin mahaukacin zafin nama tareda wani sabon salon yaki wanda shi Ragazalu bai san dashi ba
Ai kuwa yana fara wannan salo take ya rikita shi da mugayen hare hare
Ya kasa kokarin mai da martani sai yunkurin kare kansa kawai yake
Wannan ne ya baiwa Amsadur ras damar rikita masa tunani tareda toshe masa kofofin tsira
Cikin kankanin lokaci ya dinga dankara masa sara da suka jini yana zuba ajikinsa
Saboda zafin saran har kwalla ihu yake ba tareda ya sani ba
Nanfa hankalinsa ya dugunzuma ya dimauce ya fara kokarin guduwa alokacin da yaji jiri yana dibansa yana layi zai fadi saboda jinin daya zuba jikinsa
Koda Amsadur ras ya gano nufinsa sai ya shammace shi
Kafin ya gudun ya caka masa takobinsa a idonsa saboda karfin sukan saida takobin ta fasa idon ta bullo ta keyarsa Jini yayi tsartuwa daga cikin idon nasa
Take ya kama da wuta ya kone kurmus, tokar ta tashi tabi iska
Da gama samun wannan nasara sai ya goge jinin jikin takobinsa tareda mai da ita cikin kufe
Har ya kama hanya zaici gaba da tafiyarsa kwatsam sai yayi boka hulbaz ya bayyana agabansa
Kafin yayi wani yunkuri tuni ya jefo masa wata murtukekiyar sarkar tsafi ta kanannadeshi
Saboda karfin matsar da tayi masa saidata matse jikinsa ya kankance ya koma kamar girman kwado
Take Boka hulbaz ya fito da wata karamar kwalbar sihiri ya budeta
Nantake wata iska mai karfi ta fito daga cikin kwalbar ta zuke aljani Amsadur ras zuwa ciki
Sannan ta kulle kanta ta koma hannun hulbaz shi kuwa ya jefata ta cikin aljihu suka bace gaba daya
Basu bayyana ako'ina ba sai cikin kogon tsafin sa, da bayyanar sa sai ya fito da kwalbar da Amsadur ras yake ciki ya ajiyeta akan wani teburi
Ya tsaya ya kura masa idanu yana nazari tareda murmushi daga can sai kuma ya kyalkyale da dariya yace
Hakika ka tabka babban kuskure
Da har kake son shiga tsakanina da mahaifina amma Yanzu karshenka yazo baka isa ka iya fita daga cikin kwalbar nan ba aciki zan ta gana maka a zaba har sai ka mutu.
Amma kafin nan Zanso na karasa aikin dake gabanka, na kai sakon daka dauko ka kaiwa Hushairul hasnal da kuma ci gaba da yiwa su farhan hidima, duka inaso kagani da idanunka har zuwa sanda zan ga bayansu gaba daya
Ammafa kada kayi tunanin sakon da zaka kaiwa mahaifina shi za'a fada masa
Domin Idan kida ya canza dole ne rawa ma ta canja,
Yanzu take zan tura hadimina garesu a matsayinka Yaci gaba da hidimar da kake yi musu
Amma fa shi babu abinda zai dingayi musu face cin amanarsu da kuma raba kawunansu
Kaga kenan kota halin kaka burina zai cika kamar yadda na tsara ba tareda ya rushe ba
Yana gama fadin haka saiya takarkare ya fara karanta wasu dalasiman tsafi afili cikin daga murya
Aikuwa Faruwar hakan keda wuya sai kasa ta tsage da kanta
Wani Shirgegen mummunan bakin aljani ya ratso ta cikinta ya fito
Hakika da ace za'a ajiye wannan aljani atsakiyar mutane ba tareda ya cutar dasu ba ma ba zasu iya jure kallonsa ba Domin kallon sa kadai ya isa ya iya juyar musu da tunani koma ya janyo rasa rayukansu Gaba daya saboda munin da yake dashi
Koda bayyanarsa sai ya sunkuyar da kansa kasa cikin girmamawa yace ya shugabana na iso wacce bukatace dakai ka gaggauta sanar dani na biyama
Dajin wannan batu sai yayi masa nuni da Amsadur ras yace
Ya kai Ru'uzal inaso ne Yanzu ka rikide ka koma siffar sa
Sannan kaje ka ci gaba da aikin da yakeyi bisa umarni na

Yana jin wannan umarni sai yayi shiru Yana nazari daga can kuma sai ya dago yace ya shugabana ka sani Wannan aiki daka bani yafi kowanne aiki wuya domin kama da wane bata wane
Da wuri asirin mu zai iya tonuwa, dajin haka sai ya tuntsure da dariya daga can kuma sai yace
Kada ka damu da wannan domin hatta kwakwalwarsa sai mun kwaikwayi irin tasa an dasa maka ita acikin kokon kanka
Yana gama fadin haka saiya nuna shi da yatsa tareda karanta alkaluman tsafi
Faruwar hakan keda wuya sai shima ya kankance ya koma daidai girman da aka maida Amsadur ras ya sanya shi acikin wata kwalbar daban
Sannan ya bude kan Amsadur ras ya ciro kwakwalwarsa ya musanyata data aljani ru'uzal
Daga bisani a hankali Wani jan hayaki ya dinga fita daga cikin kwalbar da ru'uzal yake ciki
Koda gama fitar hayakin sai ya tattare aguri daya ya dunkule ya koma siffar Amsadur ras sak babu banbanci, ta yadda komai kallon kurullan mutum bai isa ya gane bashi ne ba
Shi kansa Amsadur ras sai da yayi matukar mamakin wannan al'amari amma daya tuna cewa lamari ne na tsafi sai ya daina mamakin da yakeyi
Ba tareda bata lokaci ba aljani Ru'uzal ya bude fuka fukansa ya tashi sama tareda yiwa maigidansa sallama don cika umarninsa

WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GA ALJANI AMSADUR RAS BAYAN YA FADA TARKON BOKA HULBAZ
++++ ++++++ +++++++
Acan birnin sin kuwa bayan gimbiya huraisa ta koma cikin turakar ta
Ta kwanta sai barci ya gagari idanunta ta kwanta da tarin sake sake a sannan ta gane tana matukar kaunar farhan a zuciyarta
Saboda haka ya zama tilas ta sanar dashi halin da take ciki tun kafin ta makara
Haka dai tayita sake sake azuciyarta har barci ya sace ta
Kashe gari tun da duku dukun safiya ta farka daga barcin da take
Tana farkawa ta tashi ta shiga makewayi ta biya bukata sannan ta watsa ,
Daga makewayin saita wuce zuwa dakin kwalliyarta ta caba kwalliya irin wacce bata taba yin kamarta ba
Sannan ta dauko wata doguwar riga mai launin kore da ratsin zinare ta sanya ajikinta
Hakika rigar tayi matukar yi mata kyau da kuma tsayawa ajikinta
Gashin kanta kuwa ta ware shi ya zuba agadon bayanta har zuwa kasan mazaunanta
Kai a wannan lokaci babu wani namiji da zai yi

Please Login or Register in order to submit comment