Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a kawo min mana" nan ya shiga bubbuda ledojin yana kallon kayan baki
bude inna tayi maxa tace "maxa kuje can guriin xainabu gani nan xuwa" da sauri kuwa
suka juya suka bar wajen, sannan inna ta dinga kwasar kayan tana shiga dasu dakinta Aliyu na
binta da kallo "Allahu akbar.. Yanxu har da maltina aka kawo min?? Lah har da madara ni rahma,
amma mutanan nan anyi mutanan kirki."Aliyu ya bude baki yana kallonta sae kace warce bata taba
shan madara ba ko malt, ita da duk wata abba ke jido mata su dayawa, amma ko sati biyu
ba sayi take shanyewa da yara. "kai Allah ya shima wannan yaron Albarka" Aliyu ya dubeta yace
"wani yaro?" au na manta ne Allah ya shima maimuna Albarka xance, ko da yake ma duk
Daya ne, don dan ta da ya dawo daga waje ne yayo min tsarabar. Aliyu ya tabe baki ya jawo
Abincin gabansa xai fara ci akayi sallama faruuq ya shigo palon bayan inna ta amsa da karfinta,
Mikewa tayi ta rasa inda xata sa shi sae ca take "sannu da xuwa dan Albarka," ya nemi guri ya
xauna ya gaidata ta masa cike da jin dadi, sannan ya ba
Aliyu hannu sukayi musabaha, da dan fara'arsa Aliyun ya karba don bai san sa ba. Inna ta
Mike ta bude fridge ta jido masa lemo kusan kala hudu da ruwa roba uku, ta dire masa a gabansa
Tana tambayensa ya hanya, sannan ta shige ciki ta fito da cin-cin da alkaki bakin nan nata yaki
rufuwa. Godiya ya dinga yi mata, don yana jin dadin yanda inna ke nan nan dashi, ko xaka ci
abinci ne, bari na kawo maka cokali kuci tare da Aliyu, wannan shine Aliyu jikana da nake baka labari,
dariya ma abin ya ba Aliyun, ta dauko cokalin ta saka masa tace suci tare. Aliyun bai yi musu
ba ya sauko yana cewa ki dae yi a hankali karki fadi da wannan barin jikin da kike yi. Bata ko
tanka masa ba tace "wannan shine faruuq saurayin intisaar ae nasan baka san shi ba, Haisam ne
ya san sa," dago kai Aliyu yayi yana kallonsa, nan da nan dan fara'ar dake fuskarsa ya bace, inna
tace to kuci abincin mana kar ya huce, ajiye cokalin hannunsa yayi fuskar nan tasa a yatsine yace "ya
dae ci, amma ni wannan ba isar mu xai yi ba," faruuq ya dago yana kallonsa, ya gane
nufinsa,don hka sae yayi murmushi yace to ni bari naci tunda bako ne ni, da sauri inna tace eh
hakan ma yayi sae ya hakura ayi na dare. Hade rai Aliyu yayi yana kallon inna yace
"kamar ya na jira na dare? Ban gane nufinki ba?"
Inna ta mike ta tabe baki hade dacewa "maida wukar dan nan" sannan ta shige daki sae ga ta ta
Fito da garin rogo da suga ta xube masa a gabansa tace "ka debo ruwa a pampo ka jika kasha don
ruwan kenan na kwaso wa faruuq.
Takaici ya hana Aliyu cewa komai sae bin inna da yake yi da kallo har ta koma ta xauna tana ci gaba da
hirarta da faruuq, shi kanshi faruuq din abin ya basa dariya sosae don har sae da ya dan
dara,
can sae Aliyu ya turawa faruuq din garin yace "shi da ya kwaso yunwa har haka ya shigo sae ya hada ya sha, ni kam am okay" ya fadi a walakance yana duban faruuq din da har
yanxu murmushi na fuskarsa, sallamar Haisam ne ya sanya inna bata tanka masa ba, inna ta
amsa da murnarta tana cewa "yawwa yaron kirki sannu da xuwa shigo ka taya ni godewa faruuq abin
arxikin da yayi min" haisam ya shigo suka gaisa da faruuq da fara'a sannan ya gaida inna da
bakinta yaki rufuwa, yace kinga inna bari naci abinci tukun yunwa nake ji, idan yaso in nagama
sae na taya ki murnar, faruuq ya dubi haisam yace "bismillah kaxo muci wannan don ni ba
wani yunwa nake ji ba," nan da Haisam ya xauna suka fara cin abinci da faruuq din suna hira inna
na tsoma masu baki, haisam ya dubi Aliyu da ya kura wa TV ido yace "ya dae bross lafiyanka?,
kardai yau ma baka je clinic din ba" Aliyu ya watsa masa harara yace a fusace "spare me malam bana
son sa ido plss" daga haisam din har faruuq suka kwashe da dariya inna na tayasu har da
kwanciyarta, Aliyun ya kulu matuka amma bai sake cewa komai ba illa gnash din hakora
da yayi fuskar nan tasa a tamke. Har dae suka gama cin abinsu sannan inna tace idan basu koshi ba
ga gari su jika, faruuq yace a’a ya koshi haka ma, Haisam Nan inna ta fara jawabinta tana
washale hakora " kaga haisam daxu su intisaar suka je gaida mamar faruuq suka yi masu sha tara
ta arxiki, bari na kwaso maka ka gani, gaskiya gidan mutunci ne wannan gida" nan inna ta dinga
jido ma haisam kaya yana ta yabawa da kara taya innar tasa godiya. Ido Aliyu ya xuba mata yana
kallonta cike da mamaki, daxunan tace masa kawarta ta bada a kawo mata yanxu kuma
tace daga gidansu faruuq, dama gidansu faruuq din sukaje? "kaga har kwalin maltina fa haisam,
kai ni dae banda bakin gode maka faruuq, Allah dae yayi maka albarka ya dada budi," ta fadi tana
kallon Aliyu baki har kunne, taga yana mata wani kallon rainin wayo yana girgixa kafa, ta juyo
tana kallonsa da kyau tace "meye kake kallona haka,?
Ka taba kawo koda gwangwanin madara daya ka kawo min gidan nan ne bare maltina? Kuma
Don yanxu na samu me min sae ka dinga min bakin ciki? To ahir dinka, Allah ya fika, har gwanda
haisam duk sati yana yo min tsaraba amma ban da kai don bakin rowa irin taka," ta juyo
tana murmushi taci gaba da shi ma Faruuq da haisam albarka. Ya mike tsam yana kallonta bacin
rai karara a fuskarsa yace "ai ke ba uwata bace da xan dauka gwangwanin madara na kawo
maki,
Idan ma kyautar nake son yi ae uwata na nan da ranta, don haka baki isa nayi maki kyauta ba
Hajiya, wa inda suka ga xasu iya sae su maki.
Aikin banxa kawae aikin hofi, mutum ya tsufa bae san ya tsufa ba" yana kaiwa nan ya fice
Ba tare da ya jira cewarta ba, sashin hajiyarsu ya
nufa, yana shiga ciki rae bace ya fara
Magana "mumy kina gidan nan xaki bar 'yar ki ta fita
raka wata banxa can gidan saurayi? Hajiya ta mike da sauri tana cewa wa kenan? Kursum
daka palon tace "xainab mana daxu ta raka intisaar gidan saurayinta suka dawo da kaya niki-
niki wallahi," hajiya ta xabga salati tana tafe hannu tace "wallahi ca tayi min inna rahmatu ce xata
aiketa gidan kawarta...." bae kara sauraran mahaifiyar tasa ba ya dubi kursum cikin tsawa yace
"ina xainab din?" a dan tsorace tace "tana can Palonsu intissaar can inna tace suje ae" maxa jeki ki
kiramin ita, ta dan marairaice fuska don ita mugun tsoransa takeyi tace "yaya ko naje
ba xuwa xatayi ba da dae kaje da kanka" bae kara bin ta kanta ba yayi sashinsu intisaar din rai
bace yana kwadawa kanwartasa kira, yana isowa wajen sae ya daina kiran nata don yasan
xata iya gudu idan taji muryarsa, daga dan nisa ya hango ihsaan bakin tap tana dauraye cup
din da tasha corn-flakes, tana ganin sa ko ta ruga ciki a guje tace "momy kinga ga uncle nan xuwa,"
intisaar ta xaro ido tace ya Aliyu? Ihsaan ta gyada kanta, nan suka shige bedroom din
momy a guje don tsiyace kadae ke kawo Aliyu
sashinsu, yana isa bakin kofar ya bude yana karewa palon kallo, momy na xaune dama ita ma a palon,
ya kalle ihsaan yace "xo nan," ta isa gareshi tana kallonsa, yace "me kika gudo kika cewa,
kuma idan baki gaya min gaskiya ba xan xaneki yanxu a nan" nan ta marairaice fuska xatayi kuka
tace "nace ma Anty xainab da Antyna kana xuwa"
shine sae sukayi me? Ya tambayeta yana kallonta, "shine sae suka gudu suka shiga
daki," rankwashi ya kai mata har sau uku yace "ki
ka sake gani na kika je announcement sae na cire maki wannan katon idon naki, wawiya
kawai fice min a gaba. Ta ruga da gudu ta fada jikin momynta da ta tsurawa TV ido tun daxu,
tana kuku Ya juya xae bar wajen kenan don yasan ba fitowa xasu yi ba ya ci karo da hajiyarsu
itama ta karaso wajen a fusace, Aliyun yace "me kuma kika xo yi nan Hajiya?" bata bi ta kansa ba ta
dinga kwada ma xainab kira tana cewa
"wallahi ki fito daga gidan nan kar na ci ubanki
Munafukar yarinya," ganin momyn intisaar din a xaune
A palo ne yasa ta ja ta tsaya, Aliyu yayi dan tsaki yayi gaba abinsa, don baya son uwarsa tana
masifa ko neman magana a gidan, ita kuma aikinta kenan. "Zainabu! Ki gya min dalilin sa 'yata
bin watsatsiyar yarki gidan saurayi don a bata ta?"
hajiya ta fadi fuskarta a tamke, ko kallo bata ishe momy ba da ke ta aikin kallonta tana
rungume da 'yar ta, hakan ya kara hassala hajiya don tana matukar bakin cikin sharesu da
momyn ke yi a gidan, kenan ma mahaukata kawae ta maidasu don ba dai amata abu ta tanka a
gidan ba, cikin daga murya hajiya tace "wae ba da ke nake ba ko kurama ce ke?" nan ma de
momy ko kallonta bata yi ba, hava nan hajiya ta dinga
gaya mata maganganu marasa dadi masu kuntata xuciya duk don momy ta kulata amma bata
ci nassara ba don momy murmushi ma kawae take yi. Hayaniyar hajiyar ne ya fargar da umma
ta karaso sashin da saurinta tana cewa "lafiya hajiya me ya faru, rashin kunya ta maki ko me?"
ina fa,, yawon iskancin da da ta sa 'yar ta take yi, shi xasu koyawa xainab dita, tunda gashi yau
har shiryata tayi suje gidan saurayin 'yar tata. Umma
ta xabga salati tana jujjuya kai tace "wallahi kursum taxo ta sameni wae xainab ta bi intisaar
gidan saurayi ya cika su da kaya duk na tsamman shirmanta ne shiyasa ban tanka mata ba"
hajiya tace "Allah ya isa tsakanina dasu," umma tace "to yanxu ina shegiyar xainab din take" bata jira
amsa ba ta afka palonsu intisaar din ta tsaya
gaban momy tana cewa "ki fito mana da 'yar mu kar mu aki abinda baki xata ba gidan nan yau,"
tana magana ne tana nuna momy da dan yatsa, momy tayi murmushi mai sauti, ta kama hannun ihsaan
suka shige bedroom ta kulla kofar. Galala umma ta bita da kallo, hajiya ma ta shigo palon
tace "idan ba tsoro ba dan uban mutum meyasa bae tsaya ba" nan suka dinga xaxxaga mata
rashin mutumci kwando-kwando suna xage-xage, gori kam ta sha shi kala-kala, abinda ya fi bata
masu rai bae wuce yanda ta barsu su kadae suna ta haukansu ba, don a da can idan suna mata
tayi shiru har dadi sukeji a nasu tunanin tana tsoransu ne,.
Ido Aliyu ya xuba masu yana kallonsu, yayi murmushin da xa a iya kiransa da na mugunta
sannan ya hade rai yana kallon xainab din yace "ina kuka je jiya?" ta yarfe hannu hawaye na
sintiri a fuskarta tace "don Allah kuyi hakuri..."
wani irin tsawa ya daka mata yace "it seems kina wasa dani ko?" cikin kuka tace "aa yaya"
gud! Gaya min inda kuka je jiya. Ta juya tana kallon intisaar dake kuka wiwi sannan ta kalle
abban nasu da ya Aliyun tace "gidansu faruuq muka je
gaida mahaifiyarsa" abba yace "waye faruuq din?" saurayin intisaar ne," ta fadi, kanta a
sunkuye.
Cike da mamaki abba ya tsaya kallonsu,
Aliyun yace "amma ina kika ce mun xaku jiya?" "aa
Inna ta...." wani irin tsawa ya daka mata yace "rufe min baki kar na taka ki" yayi hakan ne don baya
Son Abba yasan da ixinin inna suka je, kawae so yake
ya lallasa su barin intisaar. Xainab na ganin hakan tasan yau kam sun banu, nan Aliyu ya dinga
tsarawa abba yanda suka yi jiyan da irin karyar da sukayi mashi, xainab ta san inna ce kadai
gatansu yanxu don abba yayi fushi matuka, da dubara tashiga yi ma kursum tex da wayan
dake hannunta kan cewa ta kira masu inna suna palon abba xa ayi masu duka, duk a rude take,
ganin yanda Aliyu ke tayi wa abba tsari yana dada bata masa rai. Ba a jima ba, kursum ta maido
mata reply, ta bude da sauri hannunta na karkarwa taga me tace, "NO" abinda ta gani knan
boldly
wato baxata turo innar ba. Ta kara sautin kukanta tana kallon intisaar da ta kife kanta
ita ma tana yi, tun ba yau ba tasan kursum muguwa
ce. To wa xata kara yi ma tex yanxu? Don kursum ce kadae hope dinsu, ita ma tace no. Yaya
haisam ta tuna, don haka da hanxari ta shiga yi masa tex duk da baya gidan, ya taimaka ya
kira masu inna taxo. Kafin tayi sendin Aliyu ya
ganta
ya fixge wayar da sauri yana cewa "you re
vry
stupid, wat do yhu fink yhu re doin?" abba
ya
karba wayan ya ajiye gefensu yana kallonsu.
Haisam yyi dariya sosai da yaga tex din, don
sbda tsabagen masifa Aliyun yyi sendin bai
sani
ba. Ai kam yana kiran innar ya gya mata ta
taho
da gudunta tana salati. Tun daga bakin kofa
ta
dinga kwada wa abba kira, hkn ba karamin
bta
wa Aliyu rai yyi ba, don yyi niyar yyi masu
laga-
laga ne, sai yaji kmr ya hankadata ta koma,
nan
ta sake masu kuka tana cewa "ynxu Bukar
don
na tura yaran nan su gaida uwar yaron nan
me
kirki shine nayi laifi?" Abba ya girgixa kai
yace
"dama ke kika ce su je?" ta goge hawayen
dake
idonta tace "eh mana," basu gaya min ke
kka ce
suje ba ne." ya kallesu yace "ku tashi ku tafi."
yyi
hkn ne don baya son uwartashi ta daga
masa
hnkli. Aliyu ya dan bugi kafarsa a kasa yace
"shit" inna ta dubi hajiya da umma dake
xaune a
palon kmr su hadiye xuciya don takaici tace
"to
munafukai ae sae a tashi a bashi waje kuma
ko,"
tayi tsaki ta wuce tana surutanta, don ana ta
tunanin su suka gya masa, duk da su din
suka
gya masa.
.
Suna fita Abba ya girgixa kai cikin damuwa
yace "ni bn san me ke damun inna ba, tana
tsufa
ne hnklinta na komawa na yaro," hajiya ta
mike
ta tabe baki hade dace wa "kawae de ta
kare
matarka ne, amma ka dae yi bincike da
kyau."
tana kai wa nan ta fice, umma ma ta bita a
baya
tana cewa "mu dae Allah ya rufama 'ya yan
mu
asiri kar a sa su a hnyar da bae dace ba, don
wannan lamarin akwae abun dubawa a
ciki"
momy de bata ce komai ba, amma tasan da
ita
suke, ta mike itama xata bar palon Abba ya
kirata ta dawo, Aliyu ma ya tashi ya bar
masu
palon cike da jin haushin inna, ko waye yaje
ya
gya mata ma oho. Suna tsakar gida a tsaye
ita
da xainab suna ta dariyan abinda ya faru
jiya da
safe, hajiya da umma sun je barka, inna tana
can
sashinta, su biyun kadae ne a tsakar gida,
shirun
da intisaar tayi ne fuskarta ya bayyana
alaman
tsoro ya sa xainab ta dakata daga surutun
da
take yi tace "me ya faru," tana waige-waige,
da
sauri intisaar ta fixgota da gudu suka je
bayan
wani flower suka buya, xainab na maida
numfashi a tsorace tace "wae menene?" ita
din
ma numfashin take mayar wa tace "ya
Aliyu."
xainab tace "a ina kika..." tsit tayi ganin
Aliyun ya
doso ta inda suke, cikin kasaita yake tafiyar
tasa,
yana sanye da t'shirt fara kal, da 3quatre
shima
fari tas, intisaar ta bi shi da kallo da
idanuwanta
kmr xasuyi magana, farar kujerar roba ya
dauka
ya ajiye ta opposite inda suke ya xauna.
Basu da
wata fargaba don sun tabbatar idan ba
kusa da
flowern ya xo ya tsaya ba baxae gansu ba,
ya
ciro wayrsa daga Aljihu yana dubawa, suka
ga yyi
murmushi mai kyau har sae da dimple dinsa
ya
nuna, ya lumshe manyan idanunsa ya sake
budesu, ko me ya gani oho. Ashe dae ya
Aliyu na
murmushi, tambayr da intisaar tayi ma knta
knan
a xuciyarta, nan dae ta tsaya ta kare masa
kallo
sosai, don ita kullum kallon tsoro take masa
a
gidan. A xuciyarta tace "ashe dae yana da
kyau
har hka," ta tsura ma sajensa da ya kwanta
luf-
luf a fuskarsa ido, daga sama xuwa kasa ta
dinga kallonsa ko kifta ido bata yi, ashe dae
shi
din kyakkyawa ne sosai, amma duk da hka
faruuq dinta ya fisa kyau tasani, xainab ta
xungureta tace "ke wannan kallon fa?" a
tsorace
intisaar din tace "da'alla dubi yanda kika
bani
tsoro."xainab tace "to naga kina neman
cinye min
yaya da ido, intisaar ta tabe baki tace "ni
kallon
mamaki nkeyi masa" to wae taya ma akayi
kika
san yana xuwa? Xainab ta tambaya tana
kallonta, kamshin turarensa, intisaar ta bata
amsa ba tare da ta kalleta ba. takun da suka
ji
yasa suka kara labewa sosai, momy ce taxo
ta
wuce, bai ce mata ba, bata cemasa ba har ta
wuce sa, da alama sashin inna xata, sae da
ta
wuce shi sannan ya bita da kallo har ta kure
masa, yyi murmushin da intisaar ta gaxa
gane ko
na menene, sannan ya cigaba da danna
wayarsa,
xainab tace "yau mun shiga uku hka xamu
ta
tsayawa ni kam na gaji wllh" intisaar bata
tanka
mata ba ta dan kara satan kallon Aliyun,
taga
kara hakikincewa yyi ma kan kujerar. Ihsaan
ce
taxo wuce wa tana kuka, kila ta tashi bata
ga
momynta ba da yayarta, don bacci take yi,
xata
wucesa ya fixgo ta yace "cum hia, wa ya
dokeki?"
bata ce komai ba sae kallonsa da takeyi, ya
daura ta kan kafarsa yana cewa "idan kika
sake
kuka xan maki allura" ba shiri tayi shiru ya
dago
wayrsa yana ta nunamata ko pix ne ko
meye ma
oho dae, su dae hka suka dinga lekosu har
daga
karshe suka ga ya sauke ta ya mata mgna a
hnkli ta ruga sashinsa da guda, ba ajima ba
ta
dawo rike da chocolate, suka ji yace mata
"run..
Momy tana wajen inna je ki sameta," da
gudu
kuwa tayi sashin innar. Idan ba don intisaar
da
ta dinga rike xainab ba da tuni ta mike ta
bar
wajen, ita kam tsoran abinda xai yi masu ne
yasa ta dinga rike xainab kar ta tona masu
asiri.
don sun gaji sosai gashi aliyu yaki barin
wajen
har sunyi kusan awa biyu a durkushe,
momy da
ihsaan ma tuni suka xo suka wuce. Ba su
suka
bar bayan flowern ba sae da aka kira la'asar
Aliyu ya wuce massallaci. Tana xaune gefen
inna
da ta dage tana ta kirgan kudi 'yan dubu
daddai,
da ta kirga sai ta mikowa intisaar ta duba
ko dai
dai ne, intisaar kam ta xuba mata ido don
bata
san inda ta samu kudin ba, har dae daga
karshe
suka gama kirgan kudaden inna ta dubi
intisaar
din bakinta a wangale tace "nawa knan
gaba
daya?" intisaar tace "dubu dari biyu da
hamsin,
ina kika samo su inna?" ba tare da inna ta
kalleta
ba tana kkrin hada kudaden waje daya tace
"fili
na na saida." intisaar ta xaro ido hade da
bude
baki tana kallon inna. Sallamar haisam ya
sanyata rufe bakinta, inna ta amsa mashi ba
tare
da ta lura da halin da intisaar ta shiga ba ya
shigo, suka gaisa yace "kina sha'aninki inna,
ina
kika samo kudi hka?" ya tambayeta yana
karewa
palon kallo, a xuciyarshi yana cewa kar dae
wani
abun inna ta kuma saidawa, don saranta
knan, in
dae bata da kudi to bata ki koh plaxman
palonta
ta saida ba, hkn kuma na bata wa abba rai
sosai
ba kadan ba, don duk abinda yke mata bata
gani
sae ta saida wani abun palonta ko daki,
"wllh fili
na na saida haisam" haisam yace "mene?"

Ba tare da inna ta kallesa ba tace "nace
mka fili na na saida. Ko bka ji ne" ya nemi
kujera
ya xauna yana kallonta cike da mamaki yace
"wani filin inna?" don dai shi yasan a ynxu
hka
inna bata da fili, idan ba dae wanda ake
mata
gini taje ta saida ba, "wannan din da
babanku ya
siya min" ta fadi tana mikawa intisaar
kudaden
ta kai mata daki. Haisam ya yo waje da ido
"yace wani filin abba ya baki?" inna ta hade
rai
tace "na jan bulo mana" haisam ya saki
salati
yana kallon innar, inna tace "kai ni don Allah
ku
rabu dani, ina da bukatar kudi kuma baxan
saida
kaddarana ba?" haisam yace "ya salam!
Ynxu
inna abba ca yyi maki filin naki ne? Daga ya
baki
takardu ki ajiye masa sae ki je ki saida fili?
Wai
ma nawa kika saida filin?" "ni dubu dari
biyu da
hamsin aka siya," inna ta fadi a marairaice.
Haisam ya mike da sauri yana kallonta ya ma
kasa cewa komai," filin abban kika saida
masa
dubu dari biyu da hamsin? Kin san nawa ya
sayi
filin inna, haisam ya girgixa kai yana kallon
innar
cike da takaici, ita kam sai wuri-wuri take
da ido.
Aliyu yyi sallama ya shigo yana cewa "har
kin
dawo daga yawon inna?" ya kalli haisam da
yanayinsa ya sauya xuwa bacin rai yace "me
ya
faru guy?" Aliyu filin abba taje ta saida dubu
dari
biyu da hamsin wae" haisam ya fadi cike da
jin
haushi, Aliyu ya xaro ido yace "wat?" filin da
yke
cewa xai fara gini cikinsa nxt yr?" dariya
Aliyu ya
dinga yi har da dafa bango, intisaar kam ido
ta
xuba masu tana kallonsu ita ma tasan inna
bata
kyauta ba, tuni inna aka fara hawaye, irin
dariyar
da Aliyu yake yi ne ya kara kullar da haisam,
to
meye abun dariya a nan, ta rangada wa
abbansu
asara, don ko shi bai sayi filin hka ba, cikin
karkarwar murya inna tace "to ni ina nasan
filinsa
ne, da naga bai sake min mgna ba ai nayi
xaton
ya bani ne, kuma Aliyu ba kai ka bani
shawarar
ba to?" Aliyu ya xaro ido yace "wa? Aa karki
sake
saka ni cikin wannan case din Hajiya" inna
tace
wllh kai ka sani, kana ji ko haisam, jiya ya
shigo
da daddare nake ce mashi bnda kudi kuma
ga
bikin jikar aminiyata ya taso bari bukar ya
dawo
na tambayeshi kudi, sae Aliyu yace min ae
Bukar
bai da kudi ynxu hka sae dae idan xan saida
kujeruna ne na biya bukatata, to naga dae
taya
xa ayi na saida kujerun palona, palo ya
xamo
wayam, kuma kwanakin baya ma da na
saida
fridge dina ma ae sae da bukar yyi min
masifa,
to yana fita a jiyan sae na tuna ai akwae
takardun filin da bukar ya bani......" Aliyu ya
daka
mata tsawa yana cewa "ke inna rahmatu
wllh kar
ki saka ni cikin wannan case din na gya
maki,
idan dae mutum ba hauka ya fara ba ta ya
xai
kin kima kujerunsa ya saida don an bashi
shawarar, ni dama wasa nke maki, kuma
magana
ce na gya maki." tuni inna aka fara kuka
wiwi,
Aliyu ya fice yana dariya, Haisam kam kasa
cewa
komai yyi, tun ba yau ba yasan Aliyu mugu
ne,
idan ba hka ba taya xa a saida kaddarar
mahaifinsa mai muhimmanci yayi ta dariya.
Ya
juya ya fice kawae ba tare da yace da inna
komai
ba, to waye ma yyi mata jagora taje tayi
wannan
aika aikan, Aliyu na fita yaje ya sami
hajiyarsa
yana ta dariya ya bata lbrin abinda inna tayi,
ta
hade rai tace "to meye abun dariya a nan
Aliyu,
gadonku fa ta walakanta kke dariya hka?"
ya
mike yana kallon umman tashi yace "ni
banyi
depend a gado ba mum, Allah ya hore min
don
hka, 4 ol i care," ya fice yana ci gaba da
dariyarsa don yasan drama xa ayi a gidan
yau
idan abba ya dawo. Abba ne tsaye kan inna
yana
faman bambamin fada kmr xae maketa,
inna ba
baki sae idanuwa, "kinsan nawa na sayi filin
ne
xakiyi min hka inna, daga baki ajiya sae ya
xama
naki, ina aka taba yin hka? Bbu shawara
bbu
komai xaki je ki walakanta min abun da
akalla
xan iya saida shi miliyan daya da rabi."
hajiya da
umma dake palon ji sukayi kmr su shide
don
murna, Aliyu ya kasa hadiye dariyar dake
cinsa
ya fasheta, abba ya juyo kansa ya dinga
masifa
kmr xai maresa, ba shiri ya kame kansa, don
ran
abba yyi mugun baci ranar. Ganin ba sarki
sae
Allah yasa inna ta fashe masu da kuka tana
cewa "tunda yusufa ya rasu dama nake
shan
wahala a duniyar nan, daga kai har 'ya
yanka
bakwa tsinanani da komai, ni ke yi ma kaina
duk
bukata, Abba ya bude baki yana kallonta ya
ma
kasa cewa komai, shi din ne baya mata
komai?
Gnin ta dage sae rera msu kuka take ne
yasa ya
shiga bata hkri, tce "hka kawae baxan
kyautatawa
aminiyata ba jikarta xatayi aure, kuma
nasan idan
na tambayeka ba bani xakayi ba," Abba ya
girgixa kai yana mamakin uwartashi, duk
juma'ah
sae ya bata dubu goma bayan abubuwan
da yake
siyo mata duk karshen wata sannan ya
damka
mata dubu ashirin ko tana da bukatar kudi,
amma yanxu kiri-kiri tace bbu mai taimaka
mata
a duniyar nan sae Allahnta, komai ita take
ma
kanta. Abba yace "to shknan inna, Allah yasa
hkn
shine mafi alkhairi, kudaden sun isheki de
ko? Ta
dan fara kame kame tana goge kwalla tace
"ni
idan san samune akara min dubu hamsin,
ko
kuma dari ma." takaici yasa abba gyada kae
kawae, ya dubi Aliyu yace anjima ka ciro
mata
dubu hamsin Ali, xan bka, "tab! Ai ni abba
accnt
dina ko dubu goma bai kai ba ina ga ma."
... Inna ta galla masa harara tace "Allah ya
dauwamar dasu a hka," Haisam yace
"anjima xan
ciro na kawa maki inna." nan ta dinga sa
masa
albarka, abba yyi mata sallama ya fice daga
palon nata cike da jin haushin hali irin nata,
Aliyu
ya bi bayansa yana cewa "wannan ai sata
kiri-kiri
ne kawae, daga an baki ajiye sae ki
maidashi
naki" bai jira me xata ce ba ya fice da sauri
yana
dariya. Haisam na fitowa daga palon innar
umma
ta aika a kira mata shi yaje, nan kuwa ta
balbalesa da masifa tana cewa" kai dinnan
soko
ne wllh, Aliyu ya fika wayo nesa ba kusa ba,
kana tunanin idan ka dauki kudin naka har
dubu
hamsin ka bata Alhaji bka xai yi ne? Kai dae
bn
san wani irin yaro bne Allah ya bani, don
meyasa
baxakayi koyi da Aliyu ba, duk ka bi ka tare
gurinta sae kce ta asirce, wllh idan baka yi
gaggawan sauya wannan mugun halin
naka ba
sae na saba mka" haisam ya girgixa kai cike
da
takaicin hali irin na uwartasa yace "Allah ya
kyauta! Sannan yafice a fusace. Shi kam
Aliyu
hajiya yaba masa ta dinga yi tana sa masa
albrka, shi dae bai tanka mata ba. Da
yammacin
ranar Haisam ya kaita gidan aminiyartata
bayan
ta

1 Comments On INTEESAR 1 TO 4
avatar
hamadou

1 year ago

Reply

Compte gogle

Please Login or Register in order to submit comment