Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaku shiga ciki bane damuwata ai abinda yafi hakama ya dace ayi maku kufa bayi ne kuma yan wahala wulakantattu marassa 'yanci"a zahiri ko murmushi tayima Uwar nayi tace"ni kaina mulkin zalincin da akeyi a Masarautar nan ya ishe ni kuma naji dadi dana ga jajircewa da rashin tsoro a cikin idanuwan ki ta hakane kadai zan iya taimaka maku da gudun muwata,dan ganin kun kwaci hakkin ku a wajen Hamza duk da kasancewar shi Wan uwa a gareni,amma zalincin da aka aikata ga Yusrah ya taba mani zuciya kwarai da ainun!kisani ina bayan ku dari bisa dari saidai ina son duk abinda zakuyi ku dinga shawara dani zan baku goyon baya yanda ya dace."....ikon Allah ko yaushe gimbiya Masau'da tazama mai tausayi ga bayi bayan ba wadda mu kafi fuskantar matsaloli da wahalhalu a wajensa kamar ta,a iya sanin da nayi mata bata kaunar bawa tsakanin ta da bayi sai wulakantarwa da tozarwa.....gashi lokaci kankani ta sauya tanajin tausayin mu ko dai yanzun sun daina jituwa da Hamza ne shiyasa take neman yi mashi bore? kodai kawai taji tausayin mune har cikin ranta shiyasa take san ta taimake mu? A jiyar zuciya ta shide tace."mu dai indai zaki bamu hadin kai akan damuwar mu ba ruwanmu da sauyawar ki dan kema ba tabbas ke gareki ba kuma baki da gwani."dago kanta tayi tana murmushi tace."nayi nazari iya nazari dan inga da wa'anne kalmomi zan iya godewa uwar gijiya ta dasu amma na rasa.....ina rokon Allah yasaka maki da mafificin alkhairi saboda samun jajirtacciya irinki a cikin Masarautar Burhaan bakaramar nasara bane mungode da goyon bayan da kika bamu yanzun haka zanje in samu yan uwana insanar dasu komai saimu sake sabon shiri komai kenan zakijini Allah yakara maki daukaka."hmmm ai daukaka ta bai wuce ingan ni a bisa karagar mulkin Burhaan ba,a matsayin na sarauniya Masau'da ba yar Sarki Kabir Usman ba,daga lokacin shikenn burina ya gama cika in taka duk wanda naga dama a lokacin dana so......a zahiri murmushi ta kuma saki tace"Amin Mairo naji dadin addu'ar ki agareni sannan ina sauraranki dan haka kije kukara dage damtse akan kudurin mu."insha Allahu yanzun kuwa."jijina kai tayi tace."nasan idan nace ki tsaya kiyi liyafa anan baka zaki saki jikin ki da kyau ba....kinga duk wannan garabasar ta ki ce keda iyalanki a matsayinki na uwar bayi, kuma tsohuwar mai kula da sashen mijina Sarki Abduljalal,ki saka yan uwanki su kwashe muku kuje kuci kusha kafin naji amsoshin ku"Farin ciki ya dira a zuciyar Uwar bayi ganin irin kabakin da Gimbiya ta hada mata
"lallai kam bansan wane kalar farin ciki zai samu yan uwana ba idan sukaga wannan sha tara na arzikin sabida raban da inci makamancin wannan abincin tun lokacin Sarki Abduljalal nada cikakkar lafiya tabbas shidin mutumin kirki ne sai gashi kina koyi da halayen mijinki, gaskia duk wani bawa dake cikin Burhaan ya gama samun uwar daki jajirtatta kamarki muna godiya mai tarin yawa."murmushin yake kawai tayi mata."Yaro yaro ne bai san wuta ba sai ya taka ba abinda ya sauya daga cikin zuciyar Masau'da ba saima tarin manya manyan kudurai da nike dashi walahi koni kaina ina neman tsari daga kaidina,da kikema Abduljalal fatan alkhairi gwara matacce da shi sakarkaru da ku walahi saina shayar daku bakar guba,nidai fatana ku maraman baya har in gama cima burina in kawo karshen Hamza."a zahiri tace"kai Mairo ji nike kinfi kowa iya fatan alkhairi duk abinda nayi maku yiwa kaine kedai ki dauki kayan da nahada maku kije ina sauraron ku."Allah yatai maki uwar marayu,saikin jini."gyada mata kai kawai tayi cike da tausayin kalar rayuwar da zasu fuskatan ka."
Tana fita Talatu na shigowa ta zauna gabanta suka hau maida yanda akai."Hhhhh Talatu kinga uwar bayi tafita jikinta na rawa taga abin duniya wai harni take kira da uwar marayu."take ta daure fuska kamar ba ita tagama kecea da dariyar mugunta ba tace."hmm lallai kam aini saidai in karasa maraya."gaskia ne uwar gijiyata basu san dawa suke magana ba fatana ki zama Sarauniyar Burhaan komai ya dawo a kalkashin ikon ki,a lokacin zasu san wacece uwar marayu."Bassu kawai Talatu dani suke zancen."dariya suka sake cewa da ita......

JAMEEYc'þ

*SADAUKIN BURHAAN*
_(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_
A Kingdom Story=ØQÜ

*NA*
*JAMEELA JAMEEY*
_(Ya'r Mutan Kankia)_

*BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM*

_SHAFIN KYAUTA_

BABI NA TARA

Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira Wari Ukku(300)Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello. Kituro shaidar biyanki ta 08160508316.

_Shafin kyauta ya kusa karewa yar uwa hanzarta ki mallaki naki domin tafiyar ta musammance._

"Barka da war haka uwar gijiyata kiran ki ya riskeni ina fatan lafiya."?sunkuyar da kanshi yayi kasa yana sauraron abinda zatace mashi...a Wage ta kalle shi daga sama har kasa,a hankali ta mike tsaye tafara kewaye shi cike da takun kasaita tana mashi kallan kaskanci tafi minti ukku tana zagaye Sadauki kafin ta koma ta zauna saman kujera ta harde kafa Waya saman daya tana karkadata a hankali cigaba da watsa mashi wulakantaccen kallo tayi a gadarance tace"sai yanzun kirana tafara samun ka."? "Allah yaimaki yawan rai ko wancan lokacin da kiranki ya samenu bani lafiya zazzabi ne ya rufe ni shiyasa banzo ba."Kai Umar."ta daka mashi firgitatar tsawa tace."Kai har kanada wani zabin da ya wuce nawa? kai har wani 'yanci gareka da zakace saboda baka lafiya bazaka ansa kiran uwar gijiyar kaba."?kafeta da manyan idanunsa yayi masu tsananin haske da tarin kwarjini a cikin babu abinda ya tsana a duniya kamar ranin wayo."bada kai nike magana ba"ta kuma daka mashi gigitattar tsawa,ransa ne ya sosu yanda mace ke juyashi kamar wata waina son ranta dan kawai yana bawanta."Ni mizance maki tunda nafada maki uzuri na...."wani irin gigitaccen mari ta dauke Sadauki dashi zuciyar ta na tafasa,kallanta kawai yake daga sama har kasa yana al'ajabin halayen ta"harka isa ina magana kana yi! waye kai?da har gimbiya Zubaina na magana kana maida mata son ranka."? Tunda ta mari Sadauki mamaki ya kama shi koda ya kasance bawa amma bazai juri wulakanci kalar wanann ba"Allah ya huci zuciyarki Umar na tuba...bansan hakan zai bata maki rai ba ne,Allah yabaki hakuri."wawa da kai! kada kaga dan inajin nauyinka ka dinga yin abinda kaga dama a cikin Masarautar walahi tsab zan koya maka hankali! ka bude kunawan ka kaji abinda zan fada maka da kyau."wawa dakai!"abinda yake maimaitawa kenan kalmar da tayi masa girma a zuciya wai shi take kira da wawa,daurewa yayi ra hanyar danne bacin ransa yace."shikenan,ina sauraran ki"Wan uwana yazo mani da magana akan ka yana so ka kasance dashi zai saka daga cikin Jaruman Masarautar nan saboda ya baka gwaji zakuyi gasa,shine nace zan fada maka idan ka amince shikenan,amma kasani kana a kalkashin ikona, kana bukatar kasancewa da yaya Ammar."?
rasa abinda zai ce mata yayi....yasan dai zama da Yarima Ammar a wajen shi bakaramin cigaban shi bane Kasancewar yana son ya mai dashi dan uwan sa kuma yafi masa zama a kalkashin mace sannan kuma yana ganin muddin yace ma Zubaina yafi son zama dashi sai taga kamar baidamu da ita bane shiyasa kuma abinda ya fahimta ita din ta damu dashi sosai."Umar kafaman ra'ayin kan ka"dago kanshi yayi dake sadde kasa yace."Allah ya yaimaki uwar dakina banda wani zabi da ya wuce naki a matsayi na bawan ki banda wani ra'ayi ko zabi daya wuce naki."sanyayyar ajiyar zuciya ta shide wadda ba lallai ka gane tayi taba tace."Umar ada kabata mani rai saboda ni nadamu dakai kana nuna halin ko in kula akaina sannan uwa uba baka bin umurni na bayan kowa yasan tunda Zubaina take ba wanda ya taba yimata gardama ko ta taka dokarta sai.kai wannan dalilin yasa na kara jurewa har hannuna ya sauka a saman kuncin mutun mai dibin daraja a wajena banji dadin abinda ya faru ba Umar."a hankali ya dan rankwafar da kanshi sannna yace."nima banji dadin yanda naga ranki ya sosu ba ina fatan zaki yafema Umar"murmushi ta sakar masa tace."bakomai Umar yanzun zan ma yaya Ammar magana....kasani nidai bana san kana mani nisa shiyasa kaga nadamu da kai ya dace kana zuwa akai akai."shikenn gimbiya ta yanda kike so haka za'ayi."Umar ga abinci nan kadauka kaci,na fahimci kamar baka karya ba."rausayar da kanshi yayi yace."eh hakane saidai ni ban cika damuwa da karin kumallan safe ba, nagode ranki shidade"Aaa Umar in dai ka amince kana kalkashin ikona toh kaci abincin nan dan kai kadai nasa aka kawo shi."jinjina kansa yayi yace."nagode."ba haka yaso ba saboda bai son ya kara bata mata raine shiyasa yadauka ya ci kadan sannan yai mata godiya hakanan ta kyale shi gudun karta ta kura mashi amman tasan bai koshi ba yana shan ruwa ya nemi izinin tafiya so yake yaga Abban shi tunda suka tashi yau basu hadu ba."toh Umar kagaida gida."badan taso ba tabar shi ya tafi arayuwar ta idan tana tareda Umar takanji nishadi a cikin zuciyar shi nan tayi mashi izinin tafiya koda ya kusan sansanin bayi a hanya ya hadu da Yarima Ammar zuwa yayi yakai gaisuwa fuskar Ammar a sake ya amsa"ina fatan kasamu sakona a wajen gimbiyar ka"Eh Allah yakara maka girma da daukaka nasamu amma a wajen ta zakaji komai."badamuwa Umar "nagode ka huta lafiya."yana shiga dakin su ya iske Ado baidawo ba zama yayi saman tabarmar kaba,yana tuna yanda sukayi da Zubaina, wai shi zata mara gaskia ba dan tana uwar dakin shiba kuma gimbiyar Zairana da sai ya raina mata hankali,amma baida zabi tunda a kalkashin ikonta yake.....
________________
Koda Asma'u tagama shiryawa cikin wata atamfa tayi mata kyau sosai,jikinta yayi kyau jegon da takeyi ya karbeta sosai tana gama cin abincin ta sannan ta fito falo ta zauna.
Baki daya suna zaune falo gefen Halimatu ta zauna nan ta iske Shattimah yana ba Umma labarin abubuwan da suka faru dasu har saida suka zubda masu hawaye cike da tausayin halin da suka shiga,ga tausayin Sadauki daya ratsa su a take takara son Asma'u aranta da Wan Sadauki tunda Asma'u tace mata sunan shi Ahmad sunji dadi kuma nan Hajia Mansura takara yaba ma danta akan jajircewar da yayi."Allah yaimaka albarka Ahmad yanda ka taimaki matar dan uwanka kayima zumunci hidima kaima Allah yabaka wanda zaiyi maka."Amin Umma."janyo Asma'u tayi jikinta tace."Sannu ya'ta ki kwantar da hankalin ki nan ma gidane duk abinda kike so zamuyi maki kinji."toh Umma nagode Allah yakara girma."Amin."Allah ya kubutar dasu cikin halin da suke ciki Allah ya toni asirin su Hamza."amin Umma ai mutanen Burhaan ba Allah aran su."Allah ya maida masu aniyar su."amin."

Sarki Abdurrahman bai samu damar zama fa'da ba saboda ya tafi wani taron Sarakuna a kasar Kesar,saidai dan uwanshi Abdussalam.
sawa yayi aka kira mashi Ado ya yana zuwa yakai gaisuwa sannan ya akai mashi izinin zama ya zauna."Ado nakira ne domin in tambayeka akan yaron nan Umar tun ranar daya fanshi Aryan a wajen gasar nan da akayi nakasa mantawa da yaron nan a raina,wanene Umar."? "Allah yataimakeka Umar dai ba kowa bane face bawa kamar yanda kasani...na siyo shi a kasuwar gobir kamar yanda aikina yake, kuma gimbiya Zubaina ita ta bukaci in samo mata bawa jajirtacce shiyasa na shiga filin da'ga har aka saidamin shi,wannan shine abinda nasani gami da rayuwar Umar."gaskia ne Ado baza'a kira Umar a bawa ba ni kaina nayi zaton ko Wan dan uwanka ne bacin da hakan ya bayyana a tattare dashi,saidai kana ganin Umar baida wata illa kuma zaici gaba da yima yar mu hidima."? "Eh ranka shidade,Umar mutumin kirki ne kuma bai cika damuwa da harkar kowa ba hidimarsa kawai yakeyi."tabbas Umar ya cika Jarumi zaka iya tafiya"toh ranka shidade katashi lafiya Allah yakara maka nasara"Amin."sarkin zagi ya amsa.

*Ku hanzarta ku mallaki naku domin wannan tafiyar ta dabance,na tabbata bazakuyi dana sanin siyen sa ba,kunji salon Izzah ko Mulki to yanzun wasan zai soma domin ba'ayi komai ba,kedai ki kasance da Jamila yar mutan kankia*=Ø
Þ

*BURHAAN*
"Ke uwar me kikeyi nan? nafahimci kune masu yimana lekan asiri ko?ku ke fidda mana sirrika a waje ko? yau kashin ku ya bushe."jikinta na rawa ta zube kasa."Allah yataimakeki kimin aikin rai walahi bada wata manufa mukazo nan ba tsautsayi ne ya giftama hanya ne ta biyo damu tana shiyasa,kiyi mana aikin rai"kuyi mani shiru munafukan banza munafukan wofi,yau dinnan sai kun kwashi kashinku a hannu."muntuba kimana aikin rai tsautsayi ne ya biyo damu tanan bamu san an hana bi tanan din ba."Maimuna maza kije ki kiramani Darwami ya koya masu hankali."angama uwar gijiyata Allah yabaki nasara."Goggo ni nasan halin wa'annan mutanen kingan su nan suna bayan Mardiyyah shiyasa suka kara zama munafukan gaske"yau din nan saina koya masu dasari daganan bazasu sake munafurci ba."suko duk sungama tsorata da lamarin gimbiya Saude sun san ba imani garesu ba,danko Jummai da ladidi saidai ido suke ranawa dan sun san bazasu ragama suba ko kadan kasancewar su hadiman gimbiya Mardiyah.....
Koda darwami yazo ba irin wulakanci da bai masuba ga dukan su yanayi kamar wasu jakuna hatta gimbiya Safiyya saida ta tausaya masu, dan tasan cutar da akeyi a cikin Burhaan ya wuce misali,amma dole mutun yasaka ido koda suka gama dakuwa sawa tayi suka dinga shara da debe ciyawu kullin sai darwami yai masu bulala talatin.
Sarki Abduljalal ne kwance,zuwa yanzun ciwon shi ya wuce misali sauki sai wajen Allah yanzun ko furar da yake samu yasha ada ta gagareshi,shi kanshi Saminu zuwa yanzun ya fara fidda rai da samun Mai martaba,yauma haka ya tashi da amai yana ta suma duk ya gama galaibaita amma kaf Burhaan daga Saminu sai su ladidi su kadai keba Mai martaba kulawa,wannan kenan

Galadima Hamza tareda kaninsa Abdullahi suna tattaunawa."Abdullahi ya dace ace zuwa yanzun Abduljalal ya mutu yaka mata ace kowa ya manta dashi a cikin Masarautar nan....kuma ga kalubalen daje fuskantar mu a kowane lokaci ga Masau'da na kulamana munafunci da sharri kullin so take ta yaWa maa da'na sharri a wajen manya manyan kasar nan,dan ya tabamani darajar mulki na,yanzun mikake ganin yakama ayima muguwar matar nan."? Shiru Abdullahi yayi yana sauraron dan uwan nashi aransa yana ayyana abubuwa da yawa."Hmm Hamza kenan!koda kasamu duniyar ka hatta ni da muke takamar cikin mu daya mantawa kayi dani sai yanzun zaka nemi shawarata wato so kake na baka goyon baya ka kara mantawa dani walahi bata yuyuwa ni kaina sai inda karfina ya kare bazan zauna ba wankin hula ya kaini dare ba idan har akayimin ban rama ba,lallai kam da ban haihu ba" dan murmushi ya kakaro a saman fuskar shi yace."Allah yataimake ka ni kaina lamarin nan yana bani mamaki ainun.....narasa abinda zan fada komai ya cakude yanzun dai ya kamata muje wajen Goggo nasan ita zata samar mana da mafita"Shikenan Wan uwana haka za'ayi."Hmm sai yanzun kasan ni Wan uwan ka ne amma da kasamu duniya saika manta dani daga kai sai matarka da ya'yanka ko Goggon baka damu da ita ba!ai Masau'da tafika gaskia kaci amanarta ne shiyasa zata rama abinda kai mata"yanzun tashi muje muji yanda zamuyi akan wannan matsalar da muke fuskanta."mikewa Abdullahi yayi suka tafi wajen mahaifiyar su.

&&&
Gimbiya Saratu zaune a sashen ita da bokarta sunata sihirin su daman aikin su kenan sun riga da sun saba da kulle kullen su na tsafe tsafe....suna cikin hada kullaliyar su saiga mai kulawa da bangaren ta ya shigo yafada mata tayi bako,tace ya shigo da shi bayan sun shigo ya basu waje...cikeda mutuntuwa Wan aiken nan ya bata takarda yace."daga Masarautar Burhaan gimbiya Masau'da ta aiko ni."madallah."ta amsa cike da murna da tarin farin ciki tana shirin ganin kalar albashir din da yarta ta aiko mata dashi,nan tasa aka bashi masauki ya huta kafin zuwa gobe....bakaramin dadi yaji ba,nan gimbiya Saratu ta bude takardar yarta cike da zumudi tafara karantawa...

_Bayan gaisuwa mai tarin yawa dafatan kina lafiya...Umma kamar yanda kika sani kinbar Masarautar Burhaan da tarin nasarori dayawa amma yanzun nasamu damuwa kamar bani a kowa banbancina da baiwa kadan ne! galadima Hamza yazama Sarkin Burhaan saidai shi kadai yake cin karan shi ba babbaka sai kuma uwar shi,ya manta dani kwata kwata...koda nayi mashi magana har marina saida yayi ya wulakanta nu har yana ikirarin sai ya ga bayana zai kashe ni yanzun haka komai na Burhaan ya katantane banda bakin zalinci ba abinda ya aje har ni bai kyaleba nazama abin tausayi na shiga damuwa marar misaltuwa umma,dan Allah kitaimaka mani ina bukatar agajin ki dake na dogara...inafatan zaki kasance cikin aminci bissalam daga yarki Masau'da Kabir Usman Burhaan_

Zazzafar ajiyar zuciya
gimbiya Saratu ta sauke ta gama duba wasikar yarta bakaramin tashin hankali ta shiga ba da tsananin fargaba zufa je tsatsifo mata tana sharcewa ranta a dagule ta kalli bokanyar ta tace"lallai kam Hamza ya tabowa kansa fitinar duniya ni za'aima dibar albarka da raina za'a wofintar mani da ya'ta! Hamzan banza Hamzan wofi!yoni inda ace Masau'da da tasha nonona batayi tunbiWi ba ita kadai zata iyayin maganin karamin Wan iskan nan,wato nagama yimasu wahala shine zasu manta mani da yar diyar tawa gefe ko?sucigaba da cin karan su ba babbaka,walahi muddin na haihu sai na maida Hamza ya zama abin tausayi a cikin Burhaan sayayi dana sanun cin amanar ya'ta da yayi....ita kanta Saude saina bata mamaki sai sunsan suna magana da gimbiya Saratu Sarauniyar Yurii ya zama dole ya'ta sai tazama Sarauniyar Burhaan komai rintsi komai wuya koda zan rasa raina."kwarai kuwa gimbiyata umurnin ki kawai nike jira."ba saina tsaya yimaki bayanin komaj ba ina san kiyi gaggawar hada mani da asirrai zanba wannan bawan yakaima ya'ta bazai bar Masarautar nan ba sai mun hada mashi manyan asirran da za'a kai ma Masau'da sai mun ladabtar da wa'annan matsiya tan mutanen maza kifara aikin ki."Angama sarauniya ta yanzun kuwa,me kikeso ai mashi kisa ko a haukatar da shi? ya susuce yanda daya tunkari karagar mulki zata dinga bashi tsoro har sai ya'ta ta mulki Burhaan yanada ranshi da hankalin shi, kinga karshe bakin ciki da takaici su zasuyi ajalin shi...kinga in mukace za'a haukata shi ko kashe shi ai bamu more masa ba saboda baisan Masau'da ta zama Sarauniya ba,amma idan yagani da idan shi kinga mun cika burin mu."dariya suka sheke dashi tace."mu keyi amma mu kejin tsoran ku kina wuta yanda ya kamata a gujeku sarauniya Saratu yanda kike so haka za'ayi."cigaba da aikin ki nasan zakigama komai da wuri"umurin ki abin tunkaho agareni angaishe da sarauniyar Yurii uwar gida ga Sarki Kabir Usman an buga dake anbarki Allah yataimake ki."Jinjina kanta tayi tabajin dadin kirarin da bokatar keyi mata.

JAMEELA JAMEEYc'þ


Share
Saboda Allah

*SADAUKIN BURHAAN*
_(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_
A Kingdom Story=ØQÜ

*NA*
*JAMEELA JAMEEY*
_(Ya'r Mutan Kankia)_

*BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM*

_SHAFIN KYAUTA_

BABI NA GOMA

Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira Wari Ukku(300) Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.ku tura shaidar biyan ki ta wannan lamba 08160508316.

Tankameman waje ne daya gaji da tsaruwa da ado ba abinda babu a wajen yasha kayan alatu na more rayuwar yau da kullun Sarakuna ne cikeda wajen cikin babban dakin taron Masarautar Kesar kowa ya zauna suna tattaunawa akan wasan da za'a gabatar a watan gobe inda za'a saka gasa a tsakanin Masarautun Nahiyar baki daya.
Sarkin Kesar ya kara yima Sarakuna godiya mai yawa yanda suka karbi takarda gayyatar da yayi masu sannan aka zabi kasar shi a inda suka gabatar da zaman ya cigaba da cewa."kamar yanda kowa ya sani an tsaida inda za'a gabatar da wannan muhimmin wasan idan Allah yasamu cikin rayayyu za'a gabatar dashi cikin Masarautar SIRIKA saidai nayi mamakin rashin ganin Sarki Abduljalal duk da kasancewar Sarkin Sarakuna kuma uba agaremu ya kamata ace idan irin wannan taron yatashi ya dinga zuwa ko ya aiko da wakilin shi,kuma zanyi anfani da wannan damar wajen kara mika godiyata ga Masarautar Burhaan yanda suke ba da taimako ga kasashe daban daban...
zamu tsaida lokacin da zamu kaima wannan adalin Sarkin ziyarar bazata bayan angama gabatar da gasar da za'a gabatar bada jimawa ba."kowane Sarki yayi amanna da maganganun Sarkin Kesar din sannan sun kara goya masa baya akan ziyarar da zasu kai Masarautar Burhaan din."gaskia ne munji dadin maganganun ka Allah ya muna mana lokaci lafiya kodan yanda Abduljalal ke daukar gabata da taimakon al'umma ya cancanci ayi mashi ziyarar ba zata domin mu gaida shi mun tabbata zamu samu karamci sosai kuma zaiji dadin ziyarar da zamu kawo mashi."cewar Sarki Abdulwahab.
Sarki Abdullatib(Sarkin Sirika)ke tambayar Sarki Abdurrahman maganar yar shi gimbiya Zubaina."nasamu labarin tayi aure banji dadi da baku gayyaci Masarauta ta ba."Sarki Abdurrahman yace."ban kyauta ba saidai ina maka albishir...wannan wasan da za'ayi da ya'ta Zubaina zanzo yanda kowa zai ganta kuma ai kaga Masarautar ka nan za'ayi wasan kaga sai takara sanin iyayen nata sosai"da naji dadi Allah yakaimu lafiya."Amin." bayan sun gama gabatar da muhimmin zaman da sukayi suncima matsaya suna gamawa kowa ya koma masaukin shi abin yayi tsari sosai.bayan Sarki Abdurrahman yakoma masaukin shi yagama kimtsawa zai kwanta aka sanar masa da isowar Sarkin Sirika,bayan ya amsa mashi sallamar da yayi mashi ya samu waje ya zauna suka kara gaisawa"nasan zakayi mamakin sake ganina bangaren ka"hakane amma nasan koma minene yanada matukar mahimmanci."kwarai kuwa akan maganar Sarkin Burhaan ne gaskia yaka mata ace wannan wasan da za'ayi ya halarce shi sannan yazo mana Jaruman shi,musamman Sadauki muna bukatar ganin shi."Murmushi Sarki Abdurrahman yayi."ni kaina zanso inga wannan yaro badan komai....saboda inada labarin Jarumta da jajircewa irin ta yaron nan."gaskia ne."ajiyar zuciya marar sauti Sarki Abdurrahman ya saukar yace."Kwanaki na gayya ce su zuwa Zairana wasan daba kuma sunzo saidai banda Sadauki kasancewar bai jima dayin aure ba."shiru Sarkin Sirika yayi yana sauraron Sarkin Zairana(ikon Allah....yanda ya'ta Rahama ta sussuce akan son Yarima Sadauki ace yayi aure ban saniba ya zanyi yanzun? ya'ta daya tilo ace zata rasa abinda take so shekara da shekaru tabbas akwai damuwa."a zuci yake sakesaken sa....maganar Sarki Abdurrahman ta katse mashi sakar zucin da yakeyi."Ashe Sadauki yay aurei."? "ya jima da aure shiyasa ma bai samu damar zuwa ba,amma nasan wannan karon mahaifin shi zai turo shi,ni kaina yaron nan yai mani Allah yai mashi haiba da tarin farin jini,kuma yayi suna a ko ina"Allah yakaimu lokaci lafiya nima zanso in sansa a zahiri kamar yanda na kiyaye sunan shi.."murmusawa Sarkin Sirika yayi.sannan sukaima juna sallama ya koma masaukin shi.
Koda asuba tayi kowa ya gama shiryawa sannan sukaima juna sallama....kowa yayi zummar komawa Masarautar sa,suka rabu cikeda kewar junan su....cikin ikon Allah lokacin da biyar din yamma tayi Sarki Abdurrahman ya dawo gida bakaramar murnar dawowar shi akeyi ba abin ba acewa komai kwana biyu kadai da yayi baya nan ji suke kamar yayi shekara bai nan,suna jin dadin Sarkin nasu,su Ammar sukazo yima mahaifin su barka da wowa,sun jima a turakar sa suna fira irin ta uba da ya'yan sa ana kiran sallah kowa ya tafi masallaci domin yin sallah.
______________
Iso yasa akayi mashi har cikin turakar gimbiya Zubaina tana zaune ta gama sallah tana karatun alqurani mai girma saiga Fadila tazo ta zube gefenta har saida takai aya sannan fadamata zuwan Yarima Ammar,a zahiri tayi mamakin zuwan shi duk da ba yau yafara kawo mata ziyara na amma saita ce ya shigo yana shigowa ya zauna akan kujera,ta gaishe da yayan nata cikeda girmamawa ya amsa cike da sakin fuska..."kinsan ance mai nema baya taba fushi....dama akan maganar da mukayi da ke shine nazo inji amsarki."hakane yayana nima nayi magana da Umar shima ya nuna mani gamsuwar hakan saidai gaskia ina son Umar ya kasance a wajena....saidai kamar yanda zakuyi gasa kuma naga kunasan zaku tafi dashi na amince da hakan,saidai ina bukatar aiki da Umar."shikenan mungode saidai naso ace baki daya Umar ya dawo kalkashin ikona bansan in ganshi yana hidima amatsyin bawa kyanshi ya kasance a cikin manayan Jaruman Zairana"sihirtacciyar ajiyar zuciya ya sauke yace."kayi hakuri gaskia zama da Umar kadai yasa naga kyawawan dabi'u attatare da shi kuma nakara samun ilimi daidai gwargwado nasan zaka fahimce ni"ba damuwa zanyi nazari akai....saidai kisa aranki daganan har sai mundawo GASA sannan zaki ga Umar,saboda muna

Please Login or Register in order to submit comment