Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta sauka lafiya",
Saida ta jinjina kai sannan tace "ina son ka sani da rayuwa da mutuwa duka a hannun Allah suke, ka dauka dama rai arone aka bamu kuma a ko wane lokaci wanda ya ara mana zai iya zuwa karvar abnshi, Allah baya barin wani dan....." bata gama fadi ba sakamakon tsawa da mal. Sani ya daka mata yace "me kike nufi? Kina nufin matata ta mutu ko kuwa danda ta haifa? Karki mayar dani sha3 mana",
Qaramin likitan ya fito duk yayi xufa yace "malan daga fadan gaskiya sai ka mata wannan tsawar? Matarka ta samu zubar jinu sosai tare da mummnar faduwar gaba kafin ta fara naquda, babu wanda ya isa ya qetare lokacin da allah ya tsara mashi. Matarka ta rasu munyi iya qoqarin mu dan ganin mun ceto rayuwarta amma da yake iyakar rayuwar kenan bamu iyaba, kayi haquri amma an ceto jinjirin namiji ne kuma lafiyayye",
Wata irin nadama tazowa mal. Sani, kuka yake sosai ya shiga dakin ya rungume gawar matarshi yana fadin "ki yafe mn Rabi'atu, na soki sobda bazan taba iya yiwa wata mata shiba, nine na kashe ki Rabi'atu kuma a shirye nake da kai kaina ga hukuma tun kafin naje ga bbar hukuma", ya miqe tsaye yace "yalla6ai ku kira 'yan sanda su tafi danI a yanke min hukuncin kisa, wlh nune na kashe ta, likita bani da wata sauran rayuwa data rage min a doron qasa, don allah ka kaini a yanke minhukuncin kisa".
Babu musu kuwa likita ya kira 'yan sanda tare da shaida masu duk abnda mal. Sani ya fada da bakinshi, su kuma basuyi wani bincike ba kawai suka tura kotu, jin gamsasshiyar hujja daga bakin mal. Sani yasa aka yanke mashi hukuncin daurin rai da rai babu wani bincike, basu tambayeshi ta wace hanya yabi ya kashe matarshi ba kawai aka tafi dashi prison.

Marwan kuwa yana zaune ya hada kai da guiwa yana tunanin hakun daya tarar da mamanshi ciki har zuwa asibiti da sukayi tare, duk baisan an tafi da babanshi ba, gajiya da yayi ga kuma yunwa yasa ya miqe tsaye yana ta kuka yana kiran "Abbah! Abbah" amma shiru, sosai yaqara fashewa da wani kukan.
Dr. Nasir na bakin gawar Rabi ya rasa ya da zayyi da Ita, a hankali yake jiyo kukan Marwan, da sauri ya fita dan ganin wanda yake kuka, ganin Marwan yayi har ya galabaita, likita yace "yaro me ya faru kake kuka?",
Marwan yace "babana nake nema, kima gashi mamana bata da lafia, can naga an shiga da ita har yanxu bata fito ba", jin hakan ya tabbatar wa Dr. Nasir cewa marwan dan mutumin nan ne, jan hannunshi yayi cikin tausayi ya kaishi gaban gawar mamanshin.

Dedicated to Rerbee'ark sk mshโ™ฅ

Princess Amrah
โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ
[6:45pm, 11/04/2016] ๐Ÿ’“Amrah๐Ÿ’“โœ๐Ÿผ:

โ˜˜๐Ÿโ˜˜ZAFIN SOโ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ ๐Ÿ

โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ

1โƒฃ5โƒฃto1โƒฃ6โƒฃ
Na Amrah
โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ

Cikin natsuwa Dr. Nasir ke magana yace "ya sunanka?",
"Sunana marwan",
"Gud, Marwan an saka a islamiyya kuwa?",
"Ehh an saka ni harda tahfiz ma inayi",
"Yauwa Marwan, an taba baku labari akan mutuwa?",
"Ehh ana fada mana, kuma har malamin mu yace duk kan mai rai sai ya dandani mutuwa, kuma komai sonka da mutun Allah bazai barshi dankai ba, komai girma komai qarantar mutun idan lokacinshi yayi sai ya mutu",
Sosai maganar marwan ta ratsa dr. Nasir. Cikin mamaki yace "marwan shekarunka nawa?",
"Am 8years old",
Da dabara yace "tou marwan indai ka tabbatar da cewa Allah shine yake bayarwa kuma yake qwacewa ka fada mn",
"Ehh na yarda",
"Yanxu idan ka arawa wani pencil dinka na makaranta zaka koma ka karbi abnka?"
"Ehh zan koma"
"Tou Marwan, Allahn daya raya mamanka ya bata aron rai tou yau ya karbi abarsa, ina so kayi mata addu'ah ka fawwalawa Allah komai dan daman shine ya ara mata",
Marwan yace "tou unle na yarda kuma Allah yani kan mamana",
"Ameen" dr. Yace. Tare da miqawa marwan jinjirin data haifa.


Ya karba yana ta kallonshi yaro mai kyau mai irin fuskar mamansu, saI daya kalli jinjirin yaji wani irin kuka mara control yaxo mashi tausayin qaninshi na matuqar addabarshi, bayan ya gama kukan ne yace "uncle ina babana?",
Bai boye masa komai ba ya fada mashi, wani irin haushi yaji gashi bai san kowa a danginsu ba.


A babbar masallaci dr. Nasir ya sanar da mutuwar Rabi, anan aka dauko gawarta aka kawo, ta samu masallata sosaI tare da yan rakiya, aka kaita kushewarta.
Dr. Nasir kuma yayi alqawarin daukar su marwan tare da riqesu tsakaninshi da Allah. Yayiwa jinjirin huduba da sunan babanshi "SANI".

Dedicated to Rerbee'art sk mshโ™ฅ

Princess Amrah๐Ÿ˜˜
โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ
โ˜˜GORGEOUS HAUSA WRITERSโ˜˜
[8:28am, 14/04/2016] ๐Ÿ’“Princessโœ๐Ÿผ: [4:02pm, 13/04/2016] ๐Ÿ’“Amrah๐Ÿ’“โœ๐Ÿผ:

โ˜˜๐Ÿโ˜˜ZAFIN SOโ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ ๐Ÿ

โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ

1โƒฃ7โƒฃto1โƒฃ8โƒฃ
Na Amrah
โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ

Haka sukaci gaba da rayuwa gidan Dr. Nasir, baya nuna masu komai face tsantsar soyayya, matarshI Saude kuwa ta tsane su, kullun sai tsana da tsangwama, Sani da ake bawa madara bata kula dashi sai dai me aikinta Zulai ce ke bashi madara aduk lokacin daya dace, Marwan kuwa kullun da kalar azabar da take gana mashi, danta Shahid ma har dukan marwan yakeyi idan babanshi baya nan.
Kwatsam wata rana Dr. Nasir baya nan Saude ta aiki Marwan da kudi yaje shago, a hanyarshi ta zuwa ne ya yarda kudin, ya neme su ya rasa, yaita kuka dan yana tsabar tsoron masifar Saude.
Kawai ya yanke shawarar yaqi komawa gidan, haka yaita tafiya bai san inda zaije ba. Tun daga nan nima na tafi na barshi dan karmu 6ata tare, har iwa yanxu ban san inda Marwan yake ba.

A 6angaren gidan su kuwa jin Marwan shuru bai dawo ba yasa Saude tace danta Shahid ya tafi ya nemoshi, yaita nema amma bai ganshi ba ya dawo gida. Tuni Saude ta tsure dan bata san abnda zatace wa mijinta ba. Har bayan isha Babu Marwan babu alamanshi, Zulai tafi kowa rudewa saboda tana son marwan amma gashi uwar gijiyanta ta kasa daukar wani mataki akan 6atan yaron.

Dr. Nasir ne ya dawo shahid ya fara bashi labari, yace "dady mamy ce ta aiki Marwan shine har yanxu bai dawo ba",
Cikin kidima Dr. Nasir yace "Marwan din? INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN", da sauri ya qarasa cikin gidan yana kwalawa Saude kira.

Dedicated to Rerbee'art sk mshโ™ฅ

Princess Amrah๐Ÿ˜˜
โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ
[8:04am, 14/04/2016] ๐Ÿ’“Amrah๐Ÿ’“โœ๐Ÿผ:

โ˜˜๐Ÿโ˜˜ZAFIN SOโ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ ๐Ÿ

โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ

1โƒฃ9โƒฃto2โƒฃ0โƒฃ
Na Amrah
โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ

"Ina kika aiki Marwan da har yanxu bai dawo ba? Saude tun yaushe na hanaki aiken Marwan? Idan gaskiya ne me yasa bakya aiken Shahid tunda yama girmi Marwan?",
Da in ina Saude ta kasa bashi ansa, "d d...dm..ma..naa ras..."
"Yi mn shiru Saude! Tunda abn naki hakane zan nemo wanda zata ci gaba da kula mn da Sani, Zulai ta ringa taimaka mata, na kula ke kam bazaki iyaba, ina nufin zan qaro aure dan Sani kawai",
Da sauri ta zabura tace "aure alhj.?! Aure fa kace? Saboda wannan shegen yaron da baida asali zaka qara aure?"
" Ke kikaga shegun yara Saude, nikam ban hada kowa dasu ba, na daukarwa kaina alqawari a idanuwan mutane a cikin babban masallaci tun kafin a dauki gawar mamansu, kina so inci alqawarin ne? Tou ni ban iya wannan ba, da hankalI na da komai bazaki sani jin kunya a idanuwan mutane ba, kuma yanxu zan fita neman Marwan, matuqar ban ganshi ba tou kema sai kin kwana a seil",
Sosai Saude ke kuka tana fadin "wato alhj. Ni kake so ka tozarta ko?" Taci gaba da kuka ko kulata Dr. Nasir bayyi ba ya nufi bakin motarshi.


Tunda ya fita yake neman Marwan lungu da saqo amma babu ko alamunshi, har saida ya jigatu sannan ya nufi police station, harda hotonshi ya gwada masu (wanda ya dauke shi a waya yana riqe da Sani), ya basu wadatattin kudi sannan ya tafi gida daka ganshi zaka gane yana cikin damuwa mara adadi.
Ya shiga gida kanshi a dafe bai kula kowa ba sai zulai daya gani yace "ina Sanin yake? Ko shima an barshi ya tafi?",
Cikin tsoro tace "yana daki yallabai, na gama bashi madara ne yayi bacci",
Bai gama jinta ba ya isa dakinta, ya samu shi cikin net dinshi kwance yana bacci, a hankali ya bude gidan sauron ya sumbaci Sani a goshi tare da fadin "insha Allahu zan riqeka fiye da yanda iyayenka zasu riqeka, zanyi bakin kokari na ganin ka samu farin ciki har qarshen rayuwarka, dan uwanka daya 6ata ma insha Allahu zan bada kudi ko nawa ne indai za'a ganoshi",
Rifewa yayi yana share 'yar kwallar data fito mashi yabar dakin.

Dedicated to Rerbee'art sk mshโ™ฅ

Princess Amrah๐Ÿ˜˜
โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ
[8:19am, 14/04/2016] ๐Ÿ’“Amrah๐Ÿ’“โœ๐Ÿผ:

โ˜˜๐Ÿโ˜˜ZAFIN SOโ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ ๐Ÿ

โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ

2โƒฃ1โƒฃto2โƒฃ2โƒฃ
Na Amrah
โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ


'Dakin shi ya shiga baiko bi ta dakin Saude ba, wai shi a nufin shi yana gwadata ne yaga ko zata shiga dakinshi ta tambayeshi labarin Marwan saboda taga sanda ya shigo amma ta koma dakinta wai ita a dole mai kishi, shiru shiru bata fitoba har bacci ya daukeshi. Qarfe ukun dare ya farka da tunanin rashin ganin Marwan, tashi yayi ya dauro alwala, ya hau sallar da koshi bai san adadin wadda yayi ba, ya hau adduah "yaa Allah ka bayyana mana wannan yaron, idan kuma 6atanshi alkhairi ne Allah ka kaishi wuri mafi alkhairi, Allah ka kareshi da kariyarka ya Allah" kuka yaci qarfinshi ya tsaya da addu'an.

Washe gari da sassafe baiko nufi aikiba saida ya fara zuwa gidan momma (mamanshi) ya gaishe ta tace "Nasiru ya kwanan yaran dasu saude?",
"Lafiya ba lafiya ba momma",
"Me ya faru?" Cikin kidima ta fadi haka tana mai son jin abnda ya faru,
"Momma marwan ne Saude ta barshi ya fita tin jiya bai dawo ba, har police station naje amma sam babu wani labari, sai daga baya Shahid yake bani labarin kalar azabtar dashi da sukeyi shida Saude",
Miqewa momma tayi tace "na shiga uku! Marwan din?! Amma kuwa Saude bata kyauta ba, dama kalar riqon da takewa marayun Allah kenan? Tou shi kuma Sani ya maganarshi? Tana dai feeding dinshi yanda ya kamata ko?",
Jin tambayoyin momma bazasu qare ba yasa a taqaice yace "Sani ma zulai me aiki ta barma shi wai ita ke kula dashi, tou ni a gani na kawai in qara aure ko zan samu mai kula dashi tunda ita bazata iya ba",
"Shawara me kyau kenan Nasiru, dama akwai Maryam 'yar qanwa ta, kamilalliyar yarinya ce mahaddaciyar Qur'ani, wannan shekarar ta gama makaranta, insha Allahu yau zan tinkari mahaifiyarta da maganar, kome kenan zan kiraka",
"Tou momma nah, shiyasa bana gudun kI da duk shawarar dana ke nema, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi".

Dedicated to Rerbee'art sk mshโ™ฅ

Princess Amrah๐Ÿ˜˜
โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ
โ˜˜GORGEOUS HAUSA WRITERSโ˜˜
[8:59pm, 17/04/2016] ๐Ÿ’“Princessโœ๐Ÿผ: [8:16pm, 17/04/2016] ๐Ÿ’“Amrah๐Ÿ’“โœ๐Ÿผ:

โ˜˜๐Ÿโ˜˜ZAFIN SOโ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ ๐Ÿ

โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ

2โƒฃ3โƒฃto2โƒฃ4โƒฃ
Na Amrah
โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ

Cikin sati bayu aka gama maganar auren Dr. Nasir da Maryam. Ba'ayi wani abu ba sai walima.
Saude tasha kuka ita a dole mai kishi, ganin bata da yanda zatayi yasa ta dangana. Gida daban aka kai Maryam, saboda Dr. Nasir yasan baza su ta'ba zaman lafiya ba matu'kar ya had'e Saude masifaffiya da Maryam nitsatstsiyar yarinya.

Kwananta uku a gidan shi ya kar'bo Sani, sai da ya sai mashi komai sabo kafin ya kaishi, har da madarar da ake bashi mai kyau da tsada.
Sosai Maryam taji dad'in Sani, saboda ita dama can maI son yara ce, musamman Sani da Dr. Ya aure ta musamman saboda shi.


Kula sosai yake samu wurin Maryam, ko kukan shi bata son ji. Tsakanin ta da Saude kuwa ko ta kai mata ziyara bata ko kallon inda take, magana ma bata ansawa idan tayi mata. Sai harare harare. Da zarar Sani yayi rarrafe ya nufi inda take kamar taga kura take mashi. Ta kai da tsoron ta ma yake ji, ko gidan sukaje baya nufanta.


Marwan kam babu ko labarin shi, anyi nema har an gaji, Dr. Nasir yace ma Maryam "ni har ma na fawwakawa Allah komai, fata na dai Allah yasa yana lafiya a duk inda yake",
Maryam tace "Ameen ya Allah".
Kwance tashi babu wita wurin Allah har Sani ya shekara hud'u ya shiga makaranta, yana da haza'ka sosai dan duk class d'in su babu mai 'ko'karin shi. Har Dr. Yana yawan mamakin Sani, bai ta'ba ganin yaro kamar shi mai sharp brain ba.

A haka har ya gama Secondary School, a lokacin Maryam nada yara uku duka mata, babbar itace Zarah, mai bi mata kuma Futha, sai autar ta Khairat. Duk a cikin yaran Sani yafi sha'kuwa da Futha, suna shiri sosai har idan bata ganshi ba bata jin dad'I. Kwatsam da gamawar shi gwamnati ta d'auki nauyin fitar dashi UK karatu. Futha tasha kuka kafin su rabu, sai da yaita bata baki kafin ta amince.

Dedicated to Rerbee'art sk mshโ™ฅ

ยฉPrincess Amrah๐Ÿ˜˜
ยฎEHWยฎ
โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ
[8:28pm, 17/04/2016] ๐Ÿ’“Amrah๐Ÿ’“โœ๐Ÿผ:

โ˜˜๐Ÿโ˜˜ZAFIN SOโ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ ๐Ÿ

โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ

2โƒฃ5โƒฃto2โƒฃ6โƒฃ
Na Amrah
โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ

Sani bai dawi Nigeria ba sai da yayi Ph. D ya zama professional Doctor. Ranar da zai dawi Futha ta had'a mashi abubuwan jin dad'I, tayi gayu sosai na dawowar d'an uwanta.
A Airport suka d'auko shi ya 'kara kyau sosai dan dama indai wurin kyau ne to baza'a barshi ba.


Wata d'aya da dawowar shi ya samu aiki a FEDERAL INLAND REVENUE branch d'in Katsina, Dr. Nasir yace "to Sani kaga dai ka samu aiki mai kyau, yanzu abunda ya rage maka kawai aure, bana so ka fara zuwa Office ba tare da aure ba, me kace?".
Susar 'keya ya fara sannan yace "Dady dama....." sai kuma yayi shiru.
"Dama what? Talk Sani",
"Dady ina son ka nema mun wadda zan aura, saboda banda budurwa" ya du'kar da kanshi cikin kunya.

Dad yayi murmushi irin nasu na manya sannan yace "dama haka nake son yi, na dad'e dayi maka mata, kuma matar ma wadda kuka sha'ku sosai da ita",
Kanshi ya d'ago yace "to Dad godiya nake, Allah yasa ta zama abokiyar zaman alkhairi".
Dad yace "Ameen".

Sani bai ko tsaya jin wacece za'a aura mashi ba, da mamaki ya tafi dan yasan a iya sanin shi babu wata mace wadda ya sha'ku da Ita, a iya sanin shi Futha ce kawai, to ai kuma Futha blood sister na ce. Ni kuma Amrah nace "ba wani blood sis, kaine dai kake tunanin haka amma ba haka bane" mudai je zuwa zaka san ko wacece zaka aura.

Dedicated to Rerbee'art sk mshโ™ฅ

ยฉPrincess Amrah๐Ÿ˜˜
ยฎEHWยฎ
โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ
[8:40pm, 17/04/2016] ๐Ÿ’“Amrah๐Ÿ’“โœ๐Ÿผ:

โ˜˜๐Ÿโ˜˜ZAFIN SOโ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ ๐Ÿ

โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ

2โƒฃ7โƒฃto2โƒฃ8โƒฃ
Na Amrah
โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ

A ranar da Dad ya shaidawa Sani da Futha cewa zai had'a su aure ba 'karamin mamaki sukayi ba, babu wanda ya iya tankawa a cikinsu, sun d'auki misalin awanni biyu a haka bayan Dad ya basu wuri ganun basu da niyyar magana yace "su same shi a d'akin shi idan sun tashi jin labari". Tashi sukayi Sani na gaba Futha biye dashi kowa da kalar tunanin da yake.

Sun samu Dad yana karatun jarida, jin alamun su yasa ya ajiye yace "kun shirya kenan?", kai kawai suka d'aga yace "kuje ku kira Khairat da momy'n ku, na riga da na kira Zarah tana kan hanya ma".

Cikin 'kan'kanin lokaci duka suka hallara har da Zarah dake da tsohon ciki. Cikin dattako ya fara da "naaan duk kan ku zakuyi mamaki abunda zai fito daga baki na, to ba abun mamaki bane kuma ya zama fole na fad'e shi, bana so wani ya bani wata fassara haka kuma bana so inji wata magana daga baya", nan ya hau basu labari tun farko har 'karshe, duk abunda ya faru sai daya fad'a har da labarin Malan Sani da akaiwa d'aurin rai da rai a gidan yari, da kuma Marwan daya 'bata tun shekaru 29 da suka wuce. Sunsha koke koke, Sani ma yayi kuka tare da yin godiya ga Dr. Nasir saboda irin ri'kin da yayi mashi, bai ta'ba nuna bashi ya haife shi ba, baya nuna banbanci tsakanin shi da Shahid yaron daya haifa, har ma yafi nuna kulawa a gareshi saboda Shahid shaye shaye yake babu abunda baya sha, shi yasa ma baI wani damu dashi ba. Saude tayi masifar har ta gaji.

Cikin mako uku aka gama hidimar biki, Futha ta tare a katafaren gidan da Dad ya mallakawa Sani.

Dedicated to Rerbee'ary sk mshโ™ฅ

ยฉPrincess Amrah๐Ÿ˜˜
ยฎEHWยฎ
โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ
[8:57pm, 17/04/2016] ๐Ÿ’“Amrah๐Ÿ’“โœ๐Ÿผ:

โ˜˜๐Ÿโ˜˜ZAFIN SOโ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ ๐Ÿ

โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ

2โƒฃ9โƒฃto3โƒฃ0โƒฃ
Na Amrah
โ˜˜๐Ÿโ˜˜


Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment