Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sund'anyi gudu, kasancewar harabar gidan akwai mutane motocin suka tsaya ak'ofar gida, ta amaryace kawai tashiga cikin gida.
Anty Mamie dakanta tazo tafiddo Aysha, Wanda ganin Anty Mamie yasakata kuma rushewa da kuka, lalashinta tashigayi.
Anma bak'i tarbar mutunci, amma hajia babba da Anty zuwairah ko lek'owa basuyiba, Anty shikurah komai itakam tana aciki, ankai amarya Aysha d'akin Anty Mamie, kafin da daddare amaidata 6angarenta.
Daga ita sai ifteehal a d'akin, saikuma wasu y'an uwansu su uku, zee da Saleema da Mimi. Hirarsu sukeyi cikin nutsuwa, amma Aysha batacewa uffan, tana kwance kangado tana saurarensu dabinsu da ido.
Amal takawo musu abinci.
Sukad'ai sukaci, amma Aysha ko saukama tak'iyi daga gadon Anty Mamie.

Gayyar ciki da gaskiya fans kuwa aii dole aka bud'e musu d'aki guda agidan, dukda hakama yamusu kad'an, sundaiyi manege ne kawai, Dan kowa yasan hidimar biki yanda take, Baka Neman komai kasamu yanda kakeso.

Haka akaciga da y'an hidimomi har zuwa 8 Na dare.
Kowa yafara shirin dinner da abokan ango suka shirya, wadda shima baisan da itaba saida suka dawo daga Kano, babu yanda zaiyi tunda sunriga sungama komai, amma baiso hakanba gsky.


_________________
Amarya Aysha ansha kwalliya, Hamdiyya tamata danta iya sosai, tasaka popul d'in doguwar riga, aka nad'a mata farin ashoke, tayi k'yau harta gaji, kowa fad'i yakeyi masha ALLAH, itakam gabanta sai fad'uwa yakeyi, tana tunani had'uwarta da ya khaleel, tunda tasan dolene amota d'aya zasu tafi.
Isowar Anty shikurah ce ta katse tunaninta, ''Aysha tashi muje Yaya Na jiranki".
Cikin marairaicewar murya Aysha tace, "wlhy Anty Ama kamarma afasa".
Dariya Anty Ama tayi, " kiyi hak'uri kinji Aysha, shima ya khaleel d'in bada son ransa baneba, abokansa Na wajen aikine suka shirya batareda saninsaba, kinga kuma babu damar yace bazakujeba yasakasu asara". Kinga tashi muje karsuyita jira.
Dole Aysha tamik'e, Anty Ama tarik'e hannunta, saima yanzu talura duk mutane sungama tafiya, gidan yayi shiru, Dan harsu hajia babba duk anacan😂.

Anty Ama tabud'ema Aysha motar dake gabansu, zuciyar Aysha sai harbawa takeyi, ahaka tarumtse idanu tashiga tana karanta addu'a aranta.
Kamshin turarensane yadaki hancinta, ta sauke numfashi da k'yar tareda had'iyar yawu.
Lafewa tayi ajikin murfin motar bayan Anty Ama tarufesu.
Ema...dake gaba zaya tuk'asu yace, "antynmu barka da dare".
Yanda hausar tasa take gura-gura yaso bama Aysha dariya, amma saita dake tad'an murmusa tareda amsawa, takula ya khaleel ya yarda ta tuk'in EMA gaskiya, indai bashi zai tuk'a kansaba to zakaga Emanuel ne driver d'insa.
Ta gefen ido tasaci kallon boss d'in, Wanda yayi tsit tamkar babushi a motar ma, sanye yake da popul d'in shadda irin ruwan kayan jikinta, d'inkin babbar Riga, sai farar hula akansa, yanata zabga k'amshi. Muryarta can k'asan mak'oshi tace, "ina yini?".
Idanunsa dake a lumshe yabud'e ahankali, ya saukesu akanta, kwalliyar Tamata k'yau yafad'a aransa.
Jin bai amsa mataba yasaka Aysha d'ago idanunta masu yalwar gashi ta sauke akansa, azatonta baijitabama.
Da sauri ta janye idanunta saboda kallon ido cikin ido dasukaima juna, wani kwarjini Na musamman yak'ara mata, kanta tamaida taduk'ar tana kallon zanen material d'in jikinta.
Babu wanda yasake cewa komai har suka Isa wajen dinner d'in.
Abokan ango suka fito domin yimusu rakkiya, sunfara tafiya Taheer ya gwargwad'a masa wani Abu a kunne.
Saida ya hararesa sannan.
Taheer yamatsa baya yana dariya.
Batareda Aysha tayi zatoba taji yarik'o hannunta ya rumtse anashi, atare sukaji shock, ya khaleel ya sauke sassanyar ajiyar zuciya, yayinda Aysha taji wata kasala tadaban, wadda ta k'ara haddasama tafiyarta sanyi ainun.
Wajen atsare kuma cikeda jama'a, suna shigowa aka saki tafi, su Ammah ana gaba-gaba itada inna da baba jummai Maman hajia babba, Ammah sai baza hakwara takeyi Dan dad'i😁.
Saida Aysha ta zauna sannan shima yazauna kusada ita, Dan kujera d'aya aka ajiye musu, amma basu matsuba saboda tanada d'an fad'i.
Anfara gudanar da abinda yatara mutane batareda bata lokaciba, ayshadai tayi tsit tamkar ruwa ya cinyeta, tamkar ance tad'ago idonta yasauka akan Anty kubrah da glory, bak'aramin tashin hankali Aysha tashigaba, takai dubanta kan Anty meerah wadda tahango itama hankalin nata atashe yake.
Innalillahi kawai Aysha take ambata azuciyarta, tsabar rikicewar datayi batasan ta d'ora hannunta kanna ya khaleel ba, jin tana Neman jimasa ciwo a bayan hannu yasashi juya hannunta yasak'ala nasa aciki, yatsunsu suka sark'e cikin najuna, tamatse kammm kuwa batareda tasan mitake aikatawaba, kallonsa yamaida direction d'in datake kallo saiyaga momynsace awajen da wasu mata biyu da kubra, yamaido kallonsa ga Aysha da idanunta ke zubar da siraran hawaye.
Matso da bakinsa yayi saitin kunnanta, batareda tayi zaton maganar tashiba taji saukarta cikin kunnenta.
Bashiri tadawo cikin hankalinta, tafara k'ok'arin zame hannunta, bai hanataba yasaki hannun nata, tareda mik'a mata hanky d'insa alamar tagoge hawayenta.
K'ar6a tayi, tanamai satar kallonsa, Yakuma maimaita tambayar tasa.
Suwanene su?.
Gaban Aysha Yakuma tsananta bugawa, muryarta Na rawa tace, "suwaye?".
Kafeta yayi da idanunsa, tayi saurin janye nata.
Yace, " ya ina tambayarki? Kuma kina tanbayata?, banason shirme suwanene sud'in?, miyasaki kuka akansu kuma?.
"Basu nakema kukakaba, nibanma sansuba, natuna Abbah ne kawai".
Bai gamsu da zancentaba, amma ya shareta baisake cewa komaiba.
Haka biki yacigaba da gudana, duk motsin Anty Kubrah da Anty glory akan idon ya khaleel da Aysha yake faruwa, kowa kuma da abinda yake kitsama zuciyarsa akansu.
Meerah kam tuni tabar wajen dinner d'in, saboda bata buk'atar su Anty glo su ganta.
Aysha da ya khaleel suka mik'e a k'ark'ashin jagorancin mc sukabi dukkan manyan iyayennan suna godiya agaresu, (Dan kowa zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zai kama gabansa).
Lokacin dasuka Isa wajensu Ammah sai Ammah tajawo Aysha ta d'ora akan cinyarta, tana kukan farincikin ganin wannan rana ta auren a khaleel.
Shikam yazauna kusada ita yana share mata hawayen da hannunsa yana murmushi, nanfa camera tafara aikinta, masu d'auka a waya nayi masu camera d'in da aka d'akko nayi.
Konifa abin ya birgeni.
Momy kam dasukaje gabanta saita dafa kan ya khaleel kawai, taki kallon ko Aysha.
Ganin haka ya khaleel yakamo hannunta itada Ayshar yahad'e waje d'aya yarumtse, cikin sanyin murya yace, "ga momyna farincikina, ga matana amanata, namik'a muku amanar kaina, banida abokai mafi kusanci dani samadaku Momy & Aee'sha!".
Hakan ya Sosa ran Momy, wai miyasa zai had'a matsayinta dana Aysha?, tazare hannunta batareda ta tankaba.
Aysha kam taji dad'i harcikin ranta, sai damuwarta tad'an ragu, ganin kodai Yaya, ya khaleel d'in yadamu da ita.
Idanun Anty glo nakan Aysha, sotake tatuna Inda tasan mai irin yanayinnan amma takasa tunawa.
Kubrah kam wani d'acine aranta da kishi, tadad'e tana nunama ya khaleel d'in k'auna amma yana shareta, sai yanzu Dan abin kunya zai kwaso y'ar cikinsa amatsayin matarsa, ita kanta hasashen inda tasan matar tasa takeyi amma takasa tunanowa.
Dasukaje wajen Anty Mamie kam tamkar ta cinyesu, itama rungume ayshar tayi tana kukan dabatasan dalilinsaba, tashafa kan ya khaleel tana saka musu albarka, da fatan nasara a Auren nasu.
Komai ya gudana cikin nutsuwa da tsafta, zuwa 10:30mp aka tashi.
Yanzukam Aysha batareda ya khaleel suka tafiba, mota d'aya suka tafi da Ammah.
Shikuma yatsaya sallama da abokan arzik'i wad'anda zasuyi asibancin tafiya gida.

Koda suka dawo gidan babu 6ata lokaci aka shirya Aysha akamata rakkiya 6angarenta.
Tana kuka darok'on ifteehal takwana dan ALLAH nan suka barota suna dariyar shak'iyanci.😂
Bayan tafiyarsu saita kifa kanta akan filo tana kuka mai tsuma zuciya da tausayin kanta, kowane irin zama kuma zasuyi da mijin nata? Ya rayuwa zata kasance da surukarta? Makiyarta, wadda taso ruguza rayuwarta tun tana y'ar k'arama, ga k'annen miji da yayyensa marasa mutunci

Acan kuma hankalin hajia babba tashe, Dan Anty glo da kubrah sungano ayshace amaryar bayan dogon nazari, dasake ganinta dasukayi lokacin da'aka dawo dinner ta wanke kwalliyar fuskarta, aka rakota wajen hajia babba amatsayin surukarta.
Hankalin hajia babba amatuk'ar tashe yake, su Kansu su Anty glo hankalinsu atashe yake, haryanzu suna zaton Aysha da meerah suna cikin islands UK Ashe bahaka baneba, ya akayi suka dawo gida Nigeria? Lallai kam lik'o Na Neman 6alle musu kuwa.
Hajia babba sai safa da marwa takeyi, gawata uwar zufa dake keto mata, shin ya'akayima takasa gane Aysha?, bazai yiwu d'anta yazauna da KARUWA ba.



Aysha ba karuwa baceba☹😏.


Ya khaleel dabaisan hidimar da akeyiba yashigo gidan kusan 12pm, tawaccan k'ofar yabi 6angarensu kenan, gaba d'aya jikinsa a sanyaye yake, waishine da mata yau, yanzu bashida hujjar k'in zuwa gareta sai ALLAH ya rubuta masa zunubi, tundaga lokacin da'aka d'aura auren dukkan hak'k'inta yadawo kansa, guda d'aya yatake sai ALLAH ya kamashi da laifi.
Shikad'ai ya iso gidan, babu rakkiyar kowanne aboki.
Da addu'a yatura k'ofar falon yashiga.............✍🏿




Yasin yatsuna zafi, zand'an huta gaskiya😿🤕🤧.







😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😘😘😘😘😘😘😘
*_Typing📲_*



🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_


*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🤲🏻😭



*_part 2_*
(littafi na biyu📕)


1⃣1⃣

A tsakkiyar falon yatsaya, yanamai binsa da kallo daki-daki, komai ya birgesa da k'ayatar dashi, gawani sassanyan k'amshi Na tashi, Wanda akasan duk gidan amarya dashi, yadire ledojin hannunsa Wanda shima baisan miye acikinsuba, Dan youseef ne yabashi.
Rasa d'akin dazai dosa yayi, baisan ainahin d'akin da matar tasa takeba, yay shiru yana nazarin d'akuna ukku dake cikin corridor d'in, zuciyarsace tafi karkata dana k'arshe, cigaba yayi datakawa ahankali, kaikace yana tsoron Isa ga d'akinne. Harya k'arasa jikin k'ofar.
Zuciyarsa tashiga harbawa da sauri-da sauri, shikam ba jarumi baneba awannan ga6ar, zai iya rantsuwa baita6a kasancewa dawata mace daba muharramar saba Na tsawon minti talatin, dagashi sai ita, saidai abokan aiki, suma basukad'aiba gaskiya, dolene kasamu akwai wani taredasu.
Cikin rinmtse ido yamurd'a handle d'in k'ofar yashiga, bashida za6in daya wuce hakan, musamman idan yatuna da lectures d'in malamai data gudana a wajen waleemar auren nasa.
Sallama yayi amma babu amsa.

Jikin Aysha ne yafara rawa, danjin muryar Wanda batayi zaton ganiba a wannan lokacin, takuma cusa kanta acikin filillukan da aka k'awata kwalliyar gadon dasu, gaba d'aya jitai yau soyayyar datake masa tagudu, sai d'unbin tsoro da firgici dasuka maye gurbinsa.
Cikin takun nutsuwarsa da jarumtar data zame masa halittar jininsa yak'araso gaban gadon. suduka zuciyoyinsune suka k'ara karfin gudun harbawa, saboda kusanci dasuka samu dajuna.
Ya d'an lumshe idanunsa, tareda kauda kai daga kallonta, yama rasa ta'ina zai fara?.
Jinsa tsaye akanta yakuma karyar da jarumtarsa, rauni da d'unbin fargabane kawai keta gudu da bugawar zuciyarta, tsoronta yakuma hauhawar farashi lokacin dataji ya khaleel yazauna abakin gadon, kusa gab da k'afafunta, da'ace zata motsama dolene koyaya ta ta6ashi.
Wata jarumtace tazo masa alokacin daya tuna da wadda yake tare. Cikin muryarnan tasa, maikad'a hanjin marajjin magana yace, "k! tashi mana".
Shiru Aysha batako motsaba.
Yakuma fad'in "bak'ya jinane!!".
Yanda yay maganar ad'an tsawace, amma cikin sanyin murya yasa Ayshan tashi zaune, idanunta nacigaba da zubar da hawaye, tagefen ido tasaci kallonsa, tsoro yasake kamata saboda cin karo da fuskarsa a d'inke, kamar yanda tasanta.
Shima satar kallon nata yakeyi, yabi zara-zaran yatsun hannunta da kallo, lallen yamata k'yau sosai, daga bak'in har jan, yanda take hawaye saita bashi dariya, yau kam babu bakin rashin kunya, tausayinta yad'anji aransa, dan masu iya magana kance *aure yak'in mata*, amma yasan halin kayarsa, zumace saida wuta.
Mik'ewa yayi tsaye yana fad'in tashi muje.
Saida yakai bakin k'ofar sannan Aysha tamik'e da k'yar, bata sameshi a falonba, saikawai tasamu kujera ta zauna, jitake gabad'aya auren yafita aranta.
Fitowarsace takatse mata tunaninta, saiyanzu tama kwalliyar tasa kallon tsaf, kayan d'azunne ajikinsa, amma yanzu yaje yacire babbar rigar, sai wando da riga y'ar ciki wadda dakad'an tawuce d'uwawunsa, yakuma cire hularma, sai kwantaccen gashinsa, Wanda baicika yawaba saboda askewa dayakeyi, hakama sajensa kwance yake luf, da'alama yad'an kwana biyu bai aske sajen nashiba, yasha gyaran fuska, wadda tafito da ainahin chocolate color d'insa, ya khaleel k'yak'yk'yawane, amma bazaka cedashi k'yawu ajin k'arsheba, komai nasa yana tsaka tsaki, idonsanefa dai ALLAH yabashi masha ALLAH, Dan manyane tubarkallah, ko mace sai haka wajen k'yawun idanu da girma, gasu farare tas, idan ransa ya6acine kawai zakaga sunyi jaa da k'ara fitowa, yanada k'yawun mai k'ayatarwa, Wanda zamu iya cewa kwarjininsane ya kuma fiddo taswurar k'yawun haibar tasa.
Batasan yak'araso falonba, saimaganarsa taji yana fad'in "k tashi ki d'auka min filet da cup".
Jikin Aysha amace tamik'e, saidai batasan inane kichin d'inba, amma tayi tsaye takasa tanbamayarsa.
Tsaf yalura da nufinta, amma saiya shareta yad'auki remote yana k'ok'arin kunna TV.
‘‘ya khaleel inane kichin d'in?”.
Shiru yamata, saida yamula Dan kansa sannan yanuna mata da hannu.

Kichin d'in yayima Aysha k'yau sosai, komai atsare gwanin sha'awa, kala biyune kawai a kichin d'in, jaa dakuma Fari, kamar yanda falonta yake, ta d'auki filet da cup tad'ora bisa wani madaidaicin tire tafita.
Yana zaune inda tabarsa, gabansa taje ta ajiye, ya nuna mata ledojin batareda yayi maganaba.
Itama bata tankaba tasakko, harzata fara bud'e ledojin yasaka hannu yazare gyalen dake lulu6e da jikinta, saboda kid'ima saida Aysha tajuyo ta kallesa, harara ya sakar mata, tayi azamar janye idanunta da kwallah suka fara taruwa aciki.
Ta d'auka tabud'e, ledar farko kayan fruit ne aciki, d'ayar kuma gasassun kaji guda hud'u, saikuma d'ayar ledar fresh milk ne aciki.
Kaza d'aya tasaka a filet d'in tanata tashin k'amshi, tabud'e fresh milk tazuba a cup d'in.
Tad'ago ido ta kalleshi, ganin idonshi akanta, ta janye nata, tanaso tacemasa tazuba amma takasa magana.
“Shin waike kinzama kurmane yau?”.
Kanta ta girgiza masa. Yace, "dabakinki nakeson ki amsa mini, dama Ashe ked'in mara kunyar k'aryace?".
Itadai bata kulashiba tace, " nazuba maka".
“kin zuba mana dai, ko kina nufin wad'annan kwala-kwalan idanun naki ba yunwa baceba?”.
Shiru tayi bata tanka masaba, aranta tace, “dayakema talle bazatama Audi goriba, kaima kanada kwala-kwalan idanun, komawa tayi jikin kujera tayi shiru.
Shima baisake cewa komaiba yasakko k'asan yazauna kusada ita, yunwa yakeji, rabonsa da abinci tun breakfast dayayi a Kano, fresh milk yad'auka yafarasha da bismillah.
Saida yasha kusan rabin kofin sannan yacire tareda d'ora kofin kan bakin Aysha, d'ago idanu tayi suka had'a ido, takuma marairaice fuska ALLAH ya khaleel nak'oshi.
Eh nasan kin k'oshi, nima aibance baki k'oshinba, ina jaddada sunnar manzon ALLAH ne (SAW), Dan haka bismillah.
Akunyace Aysha tabud'e baki ta kar6a, baicire kofinba daga baki ta saida yaga ta shanye.
Namanma koda yaci saiya kai baki ta, danma karta masa gardama saiya kuma had'e fuska, duk kunya ta dabaibaye Aysha, amma babu yanda zatayi, dole taita kar6a, ganin zaisata amai tace wlhy nak'oshi ya khaleel.
Daina bata yayi yana fad'in gulmammiya, dama kinaso kiketa wani dojewa, amare natsoron cin kazar amarci amma ke kincinye guda d'aya sukutum, ammadai kinji kunya gaskiya.
Aysha batasan sanda murmushi ya su6uce mataba, can k'asan ranta kuma tanajin nishad'i, ya khaleel ya ciyar da ita da hannunsa, batayi zaton samunsa da sauk'i hakaba, ganin halin ko'in kula dayake nuna mata kafin auren Nasu, azatonta kafin auren zata had'a watama bata ganshiba wlhy.

Wringing d'in wayarsane takatse tunanin Aysha, shima cikin matuk'ar mamaki yace, "wanene a darennan haka? Yay maganar yana ciro wayar daga aljihun rigarsa, Momy kuma? to ALLAH yasa dai lafiya? Ya kalli agogon dake tsintsiyar hannunsa sannan yad'aga wayar.
Maimakon muryar Momy saiyaji ta Anty Zuwairah.
‘Khaleel kana gida kuwa?’ tafad'a akid'ime.
“eh ina gida, amma lfy a darennan?”.
Babu lafiya khaleel, momyce keta murkususu harda suma cikinta Na ciwo.......
Da sauri yamik'e yana fad'in, "subahanallah, ganina zuwa", baijira amsartaba ya yanke wayar. Amma zuciyarsa Na mamaki, ganin babu dad'ewa da dawowarau wajen dinner. koda yake ba'a mamaki da ikon ALLAH, saima ta iya mutuwa, wannan kad'an daga ikonsane.
Aysha tace, “lafiya kuwa?”.
“momyce babu lafiya, bara nadubo jikin Nata ”.
To kawai Aysha tace, tareda fad'in, “ALLAH yabata lafiya”.
Yana tafiya yana amsawa.
Kokad'an batun baikama hankalin Ayshaba, tabbas tasan makircine, saidai tana tsoron kullin nasu.
Da sauri tamik'e tashiga bedroom d'inta, wayarta tad'auka takira Anty meerah.
"Lil sholy lfy kuwa da daddarennan? Ina kikabar mijin naki?".
Yafita wajen Momy.
Kamarya sholy?.
Aysha ta zayyane mata komai tana hawaye, tak'are maganar da fad'in Anty meerah wlhy inajin tsoro".
'Dolene Aysha, Dan tabbas akwai abinda suka shirya, su Anty glo shaid'anune, nasan sun sanarma surukarki komai, yanzu ki kulle ko ina, kuma ki ajiye waya a hannunki, dakinji abinda bai gamshekiba ki kira ya khaleel ki sanar masa'.
" Anty meerah banida number sa".
'Babu damuwa, bara nad'auka a wayar dadyn Raudat Na turo miki, ALLAH yasa da ita yake aiki, dannaga waya d'ayace a hannunsa k'aramar Nokia'.
To amin, baradai Na turo miki.

Babu dad'ewa Anty meerah taturo mata number ya khaleel, gaba d'aya a tsorace take, duk motsin dataji saita k'ara k'ank'ame jikinta tana addu'ar daduk tazo bakinta, tun tana saran shigowarsa harta fara fidda rai, har karfe hud'un asuba tayi, iskar asuba datake busowa ta taimaka barci 6arawo ya sace Aysha batareda ta shiryaba.

Ya khaleel kam tunda yafita da sassarfe ya isa 6angaren hajia babba, cikin halin ciwo sosai ya isketa, yazauna abakin gadon kusada Anty Shukurah, suna d'akin itada Anty zuwairah da Anty glo da kubrah.
Hajia babba tarik'e hannun ya khaleel tana fad'in zan mutu Ibraheem.
"Ba zaki mutuba Momy". 'Anty zuwairah why not asanarma Dady mutafi asibiti'.
'A'a Ibraheem karku sanar masa, yana tareda bak'i'. Hajiya babbace mai maganar tana murk'ususn ciwo.
Badan yasoba ya hak'ura, haka sukaita zama jigum-jigum, da barci yad'an figeta, sunfara yunk'urin tashi saita farka tana ihu.
Glory da kubrah saisu kalli juna a sace suna y'ar dariya. haka suka kwana zubur batareda sun runtsaba.
Saida sanyin asuba yafara busawa, ALLAH yaymusu maganinta barcin gaskiya ya saceta.
Daga Anty Zuwairah har Anty shukurah sun galabaita da barci, glory da kubrah kam dake sunsaka kansune basu damuba, ya khaleel madai da sauk'in damuwar, Dan yarigaya yasaba, tunda wani lokacin aikin dare yakan kamasu.
Ganin barci ya d'auketa yazare hannunsa dake rik'eda nashi ahankali, kuje kud'an kwanta tunda barci yad'auketa, zuwa Safiya idan ALLAH ya kaimu saimu tafi asibiti.
anty zuwairah tace, “to khaleel sannu da k'ok'ari, anbar Aysha dai ita kad'ai”.
“ALLAH yasa bata kwanta cikin tsorob”. ‘cewar anty shikurah’.
"Yazatayi Anty Shukurah,? Inma tanajin tsoron aii dolene ta dainashi, tunda nid'in ba mazauni baneba”.
Hakane
"Amma Dukda hakadai akwai tausayi, amarya guda adaren farko babu ango". Kubrace da wannan maganar.
Batareda ya tanka mataba yafice abinsa.
Anty zuwairah ta ta6e Baki, yayinda kubrah taraka bayansa da harara tana maganar k'asa-k'asa, (wadda nima banajinta).

Koda tashiga saiya fara cin karo da kayan dasukaci abinci.
Tattaresu yayi da sauran naman duk ya kaisu kichin, ya ajiye komai Inda yadace, sannan yad'auki gyalenta yanufi d'akinta dashi. Akan gado ya hangota k'udundune da bargo, dagani kasan tayi barcin cikin tsorone, girgiza kansa kawai yayi yafice bayan ya ajiye gyalenta kan sofa..
d'akinsa yashiga komai tsaf, sai babbar rigarsa da hula d'aya cire ya ajiye bakin gadon, jin Anfara kiraye-kirayen sallar farko yacire kayansa yashiga wanka yad'auro har alwala, koda yafito jallabiyya kawai yazira bayan ya tsane ruwan jikinsa, ya shinfid'a sallaya ya kabbara sallah, raka'atainul fijir yayi, sannan yafita masallaci.
Saida yafara shiga d'akin Aysha, tana nan yanda yabarta kwance, tunanin yanda zai tada ita yatsaya yi, ganin lokacin sallah zai kwace masa yad'an duk'o Kansa saitin Inda take kwance ya yaye bargo data lullu6a, yanda Kasan idonta biyu, tamik'e azabure tareda kwallah k'ara!!.
Da sauri ya ruk'ota, "k Aee'sha nutsu mana nine, yay maganar tareda rungumeta ajikinsa".
Jin muryarsa yasakata sakin kuka tana sauke ajiyar zuciya.
Baice komaiba, saidai buga bayanta dayakeyi ahankali alamar lallashi.
Aikam sai sabuwar shagwa6a tatashi ga Aysha, tacigaba da raira masa kukan, jin ana shirin Shiga masallaci ya janyeta daga jikinsa, kinga bara natafi masallaci, kema kitashi kiyi sallah, da hanzari yafice batareda ya kalli fuskartaba.
Wani kukan Aysha tasaki, saida tayi mai isarta sannan tatashi ta d'auro alwala tayi sallah, tana idarwa takoma gado,

Please Login or Register in order to submit comment