Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta fada haka
al'amarin ya kasance domin kullum sai ta
taimakawa bako ya taka sawayensa. Tun yana
yi da kyar da ciza lebe, har ma ya zo ya daina
dogara sanda ya fara tafiya tatata, tamkar
kankanin yaro mai koyon tafiya. A hankali
kafafunsa suka warke sarai ya zamana yana iya
tafiya sosai. A ranar da ya kwana goma sha
hudu ne ya samu cikakkiyar lafiya, har ma ya
kece da gudu a harabar gidan Abul Ishmira,
sannan kuma ya dauko takobinsa ya kama wasa
jini
da ita, yana bai wa kansa horon yaki. A
wannan lokaci Ishmira, Farila da Abul Ishmira
na zaune a gefe daya suna ta kallonsa kawai
cikin tsananin mamaki, domin ba su taba ganin
mutumin da ya iya sarrafa takobi ba kamarsa,
sannan ga shi da iya yin tsalle-tsalle da yin
alkafira a sama tamkar tsuntsu mai fukafukı.
Rayan bako ya gaji da bai wa kansa horon
fada da takobi sai ya zauna ya yi shiru, ya shiga tunani. Koda ya yi nisa a cikin tunaninsa sai ya
fashe da kuka. Al'amarin da ya matukar bai wa su Abul Ishmira tausayi da mamaki kenan.
Farila ta dubi Abul Ishmira ta ce, "Ya kai mijina
yanzu me zai hana mu tambayi wannan bako
labarin sa, tabbas wannan kuka da yake yawan yi akwai dalilinsa."
Abul Ishmira ya dubi Farila cikin alamun
karayar zuci ya ce, Ya za a yi mu ji bayani
daga bakin wanda bai taba magana da mu ba,
tsawon kwana goma sha hudu? Ina kyautata
zaton wannan yaron kurma ne."
Koda gama fadin haka sai Ishmira ta mike tsaye
ta tafi ga bako kai tsaye, su kuwa su Farila sa
suka bi ta da kallo kawai. Yayin da Ishmira ta
iso daf da bako sai ta zauna gabansa suka dubi
juna sannan ta ce, "Zuciyata da idanuna ba su
gamsu cewa kai kurma ba ne. Ya kai wannaan
bako ina son ka budi baki ka ba mu labarinka
idan har baka kasance mai butulci ba bisa ceto
rayuwarka da na yi daga can bakin kogi na kawo
ka nan.
Sa'adda Ishmira ta zo nan a zancenta, sai
bako ya sa hannu ya share hawayen idanunsa, Sannan .ya budi baki ya ce, 'Sunana Umairu bin Azwaba. Na kasance da ga sarki ham na birnin
Mazdur guda daya cal tilo a duniya. Yake
wannan budurwa ma'abociyar kyawu ki yi sani
cewa labarina yana da tsawo kuma akwai abin
tausayi a cikinsa, amma duk da haka zan yi
kokari na gajarce muku shi kafin na fara baku
labarina ina son na fara da yi muku godiya bisa
ceto rayuwata da fatan zan zamo mai amfani a
gare ku, ko kuma na yi muku sakaiya wata
rana."
Kimanin shekaru ashirin da biyu baya
sa'adda ban fi shekara biyar ba a duniya. Na taso
a cikin gata, jin dadi da walwala kasancewata
dan sarki guda daya tilo a wajen mahaifina,
sarki Ilham.
Mahaifina da mahaifiyata suna matukar
sona, kuma duk abin da na furta ina so in dai
akwai shi a cikin duniyar nan sai sun ba ni shi.
Sarki Ilham na da karfin mulki da kuma
tarin dukiya mara adadi. Babu abin da ya ke so a
rayuwarsa face adalci da zaman lafiya, domin ya
kasance mai tausayi da taimako ga talakawansa.
Wannan halaiya ta sa ce ta sa ya sami farin jini mai yawan gaske a wajen jama'ar birnin Mazdur
har ta kai cewa ko da wasa mutum ya zagi sarki
ko ya aibata shi take za a yi masa rajamu. Duk
inda sarki Ilham zai je ina tare da shi, kai ko
kwanciyar barci. Kai ko kwanciyar barci, tare muke sai dai mahaifiyata ta dauke ni daga kan kirjinsa
ta kai ni dakina ina ta barci ban sani ba.
Shakuwata da mahaifina ta wuce duk yadda
mutum zai tunano, domin ina farkawa da safe
Sunansa nake fara ambato, Da zarar na bude ido
na ga baya kusa da ni sai na ruga turakarsa na
riskishi. Nan zan zauna mu ci abinci tare ya yi
mini wanka, ya sauya mini tufafi, sannan shi ma
ya je. ya yi wanka ya kintsa mu tafi fada tare.
Wani abin al'ajabi kuma shi ne ni da mahaifina
kamar an tsaga kara ne, in ba don ni yaroba ne
shi kuma babba da sai a ce Hassan da Usaini ne.
Gaba daya mutanen kasar mu ma'abota
addinin bautar dutse ne, kuma duk shekara mu
kan je bayan gari mu. taru a gaban wani katon
dutse, wanda har yau ba a sami wani dutse mai
girma ba kamarsa a duniya. Muna kiran wannan
dutse da suna Gaubul Sabar.
A bisa al'adda duk shekara idan muka je gaban wannan dutse gaba dayanmu muna yin
Sujjada ne a gare shi babu wanda zai dago kai ya
mike tsaye har sai sarki ya bada umarni.
Shekarar da ba zan taba mantawa ba ita ce
shekarar karshe wacce muka ziyarci Gaubul
Sabar. Bayan mun yi sujjada a gare shi izuwa
tsawon yan dakiku sai mahaifina sarki llham ya
mike tsaye yä umarci jama a da su mike. Koda
muka dago da kawunan mu sai na ga mahaifina
na zub da hawaye, al'amarin da ya razana ni
kenan, kuma ya firgita dukkanin jama'ar birnin
Mazdur. Cikin matukar damuwa mahaifiyata ta
matsa kusa da shi ta kama hannayensa ta ce,
Yakai sarki mai adalci ka yi sani cewa
hankalin jama arka ya dugunzuma saboda ganin
zubar hawaye a idanuka domin sabon al'amari
ne a gare mu baki daya. Tun da ka hau kan
karagar mulki sama da shekaru ashirin duk
shekara sai mun zo nan mun yi bauta tare da kai,
amma ba mu taba ganin ka yi kuka ba, sai yau.
Ina dalilin wannan kuka na ka?"
Yayin da sarki llham ya ji wannan
tambava sai yà sake fashewa da matsanancin
kuka. al'amarin da ya kara karya zukatanmu kenan, har nima na ruga gare shi na fada kan
kirjinsa ya rungume ni yana mai dada ci gaba da
kukansa. Da kyar mahaifiyata ta rarrashe shi ya
daina kukan. Bayan ya nutsu sai ya kama kallon
jama'arsa daya bayan daya, yana kwallah. Daga
can sai ya yi ajiyar zuciya, sannan ya ce,
"Ya ku jama'ar birnin Muzdar kun sani
cewa duk shekara idan muka zo nan mai girma
Gaubul Sabar yana fada mini abubuwan da za
su faru gare ku a cikin shekara walau na alheri,
ko na tsiya. Sannan ni kuma na sanar da ku.
Haka ne ko?"
Jama'a suka amsa gaba daya, "Haka ne ya
sarkin mu mai adalci."
Sarki Ilham ya ci gaba da cewa, "To yau
ma kamar ko yaushe mai girma Gaubul Sabar ya
yi mini ishara bisa abin da zai samemu Ku yi
sani cewa ya gaya mini cewa a wannan shekara
wata babbar masifa za ta afko mana wacce za ta
zamo sanadiyyar mutuwarmu gaba daya, face
mutum daya daga cikin mu wanda bai sanar da
ni ko wanene ba. Za a rushe wannan kasa tamu,
a kone gidajenmu, a malale birnin mu da
Jininmu yadda har abada ba za a tuno da ire-iren mu ba. Mai girma Gaubul Sabar ya tabbar mini
da cewa ba zai iya ceton mu ba, daga wannan
masifa idan ta zo mana, amma ya ce wannan
mutum guda daya wanda zai tsira a cikin mu
komai daren dadewa zai dawo wannan birni
namu ya kafa sabon gari kuma ya mulke shi.
Wannan masifa tabbas tana nan tafe, kuma za ta
zo mana ne a lokacin da ba mu sani ba, amma
lallai za tazo ne. a cikin daya daga cikin lokuta
uku. Ko dai ta zo a farkon shekara ko kuma a
tsakiyar shekara ko a karshe."
Sa'adda sarki Ilham ya zo nan a zancensa
sai jama'a suka rude, wasu suka kama ihu, wasu
Suka kama koke-koke, kai wasu ma tsalle da
birgima suka yi ta yi, kamar sun zautu. Masu
nutsuwa ne suka hau rungumar yanuwa suna
hawaye da jimami cikin tsananin bakin ciki.
Daga wannan rana mutane suka rasa
sukuni, a cikin birnin Mazdur, har ma wasu suka
fara hada nasu-inasu da nufin yin hijira. Koda
sarki ya sami labarin abin da ke faruwa sai ya
tara jama'ar birnin kaf ya sanar da su cewa ko da
fa mutum ya yi hijira ba zai tsira ba, daga
wannan masifa domin duk inda ya je bai isa ya tsira ba, sai masifar ta riske shi. Koda jin
wannan batu sai hankalin jama'a ya kara
dugunzuma fiye da da can, kuma aka rungumi
kaddara bisa dole saboda an san cewa sarki
ilham bai taba yin karya ba, kuma duk abin da
ya fada yana tabbata a iya tsawon shekarun
mulkinsa.
Haka dai jama'a suka Ci gaba da rayuwa
cikin fargaba, zullumi da tashin hankali.
Tsananin fargabar tasa wasu ma suka dunga
kamuwa da cuta. Abu dai kamar wasa farkon
shekara ya shude lafiya lau babu abin da ya
faru. Ai kuwa da shekara ta zo tsakiya sai fa
jama'a suka dada firgicewa, musamman a ranar
cikar watanni shi da na shekarar. A wannan rana
har dare ya raba kowa na cikin gidansa a zaune
duk an kulle kofofin gidaje, masu kuka na yi
masu addu'ar ban kwana na yi.
Lokacin da dare ya raba sosai ina kwance
akan kirjin mahaifina ina ta sharar barci sai
mahaifiyata ta shigo cikin turakar ta riskemu. A wannan lokaci mahaifina ko rintsawa bai yi ba, idanunsa na zubar da hawaye ya kura mini ido
yana shafa gashin kaina. Ko da mahaifiyata ta data ganshi cikin wannan hali sai hankalinta ya dungunzuma ita ma ta fara kuka. Cikin karfin hali ta zo daf da shi ta zauna, suka dubi juna,
sannan ta ce, Ya kai mijina ina dalılin zubar wannan
hawaye a idanunka a yanzu? Ka yi sani cewa a iya rayuwata ta Zama da kài wannan ne karo na biyu na taba ganin hawayenka."
Sarki Ilham ya yi ajiyar zuciya ya ce.Yake
matata a bar begena dare a rana shin ba ki ji
Wata irin iska mar şanyi ba, tana kadawa a çikin wannan dare" Mahaifiyata ta ce, "Kwarai kuwa ina jin Wannan iska a Yanzu haka."
Shin ba ki ga mikiyoyi ba a sama suna shawagi?"
Ta ce, Kwarai kuwa na gan su.
Sarki lham ya ce, "Ki yi duba i zuwa
waje ta cikin ta ga abin da kika gani ki zo ki
da ni."
Koda jin haka sai mahaifiyata ta ruga gaban ta
gar dakin ta dube ta ta leka. Cikin razani ta rugo
da baya ta fadi gaban mahaifina ta ce, "Na ga
bishiyoyi na rangaji tamkar za su tunbuko daga cikin kasa kuma na ga koramai da fadamom
Suna fantsama kamar za su Cinye birnin nan."
Sarki Ilham ya fashe da kuka ya ce, "Duk
wadannan abubuwa da kika gani ba komai ba ne
face alamomi na zuwan masifar da za ta shafe
mu. Tabbas wannan masifa za ta zo mana ne a
gobe da sassafe. Ba wani abu ba ne ya sa kika
ga ina kuka ba face bakin cikin zamu mutu tare
da wannan da na mu Umairu wanda ya kasance
karamin yaro dan shekara biyar. A rayuwata ta
duniya ba ni da burin da ya fi bayan raina
Umairu ya gaje ni, ga shi kuma zan mutu tare da
shi, shi kenan ba za na bar baya ba. Ko na mutu
babu wanda za a kalla a tuna da ni duk da
cewa na yi suna na shahara a duniya. Ki dubi
dukiyar nan da na mallaka haka za mu tafi mu
BArta a banza."
Sa'adda sarki llham ya zo nan a zancensa
sai mahaifiyata ta fashe da kuka ta rukunkume
shi, al'amarin da ya janyo na farka daga barci
kenan a razane. Koda na' ga iyayena na suna kuka sai
nima na kama kukan aka rasa wanda zai
rarrashi wani a tsakaninmu. Daga can sai na
daina kukan na dubi mahaifina na ce


DAJIN MUTUWA
littafi na daya 1
Na Abdulaziz Sani M gini
Typing - Shuraihu Usman
Part 1F.
Ya kai Abbana ka ce akwai mutum daya
da zai tsira daga wannan masifa, to wai shin
wanene wannan mutum kuma ta ya ya zai
tsiran?"
Koda jin wannan tambaya sai mamaki ya
kama mahaifina ya kura mini idanu kawai. Daga
can sai ya ce, "Ya kai dana ka yi sani cewa mai
girma Gaubul Sabar bai sanar da ni kowanene
ba, amma ya gaya mini cewa wannan mutum zai
tsira ne ta hanyar buya a cikin wani karamin
dutse wanda tsawonsa da fadinsa bai wuce
kamu uku ba."
Na sake tambayarsa cikin yanayin
mámaki na ce, Ta ya ya mutum zai iya shiga
cikin dutse alhalin ba kofa gare shi ba?"
Mahaifina ya ce, "Da ikon mai girma
Gaubul Sabar hakan za ta faru."
Da wannan faruci sarki llham ya tsuke
bakinsa ya kara rukunkume mu a kirjikinsa, ni
dai ban san sa'adda barci ya sake sace ni ba.
tsananin rugugin rushewar gidaje, ihun
mutane da girgizar kasa ne ya farkar da ni daga
barci. Ina bude idanu na ji an sunkuce ni an yi
jifa da ni sama, tamkar an cilla takarda, sai gani a can kololuwar sama kai ka ce daga cikin baka
aka harba ni. Koda na leko samą sai na ga
wadansu irin halittu masu tsananin muni da ban
tsoro sun cika birninmu gaba daya. Su dai
wadannan halittu babu abin da mutum zai iya
siffanta su face dodanni. Idan suka kama mutum
sai dai ka ga sun sa hannu sun yaga shi tamkar
sun ya ga tsumma ko takarda. Nan fa jini ya
rinka fantsama da malala. Ina can kokoluwar
saman na hango sa'adda wani mugun dodo ya
kama uwata da ubana da yanyatsu bibbiyu
kawai sai ya wangame katon bakinsa ya Cusa
kawunansu ciki ya gutsure ya taune. Ganin
wannan al'amari ne ya sa na suma a sama. Ban
san abin da ya Ci gaba da wakana ba, sai bayan
na farfado kawai sai na tsinci kaina a cikin dutse
a rufe ruf, kuma ga shi babu wata alamar kofa ta
fita daga cikin dutsen. Wani abun mamaki kuma
shi ne ta cikin dutsen ina iya hango gaba dayan
cikin bimin mu tamkar a cikin gilashi nake.
Babu abin da idanuna ke gani face tarin
gawargakin mutanen birnin mu duka, ga jininan
yana malala yana gudu a kan kasa kamar
cibiyar ruwa ta balle, su kuwa dodannin nan sai kaiwa da kawowa suke suna ta dube-dube ko
su ga wani sauran me rai, amma ba su ga Kowa
ba. Babu abin da ya fi ba ni mamaki, face dutsen
da nake ciki a tsakiyar wadannan dodanni yake dan mitsitsi, a gabansu, amma sam ba sa iya
ganina. Kuma babu wanda ya shuri dutsen, ida
ma suka zo Wucewa ta kansa sa dai na ga su
daga kafa sun shallake shi. Koda na dubi yawar
gawarwakin al'ummarmu kuma na tuno da irin kisan gillar da aka yi wa iyayena sai na fashe da
kuka na kama ihu a cikin dutsen, domin a
lokacin gaba daya rayuwar duniya ta fita daga
sha'awa ta. Burina kawai dodannin nan suji ihuna su fito da ni daga cikin dutsen su kashe ni.
Amma sai duk ihun nawa ya zamo a banza,
domin babu wanda ya ji kuma babu wanda ya
ganni.
Bayan kamar rabin sa'a sai
na ga
dodanin nan sun daga wata bakar tuta wadda a
jikinta akwai hoton zanen farin hankaka, kawai
sai suka kama tsalle da gurnani, mai nuna
alamun samun nasarar yaki. Ba zato, ba
tsammani kuma sai na ga wani aljani yana
saukowa daga can sama sai kada manyan
fukafukansa yake. Zaune akan aljanin wani
gabjejen mutum ne bisa kujerar zinare, sanye da
kayan sarauta, kuma fuskarsa a rufe da hular
karfe, ba a ganin komai na sa face idanunsa,
hancinsa da bakinsa. A jikin kirjin rigarsa,
akwai wannan hoton zanen farin hankaka.
Koda aljanın ya sauka kasa, sai wannan
sarki ya dubi gabas, da yamma, kudu da arewa.
Bayan ya ga fululun gawarwaki sai ya bushe da
mahaukaciyar dariya, cikin tsananin farin ciki.
Lokaci guda ya daina dariyar ya dubi dodannin
nan ya ce,
"An gaishe ku manyan dakaruna, tabbas
yau kun hutasshe ni yin farautar makiyana,
domin kun kashe babban abokin gabata, kun
rushe mulkinsa kun shafe jama'arsa, daga doron
Kasa, don haka kun goge dukkan bakin cikin
rayuwata."
Yana gama fadin hakan ya sake bushewa da
dariyar mugunta. Shi kuwa aljanin da ke dauke
da shi sai ya bude fukafukansa ya tashi da shi
sama ya lulaka cikin gajimare. Har suka kule a
sama ban dainan jiyo sautin dariyarsa ba. Har
vau, har gobe na haddace sautin muryarsa da sautin dariyarsa ba zan taba manta su ba
Bayan bacewar sarkin ne wadannan
dodanni ma suka yi sahu-sahu suka kama hanya
suka bar cikin birnin namu. Sai da sa'a uku ta
shude sannan suka gama fita daga garin, saboda
tsananin yawansu haka kuma ban daina hango
su ba sai bayan wata sa'a ukun. Bayan
bacewarsu ne dutsen da nake ciki ya tsatstsage
ya fashe na fito daga ciki. Ai kowa ina fitowa na
ruga izuwa inda gangar jikin iyayena ke zube ba
kawuna na fada kan su na yi ta shara kuka. Sai
da na jima a haka, sannan na mike tsaye na ja
gangar jikin na su izuwa cikin irin wutar da ta
kone gidaje na jefa su ciki. Nan take na ji
zuciyata ta kekashe na daina jin tsoron komai.
Kawai sai na kama tafiya na bar cikin birnin na
nausa jeji na yi ta tafiya babu abin da ke fado
mini a rai face tunanin daukar fansa. Duk
sa' adda na runtse idanuna sai dai na ga hoton
zanen farin hankaka kuma sai na dunga jin
muryar wannan azzalumin sarki a cikin dodon
kunnena gami da sautin dariyarsa.
Daga wannan rana na zamo tamkar dabba domin abani da gida sai daji, bani da yanuwa sai dabbobin dawa bani da abina sai
yayan itatuwa da kuma naman da na iya
farautowa. tun ina shekara biyar din na iya
farauta a daji kuma na iya boya a duk sa'adda
naga abin tsoro ya zamana ina kwana akan
bishiyoyi kamar dan biri. Sai dana shekara goma
acikin irin wannan rayuwa sannan wata rana na
hadu da wani mafarauci mutum mai kirki wanda
ya tafi dani izuwa gidansa inda matarsa
ta rukeni tamkar dan cikinta a cikin wani daji daketa
yamma da wani. Babban birni da ake kira
madarul Aswar. Sai da na shekara uku a gidan
wannan mafarauci ba taba shiga cikin birnin
madarul Aswar dani ba. Haka kuma bai tab6a
tambayata labarina ba kuma nima ban taba
tambayarsa nashi labarin ba da kuma dalilin
zamansa a cikin wannan daji. A zaman da
mukayi ya koya min farauta ainun kuma ya bani
sirrikan tsafi da yawa domin na kare kaina bisa
mugun abu.
Katsam sai wannan mafarauci ya kwanta
cutar ajali al'amarin daya dugunzuma hankalina
dana matarsa kenan muka rasa abinda ke mana
dadi a duniya. Magani kuwa babu irin wanda bamu yi nema ba mün bashi amma duk a banza.
Daga sannan kullum muke fita farauta na nemo
abinda za'a ci a gidan mafarauci har tsawon
kwana arba'in Hakika a wannan lokaci na tsinci
kaina a cikin hadari da mütukar damuwa saboda
sabon da nayi da maigidana kasancewar yana
debe min kewa kuma na daukeshi tamkar
mahaifina.
Wata rana na dawo daga farauta cikin
tsananin farin ciki sakamakon samun nasarar
kamo Barewa da gada sai na iske matar
mafarauci zaune a gaban maigidanta wanda ke
kwance tana ta sharar kuka, shima kuma hawaye
na zuba a idanunsa. Al'amarin daya tayar da
hankali na kenan na yarda abin farautar tawa na
ruga garesu da zuwa sai na durkusa a gaban
maigidan nawa na kama kuna sannan na kama
hannayensa na ruke nace yakai Abbana ina
dalilin zubar hawaye a idanunka? Shin ka fidda
rai da sanmun lafiya ne? A rayuwarka? Ni Kama
nayi imani cewa in dai da rai'akwai rabo. Bisa
mamakI sai na ga fuskar mafarauci ta fadada da
murmushi daga bisani kuma sai ya fashe da
kuka ya ce, "Ya kai dana ka yi sanin cewatabbas wannan cuta tawa ba ta tashi ba ce, ita ce
ajalina. Ba komai ne ya sa ka ga muna wannan
kuka ba ni da matata face za mu rabu a lokacin
da ba mu samu damar cika burın rayuwar mu
ba. Wannan buri kuwa shi ne na samun da wato
magaji wanda muke sa ran nan gaba shi ne zai
zamo sarki a wancan babban bimi na Madarul
Asuwad.
Ko da mafarauci ya zo nan a zancensa, sai
na kara cika da mamaki na ce, "Ya kai Abbana
ya za a yi dan ka ya zamo sarki alhalin bai gaji
sarauta ba?"
Mafarauci ya yi tari har sau uku, sannan
ya ce, "Ya kai dana Umairu ka yi sani cewa
sarkin da ke mulki a wannan birni na Madarul
Aswad a yanzu kanina ne uwa daya uba daya.
Sunansa Zalulu bin Asmar, ni kuma sunana
Hulairu bin Asmar. Tsakanina da shi bambancin
shekaru biyu ne kacal. Tun da muka taso muna
yara halayenmu suka bambanta, domin ni na
kasance mai hakuri, tausayi da jin kai. Shi kuma
sai ya zamo mai taurin ka, azzalumi da bakar
zaciya. Bisa wannan dalilina mahaifinmu sarki
Asmar ya kaunace ni fiye da Zalulu, kuma tun muna yaran sarki Asmar ya tabbatar mini da
cewa nine zan gaje shi Koda dan uwana Zalulu
ya fuskanci cewa lallai in dai mahaifinmu na
raye ba zai taba yin sarautar birnin Madarul
Aswad ba, sai hankalinsa ya dungunzuma ya
shiga tunanin hanyar da zai bi ya yi maganin
wannan matsala. Ita ma mahaifiyarmu wacce
ake kira Hasmira ko kadan ba ta kaunar Zalulu
saboda mugayen halayensa da taurin kansa na
kin jin magana. Akwai wata rana da ta rufe shi
da fada akan wani laifi da ya yi na zaluntar wani
bawa kawai sai ran Zalulu ya baci ya zagi
mahaifiyarmu. Nan take kuwa ta daga hannu ta
shara masa mari, ta sake daga hannun da nufin
ta kara masa marin sai ya yi wuf ya kauce ya ce,
"Akul kika kuskura kika kara marina.
uwata ki yi sani cewa na rantse da darajar
karagar gidan nan daga yau da ke da ubana kun
daina zama matsala a gareni. Na san bakwa
kaunata kun fi son danuwana Hilairu kuma shi
kuke so ku bai wa mulkin kasar nan. To 1na
tabbatar muku da cewa wannan mafarki na ku
ba zai taba tabbata ba. Ni kam na hakura da ku a
matsayin iyaye tuni zuciyata ta aminta da cewa ni maraya ne. Wannan gani da kika yi mini a
karshe a
yanzu shi ne zai zamo gani na karshe a
rayuwarki. Tabbas in kuwa kika sake ganina a
rannan za ki mutu." Zalulu na gama fadin haka
ya juya ya fita daga gidan sarautar. Daga
wannan rana ba mu sake jin duriyar Zalulu ba,
har tsawon shekara uku, kai ko wanda ma ya ji
labarinsa ba mu samu ba.
Rana daya aka wayi gari sarki ya kamu da
matsananciyar rashin lafiya.Nan da nan
likitocin sarki suka taru a kansa suka yi ta aikin
su suna bincike. Yayin da bincike ya yi tsamari
sai aka gano cewa guba guba aka bawa sarki a cikin
shayi ya sha kuma ba wani ba ne ya yi wannan
barna ba, face mai dafa masa abinci wani
mutum wanda ake kira Mahakuf.
Asalin Mahakuf bawa ne wanda ya yi
zamani da kakanmu, kuma ya zauna da shi bisa
gaskiya da amana, don haka nema mahaifinmu
sarki ASmar ya yarda da shi dari bisa dari ya
amince da shi a,matsayin mai data masa abinci.
Koda aka gano cewa Mahakuf ne ya
zubawa sarki guba a shayi, sai fadawa suka ce a
tafi da shi filin fada a sare masa kai. Duk da cewa sarki Asmar na cikin
matsanancin hali sai ya budi baki ya ce, kada aje a kashe Mahakuf a zo da shi yanzu gabansa
tukunna. Nan take aka zo da Mahakuf a daure
wani irin
cikin sarka aka gurfanar da shi. Cikin matukar
kunya Mahakuf ya sunkui da kansa kas ya kasa
hada idanu da sarki. Shi kuwa sarki Asmar sai
ya dago kai da kyar ya budi baki cikin dauriya
yana mai duban Mahakuf ya ce,
Ya kai amintaccen bawana kai kuwa
wane laifi na yi maka wanda ya cancanci
wannan horo mai tsanani a gareni har ka nemi
rayuwata? Ni dai na san cewa a iya zamana da
kai ban taba ha'intar ka ba, kuma ban taba cutar
da kai ba. A sanina a duk duniyăr nan, kai ne
mutum na daya wanda nafi aminta da shi,
asalima da kai nake shawara bisa dukkan
al'amurana. Babu wanda ya
tamkarka. Na baka amanata, ka ba ni taka. Me
ya sa yanzu ka Ci amanata alhalin kai yardajjene,
kaSan sirrina
har a wajen mahaifinmu?"
Sa'adda sarki Asmar ya zo nan
a
zancensa, sai bawa Mahakuf ya fashe da kuka
ya ce, "Ya kai sarki mai adalci ka yi sani cewa wannan barna dana aikata ba a son raina ba ne
an yi mini dole ne. Kuma ba wani ba ne ya
tursasani ba na aikata hakan face danka Zalulu.
Ka yi sani cewa tsawon shekaru uku da bacewar
Zalulu tun a sannan ya sace dana Imal yaro dan
shekara bakwai, wanda shi kadai gareni a
duniya.
Zalulu ya yi garkuwa ne da dana Imal a
matsayin idan ban zuba maka wannan guba ba,
Zai kashe shi. Tsawon shekaru ukun nan kullum
da daddare sai Zalulu ya turo an sace ni cikin
dare an kaini can wani daji in da ya kafa sansani
na mayakansa yan tawaye kimanin su dubu dari
biyu da doriya. Anan ne ya boye dana Imal.
Kullum idan aka kai ni sai ya sa an yi mini
bulala ashirin, sannan kuma ya fito da dana ya
nuna nmini shi ya ce in dai ban aikata abin da
yake s0 ba, a bakacin ransa. Kullum idan aka
dawo da ni gida sai na yi ta kuka, saboda na san
cewa ba zan iya cin amanarka ba."
Ko da Mahakuf ya zo nan a zancensa sai ya tube rigarsa, nan take aka ga tabon bulalu a
bayansa rudu-rudu. Gaba daya fadawan da ke
wajen sai da tausayi ya kama su saboda ganin
yadda aka yi kaca-kaca da bayans tsoho
Mahakuf mutumin da ya fi shekaru casa'in a
duniya. Mahakuf ya share hawayensa ya ci gaba
da bayani ya ce,
"Ya kai sarki mai adalci ka yi sani cewa
Zalulu bai ba ni gubar da zan zuba maka a shayi
ba, sai da shekaru ukun nan suka cika, wato
kwanaki uku da suka gabata, A ranar ne ya ce da
ni lallai a gobe da safe yake son na zuba maka
wannan guba idan kuwa na ki lallai zan tsinci
gawar dana Imal a kofar gidana da yammacıi.
Kuma a lokacin ne ya tabbatar mini da cewa
lallai idan har ka sha wannan guba ba za ka
wuce kwana uku ba, a duniya. Wannan shi ne
dalilin da ya

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment