Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har saida yayi mashi ligib, sannan yasa akai shi magar kama aka rufe shi.
A tsora ce ta mike tsaye lokacin da sako ya isa
kunnuwan gimbiya Masau'da da sauri tata tafi wajen Hamza, har lokacin yana zaune cikin fa'da ta shigo batareda neman izini ba,yanda suka gatan ta a harzuke baki daya wajen duk suka fita suka basu waje daga shi sai ita,bayan sun gaisheta ta fara magana cike da gadara"Dama akwai lokacin da kafara hana ayi aike a cikin Masarautar nan? ko kuma wannan wani saban fi ilin ne na daban wanda da bansan da shi ba."?
Kallan kaskanci yake jifanta dashi daman yasan zatazo shiyasa tasa aka garkame amintaccen bawanta gidan yari mikewa yayi cikeda gadara gami da ratsastsiyar izzah yace."Ke Masa'uda bude idanuwan ki ki kalleni da kyau kinsan nafi karfin rashin da'arki na fuskanci kaf Masarautar nan cikarta da batsewarta ba wanda ke haye mani kai tsaye batareda ko War ba saike!wannan shine karon karshe da zaki sake yin wannan gigin walahi matukar kika kara shiga gonata sai na baki mamaki kuma ni na bada damar kar a sake abar kowa ya sake shigowa Masarautar nan daga dan gida har bako muddin ya shigo cikin Burhaan a tabbatar da an gurfanar da shi a gabana....balle wani wulakantaccen bawan ki, nina bada izini da kar a kuskura abar shi ya wuce har sai angur fanar mani dashi naji wane munafunci yaje ya aika ta."hhhhh Hamza kenan,walahi kayi karya ace amatsayina na gimbiya Masau'da kuma Sarauniya Burhaan ace ni zanyi aike kace zaka tuhume shi,wanann ba hurumin kaba ne dan haka kayi gaggawar sakarmin bawana cikin kwanciyar hankali."dauke ta yayi da mummunan mari"ke harkin isa ki dubi idanuna kifada mani wannan kalmar?bazan saki ba kiyi gaggawar barin fa'dar nan tunda ba nan aka haifi ubanki ba ina gargadar ki daga rana irin ta yau kada inkara ganin kafarki nan,idan ba haka a walahi da kike ganina nan banda ragi balle rsgowa kuma banda kara,tsab zan zaneki kuma saina kaiki cikin turakar bayi zan wulakanta ki,shasha sha"Hamza ni kamara."?murmushin shakiyanci yayi yace"Kina mamaki ne? idan bai shigeki ba sai inkara maki wani."Lallai Hamza walahi daga yau hannunka yagama taba fuskata,idan ko ka kara marina nayimaka alkawalin nadama da tarin dana sani kuma walahi saina rama"hhhhhhh yaro yaro ne baisan wutaba sai ya taka yaro man kaza,Hmmm Masa'uda kike kowa ma?ko mijin ki Abduljalal bai isa ba balle kaskantatta irin ki da bai wuce in wulakanta ba."saidai mu wulakanta juna Hamza nafada maka kayi kadan ka tuhumi bawana koda kuwa abinda yayomin ba mai kyau bane wannan kuma bai dameka ba kuma ina kara fada maka da babbar murya ka fiddo min bawana ina fatan ka fahimta."ko amsa bai bata banda wulakantaccen kallan kinyi kadan da yake aika mata a fusace ta fita ta nufi gidan yari......

```Allah sarki dayake bukatar ta ce yau ga gimbiya Masa'uda ta kama hanyar zuwa gidan yari,amma da aka kama abokiyar zamanta da diyar mijin ta,harta manta dasu a duniya,balle suyi tunanin zata kai masu ziyara rayuwa kennan```

_Allah karabamu da sharrin makiya mahassada ka rabamu da mugayen mutane Amin ya rabbil alamin=ØOÞSadaukin Burhaan na kudine akan naira 300 ki tuntubi wannan layin 08160508316.

"Goggo ki umurci Hamzanya fito min da Wana na gaji da abin da yake mani ba yanda za'ayi ace ya dinga wulakanta mani iyalina, dan kawai yana takama da mulki shine zai dinga aikata abinda yaga dama a lokacin da yaso na rantse da girman mulkin gidan mu idan har yace zaici gaba dayi mani wulakanci billahillazi la'ilaha illahuwa sai kowa yaji mu dashi cikin Masarautar nan." ajiyar zuciya mai zafi ra sauke tace "Yanzun Abdullahi akan Turaki zaka dinga tada jijiyoyin wuya har kake son ka wulakanta dan uwan ka abanza da wofi."Gwaggo Wan uwa fin Wa yayi ina son da'na dole inyi magana ai."suna cikin magana sai ga hamza ya shigo ya tadda Abdullahi nata masifa,"ni dai nafada maki Goggo kiyi gaggawar sa shi ya sakar mani da'na dan bazan iya jurar ganin shi haka ba."kuka ta kece dashi tana."Abdullahi ni!kake gayama mugayen maganganu irin wannan duk akan d'anka kake wannan kumfar bakin."daga fadar gaskia."rabu dashi goggo bazan saki dan nasa ba yayi abinda zaiyi,ni zaka dinga gayama haka kana man tirere"nayi maganar ko akwai abinda zakayi."?mamaki a saman fuskar Hamza ya fahimci lamarin Abdullahi so yake ya ta'azzara bai tashi tashen kunyar shi ba saida tsufa ya soma taso mashi sannan yake tashen fitsara."Abdullahi Hamza kake fadama magana?shi zaka ce yai duk abinda zaiyi,da raina ban mutu ba kuke so ku wulakantani aje ace gakucan kuna musanyar yawu da junan ku,ciki daya fa ba wasa ba, yayan ka zakacima mutunci akan Wanka lallai Abdullahi kace wani abu."Amma Goggo ai kema kinsan ba'a kyauta manba,dan yana takama yana yayana bashi zaisa ya daukarmin Wa ba yana wulakanta shi duk yabi lalace yanda yake son ya'yan shi suna yanda sukaga dama a cikin Burhaan haka shima Turaki yanada 'yanci, ai shima da'ne,kum kema uwace ya zakiji idan akaima danki haka? indai kina so ki ga ya'yanki cikin hadin kai mai daurewa toh kisa d'anki ya sakarmin da'na."lallai Abdullahi ina sarkin Burhaan kake cacar baki dani toh bazan saki Turaki ba sai naga karfin ikonka,tunda kanuna mani tsaurin ido, ni dama tuni nike zatan kanajin haushina Abdullahi dan kaga nike mulkar Burhaan,kanaso kahade mani kai da Masa'uda ko? walahi kar nike kallan ka."lallai Hamza haka kace?tunda nike bantaba zuwa wajen Masa'uda ba da sunan in hada kai da ita dan in cutar da kai, lallai kam idan nayi haka da nayi asara! amma tunda tanan ka bullo yanzun zan hada kai da ita zan mai data tamkar uwata."zuwa lokacin Hamza yakai bango baisan sanda ya shaki Abdullahi ba ya bugar mashi fuska take jini ya balle,Saude tafara ihu hakan yasa Masa'uda shigowa da sauri zata wuce taji ihun ta tana isowa da da sauri ta shiga tsakanin Hamza da Abdullahi.
Kallan kaskanci take aika Hamza tana murmushin keta da mugunta tace."Haba Hamza yanzun har lalacewar taka har takai haka da jininka kake fada? La'ilaha ilallahu...Goggo tun baki mutuba har zuri'arki ta farrake sun fara jin hushin junan su, abin mamaki....kaiko Abdullahi miyaja maka fada da yayanka kamar mahaifin kane fa a gareka"cikeda kissa take maganar."karki kara cewa mahaifina ne walahi da wannan abun!gwara Abduljalal yafi min koda yana mulkinsa ba kalar cin fuskar da ba muyi mashi,amma shi tattashin mu yake baisan yaga ko kadan munyi mashi bore amma sai Hamza da muke ciki daya dan haka muddin yaki sakarman da'na ba ruwana da mahassada sai inda karfina yakare walahi"bango Hamza yakaima duka sannan ya watsama Masa'uda wulakantaccen kallo yace."mi yasa kike saka mani ido ne me ruwanki tsakanina da dan uwana, kika kuskura na lissafa ukku walahi saina karya ki."maida wukar bani nakai zoman ba kajj Sarki Hamza idan haka ake Sarki da anyi asara ace Sarki ba aji ko kadan Allah ya kyauta."a fusace yai kanrta da sauri Abdullahi yaja hannun Masa'uda suka bar dakin, duk kiran da Saude keyi mashi a banza,shiko Hamza runtse idanun shi yayi yanajin dacin maganganun Masa'uda koda ya bude ba Abdullahi ba alamar shi, wani irin kuka Saude ta fasa ta fadi kasa tana."Kun tona mani asiri Hamza yanzun wannan na nuna Abdullahi yakoma bayan Masa'uda."tsaki Hamza yaja ko kallan uwarsu baiba balle tasa ran zai bata hakuri ya fita a fusace ya nufi fa'da ranshi na mashi daci saboda ance yayi bako daga Sirika.....
Yana isa fa'da kowa ya mike aka gaishe shi sannan ya zauna cike da izzah bayan yan sakanni magatakarda ya anshi sakon da aka aiko,nan Sarki Hamza yaba magatakarda damar karanta sakon da aka aiko mashi.....

_Assalamu alaikum_

```Sakon gaisuwa marar iyaka daga Sarki Abdullatib Muhammad zuwa ga Sarki Abduljalal Muhammad ina fatan sakona ya riskeka fatan kana cikin koshin lafiya,ina mai shaida maka ranar sha bakwai ga watan jiya munyi taron Sarakuna amma bamu ganka ba,duk da kasancewar Sarkin Sarakai kuma kaine shugaban taron nan,zamu gabatar da gasar nan a Masarauta ta a watan gobe sha shidda ga watan jumada akhir,muna gayyatar hazikan Jaruman masarautar ka,da fatan za'a karbi sakon gayyatar mu daga Masarautar Sirika zuwa ga Masarautar Burhaan,bissalam```

Tunda hamza yaji an ambaci Sarki Abduljalal wani irin bakin ciki ya turnike shi, jiyake kamar ya fasa ihu amma ya daure yace aba dan aike masauki kafin gobe za'aba da sakon da zai maida ma Sarki Abdullatib kafin lokaci yayi.

Yana komawa sashen shi sai musiba yakeyi."ina Sarkin shine za'a dinga jinjine gefe kamar wani katako kowa Sarki Abduljalal nagaji."aganin shi hakan kamar cin mutunci ne ace yana gabatar da mulki amma za'a rubuto wasika da sunan wancan miskinin Sarkin,sunan da yasa Abduljalal kena Miskini saboda bai iya komai, yazama dole yasa Shamaki ya na Washi a matsayin Sarki na dindindin sannan yasa ya turama sauran Sarakuna takarda dan su shaida shine Sarkin Burhaan.


_Yar Mutan Kankia cec'þ_


Share
Pls

*SADAUKIN BURHAAN*
_(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_
A Kingdom Story=ØQÜ

*NA*
*JAMEELA JAMEEY*
_(Ya'r Mutan Kankia)_

*BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM*

_SHAFIN KYAUTA_

BABI NA SHA BAKWAI

Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira Wari Ukku(300)Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.kituro shaidar biyanki ta wannan layin 08160508316.

*BURHAAN*
Tafe take cikeda izzah tana taka kasa kamar bata so sai shan kamshi takeyi ba inda ta zarce sai babban gidan yarin Gilba,tana isa baki daya hadiman dake wajen suka zube kasa suka kwashi gaisuwa daga masu hannu tayi cikeda gadara da sauri mai tsaran gidan yarin ya iso gabanta ya zube jikin shi na bari ya gaishe ta cike da girmamawa."ina bukatar ganawa da bawa na."angama ranki shidade." da sauri ya bude mata kofa,ita da baiwar ta Talatu suka shiga tana take mata baya tsaye tayi ta harde hannayen ta saman kirjin ta tana karema illahirin gidan kallo gaba da yamma kudu da arewa juyawar da zatayi ta hangi gimbiya Mardiyyah ita da hadimai sunata aiki,murmushin gefen baki ta saki a hankali take tako zuwa wajen Mardiyah tana aika mata kallan kaskanci da wulakanci."Baiwa ta,ashe aiki akeyi."duk hadiman dake wajen suka zube duka gaisheta daya bayan daya suka bar wajen daga ita sai Mardiuya da har yanzun taki dago kanta bare ta kalli inda take."sannu ko."?ta kuma fada tana dan yamutsa fuskar ta."a hankali ta mike tsaye tana aika mata ballagazazzan kallo mai dauke da tsantsar tsanar ta cikin kwayar idanunta,ta watsar taci gaba da aikin ta ganin taki yi mata magana hakan yasa ta koma nesa daga ita,ta kira wani bawa yana isowa tasa yai mata kiran gimbiya Mardiya."Allah yataimaki gimbiyar Burhaan, gimbiya Masau'da nasan ganin ki." kallan kaskanci take aikama Masa'uda kallan kinyi kadan"kaje kace mata idan tana bukatar ganina zata iya zuwa ta iskeni da kanta"Angama Allah ya fiddaki cikin kuncin da zalincin da azzalumai suka saki muna tareda ke uwar marayu."
Koda Mardiyyah na cikin gidan kaso amman har yanzun bayi na mutunta ta fiye da kima kuma ta kara samun daukaka marar misaltuwa bata taba sanin tana da masoya kamar haka ba saida ta tsinci kanta a cikin halin rayuwa...yana zuwa ya fada mata sakonta kaf ba abinda ya rage..murmushin takaici tayi sannan tayi mashi izinin tafiya."Allah yataimakeki gimbiyar Burhaan me zai hana kisa ayimata dukan tsiya wanda sai tayi dana sanin fada maki kalar wa'annan maganganun."Aaa Talatu bakiga yanda duk ta lalace ba kullun cikin ukuba take,hmm Hamza kadai ya isheta ko a haka akabar ta lallai tasha ukubar rayuwa,yanzun bata gabana ta Hamza nikeyi,muje gunta."....zaune suka isketa ita da gimbiya Juwairiyyah da bayi sunayi mata tausan kafafun ta,tsaye tayi akan su tana aika masu da kallan tsana tanaji kamar ta halakasu a cikin zuciyar ta,tsawa ta daka masu mai razanarwa har saida suka razana."ku baceman dagani munafukan banza munafukan wofi."da sauri bayin nan sukabar wajen ya rage daga Juwairiyyah sai gimbiya Mardiyyah, kallan kaskanci take jifan su dashi a hankali tafara taku tana dukan tafin hannun ta cikin dayan hannun ta takai gauro takai mari a harzuke tace."Ke har kin kai matsayin da sarauniyar Burhaan zata kiraki kice bazaka ki zoba a matsayin ki nawa? ta baiwa wulakantatta wadda bai wuce in saidaki ba." gefe gefe gimbiya Mardiya ta duba sannan ta kalli bangaren damar ta da haggun ta kamar nai neman wani abu."ke mi kike dubawa ba dake nike magana ba."? Sai a lokacin gimbiya Mardiyah ta kalle ta."Au ai Sarauniyar nike nema yaushe kika iso nan din."da sauri gimbiya Masa'uda ta runtse idanun ta tanajin dacin maganar ta tace."kwarai kuwa nice Sarauniyar,kisan abinda zaki dinga fadaman idab ba haka sai kin banbance tsakanin aya da tsakuwa."A wulakance gimbiya Mardiyah take aika mata da gantalallan kallon da ita kanta saida ta raina kanta da kanta"Hmmm ta yaro kyau take bata karko.....Masa'uda kenan! ashe da Sarauniya nike magana ban sani ba? lallai karfin halin ki na burgeni,wannan wasan yai mani dadi....karki manta turakata kikazo kika iskeni kuma nike da iko da nan wajen,kidawo cikin hankalin ki tun da wuri idan ba haka ba hmmm kema kinsan sauran."karya kike walahi kina baiwata kice zaki gyara mani zam kinyi kadan."
"Ko? ki dubeni da kyau Masa'uda kada ki manta kina gaban gimbiya Mardiyyah matar Sarki Abduljalal uwa ga Sadaukin Burhaan magajin gobe mai jiran gadon karagar mulkin Masarautar nan..."ya isa kada bakin ki ya kuma gigin kira wannan shegen yaron a gaban idanuna."ke din banza kema kinsan ba'a haifeki ba....kice zakizo har cikin gidana a cikin turaka ta sannan kice zaki nuna min gadara kinyi kadan,daga yau sai yau muddin lallatattun kafafun ki suka kara takowa har inda nike lallai saina nuna maki karfin ikona"mamaki da al'ajabi ya gama kashe Masa'uda."ni zaki kalla ki dinga fadaman kallar waWan nan bakaken maganganun."? "Kwarai kuwa...matukar baki bar wajen nan ba sai nasa duk bayin dake nan wajen sun lakada maki dukan tsiya."nidin Mardiya."ko kina tantama? Hamza yayi kadan yadubi kwayar idona ya gayaman wa'annan maganganun ba tareda nasa yayi nadamar hakan ba,balle ke da baiwata tafita daraja da komai sakara wawiya dakikiya dake."kuka ne kawai Masa'uda batayi ba saboda bata tsammaci haka daga gareta ba."walahi harna manta dake a cikin tarihin rayuwa ta,sai yau!yau dinma da kyal na shaidaki tsabar lalacewar da kikayi...zaki iya kama gabanki tunkan dare yayi maki."Lallai kam! dama tabaki Mardiyyah har yanzun baki ladabtuba,da kike gadarar ke matar Sarki Abduljalal ce ai kin makara da wannan gwara gawa dashi kinga baida wani anfani... balle wani banzan Sadauki wanda ma anmanta da rayuwar shi baki daya haka zaki karata a matsayin baiwa ke da yarki."ni nafi karfin intsaya ina cece ku ce dake dacan banyi ba,balle yanzun danasan darajar kaina data rayuwar iyalina,da kike ikirarin gwara gawa da mijina,ai cuta ba mutuwa ba,kuma zai warke da iznin Allah kuma zanci gaba da ansa sunan yar Sarki jikar Sarki matar Sarki uwar Sarki kuma kakar Sarki, kinga ko nafiki daraja nesa ba kusa ba,sannan awajen ku ne labarin Sadauki ya kau....saidai kisani kullun sai bayin Burhaan da sauran mutanan kirki sunyi masa addu'a saboda kullin zuciyoyin su cike suke da began jajircetacce kuma Jarumin nan dake saka zukatan azzalumai razana a duk lokacin da aka ambaci sunan sa sai tsoro da fargaba ya cika zukatan su,yayin da talakawa suke kasancewa cikin nishadi da annashuwa kuncin dake cikin zuciyoyin su na wankewa wannan ba kowa ba ne sai Muhammad Abduljalal Muhammad Sarkin Burhaan wanda gadon karagar mulkin Burhaan ke jiran shi cikeda bege....hmm ni nafi karfin ki,Masa'uda."Dafe kanta tayi da sauri ji take kamar kwakwalwar ta zata tarwatsw zuciyar ta kamar zata kufto daga kirjinta ba kadan maganganun ta suke neman haukatata ba,baya baya tayi zata kife kasa da sauri Talatu ta tareta ita kanta duk jikinta yai sanyi likis karfin hali kawai tayu tace."Ni kike gayawa magana son ranki sai nayi maganin kidani kike zancen.....karki damu Mardiyyah zaki ga abinda zan maki a halin yanzun batake nike ba."hmmm ina jiranki ni har akwai abinda zaki iya yiman wanda Allah baiyi man ba?ba abinda ban gani ba na rayuwa! indai kece ina sauraran duk wani makircin ki a tafin hannuna yake kuma narigaki nace Allah"kifadi son ranki zamu gauraya"ke Masa'uda kama gabanki tunkan dare yayi maki"zantafi dan ba nan kadai nazo ba amma ki saurari sako na"damuwarki ce,sakarai marar hankali."Har ta juya zata tafi ta dafa kafadar ta,a kufule Masa'uda ta juya."kunyi sake Wan zaki ya girma ku jira saka makonll ku bada jimawa ba."dariyar shakiyanci gimbiya Mardiyah ta kece da ita hakan saida yai sanadiyar bugun zuciyar gimbiya Masa'uda rasa abin cewa tayi,guiwa sage ta tafi kamar tayi kuka taga ba abinda ya sauya ga kishiyar tata maimakon tayi sanyi sai takara ke kashewa bata tsoron kowa domin kwayar idanunta sun shida hakan.
harta isa sashen maza bata kula ta iso saida Talatu ta hankantar sa ita sannan tasa wani babban mai kula da sashen, yakaita wajen bawanta Yautai koda ta isa yana ganin ta take yafara murna kamar wanda aka ba kyautar hajji,sawa tayi aka fiddo shi suka samu waje suka zauna ta fara yimashi magana da ido."barka da zuwa uwar dakina"yawwa Yautai ina sakona."zai magana kenan yaga Hamza, tsaye akan su tunda aka ga Masa'uda ta shigo gidan kaso akafada mashi, hannuwan sa hade a kirjin sa su kawai yake kallo da ido yautai yai mata nuni amma taki waigawa dan tagane Hamza ne."Allah yataimakeki danaje kasuwar ban same shi ba hakan yasa nadawo,ina shigowa sai sarkin kofa ya tareni sannna Sarkin horo ya tafi kiran mai girma Hamza,dana duka wajen wani ganye mai duhu banfi minti biyar ba saiga Darwami ya kama ni yakaini gaban fa'da daga nan aka gurfanar dani a nan wajen Allah yakara maki daukaka, harda taro da sile duk an kara mani dasu,ina maki fatan nasara uwar dakina, sannan kada kajarki ta rinjaye ki ki manta da ragamar ki cikin wani hali....."tsawar da Hamza ya doka masu ne yasa su tashi,murmushi kawai tayima Yautai sannan tace."shikenan zaka iya komawa inatareda jikkata duk rintsi duk wuya sannan akalata na tare dani ka kwanar da hankalin ka."godiya nike uwar dakina,Allah yakara maki girma da daukaka."dan danan Hamza yasa aka kara garkame Yautai saida yasha duka sannan. kallan bacemin dagani tunkan na wulakan taki a bainar jama'a ya aikama gimbiya Masa'uda,yayin da itama take masa kallan kayi kadan.... sannan ta juya tacigaba da tafiya Cikeda izzah gamida kasaita harta fita ranta fas tasamu labari mai dadi,haka ta koma tana jiran dare yayi kafin su dauko sakon su.
______________
Tafidah ya iso kasar damagaram ba inda ya sauka sai cikin katafaran gidan su Shattimah koda mai gadi ya ganshi ba karamar murna yayi ba,da sauri ya dauki kayan Tafidah ya kai mashi har cikin gida yana mashi maraba da zuwa a cikin katan daki ya zauna hadiman gidan suka dinga kawo gaisuwar su ga Tafidah.
yar aikin gidan ce keta dauko kulolin abinci tana ajewa a saman wani katan kafat da kawatu da taein kilissai masu ban shia'awa da birgewa tana ganin Tafidah itama da saurin ta tazo ta gaishe shi sai murna takeyi ya ansa cikin farin ciki da sauri taje ta fada Hajia Mansura tayi babban bako."wanene Lami."? "Ranki shidade gani da ido ya kori ji Allah yataimake ki."batare da bata lokaci ba Hajia Mansura tana shigowa falon idanunta sukayi tozali Tafidah wani irin farin ciki ta lullube cikeda bage da tarin jin dadi ta rufesu da sauri suka rungume juna sai jin dadi sukeyi kowa da kalar farin cikin da yake ji a cikin zuciyoyin su"Mukhtar ashe da rabon zan kara ganinka?nayi kewar ka da'na."Kidaina kuka Umma nayi kewar ki."kama hannunsa tayi suka zauna tace."ko bakace komai ba da angan ka ansan kana cikin damuwa ka daina damun kanka."Umma narasa yanda zanyi na cire kaina cikin damuwa amma nakasa,kullun cikin zullumi da tunanin nike kwana,idan na tuna halin da yan uwana suke ciki"haba Mukhtar ka daina damuwa Allah natare dasu a duk halin da zasu kasance,komai zaizo cikin sauki da izinin Allah... muje ka shirya kaci abinci."har daki Hajia Mansura ta raka Tafidah masu aiki suka aje mashi kaya sannan ta fito.
saida gaban shi ya fadi daya shigo dakin abubuwa da dama yake tunawa amna rayuwar su,hakanan yaji ranshi ya bashi Shattimah ya dawo gida kanshin turaren da dakin ya kama kadai ya bashi tabbacin hakan,tashi yayi ya shiga wanka.
"Nikan Lami har yanzun yaran nan basu dawo ba?ga Mukhtar ya iso ba kowa a gida sun maida hawan dokin nan kamar ibada haba."Hajia ai kinsan haka suke amma yanzun zasu dawo."Allah kyauta har yanzun Asma'u bata tashi ba."Eh Hajia saidai Ahmad shima yaba wajen Indo."ai shikenan." shiryawa yayi cikin wani yadi mai ruwan madara bakaramin karbar sa yayi sosai yai masa kyau turare yadan shafa arabian perfumes yana gama kimtsawa ya koma saman gado ya kwanta daman duk ya gaji ji yake baki daya jikin shi kamar ba nashi ba.
tana tashi wanka kawai tayi sannan tayi sallah tana gamawa ta shiryawa sannan ta wuce dakin Umma isketa tayi zata fito gaishe ta tayi."yawwa ya'ta anta shi."eh Umma."riko hannun ta Umma tayi suka fito falo."ya'ta yau kinsha bacci ya kike jin jikin ki? "Bakomai, kawai kasala nikeji amman yanzun naji dadin jikina."sannu."inda suke cikin abinci suka shiga shiryawa.
Gajiya da kwanciya yayi ya tashi ya zauna saman gadon ya dauki alqurani yafara karantawa cikin sanyin murya yajima yana ta karatunsa yana kara samun natsuwa cikin ruhinsa. Tunda ya doso wajen yake jiyo karatun alqur'ani na tashi a hankali muryar datayi sanadiyar bugun zuciyar shi yayin da yaji gaban shi Na faduwa, sanyin kamshin turaren daya tsaya masa cikin kwakwalwar sa ya fara sunturi cikin hancinsa kara saurin tafiyar sa yayi saboda ransa da gangar jikinsa yabasa ba mai irin wannan kamshin sai Tafeedah saidai yana kokon tan hakan duk dayasan komai jimawa zaizo kodan ya nemi labarin su duk tako daya da zaiyi na kusanci da dakin haka yake kara jin sautina karatun alquranin jikinsa na rawa yasa hannu ya bude dakin idanunsa sukayi arba da Tafeedah baki daya numfashin shi ya tsaya cak na wucin gadi tsabar mamaki,shi kanshi Tafeedan yanajin anshigo dakin yasan aminin nasa ya dawo,a hankali ya dago kanshi yayi ido hudu da Shattimah wanda ya gaza kwakwaran motsi tsabar mamaki,wani irin sanyayen murmushi suka sakarma junan su mai narkar da zuciya da sauri Tafeedah ya aje quranin ya mike yana nuna Shattimah ya kasa ko magana tsabar farin cikin daya lullube zukatan su ba abinda keyi sai hawayen farin ciki da sauri cikeda garaje suka rungume junan sy sai kuka sukeyi kamar wa'anda aka aiko ma sakon mutuwa,sun kusa minti biyar a rungume da junansu kowa najin yanda kirjin dan uwa shi ke bugawa haka hajia Mansura ta shigo dakin ta iske su sunata kuka kamar me, tsayawa tayi tana mamakin kallar kaunar da sukema junan su, magana tayi masu amman ba mai jinta a cikin su har saida ta shigo sannan ta tabasu sannan suka saki juna, saman gado Tafeedah ya zauna,ya rasa mi yakeji Hajia ta zauna ta riko hannayen su tace.


*Yar Mutan Kankiac'þ*

*SADAUKIN BURHAAN*
_(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_
A Kingdom Story=ØQÜ

*NA*
*JAMEELA JAMEEY*
_(Ya'r Mutan Kankia)_

*BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM*

_SHAFIN KYAUTA_

BABI NA SHA TAKWAS

Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira Wari Ukku(300)Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello,shaidar biyanki ta wannan layin 08160508316.


_ZAIRANA_

Fadila tagama hada kayan uwar dakin ta tsaf a cikin jikka,itama ta samu wata karamar jikka tasaka kayanta,bata jima da gama kimtsa kayan su ba sai ga gimbiya Zubaina ta fito daga wanka da sauri Fadila ta isa wajenta ta zube saman gwiwar ta tafara tayata shiryawa."Allah yataimaki gimbiya mu kadai ake jira."masharci ta dauka ta fara sharce mata dogon gashin ta a hankali."dawa dawa kika ga za'a tafi."Allah yakara maki lafiya,harda Umar duk nagani sai kuma uwar bayi."daure mata dogon gashinta tayi da ribom sannan tace."yayi kyau."a hankali gimbiya Zubaina ta mike ta dauki kayan su na al'ada ta saka kana ganin ta zakasan ita din cikakkar buzuwa ce kayan sunyi bala'in yimata kyau kuma sun karbi fatar ta sosai,jar alqabba

Please Login or Register in order to submit comment