Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

GIDAN MATI
©BINGEL MITA & RUFAIDA OMAR
Hausaebooks
Shuraih Usman
http://shuraih.waphall.com


Buguzum-buguzum ta sanyo kai cikin gidan
tana wak'a.
"Ahayye iye nana..."
D'if ta dakata gami da sakin baki adalilin
abinda ta hango a tsakar gidannasu.
Maigidansu Mati a k'ofar d'akin kishiyarta
Abulle zaune su na hira da dariya. Ganinta
ya sanya Mati yin tsuru da idanu yayin da
ita kuwa Abulle ta washe baki, cike da
dabara ta fiddo takardar naman da ta 6oye
a bayanta ta warware ta d'auki tsoka d'ayan
da ya rage ta jefa a baki ta na tauna gami
da fad'in.
"Maigida kana burgeni, kana kawomin irin
wanda na ke so."
Mati ya watsamata kallon muguwar mace,
shaf a tunaninsa dagaske ta yarr da takardar
tsiren, ashe makirar abinda ta shiryamasa
kenan. Ya numfasa gami da share zufa ya na
duban Nene batare da ya ce uffan ba.
Nene wacce zuciyarta ta gama kaiwa bango
ta fisge mayafin kanta ta had'iye miyan da
ya taru a bakinta tsabar na ranta ya biya ta
ci d'amara ta hau tafa hannu.
"Allah na godemaKa da ka nunamin abinda
ke faruwa a bayan idona! Ashe daman cuta
ta ake yi ana dawowa idan bana nan? To yau
dubunku ta cika Mati, yau sai an bambance
tsakanin aya da tsak'uwa!"
Jin haka ya sanya Mati mik'ewa ya hau
fad'an k'arfin hali da borin kunya.
"Ke ya isa! Yimin shiru dak'ik'iya kawai! Kin
shigo gida ba sallama ba komai sai wak'en
banza sannan ba ki tsaya kin ji dalilin
dawowata ba yanzu kishi zai kaiki ya baro
ki!"
Kafin Nene ta samu bakin magana, Abulle
ta saki wata dariya irin ta wadanda duniya
ta yiwa dadi.
"Kai namiji, namiji akace buhun k'aya.
Sannunka munafuki, inace mun fi awanni
biyu tare? Duk dai abinda za'ayi sai dai a yi
don ba na tsoron kowace mai yanayin
kul6a, miji ne mun yi aurenmu na soyayya
muna zaune lafiya yana kawomin kayan
mak'ulashe koda kuwa ba kwana na ba, sai a
mutu!"
Da jin haka Nene ta zabura ta yi kanta ta na
faman surfa ruwan ashariya.
"Yau sai na nakasa ki tsohuwar bazawara
mai bin maza, saidai wannan tsohon gurgun
ya k'ara haifar wata."
Ai sai su ka shiga kokawa, Nene ta daddage
ta ba ta kyakkyawan cizo a mamanta wanda
ya ke fata ce kawai. Wani ihu Abulle ta saki
gami da fad'in.
"Kan uban can!" Ta cafki jan gashin kan
Nene mai kama da gemun ɗan Bunsuru ta
hau ja da k'arfi, ta kuwa shiga ihu har
zaninta na fad'uwa sai ga ta zirr babu ko
d'an bante. Mati ya tafi da gudu ya d'auki
zanin ya na kokarin suturceta ganin
magulmatan makwaftansu wato Gidan Delu
da Gidan Shafa har sun soma lek'e ta
Katanga.
"Menene haka? Ke Abulle don iyayenki
sakarta!"
Wani turi da Abulle ta yiwa Nene sai kuwa
ta jefata jikin Mati su ka yi kyakkyawan
zubewa a k'asa abinka da siririn mutum. Da
sauri Nene ta mik'e ta suturta jikinta ta na
huci.
"Shegiya mai kalar mayu zan yi maganinki a
gidannan, za ki san kin shigo gidan Nene."
Wani banzan harara Abulle ta watsamata
sa'ilin da ta ke gyara zaman rigarta.
"Yanzu aka fara tashin hankula a gidannan
muddin ba za ki fita a harkata ba. Mace ba
ta ajiye komai ba sai ta ci ta yasar da k'aton
kashi a masai! Gwara ni, tunda ko ba komai
na yi 6ari an ga shaida!"
Nene ba ta jira komai ba ta nufi wajen
girkinsu ta rarumo ta6arya ta taho a guje,
ai Abulle na ganin haka ta fad'a d'akinta, ga
shi ta kasa d'aga labulen kaban k'ofar d'akin
hakanan kawai ta turo kyauren.
Nene ta tsaya ta na huci ganin Mati ya sha
gabanta.
"Shegiya kai, ashe ke 'yar iskar k'arya ce, yo
ki tsaya mana idan ban nakastaki ba anan."
"Haba Nene, ya isa hakanan, muje daga ciki
ki ji."
Fad'in Mati hankali a tashe don shi har ya
rasa ma yanda zaiyi ga makwafta 'yan gulma
na kallo.
"Haba ke kuwa Nene, ki yi hakuri mana."
Fad'in Delu kenan cike sa tsegumi.
Wani banzan kallo Nene ta watsamata, sai
lokacin ta lura da tarin magulmatan
makwaftansu da ke lek'e.
"Kai! Allah Ya tsaremu da munafukai,
mutane ba su ajiye komai ba banda
munafunci da gulma, dadin abin dai mijina
bai ta6a jibgata ba kuma bai ta6a haikewa
wata ba."
Delu wacce tasan ita miji ke jibga ta ja tsaki
ta ce.
"Oho dai! Duk acikin so ne." Daganan ta bar
lek'en tare da yanmatan yaranta uku. Ita
Shafa salin alin ta sauka ba ta ce uffan ba,
to ina bakin magana tunda tasan da gaske
mijinta kwarto ne na a kwantanta.
Dakyar dai Mati ya kashe rigimar tare da
alk'awarin zai kawomata na ta k'unshin
tsiren. Abinka da kwad'ayyiya kamar
Asma'u a gari, ba musu ta hak'ura.
*** *** ***
Abulle ta ta6e baki.
Mati bai ko kula ba ya ci gaba da
maganarsa.
"Sanin kanki ne dai Inna ba ta damu da
zuwa k'auyen nan ba tunda Baban su Ladiyo
ya d'and'ana mata zaman birni, yanzu kuma
musamman don ni za ta zo ayi zumunci.
Don Allah Abulle, ke ce k'arama, ke ce
kuma ba ta sani ba, ki taimaka ku zauna
lafiya har ta tafi. Sannan inda hali inason ayi
wani abu."
"Menene shi?"
Ta fad'i da sauri.
Ya yi shiru sai kuma ya numfasa ya sassauta
murya.
"K'aryar ciki."
Gaba daya ta zaro idanu ta na dubansa. Ta
murza bajajjajen hancinta.
"Yi min gwari-gwari dai."
Ya hau bayani.
"Inna ta sanarmin cewa muddin ta tarar
kema ba ki da ciki to lallai za'a samu
matsala don kuwa sai na sake ki na yi wani
auren. Ni kuma kinsan dai ina sonki ina son
zama da ke, don.."
"Tsaya tsaya Mati, shi ke nan wannan abu
mai sauk'i ne zan yi, sai dai menene ribar?
Wace kyautar bajintar za ka samu bayan
hakan don nasan halinka, ba ka aikin
banza."
Ya yi 'yar dariya ya shafi sumarsa.
"Kai kai Abu tawa ta kaina, kina da saurin
fahimta kam. To bari ki ji, akwai wata
tafkekiyar gona ta Inna da kuma gida da ta
ke bayar da haya ana biyanta balas duk
karshen wata, ba yanda ban yi ba akan ta
bani gonar ta k'i, to ta tabbatarmin za ta
bani har da k'arin gidan nan ya zama
mallakin jikanta."
Abulle ai sai ta hau tsallen murna da sakin
gud'a.
Mati ya hau rufemata baki a tsorace.
"Ke ki rufamin asiri kada waccan ta ji."
Tunanowa da Nene da ta yi ne yasa ta
saurin sai ta kanta.
FIKRA WRITERS ASSOCIATION
*GIDAN MATI*
©ƁINGEL FULANI & RUFAIDA OMAR
Daga waje kuwa Nene na jin haka sai ta yi
wuf ta fito daga maɓoyarta, can baya take
zagayawa ta hau kan ɗan dutse tana kasa
kunne a ƙaramar tagar ɗakin Abulle. ta na
yi tana leƙa bayanta ko wani zai taho
wucewa kasancewar daga nan ana hangen
waje a dalilin gajartar katangar.
. Ɗakinta ta shige da saurinta, jiki na
rawa ta hau sauke kwallayenta tana faɗin;
"Idan sammako ku kayo, ni asubanci na yi."
Ta fiddo wani maganin gargajiya wanda
tayi mugun tsanar warinsa, sannan ta mai
da kayan ta afka garin kusan rabi a baki. Kan
ka ce mene wannan cikinta ya murɗa ga
yunƙurin amai da ta soma. Ai a guje ta fito
ta isa gaban makwararar ruwa ta hau sheƙa
aman iyakar ƙarfinta tana nishi yanda ta
tabbatar za su tsinkaya...
"Ni fa kamar kakari nake ji." Cewar Mati
yana kallon Abule.
"Kai fa daɗi na da kai har yanzu baka
bambance kukan Jakinka dana Akuyar
Delu."
"To idan ma itan ce kinyi zaune salon tamin
ta'adin da ta saba?"
Ya faɗa yana mai mi'kewa tsaye, itama da
sauri ta mi'ke tana mai rufa masa baya.
Ita ɗin ma ta wajen jin tahowarsu ya
sata zubewa gefen kwatamin tana mai ri'ke
cikinta da faɗin "Wayyo! Mati..."
Da gudansa ya 'kara so wajen yana mai
janyeta gefe.
"Ikon Allah! Nene ashe ke ce. Sannu me
kika ci ne haka?"
"Ba komai tun safe nake jin tashin zuciya da
rashin jin daɗi."
Ta faɗa da ƙyar tana sauke numfashi.
"A'a irin wannan ciwon ai ba na shiru ba
ne Nene, karki manta da haka Sahura ta
mutu da irin shirun nan."
"To Mati ana ta kai wa yake ta larura?
Taimaka min zakai Abule ta dubomin 'Yar
Magaji, ji nake kamar ana daka yaji a
kirjina."
"Huu'umm!" Abule ta faɗa tana tafa hannu.
"Ai wallahi da aiken kishiya gwamma na
jibgi Uwar miji. Kai ni ban ma yarda da
wannan ciwon ba. Saboda Allah Mati baka ji
warin tazargaje ba?"
Ta faɗa tana mai ɗaɗɗaga hanci sama.
"Me kike nufi ne? Kinga Abule ban san
fitina, ya mutum na halin ciwo kina kawo
shashanci. Idan na isa dake to maza ki je ki
dubomin 'Yar Magaji."
. Mintuna kaɗan Abule ta dawo da 'Yar
Magaji biye da ita ta rataya wata tutturna
jaka me kama da ta wazirin Sarkin kutare.
Kallo ɗaya tama Nene maƙaryaciyar
zuciyarta ta kisa mata menene,
dan haka ta kalli Mati da murmushi.
"Malam ai ba wata larura ba ce mai girma,
ƙaruwa ce zaku samu, a taƙaice dai Nene
ciki gare ta har na tsawon wata biyu."
"Kan babban bala'in can! Alkur'an
wannan ƙarya ce."
Abule ta faɗi tana mai buga tsalle gefe,
kafin kuma ta yi ɓarin da Nene ke kwance.
"Ke Nene ki ji tsoron Allah, ina ce ba
shekaranjiyar nan muka gama rikici kan
tsumma na da kika yaga kikai kunzugu da
shi ba?"
"Wayyo Ni Abule! Yau na ga abinda yafi
'karfina, wai cikin ma har kinsan ya yi wata
biyu sai ka ce wacce kika haɗa iri da Mayu.
ke kam 'Yar Magaji anyi tantiriyar
ma'karyaci wallahi. Matar da ake raɗe-
raɗen Aljanu sun sace mata mahaifar ne ke
da ciki?"
"Ke! Ke! Abu kin cika mana kunne da
shegen karaɗi. Ki tsayamana abu abin a
sannu idan ma ƙaryar ce ai 'Yar Magaji za ta
faɗi.
"Wane irin bi-sannu Mati? Ai fa magana ta
riga ta ƙare, Nene dai ciki gare ta, maganar
ganin jini kuma wanann a bayyane yake, ko
Magaji ka tambaya zai idar maka wannan
zance. Lalle ne akwai Matan dake jini da
ciki. "
"Ke kuma Abule da kika haɗa Ni da
Maita ina jin dai tsohonki shi ne Bazawari
na? Dan haka bushiya dai ba zata wa
Kunkuru gorin ƙafa ba , ko zaki mutu dai
Nene ciki gare ta na wata biyu."
"Kai kuma yanzu ya rage naka sai ka dinga
mata abinda take so. Ni kaga tafiya ta."
Muna zuwa...*GIDAN MATI*
©BINGYEL FULANI & RUFAIDA OMAR
"To ai sai ki kauce daga samanmu tunda
dai shegen baƙin cikinki ya jawo kinji
abinda Tsohonki ke aikatawa a waje."
Mati ya faɗi yana hararar Abule da
tayi tsaye hannu bisa ƙugu tana jinjina
maganar 'Yar Magaji.
"Oho dai, daɗin ta Bazawari aka ce
ba Ɓarawon Jakai ba."
Ta faɗa tana hararar Nene dake yatsine-
yatsine.
.
"Kyale ta kinji Nene uwargidan Mati, muje
na raka ki ɗakI ki kwanta, daga yau ko
tsinke ban yarda kin ɗage a gidan nan ba,
wanda ba zai iya gani ba yayi zuciya mu gani
a ƙasa." Ya faɗa cike da lallami.
Ita ɗinma miƙewa tayi cike da
kwarkwasa har da riƙe rigar Mati. Gab da
zata ɗaga labulen kabar ta ne ta waigo ta
kalli Abule fuskarta ɗauke da murmushin
kaɗan kika gani.
Dogon tsaki itama taja tana hararar ɗakin
bayan shigewarsu. "Wai Kura ce ta samu
damar miƙe ƙafa, ayi dai mu gani, muna
nan za ka zo kana min 'yar murya. Har
yaushe ma akai daren?" Jin shiru ba su
amsata ba sai tashin dariyarsu da take ji ne
ya sata juyawa a fusace zuwa na ta ɗakin.
Kwana biyu gidan shiru daga uhumm
sai hu'umm wai uwargulma tayi cikin shege.
Duk san Abule na ta gane gaskiyar cikin
Nene abun yaƙi yiwuwa. Sai ma barinta da
takaicin arba da ledar Burodi da Tsire da
take yi kullum safiya. Idan ma ta yi dakon
hana ido barci dan a kasa da ita Mati baya
shigowa gidan sai dare ya raba, kafin ta
gama barcinta ya kaɗa na sa Jakan yayi gaba
tsabar rashin gaskiya.
Sauri take ta isa gida, dan ta fara
gwada maganin saka laulayin da Gwaggonta
ta bata ta dinga shansa duk dare, bayan ta
sanar mata da abinda ke faruwa a gidansu.
Ta tsinkayi muryar Delu na kwaɗa mata
kira.
Kamar ba za ta tsaya ba, sai dai taja tunga
ganin Delun harda ɗan gudunta.
"Uhm! Tunda na taho nake Addu'ar
Allah ya sa na ganki, dan kuwa ba za ai
wannnn cin Amanar a gaba na ba."
Gabaɗaya ta mai da hankalinta kanta
"Me ya faru Delu? Na sanki baki maganar
banza."
"Ke dai Allah ya raba mu da Miji mai
ɗabi'ar hankaka. Mati na gani yanzun nan
gun 'Yarbaiwa mai Fara ya sai har ta Naira
Hansin wai Uwargida ke kwaɗayinta, baki
ganta ba fal ledar..."
"Fara fa kika ce? Farar da tunkan muyi aure
yake min alƙawarin cinta?" Ta tari
numfashinta.
"Idan ƙarya nake miki wannan zance tsawar
bana ta sauka gonar Malam Alkur'an."
"A'a me na jan masifa? Zai yi fin haka ko
dan ya nunan shi Namiji ne kwandon zawo,
barni da shi, yau ko zai mutu ba za ta ci
Farar nan ita kaɗai ba. Ke har ke sai kin
ɗanɗana, na gode miki Delu, bari na ƙarasa
gidan.
Da sallamarta gidan ta yi jifa da
kallabin kanta gefe, luma yatsunta ta yi
cikin gashinta ta fara wargaza shi, kan kace
mene wannan ta tada hankalin gashinta ya
yi tsaitsaye tamkar gemun Mahaukaci da ya
shekara ana jifansa. Nene dake gefe ana
ƙoƙarin sai ta kai, sai gani tayi Abule ta
zube tana wani nannaɗewa, doka ihun da
zata yi sai ga shigowar Mati yana mai da
aljihunsa baya. Ganin Nene jiki na ƙyama
ya sashi yin wurin Abule yana salallami.
"Karka ƙaraso! Kana ƙarasowa idan muka
fyauɗe ka sai ka dangana da Gyatumarka"
Yaji murya na gargaɗinsa kamar ta
Kuyangar Kutare.
Turus! Yayi ƙafafuwansa na rawa kafin kuma
ya zube ƙasa yana kallon yarda Abule ke
naɗewa bakinta na dilalar yawu.
"Kiyi haƙuri Abule wallahi bansan kina da
larura ba."
Ya faɗa kamar zai fashe da kuka.
Taja majina.
"Kai! Ka iya bakinka, wanann ba lalura ba ce,
kai ne ka kira mu da kanka da kake taɓa
mana Goɗiya kana sa ta kuka."
Ta faɗa tana zare manyan jajayen
idanuwanta.
"Ƙarya take min bantaɓa sa ta kuka ba,
Nene shaida."
"Munafuki menene wannan a aljihunka na
hagu?"
"Fa..fa ...fara ce."
"To wa ka siyo wa?"
"Abule mana, ita ce Amarya ta da bana iya
motsi sai da ita."
"To bawa waccar ta kawo farar nan
gabanmu, gargaɗin ƙarshe kuma ka kuskura
ka ƙara kawo ko Dusa ce ba ka haɗa da
Goɗiyarmu ba sai mun musanya mata
yaron cikin da take ɗauke dashi da
Kadangare."
"Ban..ban..gane ba..."
"Au! Dan fitsara ma baka San Goɗiyarmu na
da cikin ka ba?"
"Na sani, ku yi hakuri. Ke Nene miƙa musu
Farar mana."
Ya faɗa yana jefa mata kullin ledar dake ta
kyallin mai .
Abule ta kalla idonta kamar zai faɗo dan
tsoro, gani take kamar bakinta ma ya koma
gefe, dan haka ta Yi baya cikin hawaye.
"Ba zan iya ba Mati."
"To kuwa zan fita na barki da su, ki miƙa
musu ko za su tafi."
Ya faɗa da tsawa.
A ɗarare ta miƙa ledar gaban Abule dake
naɗe, a guje ta juya zuwa ɗakin ta ta lafe
bayan kaba tana hangen su.
Ƙatuwar Hamma Abule ta saki, kafin kuma
ta ɓingere gefe maƙale da ledar farar ta.
Akwai alamun Borin ya sauka.
*** **** ***
Muna zuwa
*GIDAN MATI*
©BINGEL FULANI & RUFAIDA OMAR
Assalamu Alaikum mutan gidan." Fad'in 'yar
doguwar dattijuwar kuma tsamurmura mai
sharɓa-sharɓan tsagu a gefen bakinta, bak'a
ce wuluk kamar d'anta Mati. Mati ne a gaba
d'auke da k'aramar akwatin kayanta, ita
kuwa tana biye da shi a baya.
Abule ta soma fitowa daga d'aki sai Nene
daga band'aki suka saki baki suna kallonta.
'Ikon Allah, wai na kwance ya fad'i.' Cewar
Abule kenan a k'asan ranta ganin shigar da
surukar ta su ta yi, wata k'aramar Atamfa
Super ce ajikinta an mata dinkin riga da
siket sai wani babban mayafi da ta yafa a
kafad'a ba rufin kai ba. Fuskarnan ta sha
farar hoda, ba'a gane wa sakamakon bakin
fatarta da ya ciza saidai kuma kana gani ka
rantse yanayin hunturu ne wanda ya yi
sanadin da fatar fuskar nata ya bushe ya yi
furu-furu, ga uban jan janbaki da ta lafta a
le66anta masu tudu.
A hankali Nene ta maida dubanta ga Abule,
akayi sa'a itama ta kalleta sai kuma suka
sauke ajiyar zuciya kafin kowaccensu ta
shiga rububin tarbarta da amsa sallamarta.
"Waalaikumussalam, lale maraba." Fad'in
Nene kenan ta karasa bakinta a washe ta
kar6i akwatin Inna, caraf itama Abule ta
sanya hannu da zummar kwacewa ta kai
nata d'akin.
"A'a menene haka? Yaushe akayi daren
kuma da har ace gari ya waye? Malama
sakarmin." Cewar Nene ta na k'ara jogana
akwatin a jikinta.
Dole Abule ta saki tana harararta ta karasa
wajen Inna cike da kissa ta ce.
"Maraba Inna."
Inna ta hau k'arewa Abule kallo, eh kam ta
yarda da rahoton da Aminiyarta Ladidi ta
kai mata game da Amarya d'an nata. Ta
tabbatar mata tafi Nene tsafta kuma ta ga
alama. Sai dai kuma ta kasa fahimtar me ya
ja Mati ga aurenta? Wannan abu a dunk'ule
haka?
"Yauwa sannunki kema."
Ta fad'i tana mai k'arasawa ta zauna a
saman tabarmar da aka shimfid'a. Nene za
ta yi ciki da kayanta ta yi saurin dakatar da
ita.
"A'a 'yarnan dakata."
Zani na kuncewa tana sake d'aurawa ta
karkata k'ugu ta tsaya gami da dire akwatin
tana jan majina.
"Na'am, to."
Inna ta yamutse fuska.
"Ai kuma sai dai wannan karon ki hak'ura
don a d'akin ita 'yar uwarta ki zan sauka. Na
gayamaki bana son kwana kan wannan
gadon naki mai warin hammatan wanzamai,
da kyar idan kin chanja wannan tsohon
zanin gadon wanda na gama yayinsa tun
jegon mijinki. Ba wa abokiyar zamanki
akwatin na ga na ta kamun ludayinta."
Ai sai Abule ta kece da dariya, kallon
banzan da Inna ta watsamata ne ya sanya ta
nutsuwa. Nene ta cika ta yi tam! Yau ita
Inna za ta ci wa fuska akan Abule? Lallai ya
dace ta zage damtse.
Tana numfarfashi ta zauna, Inna ta dubeta
sannan ta k'ara duban Mati.
"Wai ni Mati wacece me juna biyun a
matanka?"
Mati ya hau washe baki.
"Ai duka biyun ne."
Inna ta kwalalo idanu cike da mamaki tana
duban Nene, karshe ta sauke idanunta akan
Abule da ta zauna tana wani sussunne kai
ita a dole kunya. Sai kuma ta hau tafa
hannuwa da shewa.
Farin ciki ya cika su don a zatonsu ta yarda
suna da cikin. Sai dai ga Inna kuwa sam
zuciyarta ba ta amince Nene na da ciki ba,
shekaru nawa da aka yi ta rad'e-rad'in ba ta
da mahaifa, ai kuma ta saka ayar tambaya.
Dabara ta zo wa Inna.
"Yau na ga abin al'ajabi, to ai shikenan,
zama ya kamani a k'auyen nan duk da ba na
so, amma zan zauna har na ga 'ya'yanka
Mati."
Hanjin cikin Nene da Abule ya kad'a sai dai
kowaccensu ta yi fuska. Mati kuwa wani
dad'i ne ya mamaye zuciyarsa ganin burinsa
ya kusa cika.
Abule ke da girki ita ta shiga hidima da
Inna, Nene kuwa d'akinta ta fad'a tana
tunanin mafita nan gaba.
*** *** ***
Bayan kwanaki hud'u da zuwan Inna ana
zaman lafiya kowacce ta ciki na ciki. Karshe
kuma sai Mati ya tsuro da wuni a d'akin
Abule wai hira da Inna, haka za ta yi ta
tsinkayo dariyarsu.
Da abin ya isheta ta shirya ta nufi gidan
'Yar Magaji don neman mafita. Tana isa ta
zayyanemata komai, 'Yar Magaji ta buga
uban tsaki.
"Ke ce ai ki ka yi sake da ba ki mallake
Mati tun fari ba, yanzu da komai zai zo ma
ki da sauk'i."
Jin haka Nene ta gyara zama.
"To yanzu ya za'ayi."
'Yar Magaji ta d'an yi jim, sai kuma ta saki
dariya ta mik'e ta fad'a d'aka. Can sai ta
dawo d'auke da k'ulli ta mik'amata. Nene ta
hau jujjuyawa.
"Na menene?"
'Yar Magaji ta d'an murza hanci tsabar warin
da bakin Nene yake yi kamar na 'yan ga
ruwa.
"Kinga wannan, k'asar k'ark'ashin gadon
ma'auratan da suka tsufa tare ne suna
soyayya, matuk'ar kin yi turare da shi na
kwanaki uku Mati ya kusanceki to an gama."
Nene ta girgiza kai.
"Matsalar mun fi wata biyar bai nemeni ba,
ni kinsan na tsani a maisheni jaka."
Wani kallo 'Yar Magaji ta yi mata sai kuma
suka kwashe da dariya 'Yar Magaji na kauda
kai.
"Dad'ina da ke ba dai warin baki ba."
Nene ta muskuta tana shafa bakin.
"Um to ya na iya da abinda ya fi k'arfin
wuta?"
Ta6e baki 'Yar Magaji ta yi.
"Ke ki ka so, ni yanzu dai kinsan ina jiran
kaso na, makira ai ina shigowa daman na ga
yanayinki na gane makircinne ya motsa."
Nene ta dara.
Suka gama k'ulle-k'ullensu dai Nene ta
koma gida da zummar soma gabatar da
aiki.
*GIDAN MATI*
©BINGYEL FULANI & RUFAIDA OMAR
Inna ta d'aga hanci sama taja iska, sai
kuma ta furzar ta baki tana hararar
kwanukan da Nene ta aje gabanta.
"Uhm ni wai da mushe kikai miyar ne
Nene?"
"Me kika gani Inna?" Nene ta fad'a tana so
sa kai.
"A'a gani nayi tunda kika doso gurinnan ya
cika da tsami da k'arni tamkar wacce ke aiki
a kwata ko mutuware."
'Ai fa, komai na yi ban burge ba, to ai sai
dai ki mutu, aikin na Mati ne, mallaka kuma
tawa ce, sai shegen kinibibi da wani bakinta
kamar na ba'kar Akuya...' Ta faɗa da
gunguni
"Me kike cewa ne?"
"A'a cewa na yi Binta Sudan ne na balbala a
jikina saboda kiji ƙamshin."
"Ko kuma Binta Maliya ba? To wanann dai
ƙarni yake sai a sake lale, ki kwashe
kwanukan nan daga gabana, anjima zansa
Mati ya karbomin Abincin daga gidan Larai."
"Uhm gaba ta kaini, dama ke na tsamewa
kai da ƙafar kazar." Ta faɗa da 'kun'kuni
tana tattara kwanukan.
"Baki ji ba" Inna ta fad'a
"Ina ji Inna" Ta fad'a tana gabda barin
d'akin.
"Idan gyaran zaki yi ki fara gyara can cikin,
shi ne ko da kinsa turaren zamu ji dadinsa,
amman wanann in gayamiki gaskiya yau sai
an turaramin dakin nan da miski zan iya
zamansa. Yanzu haka sai na sha kanwa
sabida kumburin ciki."
"To masharranciya." Nene ta fadi a hankali
tana barin d'akin a fusace.
Abule dake maƙe a gefe tana sauraro ta
k'yak'yace da dariya tana juyawa Nene
mazaunai. Nene ta yi kwafa tana gyaɗa kai,
kafin kuma ta yi dakinta tana mai sauke
kaba.
Gab da Maghriba Abule na
tsakar gida tayi ɗaurin kirji, da zabira a
hannunta tana tsifar kai. Can daga k'ofa
kuma Nene ce zaune tana gyaran Tafasa
tana yi tana sakin habaici a waƙe.
"Munafuncin dodo dai mai shi yakan ci, yau
ba jumma'a ba idi ba, ba kuma kwanan
mutum ba ya d'au niyyar wanka harda tazar
kai na asara." Nene ta faɗi da karfi

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment