Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kan gadonta ba sai bakwai tayi wanka a gurgurje tasa kayanta ta dauki wayarta ta cire kudin da Habeeb yabata jiya ta ajiye a wardrobe ta juya zata dauki wayarta taji an bude qofar an shigo.
Gabanta ya fadi lkcn da taji qamshin turarensa ta juyo a fusace ta kalleshi shima ita yake kallo ya tako gabanta ya tsaya tare da sanya hanunsa ta bayanta ya dora bakinsa a wuyanta yayi peck nata ya dago fuskarta yana qoqarin dora bakinsa a nata ta janye da sauri tare da tureshi yayi baya ya tsaya yana kallonta tundaga sama har qasa ya sauke numfashi yace “kin tashi lfy My Wife" harararsa tayi tace “kauce ka bani guri ni na wucce" tana fadin haka ta figi jakarta ta juya zata fice yayi saurin janyota ta cake tare da hankadeshi ta fice da sauri ya cije lebansa tare da lumshe idonsa yace “duk inda kikaje zaki dawo gareni"





Shima fitowa yayi daga dakin ya dawo parlour ya tarar da ita gurin Baffa suna gaisawa tana ganin fitowarsa ta tashi zata fice Baffa yace “Nafeesatu ki tsaya ga danki nan ya saukeki mana tunda ba lfy kika cika ba" wani takaici ne ya cikata ta juyo ta galla masa harara ya daga mata gira ya zo ya giftata ya wucce tare da zare key din motarta a hannunta ya fice ta jima a tsaye kafin taja qafarta ta fita ta tsaya a jikin motar tana wani huci ji takeyi kamar ta rufeshi da duka.
Murmushi yayi ya bude mata qofar ta shiga ya zagaya ya shiga ya dora hannunsa saman dogayen yatsunta yace “Baffa bai taba burgeni irin yau ba" bata bashi amsa ba ta bude system dinta ta fara dubawa bawai don tana gane komai ba sai don bazata iya jure rainin hankalin yaron ba kadan ya rage ya sanya jininta hawa haka suke tafe tafiya irinta kurame, sunyi tafiya me tsayi kafin su shiga arear da office din nasu Nafeesah yake yayi parking a parking space din ta sanya hannu zata bude qofar yayi sauri danna mata key yace “ina buqatar amsar mgn ta ta jiya Mummy na saboda nasan abinyi Allah ki daina rainani a zahiri nake yaro amma a badini ni ba yaro bane inason aure kuma na shirya yinsa a kowanne lkc daga yanzu saboda ni nasan kaina idan banyi aure yanzu ba Allah akwai matsala, ki fahimceni My Feesah qaninki Nasir yana sonki kuma zai rayu dake"




Harararsa tayi tare dayin tsaki ta sake jan murfin motar ya riqota da sauri yace “wlh kinji na rantse matsawar baki bani amsa ba saidai muyita zama anan dama Abbane ya aikeni kinga idan na koma sai nace masa naje zance ne dama da naje gaisheshi na fara yimasa hannunka me sanda" haushine yasata ture hannunsa tace “waikai wanne irin mara kunyan yarone kaine Naseer yanzu tsabar idonka babu ruwa a ciki ni kake kallo kake fadawa wadannan banzayen maganganun Naseer meyasa ka rainani ne yaushe ma ka balaga ne ko kuwa irin naka tashen balagar kenan kazo ka rinqa yimin wadannan matsiyatan kalaman meyasa Naseer meyasa..."
Kawai sai ta fashe da kuka ta buga kanta saman dashboard tace “nikam na shiga ukuna ni Nafeesah masifa daga wannan sai wannan Ya Allah ni yaushe zanyi farin ciki ne" yanda take kukan yayi mugun razana shi ba yau ya fara ganin kukanta ba amma nayau yafi kowanne daga masa hankali saboda yasan shine sanadin komai kawai don yace yanasonta ne take wannan kukan, jikinsa yayi sanyi ya bude motar ya fita da sauri tare da bude ya tsaya a kanta ta jima tana kukan shikuma ya kasa bata hqr kafin ta saki niqaf dinta ta dauki baqin glass tasa a idonta ta zuro qafafunta ta fito ta shigeshi a gurin.




Binta yayi da kallo yana ayyana abubuwa da yawa a ransa aikin ma dole ta dainashi don bazai jurewa matarsa tana fita tana barinsa a gda da sassafe haka ba komawa yayi cikin motar ya jima yana tariyo kalamanta “ko kuwa irin taka tashen balagar kenan da tasa kakw zuwarmin da wadannan matsiyatan kalaman?" Sosai wannan kalma ta caki zuciyarsa ya qudurta a ransa dole ne ya nunawa Nafeesah shifa ba yaro bane cikakken namiji ne fiye ma da sauran maza yasa a ransa duk ranar data qara kiransa yaro wlh sai ya nuna Mata ya wucce tunaninta kuma saiya nuna mata tsaf zai iya cika mararta komai zurfinta saiya ritsata harma yayi mata ciki ta haihu………….





More comments
More typing




*Mrs Dr M.A...✍🏻*


[4/22, 9:58 AM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )


*( F.W.A)🖌*

https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/



_Sayi daya a baka daya kyauta Mulkin Gargajiya da Auran Bazawara (Luwai)_


_Karku manta single section 200 ne VIP 500_


_Tura ta wannan account number_ : _0255526235_
_Fauziyya Tasi'u Umar GTbank_


_Ko katin waya MTN ta wannan number_ : _09031307566_ _sai kiyi screenshot ki turo ta wannan WhatsApp_ _number din_ : _09013718241_

Saina jiku👌🏻

*AURAN BAZAWARA*
*(LUWAI)*


_typing_ ✍🏻



*UMMUH HAIRAN...✍🏻*


*4*



Key yayiwa motar ya fita daga harabar ma'aikatar ya nufi companyn Abbansa yayi abinda zaiyi ranar ko aikin kirki bai iyaba saboda gabadaya zuciyarsa babu dadi tunanin Mummynsa ne ya hanasa sukuni ga damuwar ganin yanda maganganunsa suka sanya ta dauki fushi na gaske dashi, dama yasani wannan dabi'arta ce a wannan karon duk wanda yazo Mata da mgnr soyayya tsanarsa takeyi balle kuma shi da tariga ta rainashi take masa kallon yaro gani take kamar baikai matsayin da zata iya rayuwa dashi ba.
Da wannan tunanin ya tashi ya nufi gdan babbar yayarsu Aunty Amina saboda ita kadai ce yake fara tunkara da mgn ko wacce iri ce kuma ta bashi mafita yayarsa ce ubansu daya.

******

*TUSHEN LABARI*


Alh Tahir Jafar Rano shine cikakken sunan Mahaifin Naseer wanda yake yayane a wajen Alh Hayat Jafar Rano wato mahaifin Nafeesah asalinsu mutanen Rano ne ta jihar Kano wanda harkar aiki takaisu garin Abuja Alh Tahir da Alh Hayat irin yan'uwan nanne na gani kasheni da wani baya tabajin cikinsu, matar Alh Tahir ta farko itace Hajiya Rabi'ah wadda ya aurota aure irin na ladan noma ma'ana matarsa ce ta rufin asiri tun bashi da komai take tare dashi a garinsu Rano da yaransu uku Amina itace babba sai Jamila wadda take Saace a gurin Nafeesah da sati biyu Jameelah ta girmi Nafeesah wadda itace ya ta farko a gurin Alh Hayat kasancewar shi bayan yayi auren Saida suka dauki shekara uku sannan Hajiya Juwaira ta haihu ana haka Abba Tahir ya qara aure ya auro Hajiya Nafisa bafulatanar Gombe tana zuwa babu dadewa Allah ya basu rabo ita da uwargidan suka haihu kusan lkc daya Jafar shine aka fara haifa dane a wajen Hajiya Rabi'ah wanda suke Kiransa Maje Rano saboda Saida suka tafi bikin sallah Rano acan aka haifesa bayan sun dawo da sati biyu Hajiya Nafisa ta haifo danta itama namiji Wanda ya amsa sunan Naseer lkcn Jameelah da Nafeesah sunada shekara bakwai a duniya nan fah aka rinqa daru a tsakanin yaran Jameelah take hana Nafeesah daukar Maje Rano ita kuma gata Allah ya jarabceta dason yara tun tana qarama hakan yasa ta daina zuwa gdan tanata kuka tana cewa da Hajiya Juwaira itama ta siyo mata Baby irin nasu Jameelah sosai abin yake taba zuciyar iyayenta duk da sunsan quruciya ce to lkcn da aka haifi Naseer nefa tunda taje gdan ta gansa ta tattara kayanta tabar gdan iyayenta dake kusa suke ta koma gdan Alh Tahir ta tare a dakin Hajiya Nafisa tun Hajiya Nafisa tana hanata danta tana korarta harta sake matashi kullum yana gurinta itace komai nasa tun basuyi arba'in ba ta fara daukeshi ta gudu dashi gdansu tace nasune danta ne.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya shaquwa tsananin Naseer da Nafeesah abun baa cewa komai kyakkyawan yaro me shiga rai kamar uwar goyonsa lkcn da ya fara wayo ko makaranta da aka sashi kuka ya rinqayi saida aka mayar dashi tasu Nafeesah kasancewar ita da Jameelah matakin karatunsu daya inda Aunty Amina take jss 3 sukuma suna primary 4 to da zaa sanya Jafar da Naseer play group sai aka sasu wata a kusa amma Nasir ya rinqa kuka yana cewa Mummy na wannan dalilin yasa ba arziqi Alh Tahir ya dawo dasu tasu Nafeesah shikenan aka samu lfy.




Shaquwar yaran burge kowa takeyi amma banda Hajiya Nafisa itadai batason alaqar dan nata da Nafeesah ko kadan dan dai bata Isa tayi komai bane a family din amfi qarfinta saida takai ta kawo Naseer ya tattare komai nasa daga gdan iyayensa tun yana shekara uku ya koma gdansu Nafeesah gdan nasu ma yace shifa a dakin Mummynsa zai zauna hakanan suke zaune komai nasu tare hatta bacci idan zasuyi suna manne da juna hakanan shekaru sukayita tafiya Nafeesah tana girma surorinta suna bayyana tanada 14 years Naseer yanada bakwai komai na matantakarta ya bayyana qirjinta ya fara cika amma duk da haka bata raba kanta da Naseer ba saboda kallon yaro takeyi masa har lkcn idan dakinsu daya ko an rabasu sai ya dawo kuma shi bazai kwanta a shimfida ba saida kansa yana qirjinta idan ta hanashi kuma yace “Mummy na kinsan akwai lkcn da zaki hanani kwanciya a jikinki meyasa kika sabarmin da hakan tun farko?" Idan yayi Mata wannan mgnr dole haka take qyaleshi hatta yankan farce Naseer bai iyaba komai itace takeyi masa duk sallar idan akabasu kudin kashewa sai ta karbe nasa ta bashi nata shikuma nasa ta tara masa ta siya masa kayan wasa a hakan kuma duk sallar duniya sai tayi masa dinki ko ta siya masa yan kanti.
Wannan dalilin yasa Hajiya Nafisa ta sake sakin jikinta da rainon Nafisa ga danta abubuwa da yawa idan tace masa yayi sai yace shi saiya tambayi mummy dinsa iyayensu maza sunajin dadin hadin kan yayan nasu biyar lkcn da Nafisa take SS 3 ne lkcn Baffanta ya qara aure ya auri Hajiya Zainab wadda suke kiranta da mama to dama duk wata rigima guri take samu itama Mama da tazo taga kan iyalan a hade yake haka ta zauna dasu da zuciya daya ta kama Nafeesah da Naseer ta riqe dama sauran yaran gdan kuma tun daga kan Nafeesah Allah bai qara bawa Baffa haihuwa ba.





Lkcn da sukayi candy lkcn akasa bikin Aunty Amina satinsu biyu dayin candy lkcn sunada 18 years Naseer da Jafar sunada 11 years aka fara hidimar bikin komai nasu iri daya akayi musu yammatan sunsha kyau sosai sun hadu iyakar haduwa musamman Nafeesah da kyawunta yake daukar hankalin kowa tunda aka fara bikin take haduwa da samari kala² kowa sonta yakeyi amma taqi bawa kowa fuska.
Ranar dinner ne da daddare sunyi kyau su hudun kamar aljanu Nafeesah tana riqe da hannun Son dinta inda Jameelah take rike da hannun Jafar haka suka shiga kallo ya dawo kansu sukasha hotuna sakin hannusa tayi tace “My Son tsaya Ina zuwa na manta wayata a mota kaji" riqe hannunta yayi yace “Aa mummy na ki tsaya na dauko miki" sunkuyawa tayi tayi kissing lips dinsa tace “kasan banason musu ko?" Daga mata kai yayi tace “to ka jirani" tana fadin haka ta saki hannunsa ta nufi wajen hall din da sauri tana tafe tana gyara agogonta ji tayi tayi karo da mutum tayi baya da sauri tace “Subhanallahi" dagowa tayi kawai taga wani kyakkyawan matashin saurayi fari tass dogo sosai sanye cikin blue din shadda da hula blue yayi kyau sosai shima.





Kallonta yakeyi da kyawawan fararen idanunsa da take ganin wani ruwa ruwa a ciki a hankali ta sakeja da baya tace “kayi hqr don Allah ban kula ba" ajiyar zuciya yayi yace “bakiyimin komai ba dama nazone saboda ke Nafeesah" kallonsa tayi da sauri tace “ni kuma" daga mata kai yayi yace “kin tuna ranar da wani mutum akan farin doki a gefen bolar dake bayan gidanku ya rogeki ki basa ruwan dake hannunki zaisha kika bude jakarki kika dauko gudan robar faro kika bashi?"




Daga kanta tayi ya sakeyin murmushi yace “to nine tun ranar nake bibiyarki kuma nake burin mallakarki yau burina ya cika na sameki kuma na mallakeki matsayin mata sunana Anwar..." Yana fadin haka ya dafata kawai jikinta ya dauki wata girgiza ya rikide ya zama haske ya shige jikinta ta saki wata firgitacciyar qara daidai lkcn da Naseer ya gaji da jiranta ya nufo inda yake tunanin ganinta hasken gurinne ya bashi damar hangota a gasa tanata juye² tana riqe wuyanta tana wata jijjiga, da gudu ya nufota ya fada jikinta ya qanqameta yana jijjigata yana fadin “Mummy! Mummy!! Mummy na!!! Meye ya sameki tashi Mummy ki tashi kada ki bata jikinki da qasa tashi muje mu yanka cake Mummy ki tashi don Allah ki tashiiiii" kukansa ne ya janyo hankalin mutane gurin ciki harda Mukhtar wanda yake aboki ne ga mijin Aunty Amina suka ciccibeta suka sata a mota Mukhtar nayi mata fifita Sani mijin Aunty Amina yana tuqa motar shikam Naseer kuka kawai yakeyi yana kiran “Mummy na ki tashi kada ki mutu ki barni waye da dakeki waye yayi miki fada Mummy na"




Suna zuwa gda aka hau mayar da zance kowa baisan asalin abinda yake faruwa ba kawai dai kowa cewa yakeyi yajiyo ihunta daga haka shikenan, asibiti suka kaita amma a banza har dare ya raba baa samo kanta ba kukan da Naseer yakeyi ne ya sanya masa shima wani mugun zazzabi ya rufeshi da yasa shima aka bashi nasa gadon............







More comments
More typing




*Mrs Dr M.A...✍🏻*
[4/22, 9:58 AM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )


*( F.W.A)🖌*

https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/



_Sayi daya a baka daya kyauta Mulkin Gargajiya da Auran Bazawara (Luwai)_


_Karku manta single section 200 ne VIP 500_


_Tura ta wannan account number_ : _0255526235_
_Fauziyya Tasi'u Umar GTbank_


_Ko katin waya MTN ta wannan number_ : _09031307566_ _sai kiyi screenshot ki turo ta wannan WhatsApp_ _number din_ : _09013718241_

Saina jiku👌🏻

*AURAN BAZAWARA*
*(LUWAI)*


_typing_ ✍🏻



*UMMUH HAIRAN...✍🏻*


*5*




Kwana uku tayi a asibitin batasan waye ke akanta ba sai daga bisani ta farfado shima taimakon abokin Baffanta ne da yace a gwada mata Addu'a saboda abin yafi kama da shafar aljanu aikuwa ana farawa sai gashi ta fara samun sauqi ta dawo hayyacinta, Wai ranar zo kuga murna gurin Naseer ya rinqa rungume ta yana shigewa jikinta itama murmushi takeyi masa tanason tuna abinda yayi sababin zuwanta asibitin amma ta kasa, a ranar aka sallameta suka koma gda akaci gaba dayi mata addu'o'i tunda sun fahimci ciwon nata bana asibiti bane, tun daga wannan lkcn shikenan Nafeesah ta zama wata firgitacciya ko yaushe tan daki a zaune cikin tagumi idan kaga fara'arta to ita da son dinta ne ko zaman parlour batayi ga samari sun sata a gaba ciki harda Mukhtar abokin Sani mijin Auntynsu Amina amma bata kulasu garama Mukhtar shi takan dan tsaya su gaisa ta qara gaba a kuma wannan taqin ne Habeeb Wanda yake kamar qanine a gurin Hajiya Juwaira mahaifiyar da babansa da baban Hajiya Juwaira uwa daya uba daya suke shima ya danno kai da qarfinsa kan cewa yanasonta da aure amma shima ta shafawa idonta toka tace bataso.




Mukhtar dai shine ya ciri tuta tunda sannu² har ta fara tsayawa suyi hira dashi yana yada manufarsa har takai manya sun shiga mgnr da farko babu wata matsala tafiyar tasu amma tunda akasa lkcn bikinsu gaba daya ta birkice masa ta haukace masa tace masa itafa ya hqr da auranta Idan ba hakaba zata kasheshi, bai wani dauki kalamanta da muhimmanci ba saboda yasan ba ita kadai bace haka ya rinqa tausarta yana sanyaya mata zuciya saboda shidai Allah ya sani sonta yake da zuciya daya yake sonta kuma zai iya hqr da kowanne yanayi da zai fuskanta daga gareta.
Bikin yanata matsowa shikuma Naseer yana janyewa daga gareta kullum idan kaganshi cikin damuwa yake gabadaya ya rame takai ta kawo ko waje baya fitowa saboda damuwa kullum yana kwance a daki saboda yanda yakejin haushin Mukhtar da yake qoqarin rabashi da Mummynsa yasha tambayar Abbansa yace “kuma yanzu Abba idan akayiwa Mummy na aure tafiya zatayi tabarni?" Idan yace masa “Eh" kawai sai yasa kuka saboda ko kadan bayason abinda zai rabashi da Mummynsa.





Ranar data kama kuwa zaa fara bikin zazzabi ne me zafi ya rufeshi saboda yanda yakejin zuciyarsa kamar zata fashe to itama Feesah kusan baa cikin hayyacinta ake bikin ba saboda kullum cikin mugayen mafarkai take da Anwar yana jaddada mata shifa shine mijinta shi kadai kada ta sake tayi aure da cikinsa a jikinta batada wani miji a duniya bayanshi ya rufa mata asiri ne ya boye cikinsa dake jikinta saboda kada tazama abar zargi a gurin mutane kullum idan ta kwanta abinda yake nanata mata kenan har yana cimata alwashin sai yasa duk wani namiji dake rayuwa a doron duniya ya tsaneta ta yanda babu Wanda zaiyi sha'awar auranta.
Hakadai ta rinqa daurewa tana boye damuwarta har ranar daurin aure aka daura na jameelah aka daura nata tunda aka daura take kuka shikuwa Mukhtar murna yakeyi burinsa ya cika da daddare aka dauketa aka kaita gdansa abin mamaki mutane suna watsewa taji cikinta yana murdawa ta rinqa murqususu hakanan dai daqyar ta samu ciwon ya lafa Mukhtar suka shigo da abokansa ya shigo dakin ya taddata a zaune a tsakiyar gado yayi murmushi ya zauna kusa da ita tare da janye mayafin jikinta yace “wannan ranar tafi kowacce rana muhimmanci a gurina Ina cikin farin ciki"




Kama hannunta yayi suka fita abokan nasa sukayi musu nasiha tare da addu'ar zaman lfy sukayi musu sallama suka tafi ya rakasu ya dawo ya kama hannunta suka koma ciki ya zare mata lifayar jikinta ya rungumeta a hankali itadai duk a tsorace take hakanan ya jata sukayo alwala sukayi nafila sannan yajata suka kwanta a wannan dare Mukhtar yayi kwanan farin ciki ita kuwa Feesah tayi kwanan wahala shi ya rinqa taimaka mata tana kula da kanta yanata zuba Mata sannu tare dasa mata albarka.
Da safe ma haka ya rinqa tattalinta yanata yimata sannu inda ita kuma cikinta yake ciwo iyakar tunaninta ta dauka ziyarar baqon yanayin ne yasata ciwon cikin amma ina tanada sati a gdan ta lura da kumburin da cikinta yakeyi da farko bata dauki abinda muhimmanci ba Saida tayi sati biyu ta lura duk rigunanta sun fara yimata kadan Mukhtar ne yace suje asibiti shima hankalinsa ya tashi abin tsoro da tashin hankali suna zuwa asibitin akayi mata text akayi mata gwaje² aka tabbatar da cikine da ita har wata bakwai............






More comments
More typing





*Mrs Dr M.A...✍🏻*
[4/22, 9:58 AM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )


*( F.W.A)🖌*

https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/



_Sayi daya a baka daya kyauta Mulkin Gargajiya da Auran Bazawara (Luwai)_


_Karku manta single section 200 ne VIP 500_


_Tura ta wannan account number_ : _0255526235_
_Fauziyya Tasi'u Umar GTbank_


_Ko katin waya MTN ta wannan number_ : _09031307566_ _sai kiyi screenshot ki turo ta wannan WhatsApp_ _number din_ : _09013718241_

Saina jiku👌🏻

*AURAN BAZAWARA*
*(LUWAI)*


_typing_ ✍🏻



*UMMUH HAIRAN...✍🏻*



*6*




Kallon kallo suka tsaya sunayi tsakanin ita da mukhtar, yanayin kallon da yakeyi mata da gani kasan na tuhuma ne gumi sai karyo masa yakeyi, cikin mamaki da tashin hankali yace “haba Dr sake gwadawa dai ka gani ba cikine gareta ba inma akwai bai wucce na sati biyu ba" yanda yayi mgnr yayi mugun daurewa likitan kai yace “To mallam ko zakuje want asibitin ne mudai iyakar sanin mu wannan harka aikinmu ne kuma na'urarmu bata qarya indai mukace akwai to akwaishi"
Yana fadin haka ya juya yabarsu a tsaye Mukhtar ya sake juyowa ya kalli Nafeesah ya kalli cikinta da ya girma sosai ya juya ya fita a matuqar kidime, ta jima a tsaye cikin mugun tashin hankali batare data iya tunanin abinyi ba “shafa cikinta tayi wasu hawaye masu zafi suka zubo mata tace, a falo ta tarar dashi yanata safa da marwa tana shiga ya nufota da sauri ta rinqa ja da baya har ya ritsata a bango ya damqi wuyanta ya hada kanta da bango ya shaqeta yace “ki fadamin uban cikinnan kafin na kasheki"



“Ciki? Ni kuma? A Ina na samu ciki to?" Dawowa yayi fuskarsa babu yabo babu fallasa ya riqo hannunta da qarfi yajata suka fita daga dakin ya cillata a mota ya shiga yaja suka tafi, ba gda suka nufa ba wani babban asibitin kudi suka sake zuwa nanma sukayi bincikesu suka sake tabbatar masa da cikinne da ita, take wani gumi ya fara karyo masa inda ita kuma taketa sharar hawaye tsawa ya daka mata yace “banason kukan munafurci muje gda kiyi kukan da dalili wlh saiki. Fadamin uban cikinnan da aka munafurceni aka lullubeshi aka kawomin ke dashi"
Yana fadin haka ya fice da sauri kamar zai tashi sama amma ga mamakinta tana zuwa ta tarar ya shiga mota harma ya tayar yaja ya fice tabisa da gudu amma ina ko kallonta baiyi ba fita tayi tana kuka kamar ranta zai fita ta tari texi ta fada mata inda zata sauketa ta shiga yaja suka tafi suna zuwa qofar gidan ta sauka ta ciri kudinsa ta bashi ta shiga gdan, a falo ta taddashi yanata safa da marwa ta raba ta gefensa zata wucce ya fincikota da qarfi sa sauke Mata wani kyakkyawan mari a fuskarta daya sanyata ganin wasu tartsatsin wuta a Idanunta ya sake hadata da bango yace.




Raini da qaramin wulaqanci ne bazan dauka ba ki fadamin uban da yayi miki cikin nan da kike neman liqamin" dagowa tayi idanunta na shararar hawaye tace "zargina kakeyi Mukhtar ka yarda cikine dani kenan?" Wani mugun kallo ya watsa mata yace “kinason kicemin ba cikin ne dake ba qazafi nayi miki kenan ko kuwa duka asibitoci ukun dana kaiki qarya sukayi miki? To bari kiji na fada miki wlh bazan yarda ba bakuma zan lamunta ba Nafeesah Allah ya isa tsakanina daku kin cuceni kin cuci rayuwata ciki wata bakwai kika lullubeshi kika kawomin gdana Wanda na tabbata iyayenki basuyi miki wannan tarbiyyar ba kin zubar da tasu a titi amma kanki kika cuta, ki ficemin daga gdana kafin na illataki"
Kuka takeyi sosai kamar ranta zai fita ta riqo hannunsa tace “na roqeka duk rintsi kada ka rabani da igiyar auranka kada ka mayar dani bazawara akan wannan dalilin wlh Allah kenan bantaba aikata zina ba na fara sabawa dakai kaji don girman Allah" tureta yayi ya wucce ya shiga dakinsa ya jima a ciki yana zagaye dakin ya rasa ina zaisa kansa zuciyarsa mugun tafasa yakeyi ya rasa ina zai sanya rayuwarsa ya huta.




Fitowa yayi cikin shirinsa ya wucce ta gefenta tana zaune tanata aikin kukanta yini tayi a zaune a gurin tana kuka tana fadawa Allah ya kawo mata dauki cikin wannan muguwar jarabawa tata wajen la'asar ta miqe daqyar ta shiga kitchen ta fara girki tanayi tana kuka tana aikin harta gama bayan ta gama ta shiga dakinta tayi wanka ga mamakinta sai taga cikinta ya shafe babu alamunsa ta rinqa murna tana yiwa Allah gdy harda kiran Mukhtar ta fada masa bai wani dauki abinda muhimmanci ba ta sauke wayar taci gaba da aikinta.
Sai kuma me? Ta gama shirinta tsaf ta fito daga dakinta kawai sai taga Mukhtar a kwance saman kujera three siter da wayarsa a hannunsa, batare da tunani ko damuwar komai ba ta nufeshi ta tsaya akansa sai taga ya qara mata wani haske,

Please Login or Register in order to submit comment