Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wadda takeson ta rungume ta da hannu bibbiyu, domin ta Yarda Auren ta da khaleel shine mukaddarin rayuwar ta, *AUREN GADO* ne wadda zai juye ya zama hasken rayuwar ta, farin cikin ta, domin da mommy tace ya saketa sai da ta jita kamar numfashin ta zai tsaya, wane irin saurin shakuwa tayi dashi ba tare da ta shirya ba, tanaji kamar sun dade dashi fiye da Ahmed sometimes tana mantawa da wani Ahmed ma,

Sallama yayi ciki ciki ya tsaya tareda yin Ajiyar zuciya ganin ta tana sha'anin gaban ta bata kuka, dago kanta tayi ta amsa tare da cewa "Mommy ta tafini ne? " yes. Yafada yana matsowa ya zauna tareda fuskantar ta yace " my diamond, zan angwance fa, kinsan ni d'an gata ne Yaya na mata biyu yabarmin yace in more, ta farko na dauka a bude take amma itama dal take a Leda ga kuma Amarya wadda ranar da ta Kwana Washe gari yatafi ya bar ni da ita, my brother really loves me. wani irin kallo take yi mai Wanda bai gano fassarar shiba. Ki tayani murna idan na Kwana nan gobe zan canja sheka, wo ni d'an gatan Yaya na. Yafada yana kwanciya agadon tareda mirginawa kusa da ita. Saurin sauka tayi kasa, "me zakaci"? Saurin juyowa yayi ya zuba mata ido kamar ya mareta, he hate this character of her I don't care about him, that means shike haukar shi akanta a kullum, ke wai me kika mayarda ni ne idan Ina important magana ki rika kawo min shirme ko banda lokaci sai na cin Abinci? Am telling you Aure Mommy zatayi min yau ko gobe why can't you show your concern? Yanzu ta gano shi yanayi ne purposely saboda ya gani ko zata damu to bazata nuna mai ba ai da wayon ta. "Ikon Allah" me kake son inyi? Yanzu gashi ka fada Mommy take so kayi Auren kaima what is new? Na saba da hakan Wanda nayi Auren soyayya dashi ma an Auro mai ita hankalina bai tashi ba sai yanzu da kai kafadamin kana Aure na ne saboda cikon burin Yayan ka , Toh me zanyi dukkan mu zabin shine kuma umarnin Mommy zakabi don kasamu tsira don haka banda damuwa she is welcome.
Ta kureshi kamar ya dora hannu akai yakeji ya kurma ihu cikin sauri ya duro tareda fisgota rashin sanin madafa yasa ya cafke bakinta da ke fadamai Abun haushi yafara tsotsa cikin mugunta harda ciccizawa yakeyi idanun ta a waje ga zafi gashi takasa ture shi saida yayi son ranshi ya tureta tareda nuna ta da yatsa, " karki kuma furtamin kinyi Auren soyayya a rayuwar ki me kike nufi da nawa Auren, what is wrong with me? Niba namiji bane ko bankai ki soni kiyi kishi na ba? Look ni inada kishin Abinda yake nawa koda ace ke zabin Yaya na ce now you are under me, ikona ce ke you must love me, dole kiyi kishina dole. Yafada yana fita saboda takaici yarasa Ina zai saka ranshi kishin ta yayi yawa a zuciyar shi,koda yayan shi ne ta Aura Abun na tabashi kuma duk da yasan ita din tashi ce zuciyar shi taki convincing dinshi sai ranarda yaga tazamo shi yazamo ita, don haka he is ready to make her his completely.
Zama yayi tareda yin dariya, this guy is strange, kalli yanda yake reacting itafa ta ma gano shi yanzu kamar yanda yake fada akwai boyayyen Al'amari a kasan zuciyoyin su ita mace ce don haka bazata taba bada kai da sauri ba dole shine zai sauke wannan ego din ya fada mata zuciyar shi, tagano shi fiyeda yanda yake tunani, tana sane da kalaman fauziya akan yaki kusantar ta, ace mace wayayya like her yakasa kulata Amma ita daren farko yanuna mata shifa namiji ne kuma yanada lafiya, Wanda ita sheda ce domin idan ya rikice mata har tsoro takeji.
Part din Mommy ya nufa Wanda yayi dai dai da shigowar motar kawun su, yayi saurin boye fushin shi ya nufeshi, suka gaisa yace " muje cikin gidan Ina Hajiya"? Mommy na ciki Ya fada suna tafiya, tana zaune a falon tana kada kafa, suna sallama ta mike tareda cewa " gwara daka iso domin jini na nagab da hawa saboda bakin cikin khaleel. Kallon ta yayi kawai domin yasan korafinta baya karewa, mommy me nakuma yi kince in Amince da zancen Auren salifa koda bana ra'ayi na Amince now what? Oh fadamai kakeyi nice nasaka khaleel nagode kaji shiyasa nake kukan Rashin Ahmed. Tasa kuka, tareda zama, kawun nasu ma zama yayi ba tare da yace uffan ba, saida sukayi shiru yace " Toh nidai nasaba da mugayen kalaman ki balkisu ba tun yau ba idan na yanke hukunci akan yarana kice namiki shishigi kuma idan fitinar ki ta tashi sai kin nemo ni kuma kinsan bakina ba shiru zaiyi ba, don haka ni na isa nace khaleel bazai yi irin Auren da ki ka yi wa Ahmed ba, kina maganar nadama Hajiya balkisu har yanzu baki san Annabi ya faku ba, da zaki gano ita wadda kikeso din ranar da kika Aurota aranar ya Kwana asibiti, da Naziya ce da baki kauna da kince itace ta kashe miki yaro, Amma da yake bakya tsoron Allah kinyi mukus, yanzu ko mutuwar Ahmed bai isheki ishara ba, duk bakiga ya dace ki kyale komai ki barwa Allah ikon shi ba, naji kin kashe Auren da kika kulla ba tare da yaro ya Amince ba tun farko, wannan badamuwa ta bace yarage naki Allah ne ke nuna miki komai cikin sauki inda ke mai kwakwalwa ce Amma toshashshiyar madiga....... "Ya isheka Muhammadu", don bazan ce Alhajin ba, ko ince modu kamar yanda kowa ke kiranka tunda kaki Kama furfurar ka, kuma kuji nan, wallahi in har ban Aurawa khaleel salifa ba sai in ba na numfashi, kuma kai kaji idan baka Aureta ba banyafe maka ba duniya da lahira mu zuba ni da ku shege ka fasa. Ta mike fuuu ta shige dakinta tareda mugayen kud'uri, "kawu kaji me tace? Ya fada cikeda damuwa domin kalmar ta girgiza shi, naji khaleel kuma mahaifiyar kace bamuda yadda zamuyi da ita, sai Addu'a, yanzu dai ya za'ayi? Ko ka Amince ne a daura Auren? "Eh kawu ayi mata yadda takeso ai ba akaina zata zauna ba,
Yafada tareda ayyana wani kud'uri a zuciyar shi, Wanda shikadai yasan tsiyar da ya shuka, haka ya raka kawun shi tareda zancen zai samu iyayen yarinyar ai shi namiji ne zai iya rikesu duka don haka karya damu, koda kawu ya tafi bai iya komawa part din Naziya ba, dakin shi na nan ya shiga ya canja tareda barin gidan,
Direct gidan malam yaje.......... 🖊





*Matar Soja*










3⃣7⃣&3⃣8⃣



08032252760
08175479641 contact this numbers for more information



........... Sun dade suna tattaunawa da malam akan rayuwa Kafin ya koromai zancen Karin Auren da Momy keson yi mai, Sai da yayi shiru malam yace "yanzu meye matsalar ka? Baka da muhalli ne, ko baka iya daukar nauyin mata biyu ne? Kuma meye dalilin sakin ita dayar Matar taka ba akan ka'ida ba? Yanzu dai nasan ba mata hudu ba Kanada karfin da zaka ciyar da Unguwa guda ma, sannan lafiya kana da ita, sauran ka Adalci, karike Amanar su tsakanin ka da Allah kabi umarnin mahaifiyar ka kasamu tsira kamar d'an uwan ka. Haka suka dade sai karfe kusan biyar yabar unguwar, tun fitar shi take jin ba dadi domin ta saba dashi yanzu tafara sanin dadin Aure zaman ta da khaleel, shine ya nuna mata ita mace ce mai daraja da lafiya a tareda ita, domin duk lokacin da ya kusanto jikinta bata iya misalta dadin da takeji hade da nishad'i, kewar shi ta dameta sosai har waya ta dauka sau ba adadi' tana dubawa tareda tunanin kiran shi sai takasa, to me zatace mai inta Kira? Ganin zata damu da yawa yasa ta janyo wayarta ta fara karatun littafin ta, y'ay'an gata yasata cikin nishadi' sosai, saida taga yamma yayi ta mike ta shiga kitchen, ta shirya mai dinner lafiyayya irin wadda tasan yakeso, Kafin tayi wanka, duk Abinda takeyi a yanzu bin zuciyar ta ne domin tana samun farin ciki ba tare da tayi tsammanin samun shi ba a cikin wannan Rayuwar Auren.
Yana tafe a hanya yana duba waya, wato ba zata iya neman shi ba koda zai shekara baya gidan? Don haka saida yayi magrib ya shigo cikin part din, lokacin tayi wanka ta saka simple gown tana zaune tana lazimin ta, ya yi sallama ciki ciki, tareda wucewa gefen gadon ya zube rigin gine, nasihar malam ta ratsa shi Amma baya jin kudurin shi zai canja sai dai ya kiyaye fadawa halaka Wanda yasan duk ta inda zai bullo ma Al' amarin, saida ta kammala ta mike tareda juyowa tace sannu da zuwa. Bai amsa ba bai bude idanun shi ba, harta juya tafita, saida ta juya yabita da kallo tareda sauke Ajiyar zuciya, ya tashi zaune yana shakar kamshin da tabar mai,
Shigowa tayi dauke da tray, binta yayi da ido kur harta Ajiye akasan gadon kan small carpet, baice uffan ba, tace " ga Abinci. ba tare da ta kalle shiba, "come here". Yafada cikin bada umarni fuskar shi a hade, ta dago kai, kallon da yake aika mata kamar yana Amfani da igiya yana janyo ta ne, ba musu ta mike, remove that hijab. Ba musu ta cire tareda ninkewa ta juya ta Ajiye inda take Ajewa, duk yana binta da kallo wani irin nishadi yake jinshi a ciki a duk lokacin da suke tare, dawowa tayi zata koma kasa ya riko hannun ta tareda janyo ta ya dora kan kafar shi, " kina wahalar da ni da yawa fa" Ya fada yana mai dora hancin shi a wuyan ta, kamshin ta mugun rikita shi yakeyi,
Nafita baki damu ba, nadawo kin nuna baki yi kewa ta ba, bayan rabin zuciya ta na nan tunfita na, Ina tunanin ki nadawo ba hug ba welcome back kiss umm why kike horani? Never mind gobe zakiga Amarya ta am getting married again. Yafada tare da dago idanun shi ya na kallon kwayar na ta idon domin yaga reaction dinta, Wanda Sai da taji zuciyar ta tayi wani irin tsalle kamar zata fito, kalmar ta caketa fiye da tunani, kallon are you serious? take mai, Wanda ya ganota domin yana karantar kowane movement dinta saboda ya gano ainihin meke ranta, " am serious, am getting married, Salifa zan Aura gobe insha Allahu, ai badamuwa ko? Tunda kinga yanda Auren ki yazo ba shiri haka nata ma All this romance karki damu I can handle but for you. Wani irin zamewa tayi ta sauka kasa tareda fasa kuka mai karfi ba tare da ta shirya ba, jitakeyi idan batayi ba zuciyar ta zata fashe, zancen romance da wata, kwakwalwar ta bazata iya dauka ba,
Wani irin farin ciki yaji har kasan zuciyar shi, so he is right tafara jin shi a zuciya tunda har tafara bayyana kishin ta, Abun da yake kaunar gani a wurin ta, she dai yana so yaga kishinta akan shi wannan reaction din nata kawai yasa ya ji shi yana yawo a sararin samaniya saboda farin ciki, tuni zuciyar shi ta wanke fes ya sakko kasa kusa da ita zuciyar shi kamar Auduga fuskar shi kamar wata daren goma shabiyu,
Jikin ta ya shige tareda rungume ta gam a kirjin shi, yace you have the right baby cry for me, I want it, I love that, I need your jealousy, and only you have the right over Ibrahim, love me please love me. Dago fuskar ta yayi tareda dora bakinshi dai dai hawayen dake gangarowa yafara lashewa yana bata wani irin salo mai kashe jiki, tuni kukan ya dauke dif. Saida ya sude hawayen tas ya dora goshin shi saman fuskar ta, " tell me meye matsalar? " ba kya son inyi Auren ne? Daga kai tayi kai tsaye, " why baby" ? ni banaso. Tafada tana tura baki, "ba akanki zata zauna ba ai". You are going to touch her. Tafadi gaskiyar Abinda zai janyo mata ciwon zuciya, yanda yake romancing dinta ta ke jin dadi ba zata so ya yiwa wata ba. Wani irin mugun kishin shi taji tanaji fiyeda Wanda taji lokacin Auren Ahmed.

"To ai kishiyar kice Already nagani ba Fauziya bace". Ture shi tayi ta mike kaje kayi ni ban hanaka ba ka Auro goma ma ba ruwana. Dariya yayi mai d'an sauti ta farin ciki, ya matso tareda fisgota ya rungume west dinta ya dora kanshi a kafadar ta, Hhhh admit it my diamond, kina kishina, kokarin ban bare hannun shi takeyi takasa, " wait let have a deal with you", Amarya ta is coming today or tomorrow, yanzu nayi Alkawarin if you give me chance, nasameki I will not touch her I promise you, yanzu Ina jiranki daga yau zuwa gobe bazan zo kusa dake ba if you are ready meet me Ina gefen mommy, and make sure you dress sexy. Ya dago tareda kashe mata ido ya bar part din, saida ya dauki duk Abinda yake so yafita ta bishi da kallo, zubewa tayi kan gadon tareda dafe kirjin ta,
Dole ta Amince wa zuciyar ta akwai soyayyar khaleel mai karfi data shigeta farat daya ba tare da ta shirya ba, son shi ya damki zuciyar ta gangar jikinta tana jin kishin shi fiyeda tunani, domin karatun da takeyi yasa ta gama gano cewa shima akwai sonta a zuciyar shi, yes bazata so ya kusanci wata ba Amma kuma tasan hukuncin ubangiji zai iya hawa kanshi, tana da ilimi tasan komai bazataso kanta dayawa ba Amma zatayi Abinda ya dace, zata bashi mamaki she is ready ta mallaki mijinta ta hanyar da takeso don haka zata dage ta cire kunya tabashi kulawar da ta dace, meye kunya a cikin Aure, bayan cikon addini ne sunnah ce ta manzon mu ( s.a.w )mai k'arfi, Ina koyarwar da yan uwa da kuma iyayen ta su kayi mata? Da kanta tabawa kanta shawara, don haka she is ready now. Aunty Raliya takira tareda tanbayar ta yanda zatayi da wasu magunguna da tabata. Dariya da farin ciki Aunty tayi tace " Naziya mafarki na zai zamo gaskiya, domin na hango ki cikin farin ciki a gidan khaleel, na hango miki rayuwa mai cikeda nasara da kuma Albarka, kin gani ko haka Allah ya tsara, naji zancen Auren shi wurin zarah, don haka ki dage ki rike y'an cinki da martabarki, kinga kece ta biyu.. " ai ita tafita dayar Aunty. Tafada kai tsaye. Toh Allah ya kyauta gaba nasan ayi haka, kuma ko yanzu kirike Allah ki rike Azkar ki kula da kanki gyara shine mace idan kikace bazaki gyara ba zaki zama bola a gidan mijin ki. Ta bata shawari masu Amfani da suka Kara mata kaimi da daura damara.

A ranar bata kuma ganin shiba har Washe gari, ko wayar shi bai kirata ba, tasan he is serious kuma zata nuna mai ita din mace ce mai dauke da nata irin Salon, Kwana tayi a internet tana koyan salo Kala Kala Wanda tayi Amfani da nata, da safe tana tashi ta tura mai text, "good morning husband, how was your night? Ta tura hade da Alamar hasken rana da kuma hoton teddy bear mai dauke da hoton zuciya.
A zaune ya Kwana a part din mommy yana aiki a computer tareda yin booking flight to bangkok shirin shi yakeyi sosai domin yanada tafiya agaban shi da ya kirkiro wadda zata zama da manufa biyu, yanayi Amma rabin zuciyar shi na wurin ta, yana a takure ne sosai Amma dole ya daure yayi wannan aikin in yana tare da ita ba uwar da zai tsinana sai lalubeta karshen ta yayi aika aika batareda ya shirya ba, don haka har Asuba idon shi biyu haka yake famar aikin shi, saida yayi sallah yaci gaba,
Sakon ta da yashigo ne yasa ya dauki wayar tashi duk da baisa rai daga ita bane, ware idanun shi yayi, yayi saurin budewa. Farin ciki ko ihu zaiyi saboda murna, sakon nata means a lot to him, ya karanta yafi sau Ashirin harda ture laptop dinshi yayi gefe ya kwanta yana runtse idanun shi, tareda dora wayar a kirjin shi. Saida ya dauki lokaci kafin ya daga ya fara mata reply, " Hmmm morning wife, are you missing your husband touch?
Tana zaune tana jiran sakon shi ta kagu, taji shigowar text harda tashi zaune tayi ta bude, ba amsar da take so taji ba kenan taso taji yace mata yakasa bacci like her amma let go, ta mayar, " I can't help it".
Wani irin buga kafa yayi, duk kalmar da tafito tanada muhimmanci a zuciyar shi,
"Me too I couldn't sleep all night long.
Mayar mai tayi, " then come back.
"Really? "Yes. Saurin kiran ta yayi, tayi dariya tareda picking, Ajiyar zuciya ya sauke yace " are you serious baby?
" uhm. " you know what am going to do if I come. "Is your right". Tafada kai tsaye. "Really baby"? Yafada with so much excitement, Zaki sani in karya duk wani plan dina baby, ko yanzu tun text dinki na farko look at me, bafa ganin ki nayi ba am hard like rock, you are the only woman who can move the man in me, duk lokacin da na kusanto ki zanji inada cikakkiyar lafiya, do you feel the same baby? " um um please stop it ina jin kunya zankashe. Tafada tana rufe fuskar ta kamar yana ganin ta, shy baby look ba kunya a rayuwar Aure kinga am frank so nake ki zama kamar ni idan bukata na kikeyi koda Ina office just give me a call and tell me, husband please come back it scratching me. Wani irin dariya yabata harta kyalkyace tareda rufe baki, he is funny wallahi, wani irin farin ciki ne ke bin zuciyar shi jin dariyar ta akaron farko, Alhamdulillah Yafada, "my diamond" tayi shiru domin sunan yana yimata dadi is she really a diamond? , yace " stay happy always, yaja numfashi yana mika, " please come to mommy side kinji am so so so honey bazan iya fitowa a hakaba ta cika wandon you can come.
"Da safen nan Mommy na nan inajin tsoro." dodo ce ita kizo please kiga Abinda kikayi coursing Yafada yana mika tareda dafe jikinshi gam yana runtse idanun shi saboda zafi domin na yau daban ne.
Kashe wayar tayi ta nata saka da warwara, saida ta dauki lokaci ta mike, tafada wanka ta mulke in and out na jikinta da kamshi, ta samu wata Oman gowan mai shegen kyau da tsada kamar weeding gowan ta zura light brown taji adon dutsina kamar wata princess, Naziya akwai sirrin kyau da iya ado kuma duk shigar da tayi saita fito tayi kyau.
Kitchen dinta ta shiga ta samu madara mai dumi tasha domin batajin yunwa,
Batasan me yasa zuciyar ta ke ingizata zuwa gareshi ba, don't blame her, domin khaleel ba irin mazan da zuciya ke iya jawa aji bace duk ego din Naziya ya hambarar cikin sauki, Wanda shi a gefen shi yasan ba zata zoba don haka juyi yayita yi kafin ya zabura ya iya watsa ruwa ya dawo dai dai, mommy ce cike da farin ciki ta turo kofar dakin nashi lokacin ya shirya cikin wata dakakkiyar shadda green tana maiko sumar shi yake tajewa, fuskar ta a Washe tace d'an Albarka bazaka fadamin a nan ka Kwana ba? Aida tuntuni an kawo maka breakfast, yanzu zoka ci kaji. Tafada tana ajiyewa a kan gadon, " good morning mommy. Yafada yana zama gefen ta, ya riko hannun ta, he love her but he hate her ways of thinking, takasa gano illar Auren da zatayi mai, saida yaci yagama tanata tsaro mai zancen Auren tareda cewa "nasan zaka dawo hanya ai don kaima kasan baka kyautawa rayuwar kaba khaleel duk fadin kano an san da arzikin ubanku tun yana raye bare yanzu da kuka Kara bunkasa kuka ginu ace baka Auren Y'ar da duk kano zata dauka asan yes kayi aure nima infita anuna ni ace ga surukar wane kuma uwar wane y'ay'an ka su fita a nuna su ace jikokin wani ne a garin kano ai shine farin ciki. Saida ta gama yasa tissue ya goge bakin shi ya juya dakyau ya kalleta ya riko hannun ta, " Mommy na meye laifin Naziya? Tana da mugun haline? Gidan su ba tarbiya ne? "Talauci ne banaso kasani bankaunar hada iri da talaka shiyasa nafada maka karka sake ka hadomin jini da talauci. " Hmmm mommy meye ribar Auren fauziya danayi? Meyasa kike so ki hadani da salifa? Mommy I don't want to argue with you, banaso kice na bijire miki amma ni har a abroad nasha ganin ta tana yawon banzan ta,.... "Dakata, sunada kudi Ina kakeso ka gansu a Zaure da Almajirai ko suna kulle a gida bayan sunada Abinda zasu huta? " mommy understand yarinyar nan gwara fauziya da ita you... "Quit Ibrahim Aure dai yau sai andaura kuma yau zata tare yau nake so ka shiga dakinta domin jikoki nake so daga tsatso mai daraja ba gidan malamai ba.
Mikewa yayi OK sai tazo tayi gadi tareda zaman jiran agama budar kai, ai al Ada ce mai muhimmanci dataja har yayana yabar duniya baisan dadin Aure ba. Ya dauki key ya fita abin shi, yabarta sake da baki, khaleel baya wani ganin girmanta take gani baisan mutuncin taba kamar Ahmed, "Allah ya jikanka yaron Albarka". Tafada tana share hawayen kewar Ahmed tafita da kayan Abincin da yaci.

Yana fitowa tana fitowa cikin adon ta mai daukar hankali, tayi matukar tafiya da hankalin shi, saidai ganin mai gadi da masu aiki dake kai kawo yasa yaji wani irin mugun kishin ta tuni ya hade rai yayi saurin cewa " go back, cikin kausa shashshiyar murya, mai cikeda umarni da tsantsar kishi, yayi saurin rufa mata baya, domin bata tsaya wata wata ba ta juyan saboda yanda fuskar shi ta juye kamar bashi bane dazu yake kwantar da murya a waya, a tsaye ya ganta ya doge daga nesa, ban lamunci ganin adon ki awaje da rana ba bayan kinsan akwai gardawan banza a ko Ina, wallahi zakija musu asara idan kika kuma fita batareda hijabi ba, ke ki nemo nikab kirika sawa if necessary sai kinfita da rana. Ya juya ranshi a bace, by the way, Ina ma zataje? Ya manta y'an da sukayi da ita a waya saboda kishi,
Yana tuki yana dukan sitiyarin motar shi, saida ya koma gefe ya faka motar ma ya kife kanshi, bai taba tunanin yanada zafin kishiba sai akanta, zuciyar shi har wani tsalle takeyi, kuma gashi dole ya fito da ita ayi mata passport, domin shi kadai yasan shirin shi, dukan iska yayi, Allah yagani bazai kawowa wani katon banza Matar shi ta tsaya yana kallon ta cikin camera ba zai iya shake shi, wayar shi ya ciro tareda kiran manager dinsu yace yaza'ayi asamu mace photographer tazo tayiwa madam a gida? Yace za'asamo mai yau, yayi Ajiyar zuciya tareda kiran ta, kamar jira takeyi dama tunfitar shi take dariya kishin shi ma dariya yabata domin tana tunanin bayau suka saba ganin taba a gidan, wani irin farin ciki takeji a zuciyar ta now she relax domin inda kishi da so, don haka tanaji a jikinta yana sonta domin Abinda yakeyi da ita yafi karfin wasiyyar d'an uwan shi, tanata tunanin moment dinsu dashi taji karar

1 Comments On AUREN GADO
avatar
abdulkarim

1 year ago

Reply

Masha allah novel yayi dadi

Please Login or Register in order to submit comment