Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rigingimu za su balle a cikin gidan nan da cikin majalisata. Yaki zai barke za'ayi asarar miliyoyin rayuka da dukiya, kuma
daya daga cikin ku ba zai sami damar gadona
ba, face kun yi abu guda. Wannan abu kuwa shi
ne ya zama wajibi a gareku ku 'ya'yana, wato ku
takwas din nan ku yi shiri a ranar da aljalina ya
Cika ku tafi izuwa Dajin Mutuwa, domin ku
SamO wadansu abubuwa gudu uku wadanda da
Su ne za ku hada wani magani wanda in
dai
kuka zuba shi a cikin kogin birnin nan ba za a yi
tashin hankali ba, kuma ba za a yi asarar rayuka
da dukiya ba, kuma tabbas sai daya daga cikin
ku ya gajeni, Wadannan abubuwa uku da za ku
samo a Cikin dajin mutuwa sun hada da
hawayen wani tsohon rikakken kure, wanda ya
shekara tamanin da bakwai a duniya, duk duniya
babu wani kure mai karfi da shekaru tamkarsa.
Abu na biyu shi ne za ku ciro kwayar idanun
wani, batoyi, Wanda ya shekara dari da uku a
duniya, Shi dai wannan batoyi girmansa yafi na gwiwa Sau goma kuma girman fukafukinsa guda
ya ninka gangar, Jikinsá, Yana iya yin tafiyar
kwana saba in, a sararin 'sama ba tare da ya gaji ba, kO ya bukaci abinci, ko ruwän sha. Idan ya fara fesar da wuta daga bakinsa sai ya kwana
bakwai bai saurara ba. Kwayar idon nasa guda
daya ce jal manne a tsakiyar goshinsa. Yanan
ya surar giwaye goma da kafafuwansa guda
biyu a lokaci guda ya kai su shekar ya'yansa su
Cinye. Ya zama dole ku ciro kwayar idon
wannan batoyi ku hada da wancan hawaye na
tsohon rikakken kure. Abu na uku wanda shi ne
na karshe dole ne ku samo ruwan wani koggi
wanda ake kira Bahar Shufa adadin cikin salka
guda.
Kogin Bubar Sufa yana nan a can karshen
Dajin Mutuwa. Asalin kogin mahada ce ta
dukkanin tekunan duniya. Shi dai wannan kogi
ruwan cikinsa ya kasance mai tsananin haske,
kamshi, da dadin dandano. Komai dattin ruwa
in dai aka zuba digo daya na ruwan Bahar Shufa
a cikinsa sai ya tsaftace shi, kuma ya kashe
dukkanin cutar da ke cikinsa. Idan mutum ya
sha digo daya na wannan ruwa har abada ba zai
sake jin kasala ba a jikinsa kuma zuciyarsa za ta
zam fari kal ko yaushe ba shi babu bakin ciki ko
da kuwa duniya za ta taru ta kishi.
Yayin da kuka sami nasarar hada wadannan abubuwa uku kuka dawo gida tarc da
Su shi kenan bukata za ta biya baya, kun zuDa
abubuwan a cikin kogin birnin nan.
Lokacin da sarki Sharudul Amman ya zo
nan a Zancensa sai gaba dayanmu muka zazzaro
Idanu, hankalin mu ya dugunzuma fiye da
koyaushe. Babban cikin mu wato Mukairu ya
dubi sarki a nutse ya ce, "Ya kai Babanmu
hakika ka zo mana da babban al'amari wanda ya
fi karfinmu. Shin ka manta ne cewa bokan da ya
ZO mana ya ce ba a shiga Dajin Mutuwa yake,
haka kiima shi ne dajin da ke dauke da dukkanin
masifun dunIya. Ta ya ya za mu iya zuwa
daji har mu iya samo wadannan
abubuwa uku kuma mu fito daga cikinsa lafiya?
wannan
Lallai wannan daji ya ci sunansa Dajin Mutuwa.
Koda mun sami damar shigarsu duk hallaka za
mu yi dayan mu ba zäi dawo a raye ba. Gwara
ma mu zauna a gida duk masifar da za ta zo ta
Same
Lokacin da Mukairu ya zo anan a zancensa, sai
sarki
Sharudul Amman ya ce, "Kaicon namiji
matsoraci mai zuciyar mata. Ya kai Mukairu
hakika ka tabbata ragon maza. Ina son ka sani Cewa matsoraci ba shi zama gwani, har abada.
Kuma faduwar gaba asarar namiji ce. Bugu da
kari ba a samun duniya a banza dole sai an sha
wuya. Nima nan da kuka ganni akan karagar
mulki ba a banza na samu ba, sai da na sha
bakar wuya kamar ba zan yi rai ba. Ina son ku
karfi zukatanku kusa a ranku cewa mai nema
yana tare da samu, kuma da dai ku mutu
ragwage gwara ku mutu a matsayin jasruma1 ko
a tarihi ba a mantawa da ku ba. Idan ba ku
manta ba aljani boka Sahibul Furrati ya ce ya zo
ne ya bani gudunmuwa don kyautata bayana to
ku sani ba komai ba ne gudunmuwar tasa face
ya dauki alkawarin zai taimaka ya saku akan
hanyar da za ku isa Dajin Mutuwa, amma fa ba
zai ceci rayuwasr mutum daya daga cikin ku ba.
Sai dai kowa tasa ta fusshe shi, amma duk da
haka ya ce na shaida muku cewa wanda duk ya
yi abu uku daga cikin ku lallai zai iya shiga
Dajin Mutuwa ya fito lafiya.
Abu na farko shi ne hakuri, na biyu rike
gaskiya da amana. Abu na uku kaunar dan'uwa
kamar yadda za ka kaunaci kanka. Wannan shi
ne iyakar bayanin da zan iya yi muku dangane jinyarsa dare da rana. Duk sa'adda muka tuna
cewa sa ura kwanaki kadan mu rabu da sarki har
abada sai mu kama kuka, shi kuwa sarki sai va
yi ta rarrashin mu yana ba mu baki gami da kara
mana kiwarin gwiwa bisa jajurcewa wajen
mu yi
nemann samun nasara a tafiyar da za mu yi
bayan aj alinsa.
A ranar da kwanaki talatin suka cika cif
sai rai ya yi halinsa, wato sarki Sharudul
da
Amman ya mutu. Nan take gida ya cika da
koke-koke. Cikini kankanin lokaci labarin
mutuwar sarki ya ba zu ko'ina a cikin birnin
Farisa. Cikin kankanin lokaci babban birnin ya
cika da jaina'a makil aka shiga jana' 1zar sarki
Bayan an kammala bikin binne sarki sai
dukkaninmu ya'yansa mu takwas muka taruu a
waje guda inuka sa aka kirawo mana gaba daya
yan majalisar kasar suka zo. lyayen mu mata
kuma nan zaune a gefe guda. Bayan yan
majalisar sun gama hallara sai Mukairu ya mike
tsaye ya gaishe su, sannan ya sanar da su
wasiyar da sarki ya bar mana ta batun tafiya,
na zuwa Dajin Mutuwa don samo wadannan
abubuwa guda uku masu wuyar gaske don
don magance masifar da za ta barko kasar nan gaba,
kuma a fitar da sarki daga cikin mu. Ko da gama
wannan jawabi sa 'yan majalisar suka bushe da
dariya gaba dayansu lokaci guda sunan cewa, ai
wannan zanccn banza ne Yama za a yi a ce za
mu iya zuwa dajin mutuwa har waninmu ya
dawo a raye alHalin bokayen duniya sun
tabbatar da cewa babu wani mahaluki da ya san
inda Dajin Mutuwa yake, bare ma ya shige shi.
Nan dai suka watse suka bar mu suna ta
yi mana dariya. Tafiyarsu ke da wuya sai muka
yi sallama da iyayenmu mata suna kuka, muna
kuka. Muka rabu. Nan take muka kwashi
guzurinmu kowa ya kama dokinsa ya hau muka
bar cikin Farisa muka nausa daji ba tare da sanin
inda muka dosa ba.
Tun da muka fara tafiyar ko yaushe ina
manne da dan'uwana Salkuf, ba ma yarda mu
rabu. Su kuwa su Mukairu sai suka hada kansu
su shidan suka ware daga cikin mu basa yarda
mu jera tare. sai dai ya zamana cewa ko suna
gabanmu ko kuma suna bayanmu. Haka kuma
sai suka ki yar da mu ci abinci tare da su, kai ko
hira ma basa yarda su yi tare da mu kuma ba sa kwanciya a kusa da mu a duk lokacin da muka
yada zango. A takaice dai sun kyamace mu fiye
da kima. Ganin yadda 'yanmunmu ke nuna
mana tsana, sai hankalinmu ya tashi, muka rasa
abin da ke mana dadi, amma haka dai muka
rungumi kaddara, dan babu yadda za mu yi
Sai da muka kwana arba'in da daya muna
ta keta dazuzzuka ba tare da sanin inda muka
dosa ba, kuma ba mu riski wani gari ba, haka
kuma ba mu hadu da wani mugun abu ba. Da
yammacin kwana na arba'in din ne muka iso
wani surkuki mai wuyar wucewa. Shi dai
wannan wuri ya cika manyan ramuka da
manyan duwatsu wanda da kyar dawakanmu ke
iya ketarewa. Ashe abin da ba mu sani ba shi ne
wannan wuri wasu 'yan fashi ne ke amfani da shi
wajen dana tarkon kama fatake. Sa'adda muka
iso tsakiyar surkukin kawai sai muka ji mun
rufta cikin ramuka damu da dawakanmu gaba
daya. Kafin mu yi wani yunkuri an jefo mana
wadansu
raga ta lullube mu sai ga gungun wadansu
yanfashi kimanin su dubu sun kewaye mu
kowannensu na ruke da muggan makanai. Su
dai
dai wadannan 'yanfashi sun kasance karti
majiya karfi masu girma da ban tsoro.
Koda Suka kare mana kallo suka lura da
irin tufafin da ke jikin mu, irin na sarauta da
kuma dukiyoyin da muke dauke da su da guzuri
mai yawa sai suka cika da farin ciki suka hau
dariyar mugun ta. Ni da Salkuf sai muka kamu
da tsananin tsoro jikin mu ya kama kyarma
dama ga shi mu ne mafi kankanta, domin su
Mukairu sun fi mu girma da rashin tsoro. Abin
da
yafi ba mu mamaki shi ne lokacin da
yanfashin suka rutsa mu sai muka ga ko kadan
babu alamar damuwa a fuskokin su Mukairu.
Maimakon ma su tsora ta sai suka kama
murmushi. Shi kansa shugaban yangashin sai
mamaki ya kama shi ya ce,
"Ku wadannan mutum shidan me kuke
takama da shi har da ba za ku ji tsoran mu ba,
kamar yadda yanuwanku su biyu suka firgita da
ganin mu?"
Ko da jin wannan tambaya sai Mukairu
ya bushe da dariya ya ce, "Ai mu mun san ba ku
isa ku yi mana komai ba, sai dai ku yi wa
kannanmu. Kawai za ku bata mana lokaci ne a
mu."
banza
kun
ga
tafiyar Gama fadin hakan ke da wuya sai su Mukairu
suka bace bat da su da dawakansu da duk
dukiyarsu ya zamana cewa saura ni dá Salkuf
kadai a cikin ramin. Nan fa tsoro ya kama
'yanfashin da mu. 'Yanfashin suka ba zama
neman su Mukairu a cikin dajin, amma ko
duriyarsu ba su ji ba. Da suka gaji da nenman su
sai suka dawo gare mu suka fito da mu daga
Cikin ramin nan suka kwace mana dawakanmu
da dukkanin kayanmu da guzurinmu. Kai hatta
rigunan jikin mu sai da suka kwace, sannan suka
daka mana tsawa muka firgice muka ruga cikin
dawa. Hakan nan muka ci gaba da tafiya cikin
tsananin takaici da bakin ciki ga shi kafafunmu
ko takalma babu muka yi ta taka kaya da tsidau.
Kafin ajima duk kafafun mu sun yi fatu-fatu da
jini. Haka dai muka daure muka ci gaba da
gaba
tafiyar ba mu san inda muka dosa ba, kuma ba
mu san yadda rayuwar mu za ta kasance ba.
Idan muka tuno yadda 'yanuwan suka guje mu
suka bar mu a cikin masifa don mu hallaka sai
takaici ya turnuke mu mu kama kuka.
Haka dai muka wanzu muna ta tafiya a
daii har izuwa lokaci mai tsawo. A sannan ne
yunwa da kishirwa suka kama mu ya zamana
Cewa mun fara tafiyar sarsarfa muna yanke jiki
muna faduwa. Nan fa muka hanga gaba da
yamma, kudu da arewa, amma ba mu ga alamar
abinci ba, ko ruwan sha. Al'amarin da ya kara
dugunzuma hankalin mu kenan don mun
tabbatar da cewa in muka ci gaba da tafiya a
haka tabbas za mu hallaka. Kawai sai muka
kwanta kasa muka kurawa juna idanu muna zub
da hawaye. Salkuf ya dube ni ya ce, "Ya kai
dan' uwana idan na rigaka mutuwa a wannann
wuri ka rungume gawata a jikinka har naka
ajalin ya riskeka. Nima idan kai ne ka rigani
mutuwa abin da zan yi kenan, domin kada wani
abu ya zo ya raba mu. Fatana ko da tsuntsaye ne
za su tsatstsage rhu uto su tsatstsage mu a lokaci
guda"
Yayin da na ji wannan batu sai na fashe
da kuka na ce, "Ya kai danuwana me ya sa kake
batun mi uwa tun a yanzu alhalin har yanzu
muna iya yin numfashi kuma muna iya motsa
idanuwanmu da hannayenmu Shin ka manta da
wasiyar Babanmu ne? Lallai ya ce mu karfafi
zuciyar mu da samun nasara bisa abin da muka fito nema. Har ko yaushe bana fitar da
tsammanin cewa duk bala'in da muka shiga za
mu fita daga cikinsa. Lallai mu rungumi hakuri,
Juriya, gaskiya da amana da sannu za mu ga
Waraka,"
Lokacin da na zo nan a zancenna sai na
ga idanun Salkuf suna wurkilawa alamar cewa
yana suma. Nan take na dimauce na mike zaune
dakyar na rungume shi a kirjina na fasahe da
matsanancin kuka ina mai cewa, "Kar ka tafi ka
barni ya danuwana. Lallai idan ka mutu ni ma
begenka ne zai kashe ni. Haka dai na wanzu ina
ta surutai ina girgiza Salkuf wanda ya zautu har
murya ta dashe. Daga nan kuma sai na ji jiri na
diba na, take ji da ganina suka dauke ban san
abin da ya biyo baya ba.
Ba zat0, ba tsammani sai na farka na
ganmu mu biyun kwance a kan jaki,
mutum matashi na jan jakin, ya nufi wani kogon
dutse. A wannan lokaci idanuna nan budewka
da rufewa da kyar kuma ban daina jin jiri ba.
wani
Haka dai na saduda har wannan matashi ya isa
damu kofar kogon dutse. Da zuwa sai ya wata
mace tare da yarta kyakkyawar yarinya 'yar
Klmanin shekara goma sha biyu, sun rugo gare
mu. Da zuwansu sai matar ta dubi matashin ta
ce, "Maigida wadannan samarin fa a ina ka
samo su shin matattu ne ko da ransu"
Matashin ya ce, "Ai da ransu, amma suna
bukatar taimakon gaggawa. Ina tsammanin dai
yan fashi ne suka tarba su, tausayın su na ji shi
ya sa na yi tunanin ceton rayuwarsu kuma na
kare
musu kallo na fahimci cewa 'ya'yan
manyan mutanene. Maza ku taimaka mini mu
shigar da su ciki."
Ba tare da gardamar komai ba, matar da
'yarta suka ciccibeni suka shigar da ni cikin
kogon dutsen, shi kuwa matashin sai ya saba
Sulkufa kafadarsa ya shiga da shi cikin kogon.
Nan take suka kwantar da mu suka yayyafa
mana ruwa muka farfado. Ko da ganin mun
farfado sai matar ta dauko madarar shanu mai
dumi a cikin koko ta ba ni na sha da yawa,
sannan ta bai wa Salkuf shi ma ya sha ya koshi.
Mu dai in ban da kallon su babu abin da muke
yi muna masu mamakin yadda aka yi muka tsira
da rayuwar mu. Bayan mun dawo cikin
hayyacin mu matashin ya dube mu ya ce,
Ya ku wadannan samari mene nc labar
ku kuma wane tsautsayi ne ya shigo da ku cikin
wannan daji mai tsananin hadari?
Koda jin wannan tambaya sai na yi ajiyar
zuciva na kwashe labarin mu kaf tun daga farko
na zayyane masa tun daga lokacin da muka baro
gida kawo Zuwa sa'adda muka fada tarkon
'yanfashi, yanuwanmu su Mukairu suka gudu
suka bar mu. Sannan kuma na sanar da shi batun
tafiyar mu izuwa Dajin Mutuwa don samo
wadannan abubuwa guda uku kamar yadda
mahaifin mu ya bar mana wasiya.
Lokacin da na gama ba shi wannan labari
sai muka ga ya kawo gwauron numfashi ya
ajiye, sannan ya sake duban mu da kyau cikin
nutsuwa ya ce, "Samari hakika kun sha wuya, to
amma fa ku sani cewa wannan wuya da kuka
sha ba komai ba ce face somin tab1 akan wacce
za ku sha a nan gaba. Ni din nan da kuke ganina
nna kasance maharbi kuma a cikin kogon nan
aka haife ni, haka ma mahaifina har ma kakana.
Wannan sana'a ta farauta na yi gadon ta ne tun
Iyaye da kakanni, kuma sai da ya zama na cewa
duk duniya babu wani mafarauci wanda ya fi kakana sanin sirrikan daji da kuma yawo a cikin
dazuzzukan duniya, amma shi kansa ya taba ba
ni labari sa'adda nake yaro cewar yana son ya je
wani daji wanda ake kira Dajin Mutuwa, amma
ya rasa a inda wannan daji yake, kuma ya
ziyarci bokaye, sama da mutum dubu; amma bai
Samu wanda zai iyà sa shi a hanyar da zai Je
Dajin Mutuwa. Kamar yadda kuka ba ni labarin
wadannan abubuwa uku da za ku samo a can
ndajin mutuwa haka shi ma ya wasafa mini su.
A fadarsa ya ce duk wanda ya mallaki
wadannan abubuwa uku ya zuba su a cikin koko
Suka gauraye ya kurba ko da makurwa daya ne
sai ya zama mashahurin sarki, wanda ba a taba
yin kamar sa ba a durniya.
Atakaice dai ina tabbatar muku da cuwa
akan wannar. buri na neman Dajin Mutuwa
kakana ya hallaka, haka ma mahaifina. Ni kuwa
ban yarda na bi ra' ayinsu ba, amma na dace da
samun Sirrikansu na tsari da sanin sirrin daji,
don haka na hakura na yi zamana a wannan
daji tare da iyalina na gwanmace na yi ta Zama
haka har karshen rayuwata. Wannan ita
ce matata sunanta Sazira, wannan kuma yar mu ce ana kiranta da suna
Amshira.
Yaku
wadannan samari ku sani cewa wannan aiki da
ke gabanku daidai yake da tafiya neman jaki
kara
mai Raho, amma duk da haka ina mai kara
muku kwarin gwiwa domin sa'a na ga mai rabo
babu mamaki ku dace ku sami nasara. NI kam
zan ba ku tawa gudunmuwar ta neman tsari daga
sharrin 'yanfashi da muggan aljanu da kuma
muggan dabbobin dawa. Haka kuma zan koyar
da ku yadda ake ratsa daji a fahimce shi, don
sanin sharrinsa da hadarinsa, amma dole ne ku
zauna tare da ni tsawon kwana goma sha hudu,
domin samun ilmin.
Bayan nan zan rakaku har izuwa iyakar
wannan daji inda na saba raka iyayena da suka
shude, kuma inda mukan tsaya mu yi bankwana
a duk sa'adda za su tafi neman Dajin Mutuwa."
Yayin da muka ji wannan batu sai murna ta
kama mu, mu ka yi ta yi masa godiya. Daga
bisani sai na dube shi na ce,Yakai wannan
mafarauci ka sani cewa ka gabatar da iyalinka a
gare mu, kuma ka ba mu takaitaccen tarihinka
da na iyayenka, amma har yanzu ba ka fada
mana sunanka ba. KO da jin wannan batu sai ya murmushi ya ce, sunana Maruful Haz."



DAJIN MUTUWA
littafi na daya 1
Na Abdulaziz Sani M gini
Typing - Shuraihu Usman
Part 1D.
Daga wannan rana muka zauna tare da
Maruful Haz, kullum sai mun fita farauta tare da
shi yana nuna mana Sirrin dajin, kuma yana ba
mu sirrikan neman tsari iri-iri. Sannu a hankali
muka kware a sanin sirrin daji, kuma muka sami
tsari mai yawa. A cikin kwanakin goma sha
hudun ne ni da Amshira yar Maruful haz'muka
shaku ainun har takai cewa idan muka fita
farauta ba ta iya cin abinci har sai ta jira ni na
dawo mun ci tare, kai tun muna soyayyar sirrance a
zuciyoyinmu har abu ya fito fili iyayen Amshira
da danuwana Salkuf suka fahimci abin da ke
wakana
Da muka cika kwana goma sha hudu tare
da mafarauci Maruful Haz, sai ya shirya mana
guzuri isasshe ya ba mu sutura, takalma da
makamai na kare kai, sannan ya ce mu tashi mu
tafi ya yi mana rakiya izuwa iyaka. Yayin da
Amshira da Sazira suka ga mun mike za mu tafi
muna masu yi musu bankwana sai suka fashe da
kuka, saboda shakuwa da kuma sabo. Amshira
ta mike da sauri ta dubeni sosai muka kurawa
Juna idanu muna zub da hawaye, har 1zuwa dan lokaci, Sannan ta ce"Ya kai masoyina ka yi
Sani cewa babu abin da zai iya raba masoyi da
masoyinsa a duniya face mutuwa. Zan kasance
mai zuba ido da sauraren dawowarka daga yau
har izuwa lokacin tsufana. Duk da na san cewa
duk wanda ya tafi Daiin Mutuwa baya dawowa,
amma ni ina sa ran cewa kai za ka dawo komai
daren dadewa. Ka kasance mai ruke alkawari
kada ka manta da ni har abada lalla ka biyo ta
wannan daji ka daukeni ka tafi da ni kasarku, in
dai ba ka rasa rayuwarka ba a can Dajin
Mutuwa, domin na zamo abokiyar rayuwarka.
Ka sani cewa nina anan dajin aka haife ni ban
taba ganin wasu mutane ba a rayuwata face
ivayena da ku Gashi jinina ya hadu da naka ina
kaunarka, kamar yadda nake kaunar iyayena,
don haka na san cewa idan babu su kai kadai ne
za ka iya debe mini kewarsu."
Yayin da Amshira ta zo nan a zancenta,
sai na share hawayen idanuna na damke dubeta
da kyau na ce, Ya ke masoyiyata kiyi sani cewa
na dauki alkawari komai wuya komai rintsi, in
dai ina numfashi a dorOn kasa komai dadewa sai
na dawo nan na dauke Ki, mun tafi tare izuwa kasar mu. Haka dai muka yi bankwana da su
Amshira muna kuka suna kuka, muka tafi muka
bar su nan a tsaye bakin kogon dutse, tun suna
hangenmu muna daga musu hannu har muka
bace musu da gani. Shi kuwa maharbi Maruful
Haz, sai ya ci gaba da yi mana jagora muka yi ta
tafiya a cikin daji. Mu kwana nan mu tashi can
har muka shafe kwana goma, sannan muka iSO
iyaka. Da zuwa sai Maruful Haz ya tsaida mu ya
ce,
"To anan ne zan rabu da ku inan ma yi
muku fatan nasara bisa wannan tafiya da ke
gabanku, haka kuma ina dada yi muku tuni da
ka da ku manta da kiiyaye abubuwan nan uku,
wato; hakuri, juriya, gaskiya da amana. Sannan
ko da za ku hadu da 'yanuwanku nan gaba ku so
su kada ku saka musu da abin da suka yi muku a
baya. Tabba in kuka yi haka za ku iya samun
nasara bisa abin da kuka fito nema. Magana ta
da ku ta karshe ita ce ina son na roke ku wata
alfarma guda daya."
Cikin muka dubi Maruful Haz, na ce,
"Fadi bukatarka kowacce irii ce in dai muna da
iko tabbas sai mun biya maka ita." Yayin da Maruful Haz ya ji haka sai
idanunsa suka ciko da kwallah ya ce, "Ina son
ku gafarce ni idan na saba muku a lokacin da na
zaunan da ku, domin nasan cewa abu ne
mawuyaci ku dawo ku riskeni a raye
Koda ganin zubar hawayen Maruful Haz
da kuma jin wannan batu nasa sai hankalin mu
ya dungunzuma muma muka fara hawaye. Na
dube shi cikin tsannanin tausayiu da damuwa na
ce, "Ai mu a zamanmu da kai babu abin da za
mu ce sai godiya. Kai kuwa menene dalilin da
ya sa ka ce ba lalai ba ne mu dawo mu riske ka a
raye ba?"
Maruful Haz ya yi ajiyar zuciya, sannan
ya ce, "Dalilin da ya sa kuka ji na fadi haka shi
ne idan har za ku sami nasarar shiga Dajin
Mutuwa har ku fito lafiya a kallah sai bayan
shekara goma. A yanzu haka wani boka ya
tabbatar mini da cewa ba zan shekara goma ba a
duniya. Lallai wannan shi ne ganina da ku na
karshe. Ya kai Shafaru idan kun dawo daga
Daiin Mutuwa a raye ka cikawa 'yata alkawari
ka zo ka dauketa ka tafi da ita kasarku ta zamo
abokiyar rayuwarka." Koda gama wannan jawabi sai muka
rungume Maruful Haz gaba dayanmu muka
fashe da kuka ina mai cewa, Lallai zan kasance
mai cika alkawari."
Sai da muka shafe sama da rabin sa'a a
tsaye rukunkume da juna muna kuka, sannan
muka rabu. Maruful Haz ya juya da baya ya tafi
abinsa muma muka nausa gaba ba tare da sanin
inda muka dosa ba.
Haka dai muka ci gaba da tafiya a dajin
kwana nan mu tashi can. Da yake wannan karon
mun san sirrin daji ko kadan babu tsoro da
fargabar komai a zukatanmu. Duk abin da muka
gani akan hanya mun san irin abin da zamu iya
haduwa da shi a wajen don haka sai mu dauki
mataki. Kai ko rami muka gani mun san irin
dabbar da ka iya buya a ciki, kuma ko tarko
muka gani na yanfashi muna iya ganewa. Da
yake ma muna tare da tsari mun sha giftawa ta
gaban yanfashin amma ba su da ikon ganınmu
saboda muna tare da wasu layun sihiri wadanda
Maruful Haz ya ba mu.
Kwanci tashi, sai da muka shafe kwana
casa'in muna tafiya a daji ba mu hadu da komai ba, kuma ba mu ji ko duriyar yanuwan mu ba
su Mukairu.
A ranar da muka cika kwana casa'in ne
muka hango wani tafkeken gida a tsakiyar dokar
daji, wanda aka gina shi da zallan Jauhar. Koda
ganin wannan gida sai muka cika da tsananin
mamakin yadda aka yi aka yi shi kuma muka
shiga tunanin mutane ne a cikinsa ko aljanu?
Nan fa muka tsaya muna shawarar mu je ga
wannan gaida ko kuwa mu ratse hanya mu
kewaye shi. har ta kai mu da yin gardama ni ne na
dage akan cewa sai mun je mun ga abin da ke
ciki, shi kuwa danuwana Salkuf sai ya dage
dage
akan cewa lallai ba za mu je ba, don kada mu
kai kan mu ga hallaka. A karshe dai sai na
rinjaye shi da na ce da shi,
"Kar ka manta fa cewa matsoraci ba shi
zama gwani har abada."
Yayin da Salkuf ya ji wannan batu, sai ya
yi murmushi ya ce, Shi kenan na amince mu je
kawai.
Ba tare da fargabar komai ba na wuce
gaba yana biye da ni har muka je bakin kofar
gidan. wanda muka isketa a rufe. Kawai sai na kwankwasa kofar, shiru ba a amsa ba. Na sake
kwankwasawa aka sake yin shiru. Na kama
kofar na girgiza ta na ji ta a bame tam. Kawai sai muka ja da baya muka taho da gudu muka sa
dukkanin karfin mu muka banke kofar da
kafafunmu. Take kofar ta balle ta burma ciki
kai tsaye muka kunna kai cin gidan. Da shigar
mu sa muka yi arba da kwarangwal na sassan
bil'adama a zube tsubi-tsubi. Al'amarin da ya
firgita mu kenan, amma sai muka kanne muka ci
gaba da tafiyar har muka iso kofa ta biyu. Ita ma
wannan kofa a rufe take sai da muka banketa da
karfi, sannan muka shiga cikin wani bangare
dabam, inda muka iske dukiyar lu'ulu'u, zinare,
jauhar,, yakutu, da murjan1, ga sunan kamar
tulin duwatsu a banza babu mai tsaronsu. Nan
ma sai muka cika da mamaki. Haka dai muka ci
gaba da tafiya ba tare da mun taba komai ba, har
muka iso kofa ta uku. Da zuwanmu bakin kofar
muka jiyo koke-koke cikin murya irin ta
mutane.
Koda jin haka sai muka yi sauri muka
barke wannan kofa muka afka ciki. Da shigar
mu muka yi arba da 'yanuwanmu su Kumairu a daddaure cikin sarkoki suna ta rusa kuka. Gaba
daya jikinsu ya sha dukan bulala ya farfashe sai
Jini ne ke zuba. Dukkaninsu sun yi baki sun
rame matuka, in ba don ma suturar da ke jikinsu
ba, ba za mu iya gane su ba. Cikin matukar farin
Ciki suka dube mu suna masu cewa,
"Marhaban da ku 'yanuwa ku yi sauri ku
kwance mu mu tsira gaba daya kafin maridan
nan su dawo su iske

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment