Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mu."
Mu dai ba mu tsaya jiran komai ba sai
muka kwankwance su. Da kyar suka iya taka
Rafafunsu muka fice gaba daya daga cikin gidan
muka nausa da gudu cikin daji ba tare da sanin
inda muka dosa ba. Sai da muka shafe sa'a uku
muna gudu a daji, sannan muka iso bakin wata
korama. Anan ne muka tsaya gaba dayannmu
muna haki. Bayan kowa ya sha ruwa ya wanke
jikinsa sai muka bude jakarmu ni da Salkuf
muka dauko abinci mai yawa muka bai wa su
Mukairu. Ko da karbar abinci sai suka dasa
masa wawa tamkar a ajiye gafiya a tsakiyar
karnuka. Haka dai suka yi ta cin abincin wannan
nan ture wancan, tamkar sun shekara ba su ci
ba. Bayan sun nutsune hankalinsu ya dawo
jikinsu sai muka kwashe labarin mu muka
muka
raiyane musu, tun daga lokacin da suka gudu
suka bar mu a tarkon yanfashi kawo izuwa
sa'adda muka hadu da su. Ko da jin wannan
labari na mu sai dukkaninsu suka fashe da kuka,
suna masu neman gafarar mu bisa abin da suka
vi mana kuma suka yi ta yi mana godiya, da
muka ceci rayuwarsu a yanzu.
Nan take Kumairu ya shiga ba mu na su
labarin bayan rabuwar mu, inda daga karshe ya
shaida mana cewa wasu
maridai ne ma'abota
karfin damtse da karfin sihirin tsafi suka kama
su suka kai su wannan gida suka daure su
kullum sai sun yi musu bulala ashirin-ashirin
kafin su fita daji farauta. Al'adar wadannan
maridai shi ne cin naman mutane, amma idan
suka kama mutum sai su daure shi su yi ta zane
shi kullum har tsawon kwana arba'in sannan su
kwance shi su gasa shi su cinye. Lokacin da
maridan suka kamo su Mukairu suka zo da su
wannan gida sun iske cewa akwai wasu
mutanen a daure kamar su wadanda kwanaki
Kadan ya rage musu a cinye su. Ai kuwa da
Kwanakin suka cika a gaban su Mukairu aka gashe mutanen aka cinye su. Mukairu ya ce,
"A yau din nan da kuka zo kwanan mu
talatinda tara, ana yi mana bulala kullum
ma'ana a gobe ne za a gashe mu a cinye. In da
ba ku zo yau ba kun cece mu da tabbas gobe za
a gama da mu."
Koda jin haka sai muka kankame su
Mukairu muna masu taya su farin ciki da suka
kubuta daga hannun
wadannan mugayen
maridai masu cin naman mutum.
Bayan an gama wannan tattaunawa muka
yanke shawarar mu tashi mu ci gaba da tafiya
don ba mu sani ba ko maridan nan sun biyu
sawun mu. Nan take kuwa aka kama hanya aka
yi ta tafiya ba tare da sanin inda aka dosa ba.
Mu kwana nan, mu tashi can muka wanzu
muna ta tafiya a daji har muka sake shafe
kwanaki ashirin da tara, amma ba mu sake
saduwa ba da wani mugun abun.
A ranar kwana na ashirin da taran ne
muka shigo cikin wani irin daji mai ban tsoro
dominya tara manyan tsaunika, dogayen
bishiyoyi da manyan duwatsu. Haka dai muka
yi ta ratsa wannan daji har tsawon sa'a uku ba mu ga karshen ba. Al'amarin daya dugunzuma hankalin mu kenan. Kwatsam muna cikin tafiyaa
sai muKa ga wasu irin halittu suna saukowa daga
sama kamar tsuntsaye bila adadin babu iyaka.
Kafin mu yi wani yunkuri halittun sun yi mana
kawanya babu damarguduwa ko neman
matsera. Kawai sai su Kumairu suka dafa wani
kambu dake jikinsu take suka bace bat, muka
neme su sama da kasa muka rasa, sai dariyarsu
muka ji Suna ta kyakyatawa. Su ka bar mu nan
tsaye mu biyu kacal a tsakiyar halittun masu
siffofin aljanu. Nan fa muka yi ta matsa layun
nan na iikin mu wadanda Maruful Haz ya ba
mu, don mu bace, amma sai abu ya faskara.
Muna ii, muna gani halittun nan suka
kama mu suka tashi da mu sama, sai da suka kai
mu can saman wani tsauni mai tsakanin tsawo
Sannan suka dirga damu a gaban wani kerarren
gida, wanda aka yi shi da zallan zubardaji. Da
Zuwa sai kofar gidan ta bude da kanta aka shigar
da mu ciki, sannan kofar ta rufe kanta. Nan fa
aka yi ta tafiya da mu har tsawon sa'a biyu Sannan muka iso wata wangamemiyar fada
wani
karaga
zaune akan wata shirgegiyar basamuden aljani ne mai mummunar siffa.
Aljanin na da rafkeken kai mai kama da na
alade. Hannayensa da kafafunsa irin na biri ne.
Jelarsa kuwa katuwa ce kuma doguwar gaske
duk jikinta kahonhona ne. Girman farcen
hannunsa guda ya kai na hauren giwa. Koda aka
zo damu gaban aljanin sai ya sa aka zaunar da
mu bisa wasu kujeru manya aka dauremu
tamau, da sarkoki.Aljanin ya dube mu ya fashe
da mahaukaciyar dariya mai kama da tartsatsin
aradu, sannan ya ce da mu.
"Marhaban da shaidanun bil'adama masu
Son shiga cikin gonar Sirrin mu. Ku yi sani cewa
ni ne boka Shukurul Akwar, wanda ke kiwon
tsohon kure, na Dajin Mutuwa. Bincike ya nuna
mini cewa za ku je Dajin Mutuwa ku zamo
sanadin mutuwar wannan kure nawa, wanda na
shekara tamanin da bakwai ina tsumashi a cikin
tsumin tsafina. Lallai ruhina na tare da ruhin
wannan kure idan kuka hallaka shi tamkar kun
hallaka nine don haka gwara ni yanzu na fara
hallaka ku don an ce ka kashe makashinka kafin
makashinka ya kashe ka."
Lokacin da Shafaru ya zo daidai nan a labarinsa ne rana ta fadi, gari ya soma yin duhu,
don haka sai boka Shamakalu ya daga masa
hannu ya tsaida shi ga barin zance mai dadi.
Boka Shamakalu ya dubi dakarun sarki Hamaru
wadanda suka zo da Shafaru ya ce, "Ku koma
ga sarkin ku ku ce da shi Shafaru ya kawo
mini wasika kuma na ji abin da ke cikinta. Ni
boka Shamkalu na ce ba zan bar birnin Farisa
ba, kuma ba zan yi wa Shafaru komai ba. Duk
abin da sarki zai yi sai dai ya yi kuma ba zan
fadi komai ba, sai gobe bayan Shafaru ya gama
bayar da wanan labari da bai karasa ba, don
haka yanzu na umarci kowa da ya tafi izuwa
gida in ya so gobe da safe a dawo nan don jin cigaban labarin Shafaru. A halin yanzu zan ruke
Shafaru ya kwana tare da ni."
Ko da gama fadin haka sai boka gama fadin haka
Shamkalu ya nunan sarkokin da ke jikin Shafaru
da danyatsa guda duk suka tsinke suka fadi
kasa, sannan sai ya kama hannunsa ya ja shi
iZuwa cikin wannan gida nasa inda rijiyar
kwankwamai take. Koda faruwar haka sai
jama'a suka watse kowa ya kama gabansa.
Yayin da boka Shamakalu da Shafaru suka kadaita a cikin wannan gida sai Shamakalu
ya yi tsafi take wata aljana ta bayyana ya sa ta ta
yi wa Shafaru aski ta gyara fuskar nan tasa ya yi
kyau, sannan ta yi masa wanka. Aka kawo tufafi
mai kyau aka ba shi ya sanya, aka sa masa
turare mai kamshi. Sannan aka kawo masa
abinci iri-iri sama da kala goma irin na sarakai
aka ba shi ya ci ya koshi. Rabonsa da shiga irin
wannan ni'ima shekara ashirin da daya kenan.
Bayan ya sami nutsuwa sai boka Shamakalu ya
dube shi ya ce,
"Yakai Shafaru ka yi sani cewa har abada
danuwanka sarki hamaru ba zai taba kaunarka
ba, kuma hankalinsa ba zai taba kwanciya ba
face ya ga baka numfashi a doron kasa. Ina so
ka sani cewa shi makiyı har abada makiyi ne,
kuma ba zai fasa farautar makiyinsa ba, in dai
yana rage. Yanzu zan baka wani labari wanda
zai tabbatar maka da gaskiya ta." Boka
Shamkalu ya yk gyaran murya ya fara bayani
kamar haka:
A wani bangare can na duniya akwai
wata rana da wani abokin gaba ya tsira da kyar
daga hannun abokan gabansa, bayan sun kusan hallaka shi ya tsere akan dokinsa yayi ta gudu a daji cikin halin suma har ya isa nahiyar da ba ta su ba, dokinsa ya yarda shi a gabar wani kogi inda ya samu ya farfado. Farfadowarsa ke
da wuya sai ya jiyo motsin tafiya daga cikin
wadansu bishiyoyi. Cikin matukar karfin hali ya
daga hannunsa na dama ya dora shi akan kufen
takobinsa duk da ya san cewa ba zai iya kodá
zare takobin ba. Sannu a hankali motsin tafiyar
ya kara yawa har ya fara jiyo sautin murya.
Koda ya gane cewa muryar ta mata ce sai
hankalinsa ya dan kwanta, domin ya san cewa
ba abokan gaba ba ne suka biyo bayansa.
Ba zato, ba tsammani sai ga yanmata
guda bakwai dauke da tuluna sun iso wannan
kogi da nufin dibar ruwa. Koda suka yi arba da
Wannan mutum da kuma dokinsa a cikin kogin
Suka ga jini na malala akan ruwa sai suka rafka ihu suka yarda tulunan na su suka juya da baya
da gudu. Sai da suka yi nisa sannan suka tsaya
Suna haki daya daga cikin su wadda ta kasance
Kyakkyawar gaske ta gaban kwatance ta dubi
Sauran ta ce da su.
"Wai shin ku menene dalilin wannan gudu na mu, ca nake mutumin da muka gani a cikin rafin can ba zai iya cutar da mu ba, ku dubi halin da yake mana ba mamaki ma yanzu in muka koma mu tarar ya mutu. Yanzu shi kenan mun hakura da debo ruwan kenan?"
koda jin wannan batu sai jikin ragowar yan matan yayi sanyi wadda ke kusa da ita ta ce "haba ishmira shin kin manta ne akwai yan sumame da yawa a nahiyarnan ta mu?babu mamaki mutumin da muka gani a kwance ba shi kadai bane akwai yan uwansa a labe sun dana mana tarko."

Ishmira tayi murmushi ta ce " ai kuwa in dai akwai wasu a laben ba zamu iso nan batare da sun cimmana ba. nikam ba zan koma gida ba babu ruwa, lallai sai na koma rafinnan wacce taga zata iya ta biyoni, wadda bazata iya ba ta tafi gida" ishmira na gama fadin haka ta juya da baya ta nufi hanyar rafin, ragiwar yan matan bakwai sai sukayi kasake suna kallon juna, wata matsoraciyar gaske wadda ake kira banisa ta zura a guje zuwa cikin kauyensu

lokacin da su ishmira suka dawi bakinrafin sai suka iske wannan mutum a cikin kogin
kamar yadda suka bar shi dazu. Gashi dai
tsamo-tsamo a cikin ruwa yana numfashi da
kyar, amma ya kasa motsi. Ishmira ta kare masa
kallo ta ga ashe saurayi ne kyakkyawa, wanda
bai fi shekaru ashirin da shida ba, ga shi da kira
irin ta sadaukai, kuma babu alamar kamanin
mugunta a fuskarsa. Koda ta gama wannan
nazari sai ta ruga cikin ruwan sannan suka yi
kama-kama ita da sauran yanmatan suka dora
shi akan dokinsa. Daga nan kowacce ta cika
tulunta da ruwa. Ishmira ta kama linzamin dokin
yana kwance a kai taja suka yi gaba izuwa cikin gari.
Sai da suka yi nisa da barin rafin, sannan
suka fuskanci cewa Banisa ba ta tare da su.
Ishmira ce ta fara tambaya, Ko akwai wanda ya
ganta?"
Badura wadda ta kasance babbar cikin su
ta ce, "Ai sarkin tsoron tuni ta ruga gida."
Gaba dayansu suka bushe da dariya. Daga
nan suka ci gaba da tafiya, suna ta hirar su har
da batun wannan bako da suka tsinto a kogi har
suka iso cikin kauyen Madinatul Asmal.
Madinatul Asmal karamin kauye ne na
ma'abota addinin Musulunci a cikin yankin
kasar Turkiya. Shi
dai wannan kauye
haramtacce ne ga sarki Sharmuzul Bazabur
wanda ke mulkin birnin Turkiya, domin asalin
kauyen an kafa shi ne sa'adda sarki Sharmuzul
Bazabur ya hau kashe tsirarun Musulmai
wadanda ke zaune a cikin birninsa. Bisa dole
suka yi hijira suka koma cikin daji har suka gia
wannan karamin kauye, wanda gaba dayan
mutanen cikinsa ba Su wuce mutum dubu biyu
ba. Shugaban wadannan mutanen kauye wani
bawan Allah ne dattijo, dan kimanin shekaru
tamanin da doriya ana kiransa da suna Abul
Ishmira, wato mahaifin wannan kyakykyawar
budurwa wacce ta dauko bakon mutum daga
rafi.
In ba don karfin addu'a ba, da tuni sarki
Sharmuzul Bazabur ya hallaka mutunen wannan
kauye, domin har yau har gobe kullum yana turo
dakarunsa, suna zuwa farautar wannan kauye,
amma duk sa'adda suka iso sai Su ga kauyen ya zama kogi gaba dayansa, kuma ko tsuntsu ba sa gani a wajen Al'amarin da ya jefa sarki
Sharmuzul Bazabur cikin matsanancin bakin
ciki kenan, domin boka Asimul Abaru ya
tabbatar masa da cewa idan har wadannan
mutane suka ci gaba da rayuwa to tabbas wata
rana za su zamo sanadiyar rushewar mulkinsa,
da kuma addinin su na tsafi. Bisa wannan dalili
ne sarki Sharmuzul Bazabur ya tsananta farautar
makiyansa wato mutanen kauyen Madinatul
Asmal, kullum dare da rana.
Mutanen birnin Madinatul Asmal sun
kasance masu gaskiya, amana da jin kan juna;
don haka kowa a garin yana jin dadin zama tare
da tafiyar da rayuwarsa cikin in dadi da
kwanciyar hankali. Gaba daya mutanen kauyen
maza da mata, yara da manya kowa ka gani
akwai wata laya daure a wuyansa. Ita dai
wannan laya babu komai a cikinta face sunayen
Ubangiji tsarkaka na ismil A azami. Babban
Malamin kauyen wanda ake kira Sheikh Huzaif
bin Kasim shi ne ya raba wadannan layu iya
adadin jama'ar kauyen. Kuma ko yau aka haifi
Jariri sai an karbo wannan laya a wajen Huzaif
an sa masa a wuya. Wannar laya ta kasance
tsari ga jama'ar wannan kauye, domin idan suna tare da ita, babu wani tsautsayi da ya isa ya hau
kansu.
Da yake Banisa ta riga su Ishmira isa gida
tana zuwa ta kwashe labarin duk abin da ya faru
a rafi ta sanar da jama'ar gari. Ai kuwa nan take
aka taru gaba daya a kofar gidan su Ishmira aka
yi Cincirindo anan jiran dawowar su Ishmira
daga rafi. A wannan lokaci Abul Ishmira da
Sheikh Huzaif na zaune a can gefe guda suna
tattauna al'amarin inda Abul Ishmira ya dubi
Sheikh Huzaif ya ce, "Yakai babban malami
shin yanzu menene abin yi? Za mu zauna ne mu
ci gaba da sauraro ko kuwa za mu bi bayan
yaran nan ne don mu tabbatar da lafiyarsu?
Yayin da Sheikh Huzaif ya ji wannan
tambya sai ya yi murmushi, sannan ya ce, "Haba
Abul Ishmira yanzu ashe har zuciyarka na
tunanin wani abu zai samu 'ya'yanmu? Shin ka
manta ne cewa suna tare da kariyar Allah. Ina
tabbatar maka da cewa idan har suna tare da
layunsu babu abin da zai same su. Gama fadin
haka ke da wuya aka hango su Ishmira a tare
Sun nufo kauyen. Ishmira ce akan gaba rike da
linzamin doki, Akan dokin bakon saurayi ne kwamce magashiyan.




DAJIN MUTUWA
littafi na daya 1
Na Abdulaziz Sani M gini
Typing - Shuraihu Usman
Part 1E.
Koda ganin haka sai
hankalin Abul Ishmira ya tashi, ransa ya baci ya
dubi Sheikh Huzaif ya ce, "Yakai babban
malami ka yi sani cewa 'ya ta karya dokar
kauyenmu, lallai hukunci ya tabbata a kanta, tun
da ta dauko bako ta shigo da shi."
Sheikh Huzaif ya ce, "Kwarai ta karya
doka, to amma sai mun ji dalilin ta na karya
dokar sannan mu yi mata hukunci
daidai da
hujjojnta, idan ma tana da hujja mai karfi ba za
a hukuntata ba, sai dai mu dauki mataki daidai
da tsarin rayuwammu
Yana gama fadin hakan ya mike tsaye ya
ce, 'Ka zo da ishmira gidana da yammaci domin
mu zauna gaba daya da sauran malamai domin
magance wannan matsala. Na umarceka da kada
awulakanta wannan bako da ta zo da shi. A ceci
rayuwarsa a yanzu a yi masa duk abin da ya
kamata kafin shi ma mu yanke hukunci a
kansa."
Abul Ishmira ya sunkui da kai kas ya ce,
Haka za a yi ya babban malami."
Nan take Sheikh Huzaif ya tafi izuwa
gidansa. Ganin tafiyar tasa ne ya sa jama'a suka watse, kowa ya kama gabansa, aka bar Abul
Ishmira da matarsa Falira Su kadai a tsaye
Suma sauran kawayen Ishmira sai suka rarrabu
kowacce ta tafi gidan su. Cikin alamaun tsoro
Ishmira ta karaso gaban iyayenta rike da dokin
bako, kuma ga tulun ruwa a kanta. Kanta na
sunkuye, kirjinta na dakan uku-uku ta tsaya a
gabansu. Bisa mamaki sai ta ga mahaifiyarta ta
karbi tulun da ke kanta, shi kuwa Abul Ishmira
sai ya dauko bako daga kan dokin ya ratayo shi
a kafadarsa ya nufi cikin gida. Koda ganin haka
sai ita ma Ishmira ta ruga cikin gidan tana ma
murna. Abul Ishmira bai sauke bako a ko'ina ba
sai a cikin turakarsa. Nan take ya hada magani
kala biyu na sha, da na sha fawa ya kimtsa bako.
Ishmira ce ma ta talmaka masa wajen hada
magungunan. Jim kadan sai bako ya farfado ya
dawo cikin hayyacinsa.
Koda ganin haka sai Abul Ishmira ya
umarci Falira da ta kawo dafafiyar madarar
shanu. Take ta cika aiki. Abul Ishmira ya shayar
da bako wannan madara a koko da hannunsa.
Bayan ya gama shan madarar sai ya kwantar da
shi akan gSaboda hunturin sanyin da ke hadawa a wannan
lokaci. Shi dai bako har yanzu bai ce da kowa
kala ba, sai dai kawai ya kalli wannan ya dubi
wancan, yana dan murmushin karfin hali. Jim
Kadan kuma sai barci ya kwashe bako.
Abul
ishmira ya dubi Falira, sannan ya dubi ishmira
ya ce,
"Kada ku tashi bakon nan har sai ya farka
da kansa. Ke kuma Ishmira ki sani cewa da
yammac za mu je gidan babban maiami ni da
ke, domin ki kare kanki bisa karya dokar mu
Koda jin haka sai idanun shmira suka yi
tsuru-tsuru ta kasa cewa uffa. Falira ta yi ajiyar
Zuciya Cikin yanayin damuwa, sannan ta dubi
Ishmira ta ce, yake yata ke kuwa saboda me ki
ka yi wannan gangani alhalin kin san doka ce
mat tsauri a garin nan ki shigo da bako?"
Ishmira ta sunkui da kanta kas cikina
alamun nadama, idanunta suka ciko da kwallah
ta ce, "Ku gafarce ni ya ku iyayena ku yi San
cewa ni kaina ban san yadda aka yi ba zuciya ta
rudeni na aikata wannan laifi. Tabbas yanzu na
yi nadan a amma hakikannin gaskiya tausayi
ne yà sa ni na aikata hakan kuma gani na yi
ado, sannan ya lullube shi da bargo babu kamanni na rashin gaskiya ko zalunci a
fuskar wannan bako shi ya sa na taimake shi.
Falira ta yi ajiyar zucoya ta ce "Ai shi
kenan je ki karasa mini aiyuka a cikin gida."
Nan take Ishmira ta wuce cikin gida.
Da La'asar sakaliya Ishmira da mahaifinta
suka tafi izuwa gidan babban malami Sheikh
Huzaif. Da zuwa suka shige ciki inda suka isa
wani babban falo wanda babu komai a cikinsa
face shimfidu na fatar dabbobin dawa. Zaune a
kan shimfidar Sheikh huzaifa ne yana sanye da
fararen kaya, kuma ya nada gajeren rawani a
kansa.
Sheikh Huzaif ya kasance mutum mai
matsakaicin kaurin jiki, gami da faffadar fuska.
Yana da farin gemu, farin saje. Kai duk inda ake
neman kwarjini in aka ga Sheikh huzaif an
samu. Shekarunsa sun haura casa'in amma kuma
bai kai dari ba. Zagaye da shi wasu malamai ne
dattija Su goma sha daya, wato shi ne cikon na
goma sha biyu. Koda isowar Abul Ishmira da
yarsa gaban su Sheikh Huzaf sai suka zauna a
gefe daya bayan sun yi sallama an amsa musu.
Ishmira ta sunkui da kanta kas ta yi shiru kamar ba ta da rai dama ta sha lullubi kuma duk jikinta
a rufe yake. Zuciyarta kuwa sai bugawa take yi
da karfi, saboda tsoron irin tambayoyin da za a
yi mata yanzu da kuma rashin sanin irin
hukuncin da zai biyo baya bisa laifin da ta
aikata. Dadin dadawa kuma ba ta taba shigowa
wannan gida ba a cikin irin wannan hali na
tuhuma bisa laifi.
Bayan an yi gaisuwa irin ta addinin
Musulunci tsakanin Abul Ishmira da su Sheikh
Huzaif sai shiru ya biyo baya, tsawon yan
dakiku. Daga can sai daya daga cikin dattawan
ya yi gyaran murya, sannan ya dubi lshmira ya
ce, "Yake Ishmira shin za ki iya yi mana
ce,
bayanin abin da ya faru gare ku ke da
kawayenki yayin da kuke je rafi diban ruwa?"
Ishmira ta hadiyi miyau, sannan ta fara
bayani cikin rawar murya har sai da ta zayyane
komai dalla-dalla, ba ta boye komai ba. Koda ta
gama jawabi sai wani dattijan daban ya sake
tambayarta ya ce, "To menene dalilin da ya sa kika
dauko wannan bako mutum tare da dokinsa kika
taho da shi cikin gari alhalin kin san cewa aifi
ne a tsarin dokokin mu?" Ishmira ta amsa wannan tambaya da irin
bayanin da ta yi wa mahaifiyarta. Koda jin
wannan batu sai gaba dayan dattijawan suka yi
shiru, suna kallon Ishmira kawai kamar suna
tunanin wani abu har izuwa wani dan lokaci
kuma suka yi ta kallon junansu tamkar suna
zance da idanu. Daga can sai sheikh Huzaif ya
yi gyaran murya ya dubi Ishmira ya ce da ita.
"Hakika kin zo da hujja mai karfi, to
amma duk da haka sai kin fuskanci hukunci,
domin kin karya doka. Hukuncinki shi ne za a
tsare ki tsawon kwana uku a gida ba tare da kin
fita ko ina ba, ya zamana kullum daga safe har
izuwa faduwar rana babu abin da kike face
karatun alkur'ani mai girma."
Koda jin wannan batu sai fuskar Ishmira
ta fadada da murmushi, saboda murnar jin
saukin hukuncin da aka yi mata. Nan take ta yi
godiya, sannan ta mike ta tafi gida da sauri zuciyarta cike da farin ciki.
Da zuwa Ishmira gida ba ta tsaya ko'ina
ba sai cikin turakar, mahaifinta inda ake ajiye
bako. Da shigartka cikin dakin ta iske bako a
kwance kamar yadda ta tafi ta bar shi, kuma har yanzu barci yake bai farka ba. Ishmira ta kurawa
fuskar bako idanu, nan take ta ji ta fara Jun
Kaunarsa a ranta sai ta yi sauri ta kau da kanta
ga barin kallonsa, sannan ta yi sauri ta fice daga
dakin. Abin da ba ta sani ba shi ne mahaifiyarta
Falira na rakabe a can gefe daya tana kallonta,
kuma ta ga sa'adda Ishmira ta kurawa bako
idanu tana ta kallonsa. Al'amarın da ya bai wa
Falira matukar mamaki kenan, domin ba ta taba
gani wani da namiji da ya taba burge Ishmira
ba, sai wannan bako.
A cikin gaba dayan 'yanmatan dake cikin
wannan kauye na Madinatul Ansal babu wata
budurwa mai kyau da farin jinin Ishmira. Kusan
duk samarın garin sun nemi soyayyarta, amma
taki ba su hadin kai, al'amarin da ya fusata
mahaifinta kenan, har ma wata rana ya ce da ita
me take nufi da kin fitar da gwani daga cikin
samarinta, ko kuwa tana nufin ba za ta yi aure
ba ne, har abada, A lokacin ne Ishmira ta ce ya
kai abbana ka yi sani cewa ina son na yi aure
amma sai na ga saurayin da ya kwanta mini a
rai, ka yi hakurI a yanzu, domin duk samarin da
ke gari nan banga wanda na ii ina so ba. Abul Ishmira ya daka mata tsawa ya ce ai wannan
maganar banza ce, ya za ai a ce duk yawan
samarin garin nan baki ga wanda kike so ba. To
yaushe ne kuwa za ki ga wanda kike so alhalin
baki basa shigo mana, kuma muma ba ma zuwa
ko'ina."
Ishmira ta ce,"Ya kai Abbana ka sani
cewa na yi istahara an nuna minj cewa nan da
wani lokaci kadan Allah zai kawo wanda zan
aura har cikin garin nan. Ni dai abin da nake so
da kai shi ne ka ci gaba da rike alkawarin da ka
yi mini tun iya yarinya cewar ba zaka aurar da
ni da ba sai ga zabina."
Da wannan kalami ne jikin Abul Ishmira
ya yi sanyi. Daga wannan rana bai kara yi mata
maganar aure ba, kawo I yanzu.
Kashe gari da Asuba bayan an idar da
sallar Asuba sai Abul Ishmira ya shigar da
Ishmira cikin wani daki ya zaunar da ita, sannan
da
ya kawo Alkur'ani ya ba ta ya ce, 'Sai ki kama
karatu, don amsa hukunci. Na hore ki da kada ki
saurara face kina da bukatar abinci ko zuwa
kewaye har izuwa faduwar rana."
Ishmira ta karbi Alkur'ani fuskarta cike da murmushi ta ce, 'An gama ya Abbana."
Nan take ta kama karatu cikin zazzakar
muryarta mai dan karan dadin sauti. Shi kuwa
Abul Ishmira sai ya tafi turakarsa ya zauna ya ci
gaba da lazumi har gari ya waye, sosai rana ta
hudo. A lokacin ne Farila ta shiryo abincin
kalaci ta kawowa Abul Ishmira ta ajiye a
gabansa. Har ta juya za ta fita sai ya kira
Sunanta ya ce, "Ina labarin bakon mu shin ya
farka daga barci ne?"
Farila ta ce, 'Ya farka, amma da kyar ya
iya mikewa zaune."
Ya yi magana kuwa, kuma ya ci abinci?"
"Ko kala bai ce ba, amma ya ci abinci dan
kadan shi ma sai da aka dura masa a baki.
Babban abin da ya bani mamakı a gare shi shi
ne na ga yana ta kallona yana zub da hawaye,
kuma yana ta kallon yanayin gidan nan. Babu
yadda ban yi ba da shi akan ya yi mini bayanin
dalilin zubar hawaye a idanunsa amma ya ki yai magana. Koda jin wannan batu sai Abul Ishmira ya yi
ajiyar zuciya, sannan ya ce, 'Kada ki kara
tambayarsa komai, zai fi kyau mu ci gaba da Jinyarsa har izuwa tsawon kwana bakwai mu
gani wata kila sai ya warware sosai, sannan zai
iya yin magana idan har shi ba kurma ba ne."
Daga wannan rana Farila ta ci gaba da
jinyar bako tamkar dan cikinta, bayan ishmira ta
gama horon karatun Alkur'ani na kwana uku sai
ta karbi aikin jinyar bako ta ci gaba da yi masa
hidima ya zamana dare da rana suna tare babu
abin da ke raba su face kwanciyar barci. A
yammacin rana ta shida ne Ishmira ta samo
sanda ta bai wa bako ya rike sannan ta kama
kafadunsa ta tashe shi tsaye ta umarce shi da ya
dogara sandar ya yi tafiya. Da kyar da sidin
goshi yana zufa ya daga kafarsa guda ya yi taku
uku. Saboda tsananin zafin da yake ji a kafar
tasa sakamakon raunikan jiki har sai da ya
kurma ihu, sannan ya sulale kasa zai fadi.
Ishmira ta rugo da gudu ta ruke shi, sannan ta
zaunar da shi akan kujera, suka kurawa juna
idanu tana mai matukar tausayinsa. Al'amarin
da ya jefa shi cikin mamaki kenan, domin har
kwalla ce ta zubo mata. Ishmira ta yi murmushi
a gare shi ta ce, "Ka yi hakuri dole ne ka daure
ka ci gaba da jarraba tafiya, in ba haka ba kuwa jijiyoyin kafar taka za su lalace, su daina aiki.
Daga yau kullum za ka dunga yin tafiya taku
uku." Bako ya jijiga kansa cikin alamun
amincewa gami da yin murmushin yake.
Kamar yadda Ishmira

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment