Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

LOKACINE S5 Na Yar Mutan Kankia



_*LOKACINE⏱️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_



*Alhamdulillah,Allah abin godiya mun gode maka da kasake hadamu a karo na biyar a cikin labarin nan mai farin jini da darasi fadakarwa,nishadantarwa,wa'azantarwa harma da tunatarwa.Ya Allah kabamu ikon anfani da darussan dake cikin wannan labari kayafe mana kuraren da zamu aiwatar a ciki ameen.*

_Sallati da daukaka daraja da girma su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (SAW) da iyalan gidan sa da sahabbansa Allah kayi aminci agaresu ameen ya rabbil alameen._


```LOKACINE tabbas lokacine domin komai da kowa bai zanzuwa saita silar lokaci kuma komai da nashi lokacin gashi Allah ya saka haɗamu a cikin labarin Lokacine wanda yake kunshe da abubuwa kala kala,labarin AMINA CARANCI.```

*Masoya wannan kuma da wane salon zaizo mana andaice lokacine ya wannan lokacin yake muje zuwa💕*


_The writer of_
*•Nana Jawaheer*
*•Gimbiya Hakima*
*•Izzah ko Mulki*
*•A gidan haya*
*•Sadaukin Burhaan*
*•Sanadin Link*
*•Barawone*
*•Sanadin Soyayyar Shan minti*
*•Bayima Ya'yane1&2*
*•Bansan inda sukeba Ahalin Yanzun*
*•Daukar Fansar Budurcina*

*•Banibace*
_And_
_Know_
*•Alqalami S1*
*•Bakin jinina yajaman S2*
*•Qaddarata S3*
*•Haka Allah Yaso S4*
*•Lokacine S5*


S5/E1&2


A duk lokacin dana dubi kaina saina kara godema Allah bisa ni'imomin dayai mani domin ba abinda ya gagare shi, shike wanzar da komai a lokacin dayaso kuma yaga dama naga rayuwa iri iri maidadi da marar dadi saidai komai ke faruwa dani yanada sila da *Alqalami* wanda yagama rubuta komai kuma Allah ya wanzar dashi akan kowane dan Adam.
Idan kaga alkhairi saika gode mashi domin ba kowa kafiba yabaka yana cikin Jarabawar ka,hakama idan kaga akasin haka karka dauka cewa *Bakin jinine* yasa hakan ya faru dakai kasa aranka yana cikin *Qaddara* kowa yana fuskantar tashi Qaddarar badan komai ba saboda *Haka Allah Yaso* kuma komai daren dadewa *Lokacine* saboda komai yana da Lokaci,kuma kullin muna cinye namu lokacin.
Saidai wannan Lokacin ko zan samu cikar burina? Allah masani!

_Ya Allah kacika mana burinkan mu na alkhairi kasa mucika da imani darajar fiyayyen halitta(SAW),ameen._

*Amina Caranci kenan wadda tashiga kalubale na rayuwa iri iri,Allah kabamu ikon amfani da lokacin mu a koda yaushe ameen ya rabbil alameen🙏🏻*



_CIGABAN LABARI_


Hankalina yai masifar tashi tunda naji Baba da Daddy suna maganar saka rana duk da banji takamaimen wace ranar ce ake magana akaiba,sanadiyar korani da Mama tayi tahau yimani fada bakyau labe hakan yasa nagaza samun kwanciyar hankali kwata kwata.

Shiga nayi dakina na bude wayar da Ya Taufiq yabani, na saka Sim dina akai na kunna inajin wani dadi na musamman duk da sabon sim din daya banine na saka.

Duk abinda nikeyi hankalina nakan Baba don insan insan mi suke tattaunawa da Alhaji Abdullatib saidai ba halin haka.


Har suka tashi tafiya Zainab ta shigo daki tace inje zan gaida da Ya Mutallib.
Jikina yai sanyi hakanan na tashi zuwa falorn Baba na iske shi zaune saidai kana mashi kallo daya kasan yana cikin damuwa zama nayi ina gaida shi.

"Inayini Ya Mutallib."
"Lafiya lau Amna ya bakunta.?"
Alhamdulillah."
Shiru ne ya karade falorn sai kuma naji yace.

"Amna daman ina neman wata alfarma agareki ko zan samu.?"
Ajiyar zuciya na sauke nace.
"Inajinka Allah yabani ikonyi."
"Ameen,Kamar yanda kika sani nakamu da sonki tun ranar dana fara daura idona akan ki, kisani har gobe insonki,saidai ina fatan zaki kuma karbar soyayyata a wannan lokacin,inasan in kasance dake akoda yaushe Amina."

Hakanan nasamu kaina dayima Ya Mutallib wani irin kallo wanda narasa gane dalilin yimashi shi,saidai banji araina zan iya karbar soyayyar wani a halin da nike ciki inba Ya Taufiq ba akanmi Ya Mutallib zaizo mani da wannan zancen taya zanfara gaya mashi abinda ke raina!

"Amna kiyi magana mana tunanin mi kikeyi."
Yai maganar cikeda damuwa.

Murmushi na kirkiro bisa fuskata narasa taya zan fara yima Ya Mutallib bayanin zabin raina musamman dana tuna irin alkhairan su agareni sai inji kunya da nauyin shi sun addabeni.

"To naji abinda kace saidai kayi hakuri banji zan iya baka wannan amsar a halin yanzun amma,insha Allah kabani lokaci sai muyi magana kaga yanzun ina bukatar hutu."

"Shikenan yanda kikace haka za'ayi kuma daman kina bujkatar hutu komai kenan ina sauraranki."
Insha Allah."
fita yayi ya,niko fesar da numfashi mai zafi nayi ina tunanin lamarin.

Tunda Ya Mutallib ya tafi nikejin kaina sai ahankali Allah yasani banji zan iya son shi koda na amince ma soyayyar shi ada saboda banda zabi kuma ga irin alkhairin da sukai mani wannan shine dalilina.

Watsar da tunanin shi nayi naci gaba da latsa wayata inajin annashuwa araina.

★★★★
Bayan kwana ukku Dada ce da Umaima sukazo gidan mu, dakin Mama suka shiga.
Basu jima da zama ba nima na shigo da sallama abakina amsa mani sukayi ba yabo ba fallasa,saidai wani kallan kasa kasa da Umaima ke aika mani ban wani damu da itaba dan nasan haushina takeji taga ta dalilina ankama masu uwa shiyasa ta kullace ni.

Wayata tahau ruri har zanbar dakin sanin mai kirana naji Dada tace inzauna zatayi magana dani daidai Mama ta fito daga bedroom dinta inaganin kiran Ya Taufiq ya tsinke domin ba wanda zai kirani sai shi tunda layin sabone.


Zama nayi nace,gani.
Maida kallan ta tayi kaina tace.
"Aminatu.?"
"Na'am."
nace da ita danna kosa inji mi zatace mani.

"Inasan innemi wata alfarma agareki inba damuwa.?"
Dagani har Mama kallan ta muke duk mamaki yagama cikamu.
"Allah yabani ikon yimiki Dada."
"Ameen daman hakuri nikeson baki akan abinda Hafsatu ta aikata maki bansan ki kulli yan uwanki,kinga ga Umaima nan duk ta shiga damuwa shiyasa natisota gaba domin kiyafe mata abubuwan da suka aikatamaki."
Cikin rauni Dada tayi maganar.

Kallan Dada kawai nike domin duk duniya ba abinda natsana kamar ai mani zancen bayana bansan komai da kowa nabarwa Allah komai.

"Aminatu kinyi shiru."
Tayi maganar cikeda da damuwa.
Still shirun nayi ina aikama Umaima wani irin kallo mai saka mutun nutsuwa,jiki mace tace.

"Anty Amina dan Allah kiyafe mana abunda mukai maki nida mahaifiya ta."
Yinayi kamar banjitaba saboda nagama tsanar kaf zuriyar Anty Hafsat a cikin zuciyata.
"Na rokeki kiyafe mana dan Allah Anty Amina."
tayi maganar a raunane idanin ta har sun sauya kala.
Sauke ajiyar zuciya nayi a hankali na kalleta nace.

"Kinci arzikin Dada Umaima kuma nayafe maki saboda Allah badan halin kiba."
"Nagode maki yar uwata Allah yasaka maki da alkhairi."
"Ameen."

Mikewa zanyi dan nakosa inkira Ya Taufiq naji,ta kuma cewa.
"banji kince kin yafema mahaifiyata ba."

Baki daya na juyo ina kallan ta daga bayan dana bata ji nike zuciya natafasa kamar rushi muryata na rarrabewa nace.

"Ke Umaima ba ruwanki a cikin wannan zancen kedai kije nayafe maki amman bazan yafema Anty ba har abada itada Mami da JJ bazan taba yafe masu ba,dan haka kitsaya iyakar ki."

Na ida maganar a fusace har jikina na rawa tsabar takaici da bacin rai.
"Aminatu kinsan abunda kike faɗa kuwa yar uwar tawa zakice baki yafe mawaba."

"Mama dan Allah kada kisaka baki cikin wannan maganar wlh koda nayafe mata ba har zuciyata ba, tayama zan fara yafe mata tun yanzun bayan duniya bata gama gasa mata aya a hannun ba,yar uwar ki daban Mama ni kuma daban yanda ta daukeni nima haka na dauketa dan Allah kiyi hakuri kada ki tursasani abinda banyi niyaba."

"Aminatu ni kike gayama wannan maganar dan kawai ranki ya baci."
Cikeda mamaki Mama tayi maganar.

"Narokeki Mama kiyi hakuri kawai kibar maganar nan wlh billahi bazan yafeba a wannan yanayin da nike ciki natsaneta ban kaunarta agaban idanun ki miye Anty Hafsat bata ce mani ba takirani da karuwa fasika,tace saina wulakanta na tozarta a idon duniya ta tsine mani albarka duk agaban idanun ki miyasa baki taba cemata ya'ta ba! saini danayi abu saikice yar uwarki! Naji amman nidai banda wata dangantaka da ita yanda bata sona bata kaunata nima banson ta ban kaunar ta,kuma bazan yafe mata ba."

Kuka ya kufce mani dandanan na kuma shiga cikin wani hali na daban.

"Kyaleta Hadiza ki mata uziri amman Aminatu bakison ki rama alkhairi daga sharri mi zai hana bazaki maida mata aniyar taba."?

"Aaa Dada kibari akwai lokacin da zan ramawa Anty Hafsat alkhairi akan sharrin da tai mani amman ba yanzun ba."

Abin mamaki mikewa tsaye Umaima tayi ranta ya gama baci tace.

"Kince bazaki yafema mahaifiyata ba ko"?
Kallan kaskanci nai mata bance da ita komai ba dan bata isa inbata wannan amsar ba.

"Kisani Aminatu daki yafema Umma da karki yafema Umma uwarsu daya uban su daya,nima tawa yafiyar da kikai mani,natake na tsine mata albarka kuma da kike maganar kin tsaneta angaya maki muma muna kaunar kine! Akanki mahaifiyata zatayi life prison kin dauka hakurin danazo baki na gaskia ne na tsaneki Aminatu ban kaunar ki kuma sai nasa kinyi nadama badai kin fito gidan yari ba ga iskar duniyar nan kishaketa son ranki yar iska dake."

Tas tas tas na dauke Umaima da kyawawan maruka har guda ukku har saida tafadi kasa duk ta gigice nace.

"Naci uwar ki Hafsat yar iska dan uban daya haifeki harkin isa kizo gidan ubana ki mani kuri."
A harzuke nayi maganae cikina har rawa yake,dukawa nayi na shako wuyanta tana zaune kasa na tsugunna gabanta nace.
"ke saka idanun ki sosai cikin nawa kuma ki bude kunnuwan ki kijini da kyau! Aminatu da kika sani shekaru bakwai da suka wuce ba ita bace a yanzun! Zan iya baddaki na badda banza na zauna da yan iska wa'anda suka fiki tasha basuci galaba akaina ba bareke da iskancin naki na dandine wlh Umaima kika kuskura kikace zaki gaya mani maganar banza akan waccen uwar taki saina illataki banza karamar marar kunya dan Allah kice tak!kiga yanda zan fasa maki baki da hanci yanzun nan."


Shiru tayi kamar ruwa ya cita sai faman shafa kunci kawai take tana kwalla banda Mama datai sakake tana kallona kamar ruwa yacinyeta nasan mamakina take yanda na zama marar kunya fitsararra batasan rayuwa bace ta maidani haka kuma komai yanada lokacin shi da ba yanzun bace.

Mikewa Umaima tayi daga zubewar da tayi tana girgiza kai gami da sosa kumatunta da shatin hannuna yai kwance laba laba tace.

"Kika mareni?."
Wani bakin ciki yakara turnike ni waini Umaima ke cewa na mareta,bansan sadda na cakumota ba na buga da kasa na daga hannuna zan sakar mata duka, Dada taci dununa Mama ta wankeni da mari tana janye Umaima.

Cikeda mamaki nike kallan Mama yanda raina ya bacin nan badan uwa na uwa ba wlh da ba wanda ya isa ya gwani dani da yatsa ban karya shiba musamman yanda tsumin gidan Yari bai sakeni ba sai a hankali.

"Dan ubanki agaban idanuna zakina wulakanta mani dangi,kina hauka anya kina cikin hankalin Aminatu."?

"Mama akan wadannan zaki mareni harda zagina abinda baki taba yimani ba a duniya, sai kan wannan Umaimar da uwarta wa'anda basu da buri saina suga bayana shikenan!."

Na gwadata da yatsana ma nuniya nace.
"Ke kuma kisani indai kere na yawo zabo ba wayo wata rana zamu hadu inke yar tasha ce, nafiki iskanci wlh Umaima saina gyara maki zama saidai in ban garin nan muzuba mugani.!"

Juyawa nayi zan tafi dan innace in tsaya tabbas bazan ga girman Mama dake wajen ba zan iya illata Umaima natsaneta tsana mafi muni da dukkan zuriyar su.

Cak natsaya jin hannun Dada cikin nawa ta rikeni.
Saidai ban juyoba kasancewar idanuna sun rine kamar rushi.

"Tabbas Aminatu nasan ancutar dake sosai kuma duk abinda kikayi banga laifin kiba,asalima ko nice abinda yafi hakan zanyi wlh bansan Umaima batayi tuban gaskia ba da ban rakota baki Hakuri ba sai gashi tinkan tafiya tai nisa ta gwada mani halayenta kiyi hakuri Aminatu.!"

Bansan na rungume Dada ba ina sauke ajiyar zuciya mai masifar zafi na hana kaina kuka gaban Umaima amman dole in matse matukar zanji sassauci ahankali saitin kunnenta nace.

"Dada kiyi hakuri kuma dan Allah kidaina shiga wannan rikicin kibarni dasu har yau basusan cewa annabi ya fakuba dole indawo dasu Umaima hayyacin su inba haka zansha wahalar su matuka dan Allah kiyafe mani Dada."

"Allah yai maki albarka na fahimce ki Aminatu"
"Ameen Dada ngd."


"Ai daman nasani can ba kaunar mu kikeba muda uwar mu a Kotu gaban bainar nasi kika tsine ma uwarmu dan baki samani albarka ba saimi Dada,da sannu sai nayi maganin duk wani makiyinmu."

Sake da baki Mama da Dada ke kallanta saidai ni banyi mamaki ba,murtuke fuskata nayi ba wasa ko kadan nace.

"Ke fita kibar gidan nan ko kuwa uwarki ta haifi wata maza kifita marar mutunci."
Nasa hannu na bankada ta tsakar gida natisa keyar ta ina jan wata wayar wuta tunkan in iso tasa na kare da gudu tafita tana gunguni.

"Sai nayi maganin ki tsinanna wlh saina jefaki cikin ukuba da jafa'i
kuma ta Allah bataku ba."
Abinda Umaima ke cewa kenan.

Komawa nayi Mama sai kwalla take kallan ta banba nayi daki gashi ko kukan na kasayi dan dole nafada toilet zan watsa ruwa,karar text najiyo fitowa nayi na dauki wayata ina dubawa naga Ya Taufiq ne yai mani message buɗewa nayi nafara karantawa....



_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Pls
❣️


_*LOKACINE⏱️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S5/E3&4



Ina budewa nafara karantawa.

*Amincin Allah ya tabbata agareki ma'abociyar kayu da kyawun ɗabi'a,Haba my Queen nakira baki picking mike faruwa i need to hear ur sweet voice pls i love u"*

Zama nayi bisa sofa ina sakin murmushi a fuskata fara replay dinshi nayi sai kuma nafasa na shiga toilet na watsa ruwa sannan na fito nazira doguwar riga pink sai nasamu sassaucin zafin da zuciya ta ke mani.

Kiran Ya Taufiq nayi saidai bai picking ba,aje wayar nayi ina mamakin yanda akai Umaima ta raina mani hankali.
Nayi zurfi a tunani ringing din wayana ya katse mani tunanin dana zurma dagawa nayi.

"Aminci Allah ya tabbata ga ma'abociya kyau da kyakkyawar zuciya barka da wannan lokacin abin alfaharina,,

Sanyi da aminci naji a cikin raina nace.
"Ya tabbata agaremu baki daya masoyina,dafatan kana cikin aminci."
"Alhmdullh lafiya nakiraki baki picking ba."?
"Ina wajen Dada tazo gida shine tace tana son tayi magana dani lokacin daka kira muna cikin magana da ita ne."

"Hope ba wata matsala."?
"Eh ba komai wai ta rako Umaima tabani hakuri."

"Okay yanada kyau hakam ai,saikiyi hakuri saboda yafiya abune mai kyau ga lada."
Insha Allah nace dan bansan yasan abinda mukayi da Umaima.
Fira mukaci gaba dayi mai dadi da saka nutsuwa.

"Minal."
Ya kira sunana cikin wata irin siga mai dadin sauraro.
"Na'am,, na amsa cikin sanyin murya.
"Ya kamata zuwa yanzun musan yanda zamu tunkari iyayen mu da maganar auren mu lokaci yayi daya kamata muyi aure Minal."

Sanyayyar ajiyar zuciya na sauke domin nima abinda ke cikin raina kenan taya zamuyi aure dan shi kadaine cikar burin duk wasu masoya a rayuwa.

"Hakane Ya Taufiq kana ganin Abba bazai kuma bamu matsala ba."?
"Aaa ba wani matsala Minal daman Mami ce ke zuga shi da makirci yanzun an rasa inda take kinga cikin sauki da kwanciyar hankali zamu mallaki junan mu,kuma zamu samu albarkar iyayen mu."

Dan rufe idanuna nayi inajin kalaman shi cikin kunnuwana sannan na budesu a hankali nace.
"Alhmadulillah Allah ya ida cika mana burikan mu."
Ameen ya rabbil alameen."
"My Queen ya maganar aikin ki zaki koma ne."?
"Aaa nadaiyi report,dai almost 7yrs kaga wani process dinne daban sannan zan aje."

"Allah yasa haka yafi zama alkhairi ni daman bansan matata tayi aikin gwamnati nafiso kullin injita kusa dani musamu kwanciyar hankali."

"Uhmm dafa ina shirin neman wani ya za'ayi."?
Cikim sifar zolaya nayi maganar dan inji mi zaice.
"No pls ki manta kawai nima daman na aje aiki kinga sai ki zama MD dina ta company na shikenan sai muyi zaman kanmu,yanda zamuba ya'yan mu kulawa ta musamman ko hakan bai maki dadi ba."

Murmushi nayi inajin dadi araina.
"Yai mani mana amman sai inji wanibi zuciya ta karye Ya Taufiq."

"Akani mi kenan."?
"Sai inga kamar zamu kara fuskantar bazarana da matsaloli irin na shekarun baya sai inji kamar banda sa'a."

Nayi maganar inajin kwalla masu dumi suna shido mani a saman fuskata,dan banji zan iya daukar qaddarar rabuwa da Ya Taufiq a karo na biyu a rayuwata.
Gyaran murya naji yayi cikin sanyayyar muryar shi yace.

"Kidaina damuwar kanki Aminatu kuma kisa aranki lokaci yazo da zamu mallaki junan mu daman Qaddara ce ta rabamu gashi yanzun tasake hadamu wai bakiji aranki dan junan mu Allah ya halaccimu ba, ki duba kiga abubuwa da yawa sun faru damu har mun cire rai da sake haduwa kamar haka sai gashi Allah ya sake hadamu baki ganin akwai rabo mai karfi a tsakanin mu."?

Goge kwallan idanuna nayi inajin kwarin guiwa dajin dadin kalaman Ya Taufiq nace.
"Inafatan hakan ta kasance masoyina zanyi alfahari da hakan."

"Toh inko har hakane kisa aranki Lokacine kuma Allah zai gwada mana wannan lokacin kinji tawan."
"Allah yasa my nawan ina kaunarka."
Murmushi yayi tareda sauke ajiyar zuciya sai kuma yace.
"My life,Amma kun fasa komawa Anka ko zaku koma."?

"Zamu koma next week bansan abinda yasa Baba ya daga tafiyar ba."
"Allah yakaimu saidai naso ace Baba ya hakura kun zaman ku caranci tunda komai ya wuce."

"Nima bansan barin garin nan nasaba da shi,danma idan na tuna ba Husnata sainaji komai ya kwance mani duk narasa hope dina,,

"Kidaina damuwa insha Allah aljanna itace makoma ga Asma'u Allah yaimata rahama,,
"Ameen ya rabbi."
Nace a sanyaye.

"Babyna bari inje sallah anjima zamuyi waya akwai labarin da zanbaki mai dadin gaske,,

"Am waiting my hope Allah yakaimu lafiya kaimana addu'a."
"Insha Allah my Queen take care,,

Kashe wayar yayi hakanan na kara samun wani irin nishadi dajin dadi sai smile nike duk na manta da wata damuwa araina ina fatan Allah cika mana burin mu na alkhairi.

"Antyn Aminatu kizo Baba na kiranki yana falorn shi."
Cewar Jidda.
Mikewa nayi nakama hannun ta muka tafi falorn Baba dashi da Mama na taddasu sai Ahmad da shigowar shi kenan kusan atare muka zauna dashi gaidasu mukayi suka amsa ba yabo ba fallasa.

"Mamana."
Dago kaina nayi na kalli mahaifina nace.
"Na'am."
"Inasan kibani aron hankalin ki kiji abinda zance maki,kuma kiyi tunani mai kyau akai."
"Toh Baba insha Allah."

"Kinga dai shekaru sunja abubuwa da dama sun faru wanda bamu fatan Allah yasake maimaita manasu kuma muna rokon Allah ya gafarta mana kurakuren da muka tabka abaya."
"Ameen ya rabbi."
Muka amsa baki ɗayan mu.
Cigaba dacewa yayi.
"Yanada kyau kitsaya ki nutsu da kyau ki zabi abokin rayuwar ki,kiyi aure domin kuwa dukkan iyaye basu da buri daya wuce suga ya'yan su a dakunan mazajen su,nima zanso hakan Aminatu,kinga shekarunki sunja da ace kinyi aure tuni da yanzun akalla kin haifafa,to lokaci yayi kema da zaki zama uwa ga wasu kibada tarbiya ingantatta dan haka kije kiyi tunani kuma bawai nace cikin gaggawaba aa ki nutsu sosai innace natsuwa ina nufin ki cire son kowa da komai kiyi istihara zabin Allah duk wanda kikaji kin nustu dashi shine alkhairin ki ya'ta."

Tunda mahaifina yafara yimani wannan maganar sai naji zuciya ta takare Ya Taufiq shi kawai nikeji kuma nike gani a zuciyata inaji shine alkhairina taya zan gaya mashi shine zabina tsoro nike karya ki amincewa alhalin shine rayuwata kuma shine farin cikina kukan zuci nike bansan kwalla na shido mani abisa fuskata jinayi Ahmad yana share mani kwallana.

"Aminatu kidaina kukannan kiyi hakuri nasan dole zakiyi hawaye musamman idan kika tuna bayanki amman kiyi hakuri kisa aranki duk abubuwan da sukaita faruwa dake Qaddarar kice kuma komai yanada lokacin shi kinji Mamana."

"Toh Baba nagode Allah yakara girma da arziki insha Allah zanyi tunani."
Masha Allah."

"Sannan nadawo nasamu case tsakanin ki da Umaima,banji dadiba kiyi hakuri kuma ki dage da tsayuwar dare kina gayama Allah kukan ki ba abinda wani mahaluki zai maki sai wanda Allah ya hukunta akanki shine mai kowa mai komai kuma zai maki gata,daga yau bance ki kuma biyeta Umaima ba kinji."

"Naji Baba insha Allah zan kiyaye."
"Allah yasa yakamata ki shirya Ahmad yakaiki kije kasuwa kisai kaya kikai dinki ranar saturday zamu koma ANKA."

"To,amman Baba miyasa tunda komai ya wuce bazamu zauna nan dinba."?

"Aaa Mamana bansan inma mutanen da suka rungumeni butulci,kada kimanta a garin nan aka haifeni bansan kowaba saisu dayawan su danginane na jini amman dana fada musiba suka jugeni suke zagina suna tsinata dani da zuriya ta,fita waje saida ya gagareni nasha ciwo ga tarin bakin ciki dayai mani kanta a zuciya ta Allah yasa inada nisan kwana Aminatu da yanzun sunan ki marainiya kuma da kece zaki zama jigo ga kannenki kece katanga agaresu gashi Qaddara tafada maki Aminatu,na shiga tashin hankali marar misaltuwa narasa komai domin rashin ki yafi mani komai muni,sai nikeji inama mutuwa kikayi akan rayuwar da kika tsinci kanki a ciki hakan ya jefamu tashin hankali da nadama har suka fara neman rayuwar dan uwanki mi kike zato inna zauna nan dole inaji inagani na rabu da kowa nawa na koma inda basan kowa ba sai Allah."

Hawaye nikeyi wanda dukkan mu kowa kwallan yake banda Baba saidai idanun shi sun sauya launi nace.
"Hakane Baba amman sun nemi afuwar ka sai mu zauna kaga munsaba dasu."

"Aaa Aminatu taya kike zatan mutanen da suka maidani ɗa zasuji idan sukaga na gujesu karfa ki manta nifa Yusuf barene a cikin su amman suka 'yantani suka maidani a cikin su suka saida mani muhalli basu taba kyarata ba ko hantarata suka rungume suna jajanta mani halin dana shiga sun mini kara lokacin da kike tsaka mai wuya har zuwa sunyi Kotu duk dan su nunamin cewa sudin yan uwana ne,kina zatan zanki wadannan mutanen dan kawai yanzun dangina sunyi nadama sun dawo dani a cikin su,gaskia bazan iya butulcewa Alhaji Tijjani Bungudu ba zamu koma Anka da zama har abada saidai idan hidimar bikin ki ya tashi zan dawo cikin dangina a daura maki aure ko bikin sallah duk zan dinga dawowa gida cikin dangina shima sallar ta layya kawai banda karamar sallah can zan dinga yinta wannan shi ne halacci Mamana."
Goge kwallan idanuna nayi domin na fahimci mahaifin nawa na rike hannun shi nace.

"Tabbas Baba hakan shine daidai kuma ya kamata mu zama cikin mutane masu yawan halacci da kara kodan mu,ansa sunan mu

Please Login or Register in order to submit comment