Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nufi hanyar bedroom, bada dadewaba ya dawo dauke da waya kirar iPhone 11pro ya bata tare da cewa "ga wayanan na sayawa Kanwata" karba tayi hade da mikewa tsaye ta daka uban tsalle ta fada jikinsa ta rungumesa sosai, shi kam wani irin yarrrrr yaji ga jikinta da bala'en laushi da tsantsi kamar maciji.
Da sauri ya tureta daga jikinsa, itakam koh a jikinta saima murna da takeyi sannan tace "ngd ngd sosae yayanah, ta Mike ta fita dadan sauri sauri gudu gudu shikam bin bayan ta yayi da kallo hade da lumshe idanunsa.

Part dinsu inna ta nufa ta gwada mata wayarta sannan ta nufi dakinta.

Da daddare da misalin karfe goma najeeb ya fito daga room dinsa yanufi dakin amrah Wanda take kan gado cikin wasu hadaddun kayan bacci pink color wando da riga, tana ta danna wayarta, jin alamar an bude kofar dakinta yasa ta Dan dagowa ta kalli kofar, ganin mutum a tsaye yana kallon ta kamar xai cinyeta yasa ta saurin durowa daga kam gadon,

Shikam najeeb karasowa yayi cikin dakin ya nufeta gadan gadan ganin haka yasa ta Juyawa Dan ta shige bandaki, da sauri ya damkota ya matseta ajikinsa ya shiga shinshinar wuyanta,

Kokarin kwatan kanta take amma ta kasa, tace "Dan Allah ka kyaleni wlh ni ba yar iska bace, juyo da ita yayi yasu hade bakinsu amma taki bari, wanka mata Mari yayi saida gefen bakinta ya fashe.

AMRAH kam tashiga rokansa akan ya kyaleta amma ina yaki tun tana bashi hkr har ranta yafara baci 😑fatar jikinta ta fara sabulewa tana xama ta maciji🐍

Hmmm lalle najeeb ka taboo ruwan dafa kanka 🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣

πŸ’«Rabeauty πŸ’«
*please vote, comment and share *
[8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: πŸ’«AMRAH MACIJIYA πŸπŸπŸπŸ’«

By Rabeauty πŸ₯°πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«

*Aslm amrah fans, yh kuke, kwana da yawa, yh sallah, da fatar kowa yayi sallah lfy, Allah ya maimaita mana, kuma kar a manta da goron sallah nah, nida amrah macijiya*πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ

(11)
Suhaima kam dakin amrah ta nufa, ita kuma amrah a lokacin tana waya da jalal sai fira su keyi,

Da karfi Suhaima ta banko kofar wanda hakan ne yasa amrah saurin tashi daga kwanciyarda tayi, wani irin shu'umin murmushi tayi sannan ta kalli wayarta da jalal yake ta "hello" hands free tasaka wayar sannan tace "yayanah kasan wani abu", aa Kanwata saikin fada, kallon Suhaima tayi sannan ta maida hankalinta ga wayar tace "so nake kasake gayamin wannan kalmar daka fadamin a airport"

Murmushi yayi mai sauti sannan yace "I love you so much my darling"

Murmushi tayi itama sannan tace "nima ina sanka yayanah kuma koh wace irin kaddara xan iya dauka amma banda wacce xata rabani dakai, kuma koh wane yayi kokarin shiga tsakanin mu toh wallahi saina kawar dashi daga doron kasa" tana gama fadar haka ta kashe wayar,

Ai a harxuke Suhaima tayo kanta tana xuwa ta kwace wayar ta ta jefata da bango nan take wayar ta watse, ai da sauri amrah tayi kan wayar ta wasu hawayen bakin ciki suka xubo mata, Suhaima koh jelar gashin amrah ta damka da karfi Wanda yasa amrah sakin kara, hankadata tayi saida kanta ya bugi gado, ta shako wuyanta ta wanka mata mari ta sake kara mata wani, ai take hanci da bakin amrah yafara fitarda jini, ta sake daga hannunta da niyar kara marinta, amrah ta rike hannunta, idanta sunyi jajir sosae abunda basu taba yiba kenan saidai sukara green, amma yau kam jajir suka yi,

Dakyar amrah ta bude bakinta tace "lalle Suhaima kin tabka babban kuskure tunda uwata ta haifane ba'a taba yimin hakaba, amma yau wai nice wata ta mareni har ta fitarmin da jini hmmmmm, nida koh kallon banxa mutum yamin sainaga bayansa amma wai ni *AMRAH MACIJIYA* 🐍 aka mara,

Suhaima najin haka jikinta yadau kyarma, wasu irin fitinannun tagwayen mari amrah ta wanka mata, Wanda suka yi sanadiyar fashewar hanci da bakinta nan take ta fadi kasa, nan amrah ta sake wanka mata wasu marukan a lokaci guda, wannan karon kam gaba daya dena ji Suhaima tayi, tana kuka tace dan Allah kiyi hkr, nasan na aikata kuskure amman wlh shairin shaidanne,

Rufemun baki amrah ta daka mata tsawa hade da girgijewa ta xama shirgegiyar macijiya 🐍,

Ai nan take Suhaima ta sumeeeee.

*Mascow*

Jalal kam kalaman amrah na karshe sune suka tsaya masa arai ya rasa ina kalaman ta suka dosa, sadeeq neh ya shigo yace, "haba buddy tun daxo muke jiranka fah amma kaxo nan kanata waya da girlfriend dinka, kuma kasan yaune xa'ayi wannan tiyatar, kuma inaji ajikina inshaa Allah xamuyi nasara"

Hakane nima inaji ajikina, muje suka fito suka shiga mota direct *Mascow International hospital* aka kaisu, suna xuwa babu bata lokaci suka shiga tiyatar,

πŸ’¦Ni kuma nace all the best jalal πŸ’¦

*KANO*
AMRAH kan saida ta wahalarda suhaima sannan ta kyaleta, dakyar Suhaima ta iya Jan jikinta tanufi dakinta,

Ita kuma amrah gurin wayarta ta nufa tana xuwa ta dauki a barta ta haye kan gado tasa tafin hannunta ta shafe wayar nan danan tadawo sabuwa gal, ta tashi tasaka caji ta nufi bangaren su inna,

Tana xuwa ta xauna acan sukasha firarsu da inna,

Hajiya Sarah koh tana can tana neman yadda xata kawarda jalal, da taje gurin bokan hajiya nafeesa ce mata yayi "a gaskiya indai kinason kawarda jalal daga doron kasa toh fa saikin fitarda wannan yarinyar daga gidanki sbd indai tana cikin gidan toh fa bbu abunda xamu iyayi", toh amma boka meyasa kace haka,

Dariya ya kyalkyale da ita marar dadin ji sannan yace "ga wannan ki turarashi a cikin gidanki koh wane lungu da sako, xakisan dalilin da yasa nace saikin fitarda ita tukun" karba tayi tace ngd boka, ta fito ta dawo gida,

Tana xuwa tasaka mai aiki ta ibo mata garwashi Dan tayi turaren da boka ya bata,

Ita kuma amrah har ynx tana part dinsu inna,

Mommy kan dauko wannan turaren tayi ta bude ai da sauri ta rufe, tafarnuwace da k'ashi da kuma barkono aka hade gu daya aka nikesu,

Kunsan mee hmmmmm, wannan turaren idan amrah tajishi tohfa xata rikide ta xama macijiya kuma kunsan tana part din inna, kenan asirin amrah xai tonu koh yaya, ku biyoni kuji yadda xata kaya πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ

πŸ’«Rabeauty πŸ’«
*please vote comment nd share*
[8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: πŸ’«AMRAH MACIJIYA πŸπŸπŸπŸ’«

By Rabeauty πŸ₯°πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«

(9)
Wani irin hankadashi tayi saida ya daki bango,

A fusace ya dako, Amma me ganin yayi amrah ta rikide ta xama shirgegiyar macijiya amma bagaba dayaba,

Daga samanta xuwa kugunta tananan a mutum dinta, amma daga kugunta xuwa kasan ta yaxama na maciji, gashin kanta ya mimmike tsaye ya koma macixai, idanunta sunkara xama green sosai hatta kwayar idonta da take fara toh itama ta koma green, kunnen ta yana fitarda wani hayaki, Wanda ya turnuke dakin baka iya ganin komai,

Najeeb kam tuni xawo da fitsari sun kubce masa Dukda Baya ganin ta sbd hayakin amma behanashi ja da bayaba yana cewa

"Dan Allah baiwar Allah kimin rai wlh bansan cewa keba mutum bace Dan Allah kiyi hkr, yana kaiwa karshe ya rushe da wani irin kuka, Wanda daka jishi xakasan na tsoro neh da firgici,

Hhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh amrah ta kyalkyale da dariya marar dadin ji, dariyar da ta kara firgita Najeeb,

Sannan tace "kayi kuskure matuka tunda har kayi niyar rabani da budurcina, darajata, da kuma 'yancina, tunda nake a rayuwata ba' ataba yimin hakaba, kuma duk Wanda ya shiga gonata tohfa bana barinsa a doran kasa xan kashe shi, amma kai baxan kashe kaba sbd abu guda, shine JALALUDDEEN, kaci albarkacin sa, sbd kai kanen sane, wlh wlh wlh dabadan hakaba da saina kashe ka, kuma idan ka kuskura naji wannan xancen a bakin wani wlh xan manta da cewar kai jinin jalal neh na kashe ka,

Tana gama fadar haka hayakin dakin ya Washe ai da sauri Najeeb yabar dakin, yana xuwa room dinsa yasa key ya kulle kofarsa ya haye kan gado ya shige cikin blanket ya rufe kansa gaba daya jikinsa rawa yake.

Ita koh amrah kwanciya tayi akan gadonta daga kugunta xuwa sama ya rikide ya Ida xama na maciji, a haka tayi baccinta.

****************
Washe gari jalal kam yanata hada kayansa sbd xai tafi mascow gurin wani operation da xasuyi bama shi kadai xaijeba harda sadeeq da wasu doctors, gobe xasu tafi Abuja, saisu hau jirgin da xai kaisu mascow.

A bangaren amrah koh tana tashi daga bacci tayi wanka ta shirya cikin wata fitted gown ta material maroon wadda ta mugun yimata kyau ta kara fito da haskenta,

Fitowa tayi ta nufi part din jalal, a hanya ta hadu da Suhaima itama xataje gurinsa, taci adonta itama cikin wata riga ta yan kanti blue, wani irin banxan kallo Suhaima tayi mata, itakam batama bi ta kantaba,

Suhaima tariga amrah isa bakin kofar part dinsa tashiga yin knocking , itakam amrah tana isowa tabi ta gefenta ta bude kofar tana shiga ta banko kofar da karfi, da ace Suhaima bata matsaba da kofar ta daki fuskar ta, Suhaima kam ji tayi kamar ta buga ihu dan tsabar takaici,ace yarinya karama tana son taxamam mata jaraba juyawa tayi ta shiga motar ta tabar gidan.

AMRAH kam tana shiga direct ta haura sama inda dakinsa yake, tayi knocking, jalal kam da yake kan gado ya daura system dinsa akan cinyarsa yana wani aiki yaji ana knocking din kofarsa,

Dan kallon kofar yayi sannan yabada ixinin shigowa,

A hankali ta turo kofar bakinta dauke da sallama, amsawa yayi hade da kafeta da mayun idanunsa masu rikitarwa,

Karasowa tayi ta xauna bakin gadon ta gaisheshi, amsawa yayi still idanunsa yana kanta, dan kallonsa tayi da sauri ta sadda kanta kasa sbd ynx ba xata iya jure kallon sabah,

"kinyi kyau sosai" yace da ita, dagowa tayi tana murmushi tace "ngd" shiru suka yi for some minute sannan tace "yayana Dan Allah su nake mufita", xuwa ina? yace da ita, gurin shakatawa ta bashi amsa, OK jirani a falo ina xuwa, da sauri tace "toh" ta fita tana jin dadi, binta yayi da kallo, yana jin wani abu yana tsargar masa,

Shiryawa yayi cikin wata white gizna, yayi kyau matuka,

Falo ya nufa akan kujera ya same ta yace "mutafi koh", juyowa tayi ta kallesa tace "kai yayana kayi kyau sosai wlh kamar na saceka na tafi dakai" murmushi kawai yayi ya nufi kofa binsa tayi suka jera tanata yimai surutu,

Dan kallonta yayi sannan yace "haka xakije babu mayafi"

Hannunta ta dora kan goshinta tace "kash wlh ni nama manta ashe ban dauko mayafi bah"

Da sauri ta nufi part dinsu tana shiga ta dakko mayafinta ta fito, daidai lokacinneh mommy ta fito daga room dinta ta sakko kasa, kallon amrah tayi sannan tace "ke sai ina kuma"

Kallonta amrah tayi tace "fita xamuyi da yaya jalal"

Kan uba mommy ta fada "toh bbu inda xaki maxa woce ki gyaramin dakina"

Wani banxan kallo amrah tayi mata sannan tace "hmm bbu mahalu kinda ya isa ya hanani fita da yaya jalal Dan haka kinga tafiya ta" ta juya tana tafiya tana karkadawa mommy hips.

Tana Fitowa ta shiga gaban mota yaja sukabar gidan, direct gidan zoo ya nufa da ita,

Hmmmmm aiki jaaaa, toh kai jalal daka kaita gidan zoo toh idan taga yan uwanta macixai fah? Koh da yake babu ruwana Dan bani nace ka kaitaba eheee😏😏😏😏

πŸ’«Rabeauty πŸ’«
*please vote, comment, and share *
[8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: πŸ’«AMRAH MACIJIYA πŸπŸπŸπŸ’«

By Rabeauty πŸ₯°πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«

(10)
Suna isa yayi parking suka nufi bangaren da namun daji suke, aiko ta dakko wayarta tayi ta musu vedio da pics,

Shidai saidai ya kalleta yayi murmushi, wani bangaren taga ya nufa, tace "yayana ina xakaje?

Bangaren macixai, ya bata amsarda, gaban tane yayi wani irin mummunan faduwa, tace" yayana dama kana son macixai?

"eh amrah ina matukar kaunar macixai, amma banason suxo kusa dani, dan kallonsa tayi xuciyarta na kara harbawa, karasawa suka yi gurin macixan,

Wani maciji baki kirin yana ganin amrah ya fara xillo yanason ya fito daga cikin kejin, jalal kam yadan tsorata ganin yadda macijin yakeyi,

Itakam amrah koh a jikinta sbd tasan cewa kohya fito bbu abunda ya isa yayi mata,

Jalal kam da sauri yaja amrah sukabar gurin, yawo suka yi sosai a cikin gidan zoo din basu bar gidan zoo ba saida akayi la'asar,

Shoprite ya kaita ya siya mata chocolates da biscuits dasu cake da dai sauransu, basu dawo gidaba sai around 6,

Jalal kam yana komawa part dinsa ya Ida hahhada kayansa dan gobe jirgin 9 xasubi ya kaisu Abuja daga can suhau na mascow ya kaisu, kuma ya yanke shawarar gayawa amrah cewa yana sonta, Dukda yasan ta mai yarinya amma baxai iya cutar kansaba xai gaya mata yana sonta, idan ya dawo ya gayawa daddy ya samu matar da xai aura, dan daya aure Suhaima ya gwammace ya xauna bbu aure.


**************
Washe gari sadeeq ya kira jalal yace masa kawai su hadu a airport,

Shiryawa yayi cikin sut dinsa baki wa'enda suka kara fito da kyansa da kuma haskensa, part din mommy ya nufa ya gaya mata xai wuce, Allah ya tsare kawai tace, a ranta koh cewa take "Allah yasa jirgin ya fado duka kumutu"hmmm ni kuma nace" Amin walaka tare dake😏😏😑😑

Jalal kam harya fito xai wuce sai kuma ya juyo ya kalli kofar dakin amrah, a xuciyarsa yake cewa "dama ta fito na ganta kafin na tafi", saida yadan bata lokaci amma amrah bata fitoba,

Juyawa yayi ta tafi, har yakai bakin kofar fita daga main falo yaji ance "yayanah" da wata irin murya ta shagwaba,

Ai da sauri ya juyo, amrah ce ya gani sanye cikin riga da siket sunbi jikinta sun xauna das, ta yafa mayafi ja sbd atamfar akwai ja, karasuwa tayi kusa dashi, lumshe idanunsa yayi sbd wani daddadan kamshi daya daki hancinsa,

A shagwab'e tace "yayana ynx da ban fito bah tafiya xakayi bako sallama"

Da sauri ya sake rufe idansa sbd wani yarrr yarrr da yaji tundaga kansa har xuwa babbar yatsarsa ta kafa,

Ta sake cewa "yayana xan rakaka Airport din, ok muje, suka fito, driver yaja so xuwa airport, suna xuwa yaga harsu sadeeq sun iso shi kadai suke jira,

Bude motar yayi ya fito, itama amrah ta fito, driver ya dakko mai luggage dinsa suka nufi gurin su sadeeq,

Tun daga nesa sadeeq yake kallonta yana ganin kamannin mai gadinsu akan fuskar yarinyar,

Karasuwa suka yi amrah ta gaishesu, sadeeq yace "buddy ina kasamo wannan kyakkyawar?, bansaniba ya basa amsa karbar kayan hannun driver yayi yace" ka mayarda ita gida pls", toh mai gida,

Ya juyo ya kalli amrah yace "ranki ya dade mutafi koh", raurau tayi da ido tana son yin kuka,

Jalal neh ya kama hannunta suka Dan matsa daga gurin su sadeeq, yace "haba amrah menene haka so kike nima nayi kukan neh, nimafa ba'ason raina xanbarki a wannan gidanba, so pls take care of your self kinji, I love you, yabata peck a goshi ya juya ya tafi suka shiga cikin Airport din, yana shiga aka fara Kiran passengers suka shiga jirgin su ya daga xuwa mascow ✈️

Amrah kam tananan a inda yabarta saida driver yaxo yace sutabi sannan,

Suna isa gida, da gudu ta shiga part dinsu, mommy dake xaune a falo ce tace "subhanallah ke lfy xaki shigowa mutane cikin gida da gudu bako sallama, wannan ai iskanci neh" taja tsaki,

Amrah kam tana shiga ta haye kan gado taci gaba da kukanta, a xuciyarta Ko tana ta tunanin me kalmar take care of your self take nufi da kuma I love you,doleneh mah ta tambayi Suhaima, a haka bacci ya dauketa.

πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«
MASCOW
Sun isa lfy, har ankaisu masauki shida sadeeq, sauran doctors din kuma suka kama hotel,

Wanka yayi sannan ya kwanta bacci sadeeq kuma ya tafi siyo musu abinci.

πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«πŸ’«
A bangaren amrah koh, tana tashi daga bacci tayi sallar axahar ta fito falo taci abinci, sannan ta nufi dakin Suhaima,

Ita kuma ta fito daga wanka taji knocking, bata xata amrah bace ta bada ixinin shigowa,

A hankali ta turo kofar, kallonta Suhaima tayi ta wani hade fuska tace "uban me kikaxo yimin a daki", ayya aunty Suhaima Dan Allah abu naxo na tambayeki, tayi mgnr cikin sanyin murya, OK shigo tace da ita, karasuwa tayi ta xauna bakin gadon ita kuma ta nufi gaban mirror ta xauna hade da cewa "ina jinki", yawwa Dan Allah aunty Suhaima me kalmar "take care of your self" take nufi,

Ta cikin mirror Suhaima ta kalleta sannan tace "tana nufin ki kula da kanki" yawwa aunty da kuma "I love you", ai da sauri suhaima ta juyo ta kalleta sannan tace "waye yace miki hakan?

Saikin gayamin wnn tukunnah, OK OK xan gaya miki, kalmar I love you tana nufin" ina
[8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: πŸ’«AMRAH MACIJIYA πŸπŸπŸπŸ’«

By Rabeauty πŸ₯°πŸ’«πŸ’«πŸ’«

(12)
Mommy kam fara turara maganin tayi ta fito har main falo tanayi ta nufi bangaren masu aiki,

Amrah dake kusa da inna sunacin Dan wake taji warin wannan maganin nan da nan yanajin ta ya fara canxawa,

Inna dake kallon ta tace "fatima meya faru" bbu komai inna ta bata amsa,

A ranta koh cewa take "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un meyake shirin faruwa dani, wane shegen ne yakawo wannan maganin a cikin gidan nan, nashiga uku"

jin maganin yana nufu dakinda suke yasa ta saurin mikewa da niyar shigewa toilet, amma kamar a mafarki taji andagata sama an rafke kasa, ihu tasa nan take tafara nannadewa tana wani mukurkusu kamar yadda macixai keyi, amma still tananan a mutum inta, inna dataga haka ai da sauri tayo kanta, tana cewa "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un fatima meya sameki, fatima, fatima!!, amma ina amrah bataji da sauri inna tasa hannu ta dagota wani irin sulbi taji kamar ta rike fatar maciji da sauri taja da baya sbd ganin fatar amrah tafara sab'ulewa tana xama ta maciji, inna kam ta tsorata ainun amma bata nunaba,

Amrah koh taxama shirgegiyar macijiya 🐍, tayi kan inna, ina kam tariga data sadaqat amma jin shiru yasa ta bude idonta amrah tagani ta laulayeta tana fuskantarta, dakyar inna ta iya bude bakinta tace "fatima dama ke ba mutum bace, macijiya ce",

Eh inna ni macijiya ce kuma a gsky banso kisan hakaba nasan cewa mommy ce tayi wannan turaren, amma bansan dalilinta nayiba kuma babu abunda xan miki sbd na daukeki tamkar gwaggo tah amma inason dan Allah karki gayawa kowa koda jalal neh, amma fa Suhaima tasani da kuma najeeb,

Shikenan fatima bbu Wanda xai sani inshaa Allah, nan tasaketa ta koma ta nannade da sauri inna tatashi taje tasawa kofar dakinta key,

Sannan tadawo ta xauna tana fuskantar macijiya, tace fatima koh xaki gayamin taya kika xama macijiya,

Nan amrah ta shiga bawa inna labarinta daga farko har inda jalal ya kadeta, hawaye inna tashare tace Allah ya isar muku akan BAHUUL, shi kuma magaji Allah ya bayyanashi,

Amin amrah tace, nan amrah ta kwana sbd tayi tayi ta koma mutum amma abun yaci tura sbd turaren da mommy tayi har ynx bewashe bah,

*mascow*

Alhamdulillah su jalal sunyi nasara a tiyatar da suka yi ba'a samu matsa koh dayaba, kuma gobe inshaa Allah xasu dawo Nigeria,

Bayan sun koma masaukinsu ya kira amrah, amma bata dagaba 3missed call yayi mata amma no answer,

*kano*
Amrah kam tana bangaren inna wayarta kuma tana dakinta shiyasa, kuma alhmdllh ta dawo daidai,

Fitowa tayi ta nufi bangaren su da Suhaima taci karo ai da gudu suhaima ta koma dakinta tasa key,

Abun mah dariya yabawa amrah, tana shiga daki ta nufi bathroom tayi wanka ta shirya cikin wani material pink ta nufi gurin wayarta tana dubawa taga yayanah 3 miss calls, ai da sauri takirasa back, yana dauka yace "ina kika aje wayarki nayi ta kira no answer," ummm ina wurin inna shiyasa kuma wayar nabarta a daki tana caji, OK dama kira nayi na sanar miki gobe inshaa Allah xan dawo,

Kai haba amma naji dadi wlh amrah ta fada, kuma idan na dawo makaranta xan saki, kinaso?

" eh wlh yayanah inaso", toh shikenan, nan dai sukaci gaba da firarsu.


*Washe gari*
Inna da amrah ne a kitchen suna yiwa jalal girki, mommy ce tashigo cikin kitchen din ta kallesu a wulakance sannan tace "me wannan kuke yi batare da ixini naba eh" inna ce tace au ai hajiya naxata kinsani sbd naga yau jalal xai dawo kuma fatima ce tace amasa girki, kuma ni wlh naxata ke kika gaya mata amasa girki",

Kutumar uba mommy ta fada wani irin kallo tayiwa amrah sannan tace "kee ubanwa yabaki ixinin yiwa jalal girki, keba kowaba keba matarsaba amma kina wani shisshige masa, au sorry na manta ashe karuwarsa ce,

Da sauri amrah ta dago tana duban mommy xuciyarta na tafasa, da sauri inna takire mata hannu gudun kar asirin amrah ya tonu,

Tsaki mommy taja tabar kitchen din, karasa girkin suka yi amrah tace "inna inason ki kulamin da abincin nan naje nayi wanka sbd ban yarda da mommy bah xata iya xuba wani abu daxai illata yayanah,

Toh shikenan jeki kiyi wanka yar albarka xan jire miki abincin, toh shikenan ta fita daga kitchen din ta nufi dakinta, tayi wanka ta feshe jikinta da body spray tasa wata duguwar riga A shape ta lace tayi mata kyau sosai tayi daurin ture kaga tsiya tashafa powder da lipstick ta kara feshe jikinta da perfumes masu sanyin dadi, ta dauki wayarta ta kira jalal,

Jalal da saukarsu ynx kenan yaga Kiran amrah murmushi yayi, yayi rejecting call din, amrah koh ganin yayi rejecting yasa ta tunanin koh har ynx yana cikin jirgi, sallar axahar tayi.

πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦

Bayan wasu mintuna amrah ta fito ta nufi kitchen ta fara dauko kayan abinci inna na tayata suka jera akan dining table,

Jalal neh tsaye bakin kofa yana kallon ta, kamshin turarensa taji ai da sauri ta juyo, da sauri ta nufusa da niyar hugging dinsa, ai da sauri ya jaye yana hade fuska, yace "waike bakisan kingirma bah", hannu tasa ta rufe fuskarta alamar taji kunya tace "ya hakuri yayanah", murmushi y
[8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: πŸ’«AMRAH MACIJIYA πŸπŸπŸπŸ’«

By Rabeauty πŸ₯°πŸ’«πŸ’«πŸ’«

(13)
Da sauri aka wuce da ita emergency doctors suka dukufa a kanta,

Wata nurse ce ta fito tace ana bukatar jini da sauri jalal yace a ibi nasa,

Lab suna nufa aka duba jininsa da nata yaxo daya, ibi tayi suka fito a tare ta nufi emergency din,

Jinin suka saka mata sannan suka dukufa akan aikin su dan ceto rayuwar amrah.

πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
A waje koh jalal neh ya kira sadeeq ya sanar dashi halinda ake ciki, hankali tashe sadeeq yace gashinan xaixo,
Aa buddy kabari sai gobe ynx fah karfe 1 na dare ka bari sai gobe, shikenan sadeeq ya fada sannan ya kashe wayarsa.

πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦

A bangaren amrah koh sun cire bullet din, amma bata farfadoba sunyi mata allurai sun bata taimako na gaggawa ynx kuma sai ta Allah.

Fitowa doctors din suka yi da ita aka canxa mata daki ai da sauri jalal da inna suka Mike tsaye jalal yace "Doctor how's she?

Kallonsa doctor imran yayi yace am sorry doctor jalal mudai munyi iya bakin kokarin mu amma still bata numfashi ynx kuma saita Allah,

Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un innalillahi wa'inna ilaihirraji'un innalillahi wa'inna ilaihirraji'un kawai yake maimaitawa, inna kam xubewa tayi akasa tasa kuka, dakyar yace "xan iya ganin ta?

Eh toh a gsky bekamata a ganta ynx ba but since u are a doctor u can see her amma karkayi hayaniya da yawa sbd condition dinta, OK kawai jalal yace ya nufi room dinda take,

A hankali ya shiga ya nufi gurin gadonta kallon ta yayi sai kawai yafara hawaye a ransa yace "da ynx nine akan gadon nan ashe xata iya sadaukarda ranta a kaina, hannunta ya kama afili yace *amrah* but shiru ya sake cewa *amrah* still shiru yace pls amrah ki tashi karki tafi ki barni wlh idan kika mutu nima mutuwa xanyi a karon farko na rasa soyayyar mahaifiya banason akaro na biyu narasa soyayyar ki pls ki rayu koh Dan sbd ni Dan Allah, ya fashe da wani

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment