Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ali xan watsa maka mari," Abba ya dubi intisaar yace "ina
jin ki fateema," ita kam tuni ta fara rawan dari, ta juya ta sace kallon Aliyun, ta ga kallonta
yake yi, idon nan nasa yyi jajur. Ta girgixa kai muryarta na rawa tace "wllh Abba ni ban
san komai......" inna ta daka mata tsawa tace "to ke din ma karyatani xaki yi, bayan nace kina
wajen kuma kece shai'data,?" aa inna, ta fadi tana kokarin maida kwallar da ta taru a idonta, xan fadi
gaskiya. Ta juya ta kara sacen kallon Aliyu, har yanxu kallonta yake yi, ta ma rasa wani irin
kallo yake mata, can dai tace "Abba dama yaxo ya same inna ne akan maganar dawowarsu
Hajiya,
shine sae inna ta fara masa masifa......" fashewar dariyar xainab ne ya katse ta,
Abba yace "meye haka,? get out" da sauri xainab ta mike ta fice tana dariya. Inna kam tuni ta
Bude baki tana kallon intisaar, Abba yace "ina jin ki fateema" ta dan gyara xama tana kallon
Aliyun sannan taci gaba " shine sai bai ce mata komai ba, tana ta fada har......" murmushin da taga
Abba yayi ne yasa tayi shiru. Sai a lokacin inna Ta saka salati tana tape hannu baki a bude,
Abba ya dube intisaar yace "je ki fateema" ta mike da sauri ta bar falon ba tare da ta kalle kowa ba.
Da sauri ta shige palonsu, momy dake xaune ta dubeta tace "lafiya?" ta kirkiro murmushi tace
Ba komai. To ranar dai Intisaar ko nan da kofa bata fita ba, tana palo a xaune har da yamma,
Xainab ta shigo tana ta tuntsirar dariya, ita dai bata Ko kalleta ba ma, ta dae gama dariyar ta ta fita.
Wajen karfe biyar taji muryar inna da alamar sashinsu xata yo, da sauri ta figi hijabinta ta
fice, momy tana ina xaki amma tuni ta fice, ta canxa hanya don ma kar su hade da innar,
Ta sashinsu xainab ta bullo, xainab tace "daga ina haka? Ina xaki" ko kallonta ma bata yi ba tayi
gaba abinta, dariya xainab tayi tace "yau yarinya ta watsa ma innar ta kasa a ido," hanyar gate
intisaar tayi har wani xaxxabi ma take ji, xaune taga Aliyun a kusa da gate yana waya......
.. Yana ganin ta kuwa ya mike, ta tsorata sosai ta juya xata gudu, yayi hanxarin fixgo ta,
Ta saki kuka tace "na shiga uku me nayi....." tura ta da yayi ne ya sanya ta hadiye sauran
Maganar tata, "Allah ya taimake ki yau da sai nayi gunduwa gunduwa da ke" ita kam babu baki
Sai gyada masa kai kawai takeyi, tashi a gaba kar nayi ball dake, da sauri ta fice daga gate din
Ba tare da tasan inda xata ba. Gidan wata kawar xainab dake nan layin ta shiga, farida tayi
mamakin ganinta don tasan baxuwa gidansu intisaar take ba, nan dai ta tsaya har tayi
maghrib sannan ta kama hanyar gida, yanxu tsoranta daya gamuwar ta da momynta don
tasan inna ta gya mata. Tana isa gate tayi jigum a bakin gate din ta kasa shiga, can dae sai
ta fara leke-leken cikin gidan, taji an kirata, da sauri ta juya a dan firgice suka yi ido hudu da
faruuq,
"lah.. Ya faruuq yaushe kaxo?" yace "hmm” leken
me kike yi a cikin?"
no xainab nake jirane, mu shiga ciki," tayi saurin shigewa gidan, ya bita a
baya yana murmushi, yasan ba gaskiya ta fadi ba.
Ta juya ta dubesa tace kaje can wajen inna gani nan xuwa dama momy ce ta aikeni," to bari
Na fara gaida momyn mana," da sauri tace "a’a kadai je gun inna idan xaka tafi sae ku gaisa,"
yace ok
sannan yayi sashin inna.
Tana isa kofan parlonsu sae da tayi kusan minti biyar sannan ta shiga,
momy da ihsaan na cin abinci, ta nemi gefe ta rakube, momy ta harareta bata ce komai ba.
A haka suka gama cin abinsu. momy taje tama ihsaan wanka, ita dae tana nan a bakin kofa
A xaune. Xainab ta shigo da sallama tace "ke yar walakanci ce pa yarinyar nan, shine xaki bar
bawan Allah tun daxu yana jiranki," ta mike da sauri tace "bari nayi wanka na manta ne,"
sannan ta shige bathroom tana satan kallon momy dake shafawa kanwar tata powder. Ta saka
kayan barcinta sannan ta dora dogon hijab har kasa ta fito, ta dubi momy tace "ina xuwa momy,"
ko kallonta ma bata yi ba ta fice a sanyaye, ko me inna ta tsara mata oho. Tana isa sashin inna
ta nemi gefe ta tsaya sannan ta fara kiransa, bugu daya ya dauka tace "ka fito ya faruuq ina
nan waje," yace "baxaki shigo....." da sauri ta katse sa ta hanyar cewa "aa ka dai fito ina jiranka
sannan ta kashe wayan" ya dubi inna yace "inna ni xan tafi sai wni lkcn," aa to ina intisaar
dinm baxa ta xo bane, yace "aa tana nan waje tana jirana.
Yana fitowa ya kalleta yayi murmushi yace "sae yanxu?" bata ce komai ba sae gyada
Masa kai da tayi, sae da ya fara shiga suka gaisa da momy sannan ta rakosa gate, ya dubeta yayi
Yar dariya yace "me ya hadaki da innar taki baki San shiga wajenta?" tayi yake tace "aiki xata
sani ne shi yasa" yyi dariya yana kallonta yace "ke dae fadi gaskiya kanwata," ta kauda kai bata ce
komai ba sae hmm. To bara na wuce kar Abbanki yaxo ya same mu a nan ko?" da sauri tace
"wa?"
ya kashe mata ido yace "Aliyu mana" tace
"uhum kaga sai da safe ya faruuq yau ba hira kake san min ba" yayi dariya yace "dama ae wuce wa
Xanyi bayan kinsan kin wa inna laifi xaki turani can" bata ce komai ba sai murmushin da tayi, ya
Ciro kudi mai yawa yace taba ihsaan, don yasan ita ba karba xata yi ba, shima din da kyar ta
Karba, suka yi sallamah ya wuce, sannan tayi
sashinsu.
Tun faruwar abin suke wasar 'yar buya da inna, yau dae kam har dakinsu inna taxo ta
sameta, tayi mata tatas, ita dariya ma abun ya bata, can dae ganin ba kyaleta inna xatayi ba tace "to
naga dae inna ba sharri nayi......" dundun da inna ta kai mata ne yasa ta fashe da dariya, tace
"kai ni inna ki kyaleni, haka kawae ban ji ba ban gani ba ya Aliyu ya min duka," da kyar inna ta kalleta
Ta bar sashin nasu, momy dae bata ce masu komai ba, sai gashi da daddare wae xata wajen
inna, momy tace "amma baki da kunya wallahi" tayi dariya tace "to momy ae dae inna ta ce."
A hanya suka hadu da xainab, ta bude baki tace yau kuma wajen inna xa a? Har an manta... Duka ta kai
mata ta bar wajen da sauri, xainab ta bita ita ma tana cewa "tab ae wllh sae na rama" da
sauri ta bude kofar palon ta afka ciki tana dariya,
Inna tace "lafiya ke da wa?" ta juya da sauri xatayi magana sae kuma tayi shiru ganin Aliyu
xaune a parlon yana cin abinci... Xainab ta shigo ta da'da mata duka ita ma sannan tace "na rama"
intisaar dae bata ko kalleta ba sae kame-kamen da ta fara yi, inna tace "ku dae ban san randa
xaku girma ba," Aliyu ya mike yayi tsaki ya dube
xainab yace "get out kar na fasa maki kai," ta harare sa
tace "saboda kan nawa......" da gudu ta fice ganin ya yo kanta, ae intisaar na ganin haka ita ma
ta fice a guje, inna tace "kai wallahi mugu ne yaro nan" kofar ya rufe ya dawo yaci gaba da cin
abincinsa yana kallo. Suna xaune a palon inna,
xainab na daddanna mata kafa, intisaar kuwa kallo takeyi sae kursum dake kwance ita ma
tana kallon, inna tace "wannan yaron yace xae xo da bakuwa yau ko me xamu girka mata?"
xainab ta yatsine fuska tace wai Aliyu? Inna tace "eh," ta tabe baki tace abinda muka dafa a gidan
xamu bata mana. Khadija dake dakin inna tace "kamar ya abinda muka dafa xamu bata? Ita bakuwar
xa a ba wa dafa duka?" xainab tace "shi kuma dafa dukan ba abinci bane ba koh?" khadija tayi
tsaki tace oho. Kar ki min rashin kunya wallahi don xan fasa maki baki, xainab ta fadi tana kokarin
mikewa, inna ta fixgota tace rabu da ita.
kursum je ki ki kira min Zainabu, da gunguninta ta fice wae ita ta gaji. Ba a jima ba momy ta
iso, inna tace "zainabu shinkafa da miya xaki girka min, wae Aliyu xai xo da bakuwa, wannan
gantalallun 'ya yan sai yawo suke da hankalina.
Ta ce "to inna sannan ta fita." xainab tace "inna budurwarshi ce?" inna tace kya barni
budurwa,"
kursum tace yau akwae buduri kenan. Nan inna aka tashi aka fara gyare gyare su xainab na
tayi mata dariya kuma suka ki taya ta, intisaar kadai ce ta kama mata aikin don wae bayan
la'asar xasu iso. Momy ta gama girki ta kira xainab taxo ta dauka ta kawo sashin inna. Karfe hudu
da rabi ya shigo parlon da sallama, yana sanye da kananan kaya yayi kyau sosai, inna ta amsa
da fara'arta tana cewa "ina yarinya," yace tare muke, sannan ya dubi su xainab yace "ku kuma
uban me kuke yi a nan, da sauri intisaar ta shige dakin inna, xainab ma ta bita kursum kadae ce
taki tashi, har yarinyar tayi sallama da siriyar murya, inna ta amsa da karfinta tana wangale baki,
yarinyar ta shigo palon.
... Tana shigowa palon ya nuna mata kujera ta xauna, kursum dake kwance dama tuni ta
mike tana karewa yarinyar kallo, doguwa ce kyakkyawa fara amma da ganinta kasan ta
hada da mai, tana sanye da atamfar Holland an mata shegen riga da skirt dinkin ya dameta sosae,
sannan ta sakale wani dan guntun mayafi kalar atamfar tata yellow a wuya, make up kuwa
har da na hauka don har da su blusher, sae
wani yatsine fuska take, inna dama tuni bakinta a bude yake... Kursum ta dan sa kafa ta bugi
inna alamar ta rufe bakin, ba shiri kuwa ta rufe hade da cewa "ikon Allah! Ina yini? Yarinyar ta
kalle innar tace "sannu baba" tana taunar cingam hade
da karewa parlon kallo, inna tace "yauwa pa" Aliyun kuwa tuni yayi hanyar fridge xae
dauko mata lemo da ruwa. Inna dae ta dage sae kallonta take daga sama xuwa kasa, can sae
ta fashe da dariya, kursum ta rufe fuskarta cikin kujera dan ita ma kar tayi, don shi ke cinta,
daga yarinyar har Aliyu juyawa sukayi suna kallon inna, inna dae ta kasa daena dariya, Aliyu yace "wae
meye haka ne Hajiya?" tayi kokarin shanye dariyar tace "wallahi wani abu na tuna ne" sae kuma
ta kwalo wa xainab kira, "xainab ku xo gu gaisa da Antyn taku mana" xainab dama kamar jira
take tafito da sauri don tuntuni take son lekowa amma tana tsoran kar Aliyu ya ganta, intisaar ma ta
fito don tana san ganin budurwar tashi, gefe suka nema suka xauna, xainab ta kalle yarinyar
sannan ta kalle intisaar da ta sunkuyar da kai
saboda dariyar dake cinta, ita kanta xainab daurewa take amma da tuni ta fashe da ita.
Inna ta sake kwashewa da dariya tana kallonsu xainab din, tace "ku kawo ma antyn taku abinci
“No”a barshi kawae naci a gidanmu kafin na fito," Aliyu sae kallon inna yake cike da takaici.
Inna ta kara dacewa "to ai bamu ma san sunanki ba" sunanta safeeyna, Aliyu ya taya ta fadi. "ayya
amma wannan telan naki bai maki adalci ba, atamfa har atamfa amma ya tashi yayi maki
dinki kamar 'yar babyn roba, ae wannan riga taki ko ihsaan jikin ta baxae shigeta ba, amma
wannan anyi dan banxan tela," inna ta fadi tsakaninta da
Allah babu ko dar. Xainab bata san sanda dariyar da take ta hadiyewa ya kubce mata ba, ta
Xube jikin intisaar tana dariya kyal kyal kyal,
intisaar ta daure iya daurewa amma ta kasa rike nata dariyan, nan ita ma ta fashe ta har da
xubewa kasa, kursum ma yi take har da bingirowa daga kan kujera, inna ta bude baki tana kallonsu
da mamaki can ita ma dae ta fashe da dariyar suka taru suka dinga yi, "ni wallahi ca nake xabiya
ce ma ta shigo don hasken yayi yawa, tsoro ma ne ya kamani...." inna ta sake jefo masu. Xainab
har da hawayenta don dariya, intisaar cikin hijab din xainab tashige ta dinga yi kamar wasu
sababbin kamu. Aliyu kam kasa cewa komae yayi sae kallonsu da yake yi daya bayan daya.
Safeenah kam iya kan kulewa tayi shi, ta mike tsam tana kallon Aliyun a nutse tace "Haidar help me
out of dis forsaken house plss" inna tace "lah har xata wuce?, ko me take cewa?" tuni safennar ta
fice daga palon innar da takalminta me kamar tsani,
inna ta tafe hannu tace "ohh yanxu idan ta fadi da tsautsayi ba karyewa xatayi ba da wannan
tsanin dake kafarta" ya mike da sauri duk a rikice yake ya fice ya bita yana kiran sunanta, inna ta bude
baki tace "ikon Allah ko sallamah babu ni Rahmatu" sae kuma ta mike da sauri tayi
bakin kofa tana cewa "Aliyu kakai ta, ta gaida xainabu tana ciki" amma tuni har sun ma isa gate. Ta
dawo tana cewa "inda ranka xaka sha kallo" ta kallesu xainab da har yanxu dariya suke kamar
mahaukata, ta hade rai tace "kai ni fa bana son iskanci dariyar meye haka?" kursum ta mike
tace "na tafi wajen momy ni kam kun ga tafiyata, don yau idan ya Aliyu......" shigowar khadija ce ta sa
tayin shiru, don dama taje wanke gashi, ta dubesu idonnan na ta a xare, tace "kai!! me
kuka yi wa yaya Aliyu? Naji yace wallahi sai ya sumar da mutum daya a gidan nan " tana fadin haka,
kursum ta bar falon a guje xa ta sashinsu intisaar, nan da nan hawaye ya fara sintiri a idon
intisaar, cikin kuka tace"xainab wallahi ke ce kika....." wani axababben ihu can ciki ciki
suka ji kursum ta saki... Sallati inna ta saki ta fice a
guje tana cewa shikenan ya kashe ta!!
Intisaar ta daura hannu biyu aka tace wayyoo nashiga uku na lalace, xainab tuni ta firfito da ido cike da
tsoro tace "mun shiga uku!!!"
Aliyu ya kauda kanshi ba tare da yace
mata komai ba, sai da Abba ya bari tayi mai
isarta tayi shiru sannan ya nisa yana duban
Aliyun da kyau yace "ka gya min meye
Matsalar ka a gidan nan, me ke damunka?" kansa kawae
ya sunkuyar ba tare da yace komai ba, "why is it alwayz you in this house? Don me ba a kawo
min karar haisam sae taka? Look.. Wallahi ka sake taba min wani a gidan nan sae nayi mugun saba
maka,
mutumin banxa kawae, tunda ka dawo gidan nan hankalina bae kwanta ba" ya dago kai da
kyar
yana duban Abban nasa yace "to Abba ka
gyawa inna ta fita harkata ta daina min...." shut up!
Abba ya katse sa a fusace, " dama duk cikin 'ya yana kai ne baka da manner, amma xanyi maganinka" Abba ya mike ya shige
Bedroom sakamakon kiransa da akayi a waya, sae a sannan Aliyun ya dago ya fara kallonsu daya
bayan daya a palon, ya mike yana duban innar dake kallonsa yace "ba wata tsiya bace idan
na bar maku gidan, amma sae kun sake gani na "
sannan ya juya xae fice, inna ta mike da sauri tana cewa "to Bukar sae kafito gashi nan ya
hada kaya xae bar gidan wae" ido Aliyu ya xaro yana kallonta, ya koma inda yake da sauri, Abba
ya fito yana kallonsa yace "to tashi ka wuce" bae ce komai ba sae tiles din palon da ya xubawa
ido,
Nan Abba ya dinga masa fada kamar xae ari baki, inna na ta xuga sa, har dae daga karshe
Abba yace ya fice masa a palo, ya mike ransa a bace kamar ya hadiyi xuciya ya bar palon.
Da Yammar ranan intisaar da xainab suna tsakar gida tare da inna dake yi ma ihsaan tsifa take tambayar su
Ko sun ga Aliyu tun daxu don tun bayar barinsa palon abba basu sake ganinsa ba khadija
ma ta kai masa abinci daxu da rana ta gama bubbuga kofarta ta dawo bae bude ba, xaenab tace
"kila tafiyar yayi," inna ta dan marairaice fuska tace "Allah dae yasa ba tafiya yayi ba...."
Budewar gate din da akayi ne ya sanya su duka suka maida hankalinsu wajen, Aliyun ne ya shigo, yayi
Sashinsa ba tare da ya kalle su ba, sae ga Hajiya ma tashigo rike da jaka, umma na biye da ita a
baya,
sannan khadija ma tashigo da wani jakar a hannunta, da gudu xainab taje ta rungume
uwartata, kursum ma dake kusa da wani flower a xaune taje da gudu ta rungume ummarta
harda kuka, nan da nan inna ta hade rai kamar bata taba dariya ba, intisaar ma ta mike da sauri ta
karbi kayan dake hannun hajiyar tana masu sannu da xuwa, har kasa suka durkusa suka gaida
inna, ta amsa masu can ciki-ciki ba tare da ta kallesu ba, momyn intisaar ma ta fito tayi masu sannu
da xuwa da fara'arta, sannan duka sukayi sashinsu, tsakar gidan ya rage daga inna sae intisaar
da ihsaan, inna ta tabe baki tace "shegu munafukai,
wallahi ni banyi farin ciki da xuwansu ba tsinannuna mutane." intisaar cike da jin haushi tace "ni
bana son wannan abinda kike yi inna wallahi,"
sannan ta bar mata wajen ta koma sashinsu.
.. Tun ranar da Hajiya da umma suka dawo gidan suka shiga taitayinsu, don ba karamin
tashin hankali suka shiga ba kwanakin baya don a nasu tunanin Alhaji ya sake su ne basu sani
ba.
Kullum da sassafe suke xuwa gaida inna. Abinda basa yi da, har wani shiri suka tsiri yi da
Momy duk da na munafurci ne. Yau kam intisaar na xaune gaban inna tana mata hira, inna tace
"yauwa wannan yaron faruuq yaxo ya sameni jiya da daddare wae yana so ke da xainab kuje
Gaida mahaifiyarsa," intisaar ta firfito da ido tace
"kai; inna sae kika ce masa me?" eh nace ranar juma'a ya xo ya kai ku, gobe kenan." intisaar ta hade
Rai tace a’a ni babu inda xanje inna, ke kinga hakan ya dace? Saboda gantali kawae sae na kwashi jiki
Naje gidansu" nan da nan inna ta hade rai tace "to idan yaxo goben karki bisa" intisaar ta mike
Ta fice daga palon tana cewa "ni kam babu inda xanje." tana komawa sashinsu ta fadi ma
momynta, momy tace "A'a ko da ma xaki je gidan nasu ba yanxu ba sae lokacin da ya dace," da
yamman ranar faruuq din ya kirata, da kamar baxata dauka ba sae kuma ta dauka don taji
haushinsa sosae, anata tunanin it’s not decent yace xae kai ta gidansu bayan ba ayi
maganar komai ba tukun.
Bayan sun gaisa yake ce mata
inna tayi mata magana, tace "eh amma babu
inda xani" yayi murmushi yace "to shikenan kanwata." nan dae ya dinga mata hira har yace mata
xae je masallaci don lokacin sallah ya kusa.
Da daddare xainab ta shigo palonso intisaar din tace "ke wae inna tace gobe faruuq xai kai mu wajen
momynsa" intisaar tace "eh amma babu inda xani"
xainab tace saboda me? Ke kinga hakan ya dace?
Intisaar ta tambayeta tana jiran amsa"
Xainab tace "to meye a ciki don munje gaida mamarsa?
Ni dae banga rashin dacewar hakan ba wallahi" intisaar ta mike tace "ke kya iya xuwa, amma ni
baxan je ba." sannan ta shige daki, xainab ta tabe baki ta yi gaba abinta. Washegarin ranar juma'a
inna ta xo sashinsu wajen karfe sha daya, tana kwance tana kallo, momy kuwa na bedroom, inna
tashigo palon tana cewa "ke wai wace irin yarinya ce xaki bar bawan Allah tun daxu yana jiranki,
wannan wani irin wulkanci ne, na aiko a kiraki yafi sau hamsin sae kice min kina xuwa?" intisaar
tabe baki tace "ko ma de sauna nawa ne ni dae
ki rabu dani inna babu inda xani pa" au uwar taki ta hura maki kunne kice min baxaki ba kenan?"
da sauri momy ta fito tace "maxa ki shirya kuje, ni ban hanata ba inna" dolenta ta shirya cikin
atamfa java red colour an mata dinki riga da skirt dama gata fara sosae sae ya amsheta, ta danyi
kwalliya tayi kyau sosai sannan ta dauki hijab dinta har kasa, ta fito palo tace "momy na
tafi" momy tace "ki kama kanki, kuma ku tafi da ihsaan, sannan ki turo min xainab" ae da ita
xamu momy, momy tace "eh nasani," tana fita tayi sashin su xainab, ta hadu da khadija a
bakin kofa tana dauraye cup, tayi mata wani irin kallon
banxa sannan tace "amma de kinyi batan hanya ne ko?" tayi jim sannan tace momyna ke kiran
xainab. Aliyu ne ya fito yana dubanta yace
"get out" cikin tsawa, xainab ta fito da sauri ita ma ta
shirya cikin wani material ja, tace gani nan xuwa intisaar. Gidan uban wa xaki? Aliyu ya
tambaya yana kallon xainab din, "inna ce xata aike mu gidan kawarta wae," bae sake cewa komai
ba ya shige ciki kawae, hajiyarsu kuwa tana sashin umma suna tseguminsu da suka saba. A
tare suka je sashin inna da xainab din bayan taje kiran da momy ke mata, ita dinma ta ja mata
kunne ne akan su kula da kansu, ashe faruuq din
ma bae xo ba inna duk tabi ta axalxalesu.
Sha daya da rabi ya shigo gidan, suka gaisa sannan,
inna tace, "amma dei da wuri xaka maido su ko?" yace in'sha Allah inna. Ita dae intisaaar
hade rai ko kallonsa ma bata yi ba. Har bakin kofa ta rakosu sannan ta koma. Sae da suka
hau kan kwalta sannan ya fara hira da xainab, ita dae jinsu kawae takeyi sae wayanta da take ta
daddannawa.
Tafiyar kusan minti talatin sukayi sannan suka iso gidan nasu, yayi horn aka
Bude gate ya shiga yayi park, sannan ya bude masu kofa suka fito, da ganin gidan kasan lallai
mahaifinsa mai kudi ne sosai. Kanwarsa ya kira ta fito,da ganinta baxata wuce su ba, tayi
masu sannu da xuwa tashiga dasu ciki da fara'arta Har palon mahaifiyarsu tayi masu iso,
sannan ta nuna masu kujera su xauna ta cika su da drinks da kayan ciye ciye, ba a dau lokaci ba
mahaifiyar tasu ta shigo palon, suka sauka har kasa suka gaisheta ta amsa da fara'arta
tanai masu sannu da xuwa sannan tace suyi xamansu a kan kujerar, xainab tace nan ma yayi momy,
"a’a don Allah kuyi xamanku nan ba bakon waje bane," da kyar dai xainab ta xauna kan
Kujerar amma intisaar taki xama, hakan yasa momyn
Ta gano ita ce fateemar. Nan dae ta tambayesu ya mutanan gidan suka amsa mata da duk
Suna lafiya. Ba a jima ba faruuq ya shigo yace xae wuce masallaci tayi masa Allah ya kiyaye hanya
sannan ya wuce yana kallon intisaar amma bata bari sun hada ido ba, sae da suka fara yin
sallah, sannan aka cika su da abinci kusan kala hudu,
Ita dae intisaar ta kasa sakin jikinta ga kunyar momyn da take ji, ganin hakan yasa momyn ta
basu waje tashiga ciki, a tare da kanwarsa ummi suka ci abinci, yarinyar na da kirki sosai,
suka dinga hira kamar da can sun san juna. Karfe biyu faruuq ya shigo gidan ummi ta kai masa
abincinsa dakinsa sannan ta dawo suka ci gaba da hirarsu akan makaranta da sukeyi, sae da
faruuq ya dawo parlon sannan momy ma ta fito, nan dae aka dinga hira amma ban da intisaar da
sae dae tayi murmushi, karfe uku da rabi yace xae maidasu gida saboda traffic, momy tashiga ciki ta
hado masu tsaraba mai yawa tun daga kan atamfa har xuwa sabulai da omo da
jeweries na fashion masu kyau, da after dresses, ummi ma tashiga ta hado masu nata tsarabar na
kayan make-up da turarruka kala-kala, intisaar tace "mun shiga uku xainab, don Allah kice ma
faruuq yace su rage sunyi yawa wllh. Xainab tayi banxa da ita ta dinga godiya kawae, har kusa da
motar suka rakosu sannan ya ja motar suka bar gidan.
Ganin yayi park a wani supermarket ne ya sanya intisaar tace masa "me xamuyi a nan, yace
wannan ba matsalarki bace. Sannan ya shiga ciki, wani tsarabar ya kara hado masu, sannan
ya siya ma inna malt carton daya, da peak milks holland, aka xo aka xuba kayan cikin booth
sannan suka bar wajen. Ana gama sallar la'asar suka iso gida, ya fiffito masu da tsarabar
tasu xainab ta bude baki tana kallonsa tace "me yasa xaka daurawa kanka nauyi haka ya faruuq,"
yace ni dae ku shiga dasu ciki xanje masallaci nayi sallah yanxu, sae na dawo. Kursum ce ta taya su
suka dinga jidar kayan suna sashin inna dasu, shima dan gulma tayi hakan amma ba don
saboda da Allah ba, Aliyu suka tarar xaune a palon, inna ta mike cike da doki tace "kar dae har kun
dawo?" intisaar tayi mata alamar tayi shiru saboda Aliyu dake xaune, haka ma xainab da ta daura
hannunta a baki alamar inna tayi shiru, inna tace "ayyo
haka ne pa." Aliyu yace "ina suka je da?" da sauri inna tace "gidan hajiya Maimuna na aikesu." to
wannan kayan meye haka? Cikin in ina inna
tace
"eh eh.. au ita ce ta bada

1 Comments On INTEESAR 1 TO 4
avatar
hamadou

1 year ago

Reply

Compte gogle

Please Login or Register in order to submit comment