Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kice kenan?"
"Mairo kenan, kinsan dai bani da lokacin batawa don haka ki shiga hankalinki dani."

Tass! Abule ta dauketa da mari tana huci take fadin,"Kekam anyi bagidaja walla, yo mi naki da zaki wanke muna jikki da wanga ruwan wanki?to walla ki yi abun da yadda meki ba ruwana ta dake".

"Yauwa Abule tawa haka nake so kicimin kaniyar duk wacce ta yi damu a gidan nan."
"Barsu ta dani ina ma mace dukan tsiya walla ni bani daukar reni".

"Ni kika mara Abule?" Maman Dare ta tambaya tana dafe da kuncinta.
"Yo me zaki yi?"
"Ina zuwa zakiga abun da zanyi yanzu kuwa" ta wuce dak'inta da sauri.

Ita dama Mairo bata da karfin yin fada, dan haka tana ganin Maman Dare rike da wuka tai daki da gudu tare da danna sakata a kofarta.


Abule ta ruga kicin ta dauko bakin wuta gashi sai ci yake wanda matar Malam ta hada ta dora girki.




*Badeeyerh Beauty Queen*
[3/1, 12:35 PM] Beauty Queen: βšœβšœπŸ”±πŸ”±βšœβšœπŸ”±πŸ”±βšœβšœ
*'YAN GIDAN HAYA*
πŸ”±πŸ”±βšœβšœπŸ”±πŸ”±βšœβšœπŸ”±πŸ”±

. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​.




Β©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼



Dedicated to
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*


πŸ“š ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ πŸ‘‡πŸ½
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

πŸ“© ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ πŸ‘‡πŸ½
Zamaniwriterassociation@gmail.com

When I Am Glad,
You Are In My Smile,
When I Am Sad,
You Are In My Tears,
When I Am Walking
you Are In My Steps,
When I Am Sleeping,
you Are In My Dreams.
I Love You! Abu Uthaemin.

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*20~25*

InnaTalatu dake wanke injin nikarta ta kalle su ta yi dariya, domin duk zancen da suke yi tasan da ita suke, gashi yanzu ta kwabe musu.

Maman Akintola ce ta fito daga dak'inta dauke da buhun kankara a kanta zata kasuwa, taga wannan aika-aika dake shirin faruwa, ta ajiye buhun tare da riko Maman Dare.
"A'a Mama Dare menene yana faruwa aka, da wanini zakiyi fad'a da wuka?"

Tana haki ta kalli Maman Akintola tace "waccan shegiyar zan koya ma hankali naga alama bata da shi".
"kece shegiya wallahi ba Abule ba"cewar Mairon Ado dake makale jikin tagar dakin ta.

Abule dake tsaye rike da bakin wuta ta yi dariya tana kallon Mairon Ado tace "walla ke kau kin rako mata matsoraciya na kawai"

"A'a Mama Dare idan kayi fad'a da wuka kasen dai mai anguwa zata kai karan ka station ko? So please be patient".
Hararar Abule ta yi kafin ta juya da nufin komawa daki, rabon ayi saiji ta yi Abule na fadin "Banza da kin hwadi mun wanda bai da hankali yau walla".

Aikuwa jefar da wukar ta yi ta nufe Abule tare da cakumar rigarta ta yaga tun daga sama har kasa kasancewar doguwar riga ta sanya, sannan ta hau jibgarta kamar an aikota. Kokari take ta rama amma ba hali domin ba karamin riko Maman Dare ta yi mata ba.

Ganin ana dukan Abule yasa matar malam fitowa tana fadin "Bari na rama wa kura aniyarta" ita ma ta hau jibgar Maman Dare.

Maman Akintola ta dubesu sannan ta dubi yanda buhun kankararta ya fara ruwa, kawai ta karasa ta dauka tana cewa "Bana da kudi berinje kasuwa nawa kawai" ta fice.

Maman David ce ta shigo daga wurin saida akamunta a waje, ganin wannan fad'a na wanda ka sani, ita ma kawai ta shigar ma Maman Dare.

"wallahi ba za'ayi babu ni ba gara nima na rama abun da ya faru jiya" cewar Inna Talatu.

Itama ta shiga cikin fad'an, sai dai nata kowa duka ta keyi sabanin matar Malam dake ramawa Abule, aikuwa da karfin tsiya itama Abule ta yaga t-shirt din dake jikin Maman Dare, hade da kai mata wawan duka a hanci da ya yi sanadiyar fitar jini. Ganin wannan jini ya harzuka Maman Dare ta gabza ma Abule duka a baki, sai ga hakori ya fado daga bakin Abule. Ihu ta sanya tare da rarumo iccen data yarda ta cire rigar da aka yaga tai kan Maman Dare.

Matar Malam kuwa Maman David ta samu ta kwantar kasa tana duka kamar kayan wanki. Hargowa da hayaniyar su ta fito da sauran matan gidan, ganin irin fad'an da a keyi na wanda na sani ya sanya itama Maman Ladi shiga ta hau jibgar Maman David dake kwance kasa suka rufan mata ita da matar Malam. Iya beji na ganin haka tace "Abun nayi ne dole na shiga" ta rufan ma Abule da duka.

Gida ya rikice, ba wanda ke kokarin bada hakuri sai dai ya shiga ya rama ma wanda ya sani koya fanshe haushin shi kan wanda yake tsumayi.

Ganin ba mai rabo ya sanya Mairon Ado bude sakata, ta fice da gudu sai gidan mai unguwa.


*GIDAN MAI UNGUWA KUWA*



Zaune yake a zauren gidan sa tare da yaran shi Sani da Lado. Ya dubi Lado yace, "Ya kamata kayi aure badi Lado, ka girma da yawa ga kannen ka nasan kai suke jira"

Sosai kai ya yi yace "Insha Allah Baba a tayani da addu'a" "To Ubangiji ya yi maka zabi na gari"
"Ameen Baban mu" Sani ya amsa. Mai unguwa ya kalle shi "to mara kunya dama nasan saikai ai, tashi ka bani wuri" tashi ya yi yana dariya ya shiga cikin gidan.

Mahaifiyarsa ce zaune bakin madafi tana gyaran shinkafa. "sannu da aiki Mama kawo na tayaki" ya fadi yana niyar amsar tiren shinkafar.
"A'a Sani barshi na gode, jeka ga Hanne can a wurin dabbobi tana shara ka amsa ita sai tazo muyi girki" "to Mama" ya wuce.

Kasancewar suna zaman lafiya kamar ba kishiyoyi ba, yasa komai nasu tare suke yi. Ta taho tana fadin "Maman Sani shine zaki sanya shi aikin wahala maimakon ki bashi shinkafa ya tsince?"
"A'a Hanne gara ya amsa ai, kizo nan muyi aikin abinci"
"To shikenan na gode" ta zauna suna hira suna aiki.

Mai unguwa ya shigo yana hade fuska ya kalli Hanne "Sai a kaimin ruwan wanka bandaki"
"Malam tun dazu fa na sirka ruwan, da naga baka shigo ba shine na juye nai wanka"
"Hanne! Hanne! Hanne! Sau nawa na kira ki?"
"Uku malam" ta bashi amsa.
"To wallahi tun da girma da arziki ki nemo min ruwan wanka na, in ba haka ba billahillazi karar ki zan kai gurin ubanki."

Cikin takaici Jummala ta kalle shi tace "Malam wulakancin ka ya fara isar mu cikin gidan nan,meye na saka uba cikin wannan maganar? To wallahi na gaji da wannan halin naka"
"Yo ba sai a dakeni ba idan za'a iya, ko kuma a rama zagin"
"Ba wanda zai deke ka balle ya rama zagi, saboda munsan darajar aure, amma wallahi halin ka ya isheni"
"Aikin banza ruwan wanka nake bukata yanzu ba sai anjima ba"

Ta kalle Hannatu wacce ko dago kai ba ta yi ba dan takaici tace "Hanne juye mai ruwan sanwar can, gara ya fita ko zamu sha iska mai dadi"
"Ba inda zani ina cikin gidan nan naga mai fitar dani." ya fadi lokacin da yake shiga dak'i.


Ba wacce ta kula shi cikin su, Hannatu ta juye mai ruwan ta aje bakin kofar bandak'in.
"Malam ga ruwan nan na ajiye"
"gani nan zuwa ai 'yar magoriya, zaki fadawa makawafta zanyi wanka ko?"

Bata amsa mai ba, taci gaba da gyaran shinkafarta.

Yana fitowa ya dauki bokitin da niyar shiga bayi, sai ga Mairon Ado ko mayafi babu ta shigo a guje tana kiran "Taimako! Taimako mai unguwa uban al'umma, gidan 'yan haya zasu janyo a daure ka shekara dari a kurkuku idan sukai kisa a unguwar ka."

Sakin bokitin ruwan ya yi ya tuntsire kasa ya bita da gudu, Hannatu na fadin" Malam baka warke ba zaka koma?" Ina tuni ya fice daga gidan.



*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
[3/1, 12:36 PM] Beauty Queen: βšœβšœπŸ”±πŸ”±βšœβšœπŸ”±πŸ”±βšœβšœ
*'YAN GIDAN HAYA*
πŸ”±πŸ”±βšœβšœπŸ”±πŸ”±βšœβšœπŸ”±πŸ”±

. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​.




Β©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼



Dedicated to
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*


πŸ“š ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ πŸ‘‡πŸ½
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

πŸ“© ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ πŸ‘‡πŸ½
Zamaniwriterassociation@gmail.com


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*25~30*

Tallafe kumatu ta yi tare da duban Jummala tace "Maman Sani kina kallo ko?" "Kema ce da neman magana wallahi, yaje shiyasa ni."

Nan suka cigaba da girkinsu suna hirar halin mai gidan nasu.


*A GIDAN 'YAN HAYA*

Shigowar mai unguwa ya yi dai-dai da bugawa Maman Dare icce akai wanda Abule ta yi wannan aiki.

"Kai! Kai! Kubari nace don iyayen ku" cewar mai unguwa.

Ina! kamar basu ji ba domin Iya beji ce ta rafka ma Abule icce itama ganin Maman Dare zube a kasa tana kuka. Shake wuyan Iya beji Abule ta yi tana jijjigata, wanda ya sa juwa dibar Iya beji ta zube a kasa, Abule ta hau kanta tana duka. Ganin haka Maman Dare dake dafe da kai ta dau iccen da Iya beji ta yarda da nufin dukan Abule dashi, ganin haka mai unguwa ya yi tunanin shiga tsakani aikuwa sai a gefen kafadarshi yaji saukar iccen wanda ya haddasa mishi yin taga-taga kamar zai fadi, kafin ya samu ya tsaya a gefe dafe da kafadarsa da yake ji kamar zai cire don tsananin zafin da yake ji.

Mairon Ado dake labe tana leke, ganin an rafka ma mai unguwa icce yasa ta kurma ihu sanin cewa yanzu ba mai rabon wannan fada. Ganin ihun nata bazai yi maganin komai ba, yasa ta shiga dak'i ta dauko bokitin ruwanta tare da sheka masu Maman Ladi dake dambe a kasa. Saukar ruwan yasa suka mike a firgice suna kallon mai wannan aiki, yayin da mai unguwa ke duk'e a kasa ya dafe kafadarsa kamar ya yi kuka.

Maman Dare ta samu gefen kumatun Abule ta gantsara mata cizo wanda ya sanya ta saki Iya beji ba shiri ta kurma ihu domin taji zafin cizon. Sanadin da ko wacce ta mike tsaye kenan ana kallon-kallo. Shigowar Malam Isah da Baban Dare kenan gidan domin makwafta suna jin wannan fad'a amma suna tsoran shiga gidan. Shigar mai unguwa ma duk akan idanunsu, jin ihun ya cigaba suka san mai unguwa baiyi nasarar rabawa ba, shine suka kira mazajen a waya. Kasancewa suna kusa domin kanikawane su biyun a bakin titin kan layin.


Baban Dare nufi mai unguwa dake tsugunne ko numfashin arziki ya kasa yi, yace "Mai unguwa kina lafiya, menene ya same ki?"

Cikin zafin mai dashi jinsin mace ga kuma azabar ciwon hannu yace "Dalla daukeni ka kaini gidan Usaini mai dori kafin hanuna ya lalace, kuma wallahi sai nayi shari'a da matar ka".

Duk da Baban Dare bai fahimci abun da mai unguwa ke nufi ba, amma yasan wurin Usaini mai dori, don haka ya mike yana kiran "Esa kizo ki rike mai unguwa akaita wurin Huseni ya yi gyara annu nata". Da sauri malam Isah ya karaso don dama yana tsaye ne wurin su Inna Talatu dake zage-zage.

Suka rike mai unguwa zasu fita da shi, ya juyo yace "ke matsiyaciya! Wallahi ki jira na dawo billahillazi sai nayi karar ki wurin hukuma".


Ba wanda ya tanka shi har suka fita, malam isa cike da zullumin mai zai faru idan suka bar gidan? Sanin cewa zasu iya yin wani abun ya sanya ya kalli baban Dare sanda suka isa waje yace "Ka rike mai unguwa ku tafi nasan matan nan zasu iya yin wani aika-aikar, bari na koma gidan" ya fadi cikin harshe turanci yanda baban Dare zai fahimta.

Ya gyada mishi kai kawai tare da kara riko mai unguwa domin su tafi, fir mai unguwa ya dage lallai sai malam Isah yazo an tafe tare dashi duk da bayanin da ya yi mai, amma mai unguwa ya dage. Haushi ya kama Baban Dare yace "ke mai unguwa kina so mata namu ya yi kisa ne? Kina gani fa mun bershi shi kadai ya na fada ba meza a gida fa."
"Yo ina ruwana dasu? su kashe kansu mana, amma billahillazi sai kun kaini gidan Usaini dukkan ku."
"Haba mai unguwa taya kake tunanin dukkanmu mubar gidan? Kiran mu aka yi domin tsawatar musu, amma ganin halin da kake ciki muka zabi taimaka maka, shine kuma kake cewa su kashe kansu?" cewar Malam Isah.
"Esa berta ki shiga gida, nine kadai ze kaita gidana huseni tefi kawai" Baban Dare ya fadi.


Malam Isah ya wuce ba tare da sauraron abun da mai unguwa ke fadi ba.


Baban Dare ya kalli mai unguwa dake ta aikin sababi, ya nade hannun riga tare da daukar mai unguwa da nufin goyawa a bayan shi.

Ganin wannan aiki yasa mai unguwa daga hannun mai ciwo ya kaimai duka a baya, wanda yasa hannun kara amsawa sai kuma ya dafe tare da matsar kwalla don ciwo .Baban Dare ya kalli mai unguwa yace "ok asema hannun ki yana lafiya shine kince aje gidan huseni ko? To walah ba zen kaiki ko ina ba" ya juya ya yi shigewarshi cikin gida ya bar mai unguwa tsugunne ga hawaye nabin fuskar shi.

Makocin 'yan gidan haya ne ya tausaya ma mai unguwa tare da daukar shi a mashin suka nufi gidan mai dori.


*A CIKIN GIDAN' YAN HAYA*

Zage-zage akeyi tsakanin su, ko wacce na zagin wanda sukai fad'a tare. Ganin mazan sun dawo ya sanya sukai shiru aka koma hararar juna.

Baban Dare ya dubi Maman Dare cikin yarensu yace "Na gode da kika zubarmin da mutunci, kullum ina fada miki ki daina shiga abun da babu ruwanki kinki, to wallahi duk abun da ya faru babu ruwana" ya shige dak'i.

Tasan halin mijinta da zuciya, jikanta ya yi sanyi ta rufa masa baya ita ma.

Malam Isah ya kalle su yanda sukai tsaye suna jifan juna da mummunan kallo yace "Talatu kuna da masaniyar kun kar ya mai unguwa ko?"
"Kar ya shi kuma, ta ina?" ta tambaya a rikice.
"A'a wallahi Maman Dare ce ta buga mai icce" cewar Mairon Ado dake tsaye gefe.
"To wata shegiyar ce ma ta kira shi gidan nan?" Maman Ladi ta tambaya tana hararar Mairon Ado.

Takaici ya kama Malam Isah ganin mai makon su jajanta, amma suna kokarin mai da zuwan nashi ma abun fad'a, dan haka yace,
"Ko wacce ta kira mijinta kafin zuwan 'yan sanda gidan nan,kun san halin mai unguwa" ya shige dak'i.

Suna tsoran batun' yan sanda don haka ko wacce ta shige dakin ta, tare da neman mazajen su.


An hallarra a tsakiyar gidan.

*Kome zai faru???*

*Ina labarin mai unguwa???*



*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
[3/1, 12:36 PM] Beauty Queen: βšœβšœπŸ”±πŸ”±βšœβšœπŸ”±πŸ”±βšœβšœ
*'YAN GIDAN HAYA*
πŸ”±πŸ”±βšœβšœπŸ”±πŸ”±βšœβšœπŸ”±πŸ”±

. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​.




Β©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼



Dedicated to
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*


*WANNAN SHAFIN KYAUTA NE GARE KI ZUWAIRA MADARA. AUNTY ZETTY NAYIN KI IRIN SOSAI DINNAN, TANA YI MIKI FATAN ALKAHAIRI, ALLAH YA RAYA HANEEFAH, KEDIN TA MUSAMMAN CE.*

πŸ“š ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ πŸ‘‡πŸ½
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

πŸ“© ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ πŸ‘‡πŸ½
Zamaniwriterassociation@gmail.com


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*30~35*

Mai Unguwa zaune gaban Hussaini mai gyara, yana jiran ayi gyaran hannunshi saboda azabar ciwon da yake ji. Hussaini ya kalle shi bayan ya taba hannun yace "Mai unguwa ka samu tsagewar k'ashi a kafadar ka, garin ya hakan ya faru?"
"kayi aikin ka ba tambaya ba malam "cewar mai unguwa a fusace.

Gyada kai Hussaini ya yi yana murmushi, ya dauko wani mai ya diba sannan ya kama hannun mai unguwa da karfin tsiya. Wani ihu mai unguwa ya saki wanda ya janyo hankalin yaran gidan, suka dinga leke suna dariya.

Cikin azaba mai unguwa yace "Allah ya isa Hussaini, billahillazi ban yafe maka ba duniya da lahira azzalumi kawai".

Kara shafa man Hussaini ya yi ba tare da ya kula mai unguwa ba, ya sake riko hannun ya matsa ya shafe da wannan mai. Mai unguwa ya kwalla kara yana hawaye yana zagin Hussaini, shi kuma Hussaini saiya kama kafadar mai unguwa sai ya fanshe zagin da yake yi mishi. Ganin azabar ta yi yawa ya sanya ya warce hannun shi tare da mikewa ya share kwallar idonsa yace "Zakasan ni mai unguwa Tanko ka yi ma wannan mugunta wallahi, har da kai 'yan sanda zasu hada yau." ya juya zai fita.

"Mai unguwa kudin aiki na fa?" cewar Hussaini.
"Na karfine kazo ka k'wata azzalumi kawai"
"Haba mai unguwa, wannan fa hakkina ne."
"Naci hakkin naka, kayi abun da zaka yi." ya juya ya fice. Yana isa tsakiyar gidan ya ga dandazon yara sai dariya suke ganin ya fito. Tsawa ya daka musu, amma ina sai fadi suke "Mai unguwa ya yi kukan gyara yeeee ra go, matsoraci mai unguwa Tanko" suna shewa.

Da gudu ya bisu ga hannu a rike, aikuwa suka k'wasa da gudu suna dariya. Ganin bazai ka masu ba ya sanya ya wuce yana aikin sababi yana fadin "Yau hatta iyayen ku suma sai sun kwana ofishin 'yan sanda, billahillazi tare da 'yan gidan haya. Yanzu ma can zani na kira su." jin hannun nashi namai ciwo idan yana tafiya, yasa ya k'wance rawaninsa ya daure hannun dashi yana cije baki. Sannan ya mike hanya sai station.

*********

*A TSAKAR GIDAN 'YAN HAYA*

Kowa dake gidan ya hallara wurin wannan taro, bayan an zauna ne malam Isah ya mike da bayani kamar haka.
"Ina fatan zaku mai da hankali ku fahimci ainahin abun da ya taramu anan? Dalilin wannan taro kuwa bazai rasa nasaba da fadace-fadacen dake yawan faruwa ba a gidan nan. Misali na yau wanda ya kai mizanin babu mai hankali a cikin matan mu, ko wacce kokari take na ganin ta yi fad'a badai ta raba fadan ba yau, mai unguwa da ya kasance uban al'umma kuma matsayin mai kula da wannan gida yau shima sun ji masa ciwo a hannu. Kuyi sani cewa mai unguwa bazai taba barin wannan magana ba face ya danganta ta da hukuma, shiyasa nace ko wacce ta kira mijinta domin sanin abun yi"

Cikin takaici Baban Dare yace " sunayi fad'a kaman kaji wada beci abinci ba".Dariya wasu suka yi dajin hausar shi. Mijin Maman Ladi ya mike yace" Tabbas abun da matan mu keyi kwata-kwata basu tsare mana mutunci, sai kace mu kadaine 'yan haya cikin wannan gari, kullum sai sun ja mana jaraba wurin mai unguwa. Ranar cewa ya yi wurin sarki zai kai karar mu a koremu domin ya gaji da masifar matan mu" ya karasa cikin bakin ciki.


Haka aka dinga mai da bayani kan halayyar matan gidan, inda aka hana matan magana. Kowa ya yi ma matarsa kashedi kan wannan halayyar tasu. Ana cikin wannan magana ne suka ji jiniyar motar 'yan sanda, cikin takaici mazan suka mike da niyar fita waje, amma sai ganin 'yan sanda suka yi tare da jagorancin mai unguwa dake sak'ale da hannu a wuya kai babu rawani.


Mazan ne suka yi musu tayin zaman sulhu, amma mai unguwa yace sam babu sulhu sai dai a tafi da Maman Dare ofishi tunda itace taji mai ciwo.
"Kwarankwatsi sai an tafi da ita, matsiyaciya ita ta bugamin icce kawai don nazo rabon fad'a, shi kuma shegen mijinta ya barni a waje harda cewa wai na mutu ai basu suka kirani ba."
"Haba me unguwa kiyi hakuri mana ki fadi gaskiya" cewar Baban Dare jin bayanin mai unguwa.
"Yauwa Usmanu kaji ba? Mace yake kirana shegen kwanon" Mai unguwa ya fadi yana nuna Baban Dare.

Dariya dan sandan da ya kira da sunan Usmanu ya yi yace "afuwan mai unguwa bai iya hausa bane shiyasa"
" Yo dama an fadi mai hausar kayan banza ce? Ai dole ya kasa tunda ba muhallinsa bace" Mai Unguwa kenan.

Sauran mazan ne suka shiga maganar don ganin ba a tafi da Maman Dare ba albarkacin mijinta, sunyi ma mai Unguwa Alkawarin biyan kudin jinyar hannun shi har ya warke. Jin haka dama gashi da masifaffen son kudi, take ya amince da wannan tayin.

Nasiha sosai 'yan sanda sukai musu, tare da basu hakuri ganin an zauna tare, sannan mai unguwa ma yace "Na daina zuwa gidan nan koda zaku kashe kanku." Dariya sosai suka yi, sannan kowa ya kama kansa.


*SHIGAR MAI UNGUWA GIDANSA*

Matan na zaune tare da Lado, Sani da Buba suna hira. suka ganshi kai babu rawani, da sauri yaran suka mike cike da mamaki suna yi mishi sannu da zuwa. Ko kallon su baiyi ba ya zauna cikin zafin ciwo yana fadin "Hanne kawo min ruwa"
"Malam meyasa meka a hannu?"
"Jummala! Jummala! Kar wata banza ta kuma tambayata abun da ya faru muddin nine mai gidan nan"
"To babu mai kara tambaya Malam, kayi hakuri." taja bakinta ta yi shiru tana binshi da ido.

Ruwa yasha sannan yace "wato Jummala mata matsiyata da ban suke". Banza ta yi da shi.

Cikin hassala yace" magana fa nake kuka shareni"
"Baba kayi hakuri"cewar Lado.
"Don uwar ka na saka bakinka ne a wannan maganar?"
"Yi hakuri Malam bazai kara ba" Hannatu ta fadi tana mikewa.
"Zauna ma za anan munahika kawai, za aje dak'in don ga bala'i ya dawo ko?"
"Abince zan kawo maka Malam " ta fadi ta yi hanyar dak'inta.

Abincin ta kawo mai, amma ko kallon kayan bai yi ba sai ma cewa da ya yi ta kwashe bazai ci ba. Ta kuwa kwashe a ranta tana fadin"Mun samu na karyawa da safe".

"Baba ga wannan ka sai magani, ni zan wuce sai da safe." cewar Sani ya mika mai dari biyu.
Amsa ya yi yana dariya yace "Sani dan albarka, yaro mai halin dattijai na gode sosai magaji na"
"Yauwa Baba had'ari kayi ne?" Sani ya tambaya.

"Hmm! Sani in fad'a maka matan 'yan gidan haya ne suka kassarani yau wallahi"

Kunshe dariya suka yi dukkansu, sannan yaran sukai mai sallama suka tafi. Su kuwa matan dak'i suka shige suna dariya jin mai unguwa na fadin,"wallahi ban kara zuwa gidan 'yan hawa billahillazi kuwa".


*ANYA KUWA MAI UNGUWA? MADARA KIN YARDA DA HAKAN KUWA??*

*********

*' YAN GIDAN HAYA*

Kwana biyu an samu kwanciyar hankali babu fad'a, amma ko wacce na nan da cikin yar'uwarta.

"Ke Inno jibi ranar cika ciki fa" cewar Ladidi dake wanke-wanke.

"Ayererere" Inno tasa guda, sannan ta dora da fadin"Za muga k'wanjin mazaje masu zuciyar siyan akuya, da masu cin bashi irin na waccan shekarar.

Mairon Ado ta yi tsalle ta ja gefe tana fadin "Uban mata zanci wallahi muddin ta kasa dani cikin zancenta."
"Uba fa kinka ce Mairo kawata? Ai wanga uban Baban ta shi ad dai-dai walle" suka tafa suna dariya.

Ladidi ta yi murmushi ta kama waka"_ayye nanaye wacce mijinta bai da sulalla, wazai taimaka yaji tausai, ya aiko da gashin kaza ran dadi"

Kau! aka dauketa da mari, da sauri ta dafe kuncinta tana waigen mai marin. Inna Talatu ce tsaye gabanta.

*Hmm yanzu aka soma*



*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
[3/1, 12:45 PM] Beauty Queen: βšœβšœπŸ”±πŸ”±βšœβšœπŸ”±πŸ”±βšœβšœ
*'YAN GIDAN HAYA*
πŸ”±πŸ”±βšœβšœπŸ”±πŸ”±βšœβšœπŸ”±πŸ”±

. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ’»πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ ʀɛɑɗɛʀร​.




Β©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼



Dedicated to
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*


πŸ“š ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ πŸ‘‡πŸ½
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

πŸ“© ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ πŸ‘‡πŸ½
Zamaniwriterassociation@gmail.com


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment