Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hagu an bar hanya a tsakiya wacce
Shafaru zai bi don kowa ya ganshi.
Lokacin da labari ya riski sarki cewa
mutanen garin da sun rude da kaunar Shafaru
kowa na son a fito dashi a ganshi sai hankalin
Hamaru ya dugunzuma ya fara tunanin kada fa
mutane su kawo matsala bisa wannan wasika da
ake son lallai Shafaru ya danganata ga boka
Shamakalu.
Lokacin da fadawan sarki suka fuskanci
haka sai wazirinsa wanda ake kira Hannamu ya
dube shi ya ce"Haba ranka ya da de yaya kai da ka ke da dakaru har zaka yi shakkar wani abu,
abin da za;ayi kawai a fito da dakaru su jeru a
layi a gaban jama'a tun daga bakin kurkukun har
izuwa kofar gidan boka Shamakalu duk wanda
ya kawo rudani a kaddamar da shi kawai."
Ko da jin wannan batu sai murna ta kama
sarki Hamaru ya ce "Kwarai kuwa ka zo mini da
mafita."
Nan da nan cikin kankanin lokaci aka
baiwa dakaru umarni suka fito cikin shiri suka
jeru a layi kamar yadda aka tsara. Al'amarin da
ya tsorata mutanen gari kenan kowa ya shiga
taitayinsa. Bayan an gama wannan shiri sai aka
tura aje a fito da Shafaru da ga cikin kurkuku.
Sarki ya bada umarnin a daurawa Shafaru
sarkoki a wuya da hannu da kafafu don tabbatar
da tsaro ka da ya sami damar guduwa har sai ya
kai wannan wasika zuwa ga boka Shamakalu.
Ai kuwa haka al'amarin ya kasance sai
gashi an fito da Shafaru a daddaure cikin sarka
ana jansa da karti har yana faduwa, sannan a
tasheshi ana dukansa da bulala su kuwa
mutanen gari sai yi masa jinjina suke, wasu na
Zub da hawaye don kaunarsa da tausayinsa.
wannan lokaci tsufa ya riski Shafaru da kyar ma
yake tafiya kuma fuskarsa ta cika da gashi da
gemu tai buzu-buzu.
Kafin a fito da Shafaru tuni tsegumi ya isa
cikin kurkukun cewa so ake a hallakashi ta hanyar
bashi wasikar raddi wadda zai kaiwa boka
Shamakalu kuma shi ma Shafaru ya ji wannan
batu amma ko kadan bai damu ba domin dama
rayuwar duniyar ta isheshi saboda bakin cikin
halin da ya tsinci kansa a ciki na wulakantashi
da akayi a matsayinsa na dan sarauta aka
kulleshi a kurkuku har tsawon shekaru ashirin
da daya kuma aka raba shi da iyalansa wadanda
ya kasance kullum a cikin begensu dare da rana
kuma bai san a halin da suke ciki ba a yanzu
walau suna raye ko sun mutu. A kullum ma dai
Zuciyarsa tafi aiyana masa cewa ba sa raye wata
kila tuni sarki Hamaru yasa an hallakasu.
Sa'adda aka fito da Shafaru daga kurkuku
da kyar ya iya bude idanunsa saboda rabonsa da
ya ga hasken rana yau shekara ashirin da daya
kenan, sannu a hankali ya samu ya bude idanun
sarai. nan take aka kawo wasikar raddi aka
danka masa a hannu, sannan aka tusa keyarsa aka fara tafiya da shi yana faduwa ana dukansa
da bulala yana mikewa da kyar.
Tun daga nesa tsohuwa Shabiratu da su
Humaila suka juyo hayaniyar jama'a na karuwa
alamar cewa an kusa isowa kofar gidan
Shabiratu da Shafaru. ko da jin hakan sai
Shabiratu ta mike da sauri ta kimtsa ta dauki
wannan sarka da Amshira ta bata ta nufi kofar
fita daga cikin gidan kawai sai ta ji Amshira ta
kira sunanta, cikin mamaki ta waigo ta ga ashe
da Amshira da Humaila duk kuka suke yi. Ko da
ganin haka sai hankalin Shabiratu ya tashi ta ce.
"Ina dalilin wannan kuka naku alhalin ina
gabda cika muki burinku
Amshira ta goge hawayen idanunta ta ce "Ya ke
wannan tsohuwa mai jin kai kiyi sani cewa ba
wani abu bane ya samu kuka face tunanin abu
biyu. Abu na farko shine idan muka rabu da ke
yanzu bami san irin halin da zaki shiga ba
domin aikin da muka baki na tattare da hadarin
gaske. Tabbas mun shaku dake ainun har muna
Ji a ranmu kamar ke jinin muce. Hakika rashinki
a tare da mu zai iya haifar da mummunan bakin
ciki a gare mu. Abu na biyu shine muna
mutuwar son mu sake ganin fuskar Shafaru a
karo na karshe, tunda mun sancewa wannan wannan ce
kadai damar da muke da ita tà ganinsa a
rayuwarmu.
Sa'adda Amshira ta zo nan a zancenta sai
tausayinta ya turmuke tsohuwa Shabiratu nan take
ta ji kaunar su Humaila ta karu nin kin ba nin
kin a cikin zuciyarta bata san sa'adda hawaye ya
zubo mata ba.
Cikin matukar tausayawa ta dubi Amshira
ta ce Abin da za'ayi ku rufe fuskokinku da
mayafi ku bar idanunku kadai a waje sai mu fita
tare ku tsaya a cikin jama'a domin kuma ku ga
Shafaru amma fa kada ku kuskura wani ya
shaidaku domin tabbas nasan cewa har yanzu
attajiri Abaiwu ibin Affan har yanzu ba zai fasa
farautar ku ba. Na san halinsa mutum ne mai
riko da neman daukar fansa. tabbas wannan ido
guda da ya rasa sai ya nemi ramuwa a kansa."
Amshira ta ce Lallai zamu kiyaye
Nan da nan Amshira da Humaila suka
mike da sauri suka dauki bakaken mayafai suka
rufe jikinsu gaba daya har da 'fuskokinsu, in
banda idanunsu babu abin da ake gani sannan sai tsohuwa Shabiratu tayi musu jagora suka fita
kofar gida suka tsaya a cikin cinkoson jama'a
yayin da hayaniya ta yawaita ana ta kallon
hanya don ganin karasowar Shafaru.
Duk inda mutum ya duba dakaru ne a
tsaitsaye suna ta tura mutane baya da karfin
tsiya, wani lokacin ma har dukan mutane ake
amma saboda nacin mutanen kowa yaki gusawa
saboda burin shiga gaba don ganin fuskar
yarima Shafaru.
Yayin da su tsohuwa Shabiratu suka ga
wuri ya cika makil da jama'ą ana ta turmutsutsu
babu halin su ratsa su shiga kan gaba inda
zasu iya tsayawa su ga Shafaru sai hankalinsu ya
dugunzuma suka rasa abin dake musu dadi. nan
fa suka tsaya suna tunanin mafita domin basu da
karfin da zasu iya kutsawa su shiga gaba. Suna
cikin wannan tunanin ne dabara ta fadowa
Shabiratu. Nan take ta kira wani babban
badakare ta jashi gefe daya ta kawo dinare mai
Yawa ta bashi ta ce bukatarta kawai yasa a buda
musu hanya su Uku su sami damar tsayawa akan
gaba inda za su yi arba da Shafaru. Yayin da
badakare ya ga Wannan dukiya sai ya rude ya cika da murna, nan take ya karbe dinare ya
Boye jikinsa ya ce.
An gama wannan aiki ku biyoni a baya.
Ko da suka iso cikin jama'a sai badakare
ya daga bulala ya sa duka bisa dole aka dare
aka bashi hanya ya wuce da su Shabiratu har ya
kaisu kan gaba suka sami wuri suka tsaya.
Faruwar hakan ke da wuya sai ga Shafaru an
taho da shi duk jíkinsa a daure da sarkoki ana
jansa yana tafiyar tatata saboda gajiya da tsufa.
Yayin da Humaila da Amshira suka hango shi
sai suka kura masa idanu suna masu zub da
hawaye.
Amshira ta ce da Humaila "Yake 'yata
tabbas wannan shine mahaifinki wanda aka
rabaki da shi tun kina da shekara uku a duniya.
Ni kam banyi tsammanin cewa zan sake ganinsa
ba a rayuwa ta, lallai masu iya magana sunyi
gaskiya da suka ce mai rai baya fitar da rai ga
samun rabo.
Duk wannan bayani da Amshira ke yi
ashe wani munafukin bawan attajiri Abairu ibini
Affan waishi Kumaz na tsaye daf da su yana
sauraro. Ko da ya ji haka sai ya sulale ya ruga can inda Abairu yake ya sanar da shi cewa ga
Amshira can da'yarta Humaila ya gansu a tsaye
suna son ganin Shafaru.
Ko da jin wannan batu sai murna ta kama
Abairu. Cikin hanzari ya tura aka kirawo masa
wasu hadimansa mutum biyar ya ce suje tare da
Kumaz ya nuna su Humaila. Duk yadda za'ayi
su yi ta bibiyarsu har dare yayi sannan su
kamosu a sirrance su kaisu can gidan
shakatawarsa na bayan gari. Nan take Kumaz ya
jagoranci wadannan hadimai su biyar suka tafi
Izuwa can kofar gidan tsohuwa Shabiratu inda
ya baro su Amshira.
Kash wani akasi da aka samu shine
lokacin da su Kumaz suka iso kofar gidan
Shabiratu sai suka iske cewa tuni a lokacin an
iso da yarima Shafaru dai dai wajen don haka
wajen ya dada hargitsewa har ma an cakuda
maza da mata. Haka kuma mata masu bakaken
mayafai suna da yawa a wajen kuma duk sun
rufe fuskokinsu don haka sai Kumaz ya kasa
gane su Humaila daga cikin wadannan mata.
Yayin da Humaila taga an zo za'a gifta da
Shafaru ta gabanta sai kawa ta kai hannu ta dafa kafadarsa. Ko da Shafaru ya ji mace ta dafa
shi sai ya juyo ya dubeta. Nan take kuwa suka
kurawa juna ido, ya tsaya cak a wajen yana
kallonta cikin tsananin mamaki domin ya ga
cewa idanunta iri daya ne dana matarsa
Amshira. bugu da kari sai ya ga hawaye na zuba
a idanunta al'amarin da ya jefashi cikin wasu-
wasi kenan ya ce a ransa anya kuwa wannan ba
yata bace Humaila? Har ya bude baki zai yi
magana da ita sai dakaru suka ingizashi gaba,
nan fa yayi ta waigenta ita kuwa tayi ta daga
masa hannu tana mai ci gaba da zub da hawaye.
Shafaru yayi ta daddagewa yana son ya
dawo da baya amma sai dakaru suka rufeshi da
duka suka yi gaba da shi da karfin tsiya. A
wannan lokaci Amshira na can gefe guda
mutane sun bamban keta bata sami damar ganin
fuskar Shafaru ba. Ko da ta fahimci cewa anyi
gaba da shi sai ta fashe da kukan bakin ciki. Ana
cikin wannan haline tsohuwa Shabiratu tayi fitar
burgu cikin shammace ta ruga kan Shafaru. Ai
kuwa tana zuwa gabansa sai dakaru suka rufeta
da duka har sai da suka kaita kas. Nan da nana ta
kama aman jini, cikin tsananin karfin hali da
kama zafin nama ta danko hannun Shafaru ta danka
masa sarkar nan ta matarsa ya karba ba tare da
kowa ya lura ba. A lokacinne aka dauke
Shabiratu ranga-ranga aka fitar da ita daga cikin
jama'a aka je aka wullar da ita can waje daya
tana numfashi da kyar alamar cewa abu ne
mawuyaci ta rayu.
Lokacin da jama'a suka ga dakaru sun
yiwa tsohuwa Shabiratu laga-laga sai wuri ya
sake hautsinewa, jama'a suka firgice aka kama
guje-guje da iface-iface
Da yake Humaila taga sa'adda aka je aka
wullar da tsohuwa Shabiratu sai ta ruga inda
take ta ciccibe ta goyata a baya ta shige da ita
cikin gida. Shigarsu ke da wuya sai ga Amshira
ta biyo bayansu ta rufe kofar gidan. Cikin
dimauta da kuka suka je suka kwantar da
tsohuwar Shabiratu akan Shimfidarta suka fara
yunkurin yi mata magani don tsai da jinin dake
zuba a hancinta da bakinta. A wannan lokacin
idanun tsohuwa Shabiratu suna budewa da
rufewa da kyar.
Amshira ta dubi Humaila ta ce "MAza ki
je ki dafa ruwan dumi ki kawo mini gami da kyalle maikyau.
Humaila ta yunkura da nufin tafiya cika
wannan umarni sai tsohuwa Shabiratu ta riko
hannunta ta budi baki da kyar ta ce "Ka da ku
wahalar da kanku domin bakin alkalami ya riga
ya bushe, tabbas ba zan tashi ba mutuwa zanyi.
Ni kam yanzu zan mutu da farin ciki idar da
sakonku ga yarima Shafaru domin tabbas na
bashi wannan sarka ya tafi da ita a hannunsa.
Ko da Shabiratu ta zo nan a zancenta sai
tayi tari ta tofar da jini al'amarin da yakara
dugunzuma hankalin su Amshira
Su ka kara fashewa da kuka. Amshira ta rungume
Shabiratu a kirjinta tana mai cewa "Ya ke abar
kaunarmu saboda me zaki tafi ki barmu. Yanzu
In babu ke ya zamu yi da kadaici?"
Sa'adda tsohuwa Shabiratu ta ji wannan
tambaya såi tayi murmushi karfin hali ta ce "Ya
ku masoyana ina yi muku albishir da cewa jiya
da daddare nayi mafarki. A cikin mafarkin an
nuna mini cewa zaku shiga cikin sabuwar
rayuwa ta jin dadi da kwanciyar hankali a nan
gaba. Humaila zata zamo matar sarki mijinki
Shafaru zai fito daga kurkuku kuma zai zamo,
daya daga cikin manyam birnin Farisa. Tabbas
nayi imani da wannan mafarki don haka ina
neman alfarma guda biyu rak a wajenku bayan
mutuwata. Alfarma ta farko itace ina son idan
na mutu ku haka mini kabari na a cikin gidan
nan ku binne ni sannan idan kuka sami matsayi
ku mayar da gidanan nawa makabarta kuma
kada a binne kowa a cikinsa face wanda ya
kasance maraya ko mara dangi kamata. A yiwa
makabartar lakabi da makabartar Shabiratu.
Alfarma ta biyu itace ina son ku rinka ziyarar
kabari na ko da sau daya ne a shekara don
tunawa dani. Da wannan kalami nake muku ban
kwana ina mai yi muku fatan mafarkina ya tabbata
gaskiya. Ko da Shabiratu ta zo nan a zancenta
sai numfashinta ya sake sarkewa. Nan take
jikinta gaba daya ya sandare, idanunta ya kafe ta
zama gawa. Ko da ganin haka sai Amshira da
Humaila suka kankame gawar suka fashe da
matsanancin kuka. Ba su gushe ba suna wannan
kuka har sai da rana ta fadi sannan suka tashi
suka haka kabari a cikin gidan suka binne
tsohuwa Shabiratu sanan suka zauna suka ci
gaba da kuka suna begenta. A wannan rana dai yadda suka ga rana haka suka ga dare kuma ko
ruwa ba su sa a bakin su ba. Wannan shine abin
da ya faru a gidan tsohuwa Shabiratu bayan an
wuce da yarima Shafaru izuwa gidan boka
Shamakalu.
Al'amarin Hadiman attajiri Abairu kuwa
tunda wuri ya hargitse Kumaz ya kasa gano su
Amshira sai suka yi ta kai kawo da duru-duru a
wajen har izuwa lokacin da kowa ya watse aka
barsu su kadai a tsaye. Nan fa hankalinsu ya
-dugunZuma suka rasa abin yi, bisa dole suka
koma wajen attajiri Abiru suka sanar da shi
halin da ake ciki. Yayin da Abiru ya ji wannan
batu sai ya harzuka zuciyarsa ta kama tafarfasa
ya mike tsaye ya kama zagayale yana mai tunanin
abin da ya kamata yayi. Daga can sai ya tsaya
cak ya dubi hadiman nasa sannan ya janye
kyallen da ya rufe idonsa guda wanda ya tsiyaye
ya ce.
"Na rantse da darajar wannan 1do nawa wanda na rasa duk ta dalilin Amshira da 'yarta
Humaila duk inda suka shiga suka buya a cikin garin nan
Sal na zakulosu na dauki fansa akansu. Tabbas
Sal nayi lalata da Humaila sannan na kwakule
mata idanunta biyu da wuka tanaji tana gani. Ita
kuwa Amshira kisangilla zan yi mata na tsira
mata mashi daga kasanta sai ya bullo ta
ta
bakinta."
Ko da gama wannan jawabi sai ya
ya
dakawa su Kumaz tsawa ya ce Ku tafi ku ci
gaba da bincike duk wanda ya gano inda
wadannan makiya nawa suke zan bashi ladan
rakuma dubu da dinare dubu dari." Ko da jin
wannan batu sai su Kumaz suka rude suka
bazama izuwa cikingari.
Lokacin da aka ci gaba da tafiya da
yarima Shafaru izuwa gidan boka Shamakalu sai
aka ci gaba da dukansa da bulalai ana tusa
keyarsa. In ya fadi sai a tasheshi da sauri yaci
gaba da tundashi, jama'a kuwa suka biyo ba'yan
dakarun da ke tafe dashi du, ba a dadi tamkar
mutanen garin ne kaf za suyi hijira. A haka dai
aka iso har kofar gidan boka Shamakalu,
wannan
shine tsohon
ginin nan inda
sihirtacciyar rijiya take.
Da zuwa kofar gidan sai aka iske boka
Shamakalu a tsaye ya ruke kugu da hannayensa
biyu fuskarsa a murtuke abar ban tsoro. Tsaye daf dashi sihirtacciyar damisar nan ce tana
gurnani. Ko da jama'a suka yi arba da boka
Shamakalu da kuma wannan damisa sai suka
firgita aka ja da baya ana rakabewa saboda
kwarjinin Boka Shamakalu da kuma mummunar
siffar wannan damisa, sukan su dakarun da suka
zo da Shafaru basu san sa'adda suka saki
Shafaru ba suka ja da baya suka yi cirko-cieko
jikin su ya kama tsuma. e
Yayin da yarima Shafaru ya tsinci kansa a
gaban boka Shamakalu sai ya nufeshi gadan-
gadan ba tare da tsoron komai ba ya mika masa
wannan wasika ta raddi ya ce. masa
"Ya kai wannan bakon ga takarda daga
sarkina ya umarceni da na kawo maka, ina mai
rokonka da ka sauke dukkanin fishinka akai na
bayan ka karanta wannan wasika amma kada ka
taba lafiyar sarki Humaru domin ya kasance da
ga dan'uwana marigayi sarki salkuf." ai
Lokacin da boka Shamakalu ya ji wannan
batu na Shafaru sai ya cika da tsananin mamaki
ya dubi Shafaru ya ce "Saboda me baka son na
hukanta sarki Hamaru alhalin ya kasance
babban makiyinka a duniya, ka tuna fa cewa
shine ya raba ka da iyalinka ya daureka a
kurkuku har tsawon shekaru ashirin da daya, kai
ne ka cancanta da zama sarkin Farisa amma sai
ya karbe mulkin da karfin tsiya, shine ya jefa
iyalinka cikin mugun hali suke kwana a kwaroro
tsawon wannan shekaru kuma suka yi ta fama da
yunwa da kishirwa. Har a yanzu suna nan a
cikin rayuwar kunci da fargaba har ma ana
farautar rayukansu. Ya kai Shafaru kasani cewa
ni boka Shamakalu na san komai na dangane da
rayuwaka bisa abin da ya faru a baya dama
wanda zai faru nan gaba. Wannan wasika daka
bani ba komai bane a cikinta face sakon sarki na
cewar na hada komatsena na bar masa garinsa
saboda gadarar da na nuna masa. Ka sani cewa
idan ina son na maishe da kai sarkin farisa
yanzu take zan iya. ldan kana son na kamo sarki
Hamaru na hallakashi a gabanka zan iya. Haka
kuma zan iya sadaka da iyalanka yanzu yanzu
amma sai ka amsa mini tambayar da na yi maka
dazu cewar me yasa baka son na taba sarki
Hamaru?
Yayin da boka Shamakalu ya zo nana a
zancensa sai idanun Shafaru suka ciko da
Kwallah ya sunkui da kansa kasa sannan ya
bude tafin hannunsa ya kurawa sarkar Amshira
idanu yana mai zub da hawaye. Daga can sai ya
daga sarkar sama yana mai yiwa boka
Shamakalu nuni da ita sannan ya ce
Ya kai wannan boka mai daraja kayi sani
cewa asalin wannan sarka ta mahaifin sarki
Hamaru ce wato dan'uwana marigayi sarki
Salkuf. Hakika Hamaru ya ci darajar wannan
sarka shi yasa har abada ba zan so ya shiga
masifa ba. Abin da zan gaya maka yanzu
labarine mai tsawo amma zanyi kokari na
gajerce shi domin sai ka saurari labarin sannan
zaka gane dalilin da yasa nake kaunar sarki
Hamaru duk da cewa shi baya kaunata ko kadan
a zuciyarsa. Asalima bashi da abokin gaba sama
da ni.
Yayin da boka Shamakalu da sauran
Jama'ar gari sukaji wannan batu saijikin kowa
yayi sanyi aka yi tsit ana sauraron labarin da
Shafaru zai bayar. Shafaru yai gyaran murya ya
fara bayani kamar haka:
Kimanin shekaru arba'in baya sa'adda
mahaifinmu sarki Sharudul Amman ke mulkin birnin Kisra ya kasance yana da matan aure guda
biyu kacal a duniya. Matarsa ta farko ana
kiranta da suna Husaira kuma sai da suka
shekara goma sha hudu da yin aure sannanya
auro uwata wadda ake kira da suna Shabila
kafin uwata ta zo Husaira ta haifi yaya Shida
kuma dun son kasance maza, a shekarar da
uwata ta zo sai suka sami ciki a tare ita da
Husaira kuma suka haifi 'ya'ya maza a rana
guda. Da ranar suna ta zagayo sai aka sawa dan
Husaira suna Salkuf ita kuwa mahaifiyata sai
aka sawa danta suna Sahfaru, wato dai a wannan
lokaci Husaira na da 'ya'ya bakwai ita kuwa
mahaifiyata tana da da daya kacal wato Sahfaru.
A kwaná a tashi sai muka taso kai daya ni
da Salkuf muka cika shekara goma sha biyar. A
wannan lokaci ni da Salkuf mun shaku ainun ko
yaushe muna tare dare da rana bama rabuwa.
Kai sai da takai cewa Salkuf ta tattaro kayansa
gaba daya daga dakin mahaifiyarsa ya dawo
gaba
dakin mahaifiyata domin ba zai iya yin barci ba
idan bana kusa dashi. Wannan Zumunci da
shakuwa da ke tsakanina da Salkuf sai suka
zamo abin bakin ciki a wajen Husaira da sauran ya'yanta domin babu yadda ba su yi ba akan su
rabamu amma abu ya faskara. Yan'uwan Salkur
sun sha yi masa duka da zaba mai tsanani akan
ya daina hulda da ni amma sai ya kasance da su
in dai kuna sonku rabani da Sahfaru sai dai ku
kashe ni. Bisa dole suka hakura suka kyalemu
muka ci gaba da zumuncinmu.
Yayin da tsufa ya sake riskar mahaifinmu
SOsai sai kishin dake tsakanin uwata da uwarsu
Salkuf ya yawaita har ya zamana cewa Husaira
ta tsanemu kamar yadda ta tsani mutuwarta don
haka sai ta fara tunanin hanyar da za tab1 ta
shafemu a doron kasa. Duk sa'adda Husaira ta
shirya wani makirci a boyc don ta hallakamu sai
Salkuf ya zo a sirrance ya sanar da mu abin da
ta shirya don haka shirinta sai ya wagatse.
Al'amarin da ya kan jetata Cikin matsanancin
mamaki kenan abin da ta kasa ganewa shine
Salkuf yana labewa ya saurari duk abinda suke
kullawa ita da 'ya'yanta ba tare da sun sani ba.
Mahaifinmu sarki Sharudul Amman ya
kasance a cikin dumbin farin ciki bisa ganin
yadda muka hada kai muka so juna ni da Salkuf
don haka ne ma ya kauna ce mu soSai fiye da sauran ya'yan Husaira ya zamana cewa ya jamu
a jikinsa fiye da su domin ko yaushe mua
gabansa. Ana cikin wannan hali ne cutar ajali ta
kama
sarki Sharudul Amman, yayin da yya
fahimci cewa tabbas wannan cuta tasa ba ta
tashi ba ce sai hankalinsa ya dugunzuma ya rasa
abin dake masa dadi a duniya domin ya tabbatar
da cewa duk ranar da ya mutu ni da Salkuf da
mahaifiyata sai mun dandana kudarmu. Bisa
wannan dalili ne ya shiga tunanin hanyar da
zaibi ya kubutar da rayuwarmu daga cikin
wannan fargaba.
Wata safiya ni, Salkuf da mahaifiyata
muna zaune a cikin turakar sarki yayin da yake
kwance cikin jinya muna kuka saboda a ranar
Ciwonsa ya tsananta sai ga sarkin gida ya shigo,
da zuwa sai ya fadi ya ce da sarki ga wani
bakon boka ya zo kuma ya ceyana da
muhimmiyar magana da kai.
Ko da jin wannan batu sai ranmu ya baci
domin mun gaji da zuwanbokaye barkatai
saboda babu wanda ya 1ya share mana hawaye.
Cikin fishi mahaifiyata ta dubi sarkin gida
ta ce "Ka je ka sallameshi kawai domin bashi da.
...
DAJIN MUTUWA
littafi na daya 1
Na Abdulaziz Sani M gini
Typing - Shuraihu Usman
Part 1C.
Wani amfani ga sarki runda kafin ya zo duou
Sun zo."
koda da jin wannan batu sai sarki ya budi
baki da kyar ya ce "A'a ba za ayi haka ba. A
KOwane mutum da irin baiwarsa, a kyale
wannan bakon boka ya shigo mu ji abin dake
tafe
da
shi."
Nan take sarkin gida ya mike tsaye ya fita waje
a lokacin ne kuma Huraisa da 'ya'yanta su shida
suyka shigo cikin turakar suna muzurai da
hararar mu. Da zuwa sai suka sami wuri suka
zauna suka kama kukan munafunci su duka har
Huraisa na cewa ai basu san cewa jikin sarkii
yayi tsamari haka ba. Dama can basu damu da
rashin lafiyar sarki ba burinsu kawai ya mutu
babban dansa wanda ake kira Mukairu ya hau
karaga.
Jim kadan da fitar sarkin gidan sai gashi
ya dawo tare da bakon boka wani mtumi mai
tsananin kwarjini wanda ya kasance dogo mai
matsakaicin kaurin jiki. Duk jikinsa gashi ne
kuma babu komai a jikinsa face walkin fata
dami da guraye da kambunan tsafi, ko takalmi
babu a kafarsa. Yana da kananan idanu gami da faffadar hanci da kuma karamin baki, fuskarsa
na cike take da gemu da kasumba shekarunsa
sun haura na sarki Sharudul Amman, amma abin
mamaki shi ne yana yana jin karfin jikinsa
tamkar na saurayi matashi.
Da shigowar bakon bokan sai ya risina ga
sarki Sharudul Amman ya ce, "Gaishe ka ya kai
sarkin adalci, kai ne sarkin da babu kamarsaa
fagen
talakawansa. Ka yi sani cewa na dade da yin
hakuri,
tausayi da
taimako ga
nazari a kanka bisa wannan dalili ne na Zo
maka da wata muhimmiyar gudunmawa."
Sa'adda sarki Sharudul Amman ya ji
wannan batu sai ya dubi boka a nutse ya ce,
"Kai kuma waye, daga inan ka fito?"
Koda jin wannan tambaya sai bokan ya yi
murmushi ya ce, "Sunana Sahibul Furrati kuma
na fito ne daga Dajin Mutuwa."
Yayin da muka ji haka sai kowa ya cika
da mamaki. Sarki ya sake duban boka Sahibul
Furrati ya ce, "Shi ne Dajin Mutuwa? Sahibul
Furrati ya ce, "Shi ne dajin da ba wani mahaluki
da ya taba rayuwa a cikinsa face ni kadai. Shi ne
dajin da ba a shigarsa a fito lafiya, kuma shi ne dajin da ke dauke da dukkanin magungunan
Cututtuka na duniya kaf face cuta daya wato
mutuwa. Shi ne dajin da babu wanda ya san
ainihin inda yake face ni kadai, kuma shi ne
dajin da ke dauke da dukkanin masifun duniya.
Yakai wannan sarki ka yi sani cewa 1dan zan yi
maka bayanin abin da ke cikin wannan daji sai
mu kwana arba' in ina jawabi ban kare ba. Yanzu
dai ba abin da ya kawo ni kenan ba. Na zo ne na
gabatar da gudunmuwata a gareka, don kyautata
bayanka, amma ba zan iya baka gudunmuwar ba
face na kadaita da kai ya zamana babu kowa a
cikin dakinan daga kai sai ni, kuma babu mai
1ya jin abin da zamu tattauna.
Koda jin haka sai sarki ya dube mu gaba
daya ya ce, "Ku tashi ku fita ku ba mu wuri."
Nan' take uunianirmu muka mike muka fice.
Fitarnu ke da wuya sai boka Sahibul Furrati ya
dubi kofofin dakin da tagogin sa da idanunsa.
Take suka rufe kan su ruf.
Caba dayanmu sai muka tasru a kofar
turakar sarki a gefe gudu muka yi cirko-cirko
Laura iiran boka Sahibul Furrati ya fito, sannan
mu shiga mu ji abin da suka tattauna a bakin sarki.
Sai da muka shafe sa'a uku cur a tsaye
muna jira, sannan muka ga kofar dakin ta bude
boka Sahibul Furrati ya fito yana mai yi mana
bankwana, amma bai dubi fuskar kowa ba a
cikin mu sai ta Salkuf. Kawai sai ya yi
murmushi a gare shi ya dafa kafadarsa, sannan
ya wuce abinsa. Cikin sauri mu duka muka ruga
izuwa cikin turakar sarki. Da shigar mu sa
muka iske shi a zaune cikin annushuwa tamkar
bai taba yin cuta ba. Al'amarin da ya matukar ba
mu mamaki kenan, muka zazzauna muna masu
kura masa idanu. Sarki Sharudul Amman ya
dube mu daya bayan daya cikin alamun takaici
da damuwa kawai sai idanunsa suka ciko da
kwallah ya fara zubar da hawaye, sannan ya ce,
"Yaku ya'yana da matana ku yi sani cewa
wannan bako da ya ziyarce mu yanzu ba mutum
ba ne kamar mu, aljani ne. Tabbas ya ba ni
labarin duk abubuwan da suka faru a rayuwata
tun daga sa'adda uwata ta haife ni kawo iyanzu
kuma tabba a cikin labarin na sa babu kuskure
ko guda daya. Baya ga wannan ya sanar da ni
cewa idan na mutu

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment