Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amma ko ajikin Barde cigaba da wakewaken sa yayi ya fita ya barsu cirko cirko take Saude ta barke da kuka,itako gimbiya Masau'da zuciyar ta fas tasamu taban da zata yaki abokin gabarta dashi wato Hamza dan itama ta samu takafa tata sarautar tunda yanzun bata ita yakeba daga ™auri sai guiwa.....
_Ikon Allah yauga soyayya ta zama kiyayya tsakanin aminan nan guda biyu_ _wato Galadima Hamza da Gimbiya Masau'da koya zata kaya kubiyoni sannu a hankali zakuji cakwakiyar_ _da zata wakana a cikin Masarautar Burhaan_


_JAMEELAH JAMEEYc'þ_


Share
Pls

*SADAUKIN BURHAAN*
_(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_
A Kingdom Story=ØQÜ

*NA*
*JAMEELA JAMEEY*
_(Ya'r Mutan Kankia)_

*BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM*

_SHAFIN KYAUTA_

BABI NA UKKU

Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira Wari Ukku(300) Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello shedar biya ta wannan number 08160508316.

*Godiyar ban girma da jingina a gareku masoyana na nesa da na kusa nagode sosai da nuna kauna a book din SADAUKIN BURHAAN,sannan masu man maganar n cigaba da Izzah ko mulki nasan maybe basu fahimta ba,ai Sadaukin burhaan shine cigaban izzah ko mulki kije ki duba last page din Izzah ko mulki zakiga nasa sunan ai ngd sosai>ØpÝ*



Baki Waya hankalin gimbiya Saude yai mummunan tashi da sauri ta rike gimbiya Masau'da tana rokonta arziki akan karta bari wannan abinda yafaru ya fita....saidai abin mamaki gimbiya Masau'da taki yarda a gadarance tace."matukar Hamza bai dauki mataki akan Wansa ba saina tona asirin Barde kowa yaji abinda ya aikata ba Burhaan kadai ba saina yayata lamarin nan ya karaWe kaf illahirin Kasar Cameroon bama iya nan ba kadai sai zancen nan ya zaga sassan duniya kowa sai yaji abinda Yarima Barde ya aikatama Baiwa."
Lallai kama hankalin Saude yayi matukar tashi banda zufa ba abinda ke tsatsifo mata duk jarabarta tana shakkar tsatson su Masau'da da irin shakiyancin ta.
Ba yanda tayi iya da haka suka sabe sukabar sashen Barde a zuciyar Saude ko so take tana fita idan dare yayi tasa a badda gawar baiwar nan dan asirin jikinta dana mulkin Wanta ya rufu ita kuma Masau'da burin ta ta turo uwar bayi da wasu bayin a sashen Barde da niyar gyara zasu ganema idanun su abinda ke wakana,tasan koda za'a kashe su bazasu yarda ba sai sun nemi hakkin su ita kuma idan taga Hamza yaki basu hadin kai saita rubuta wasiku ta aikama Sarakuna da sauran masu hannu da shuni tasan zasu tayata yakar Hamza kafin tafara turo mashi da bamabaman asiran su......
tana komawa da saurinta tasa aka kira mata uwar bayi tareda yar aikenta suka dawo baki dayan su suka zube kasa suka kwashi gaisuwa fadada fara'ar ta tayi tace."Uwar bayi kije da kanki keda wasu daga cikin bayu zaku gyara sashen Yarima Barde yanzun yanzun nan."angama ranki shidade Allah yataimakeki lafiya."gyada mata kai tayi ta fita da saurinta,da shu'umin murmushi ta raka bayan ta.batareda bata lokaci ba ta kwashi bayi har hudu sukaje sashen Barde suka fara gyara ko ina sannan ta turo wasu karamin falo suna shuga sun fara aiki suka ga mutun yashe duk jini jikinta ihu suka kwada da sauri uwar bayi ta duka tana kallan fuskar ta taga ashe Yusrah ce mai gyarawa Yarima Sadauki daki,ba karamin kaduwa tayi ba baki daya wajen nan suka hau uban kuka kamar zasu mutu saboda yarinyar kirki ce, shiyasama Sadauki yace taciga da yimashi aiki, shi kanshi yarinyar tayi mashi ba ruwanta da son abin duniya kaf turakar bayi ba yarinya mai kamun kai kamar ta da sanin yaka mata ba kamar Yusrah....uwar bayi tasa aka maida mata kayanta sannan ta fito ta kirawo wasu bayin suka dauke ta sai fa'da duk abin nan Masau'da na kallan bayin nan sai murna takeyi yau asirin Barde zai tonu suna shiga fa'da dogarin Hamza ya daka masu tsawa amma sun rigada sun kekashe ko shakka babu a fuskokin su, hakan yasa Hamza ya daga mashi hannu sannan yayi shiru a tsakiyar fa'da suka shimfideta kallo daya Hamza yai mata sannan ya maida kallan shi ga uwar bayi cikeda tuhuma ba kunya balle shakka tace."danka Barde yaima yar mu Yusrah fyade ta sanadiyar hakan ta rasa rayuwar ta shiyasa muka kawoma fa'da dan ta kwatar mana hakkin mu."
ba takaran Hamza ba hatta Abdullahi dasu Shamaki da sauran dagatai da fadawa saida suka girgiza dajin maganar ta,dman anyi sa'a ranar fa'da ta cika tamkam da yan adam.zufa ke ketoma Hamza tako ina amma a zahiri sai cewa yayi."har wani yan'ci ne daku da zakizo fa'da kima mana izgilanci nasan Wana bazai taba haikema yarku ba."Allah yataimake ka idan har nayima Yarima Barde sharri raina fansa ne akansa."a fusace Galadima Hamza yace."minene aibun Abbas dan ya huta da baiwa? kwananta ne yakare shiyasa ta mutu dan haka kuyi gaggawar kauda mani da wannan baiwar tunkafin ku fuskanci mummunan hukunci."ba bayin nan kadai ba duk wanda ke cikin fa'dar nan saida maganar galadima Hamza ta girgiza su Shamaki ne ya nuna mashi rashin kyautawar hakan yace."ranka shidade koda baza'a hukunta Barde ba ya dace kai masu magana mai dadi dan su rage radadin da zuciyoyin su ke ciki a halin yanzun.*"kamar jira ya hau Shamaki da masifa sunaji suna gani aka sama Hamza ido yace."ku bace man da gani matsiyata."cike da kulewa uwar bayi tace."A halin yanzun zamu dauki yarmu dan mu kaita makwancin ta amma kasani koda irairen mu zamu kare kaf wlh bazamu hakura ba kamar yanda kace muba masu daraja bane hakan bazaisa adinga wulakanta mu ba munaji muna gani,kasani cewa bayima ya'yane....ankama mutane masu daraja an wulakanta su balle mu damuka saba da wahala da ganin wulakanci, bazamu damu da abunda zakayi mana ba,kuma bazamu fasa neman hakkin mu ba."uwar bayi ta gama maganar cikin tafasar rai da kunar zuci."ku dauketa muje a shiryata saidai kasani wadannan mutanan sune shaidar mu akan Wanka yaima yusrah fyaWe kowa yaga yanda jini Ke fita daga kasanta har yanzun idan kuwa ka gardama ba majin kunyar budewa kowa ya gani."tunkan ya musa ta bude duk wanda ke wajen saida ya kauda kai gefe har shi kanshi Hamzan yakasa magana.wasuma har kuka sukeyi sannn suka dauke ta suna kuka suka tafi da ita turakar bayi...
duk wanda ke fa'dar nan saida ya tafi harda Abdullahi ya kasa tsayawa daga shi sai dogarinsa aka bari jiyake kamar yai kuka,yasan bayin nan sun fishi gaskia amma bazai bari Wan shi ya wulakanta taba a cikin Burhaan.

Duk abin nan da akeyi labari ya karade Burhaan koda Hamza ya kira Barde ya tambaye shi bai musaba amma saiya dinga magana cike da gadara baisan sadda ya wanke shi da mari ba.
"kai mahaukacin inane da zaka kashe yar mutane ina laifin kadinga binta a hankali kana hutawarka da ita,ko kasan abinda ka aikata zai taba mulkina? da darajar Burhaan? yanzun gayacan za'ayi mata jana'iza kasani naji kunya a gaban mutane masu daraja ka wulakantani."
baki daya kwakwalwar Saude ta gama kullewa ita dai tasan daga ita sai Masau'da sukaga gawar yarinyar nan amma ya akai bayan da wowar su za'ace har ankaita Fa'da. Aranta take killata kodai Masau'da tayi mata ture dan ta huce haushinta tasan takun sakar dake tsakanin ta da Hamza ba.
Tana cikin tunanin ta taji muryar Masau'da na magana"A gaskia banji dadin abunda da Wanka Barde ya aikata ba gashi anatacin ganiyar mulki harka kara kyau gaskiane giyar mulki tana ratsaka kaga abinda Wan kuka yajama uban sa minene mafita Hamza?"dariyar sha™iyanci ta kece da ita.
"Fitarma daga gida Masau'da tunkan nayi maganin ki."Kaga kar kaiman ihu Hamza,bayan baki daya duniya ta gama sanin abin dake faruwa kuma ya amsa laifinsa duk wani mari da zakai mashi bazai wankeku ba a idon duniya yakamata a matsayin ka na mai rikon kwaryar mulkin Burhaan ka fito a gaban kowa ka hukunta Barde yanda duniya zata shaida muddin ka kasa hakan lallai bazamu yarda ba...ai ciwon ya'mace na mace ne inda yarka Safiyyah akaima haka nasan kisa ya dace ga wanda ya aika ta abin yanzun Masarautar Burhaan tasa ido taga hukuncin da zakai ma danka Barde...ka kuskura kace zaka mareni zan fita waje infadama duniya akan nafada maka gaskia shine kace zaka haike mani sabkda na kare kaina ka marina."kallan Masa'uda kawai yakeyi yana mamakin ta itama kallan Wage takeyi masa tana cika tana batsewa cikeda izzah gamida gadara a hankali ta tako zuwa gabansa tace."Hmmm Hamza kenan!ya kake ganin wannan maganar idan har ta fita waje mikake zato."? Murmushi ta kuma saki na raini taci gaba da cewa."Kaga Hamza kayima Masau'da biyyayya tunda nafika iya tuggu da iya taku idan ba hakaba nida kai muzuba mugani."kallanta kawai yakeyi yana tattare maganganun ta zuwa ma'aunin mizani domi rarrabewa."bari injema mutanan can gaisuwar rasa yarsu kafin muji abinda zaka yanke akan dan ka."kanshi ya buga a jikin bango ya fashe da marayan kuka yanajin tsananin bakin ciki a cikin zuciyar shi."Shikenan Barde kagama zubda mani ™ima da daraja inaji ina gani makiyana nayimani dariya ya kake son inyi da raina?Umma yazama dole in salwantar da rayuwar Masau'da na fahimci zata zamo mani barazana a rayuwa ta, tunda tagama sanin sirrina."lallai da ka tabbata nonona kasha ba yanda banyiba akan ta sirrin ta abin nan amma taki dama jira nike idan dare yayi mu binne gawar yarinyar nan da kanmu, shine tayi mana cinne dan tasa mulkin ka zai samu tan gyarWa."lallai Goggo kamar dai bake kika haifi ne walahi billahi saidai idan nazama gawa sannan hakan zai faru nayi imani da girman mulkin gidan mu muddin da raina saidai koni ko Masau'da........
```Allah sarki rayuwa kenan yauga soyayya tazama kiyayya shiyasa duk abinda zamu aikata musa Allah a ranmu,Allah ka rufaman asiri kasa mudace```
```Kamar yanda kuka sani wannan labarin na``` *SADAUKIN BURHAAN* *na kudine akan naira 300 kacal duk mai bukatar wannan littafi ya tuntubeni ta wannan number 08160508316 sayen nagari maida kudi gida*

*SADAUKIN BURHAAN*
_(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_
A Kingdom Story=ØQÜ

*NA*
*JAMEELA JAMEEY*
_(Ya'r Mutan Kankia)_

*BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM*

_SHAFIN KYAUTA_

BABI NA HUŠU

Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira Wari Ukku(300) Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello shedar biya ta wannan number 08160508316.



Yakasa zaune yakasa tsaye addu'a kawai yakeyi abubuwa dayawa sun sha mashi kai baki daya duniya tayi mashi ™unci yarasa inda zai saka kanshi.
zuwa yanzun har Asma'u tafara suma kamar mai iska ko wadda iska ta taba haihuwa ta gagareta koda mai gidan yace ya shigo ya duba halin da matar shi take ciki kin shiga dakin yayi saboda baisan yaga tsaraicin ta badan komai saboda ba matar shiba ce kuma yana bala'in kishin dan uwanshi duk da mutanan basu san ba matar shi bace,matar gidan ce ta fita da gudu ta kira wata tsohuwar mata aikinta kenan karbar haihuwa duk wahalar ta Allah ya hore mata dubaru na haihuwa gari gari ake zuwa a dauketa ta karbi haihuwa da sassarfa suka shigo da wani akwati akabasu waje ita da Asma'u tafara jika magani ta bude bakinta ta zuba mata ta hade a wahale sannan ta shafa mata a fuskarta baki daya cikin Asma'u ya juya da karfin gaske kamar zai tsago cikinta ya diro kasa.
matar ta shafa mata wani maganin a saman mararta cikin ikon Allah ko minti goma ba'ayiba cikin rahamar Allah haihuwa ta taho gadan gadan cikin tausayinsa da rahamar sa Asma'u ta sintilo kwakkyawan Wan'ta mai kama da uban sa kwabo da kwabo,tana haihuwar sa ta suma bata san inda kanta yake ba,daman tun tana nakudar matar gidan ta dafa ruwan zafi amma baki dayan su hankalin su ya koma kan Wan saboda tunda aka haifeshi baiyi kuka ba shiyasa hankalin tsohuwar nan ya tashi ta daga shi ta sadda kanshi kasa tana buga mashi kugu amma yayi shiru ba alamar kuka da jaririn yayi hakan yasa ta dibo wani magani ta jika ta siyaya mashi a baki kamar aikin sihiri sai a lokacin ya duka uban kuka inyarare yarare haka yake rere kuka take Shattimah yayi sujjada ya godema Allah yasan Asma'u ta sauka lafiya,aje shi gefe tayi sannan takoma kan Asma'u....
ita kuma matar gidan da tsohuwar ta kira da Zaliha ta debo ruwa ta wanke jaririnta tas sannan takara tsarkake shi,sannan ta dauko kaya ta saka mashi takai ma Shattimah shi tunda ya kalli yaron nan Shattimah ke kukan farin ciki.
itako Asma'u takai awa daya sannan ta dawo cikin hayyacin ta, wannan tsohuwar da suke kira da inna ita tayima Asma'u wanka da kanta ta gasata tsaf.
Bakaramin farin ciki ya kama Shattimah ba bayan la'asar inna tagama gyara Asma'u taba Zaliha magunguna tace abata a kunu ko a cikin fura na sati biyu nan ta kira Shattimah tace."Wan da aka haifa jifa ta same shi tun yana cikin ciki dan gaskia da kyal zai rayu koda ya rayu zai sha wahala kafin yasamu lafiya, amma a dinga yi mashi wanka da garin maganin dana baku."nagodw inna zamu kiyaye da izinin Allah."godiya ya sake yimata sannan ya bata kudi masu tsoka yakara mata godiya mai tarin yawa duk abin nan ashe Zaliha taji ba karamin tausayawa Asma'u tayiba gata da karancin shekaru amma ta hadu ta iftila'in rayuwa danma Allah yasa rayayya ce da anrasata.
bata bata lokaci ba ta hadama Asma'u kunun kanwa,ta zuba mata maganin da inna ta bata ta matsamata saida ta shanye shi tas,cikin ikon Allah sadda za'ayi mangariba ruwan nono yazo nan Zaliha ta gwada mata yanda zata shayar da jaririn ta,ba laifi yana sha.
lokacin da Asma'u ta dauki dan'ta ba karamin son shine ke shigarta ba a lokaci daya sai kallan shi takeyi cikeda so da kauna koda batasan yanda Sadauki yake da yana yaro amma tasan suna kama da jaririn ta,ana gama isha'i Shattimah ya shigo da Malan Audu sunan mai gidan kenan ya dauki dan yai mai addu'a sannan yai masu barka yaba Shattimah jaririn,sai kallan dan yakeyi yana karaji yana shiga cikin zuciyar shi,kallan ta yayi yace."wane suna kika zabawa dan naki."? Kallan shi tayi cike da mamaki"da'na fa kace karkaman ta yanzun baida uban da ya wuceka a duniya karka manta yaya Moh'd baida kamarka dan haka na mallaka maka wannan damar ka zaba mashi suna"Hmmm Asma'u kenan kinsan Sadauki bai cikin hayyacin shi komai zai iya aikatawa amma walahi duk duniya baida buri da ya wuce na wannan Wan kuma yana son shi yana kaunar shi kune iyalin shi kuma kune farin cikin shi inasan Wan uwa na kuma ina kaunar sa ji nike kamar ciki daya muka kwanta dashi...wlh Asma'u duk abinda zamuyi ma Sadauki dagani har Tafeedah bazamu biya shiba,duk cikin mu bamai mutunci da kishin dan uwan shi kamar Sadauki shiyasa kikaga naba rayuwar shi mahimmanci kiyafe mashi lallai an cutar dake amma kisani bayin kanshi bane bake kadai ba duk wani makusancin shi anzalince su wannan Wan na Muhammad Abduljalal Muhammad ne,ki fada mani mikike so a sama yaron nan."? "Shikenan na fahimce ka, kuma nayafema yaya Moh'd, ina son kasa mashi AHMAD.
arazane Shattimah ya kalleta"miyasa bazaki sama shi sunan Mai martaba ba?" ajiyar zuciya ta shide tace."ko shi kanshi abinda mahaifin shi zaiyi kenan ka canci haka kabada gudunmuwa mai yawa daga rayuwata data wannan yaron haka rayuwar Abba da Ammi harda Juwairiyyah dashi kanshi Sadauki kabamu gaggarumar gudunmuwa bamu da abinda zamu saka maka da shi daya wuce ince Allah yasaka maka da mafificin alkhairi Allah yabar zumunci mai daurewa har abada."bakomai Asma'u ba abinda ban iyayi akan iyalin Sadauki Allah yarayama na shi cikin aminci da turbar addini."Amin ya Allah."nan yaima shi huWuba yasa mashi Ahmad kamar yanda ta bukata.....
"gashi Allah yaraya Ahmad bisa sunnar ma'aiki(SAW) kuma Allah yakara maki lafiya mai anfani."Amin yayana."
_ZAIRANA_
Sadauki ne ya hada kayan wanki kamar yanda uwar gijiyar shi ta bukata yana gama hadawa ya tafi bayan sashen ta yafara wanki duk da bamasu yawa bane amma jiyayi kamar sunkai kala hamsin saboda bai saba da wahala irin wannan ba amma haka yasama kanshi jajircewa ya fara Wikar wanki kamar ba gobe bai dauraye kaya sai ruwan yakoma fas sannan....
Zubaina ba ma'abociyar zuwa bayan gida bane amma saboda ta dinga ganin wulgin Umar tana jindadi shiyasa ta zagayo baya ta zauna saman kayatacciyar shimfidar ta hadimanta nata yimata tausa amma baki daya hankalin ta na kan Sadauki koda ya karasa wankin ko kallan inda take baiyi ba ga gifta ta gefenta yayi shanyar kayan....
ita kuma duk sadda Umar yaki yimata magana ba karamin bata mata rai yakeyi ba acewar ta ai bawan ta ne dole yaimata biyyayya shi kuma baisan yawan magana shiyasa ko sun hada ido yake nuna kamar baisan da itaba bayan yagama shanyar shi ya hada kaya zai tafi ta kirashi."UMAR."tsayawa yayi saidai bai juyoba kuma bai tafi ba yakai minti Waya kafin ya juyo a miskilance tahowa yayi inda take kamar baisan taka kasa haka yake tako cikeda izzah kallan shi kawai Zubaina keyi koda ya iso tsaye yayi akanta maimakon ya duka sai ya tsaya a dakile yace mata."gani."tun daga sama har kasa take kallan shi a Wage sannan tace."haka ake girmama mutane a garin ku."? yi yayi kamar baisan da shi take ba,saida fadila tace mashi."Umar ka duka."a nutse ya duka saidai yaki kallan fuskar gimbiya Zubaina."Umar miyasa baka girmama na sama dakai."?kallan daya watsama gimbiya Zubaina saida ya haddasa mata faduwar gaba dakewa kawai tayi a kausashe cikin muryarsa mai amo yace."bangane mi kike nufiba."?Baki daya kwarjinin shi ya hanata magana saidai kallan sa da takeyi.....sake tamke fuskarsa yayi yace."kinyi shiru?karfa kimanta Umar nike kuma bawane ni marar yan'ci taya zan™i mutunta mutane bayan kullun sai Abba Ado ya fadaman waye ni da matsayina nidai bana son shiga rayuwar mutane balle wa'anda suka fi karfina,karki manta ke fa uwar daki na ce,kada kiga inayi maki magana ba yanda kike so ba,nasan da sannu zan koyi komai....nabarki lafiya gimbiya Zubaina."
Tunda taji Sadauki ya ambace sunanta sai taji kamar yafi kowa iya sarrafa shi baki daya amon muryarsa da sautinsa ke yawo cikin kunnuwanta yana ratsashi ta ko ina har ya tafi batasan ya tafi ba, saida ta dawo daga tunanin data lula sannan taga bainan a sanyaye ta tashi suka mara mata baya takoma dakinta tarasa meke damun ta gamida Umar gashi koda batasan soyayya ba tasan ba son shi takeba, dan tasan ba haka so yake ba,itadai kawai tasan Umar na burgeta amma aiba abinda zatayi da BAWA a matsayinta ba gimbiya Zubaina mai takama da kyawu gamida usuli.

Mardiyyah ce zaune a cikin gidan yarin gilba ta rasa mike mata dadi tun tana kuka har ta dangana zuwa yanzun duk tayi baki ta rame kamar ba ita ba,duk da tasamu labarin mijinta bai mutu ba amma bai hanata shiga damuwa ba musamman batan da dan'ta yayi.
labari ya samesu Barde yaima Yusrah fyade taji dadi matuka amma bataji dadiba da Yusrah ta rasa ranta ba,duk da suna gidan yari daya da Juwairiyyah amma ta rabu da haduwa da ita sau biyu a sati ake fiddo su asasu aikin wahala a nan ne suke haduwa da yarta.
Waziri Bashir ko fitowa ba'a barin shi yayi tsaro ake bashi bana wasaba, yau yana daga cikin ranakun da Hamza yaba Hajara yar waziri Bashir damar ganin mahaifinta saida aka caciketa tas sannan ta shiga koda ta isa sashen shi ba karamin kuka tashaba yanda taga mahaifinta ya lalace ya rame ko magana bai iyayi sosai tsabar azaba daya sha. koda yaga yarsa murmushi kawai yakeyi na murnar ganin tilan yarsa,saida ta duba taga ba mai kallan ta sannan ta saka hannu cikin iner dinta ta fiddo daurin fura taba mahaifinta ya shanye ta dauko wata ledar ruwa ta kara bashi ya shanye sannan ta sake ledojin cikin jikinta ba karamin dadi waziri Basheer yaji ba nan ta fadama shi ranakun da zata dinga zuwa ta duba shi,nan ta fada mashi yanda sukayi da Hamza ya tsorata yana shakkar su Hamza kuma baisan yaga abinda zai taba mashi iyali suna cikin ganawa akace mata lokacin su ya cika nan tayi mashi sallama ta tafi.

Safiyyah ce kwance magashiyan yau kimamin kwanan ta bakwai tana nakuda amma haihuwa taki kowa ya fidda rai ba irin maganin da basu bata ba amma ba amo ba labari duk ta kumbure ta suma har kabari angina mata amma saita farfado raban da gimbiya Kursiyyah tayi bacci harta manta danko Goggo saidai tayi gyangyadi daga zaune, amma tunda gimbiya Masau'da tazo dubata sau daya ba takara bi ta kansu ba,koda ta kawo masu maganin nakuda tana tafiya suka yarda shi acewar su karta cutar masu da diya....

```Haka rayuwa take duk abinda kakeyi haka kake ganin kowa yana aikatawa ga rashin yarda da kowa,ba'aima Allah dubara kaidai ka kamanta gaskia komai kankantar ta,Allah na tareda mai gaskia```

Da haihuwa ta taho gadan gadan saita koma duk wasu dubarun su sun kare har bokayen su sunyi sun gaji sai da sukaga zata wuce kiyama sannan suka fara addu'a amma saida ta kara kwana ta yini sannan Allah yakawo haihuwa a shitatan haihuwar dire tayi aiko ta diro yarta mace mai kama da yan uwanta dandai ita baka ce diyar koda suka duba suka ga 'ya mace suka haifa ba karamin bakin ciki suka shigaba ji suke kamar su kashe yar dan takaici da bakin ciki koda Hamza yasamu labarin haihuwar diyar tasa da sauri ya shigo dakin amma ana bashi yaga ya'mace ce saiya dungurama uwar diyar ba karamin tashin hankali Safiyyah ta shiga ba, duk da taso ta haifi na miji amma da taga macen sai taji tana son yarta a haka,ita ko Kursiyyah murmushin yake kawai takeyi amma badan tana murna ba dan karta nuna ma Safiyyah batasan yarta taji ba dadi dan tasan soyayyar da' da mahaifi, ba kunya Hamza yace ma Barde."ka dauko yar nan a kasheta saboda bata da anfani a wajen mu nida nikeso tsatsona suci gaba da mulkar Burhaan amma saita fara da 'ya mace."kuka Safiyyah ta kece dashi ta hana yarta taita kuka tace."ina son ya'ta a haka."Goggo ta hana su daukar mata Wiya acewar ta ai yanzun tafara haihuwar wani lokacin ta haifi na mijin,sannan Hamza ya kyale mata diyarta....ranshi ba dadi haka ya fita yana bambamin bala'i.

_Allah karabamu daga aikin jahilai minene aibun ya' mace,wani lokacin ma tafi namijin amma_ _yanzun saboda gado sai mata aita hauka kedai kinemi mai albarka,_ _ya'mace kyautar Allah ce Allah ka azurtamu da zuri'a mai anfani kuma mai tsoron Allah =ØOÞ_

Haka rayuwa ta kasance Safiyyah bata iya baccin kwarai saboda taba diyarta kariya kar a halaka mata ita,ta sama diyarta Kursiyyah sunan mahaifiyar ta,ko arzikin huWuba bata da ita ga uwa bamai ilimin addini ba bare tayi mata da kanta.....

Shiko Sadauki koda yakoma masaukin su kwantawa yayi sai yaji uban gidan sa na kiran shi,koda ya ta shi murmushi ya sakar mashi yace."sannu da dawowa."Yawwa Umar ya aiki."lafiya lau."takarda ya dauko ya bashi yana budewa yaga daurin kifi yaji dadin karramarwa da yayi masa budewa yayi yafaraci saijin dadi yakeyi.
shiko Ado duk sanda yaga Umar na farin ciki sai yasamu kan shi cikeda nutsuwa sai yaga kamar Wan shi Umar dan dai ya rasu tun yana yaro saidai shi baki ne,Sadauki ko farine kuma kyakkyawa ne ajin farko.
Ado ya tuna da sakon Yarima Ammar ya maida dubansa ga Sadauki yace."Umar idan kagama zan aike ka wajen Yarima Ammar.....

*SADAUKIN BURHAAN*
_(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_
A Kingdom Story=ØQÜ

*NA*
*JAMEELA JAMEEY*
_(Ya'r Mutan Kankia)_

*BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM*

_SHAFIN KYAUTA_

BABI NA BIYAR

*Masu tambayar nawa zasu sayi document na Izzah ko Mulki kusani free book ne Sadauki ne na kudi shima akan naira 300 kacal,Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.shaidar biyanki ta wannan lamba 08160508316.zaku iya cigaba da biyan kudin ku dan kasancewa cikin grp.*

Koda yaji Abba Ado ya ambaci Ammar hakanan yaji gaban shi na faduwa ya rasa dalili.
koda ya gamacin soyayyen kifin da Abbansa ya siyo masa kaya ya mika mashi yace."Ka kaima Ammar kace injini kaji Wan albarkana."kwatancen wajen yai mashi bai jima ba yatafi.
tun daga taskar bayi ake kallan shi kowa

Please Login or Register in order to submit comment