Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace ina
xaka, yace xan dauko kudi ne,abba yace
nawa ne a wajen ka ynxu, yace dubu biyar,
abba ya ciki dubu hudun haisam ya mikawa
Aliyun ya karbe yana kirgawa, duk wannan
abinda akeyi a kan idonsu hajiya ne, hajiya
taji kmr ta maida dan nata ciki don murna,
sae murmushi take yi, umma kuma ji tayi
kmr ta tsine ma haisam da bai yo hali irin ta
Aliyu ba, shekaranjiya tace ya bata dubu
goma yace bai da, amma sae gashi ynxu ya
kirgo har dubu biyar ya bada don a duba
wata bnxa ita kam bata san irin dan da Allah
ya bata ba, momy kam sunkuyar da kanta
tayi tana jin duk abinda sukeyi cike da
takaici, intisaar kuwa idonta ta rufesbda
axabar da take ji ko ina na jikinta ciwo yke
mata barin ma kanta sannan kuma ga
ciwon mara shima ya kunno kai, abba kam
tuni ya fice su hajiya suka bi shi a baya a
xuciyarsu suna fatan Allah yasa cikita yo,
don rahma ca tayi masu amai take ta
kwararawa, Aliyu ya dube inna yace"a bata
tea kafin na dawo, xan je siyo abinda ya
kamata," ya fice haisam ya bisa a baya da
sauri, sai da suka kai tsakar gidan sannan
yace "canjin nawa xaka dawo da knan?"
Aliyu yace kmr ya, haisam yace eh ae dubu
tara aka baka, kuma dubu takwas da dari
biyar kace, Aliyu yyi masa wani irin kallo
sannan yace "to da kafa xanje siyo
magungunan?" sannan yyi tsakiya wuce
yana cewa "dn ma kun samu xan bata lkcn"
.
. Su Aliyu na fita inna ta mike tana tambayr
intisaar din me xata ci, ta girgixa kai alamar
ba komai, xainab tace"to ki daure kisha tea
din" inna ta dauki kofin ruwan shayin ta isa
kusa da ita tana cewa "tashi ki sha kafin ya
dawo to" intisaar ta girgixa kai murya can
kasa-kasa tace "wanka xan fara yi," momy ta
shiga bathroom ta hada mata ruwan
wankan sannan ta mike da kyar jiri na
kwasarta ta shige bayin, ko da ta fito rawan
sanyi ta dinga yi, inna ta lullubetatana cewa
"ikon Allah, ciwan lkci daya ya kwantar da
ita," ya haisam ya shigo dakin yana tambayr
ko Aliyun ya dawo,inna tace "ina fa! yana
can yana sokwanci" haisam ya girgixa kai
yace "ni dae wllh inna nafi son a kaita
asibiti," inna tace "wae ni kuna bani mamaki
wllh, ga likita a gida kuyi ta kiran asibiti,"
haisam yace "to shknan, ni xan wuce kd ne
ynxu ina da wani aiki a can amma yau xan
dawo in'sha Allah," inna tace "to Allah ya
kiyaye" yace "ameen" sannan ya karasa kusa
da intisaar yana kallnta yace "Allah ya
sauwake kanwata kinji" tayi murmushi, a
hnkli tace "ngdyayana" yyi ma momy ma
sllma sannan ya fita. Da kyar inna ta lallabata
tasha kunun da ta dama mata, xainab sae
fama kallon agogo take yi dn har sha daya
ya wuce, tun kusan karfe goma da Aliyu yaje
siyo magunguna har ynxu bai dawo ba, tuni
bacci ya dauke intisaar din bayan inna ta
bata paracetamol kafin Aliyun ya dawo,
amma har karfe sha biyu bbu Aliyu bbu
lbrinsa, "kai jama'a ko dae wannan yaron
bata yyi ne" inna ta fadi tana kallon momy
da xainab dake dakin bakinta a bude, momy
dae bata ce komai ba, xainab ta tabe baki
ita ma bata ce komai ba, wasa-wasa har
karfe biyu bbu Aliyu, inna na idar da sllh
tana xaune kandarduma cikin ihu tace
"amma wannan anyi tsinannan yaro," daga
momy har xainab sae da suka raxana sbda
irin bude muryar da inna tayi, momy tace
"kai inna, kika san uxurin da ya tsayar
dashi," a fusace inna tace "yaci ubansa shi
da uxurin," ku bni waya na kira bukar,
momy tayi ma xainab ido alamar kar ta kira
mata abban, inna ta mikawa xainab din
wayar tana cewa "maxa kira min uban
nasa" xainab ba don ranta yaso ba tace ma
inna baya xuwa bayan ta kara wayr a kunne
kmr me kira, don ita da momy ta barta kiran
abban xatayi, ita kam bata san irin yayan
nata ba, basu san tuni abba ya kira momyn
yana tambayrtajikin intisaar din ba tace
masa da sauki sosae, yace Aliyun ya bata
duka magungunan tace masa eh sannan
sukayi sllma, xagi kam Aliyu ya sha shi a
wajen inna ba adadi, har da dan hawayenta,
"ni da nasan abinda tambadadden yaron
nan xae yi knan da asibiti kawae na bari
muka wuce, gashi ynxu yrnya na ta shan
axaban ciwo ba magani, shi kuma bukar na
rasa uban me xae sa ya dinga kashe
wayarsa ni kam, ynxu wa xae kai mu
asibitin gashi haisam ba ya nan," daga
momy har xainab bbu wanda ya tanka
mainna, intisaar kam jikinta yyi xafi sosae
kmr wuta, hka inna ta ishesu da mita tana
hawaye, wajen karfe uku da rabi wayan
intisaar yyi kara xainab ta dauka tana kallon
me kiran, faruuq ne, da har xata ajiye don
bacci intisaar din take yi sae kuma ta fasa ta
daga, suka gaisa ya tambayeta intisaar din
fa, tace "bacci takeyi wllh, bata da lfya," cike
da damuwa yace "subhanallahi, me ya
sameta" xainab ta yarfe hannu tace "wllh
bamu sani ba, tace dae ciki da kantake mata
ciwo," yace "tun yaushe?" tun jiya da
daddare wae,yace "ya salam! kunje clinic
ne?" tayi shiru ta rasa me xata ce, yyi saurin
cewa "ohk... Gani nan xuwa," ya kashe wayr,
inna tace "faruqu ne?" xainab ta gyada mata
kai kawai, cikin minti goma sha biyar faruuq
ya iso gidan, hanklinsa ya tashi sosae, momy
da ta bar masu dakin ya rage inna daxainab
kawae, ta tashi xaune tana kallon faruuq din
da ya sata gaba yana tambayrta inda ke
mata ciwo, cikinta t.a nuna masa da kai,
yasa hannu ya danna cikin nata ta xaro ido
tace "waii! ciwo yake min" me ya buge ki a
nan ya tambayeta yana taba goshinta da yaji
xafi sosae, ta girgixa masa kai kawae sae
hawaye, duk ya rude ya shiga lallashinta
yace "dama kina ciwon kai ne," ta girgixa
masa kai kawae, ya mike yana kalln inna
yace "bari ina xuwa yanxun nan inna," inna
tace "to dan albarka, wannan shaidanin
yaron aka ba kudi ya siyo mata magunguna
bamu sake ganinsa ba " bai tanka wa inna
ba ya fice da sauri, ko minti talatin bae cika
ba ya dawo dauke da kayan magunguna da
allurori sae ledar ruwa dan karami da xae sa
mata, ya ce wa xainab ta hado mata tea mai
kauri ta kawo mata, shi da kanshi ya shiga
bata, amma ta karba tace xata iya sha, yana
ta hada allurorin da ruwa har ta sha rabi ta
ajiye tace "ta koshi," yace "ae baki ma ci
komai ba tukunna, tuwo xa a kawo maki
kici ynxun," inna ta mike tana cewa "gskya
ne, bari naje da kaina ma xan mata ynxun
nan," da kyar ta yrda yyi inject din ta sannan
ya sakamata ruwan ya bata wasu daga cikin
medicines din tasha ta kwanta, ya xauna ya
xuba mata ido yana kallonta cike datausayi,
xainab dama tuni..
Faruuq na xaune har ruwan da yasa mata
ya kare da yake karamin leda ce, ya cire
mata don bacci ma takeyi, yana gama cire
mata ta bude ido tana kallnsa, yyi mata
murmushi yace "ya jikin kanwata," ta tashi
xaune tace "da sauki," ba tare da ta kallesa
ba, ganin tana kkrin mikewa tsaye ne yasa
yace "ina xaki kuma kanwata," murya can
ciki tace masa "2 ease my self," ba tare da ta
kallesa ba, ya taimaka mata ta tashi tsaye dn
jikinta ba kwari dukda taji ta garau ynxu,
tuwon da inna ta kawo mata ya shiga xuba
mata, ta fito ta nemi gefe ta xaunatana
kallonsa kmr xatayi kuka, ya dago kai yana
kallnta yace "kici abinci ki sha sauran
medicine dinki kanwata, kusa da ita ya
durkusa yana kallonta yace "ya dae
kanwata, cikin na maki ciwo har ynxu ne,
naga yhu re restless" ta girgixa masa kai
kawae bata cekomai ba "say somethin
mana kanwata, ina ke maki ciwo kuma?"ya
tambayeta cike da damuwa, itakam kunya
take ji tace masa mararta ke mata ciwo, don
hka tace "ni bbu inda ke min ciwo," sae
kuma ga hawaye, nan da nan ya rude ya
shiga lallashinta yana cewa "plss kanwata ki
gya min mene mana, kan bai daina
bane?,"ganin yanda duk ya bi ya daga
hanklinsa ne yasa tace "cikina ke ciwo," ba
tare da ta kallesa ba, yace "ciki kuma, ba kin
ce ya daina ba, to wae me ya buge ki a cikin
ne" a hankli tace ba shi bne, yyi shiru kmr
me naxari sannan yace "on yhur Period?"
yana kallonta, tayi shiru bata ce komai ba
kanta a sunkuye, yace "ohk ina xuwa
kanwata," ya mike ya fice. Ko da ya dawo
tana xaune a falo ita da momy da inna sae
kursum, tasa tuwo a gaba amma taki ci,
ynxu kam jkinta yyi mata sauki sosae, da
sllmrsa ya shigo falon rike da ledan magani
karfe biyar da minti goma na yamma, ya
gaida momy don tun xuwansa na farko bai
sake ganinta ba sae ynxun, ta amsa tanai
masa sannu da xuwa sannan ta mike ta bar
falon, xainab ta shigo ta xauna gefen
intisaar din tana mata ya jiki, tayi murmushi
tace "da sauki"maganin da ya xo da shi kala
uku ya dauki daya ya buda ya bata, ta karba
a kunyace xata ajiye yace tasha ynxun, inna
tace "ae hka nan take yarinyar nan bata san
magani, nayi mamakin ma da tasha wa inda
ka bata daxu," faruuq yyi murmushi kawae
yana kallnta har ta kora maganin da ruwa
sannan ya sa ta cin tuwon dake gabanta,
bude kofar da sukaji anyi irin ta mahaukata
ne yasanya su juyawa gaba daya, Aliyu ne ya
shigo dakin sanye da t-shirt fara kal da
wando three qtrshima farin, yyi kyau sosae,
hannunsa rike da leda da basu san ko meye
a ciki ba, intisaar ta sunkuyar da kanta da
sauri, faruuq kuwa kallo daya yyi masa ya
kauda kansa, kallonsu ya shigayi daddaya
da daddaya, inna tana sakace hkori ta tabe
baki tace "ae sae ka je ka tsis-tsira ma kanka
allurorin ka shanye magungunan don jikata
kam ta warke, dan arxiki wanda aka haifa
tsiya na bacci ya xo ya duba mana ita" Aliyu
ya yo waje da dara-daran idanunsa yana
kallon innar, wato shi aka haifa tsiya ido
biyu, ya juya yana kallon faruuq din da
intisaar, xainab ta labe bayan intisaar sbda
wani irin dariya dake cinta, hka ma kursum
da ta rufe fuskarta a jikin inna, Aliyun
yatsura wa faruuq din ido kmr xae shake
shi, faruuq bai ma san yanayi ba, ya dube
intisaar yace"kanwata kin ki cin tuwon ko
na taya ki ne?" ta kirkiro murmushi bata ce
komai ba, yace "au kar na taya ki?" a hnkli
tace "kaci mana" yyi murmushi yace ok,
sannan ya mike ya dauki ruwan goran dake
gabanta ya bi gefen Aliyun ya fita, Aliyu ya
bishi da kallo har ya dawo ciki sannan ya
xauna gabanta yace "to muci," a kunyace
tasa hannu cikin tuwon sannan shi ma ya
saka, inna tace "yauwa faruqu kila ma xata
fi ci idan taga kana ci," faruuq yyi 'yar dariya
ya dubi xainab yace "xo muci xee" xainab
tayi dariya tace aa ni naci nawa ae, inna ta
dubi Aliyu tace "to ka tsaya mana kerere a
ka kmr wani tsohon soja, da'alla fice ka ba
mutane waje su ga haske,gantalalle kawae
dogon bnxa, knka ka cuta ba mu ba " Aliyu
yyi huci mae xafi yana kallonintisaar din
dake cin tuwonta a hnkli ita da faruuq,"
juyawa yyi ya fuce fuuu, inna ta kyalkyale da
dariya ya dawo da sauri idon nan nasa ya
kada yace "kika ce me?" bata tanka masa ba
sae dariyar da take ta yi kawae, ya juya yyi
gaba yana cije lebensa. Kursum da xainab
suka dinga kyalkyale dariya inna na taya su,
faruuq kam murmushi kawae yke yi, intisaar
kam jingina kanta tayi jikin kujera tana
kallonsu.
.
Gajiya tayi da tsayuwa taga ba sarki sae
Allah, tayi shahada, ta kusa kai cikin gate din
tana karanto duk addu'ar da taxo mata don
duk a rude take, a dai-dai lkcn shi kuma ya
mike tsaye xae bar gidan ya wuce masallaci
don maghrib ya kunno kai, duk gidan yyi
masa xafi, wata raxanan nan kara ta saki
ganin ya mike tsaye a dai-dae lkcn da ta
shigo gidan, don a nata tunanin dama can
ita yake jira yana ganintakuma ya mike, shi
kanshi sae da ya firgita da irin karar da tayi,
ta kuma juya a guje kmr mahaukaciya xata
bar gidan, yyi saurin fixgota da karfinsa
ransa a bace, bae an kara ba sae ganin
yarinya ta sulale kasa yyi, yyi hanxarin rikota
ta xube jikinsa sumammiya, ya durkushe
wajen yana kallonta cike da mamaki, yasan
suma tayi, jijjigata ya shiga yi a hnkli ya ma
rasa abinda xae yi ya fara waige-waige
gashi bbu kowa a tsakar gidan dan gari ya
fara duhu, ruwan goran da ya fitoda yasha
ya rage, ya dauko ya bude ya shiga yayyafa
mata ruwan, a hnkli ta bude idanuwanta ta
daura kan nasa idon da ya tsura mata a
fuskarta, kuka ta saki tana kkrin tashi daga
jikinsa tana cewa "don Allah don annabi ya
Aliyu ka daina dukana, ni bn maka komai
ba....." buga mata baki yyi yace "keep mute!"
ba shiri tayi shiru, ya turata daga jikinsa
fuska a hade yace "don ki kara ja min bakin
jini wajen abbana shiyasa xaki tsiri suma da
kin ganni ko" girgixa kai tayi hawaye na
sintiri a fuskarta, ya daka mata tsawa "tashi
a kaina kar nayi ball dake munafuka kawae,"
ta mike da sauri jikinta na rawa, shima ya
mike tsaye, tayi baya xata fadi, yyi saurin
tallabota, ta fada jikinsa ya turata da sauri
sannan yyi maxa ya riko hannunta dn
faduwa xatayi, ya fara fixgarta kmr wata
dabba tana binsa jikinta ba kwari sae jiri
dake kwasarta amma bae bari ta fadi ba, yyi
sashinsu daita, har bakin kofarsu ya kaita ya
bude kofar yana kallonta, duk a tsorace
take, ya tura ta ciki har tana faduwa yyi
gaba, momy ta taso da sauri ganin yanda
'yar tata ta fado falon tana cewa "lfya
intisaar,"
.
Karfe tara abba ya shigo duba intisaar, har
lkcn inna na falonsu bata tafi ba, abba ya
shigo mata da fruits da tsire a leda ya ajiye
mata yana tambayarta ya jikin, tace "da
sauki abbana" sannan ta mike ta shige
bedroom ta bar masu falon, abba ya dubi
inna yace "nan xaki kwana knan yau?" tace
"aa dama kai nake jira, kasan iskancin da
wannan dan naka yyi mana yau" abba yyi
shiru yana kallonta, ta tabe baki tace "wllh
bkayi sa'an da ba bukar, shanya mu yyi a
nan ya gudu da dubu taran da kuka bashi,
sae wannan yaron faruuq yaxo ya dubata
kmr xata mutu" abba ya tsura mata ido yana
kallonta ya kasa cewa komai, "wllh ko minti
goma ba ayi da fitan yaron ba ka shigo, tun
safe yaki barin gidan nan yana kanta, gashi
ynxu jiki alhmdllh, yaron mutunci ne wllh"
abba ya jinjina kai cike da takaici yace "to
shknan yyi masa kyau, hkn yaga yafimasa
alkhairi," inna ta mike ta tabe baki tana
cewa "ka rakani bangarena" yace "to
sannan yyi sallama da momy, ta rakosu har
bakin kofa tana ma inna sae da safe. Karfe
goma haisam ya shigo duba intisaar, momy
tace "kar dae ynxu ka dawo haisam" yace
"wllh kuwa momy," bae bar sashin nasu ba
sae kusan karfe sha daya, suna ta hira da
momy da intisaar da ynxu bata jin ciwo a ko
ina na jikinta. Da safe ita da ihsaan suka je
gaida abba, kmr ba ita tayi ciwo jiya ba,
Aliyu na xaune a falon kansa sunkuye bayan
abban nasa yyi masa tatas, intisaar ta nemi
gefe ta xauna ganin Aliyu duk sae jikinta ya
mutu, ta gaida abba ya amsa da fara'arsa
yana tambayarta jiki, tayi murmushi tace
abba da sauki, ta kalli Aliyun da har ynxu
kansa a kasayake tace "ina kwana yaya," ya
dago yana kallonta idonsa yyi jajir ya kauda
kai murya can ciki yace "lfya lau," ta mike
tana kallon abba tace"abba sae anjima,"
yace "yauwa intisaar, kin dae sha
magungunanki dae ko," tace "eh abba
nasha" yace "to yyi kyau" sannan suka fice,
Aliyu ma ya mike yana kallon abban nasa
yace "Allah ya huci xuciyarka abba," abba ya
dauki kudin da Aliyun ya ajiye masa ya
watsar masa dasu yace "nace kaje da su
bama bukata," Aliyu yyi jim sannan yace
"kayi hkuri abba, ita ma kanwata ce bbu
yanda xa ayi na karbi kudi wae don xan yi
treatn dinta, na gya mka dalilae na nayin
hkn, kuma bayan hka ma ni bn samu na yi
treatn dinta ba " abba ya galla masa harara
yace "dalilanka na bnxa, ina ruwanka da
uwartaka da har xakayi hkn wae sbda taji
ddi, wae kae me uwa, ka burge uwarka
amma kuma ka xubda kimarka a idanun
mu, kai ko kunya ma bka ji ba, wawa
kawae, da'alla get out malam" Aliyu ya juya
jiki ba kwari ya bar falon. Da yammar ranar
ummi kanwar faruuq taxo duba intisaar,
yayan nata ya ajiye ta sannan ya wuce, sun
jima suna hira da intisaar da xainab kmr da
can sun saba sannan suka kaita gun inna,
inna ta rasa inda xata sata don farin ciki,
tsaraba ta hada mata lkcn da faruuq din ya
kirata wae yana waje don baxae shigo ba
wae, momyma ta hada mata nata abun
arxikin sannan intisaar ta rakota don xainab
tuni hajiya ta aika khadija ta kira mata ita, a
bakin gate suka gaAliyun a xaune fuskar
nan tasa bbu alamar rahama, ummi ta
gaisheshi, ya dago kai yana kallonta fuska
daure yace "lfya," intisaar ma ta gaidashi
gabanta na faduwa yyi bnxa da ita har suka
fice, ummita juya tana kallonta tace "waye
wannan kuma," intisaar ta kirkiro murmushi
tace "babban yayanmu ne" don ita ynxu
tunanin yanda xatashiga gidan yana bakin
gate din take, har bakin motar faruuq din
intisaar ta rakata suka yi sllma faruuq ya
kashe mata ido yace "sae nakiraki bbyna," ta
kauda kanta da sauri tana murmushi ta bar
wajen, ya ja motar suka wuce, ta kasa shiga
gate din ta tsaya a waje, har wani bari
jikinta yake yi don tsoro.
Dago ta momy tayi tana kallon ta tace "jikin
ne intisaar?" ta girgixa kai ta mike da
kyartace "aa faduwa nayi," bedroom ta
shige momy ta bita da kallo ta kasacewa
komai tausayin yar tata ya cika ta, ita ta rasa
abinda ke damunta. Washegari da ciwan
kan ta tashi amma bata bari momy ta gane
ba don bata son tana daga wa uwarta ta
hnkli, faruuq ya kirata da safen yana
tambayr jikinta tace yyi sauki sosae, tare
abba ya shigoda Aliyu falon nasu wajen
karfe tara, lkcn innana nan a xaune don tun
karfe bakwae ta iso sashin nasu da kunun
ta da kosae ta kawo ma intisaar, ihsaan ta
rungume abban nata ya daga ta sama yana
cewa"how re yhu momyna" tace fyn sir, ya
dubi intisaar yana murmushi yace "ya jikin
fatima? Tayi murmushi tace "da sauki
abbana," to Allah ya kara sauki, kina shan
magani dae ko? Tace "eh abba ina sha,"
Aliyu ya nemi guri ya xauna yana satan
kallon momy dake xaune tana linke kayan
ihsaan, ba tare da ya kalleta ba murya can
ciki-ciki yace "ina kwana," tayi kmr bata ji sa
ba, ya tabe baki ya gaida inna ita ma tayi
masa bnxan, ya dake yana duban intisaar
din yace "ya jiki," ta sunkuyar da kanta tace
"da sauki," sannan tace masa"ina kwana" ba
tare da ya kalleta ba yace"lfya lau," ya sata
kallonabbansa da ke kallon Tv, yace ba tare
da ya kalleta ba"kwaso min medicines din
da kike sha nagani," ta mike jiki ba kwari ta
shiga bedroom ta kwaso masa
magungunan da faruuq ya bata ta durkushe
gabansa ta xubesu tana kallonsa, inna ta
tabe baki tace "ko uban me xae yi dasu idan
ba gulma ba," bae tanka mata ba ya shiga
dudduba magungunan ya cire guda biyu a
ciki yace "ki ajiye wa innan kar ki sha," to
kadae tace, inna tayi karaf tace "akan wani
dalilin, kafi sa sanin aikin nasa ne malam,"
da'alla kwashe magungunanki ki maida
kirabu da wannan gantalallen, dariya ma
abun yaba Aliyun, abba ya dubesa
yace"sbda me xata ajiye su," ya shafa kanshi
yace "sbda aikinsu kusan iri daya ne gaba
daya, dama xan karo mata wasu ne shiyasa
nace ta ajiyesu," abba yace "no ka bari ta
gama da su tukunna sae ka bata wanda
xaka batan, shima yasan abinda ykeyi ae
yaron," Aliyun yyi shiru bai ce komai ba, inna
ta galla masa harara tace"munafukin bnx
kawae, idan yaga ubansa ya dinga yi kmr na
Allah," Aliyun ya mike yana kallon abban
nasa yace "abba xan wuce clinic sai na
dawo," inna tace "kaji makaryacin bnxa, ca
xakayi xaka je gantali,kai din aiki kke xuwa,"
ya tabe baki bae tanka mata ba, ya dan kalli
intisaar din ya watsa mata hararar tsana
yace "Allah ya sauwake," ya juya ya fice.
Suna tsakar gidagaba dayansu intisaar na
sa ma rahma rani a hannu da yamma, su
hajiya da umma anje gidan suna, momy na
can bangaren inna, haisam da abokinsa
sadeeq suka shigo gidan, dukansu suka
gaida su, sadeeq ya dubi xainab
yace"xainabu ya garin," ta galla masa harara
tace " kaji dashi malam," yyi dariya suka
wuce ciki da haisam yana satan kallon
intisaar da tun da ta gaida su bata sake
daga kanta ba, sadeeq din ya dubi haisam
bayan sun shiga ciki yace "wacece wannan
yarinyar dan Allah," haisam ya hararesa yace
ita intisaar din ce bka sani ba, sadeeq yace
wllh bn ma taba ganinta ba ni, haisam yyi
murmushi yace "kanwatace,'yar wajen
momyn ihsaan ce," sadeeq yace "waww
amma yarinyar tayi sosai," haisam yyi 'yar
dariya bai dae ce masa komai ba, sadeeq
yace "uhm naga baka son maganar, ko dae
kana ciki ne?" haisam ya hararesa yace
"kanwar tawa? Sadeeq yace "so, sae akayi
yaya? Bbu auretsakaninku ne ko me kke
nufi" haisam yyi murmushi, sadeeq
yace"yess?" Allah idandae bbu komai
tsakaninku ni kam ina ciki, yarinyar tayi ne
wllh, haisam yace "kunyar ta nake ji ne
sadeeq, amma baxan boye mka ba, sonta ya
wahal dani fiye da yanda kke tunani, but
bbu yanda xanyi, ni kam nahkura, na kuma
dauketa a matsayin kanwata ne," sadeeq ya
galla masa harara yace "amma kai wani
bnxa ne wllh, wannan ae xancen bnxa ne
kke min," haisam yace "to ya xanyi?" sadeeq
yace"tun kararta xakayi kace kana sonta,
kaga sae ayi tuwonamai na, sincerly sayin
kar ka bari yarinyar nan ta wuce ka, xakayi
babban asara," haisam yyi murmushin
takaici yace "to ae its too late, ni nan na bata
go ahead na kula samari kuma ynxu hka
akwae wanda xae aureta, kuma frndship
ma muke yi dashi, abokina ne ynxu hka,"
sadeeq yyi tsaki yace"nonsense ni kuwa xan
shigar da kaina nace ina sonta, watch nd c"
haisam yace no kar kace hka plss baxan iya
yi wa faruuq hka ba, sadeeq dae bai kara
tanka masa ba, har suka gama abinda ya
kawosu, suka je masallaci sukayi sllhr
maghrib, sannan sukayi sashin inna, har
lkcn jikin haisam a sanyayye yake, basu bar
wajen inna ba sae kusan karfe takwas da
rabi, sadeeq ya shiga ya gaida hajiya
daumma sannan ya baro haisam a falon
hajiya yace yana xuwa, xainab sadeeq ya
kira yace taje tace da intisaar haisam na
kiranta don kar ace shine taki fitowa, tace
haisam ae yana falon mu, Yace do as i
saymana kanwata, ta kuwa j
.
. Suna fitowa tsakar gidan intisaar tafara
tambayr xainab ina ya haisam din, xainab ta
nuna mata can kusa da wata flwer inda
sadeeq yake a xaune, ta karasa wajen, "gani
ya haisam," ta fadi tana kkrin xaunawa kan
wani dakali, suna hada ido da sadeeq tayi
saurin mikewa tana kallnsa,ta juya a fusace
gun xainab amma tuni xainab tayi gaba
tana dariya, donta gano sadeeq din, intisaar
ta juya xata bar wajen,yyi saurin shan
gabanta yana cewa "hva kanwarmu, ni ba
yayanki bne da har...." tayi tsaki tace "ka bni
waje malam ina da abin yi," ta katse shi, yyi
murmushi yace"to naji baxan bata maki lkci
ba, amma sae kin xauna sae muyi magana,"
tayi masa wani irin kallo tace "dan Allah ka
bni waje na wuce, ni mamata bata san na
fito ba" yyi shiru yana kallonta sannan yace
"uhum faruuq ya riga ni ko?" directly tace
masa"yeah!" yyi murmushi mae sauti yace
"to kika san ikon Allah" ta watsa masa
harara tace "kayi hkuri ka bani guri na
wuce," "to idan Allah yyi nine mijinki fa?"
xatayi magana taji an fixgota ta baya an
juyo da ita, a tsorace tace "ya..ya Ali...." marin
da ya kai mata ne ya sanya ta kasa
karasawa, ransa a bace ya fara mgna "ke
don uwarki baki da aikin yi sae tara mana
samari a gida, wannan gajan ya shigo
wancan gajan ya shigo kin maida mana
gida kmr hotel, cikin gidan nan uban wa
kikaga yana shigowa da samari, sae ke
tatatcciya,marakunya ko?, to daga yau na
sake ganin ki da wani shege a tsaye a gidan
nan sae na...." turasa tayi da karfinta har sae
da yyi ba, dan unexpectedly hkn ya xo masa,
ta koma baya tana kallonsa hawaye na
sintiri a fuskarta, ta yarfe hannu cike da
takaici tana magana "ni me na tsare mka
agidan nan ka gya min don Allah, kullum sae
ka cuceni ba tare da dalili ba, to kasani wllh
sae Allah ya saka min,kace ba ruwanka da
harka na ba ruwanka da lamarina, to ina
ruwanka da samarin da naketarawa, ka fita
rayuwata don Allah don annabi ka rabu
dani, ka kyalenini ban tsare ma komai ba
gidan nan, just let me leave my lyf am
beggin yhu " ta kara fashe wa da kuka ta
juya da gudu ta bar wajen, sororo Aliyu ya
tsaya kalln intisaar ransa a jagule, kansa ya
dinga juyamasa, ya firfito da ido cike da
mamaki, kansa na tsara masa ya dafe
maganganunta na dawo masa a ka, sadeeq
dake tsaye cike da mamaki yana kallonsu yyi
masa duban wlkcn sannan yace "to kaji dae
malam," Aliyu ya juya cikin bacin rae ya
cakumeshi da karfi yana cewa "kace me??? "
haisam ne ya karaso da sauri don dama
yana tsaye yana kallon duk abinda ke
faruwa, yafixge yayan nasa daga rikon da
yyi wa sadeeq dake ta tuntsira dariya kmr
wani xautatce, Aliyun ya tsaya yana huci
yana kallonsa kmr kirjinsa xae yi magana,
sadeeq ya kalli haisam yana dariya sosae
yace "wannan dan uwan naka yana bukatan
xuwa psychiatry a duba kwakwalwarsa
urgently" da haisam bae ja sadeeq sun fice
daga gidan nan ba da ba karamin tashin
hnkli xasuyi da Aliyu ba, barin ma Aliyun
najin haushin sadeeq din tun da ddewa.
Sashinsu intisaar din yyi kmr wani xaki ya
kasa daina tunano kalamanta, yana isa ya
tura kofar da karfi

1 Comments On INTEESAR 1 TO 4
avatar
hamadou

1 year ago

Reply

Compte gogle

Please Login or Register in order to submit comment