Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maida kudi gida.*

_________________
Ba abinda sukeyi sai gyaran wajen dawakai suna gamawa sukaci gaba da basu ruwan sha.
Du abin nan Yarima Aryan na tsaye sai kallan Sadauki yakeyi suna hada ido ya kira shi baki daya jikin Sadauki yayi sanyi shidai baisan wani abu na hada shi da masu mulki koda kuwa aike ne, koda yaje hannun shi Aryan ya rike suka tafi wajen wata katuwar baranda ya samu kujera ya zauna shiko kasa ya duka,duk da Aryan ya bashi izinin zama asaman kujera amma yaki zama tunda ya tuna da hudubar uban gidan shi Abba Ado yace karya kuskura ya dinga hada kafada da kafada da ya'yan Sarakai ya dinga basu girma,da wannan dalilin yasa Sadauki yaki zama saman kujera."Allah yataimakeka ba girmana bane ace kana dan Sarki kuma yarima in zauna kujerar daka zauna,kayi hakuri nan ma ya isheni."na fahimta amma duk daya muke kaima mutun ne kamar ni kila kafini daraja awajen Allah a zahiri kuma ka fini komai dandai kazo a bawa....kozan iya sanin sunan malamin.?"Sunana Umar."murmushi Aryan yayi yace."Masha Allah Umar amma kai bako ne ko."? "Eh bandaWe da zuwa ba"Ayyah bantaba ganinka ba sai yau,amma wakake ma hidima."? "Gimbiya Zubaina."yace cikeda kosawa."kai ikon Allah a iyasanina kanwata bata son maza nayi nata hidima saidai yan uwanta mata amma miyasa ta dauki Umar a matsayin hidiminta?a ransa yake wannan sakar zucin."wane kalan aiki kakema mata?"Ina mata wanki sai kuma tace zan kasance daga cikin masu gadin ta."bakaramin mamaki yake ba Zubaina da ko kayan ta bataso taga wani namiji ya taba, tsabar tsanar da tayima namiji amma wai harta kai da daukar Umar a matsyin mai mata wanki gaskia lamarin akwai ban alajabi da yawa."
"badamuwa Umar zan nemeka,ni kuma sunana Yarima Aryan nayi farin cikin haduwa da kai da fatan zaka rikeni amatsayin uban gida kuma abokin ka."Umar nagodiya Allah yakara girma da daukaka."Amin Umar gaskia ka shiga raina bai dace ace kazo a bawa ba."hmm nima haka na tsinci kaina."murmushi ya saki sai kuma yace"haka Allah yaso ganina mai gidana,zan koma bakin aikina sai wani lokaci."gyada masa kai kawai yayi.tunda Umar ya juya yana tafiya Aryan ke mamakin kalar tafiyar Umar a nutse yakeyinta sai kace mai tausayin taka kasa ga tsantsar kasaita gamida izzar da ta game mashi jinin jiki yana mamakin kalr kyawun Umar kuma duk da yana wahala baka cewa BAWA NE shi.....

Sarki Abdurrahman ne zaune a Fa'da anata fadanci kowa na fadin albarkacin bakin shi, yaune ake wasan INDAR da marece banyan la'asar tunda aka tashi bayi keta aiki anata gyara filin wasa ga kujeru anjere abin gwanin ban shi a'awa yau kwanan su Zubaina biyu da dawowa amma bata saka Umar a idanunta ba,bakaramin takura tayi ba,amman ta dake tana son ta dinga nisanta kanta da Umar gudun kar yashiga ranta da yawa,saboda ta fahimci bai cika shegema jama'a ba....
har lokacin wasa yayi inda gimbiya Zubaina tasha ado iya ado kamar wata sarauniyar kyau,baiwarta Fadila ta saka mata jar alkabba bisa kayanta ba karamin kyau tayi ba ita kanta tasan tayi kyau sosai.
tafiya takeyi kamar wadda kwai ya fashemawa a ciki ga wata irin kasaita da take ji a tattare da ita duk inda gimbiya Zubaina ta gifta sai an kalleta tsabar haduwar da tayi wajen bayi daban hakama na masu mukami.
ga wani irin kamshi tana bazawa,hatta sarki Abdurrahman saida ya yaba da kyawun yar sa,cikin kankanin lokaci hadimai sun kara gyara wajen zaman gimbiya Zubaina koda ta zauna kallanta ya koma kan bayi duk wanda ta hada ido dashi saiya sadda kanshi kasa baki daya hankalinta nakan nemansa saida bata gan shi baifi minti biyarba a fara wasa.....
ba tunanin da takeyi sai Umar ita kanta tana mamakin yanda akai Umar bai san mutane shi ba wani ba balle ya dinga bin ra'ayin kan shi,can ta hangi Yarima Ammar da yan tawagar shi sun taho cikin filin kauda kanta kawai tayi can ta dago kai karaf taga Umar bayan Ammar bakaramin mamaki tayiba miy ahada Umar da yaya Ammar? Ta tambayi kanta koda suka hada ido dashi mulmushi kawai yayi mata ya dauke kai bai karabi ta kanta ba....
su Ammar na zama yakama hanya zai tafi wajen bayi amma Ammar ya hana shi tafiya zama yayi daga gefen su.
bakaramin bakin ciki ne ya kama idris ba abokin Ammar ne wasa yazoyi tunda yaga Zubaina yaji bala'in sonta ya shige shi,yana haduwa da Umar yaga kyawun da Allah yaima shi sai ya fara jin haushin shi ko kadan baisan yaga Umar na rabar Ammar dan ya fahimci Ammar ya ba Umar mahimmanci....
duk abinda ake baki daya hankalin idriss nakan Zubaina ita kuma Umar kawai take kallo koda idriss ya fahimci Zubaina ta damu da Umar take yakara tsanar Umar jiyake kamar ya halaka shi ya huta,batare da bata lokaci ba aka fara wasa sai kiran Jarumai akeyi gasa ake sawa na kudi sai ku hada hannun aga wamda za'akai hannun shi kasa muddin kaci sai abaka kyauta, baki daya wasan yaima Sadauki dadi sai murmushi yakeyi idan gimbiya Zubaina ta saki kyalle za'a fara wasa haka akaitayi inda Ammar yazo ya kara da abokin gasar tashi cikin kankanin lokaci Ammar yaci baki daya wajen ihun murna sukeyi,shima Sadauki jiyayi kamar anbashi kyauta ganin Ammar yaci...
Itako Zubaina mamaki takeyi ganin Umar na murna Ammar yaci wasa.....Can aka kira Yarima Aryan saidai ba amo ba labarin shi ganin bai zoba hakan yasa Ammar yacema Sadauki ya wakilci Aryan,faduwar gaba ta samu Sadauki wasu naganin duk Jaruman dake Zairana a rasa wanda zaisa wakilci Yarima Aryan sai BAWA bawan ma Umar wanda bai san yanda tsaretsaren Masarautar Zairana yakeba?ko cikin bayin ma wasu bakin ciki sukeyi ace daga zuwan Umar har darajar shi ta Wagu da yawa ace yarima Ammar yasan da zaman shi......
Ko Sarki Abdurrahman bai taba ganin Sadauki ba sai lokacin da Ammar yace shine zai wakilci Aryan amma saida ya yaba da kalar kyawun Sadauki a zuciyar shi, wanda saida ya bayyana a zahiri,Sadauki baiyi auneba yaji mai kiran sunayen yan wasa yana kiran UMAR ADAM ba karamin mamaki yayi ba, da har aka ambaci sunan shi,yana kallan wajen bayi yaga Abba Ado na kara karfafa mashi guiwa.....
Cikeda da izzah wadda shi kanshi bai masan yanayin taba ya mike yafara takunsa na kasaita wanda yakeyi lokacin da yake amsa sunansa na Sadaukin Burhaan takun da ya zame masa jinin jikinsa kamar halittarsa ce a haka....hatta Sarki Abdurrahman yayi mamakin ganin yanda Umar yake tafiya sai kace wani Sarki ko dan Sarki.....takun dako masu Sarautar da yawan su sai ankoya masu shi!
Da haka ya tafi cikeda nutsuwa a gaban gimbiya Zubaina kallan shi kawai takeyi amma yaki kallanta,saida ta kira sunan shi sannan ya kalleta."Fatan alkhairi Umar."murmushi kawai yayi mata abokin wasan shi na isowa ya kalli Sadauki a kaskance ganin yana bawa,batare da bata lokaci ba akafara wasa....
tunda idriss ya rike hannun Sadauki da gayya daman mugun haushin shi yakeji aka fara karawa da Sadauki shiko ya dauki abin wasa tunda yaga yanda idriss yama yi mashi mugunta cikeda gayya,shima ya kara damkar hannun idriss wani irin masifaffan karfine yazoma Sadauki atake,saida yayi kamar zai karya idriss ba arziki idriss ya buga uwar kara sannan hannun shi yafadi kasa wanwar, bakaramin ihu ya kaure wajen ba hatta Mai martaba saida ya mike tsaye danko gimbiya Zubaina saida ta saki ihun murna,duk wanda ke wajen ita yake kallo hatta Umar din zuwa yayi ya kwashi gaisuwa gun Mai martaba,kallan shi kawai Sarki Abdurrahman keyi yana mamakin samun jajirtaccen bawa kamar Umar a cikin Zairana, gashi da cikar halitta sam bai cancanci ace yazo a bawa ba....haka ya gama kai gaisuwa, daga karshe yaje wajen Zubaina sai murmushi takeyi mashi tanajin dadi a ranta sannan ta bashi kudi masu yawa nan."ina tayaka murna Umar."jinjina kansa kawai yayi kamar bada shi take ba,daga karshe ya koma wajen Ammar baki daya wajen nan sai murna akeyi yana zuwa ya mikama Ammar kyautar da ya samu yace."ka rike ka nemi Yarima Aryan ka bashi."yabo na musamman yasamu a wajen Ammar shiko idriss duk jiki ya mutu, hada hannu kadai da sukayi saida yaji haduwa da Umar ba dadi....
hidimar shi kawai Umar keyi,bakaramin mamaki bane ya kama Ammar ba yana mamakin anya Umar ainahin bawa ne? yana kokoton haka a zuciyar shi,bayan waje ya lafa Mai martaba yasake gabatar masu da kyautuka hadda wa'anda suka fadi duk anbasu kyauta,nan aka sha shagali amma ba komai Sadauki ke ciba,duk abin nan idanun Zubaina na kansa tana ganin yanda bayi keta wawa,amman Umar sai yagunar abinci yakeyi kadan yaci taga ya aje abincin yasha ruwa, ya tashi yai tafiyar zai kaima Yarima Aryan sako....

_Yar Mutan Kankia cec'þ_


Share
Pls

*SADAUKIN BURHAAN*
_(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_
A Kingdom Story=ØQÜ

*NA*
*JAMEELA JAMEEY*
_(Ya'r Mutan Kankia)_

*BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM*

_SHAFIN KYAUTA_

BABI NA TAKWAS

Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira Wari Ukku(300) Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.ki turo shaidar biyanki ta wannan number 08160508316.

Koda akaima Sadauki iso ba inda suka wuce sai wajen hutawar Aryan yana ganin shi yafadada annurun fuskar sa yai mashi maraba,dukawa yayi ya gaida Aryan cikeda girmamawa yayin da Wan shiru ya biyo baya ya karade illahirin wajen."Allah yataimake ka sakone na kawo maka."kallon mamaki yake bin Umar dashi kafin ya amsa ya tambaye shi."waye ya wakilci ni."?dan shiru Sadauki yayi sannan yace."Ni ne"har yanzun bai gama mamakin kalar Jarumtar shi ha yace."Kace muna tareda babban Jarumi a cikin Masarautar tamu yanzun harka iya karawa da idriss dole a yaba maka Umar,gaskia zanso in kasance tareda kai."sadda kansa yayi kasa sosai a hankali ya dago kansa yace."Allah yataimake ka ina godiya,lallai da hakan yamin dadi domin ba karamin girmamawa bane agare ni"yaji dadin kalamann sa yace."Umar haka nan naji kayi mani araina zanso ka kasance a kalkashin ikona,koba komai gaka Jarumi kuma kalar rayuwar ka na burgeni idan kana abu kamar ba bawa ba"Allah yabaka nasara,karka kasa na manta kaina, nidai nasan bawa ne, zanso kabar ni amatsayina,saboda inajin dadin hakan sosai."Umar kenan,bazan takura maka ba,amma zanso kadawo a kalkashina"dan murmushi Sadauki yayi ya kuma sauke kansa kasa cikeda girmmawa yace."godiya nikeyi Allah yakara maka girma,saidai banda iko da kaina,kasani Umar bawan gimbiya Zubaina ne."kafadi gaskia zan nemi alfarma a wajen uwar dakin ka."Allah yakara maka lafiya nagode."kanada girmama mutane,naji dadin kasancewa dakai dahar ka wakilceni....daman ciwon ciki ya rikeni shiyasa ban samu naje wajen wasaba,saidai kwara da ban zoba,gashi babban Jarumin Jarumai ya wakilceni."ranka shidade sa'ar Allah ne kawai tasa muka kai wannan matsayi....Umar bai san komai ba sai tarin bauta,a wajen Jarumta bai san taba"nafahimci baka son ana yaba maka Allah haka kake ba kodaka nike ba"baice komai ba sai murmushin da ya kuma yi.dan shiru ya kuma gauraye wajen a hankali Sadauki ya yunkura zai tashi yace."zan koma mai gida ka huta lafiya."Umar."
Sake juyo yayi ya tsaya."rike wannan kyautar kaje kadinga anfani da kudin kaji? idan kana bukatar wani abun kaimani magana"Allah yataimakeka ina Umar da rike manyan kudadade irin wa'annan?karufaman asiri."abinda yafi haka ma zan maka kuma bana san godiya haka nike wannan yana cikin sharuddana zaka iya tafiya."Allah yakara maka girma da daukaka ka huta cikin aminci."yana komawa yabama Abba Ado kyautar sai murna yakeyi sun rasa yanda zasuyi da kudin da aka basu,nan Abba Ado ya aje kudin akasan kayan su haka suka dinga kashe kudin kadan kadan suna hidindimun su na yau da gibe.
suna cikin jin dadin su sai ga aike daga wajen gimbiya Zubaina,baisan dalilin dayasa gaban shi ya fadiba, kamar ba zaije ba sai kuma yace gashi nan zuwa.....

&&&
Akwana atashi asarar mai rai su Shattimah har sun shigo kasar Niger suka kama hanyar zuwa Damagaran.
ita dai Asma'u mamaki takeyi baki daya tafiyan da sukeyi tayi zatan Chadi zai kaita wajen Alhajin Roowan amma sai taga sun kama hanyar damagaram,basu suka shigo Damagaram ba sai bayan la'asar sakaliya kai tsaye wani irin katafaran gida suka tunkara kallo daya zakaima gidan kasan ankashe mashi kudadi ya gaji da tsaruwa anyi gininsa da tsakuwowi sai jan gargari mai daukar hankalin mai kallo...koda mai gadin gidan yan hangosu da sauri ya kara so cikin farin ciki da jin dadi ya taresu har cikin gidan suka shiga yana ma uban gidan shi maraba da hanya sannan yaima Asma'u barka da zuwa nan suka shiga ciki wani irin katan falo ne ba kowa a cikin shi,wajen yaba Asma'u ta zauna sannan yabi wata hanya ya shiga wani daki yana isa yayi sallama matar dake saman darduma ta dago kanta cike da farin ciki da saurinta ta rungume shi har kukan dadi saida tayi."Ahmad sai yanzun kadawo?"haba Umma na miyasa zaki tada hankalin ki bayan kinsan ina cikin aminci."a hakan zakace kana lafiya kaga yanda karame kuwa mike damunka."? "Umma ai rama bashi ke nuna mutun bai cikin kwanciyar hankali ba."hmm wai Wan dana haifa da cikina shine zai mani wayo da dubara"murmushi ya saki saman yalwatattar fuskar sa yace."umma ta kibar damuw kisama danki albarka."shikenn Ahmad Allah yaima ka albarka"Ameen Umma na....daman ina tafe da babbar bakuwa tana falo"kallan mamaki tayi masa tace."Allah ya shiryeka Ahmad,shine kabari muka zauna nan muna ta fira gaskia baka kyauta ba"umma hakuri zakiyi"wacece."?"yanzun dai muje zaki ganema idanun ki,tashi mutafi." riko hannun mahaifiyar shi yayi suka fito falo itako Asma'u ta sunkuyar da kanta kasa koda taji maganar su sun takora kasa dagowa tayi har saida suka zauna."Kallanta kawai Hajia Mansura keyi saidai bata ga fuskarta ba."ya'ta barka da zuwa,ya hanya."sai a lokacin Asma'u ta dago kanta sukayi arba da Umman Shattimah saida taji faduwar gaba ta dirar mata a cikin zuciyar ta"wai dama Shattimah wajen Umman shi ya kawoni! A zuci Asma'u take maganar...da sauri Hajia Mansura ta mike ta rungume Asma'u cikin tsananin farin ciki da jin dadi"ya'ta daman kice bakuwar da yake fada? yanzun Ahmad diyar yar' uwata ce bakuwa"?murmushi kawai Shattimah yaima mahaifiyar tasa,kallan su kawai takeyi cikeda tuhuma da neman sanin dalilin dayasa sukazo ba wannan ke dagama Hajia Mansura hankali ba yanda taga ya'yan nata sun rame."Dan Allah kufada mani miyasame ku duk kun yi baki kun rame."ita dai Asma'u kuka takeyi abin gwanin ban tausayi."inalillahi ashe harda jikana akazo." ta anshi Wan Asma'u dake goyo a saman bayanta."Allah mai girma daka ganshi kaga mahaifin shi yayi kama da Muhammadu kwabo da kwabo."Asma'u fada mani damuwar ku da ganin ku ba lafiya,kufadaman miyafaru."? Shattimah yai saurin taren zancen ta da cewa"Umma kibari anjima zan sanar maki komai yanzun ya kamata ta huta tayi wanka taci abinci zakiji duk abubuwan da suka faru anjima kadan yanzun abata dakin ta."Aaa Ahmad bazan ware mata daki daban ba tareda Halimatu zasu dunga kwana dan ta dinga debe mata kewa tana kulman da jikana bazan yarda ya'ta tayi nisa dani ba."Shikenan Umma,amma ai naji gidan shiru ina Ummin ta tafi."? "ta tafi islamiya,su kuma Jameel da Kamal sun hau dawakai suntafi gwaji daga ni sai ma'aikata da mai gadi."Ayyah Ummana sun barmi ke ba kowa,Abba fa."?"shi kuma ya tafi Kasar Chadi zai gana da yan kasuwa jibi zai dawo"Allah Sarki Umma na shine zasu barmin ke cikin kewa."?murmushi ta sakar ma Wan nata tace."ai yanzun duk ta kewa ya kare tunda ga ya'ta tazo ga kuma jikana sun isheni komai...tashi muje daki kiyi wanka ki shirya kinji yar albarta."Umma shine ni bazaki ce naje na shirya nayi wankan ba,shine zaki dauke yar ki ki barni."? A sifar zolaya yayi maganar sai a lokacin Asma'u tace."yaya kenan,kodai ka fara kishi ne?banda abunka ana yayin sabo wake ta tsoho"faWa mashi dai diya ta."shikenan naji nasan dai ba'a canzama tuwo suna"dariya sukayi baki dayan su cikeda nishadi."dan nema baka gajiya da rigima Ahmadu."dakinsa ya nufa yana dariya suma suka shiga daki.

Sadaukin Burhaan na kudi ne akan farashi mai sauki hanzarta ki mallaki naki domin karin bayani tuntubi wannan number din 08160508316.
_______________
"Yawwa kanwata daman ina son zanyi magana dake."a hankali ta dago kanta ta kaida dukkan hankalinta wajen shi tace."ina jinka."yau naga wani BAWA dana tambaye shi wa yakema hifima sai yace akalkashin ikon ki yake,saidai nayi mamakin jin hakan daga gareshi saidai miyasa kika Wauki namiji a matsayin hadimin ki"? sadda kanta tayi tadan saci kallan mahaifiyar dake aikin kallanta suna son suji amsar da zata basu"Umar mutumin kirki ne kuma yana da jajircewa wajen hidima shiyasa nace ya dinga yimin aiki kuma nasan zai dinga kulawa da al'amura na."gyada kai Gimbiya Amina tayi tace."hakane....saidai Mai martaba yace bai san da zuwan Umar a cikin Masarautar nan ba shiyasa nace ki nisanta kanki dashi har sai an aminta da kalar halayensa sannan za'aci gaba da mu'ammala da shi."da sauri Zubaina ta dago kanta ta kalli mahaifiyar ta tace."Umma walahi Umar baida wata matsala ki aminta dani."kinga Zubaina bai kamata ki dinga fadar abinda bakida ilimi akan sa ba bakisan waye wannan Umar din ba."shiru Zubaina tayi....Ammar ne yace"Kanwata yana ga kamar bakijin dadi duk yanayin ki ya sauya kodai bakiji dadin zancen bane."?girgiza kanta tayi a hankaki tace."kawai bana jin dadi ne"Ayyah sannu kinji autar Umma ya kamata ki huta dagani har yanzun gajiyar da kuka kwaso bata sake kiba."shikenan zanyi yand kake so"yawwa kanwata,saidai ina neman wata alfarma a wajen ki"alfarma kuma"?ta tambaya dan gasgata abinda yake fada"Kwarai kuwa"wace alfarma ce."inasan ki bani Umar ya koma kalkashin iko na."take yanayin Zubaina ya sake sauyawa batayi zatan zai kuma yi mata maganar Umar ba kallansa kawai takeyi tagaza furta komai...cigaba da cewa yayi."Jarumi kamar Umar bai kamata ace yana hidimtawa mace ba kuma ya dace ace ya kasance cikin jerin Jaruman Zairana."ya ida maganar yaba aje dubansa akanta har yanzun batace uffan ba sai dan rawa da jikinta yafara mata a sannu sannnu alamar karaya da sanyin jiki."bakice komai ba."murmushin dole ta kirkiro ta maida kanta kasa saboda idanun Umman ta dake yawo akanta."Kinga muna da wasan GASA da zamu gabatar a Masarautar KESAR a watan gobe zanso Umar ya karbi gwaji kafin lokaci."
Ttunda Ammar ya fara maganar Umar kirjin Zubaina ke dukan tara-tara jitake kamar za'a kwace mata wani abu mai muhimmanci atatatare da ita"Ya dace kice wani abu."? "Yaya ai banda abin cewa amma ina so zanyi magana da Umar abinda yace haka za'ayi."yanda kikace,ba damuwa yar gatan Abba kanwar Aryan Allah ya baki mijin da zai kulamin da ke."Amin yayana."Umma zanje wajen Adda Mufidah tana nema na."cikeda mamaki gimbiya Amina ke kallan yar tata."Da kikace mani nan zaki wuni."? "eh nayi mata alkawali ne shiyasa."kigaishemin da yar tawa"toh...yayana saikajini"ba damuwa.
Koda Zubaina ta fita ba inda ta wuce sai sashen ta jitake kamar ta kurma uban ihu tambayoyi take jerawa kanta kala kaka...miyasa yaya Ammar kesan rabani da Umar?bayan shike debe mani kewa! Saman gado ta zauna duk ta rasa abinda ke mata dadi a rayuwar ta duniya tunda ta shiga daki gabaki daya bayinta sun kama kansu sun san idan yanayin uwar gijiyar su ya sauya akwai damuwa kafin kaftawar ido kowa yabar sashen gimbiya Zubaina sai Fadila data bita har cikin turakar ta,cikeda kulawa gaminda tsantsar girmamawa tafara tambayar ta damuwar ta."Allah yataimaki uwar gijiyata hankalina bazai taba kwonciya ba idan ina ganin ki cikin wannan yanayin ba."?banza tayi mata sake sadda knta tayi kasa tace."matsayina bai kai girman da zan dinga jera maki wadannan tambayoyin ba...bazan taba yafema kaina ba idan na ganki cikin damuwa ba,na rokeki ki sanar mani damuwar ki wala Allah mu samu mafita."Sai a lokacin Zubaina ta fadama Fadila yanda sukayi da Yarima Ammar taci gaba da cewa."yanzun minene mafita?"Allah yataimaki uwar dakina....fushi bai kamace ki zuciyar ki mai kyauce ki kara hakuri saboda shiya dace da wannan kyakkyawar fuskar taki mai yalwatacciyar haiba da kwarjini,ina neman alfarma wajen uwar dakina kiyii min izini inyi kiran jajirtaccen bawan nan Umar."kallo kawai Zubaina tabi Fadila dashi take takama kanta"tuba nike ranki shidade Allah yakara maki nasara da nisan kwana."shiru ne mai tsayin gaske ya karade illahirin dakin kafin ta bude bakin ta tace."miyasa kika haka."?"Ina ganin hakan shi zai kawo maki masalaha,ta haka ne kawai zaki fahimci kalar damuwar da Umar yayi dake...kimin aikin gafara idan kalamai na basuyi maki dadi ba."bakaramin nazari Zubaina tayi akan maganar Fadila ba duk da ta gamsu da shawarar ta sosai"shi kenan kije kiyinmani kiran Umar."nabarki lafiya."
&&&
Turaki ne kulle cikin wani wulakantaccen daki wanda gwara gidan yari da shi....Anan gimbiya Saude ke azabtar da bayinta ba wanda ya san da dakin nan,banda azabataccen sauro da kudan cizo ba abinda ke aiki a cikin dakin,ba bugu ba zagi saidai azabar cizon sauro kadai da kudim cizo sunsa Turaki yayi baki jikin shi duk tabbuna tsabar cizon da yake sha na Sauraye,tsabar zalinci irin na Saude sau biyu take bashi abinci,kuma kullun sai kakar tashi ta zage shi tana cewa baida wani anfani a wajen ta tunda bai kinshin iyayen shi.
duk abinda zatayi ma Turaki bai damun shi a cewar shi komai zasuyi lokaci ne shidai fatan shi Allah yasa kada su cutar mashi da mahaifiyar shi, kuma kullin idan ya tuna halin dasu Umma Mardiyyah ke ciki sai yayi masu kwalla tsabar tausayin su dayake yi, yana cikin wannan yanayin....sai ga Barde ya shigo yana zuwa ya shararama Turaki wani irin gigitaccen mari da har saida ya rude baki daya bai gani sosai sai bijibiji da yake gani har saida ya taba mashi ido ihu Turaki ya saki ya duke kasa koda Saude tazo tsinar Turaki dinga yi tana."dan iska zakazo kayi tayima mutane kururuwa kamar wani tsohon mahaukaci ba kaga komai ba indai mune....minene anfanin ka tunda bakada kishi kwara ka mutu da ganin ka."shidai tunda ya rike kuncin shi bai kuma cewa komai ba,daman baiyi mamakin jin munanan kalaman kakarsu ba yasan tun ran gini tun ran zane daman can basu san shi tunda bata kaunar uwar shi, ko da sun wulakanta shi bai wani damuwa yasan kiyayyar da gimbiya Saude ke mashi tasamo asali tun kan yazo duniya...saida suka gama zagin shi da dungurin shi,sannan suka aje mashi balgataccen abinci suka rufe shi suka koma cikin gida sai murna suke yi suna farin ciki.
zuwa yanzun komai na Burhaan sun bi sun katan tane shi....
gimbiya Masau'da takira uwar bayi har sashenta ta hada mata kayan gara kala-kala tunda ta shigo takai gaisuwar ta wajen gimbiya ta samu waje ta zauna cike da shakku bayan wasu lokuta gimbiya Masa'uda ta kora duk wata baiwarta dake sashen ta hada tTlatu saida ta koreta ya rage daga ita sai Uwar bayi."Mairo."Allah yaja da kwanan gimbiya ta."gyara kishingidar tayi tace."babban abinda yasa nace akira mani ke inaso in sake maki maganar aika aikar da Barde ya aiwatar akan jikar ki Yusrah na fahimci baki daya maganar nan tayi sanyi bayan kuma anzalin ce ku zalinci mafi muni!shiyasa nace ai mani kiranki,kar dai kuce harkun saduda ko kuma kunyafe zalintar ku da akayi."?sadda kanta kasa uwar bayi tayi tace."Allah yataimaki gimbiyar Burhaan inamu ina yafe wannan mugun ta'addancin da akai mana!kamar yanda kika sani anfi karfin mune shiyasa....saboda muna bayi shiyasa ake mana kallan kaskanci ake wulakanta mu ako wane lokaci,yanzun haka da kika ganni da ace zan bude maki bayana ba zaki iya kallan saba tsabar duka da azabtarwar da ake mana duk ranar da mukayi zanga zanga a ranar sai an dukemu an kama mana ya'yan mu maza wa'anda sune jigonmu an kulle su agidan KASO ana lahana mana ya'ya! Allah yataimaki gimbiyata walahi ada nikejin tsoron azaba da mutuwa amma banda yanzun!zuciyar Mairo ta kekashe ta bushe barazana bata taba tsoratani abinda yasa kika ga mun daga kafa ba yanda zamuyu ne kuma raina nayi mani ciwo idan naga ana wulakanta ahalina dan kawai suna BAYI ai Koda muke bayi kowa ya shaida Bayima Ya'yane kamar kowa ba wanda ya diro daga sama haihuwar mu muma akayi."Cikeda kunar zuci take magana kama ganinta zakasan cewa lallai an cutar da ita sosai."kiyi hakuri da kalamai na ranki shidade nayi alkawali koda za'ayi mani gunduwa gunduwa sai na fadi abinda ke cikin zuciyata."shu'umin murmushi gimbiya Masa'uda tayi kasa-kasa tace."Hmm Mairo kenan, kinyi kyan kai....daman haka nike so ku fidda tsoro a cikin zuciyoyin ku ta hakane kadai zan taimake ku."zaki same mu wasu jajircewa."bawai halin da

Please Login or Register in order to submit comment