Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

a fusace tana kai masa
sara da wafta za ta hadiyeshi shi kuma Zuhairu ya rika
gocewa da kai mata sara cikin tsananin jarumta da karfin
zuciya, duk inda macijiyar ta sara a jikin jirgin ruwan sai
ka ga itacen wajen ya fashe ko ya ragargaje.
Da ragowar jaruman da suke tare da Zuhairu suka
hangi abin da yake faruwa sai nan da nan suka zare
makamansu, gwanayen harbi da kibiya suka rika sakarwa
macijiyar ruwan kibbau daga inda suke, masu jifa da
majaujawa suka rika jifanta da wasu dunkulallun karafa
masu tsini dake huda jikinta, sauran jaruman masu fada
da takubba ko mashi suka tafi ga jirgin ruwan don kai
dauki gareta, da zuwansu suka far mata da sara da suka
babu kakkautawa, macijiyar nan ta kawo wafta cikinsu ta
suri daya ta hadiyeshi daga shi har takobi da sulken
yakin da ke jikinsa, ta sake kawo sara ta samu mutum
uku lokaci guda, iska ta kwashesu ta yi sama da su
sabodá karfin saran suka zube a gefe matattu ba su ko
shura ba, jikinsu ya rika zagwanyewa yana narkewa
kamar jini, saboda masifar dafin da ke jikin macijiyar
Da ragowar jaruman suka ga haka sai suka ja da
baya a razane, shi kuwa Zuhairu ya sake tasar mata a
fusace, ya kai mata wani gawurtaccen sara irin na zaratan
sadaukai da dukkanin karfinsa, ya yi sa'a ya sameta a
lokacin da take kokarin kai masa sara, macijiyar ta yi
wani irin gunji mai tsananin karfi saboda azabar saran da
ya kai mata, jini ya yi tsartuwa sama daga inda ya sari
jikinta, macijiyar ta yi tsalle ta fada cikin ruwan kogin,
masu jifa da majaujawa da harbi da kibiya suka ci gaba
da har bin ta har ta nutse a cikin ruwan kogin, jini ya taso
sama ya gauraye ruwan kogin daga inda ta nutse.
Zuhairu ya tsaya yana saurare ko zai ga macijiyar ta
sake tasowa saman ruwa daga inda ta nutse amma har
aka shafe lokaci mai tsawo ba su sake ganinta ba, don
haka ya yi zaton ta halaka sun gama da ita, daga nan suka
kwashe gawarwakin 'yan uwansu da sauran jama'ar da
macijiyar ta halaka a cikin jirgın ruwan suka fita dasu suka binnesu, sannan suka share jirgin ruwan suka gura
duk abin da ya lalace a ciKinsa, suka zuba kayansu suka
hau suka dauki fila-filan da ake amfani da su wajen tuka
jirgin ruwan suka soma tukawa suka kama hanya da zasu
ketare kogin.
Bayan sun yi tafiya mai nisa a cikin kogin har rana
ta kusa faduwa ba su kai karshensa ba, can daga bayansu
sai suka rika jin wani kugi da gunji yana tunkaro inda
suke, iska mai karfi ta soma tahowa daga gabas tana
kada ruwan, kogin ya soma tunbatsa yana ambaliya da
tsiri sama, igiyar ruwa ta soma kadawa tana girgiza jirgin
da suke ciki sannan sai suka ji wata irin tsawa mai
tsananin karfi da ban firgici ta sake gauraye wajen,
ruwan ya sake hautsinewa yana kadawa da karfi tare da
yin tsiri sama kamar zai sha kan jirgin ruwan ya nutsar
da su su halaka, jirgin ruwan ya soma tangadi da tangal-
tangal kamar zai dulmiyar da su su halaka.
Can daga bayansu sai suka hango wannan bakar
guguwar ta keto ta saman ruwan kogin tare da iska mai
tsananin karfi sun tunkaro inda suke, gaba daya wajen ya
yi bakik kirin sararin samaniya, ya yi duhu mafi tsananin
gani daga yankin duhun dare, suka sake jin wata tsawa
mai tsananin amo da rugugi mai matukar hauhawa da
ban firgici, jirgin ruwan ya sake yin girgiza da tangal
tangal tamkar zai kife dasu su halaka, har zuwa sanda
bakar guguwar nan ta karaso inda suke, daga cikin bakar
guguwar sai ga matsafi Bahalu ya bayyana akan iska,
hannunsa rike da gorarsa na aikin sihiri tare da sandarsa
ta tsafi, ya dubi su Zuhairu ya bushe da dariya irin wadda
ya saba yi a duk sanda zai aikata wani abu na mugunta da
zalunci, ya ci gaba da kyakyata dariyar har zuwa tsawon
wani lokaci sannan ya ce de su "Halaka ta tabbata a gareku cikin wannan rana babu
shakka ba za ku kubuta daga wannan musiba da ku ke
ciki ba har sai kun halaka, kamar yadda na sanar daku
cewa ajali zai gabata gareku cikin wannan tafiya, saboda
babu wani mahaluki a fadin duniya da ya isa ratsa lardin
Ashtar bare ya je inda fadata take, saboda ma'abota tsaro
da bada kariya dake tare da ita, ya dubi 'yar uwarsa
Buniyatu ya ce da ita.
"Ke kuwa Buniyatu zan sake bada dama a gareki
kafin ku riski inda za ku halaka, ki zama mai neman
afuwa a gareni tare da yin rantsuwa da alkaluman sihiri
masu girma akan cewa za ki rabu da begen wannan
jarumi da ku ke tare da shi, tare da barin addininsu da ki
ka yi imani da shi a yanzu, ni kuma na yi miki alkawarin
zan kubutar da ke daga wannan halaka da ku ke ciki na
maida miki alkaluman tsafi da sihirinki da na rabaki da
su, na tafi da ke fadata mu zauna tare cikin salama, da
tasirin aikata abin.da ki ke son na daga alkaluman sihiri."
Buniyatu ta maida masa raddi da cewa ""Bana
bukatar taimako daga gareka ka kubutar dani, ga Allah
nake neman taimako kuma ba zan taba juya baya ga
abinda na tabbata a kansa yanzu ba, na fita daga addinin
Musulunci, ba kuma na neman ka dawo da alkaluman
sihirin da ka kwace daga gareni don a yanzu ina neman
tsari da su, kuma ba ka isa ka tabbatar da hallaka akan
mu ba, komai karfin tasirin tsafi da sihirinka har sai ranar
da Ubangiji ya so tabbatar da bakan a kanmu."
Matsafi Bahalu ya fusata da jin kalamanta masu
tsauri a gareshi ya dubeta ya ce da ita.
"Ke dai kina cikin dimuwa da bata wadda ba za ta
dawo da ke kan turbar gaskiya ba, kuma tun da kin yi
zabi da kasancewa cikin wannan hali tare da jama'ar da ki ke tare da su, to ku yi Saurare da zuwan musibar da za ta
riskeku ta kai ku ga halaka, ita ce za ta zama hanyar
salwantar rayuwarku ba za ku taba kubuta daga gareta ku
ketare wannan kogi da ku ke ciki ba,"
Yana gama ambaton wannan magana ya sake
bushewa da dariya irin ta mugunta da zalunci sannan ya
bace cikin bakar guguwar da ya bayyana a cikinta ya bar
wajen, daga nan sai suka sake jin wata tsawa da rugugi
mai ban firgici ya gauraye wajen can daga gabansu sai
suka hangi ruwan kogin nan ya dare gida biyu ya yi tsiri
sama, tsayinsa zai iya shan kan jirgin ruwan da suke ciki
ya nutse da su su halaka, sannan sai wata iska mai karfi
ta soma tura jirgin ruwan yana tunkarar inda ruwan kogin
nan ya dare gida biyu za ta dulmiyar dasu su halaka, su
Zuhairu suka ci gaba da addu'a don neman kiyayewar
Ubangiji ya kubutar da su daga wannan musiba da suke
ciki. Jirgin ruwan ya ci gaba da tafiya yana kara tunkarar
inda ruwan kogin ya dare gida biyu zai dulmiyar da su su
halaka.
Shin me zai faru?
Mu hadu a littafi na uku kuma na karshe don jin
yadda za ta kasance.
Naku har kullum mai fatan nishadantar daku
SHEHU USMAN MUHD.
07034668406, 08025433394
Ni Shuraihu Usman dana rubuta kuma na gabatat da shi a shafin dlhausanovels,com,ng ke cewa bissalam

mu hadu a kashi na uku wanda zai dau lokaci gaskiya dun yanzu bama da shi a kasa,

Ina masu Sha'awar karanta littatafan Hausa, kama daga kan na yake yake, irin na su, Abdulaziz Sani M ginj, Shehu usman Muhd, Muktar Yaron malam, Ashiru Sani Muhd, Nura Iliyasu, Nura sada , isah Muhammad, Sarana mohammed, imrana Musa, Abdurrahman Iliyasu, Kh Abdulkarim Waziri, Sani Yusuf, Rabi'u Muhammad Gumel, ibrahim Adam Usman, Mansur sufi... dama wasu marubutan na da, Nesa ta zo kusa marmaza kuje shafin www.dlhausanovels.com.ng ku downloading duk littafin da kuke da bukata zuwa kan wayarku a kyauta batare da ko sisin ku ba.
kada dai ku manta sunan shafin www.dlhausanovels.com.ng

Shuraihu Usman
08140419490
2020 - DL HAUSA NOVELS

An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

2 Comments On BAKAR GUGUWA book 2
avatar
auwal-6-7

11 months ago

Reply

Littafine hadadde wanda Na dade ina nema

avatar
abasu-kala

11 months ago

Reply

Replying to auwal-6-7

Ga shi kuwa yanzu ka sameshi

Please Login or Register in order to submit comment